Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takasa Tsayawa.

Adnan kau kuka yasa dayaga abinda takemai bakin ciki da tsanar ta da ahlinta na kara hauhauwa afarashin zuciyar shi,Ya dauki Babban alkawari duk sadda yaganshi tsaye da kafarsa sai yazama ajalinta.

Dakyal ta tsagaita ta saki ɗan murmushi mai bayyana zallar farin cikin da take ciki, Tare da daga hannuwanta sama tace.
Allah gafurun rahim, Allah nagodema daka nunaman wannan ranar A tarihin rayuwata , Ina cikin tsananin farin ciki bisa ga sakayyar dakaman cikin gaggawa, lallai Allah ba azzulimin bawan sa bane, Allah bayason zalinci baya kumabari ayi zalinci, Adnan ina takamar ina kudin, dukafa sun shuɗe, gakanan dare daya Allah yayi nashi ikon akan ka.


Wayar shi data sake kawo ihu ta ɗauka tayi sallama.

Shuru taji anyi kamin cikin sauke ajiyar zuciya taji ance ina "Mai wayar bashi mana miye alakar ki dashi.

Murmushi tayi dan tagane matarshi ce.

Tace matar shi ce ta biyu,Wacce ya boyemiki zaman dake tsakanina dashi.
Ayanzu dai mijin ki ya shiga toilet danyin wanka in ya fito zai kiraki. .

Cikin ihun tsawar dattijuwar ta kundumoma Aymah zagi da fadin wacece ita,Ita babu namijin daya isa yamata kishiya balle ma Adnan da tason Baxaitabamata haka ba saboda rantsuwa yayi da Allah akan bazai hadata da kowa ba.

Murmushi Aymah tayi kamin tace.
in son samune mizai hana kibari lokaci yayi kizo inda yake,yanzu lokacinane in yadawo gareki zaki iya masa wannan tambayar ,Kana da xakice bazai Haɗaki da Kowaba, ina kikaga ilimin da za'a shiga taro dake ke kam ai sai tsaron Yara shine ya dace dake.

Cikin ihun kuka tace .
wai kina nufin kece wannan dayaceman yana daukar haya in zaije taro? kece dama matar shi? yanzu ni yakecema marar ilimi ?ina yake yazo yabani kaf dukiyata dama ance tsintacciyar mage bata mage na tsani Adnan Allah ya isa tsakainina dashi ta karasa cikin kuka.

Murmushi Aymah tayi tace
kema kince wani abu kamin ta datse wayar tare da cire sim card din ta aje shi gefe.

Kallon shi tayi yanata zare ido da gilgiza kai tashin Hankali mabayyani A fuskar shi.

Murmushi tayi tace yanzu Allah zai fara tonamaka asiri.

Kibani wayata ai natakeki kitai kibani wuli yace a gwamutse.

( Kibani wayata ai na sakeki kitai kibani waje)

Ido ta zaro cikin farin ciki tace'' Alhamdulillah Adnan ka sakeni ta karasa tana jin hawayen farin ciki na zubomata saboda bata taba tinaniba gashi tayi alkawari bazata tabacewa ya saketa ba.


Aguje ta mike tayo kasa tana kwalama Deedee kira da fadin" Kaka kaka zo Adnan ya sakeni takarasa cikin farinciki hawaye kwance akan kyakyawar fuskar ta.

Deedee ce ta fito tana rike haɓa itama farin ciki kwance a fuskarta tace.

Kai haba amma abufa yayi dadi to yanzu ai morewa ya baki dukiyar ki sai kibarmai gidan ki.

Aa nabarmasa tace tana wani juyi cikin mugun jin dadi dan gani take kamar ta sauke Kaya..

Kai kai kai Alhamdulillah abufa yayi dadi .

Kwan!kwan!!kwan!!!taji anfara buga kofa.

Deedee ce ta bude idonta ya sauka akan Dr da Jameel da idon shi yayi bala'in ja kamar wanda Yayi kuka fuskar nan tashi a tsuke ba alamar rahma.

Lokaci daya suka sha jinin jikin su daga Deedee har Aymah.

Ina Adnan yake yace jikinshi na rawa.

Deedee ce data fahimci yau zuciyar ta motsa mai jikinta har rawa yake wajen nunamai dama tana komawa gefe.

Dr kau rikeshi yayi yana fadin kabi komi sannu Jameel ban faɗamaba dan Kai aika aika..

Fincikewa yayi kamin agujen ya fara tattaka matakalar.
Nan gabaki daya suka rufamai Baya.

Deedee kau har tayi rabi ta dawo ta ɗauki farin kayan ta ta sanya ta murje fuskarta da powder ta da Kwalli kamin aguje ta bisu .

Jameel kau yana shiga gadan gadan ya banka kofar dakunan baiganshi ba sai ana ukkun ya ganshi bai tsaya tantance komiba ya ware kwanjin shi ya hau dukan Adnan kamar ya samu jaki.

Ihu yake cikin karyayyan halshen shi yana faɗin.
Suwaye ku minaima Ku.

Deedee data shiga da fararan kaya ta bayan su tabi ta wuce tai tsaye saitin da Adnan yake ta tsaya da ɗan murmushin nan nata mai dagamai Hankali.

Munkalu wanakili kuyi akuli Natuba facen ƙalaba yace da karfi idon shi akan Deedee.

(Munƙaru walakiri kuyi Hakuri na tuba bazan ƙaraba)


Aymah kau dariya sosai yabata kamin idonta ya sauka kan DeeDee zata fasa ihu Deedee tamata alamar shiru.

Jameel ta samu ta cakumo da karfi tare da Sanya hannuwanta ta sargafo shi ta baya cikin rawar jiki tace" Jameel kallah cen.

Cak yaji komi nashi ya tsay zufar jikin shi ya shiga share wa yana maida numfashi kamin ya juyo ya riketa gam suka rungume juna sosai yanajin wani mugun yanayi a tattarr da ita.

Ido ya ɗan zaro kamin ya dagata ya zubama Deedee ido danshi kanshi saida gabanshi ya fadi da ganin ta.

*Yanzu haka kudin Likkafani ne ya gagara kai jama'a yanzu kudin da za'arufe tsiraicin mamaci ma sai ya Gagareka*
Maganar ta ta dawoma Jameel kenan itace gawar kuma nan tayo .

Koda yake ai dama itake nunamai dakin duk sai yanzu wannan Tinanin yazomai.

Saf saf saf ta shafasu ta fita .

Dr ma fita yayi ya barsu daki su ukku.

A'Hankali ya dago haɓarta ta zubamai ido shima idon nashi ya zubamata.

Wasu sakwanni masu wuyar fassarawa suke aikama junan su kamin da wuri ta kawar da kanta tana maida idonta ga Adnan daya zumabasu ido dan sai yanzu ya gane Jameel ne ashe yamai wannan mugun dukan lallai ma.

*Kina da Labarin jiya kika gama iddarki ? Jameel yace cikin wani yanayi da bazai musultu ba.

Ido ta zaro tace iddah ,iddafah kace Jameel...


Ga masu bukatar saye ku turo ta account number nah kamar haka
9064260199AMINA DAHIRU OPAY BANK
Shedar biya ta Whatsapp number nah 07038423451

❤️MATAR OGA ❤️
MALLAKI.
UMMY AYSHA

PAGE 12

*ASLM ALAIKUM DAN ALLAH ADAINA SAMUN KATIN MTN BANA AMFANI DASHI SAI CHART GLO KAWAI NIKESO NGD*


Fararan idanuwan shi ya lumshe yace .
Tabbas ya sakeki tin ranar da kika biya kudin aikin da akaman Asibiti.
Hannuta ya kama suka fito suka dawo palo inda suka iske Deedee da Dr zaune tana bashi labarin komi yana dariya.

Bayan sun sakko Deedee ta zubamasu ido tabbas sun dace da juna matuƙa .

Wayar Dr ya karɓa ya shiga inda videos suke ya nemo wanda ya masu ba tare da duk sun sani ba.

Anan aka shiga haska takarda da Adnan ya karɓa wajen Dr yana rubutu itakuma tana kara jaddadamai tabarmai duk dukiyarta, da alƙawarin vazata taba guduwa ta barshi ba Har sai in shine ya buƙaci hakan.


Ya salam ! tace tana dafe goshi wannan wane irin bala'i ne da masifa! miye manufar Adnan na tozarta ta haka? dama so yayi taita zama karkashin wahalar dayake ganamata itakuma tanamai biyayya har karshen rayuwar ta.
Lallai Allah nagodema tace a bayyane tana sake kwanciya akan kafaɗar Deedee hawaye na zubomata..


Jameel yace .
Kinga abinda ya miki ko,yanzu miye mafita?.

Murmushi tayi tace. Jameel bana da wata mafita ayanzu ,ina zani ina zan zauna Allah masani.
Ya haɗani da family na bazasu karbeni ba,Nima bazan fara yarda na kusance suba,Banama da kudin da zan iya barin garin nan yamun kat ya kwashe ni.

DeeDee tace'' zaki iya zama damu a gidan mu amma muma ba masu karfiba ne?.

Shuru tayi dan tana ganin zamanta dasu kamar D'aura dawainiyar ta ce gare su,Kawayenta kuma bata fatan kowama Yasani dan wannan sirrin tane.

Dr ne yace Yanzu Deedee abinda yadace anan shine".

Zansa mai gadin gidana ya mayar da Adnan kauyen su zan dinga biyansu suna kulawa dashi adan kwana biyu,In yaso sauran magana ma idata bayan ya dawo.

Deedee tace nifa inaso sanin tarihinki Aymah wai ubanwa yasa kika aure shi?

Aymah ta share hawaye tace Deedee tsautsayi da kuma Yaudara dayaman ashe fuska biyu gareshi.

Deedee tace Ina jinki cikin ƙaguwa.

"Sunana Ummu Aymanah.
Mahaifina da Mahaifiyata yan uwan junane saboda family nasu Auran junan su suke kamin daga baya kuma suka janye wannan Al'ada,Sukaba kowa damar zaɓen wanda yake so.
Nataso cikin gata da kuma wadataccen ilimi na addini dana zamani.
Mahaifina yana daya daga cikin masu arzikin family nasu koma nacemaku yafi kowa dukiya dama wajen mahaifan sa shine kwallin kwal kamar yanda nima nidaya ya Haifa .

A labarin daya bani Adnan Tsohon Driver sane ta fannin Hito na shinkafa da suke fitowa daga maradi su shigo da Ita Nijeriya Su sayar.
Daga baya kuma Adnan din suka rabu da mahaifina amma bai dai faɗaman dalilin rabuwar tasuba yace dai sun samu saɓani.

Ina gab da gama karatuna na secondary Adnan ya dawo rayuwar mahaifina bayan ya nemi affuwar laifin dayamasa kasancewar Babana mai hakuri ne Kuma bashi da Riƙo ya yafemai suka dawo harkokin su na rayuwa .
Sosai adnan kemai biyayya duk da kasancewar lokacin yana da Babban matsayi a fannin aikin daya fara na soja Amma bai manta Halaccin Mahaifina gare shi ba .

Bayan na kammala secondary sch ne Adnan ya nunama mahaifina ya Dade yana sha'awar ya aure ni tin ina Ƙaramata.
Yana so yabashi ni daganan ya dawo dani cikon garin katsina dan in karasa Karatun danike so nayi na likita.

Sosai mahaifina yaji dadi har dai ya sameni da magana nima na amince dan ina ganin mutuncinsa yana kyautatamun duk da Babban mutum ne naji na amince dashi Sosai.

Bayan anyi aure na dashi ne ya kawoni nan katsina inda ya zameman uwa uba gata na gidan duniya babu wanda Adnan bayamun mussamman dayaga Bantada Hankalina ba akan Rashin lfy dayake da itaba,Babu abinda ya dameni nidai kulawa da yakebani ya wadatar dani.
Duk sadda zai tafi aiki kau haka xan kwana kukan rabuwarmu dakyal dai nike barinshi yaje .
Akwana a tashi nima ya mayar dani karatuna nan na fara gadan gadan.
Adnan kanje dani taron su na manyan Sodoji da akeyi wanda ya hada da iyalin su .
Duk sadda naganni dani dashi nakanji dadi sosai yanda yake nunama duniya yana sona.

Adnan ya taka rawar gani ta fannin ilimina dan ya tsayaman har nakai matakin zama Babban Dr .
Sadda na cika shekara 14 da Aure mahaifina ya budeman Asibitin da aka kwashe shekara biyu ana ginata tawa ta kaina wacce ni banma saniba duk tinani Adnan ya budeta dan shine kan gaba wajen komi.
Ranar da aka kammala komi ne suka dakko hanya dan zuwa ayi taro dasu saidai akamana waya akan sun samu accident dukkan su sun mutu.
Bazan iya musultamaku tashin hankalin da najiba a wannan lokacin nayi kuka nagode ALLAH.

Acen Agadas akayi zaman gaisuwa.
Kwanan ukku da rassuwar su Adnan ya Tatamasu rashin mutunci akan sai sunbani Hakkina da iyayena suka mallakaman dan ya fahimci sunyi caaa akan dukiya ta.

Babu yanda basuyiba akan yabari amma ya nunamasu kakinsa na soja da son kawar da duk wanda zaici zalin dina.

Wannan abu ya masu zafi suka hada duk wata kaddara da take tawa suka bashi gabansu ya damkaman kana ya kamo hannuna muka fito.
Har munzo mota ya kamani muka koma ya bugemasu warning akan duk wanda ya cika dan halak karyazo inda mukeya isheni komi na rayuwa.

Anan suka hau rantsuwa akan zasu nunamai jinin buzaye basa magana biyu.
Suma suka sake koramu dan sunfisata mussamman da sukaga nayi shuru duk tinanin su bayan mijina nike goyo .
Nikam Alhini rashin iyayena ne ke damuna bata ihun da suke nike ba.

Bayan mundawo gida yasake shedaman na tattala dukiyata kuma na fara fita aiki shima zai koma bakin aiki an'ma maidashi Kaduna baki daya dan da yakanje yadawo..

Toh nace nan washe gari ya yi shiri ya koma wajen aikin sa nima natafi wajen aikina da bana iya komi sai tinanin iyayena .

Haj asiya kawata ce sosai tare mukai karatu .
Da kaina na dauketa aiki ina sallamata kudi mai tsoka .
Duk sadda zata fadaman matsala maza bana yarda saboda ni naga nawa ya tsallake na kowa duk da yaceman yana da matsala hakan baitaba damunaba tinda yanabani kulawa daya dace dani muna kuma addu'a da fatan samun Rabo mai Albarka.
Wannana tafiya ta Adnan itace sanadin watsewar zaman auran mu dan bai waiwayoniba saida akai wata shidda cur,bayan yazo kuma yazoman da ayyika baya da lokaci na,in'kau yana aiki namai magan sai tsawa hantara rashin mutunci daga karshe kora ya biyo baya.

Nayi kuka Nagode Allah saboda bansaba ba , Nayi nayi ya fadaman minaimasa yakiya kullum korata yake da hantara waya kau namasa ranar nabani zai iya zagina shiyasa banayi saiya nemeni.

Ahaka dai naita rayuwa ni kadai gashi bayason mutane Asiya ma ya rabani da ita Sai wajen Aiki.
Dakyal dai ya barni na ɗauki Baba Baraka bayan nakai ruwa rana tana dan taimakamsn da aiki har zuwa dai yau da Allah ya kawo wannan rabuwar da banmasani ba.

Deedee ta numfasa tana sakin murmushi tace. Tabbas akwai wata akasa kuma ina bukatar sanin wane saɓanine ya hadasu har takaiga rabuwa kuma aka sake dawowa.
Kanan miyasa ya kyautatami ki gaban idon su bayan idon su kuma ya kuntatamiki ? Mutuwar iyayen nakima inaji Ajikina akwia sanya Hannu.

Ido Aymah ta zaro jikinta ko ina ya dauki ɓari tace. Kina nufin zai iya kasheman Abbah nah da umma nah ?

Deedee tace ko daya. wanda dai yayi wannan zuciyar ta barinka kuma daga baya ya dawoma sai inga kamar fansa yazo ɗauka amma dai bari zamuji daga gare shi wata rana.

Jameel yace bari na tambayo shi.

Kamo hannushi Dr yayi yace bakaga matsalar daya samuba a yanzu,Magana zatamai wahala,kana bayyi laushin da zai iya fadin gaskiya ba kabarni da shi.
Kabari kawai a mayar dashi cen wayoyin shi kuma ka kawoman su nan na ajesu.

Am'sawa sukai da hakan yayi kamin suka tashi suka tafi Deedee kuma ta rike ciki tace .
ke ina geron yake na hada ko furace nasha.

Aymah da tabi Jameel da ido ganin duk yanayin sa ya canza ko kallonta baiba tace'' am nace yana kiching.

Deedee tace tom bari mutashi kamin nan ina zuwa ta karasa tana haurawa dakin Adnan .

Inda yake nan ta iske shi kwance yana bacci cikin wahala.

Tsaki tayi tana daɗe hanci kamin ta shiga bude bude taga jikkar aikin shi . zugewa tayi taga kudine gasunan Available.

Murmushi tayi tace to ai hikenan tinda dama kalkashin ka muke dole kacidamu dan uban ka.

Masu yawa ta kwasa sosai cikin kallabin ga kamin ta fito tana hura hanci tace da Aymah ke kwashe geron nan anjima ayi sadaka dashi nidaikam nashiga kasuwa dan yomuna cefane dan yanda ya lalace bazamu yarda kudin nan su lalace da warin kashi ba.


Murmushi Aymah tayi rashin tsoron tsohuwar na burgeta da jajircewa tace tom Kaka kidawo lfy.

Yawwa tace ta dakko mayafi ta fita.

Adaidaita sahu ta hau taje kasuwa ta kwaso kaya na alfarma kaji kau saida Deedee tasai Ashirin aka yankemata su aka gyara cikin wayo tana nuna masu Abincin saidawa zata dingayi dasu..

Napep guda tayo ta dawo .

Gab da zasu shiga kwanar taga mai sayar da Yalo ta saya kamin suka shige.

Mai napep din ya kamamata ya hau kaima ta ciki tana samai Albarka.

Tana kokarin bashi kudin shi motar Dr tayi parking suka fito shida Jameel da wani ɗan Dattijo da matasa guda biyu.

Bayan sun kamama Deedee takai kayan tasasu zubomasu gas kana ta shiga Aiki.

Wow masha Allah zanso kuji yanda gidan nan ya d'umame da girkin dattijuwar nan da babu kauyanci A lamarinta dan gas kai kace tasaba aiki dashi kodan yana karami oho.

Su Jameel kau duka palon suka zauna kowa yunwa na sake tasomasu Saboda kamshin Girkin Deedee.
Yayin da matasan suka haura sama dan gyara Adnan.

Kwance suka iske shi ya baje yana kuka kashirɓan da surutun da ba'agane miyakecewa cikin karyayyen Halshen sa.

Dakyal suka gane ashe Allah ya isa Abdulkarim yake cewa ba kakkautawa yana kuka.

Dariya suka fashe dashi kamin dan iskan cikin su yace baka tubaba ɗan Kwal uba ya karasa yanama Adnan cakulkulo da faɗin" kamoshi nan ɗan nakasashen Banza Mai kan kwakwa kamo shi nan yakarasa yana matse hancin Adnan.

Kuzo kuga zillewa wajen Adnan da kwabe fuska da sakin maganar shi cikin sauri.

Dariya gudan yahauyi harda rike ciki kamin sugama iskanci suka burkitashi kamar kayan wanki sukamai tsirara.
Nan ma saida suka dinga tsokanar shi kamin su toshe hanci suka kai shi Toilet gaban shower suka kwantar dashi ƙasa suka kunna ruwa mai bala'in sanyi ya dinga sauka kanshi.

Far far far yadingayi da ido kamar zai shiɗe kamin su kashe suna fadin ubanwa zai sanya hannusa jikinka katon banza sai kace ka daukemu jahilai irinka dole ka Bari ka jiƙa kana asama tsintsiyar da zata fiddaka.

Saida kau suka bari an dauki lokaci kana suka sanya Tsintsiyar kwakwa dake Toilet din suka hau durza shi kamar sun samu turken Dabbobin da ba'ataɓa wankewa ba.

Sosai Yake kuka yana Ɓare baki amma ba wanda yabi ta kanshi saida suka gama suka burkitashi da tsintsiyar suka hau yimai tsarki suna sokamai ita cikin fata da gangan sai ihu yake yana gwaranci.

Bayan sun gama suka sake
Kamoshi kamar Ragon da aka yanka suka maido daki suka samai kaya kana suka kamoshi suka fito dashi palo daidai lokacin da Deedee ta gama girkin lafiyayyan tuwon semo dinta dayasha miyar kuɓewa danya ga tantakwashi aciki da manshanu sai kamshi yake.

Akaro na farko Adnan yaji yana bala'in son tuwo da wannan miyar mai tado tsohuwar yunwa.
Waigawa ya fara yana baza ido yana fadin.

"A tubomani yunwa niteti
Azuboman yunwa nikeji.

Deedee ta kalle shi tace yunwa kakeji yaro a zuboma?

Da sauri ya dagamata kai tace .
zakaci abinci kuwa tinda dama ka kasayar ai dole ka nemi sabo.
In dai wannan ne nama tanaji tayi kiching ta dakko wata robar almajirai ta kawo gaban shi tace.
Dama ai saida na dibarma rabonka kar Allah ya kamamu ta karasa tana turamai kwanon robar gaban shi.

Da ɗayan hannu shi ya lallaɓa ya buɗe .
idon shi ya sauka akan garin kwaki da yaji da manja.

Kallonta yayi irin kallon ke wacece.

Ni makwafciyar kuce nazo zama da itane kamin Allah yabata miji nagari tayi auranta kaikuma kai maza ka gama akai ka kauye dan ubanka Deedee ta karasa tana zaromai ido.

Su Jameel dake cin tuwo suka hau dariya sosai irin yanda take abu da kwarin gwiwa.

Tura kwanan yayi gefe kamin yace.
Tete mate ta falko da dan fala katewa a layuwata kamin wannan tegun dukkan tu wallahi ya nuna wayanda sukamai wanka da su Jameel.
( Kece mace ta farko Arayuwata da zan fara kashewa kamin wannan shegun)
Idonshi ya suaka akan Aymah dake cin abincinta cikin natsuwa.


Kete ta karshe matiyatiya.
(Kece ta karshe matsiyaciya)

Murmushi tayi tace kamin ka kasheni aini gashi na kashe rayuwar takanwawa kawai bakauye ,Jahili yanzu zan nunama kai ba komi bane ta watsamai yawu a fuska.

Iya takaici yaji gashi kowa abinci yake ci babu mai kallon shi.
Ganin zai iya mutuwa yaja robar yafaraci da hannu sa mai lafiya.
Ukku yaci ya ture dan baitaɓa cinsa ba.
Babu wanda yabi ta kanshi saida suka gama Deedee tace'' Kai Jameel dauki wayar banza kirawo yan iskan nan masu bakin glass da matar shi tace suna zuwa ɗaukar shi cemasu yace abari zai nemosu bayajin daɗi.

To yace ya dauki babbar wayar tashi yaganta da security.

Miye possword naka yace yana kallon shi.

Adnan ya juyar dakai cikin tafasa zuciya da tinanin abinda zaimasu duk ranar daya ganshi tsaye da kafar shi.

Ganin zai batamasu lokaci yasa Jameel fizgo hannuwansa ya dangwala ta bayan wayar take ta bude ya fara shige shige last call din shi da yayi ne yabi.
Bayan an dauka ya mikama Aymah anan ta sanar dasu bayajin dadi yace subari zai nemesu.

Fatan Alkhairi suka mai ya aje wayar Aymah tace. tom tashi kabar gidan dan kaine da bari nikam dai zama daram daram sai na nemeka kazo.

Zai fara kururuwar ihu katti nan da suka hau gyara saman dakin nashi suka sakko sukai sama dashi .
Wannan Dattijon dake nuni da shine mai gadin Dr ya bisu yana nunamasu hanya.
Cen wani kauye mai bala'in nisa suka kai shi aka jingine kasan bishiya bayan sunba wanda zai dinga kula dashi 5k da ledar garin kwakin shi sukai gaba Abin su.

Ɗan sauran kudin Adnan Deedee ta dauka da yamma ta saimasu katiffai don tace ta dawo gidan saitaga abinda zai turema buzu nadi.
Dan barinsu agidan kamar sun tonama kansu asirine kuma idon mutanan shi zasu dawo kanshi wannan shawarar da suka yanke yasa Dr ba Aymah wayar tashi da suka riga suka ciremata possword gaba daya dan duk wanda zai kira ya sameta..

Da yamma Deedee taje gida tamasu bayanin abinda yafaru duka sunsha mamaki daganan sukai fatan Allah yasanya Alkhairi ta nunamasu saboda kadaici tanaso ta zauna da Aymah dan debemata kewar Iyayen ta.

Amsawa sukai baki daya dan sun aminta da shawarar Tata

Rayuwa suka fara mai daɗi Tsakanin Aymah da Deedee komi cikin jin dadi da walwala .zaman Deedee gaban Aymah ya mugun debe mata kewa da kuma dawo mata da farin cikin data rasa na rayuwa.
Adnan kau ba kasafai take tinashi ba tinda ba Alkhairi bane a rayuwarta.

Jameel kau sosai yake cikin damuwar da duk iyayen shi sunyi tambayar duniya yaki cewa dasu komi.

Da yamma yayi shirin shi tsaf yayi bala'in kyau cikin wata brown din shaddar daya dinka ga wata sallah dabai fiya sata ba ya kafa hula coffee ya fesa turaran sa mai saukin kudi wato Emergency.

Tinda ya fito Malam ke fadin masha Allah yau kuma sai ina Jameelun Deedee kamar wanda ya samomuna sirika matsala daya dai babu walwal a fuskr ka.

Dan Murmushi yayi yace zanje naga Deedee.

Murmushi kawai Inna su tayi tace dan Allah ka gaishesu da Aymah.

Tom yace kamin yakama hanya ya tafi.

Zaune suke a tsakar gidan da yanzu yazama wajen shan iskan su Deedee ta dafamasu gyada sai cin abinsu suke suna fira.

Da sallama ya shiga dukkan su suka zubamai ido bayan sun amsa.


Deedee ya gaida kamin ya dan saci kallon Aymah ya ɗan turo baki.

Itama Kallon nashi tayi kamin tayi dan murmushi tace" ina kwana Jameel.

Lfy yace yana dan hade fuska .

Deedee ta rike haɓa tace Jamalu minike gani haka wanga lamari tafa girmema?.

Pink lips dinsa ya turo yana fadin to ni ba Namiji bane .

Ido suka zaro su duka kamin Aymah tayi dariya tace "hakane kam sannu da zuwa ta tashi tayi ciki dan kawomai ruwa.

Zama yayi Deedee ta kamo hannushi tace "Dan Allah da manzon sa mike damunka Jameel, mahaifinku yace na tambayeka dan Allah minene ko son umma ne yamaka yawa?

Aa Deedee,Abu daya ne ke damuna arayuwata.
Taya zan iya samun sana'ar da zan rike ku a halin yanzu.
Deedee kayan abincin kufa yayi kasa.

Aymah maca ce Deedee tana bukatar yan Abubuwan rayuwa na mata.

Deedee tayi tagumi tace wallahi hakane da ɗan pampas din nan na zamani da suke likawa in suna haila da kuma Turaruka gata da son gayu ni nama Manta bansawo mataba danaje sayayya.

DeeDee zan koma sana'a ta ta da gaskiya bazan iya ganin Aymah ta tagayyaraba asanadina ta salwantar da dukkan abinda ke garetafa Deedee.

❤️ MATAR OGA NA ❤️

Mallaki
Ummy Aysha

Domin mallaka naki ki biya kudin ki ta account Number nah kamar haka
9064260199 Amina dahiru OPAY BANK saiki turo shedar biyan ki ta Whatsapp number nah 07038423451

Page 13

Deedee taja numfashi tace.
Hakane! shiyasa nima kaga Dukkan wani abun da zanyi na faran ta mata inayi saboda wannan yarinya Wallahi inajinta tamkar kai din nan, ina son Ummu tana da kyakyawar alaka ,tana da kuma saukin kai ,bata da kyamar talakka som.
Kai namiji ne Jameel jajirtaccen daya kamata ya tsaya da kafar sa. na baka goyon baya dari bisa dari.
Dukkan abinda kasan zakai da karfinka da gaɓɓan ka in dai aikine na halak, kai koda kwasar kashi ne kam na baka dama kaje kayi ka wadata da abinda Allah ya Hore ma..

Mahaifin ka Kuma tinda Allah yasama sana'ar shi Albarka kabar shi ya rike nashi iyalin ,kai ka zamemata garkuwa ko nace ka zamemuna, Allah ya sanya Albarka ga dukkan abinda zaka taba yamaka jagora zuwa ga neman Halaliyar ka duk inda take.

Ameen yace yanajin dadin addu'a ta.

Aymah kau dake tsaye bayan su tin sadda taji ya ambaci sunan ta ta tsaya cak.
Wasu hawaye masu bala'in zafi suka zubomata,ashe duk inda take kai farar zuciyar su Deedee da zuria ta sun wuce myan,Taya,zai wahala yazo ya kashemata? Akanta kawai.

Idon ta ta daga sama tana wani nazari.
Saidai ina lokacin bayyanuwar hakan bai ba gareta, Bayyana wannan ɓoyayyan sirrin nata kamar watsa sabuwar rayuwar da xata gina ne anan gaba .

A'hankali cikin sanyi jiki ta karasa inda suke ta ajiye masa flat din da tasamasa ruwan pure water mai sanyi dan tini suka maido fridge din Adnan palon ta na kasa.

Daya ya dauka yace Nagode kamin Deedee tace''

Please Login or Register in order to submit comment