Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

barewa yana samata a tafin hannu tanaci.

Baba Zanje in kai wannan mutumin wani wuri yace fuska ba walwala.


Allah ya tsare kawai sukecemai dan sungane wayake nufi tinda inna taba Baban su labarin aikin da aka daukai,sun son in suka cikashi da tambaya zai iya fasa fitar,Dan da alama bayason aikin kawai zayyi ne dan ya magance wata matsala ta gidan.

A ƙafa ya tafi har ya iso kai tsaye bakin motar da suka hau ɗazu ya tsaya yamai waya akan ya iso.

Kamar jira Hajji Adnanu yake sai gashi ya taho cikin jallabiya yana ware kafa jikin shi sai reto yake kamar wanda ya ɗaura laya..

Wata dariya ce taso kufcema jameel ganin yanda Alhaji ke watsa ƙafa kamar wanda ya hadu da sharrin wanzam.


Bayan motar ya buɗe bayan ya bashi key ya shiga da kyal suka dauki hanya.

Wata special hospital ya kaishi dakecen kasan su ta Aymah, Bayan an duddubashi aka bashi maganin da zai ragemai radadi kana suka taho gida .

Ko Sannu jameel baicemai ba haka yana ajeshi ya juya zuciyar shi fesa dan shi kanshi mamaki yake yanda yajisa cikin farin ciki dayaga Alhajin ma bayajin daɗi.


Aymah kau ba sallah zataiba saitayi zaune taita azkar cen ta dauki wayar ta taita chart cikin natsuwa.
Tsawon lokaci bacci ya kwasheta ta fara mafalki mai daɗi.

A furgice ta falka tana zubama waje daya ido,waye shi,kuma taya,Suwaye wayan nan yaran.

Bata da mai bata amsa hasalima saita shiga tashin hankali da kara tsinema Alh Adnan, gashinan halin daya jefata yana neman sa ta halaka har ta fara kwanciya tana mafalki da wani wanda ba halaliyar taba, Ya Allah ka warware mun ka xaɓaman abinda yake Alkhairi A rayuwata .

Washe gari da sassafe Baraka tazo ta ganta ita da Malam habu sukamata ya jiki harda dawainiyar saimata kayan fruit.

Sosai tasha hakan kuma ya masu dadi dan atare ma suka fito ta sauke Baraka ita kuma ta nufi gidan Haj Asiya.

Lokacin da ta isa wani tinani ya faɗomata hakan ya sata sauke Ajiyar zuciya ta juya motar ta ɗauki hanya.

Ido na zaro lokacin danaga Ta danna Hon Bakin get din gidan ta.

Bayan mas gadin sun buɗemata suka gaishe ta Amsawa tayi kamin ta kutsa kai ta shiga get ɗin na biyu har inda suke parking.


Cikin natsuwa ta buɗe motar ta fito daga ita sai rigar jikinta amma ta ɗora lab court akai da siririn farin mayafi.


Da sallama ɗauke a bakinta ta tura kofar palon ta shiga ..

General ne zaune ya ware ƙafafuwa tare da saita panka akan jikin shi yanata kwasar ganima iska, dagashi sai jallabiya daya ɗageta sama,gefen sa uban magunguna ne kamar za'a buɗe Chemis...

Yanajin buɗe kofa ya zabura ya tashi yayin da ko gezau idon Aymah baiba saima kallo data bishi dashi na ƙurullah kamar maison gano wani abu.

❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
*MALLAKI*
❤️ *UMMY AYSHA* ❤️


*PAGE FIVE*

*ƘORAFI*
*MUTANE SUNATA KORAFI AKAN SUNA SO A RAGEMUSU KUDIN LITTAFI DUBA DA YANAYIN GARI DA KUMA YANDA RASHIN KUƊI YAYI ƘARANCI ,TO BA DAMUWA NA MAYAR DASHI 300 KACAL INA FATAN BAZAN SAKEJIN BAKIN KOWA BA NGD*

Ga wanda yayi shirin biya ya turo kuɗin Sa ta account number nah
*0006454115 Amina dahiru access bank*
Shedar biyan ka ta wannan layin nawa
*07038423451*

""" Matsanan cin rawa jikin shi ya ɗauka, Ranshi in'yayi dubu a ɓace yake,Gani yake duk duniya babu ɗan iska kamar Aymah, Babu kuma wanda yakaita buɗewar ido, wannan ma ya ƙara tabbatar masa da zargin sa tabbas Aymah ta son duniya , Yanzu abinda ta mai har zata iya haɗa ido dashi kuma cikin yanayi na dakewa ba tsoro ba shakka.

"Barka da safiya Yallaɓai tace cikin halin ko in kula tare da raɓashi zata wuce.

Aymah!
Ya dakamata mugun tsawar da ta sata dakatawa cak ba tare data cigaba ba.

Mikikazoyi gidana,Ashe zaki iya Neman kasheni kuma ki dawo inda nike? saboda baki da tinani kuma idonki ya gama buɗe wa ko?.

Ɗan juyowa tayi tana sakin murmushi .
Kamin ta fara tako dai-dai cikin Ƙasaita tana tura hannuwanta cikin lab court ɗinta tace.
" Adnan kenan!Mene zanji,mene zai bani shakka da tsoro A tattare dakai,Karka manta Rana ɗaya naga gawarwakin iyayena kwance gabana,Kana tinanin bayan wannan akwai abinda zai sake bani tsoro ya kuma furgita rayuwata,Noo b Ayishi ba,Kana dakaga na dawo gidan ka ai kason bana da inda ya wuce nan ko ka sakeni ne ban sani ba?Abu na karshe Anan shine.
Danmi ake koya maku training? Ba saikabani amsaba amma nason dan ku kare kankune duk sadda ka ganka a fagen yaki,Tom ni banje ba, bankuma karantaba, banma iyaba,Amma iya abinda yazo raina kenan dan in kare kaina da rayuwata nama abinda nama.
Kallafa. Tabuɗema sa wuyanta da yayi duhun kwanciyar jini.
Tace na tabbata da na sake 10mnt ina hannun ka da yanzu an kaini makwancina,Na cijeka inaganin hakan ne mafita amma baima ba saboda bak'ar zuciyar ka,Hakan danama shine dai-dai, kuma wallahi azeem ko yanzu ka sake kwatan ta kai hannun ka akaina sai nama Abinda yafi wannan, karka manta ranka anan yake,Zan jure komi bazan jure duka irin nakaba dan baizo a Shari'a islama ba ta ƙarasa tana juyawa zata tafi.

Gabaki daya jikin shi yayi sanyi duk wani kudiri nashi da yayi niyya kasawa yayi a dai-dai wannan lokacin , Wato takurawar da yake mata yakai ga tama daina tsoron sa da shakkar shi, lallai ya yarda da maganar Shekh Aminu daurawa da yake cewa duk yanda kake da mace karka ƙure Hakurin ta , Dan Mace in ta tashi so gabaki ɗaya take af'kawa, hakama in ta tashi ƙi gabaki daya take fitarwa , Ya Rahman ya Raheem yace yana komawa gefe ya zauna yana cika bakin shi da iska.

Aymah kau cikin natsuwa ta haye saman tayi wankan ta mai kyau ta sanya wasu riga da wando rigar mai hannun vest ce pink sai wandon Blue yalwataccen gashin ta tayiwa parking ɗin tsakiya tare da ɗaukar katon bnt pink ta ɗaure shi ta saki jelar , kamin tazo zata feffesa turare idonta ya sauka akan ledar Humra data saya wajen UMMY AYSHA.

Murmushin mugunta tayi tare da ɗaukar ta ta ɗan goga a hannu ta murje jikinta da bayan kunnanta .
Kamin ta sanya flat ɗin takalmanta blue ta ɗauki wayarta da headphone ta liƙa a kunne ta tura wayar Aljihu bayan ta sanya suratul Rahman cikin Qira'a Sheikh Abdullahi gwani wato majabakin Pantami.
Kaɗan kaɗan ta fara sakkowa daga step ɗin dan shiga kiching ta samar wa kanta abinda zataci dan tason Baraka ba zuwa zataiba tinda sunyi da ita zata fita wani wuri.

Kamshin fitinanniyar Humra tah ya sanar dashi zuwanta.
Hakan yasashi yima hanyar ƙuri da ido ganin yanda take jujjuya jiki Kaɗan kaɗan cikin natsuwa, shigar tata ta bala'in karɓeta ta haska farar fatarta tabbas in'bakason shekarun Aymah ba zaka ɗauka layin yan 25 take dan som babu wani abu da zai tabbatar ma da tsufanta ko wani abu daya danganci shekarun ta.

Ko inda yake bata kalla ba domin zuciyarta fal take da bakin cikin shi da tsanar sa yanzu mafita kawai take nema daga mai duka.

Kiching ɗin tashiga tayi tsaye tana nazarin mima zata dafa.

Cikin ɗan sassarfa ta ɗakko cous-cous dan zaifimata saukin sarrafawa.

Shuru kuma tayi tana ajiyeshi gefe kamin ta fara nazari ko ba komi har lokacin Adnan mijinta ne ya kamata tabi shawara Baba Baraka ta sauke duk kan hakkin shi dake kanta ta yanda ko agaban ubangijinta zata fita.

A'Hankali ta fita daga kiching din kai tsaye inda yake ta nufa ta iskeshi ya daga kanshi sama ya fada duniyar nazari.

Yallabai mene kake bukatar a dafama ta fada tanayin gefe da idonta.

Kallonta yayi yaga ko ido batason hadawa dashi lllai ya taro match.
Gashi Wani kwarjini da kyau yake ganin tana masa ga masifaffan turaran dake kaimai naushi dake ƙarama farashin sa hauhawa cikin lokaci,Sai dai yason ko giyar wake yasha bazai iya aikata komi ba a wannan yanayin inba so yake da kanshi ya illata kanshi ba.

A hankali ya nunamata gefen shi tare da faɗin zauna anan Ummu Aymanah.

Kallon shi tayi da sauri ya ɗagamata kai alamar tabbatar wa.

Wani yamm taji jikinta yayi cikin lokaci taji gaɓɓanta sunyi sanyi (Mata bayin Allah,Maza na amfani da raunin mu suna muna abinda suke so Allah ka shirya mu baki ɗaya)

Inda yace ta zauna din ne ta koma ta zauna tare dayin ƙasa da kanta.

A'Hankali ya fuskanceta yace .
"Kinamun kallon azzalumi ma ha'inci ko Aymah,kina ganin bana da lokacin ki saina kudina ko,Shin Aymah so kike wahalar danasha yarana su shata,Akan mi bazaki bani goyon bayaba akan abinda nikeso,ita mace mai mutunci tana bama mijinta goyon bayane duk sadda ya nunamata yana son Abu balle ni da Halaliyata nike nema, Zahirin gaskiy kika ƙara nunamun wannan tsanar da faɗaman duk maganar datazo bakin ki zanbaki mamaki bar ganin na kyale ki yanzu.

Tsaki tayi a ranta tamayi tinanin lallashinta zayyi ko wani abu amma ina girman kan asarar sa bazai bari ba.
A zahiri kuma Murmushi tayi tace.
" In'banda abinka Yallaɓai ina mukaga Yaran da za'ace ka tayar da hankalin ka a kansu?To nikaina da zan haifama ina kaga lokacina balle na samu rabon su?

Ɗan sassanya murmushi yayi yana kara bajewa cikin kujerar kamin ya saki murmushin mugunta yace".

Aymah kece bakya da yara amma ni Adnan ina da yara guda biyar cur da Allah ya bani,kuma nema da nike nasune bana kowaba, Dan wahalar da nasha banaso ko tattaɓa kunnena yashata shiyasa na zage ina nema masu ya ƙarasa yana lumshe ido da dora kanshi akan kafaɗar ta dan kaɗan kaɗan iska keta huramai iskan kamshin jikinta mai bala'in saukar mai da kasala jinyar shi ce kawai matsala amma da tabbas yau sai ya karya Alkawari dayama zuciyar sa na tsawon shekara goma sha biyar..
.

Murmushi tayi tace ko sama da ƙasa zasu hade bazan yarda da wannan tatsuniyar ba Adnan, ba girmanka bane ta karasa jikinta na rawa duk da maganar bata shigeta ba amma faɗin yana da yara kamar barazana ne ga rayuwar ta,To taya? .

Murmushi yayi ya ɗan karkace tare da zaro wata wayar da bata taɓa sanin shi da itaba ya bata yace zaki iya tabbatar wa.

Hannunta na ɓari ta karɓa amma ta kasa sarrafa komi.

Karɓa yayi ya shiga contact
Taga mutum shidda ne kawai aciki.
1f love
2Shaheed
3Nazeer
4Saif
5Ikram
6Waleedah

Gallery ya shiga sai gashi wayar cike take da photon zaratan samari masu bala'in kama dashi kaf yaron shine suka biyo Sai wata Dattijuwa da ashekara zatakai nashi koma ta fishi dan fuskar ta ta bayyana girma duk da akwai alamar hutu a tattare da ita haka suma yaran dukan su manya ne babu karami a cikin su dan karamar ma ya wato waleedah zata iya kai 20yrs.

Hawaye masu zafi da wani mugun raɗaɗi Aymah taji suna kwararoma ta,Ga nawie Sosai da zuciyar ta tamata dama som bata da lfyn zuciya kuma duk ɓacin ran Adnan ne sanadi danma tana taka tsantsan..

Ido cikin ido take kallon shi Kamin dakyal tace .
"miye ribar haka da kayi?

Wannan sirrina ne basai kinji ba yace yana juya kai cikin faɗuwar gaban da baitaɓa jin irin taba.

Dama shiyasa baka taɓamun zancen rashin haihuwata baya damunka ba.
Koko dalilin dayasa tsawon lokacin da muka ɗauka baka damu dani ba? Ina rashin lfy da kaceman kanayi?Miyasa kaci amanata kaci amanar matar ka?

Babu amanar danaci taki Aymah.
Inada wayan nan yaron bana buƙatar kari Aymah,Kinson in dambu yayi yawa bayajin mai ko,So yara nawa zaku ajiyemun in nace kowa taita tamfatsamun haihuwa,Gashi akwai Alkawari tsakanina da madina mai girma.
Ina son matata sosai kuma kema ina sonki amma banaso ke ki haihu nafison naita ganin ki a haka,In shiga duk taron da nike so dake mussamman yanzu da kika gama Karatu kika fara aiki a ƙalƙashin Asibitin ki ta Kanki.

"Bazai Yiyuba tace a fusace tana dakamai muguwar tsawa tare da faɗin.
Dole murabu, Dole ka sakeni , Dole Adnan nabarka na samu masoyi na hakika ta karasa cikin ihun kuka da gunjin da shi kanshi saida ya furgita Yakuma tsorata dan bai taɓa ganin tayi wannan Burkicewar ba amma dayake bai iya lallashi ba baison ya zai mataba sai ido da yake rabawa.

Cikin kuma wani bala'in rawar jiki ta mike bayan ta tsaida kukan sai hawaye dake kwararomata masu zafi ta fara magana.

"Adnan sake ni inba hakaba zan ƙarar da kaf dukiyar da Allah ya bani in'makaka kotu,sakeni Adnan Kamin inmaka lahani ko in kasheka in kashe kaina bakin cikin ka ya isheni azzalumai maketaci. .

Bazan sakeki ba mutuwace zata rabamu, kan'nan bazaki haihuba saboda ina da dalilina na rashin son ki da haihuwan, in'ce wasu matan ma mahaifar sukeso a ciremusu shashasha kinsamu bandamuba ma zaki kawoman wargi,to daga yau bazaki sake fitaba wallahi azeem kinji na rantse, nidai kike cemawa zaki kaini court ko ? To bakin kofa kika sake takawa batare da na saniba Allah ya isa ban yafemiki ba.

Fita kuma in ta zama dole zansa akaiki akuma dawo dake fakat ya karasa yana mikewa yayi daki ranshi ɓace.


Wani wahalallan kuka ta sanya tana bajewa akan kujera a dai-dai wannan lokacin ji take inama ta mutu ta huta da bakin cikin da Adnan ke shimfiɗamata,Yah Allah ka kawoman mafita ta faɗa da karfi tare da cigaba da kukanta tsawon lokaci kafin taji an turo kofar an shigo.

A Hankali ta fara ɗago jajayen idanuwan ta da suka kumbura sasur sukamata nawie ta sauke su fess a kan kyakyawar fuskar shi dake daure gam kamar kowane lokaci.

Shikan shi idon ya zubamata na dan lokaci kamin kuma cikin lokaci ya ɗauke kan shi tare da mikewa da sauri ya fita daga palon yana tsinema Alh Adnanu mai kan kwakwa dayace ya shigo zai aikeshi yayi tinanin babu kowa sai shi kaɗai..

Cikim sassarfa Aymah ta mike da niyyar binshi kamar kuma an tunatar da ita wani abu ta kalli kanta kamin ta zaro ido aguje tayi sama .

Tana shiga dakinta ta baje akan gado gabaki daya kukan ta dauke wa yayi sai wani sassanya sanyi data faraji mai hade da saukar yalwa da madaukakin farin ciki a kowane lungu da sako.na jikin ta, Duk wani nawie da zuciyar ta ke mata A'hankali ta farajin Ya yaye, farin ciki na maye gurbin bakin cikin ta.


Alh Adnan kau tinda ya shiga dakin sa ya fara safa da marwa gabaki daya ciwon jikinshi jinshi yayi ya dauke,Wani tashin hankali da nadama furucin dayayi mata yakeji,Shidake da buri akanta na har abada miya kaishi fallasa asirin zuciyar shi.
Ya zama dole ya sama Aymah matakan tsaro tinda ta fara sanin wasu sirrika daga gareshi dan komi zai faru bazai iya sakinta ba,Adane dai yake tinanin zai iya lamincemata ya rabu da ita musamman dayaga ta cika matsamai da zancen hakkinta hakkinta bayason matsawa neman sa yafiyemasa komi amma ayanzu yanajin bazai iya gangancin nan ba som.
Waya ya zaro ya kira Jameel tare da bashi umarnin yayi maza yazo gashi har lokacin daya diba ya wuce.
Bayan yaje yamai waya yace yashigo .
Shigar dayayi ne idon shi yayi tozali da ita.


Alh Adnan kau yana fitowa yaga wayam Jameel baya nan sai wucewar Aymah da gudu .

Da ido ya bita kamin ya ɗauki wayar shi ya kirawo Jameel din akaro na biyu.

Sallama yayi ya shigo ran shi ɓace kamin ya zauna gefe yace barka da rana.

Yawwa Jameel dan Allah ina zaka samomun Manyan kwaɗo na rufe kofa?.

Bazai wuyar samuba Jameel din yacemai fuska ba walwala dan jiya zuwa yau ya fahimci mutum ne mai tsananin takurawa ga iyalin shi.

Ohk tom.
10k ya bashi yace siyomun masu kyau da kwari guda hudu sauran canjin ka ɗauka.

Ngd yace ya tashi zai tafi yace karɓa key din mota kaje ka dawo.

Karɓa yayi ya fita yaje ya siyo masu kyau da kwari ya kawomai.

Nagode yace tare da daga wayar shi ya kira duka masu gadin gidan.

Bayan sunzo suna sanye da uniform ɗinsu na sodoji yace yawwa umarni zanbaku kai tsaye kuduka biyar in'nan.
Dayake kowace kofar get mutum biyune sai jameel na biyar.


Yes sir suka amsa banda jameel da kanshi ke kasa yana wani nazari .

Yawwa jamilu kana jina.

Saida ya yamutsa fuska kana ya dagamai kai.

Alhamdulillah....
Masu gadin farko yabama kwaɗo ɗaya, da masu gadi na biyu sauran biyun kuma yabama jameel su duka biyun yace gashi kai yanzu Dole aikin ka ya Karu ba iya Driver kawai zaka tsayaba,Kana Wallahi azeem duk wanda yayi sakaci acikin ku saina halbeshi kunji na Rantse.

Karkubar uban kowa ya kara shigowa gidan nan kana karkubar ita kanta madam din tana fito daidai da get din farko.
Kai jamilu kofar baya zakasama kwado ka kuma sanyama ta palon nan itama kaga nan bakin kofar nan ?to yazamana nan ne wajen zamanka kullum,in kabari ta sake taka baranda wallahi azeem sai ranka ya ɓaci,Mahaifiyar ka zaka iya barinta ta shigo ta tayata zama amma bayan ku biyun nan wani ya shigoman gida sai kunga abinfa zai faru.
Gabaki daya sodojin a rikici suke amsawa yayin da jameel kuma tsuke fuska kawai yake da hura hancin sa daya karamai bala'in kyau.

Zaku iya tafiya yace.

Fita sukeyi kowanne ya dauki kwado ɗaya suka fita shikuma Jameel baiko motsa ba.

Kana da magana ne jamilu cewar general.

Fuskar sa ya dan yamutsa kamin yace .
Oga inkace ka bani wannan shugabancin Da babu takarda zamana ma'aikacin ka kamar ka hanani zaman gaban iyayena ne dare da rana sai dai in tare anan ina gadi,Kana na fadama in'kana da doka nima ina da tawa,Bana tashi bacci sai karfe goma,Banaso ka ɗauki kaslanin(RAGGO) ɗin mai gadi da zakayi dana sani ,Bazan iya wannan dokar ba gaskiya ka canja wani ya karasa yana mikewa tsaye .

Zozo jameelu kaji ko Adnan ya faɗa cikin rarrashi dan aganin sa zuciyar jameel da kuma yanda yake kaifi ɗaya zai karama Aymah tsoron nufo kofar dan in ta zaburar da wayancen shi wannan baiga alamar zai dauki raini ba.

Ina jinka jameel ya katsemai tinanin sa.

To na yarda kazo karfe goman shikenan ko ai yayi ko kuma in baka ɗakin dake cikin farfajiyar palon nan ya karasa yana nunamai wani daki dake kusa da kiching din su.

Da sauri jameel ya gilgiza kai yana ganin tsantsar jahilcin Adnan, waishi zai hada muhalli daya da matar shi lallai mutumin nan ƙasurgumin jahili ne
.

Zanzo karfe goma zan koma shidda na yamma dan nima iyayena na bukatar kasance wa dani, kasancewata babba a wajen su in hakan ya ma shikenan in baimaba kuma zaka iya samun wani..

Yayimun jameel yace da sauri yana kara tsinemai da faɗin zakaci ubanka dan iska sai wahalar dani kake kana talaka ni kuma da azziki na.

Kafaɗa ya d'aga sama yana taɓe baki kamin ya tashi zai fita yace.

Yanzu zaka dan fita dani su su kula da gidan muje ka kaini Asibitin ta akwai dokokin da zansanya amma kamin nan jirani ina zuwa yace yana haurawa saman dakin Aymah da bacci yayi gaba da ita mai daɗi.

Yaji dadin ganin ta haka
Saɗaf saɗaf kamar munafuki ya hau bincike ,Sai da ya kwashe kaf abinda yason mai amfani ne a wajenta kudi kam ya gansu kamar banza wannan ya tabbatarmai da wayandama yake bata ba wani amfani take da suba suma saida ya kwashe su tass,Ya sanya hannu zai dauke wayar ta ta falka


❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
*MALLAKI*
❤️ *UMMY AYSHA* ❤️


*PAGE 6️⃣*

*ƘORAFI*
*MUTANE SUNATA KORAFI AKAN SUNA SO A RAGEMUSU KUDIN LITTAFI DUBA DA YANAYIN GARI DA KUMA YANDA RASHIN KUƊI YAYI ƘARANCI ,TO BA DAMUWA NA MAYAR DASHI 300 KACAL INA FATAN BAZAN SAKEJIN BAKIN KOWA BA NGD*

*0006454115 Amina dahiru access bank*

,,,,,Wani kallo tamai dake bayyana tsantsar tsanar da tamai kamin tace.
" mizakayi da wayata?
Shuru ya mata tare da ɗaukar katon akwatin daya loda kayan ya fita.

Tsaki tayi tana rakashi da harara dan duk tinaninta wajen aiki zai koma.

Idonta ta lumshe tan sake budesu tare da sakin murmushi tace "waye shi"?


Adnan kau yana fitowa ɗakin shi yayi da duk kayan ya adanasu adanawa mai kyau kamin ya dawo yayi wanka ya shiry tare da dakko akwatin suka fita.

Wani katafaran Bank ne suka isa , Jameel dai zaman shi ya gyara a mota yayin da Adnan ɗin ya shiga ciki.
Ya daɗe kamin su dawo tare da wani wanda yake da tabbacin ma'aikacin wajen ne ya damƙamasa komi kamin ya shigo mota yana sauke ajiyar zuciya da sakin nurmushin mugunta...

Ta glass din Jameel ke kare mai kallo wani Mugun tsanar shi na tasiri a cikin rayuwar sa,Bai taɓa jin ya tsani abuba kamar yanda ya tsani Alh Adnan, Dan ya fahimci mutum ne mai bala'in son kanshi, Bai kuma damu da kowa ya mutuba in dai shi zai rayu,Sannan ya fahimci mugun mutum ne ga iyalin sa,In bai kuskuran gani ba kuka yaga tanayi daya shigo,To wayasa ta dawo gidan ya karasa tambaya yana sakin ƙaramin tsaki.


Hahaha jamily kaga nayi maganin komi cikin sauki ko?Na hanata fita na kuma kwashe komi nata da dukkan ƙaddarata nabama wannan manager bankin,Bance ya hada dukiyarta da tasuba saboda kudin marayu lalata ma mutum arzik suke,Amintacce nane Nan da kake ganin sa , ,Nadaicemai yatafiman dashi gidan shi dake cen janbulo ya adanaman, Aymah kau sai ta zauna dani ko taso ko taki,Yo kotaki mana tinda yanzu bana tinanin naira biyar zata iya samu ,kai asama zata samu ta gidan ubanwa zata fita ta kasheta Bayan nasamata matakan tsaro gaba da baya.

Jameel dake son jin labarin yanda abun yake yace.

"Oga kayi hakuri da shishigin da zanma.

Haba jamilu yi maganaka ba komi ina cikin farin ciki cewar Alh Adnan.

Ohk tom dama cema zanyi shagwaɓa maca ne ace ka bata ci ka bata sha kana kuma ka dinga narkamata dukiya,yo ai ba yanda za'ayi tama biyayya kana dasu tana dasu ai tin farkoma ya dace ace hakan ta faru.


Hahahha!! Alh Adnan ya sake fashewa da dariya da kuma jin daɗin maganar Jameel din yace" ko kaifa ashe kaima dan hannu ne .

Jamee.
Hmm yahajj kenan! aini abinda yasa kaga bana dariya ko yawan magana banaso a rainani ne,Shiyasama ni ko aure bazanba dan yanda nike da zuciyar nan ɗan banza duka zandingama matar,Kaga gwara in zamana haka kawai,Gashi bana son hayaniya mace tazo ta cikaman gida da yara nima kuma in cika masu gida da duka ba ita ba yaran ba.


Sosai Hajji adna6n ke dariya harda rike ciki wato jameel ma mugun kanshi ne kenan, yanaganin shi haka Ashe zai iya fiye da aikin da yasashi aiko dole ya jawo shi jiki tinda bashi da imani..

Jameel kau idon shi har wani kwallah yake tarawa wanda shi kadai yabarwa kanshi sani dan dakyal yake control ɗin kanshi .

Wlh jameel kamun dai-dai, Nima ai ban 'son raini da fitsara ,uwa uba kashiga lokacin aikina zan yaga rigar mutuncinka kuma ka fita raina ko waye kai ko,Kaga ko wannan matar tawa,wallahi shigar da take lokacina yasa na tsaneta kawai ina zaune da ita ne saboda dalilin ta dinga fitar dani kunya in zamuyi taro haka daya shafi tafiya da iyalin mu, sai inje da ita amma aikina ai shine gaban komi,yanzuma gardama zata kawoman cikin lamarin rayuwata Akan saina saketa, nikuma na kwashe komi nata da ƙaddarorinta na kaima wannan manager in yaso ya adanasu sai ranar da naso,Ina so taji wuta taji matsin da dakanta zatabani hakuri ta janye kudirinta na son sakinta da takeso nayi ta kuma karɓi tawa buƙatar da hannu biyu nikuma saina ƙaramata wani abu akan nata in ta amince.


Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un Jameel yace A ranshi, wani tausayinta na tsargama sa rai,Lokaci daya yaji ya dace yayi amfani da damar da zai samu ya taimaki rayuwar ta dan yagano babban manufa ce Adnan yake da ita akan Aymah.

Oga ina Iyayen ta to? baka tsoron su sani cewar Jameel.

Haba wane su tini sun wullah barzahu, kuma dama ita kaɗai suka mallaka dangi kuma basa kusa, Suna cen Agadas, kana a Agadas ɗinma babu hadin kai a family nasu dan bason iyayen Aymah suke ba kasancewar su Yan boko wayayyi,Som babu jutuwa a tsakani shiyasama nikaina in'tace zataje ganin gida nike hanata dan yanzu tinda aka gama zaman makokin iyayenta natsaya akabata dukiyar ta na kwasota mukadawo gida kuma bana tinanin har abada zata koma.

Ya salam.
Jameel yace yana dafe kansji dake saramai...wato marainiya yakema haka dan bata da mai tsayamata,ya rabata da kowa yana kuma azabatar da ita,in'sha Allah zai shiga rayuwarta kuma saiya taimaketa amma dole sai yaji ta bakinta, Amma Wannan auran saiyayi tsayuwar daka ya rabashi dan basu

Please Login or Register in order to submit comment