Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwalo duka idanuwan sa.

Cikin dakiya ta dago kanta tare da sanya shower ruwan sanyi ta tsarkake kanta tana cije baki ta mike tare da dafa bango zata fita duk da jirin da takeji..

Da sauri ya kai hannu zai kamata cikin fusata ta juyo cike da rawar murya tace''karka taɓani Jameel baka da amfani, ka rubutaman takardata dan baka dace daniba , Tinda ka kasa bani lokacin ka ina cikin wannan yanayi...Tul tul tashiga tari lokaci daya jini ya ballemata ta hanci da baki.

Suuu tayi zatafaɗi ya daka tsalle yayi kanta hankalinshi a bala'in tashe ya fara jijjigata yama rasa ya zai mata.

Cikin ihu ya fara jeramata kira amma ina idonta rufewa kawai yake neman yi.

"Tir da halina wallahi,Tabbas ban cancanci zama miji gareki ba nima nasani,wallahi wallahi narasaki bazan yafema kaina ba Aymah, wallahi nayi Alkawari akaro nabiyu dan Allah kitaimaki rayuwata yace cikin tashin hankali rigar tashi kam duka ta lalace da jinin ta,idama cire ta yayi tare da dorata jikinshi ya fara kwakumeta cikin gushewar Hankali kai kace nono zai bata.
Aymah ! Aymah tashi,wallahi zaki tonaman Asiri, Dan Allah kirufaman Asiri Aymah nah karkimun haka dan Allah raina fansane ga lfyn ki Aymah kitashi, Wallahi kika mutu sai na biki,domin zamana bashi da amfani, Deedee'n ki zata tsanane,iyayena zasu tsaneni,mutanan da suka bani ke zasu tsaneni, Dr Abba zai tsane Ni Kinji.

Ajiyar zuciya kawai tahau saukewa kamin ta dan bude ido ta kalleshi kwallah na zubomata maraicin datake ciki kadai ya isa ya sata kuka tin dazu suke abu daya ita mace bataji kunya ba tinda ya fadamata yazama mallakinta tazama nashi ta bashi ragamar rayuwarta,
Amma zai tsayamata wasa da hankali.

Ganin ta bude ido yasa ya mike da sauri yana fadin Alhamdulillah yah Allah.

Jikinshi har rawa yake wajen dorata a kujera dake ciki kana ya shiga hada ruwan wanka,zafi zafi yake komi,cikin sauri ya ciremata rigar nata tare da cire sket din baki daya.

Zo kuga sauke ajiyar zuciya wajen Jameel, dauriya kawai yake amma Aymah ta kashe shi tagama da rayuwar shi.

Tsabar rudewa da killing yasomata wanka saida ta lura ta mirro kamin ta janye ta nunamai sabulu.

Zanso kuga yanda akai wannan wanka mai cike da laguje laguje da neman sanya matashin Saurayin nan sumewa,dan sai yayi nisa a wankan sai yaja numfashi da ajiyar zuciya da karfi kamin jinin jikinsa ya dawo aiki..

Saida yagama mata komi kana ya nadeta a sabon towel din dake wajen ya fita da ita ya gyaramata gadon kamin ya kwantar da ita yana tinanin abinda zai samata.

Lokaci ya kallah a kallah sunci fiye da 30mn har an'mafara kiran Sallah.

Da sauri ya ɗauki kayan fruit din ya dan bata kamin ya bata ruwa ya gyara mata jikinta yasa ta fuskanci alkiblah daga kwance ta gabatar da sallolin da ake binta..

Toilet din ya fada rigar shi yabi da kallo da suk ta ɓaci.
kai kawai ya gilgiza yafito ya dauki Babba rigar yasa ya bude kofa zai fita dan zuwa ya tsarkake jikin shi ya canza kaya.

Ido hudu sukai dasu Deedee gabaki dayan su harda Maman shi dasu Manager Dr Abbah tsaye gefe yana zare ido.

Deedee kau kuka ta fasa tace *wannan ai shine ƙudira sama liman da wawan zama*, to kai jinya kayi ko fyaɗe kamata, Jamilu jibi rigar ka jibi shigar ka ....


❤️MATAR OGA NA ❤️

UMMY AYSHA
Page 23

""Jameen kau Gabaki ɗaya kunyar duniya ce ta rufe shi, kai Deedee bataiba akwai taɓargaza,cikin satar kallo ya kalli Inna su dake bin rigar sa da kallo bata ko kyaftawa..
Idon da suka hada yasa da sauri ta juya kanta gefe gabanta na bugawa.

"Jeka shirya Jameel kayi sallah kaji manager yace yana ɗan murmushi.

Wucewa yayi Dr Abba na mara mishi baya yayin da Deedee tace.
Kai kutsaya nan naga sai ƙoƙarin turo kawuna kuke kamar macizzai ai kwabari nashiga naga wane yanayi take ciki ko.

Da to suka amsa suna yaba rikicin Deedee dama ba shigar zasuyi ba fa.

Da sallama tashiga tana sake rushewa da kuka tace "Aymah ashe shegen yaron nan hawan ƙawara yamaki,kai jama'a kaga mutum sumul sumul kai akas ashe mugune.Yo aini in an'shekara ceman Jameel zai iya bugama mace iska wallahi ba yarda zanba sai gashi naga ishara,Yo wannan ai dole likita yazo ya dubaki dan wannan jini yafi karfin na budurci sai dai in mahaifarki ya taddo dogon banza dogon wofi..

Aymah kau tanajin surutun Deedee dakyal ta dan fara bude ido kamin ta saukesu tass akanta.
Dan murmushi ta saki tana mikamata hannu cike da so da kewar Dattijuwar data zame mata uwa uba .


Hawaye ta share tace. "sannu Aymah ciwo biyu baiwar Allah,nidai kam baccin ɓargona ya fara taushi danayi jinyarki, Da ace da baki ake jinya da wallahi sai dai aga kin mike ras to amma gaɓɓai ke aiki.

Aymah kau cikin ƙarfin hali taso magana nan danan jinin nan ya sake ɓallemata.

Ido Deedee ta zaro kamin ta kwallah ihu agigice tana fadin" lukuta kai dokta, zo dan uwarku zo kuga nabani wallahi ba shaketa nayiba aduba matakan tsaro na na'ura da kukesawa kuna ganin mutum da aljan dan Allah ashe Jamalun Deedee ba fyaɗe ya aikataba hifufuuuuu ni Deedee mai kunun aya za'a ɗaure ni kwana na bai kareba ta karasa cikin gaskiya da gaskiya tana rushewa da uban kuka.

Aymah ta galabaita sosai Wannan aman da tasake hakan yasa tayi luuuuu numfashin duka ya ɗauke.

Tashin hankalin da Deedee tashiga bazai faɗu ba, da kyal da rarrafe dan kafarta bata daukarta ta karasa wajen kofa ta buɗe.

Ido ta zubamasu kamar mage takasa magana.
lokacin yayi daidai da karyowar kwana Dr Abbah da wani DR Cikin sauri da zafin nama .

Da hannu ta dinga nuna masu ɗakin aguje suka shiga yayin da Maman jameyel ta kama Deedee dakyal ta mike tsaye kafarta na wani mahaukacin rawa , hawayen ma sunki sakkowa yanzu sai buguwar zuciya balle taji dadi, kawai tana ganin Aymah ta tafi ta bar ta dan bataga alamar tana numfashi ba..

Dr Abbah kau yana ganinta cikin wannan halin aguje ya fito ya fara kwalama Nursing ɗin kira .

Bayan sunzo ya umarce su da su shirya Emergency theater yanzu.

Okh sir! suka amsa a guje suka wuce.

Jameel

Kai tsaye officer din Dr Abbah ya faɗa som zuciyar shi ba daɗi.

Yana turawa Dr Abbah ma na turawa rai bace yace" Jameel miye haka?.

Dan kallon shi yayi kamin ya kawar da kai yace" kaima ka yarda da rikicin tsufan ta,? wai miyasa Deedee ke sakin magana ne duk sadda tazomata,dama A riga za'aga alamar namata fyaɗe? Hmm kajifa yafada yana cije lips ɗin sa sosai cikin takaici.

Ajiyar zuciya Dr Abba ya sauke tare da bashi wata leda yace *"ga kayan nan na sawomaka ka shirya kayi sallah, sukuma wayan nan sai kaje kasamata.

Karba yayi yamasa gdy ya aje saman kujera yashiga Toilet dan tsarkake kanshi..

Abinci yafita ya samo mashi dan yaga baici komi ba koda suka je gidan Deedee.
kamin ya dawo ya aje da niyyar in jameel din ya gama yaci Wata Nursing ce dake reception ke sanar dashi dakin mai Number 5 akwai matsala mafarin fitar tashi kenan ya haɗu da Dr Abbas suka tafi Ashe Aymah na cikin mawuyacin hali.

Jameel kau bayan yayi wanka ya ɗauki haɗaɗan pakistan ɗin daya saimai yasa kana ya fara Sallah.
Yana cikin Sallah yaji wayar da Abokin nashi keyi,dakyal yagama yana sallamewa ko Addua baiba ya fita.
Daidai lokacin da aka turo Aymah dake sanƙame akan gado zasu shiga da ita.

Yah Allah yace cikin karaya yana kama gadon aka shiga da ita.

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo mai na zallar tausayinta da kuma shaukin so da begenta daya nunku a zuciyar sa.
Cikin rawar murya ya faramata Addu'a.
Yah Rabbil Alamina kasa aikin nan ya zama silar yayewar damuwarki Sweetheart, Allah ya koro da farin ciki cikin rayuwarki Aymah,ke mutuniyar kirkice bazaki taɓa wulakantaba in sha Allah,Ribar hakurin ki na nan kusa in sha Allah, Allah yabada Sa'a matata ya karasa yana sakarmata wani zazzafan kiss a goshi.

Gabaki daya saida matan dake wajen jikin shi yawani bada yarrrrr dan sun fahimci sahihin son da yakemata wanda maza ke wahalar bayyana wa a yanzu gashi dama sun mugun dace da juna..

Dr Abbah ne ya shigo cikin shiri da wasu Dr's A bayan sa..

Dan ɓata fuska Jameel din yayi cikin kishi daya gansu tare da haɗe fuska.

Murmushi Dr Abbah yayi yana buga kafadarsa yace" in sha Allah komi zai tafi daidai kaji,ka koma wajen su Deedee ka lallashe su.

Bayaso ya shiga hurumin su da bazai fito ba.
Amma haka ya daure ya fito kofar farko yayi zaune yana buga tagumi.
Ganin babu inda zaman zai kaishi ne yasa shi tashi ya hau wani carpet din dake gefe ya fuskanci alkiblah ya fara sallah isha kamin ya ɗora da nafila yana fadama Allah damuwarshi da nema mata sauki akan aikin da za'amata.

Kimanin awa daya biyu amma basu fitoba Ya salam zuciyar shi har wani dakan sittin sittin take.
Lokaci daya Jikin shi ya fara rawa tsoro ƙarara ya bayyana ga fuskar shi.

A kasalance ya mike ya turo kofar ta biyun ya fito.
Gabaki dayan su yanda suke haka sukayo mai cah kamar k'adangarun da sukaga Taliya da manja.

An kammala Jamalu? Deedee tace hankali tashe dan tin dazu datayi mutuwar tsaye bata sake maganaba sai yanzu.

Kai kawai ya gilgizamata tare da komawa gefe ya zauna yanajin wani sanyi na huda kowace ƙofar huda gashin dake jikin sa.

Karfe 10:15pm aka bude kofar Dr Abbah ya bayyana yanata hada gumi dashi da abokan aikin nashi ..

Rufamashi sukai kowa tambaya yake ya lfyn ta.

Alhamdulillah da sauki munyi cikin nasara sai fatan Allah ya tadata lfy, yanzu muna bukatar akawomata mayafi..

A zabure Deedee tace ba komi akwai ɗan buje jikina bari in baku wannan , kanma suce wani abu ta fizge nata ta bashi tare da sauke mayafinta kasa.

Jameel ta kallah afusace tace to mata maza zazzabin gadon ne ya lulluɓeka ko kanajin ana faɗin an'kammala kai jama'a nikam badan ni na wanke kaba na kaika akama shayi wallahi da cewa zanyi mata mazane...

Banza yamata ko kallon ta baiba Saima Hankalin shi daya mayar kan kofar har inda yaga an turo gadon da Aymah ke kwance akai kamar gawa.

Da sauri ya mike ya isa wajen yana zubamata ido.
Tayi wani fresh tana sanye da blue din rigar asibitin sai Yar hula mai net da aka tura gashinta ciki, fuskar nan tata fayau,gashin gabon goshinta kam yayi luf-luf kamar wanda yasha ruwa.

Gadon ya kama A'hankali suka dinga turata har dakin da aka ware mata a vip site.
Fadar tsarin wurin ma ɓata lokacine dan komi yaji,ga na'ura sanyaya daki (AC)sai busawa take.

Sadda suka shiga Jameel yayi mata shimfida suka samu dakyal suka kwantar da ita a kai tare da sanyamata wasu naurorin a jikinta .

Dr Abbah kam Su Deedee yama iso suka shigo suka dubata cikin natsuwa kana suka fito.
Jameel ya bisu abakin wajen suka tsaya yanata watsama Deedee harara kasa kasa batama gansa ba.

Inna su tace "Wannan yaron Dan Allah ka kula da ita duba da halin da take ciki,na tabbata in itace zatama abinda yafi haka kaima shedane..

Deedee tace "ah'toh Baraka kwara dai ki waye ki faɗamasa gaskiya tinda ni ya rainani, kullum kanki ƙasa kamar k'unk'uru waike dan fari kike jima nawie, kuyita cutar kanku kuna wani sussun ne kai ,Ai Wlh babu wanda yaman nakuda babu wanda ya isa yaja kuma na ɓoye soyayyar yarona a cikina ta kumeman ko ba hakanan ba Habu?
Yo koshi yarone tsayama kuga.
kamoshi nan kamoshi nan ta fada tana jan gemen malam.
Habu.

Gabaki dayan su dariya sukasa har Jameel dake cikin damuwa saida yayi murmushi.

Tace yawwa Alhamdulillah zamu tafi zan bada sako Sadam ya kawoma na abinci da abun sallah, zai biya ta gidan ku ya hadoma da yan kayan buƙata..

Dr Abbah yace su barshi ya tanadar mai komi gobe sun kawo .

Gdy suka mai suka wuce.

Ciki ya koma yaja kujera ya zubamata fararan idanuwan sa masu shegen kyau ko kyaftawa bayayi.

Dr Abba ne ya shigo da kaya A hannusa ya aje tare da ma Jameel Bankwana akan zaije gida anjima Dr Abbas zai shigo ya dubata.

Kallon shi yayi yamasa gdy tare da fadin wannan kayan da aka jibgamata bai yawaba kuwa .

Ido ya zaro yace bakaji Sanyi ba Jameel.

Kai ya sosa yace zan Iya ragemata su ..

❤️MATAR OGA NA❤️

UMMY AYSHA

Page 24

Ido Dr abba ya zaro yana nuna mishi cttv camera dake ciki kota ina dan lura da abinda ke faruwa daga majin yacin su cikin sauki.

Ɗan tsaki yayi yace amma acen ɗakin farko babu ko?

Dr yace "Baka da gaskiyane da kake tambayata acen babu ko kayi wani abun ne?.

Ido ya dan juya yana hura hani yace "ai halaliyana ne koma miye yafaru lada zamu samu.

Murnushi kawai yayi yace lallai yaro yayi baki jiya kadai da doramasa igiya.
Murmushi sosai Jameel yayi yace Saima ta warke.

Sai da yaga Jameel ɗin ya ɗan natsu kana yamasa sallama ya fita yayin da Jameel din ya rakashi ya rufe kofar.

Toilet din ya shiga ya watsa ruwa ya ɗauro alwallah ya fito.

Akan kujerar da yake akai ya zauna yana daukar Drinks ɗin exotic ya sha dan bayajin cin komi .
Sadda ya gama ya tashi ya hau sallah yana nema mata sauki wajen mai duka.

Har ƙarfe ukku yana zaune kana ya farajin kamar motsin ta ,yana mikewa yaji ana bugo kofar .
Dr da zai dubata ne kamar yanda aka cemai, nan ya sake dudduba jikin nata ya mata allurai da sake samata sabon drive bacci ya karayin gaba da ita.

Shikam Sai da ya gabatar da Asuba kana ya samu ya dan kwanta jin yanda bacci ke fuzgar sa.

Bai jima da kwanciyar ba ya farajin nishinta kasa kasa tan fadin" Ruwa.

A zabure ya mike ya isa inda take,idonta fess akan shi, haka shima nashi da suka canza kala zuwa na mai bacci ya zubamata su a narke,cikin kuma farin ciki yace" sannu kin tashi,mikike so? ina ke maki ciwo? yanzu kin fara magana?

Dan murmushi tayi tare da jan hannunshi cike da tausayin sa dan tama jima da tashi taga ya dan fara bacci.

Cikin muryarta ta majinyaci tace "sannu da kokari rabbi yabaka tukuicin Aljannah kamun bautar da bazan taɓa mantawa ba, kana ka nunaman kai ɗan Halak ne daya gaji karam ci.

Murmushi yayi yana sumbatar hannun nata yace "duk cikin Hakkin kine daya rataya wuyana, so wannan ba damuwa bane yiwa kaine kinji...

Ido kawai ta dan lumshe mai cike da mabayyanin so.

Gira ya daga yace toya muje ayi wanka?

Harara ta bankamai ya saki murmushi da faɗin ina zuwa ya bude kofar ya fita.
Office din Dr Abbas din yashiga nan yaganshi yana sharara bacci,sallama yamai bayan sun gaisa ya fadamai ta tashi.

Tare sukayi dakin Aymah ya dubata tare da faɗin" Alhamdulillah aikin nan yayi kyau yanzu duk zamu ragemata wayan nan karafunan ya karasa yana jajjanyesu,tare da kiran wata nurse tazo ta fitar mata da robar fitsarin dake jikinta wacce tinda aka fito da ita akabar ta da ita.

Kallon Jameel yayi yace zaka dan mata brush ka wanke mata jikinta da ruwa mai ɗumi, amma sai kasa yan dubaru ba'ason tana motsawa sosai saboda ɗinkin mukesl ya haɗe...

In sha Allah yace ya rufe kofar kamin ya cire rigar jikin nashi,ya aje gefe dagashi sai dogon wando da vest ya shiga toilet ya dakko wata karamar roba tare da bude sabon brush din da Dr Abba ya ajema su, ya matsa maclean ya dan d'ago gadon kamar yanda ya cemai.

Haaaaaaa!! yace yana dan zubama gashin girarta ido data lumshe su sunyi yarr abin su ..

Kadan kadan ta fara budesu.

Ido ya zaro yana dan ja baya yace" Aymah minai miki ko na famamiki, sannu zan kiyaye in sha Allah bazan ƙara ba kinji?..

Kai ta gilgizamai cikin sanyin muryarta tace.

"Ashe dai kaine zaka zama farin cikin rayuwata, Ashe Allah zai nunaman ranar da zanga nima anaman tarairaya danake so kuma nike nafalki,ashe zan iyajin dadin miji a rayuwata,ashe zan iya moruwa da hidimar mijina akaina,Ina sonka Jameel ina sonka,ina rokon Allah yabani ikon kyautatama,ka maye mun gurbin duk abinda na rasa,na tabbata ko bana da kowa a duniya, kai ko daga sama na faɗo nason bazaka gujeni ba,ina sonku kaida family naka haduwarmu Alkhairi ce..

Cikin jin dadi da addu'arta gare shi ya ɗan gyara tsayuwa cike da burgewa yace .
shin inba ma matata ba waye zanwa,kana awajenki ne aiki amma awaje na hakkin kine nike saukewa,Aymah ke ɗin nan kin man halacci a Rayuwata da har kika iya auran bawan ki.
Karki manta Nifa ALMAJIRIN GIDAN ki ne,Amma kika kyautataman ta hanyoyi da dama , Daga karshe kika aminta da muyi AURAN YARITA dani,ni yaro ke babba, Baki taɓa damuwa akan ZAMAN TASHA danayiba, Amma kika bani so da yarda,kinyi hakuri akan zaki zauna dani duk da bana da zurfi a karatun boko amma baki damuba koda duniya zatace kin AURI UZTAS da baida ilimin boko, kedai baki damuba saboda kin duba kin hanga kinga babu wanda ya CANCANTA dake saini, AYMAH taya za'ayi bazan tashi tsaye ba koda zan zama ƊAN DAKO dan kyautata miki,,Wallahi kinmin halacci sosai kin kuma nunaman ke ƊIYAR SHEIKH ce da kuka samu tarbiyyar rashin gudun talakka,Shiyasa nayi wuf na Biya SADAKIN AURE tin kamin wani yaman kafa,Ngd ma Allah daya bani ke amatsayin MATAR AURE Na da nike alfahari da ita,Agefema zan iya gdy wa Adnan daya daukeni aiki har na haɗu dake gashi yanzu duniya ta shedacewa na Auri MATAR OGA NA..


Kuyi hkr ba yawa hannu daya ne nike amfani dashi bana sauri

MATAR OGA NA

UMMY AYSHA

PAGE 25


Ɗan farr tamai da ido kamin cike da so tace " ina sonka,ina son kalaman ka masu sanya natsuwa.

Gdy nike Hajiyata yace yana fara goge mata baki cike da lallami da kalamai masu daɗi..

Bayan ya gama yaje ya zubar ya debo ruwa a boket masu ɗumi..

Ido cikin ido yace.
zamuyi wanka Hajiyata gyara.

Ido ta zaro tace A'a ina? Nikam ka barni kawai.

Nooo jiyafa har duka na kikai ,kikace na sakeki, kawai dan naji kunyarki na kasa miki,shine kuma yau zaki canza bayan kin wayar mun dakai kin mayar dani cikakken Namiji,ina bazai Yiyuba ni zan goge matana da kaina.

Murmushi tayi tana tino kalamanta najia, sosai taji kunya ita kanta tason ta saki layi,kasa tayi da kai tace.
jiya ina bukatar taimakon ne,amma yanzu Alhamdulillah da sauki zan iyafa.

Yeh nasani amma dai kiyi hkr bazan kalleki ba zan miki ido rufe kin yarda ? Amma fa nasamiki Yaji a ido zan kai kaina Court da ba Afuwa kin yarda?.

Aaaa Aaa Babyyy som ban yarda ba,Babu wanda ya isa ya taɓan lfyn ka ya zauna kalau,Zan yi yaki da dukkan wanda zai taɓa rayuwata tace cikin shagwaɓa tana turo baki.

Ya salama saida Jameel yaji kalmar Tata har cikin kwalwar sa.

Akasalance shima yace. To naji Sweety nah Nagode kadan kadan zanmiki,banaso jikin ki ya miki nawie ba..

Shuru tayi tare da lumshe ido.

Ahankali ya yaye zanan dake rufe jikinta ba komi kam kamar yanda Yayi tinani , tsaye yayi yana zubama halittar ta ido mai tsananin kyau da ruɗa lafiyayyan mutum,tsawon lokaci kamin ya sauke ajiyar zuciya ya fara jika towel din cikin ruwan dumin yana gogeta tass, a dubarance kuma yana yamutsa ta duk abinda yake tana jinshi amma ta kasa bude ido dan wata irin kunya takeji kai aure akwai sirri acikin sa.

Shikam saida yagama kana ya ɗauki sabon zanan gadon dake gefe na Asibiti ya rufamata.

Gefe ya koma ya jingina da kofa A'hankali yace" Sweetheart.

Shuru tamai sai idonta daketa kyaftawa alamar batai bacci ba.

Dan Allah kibuɗe idonki inaso naga kwayar idonki.

Uhm uhm ni kunya nikeji tace tana turo baki.

Munfa zama daya Aymah haka zamuje gidan mh kinamun,kina so na kalli wata awaje,kinaso ki tauyeni ne har nafarajin sha'awar mutanan waje,Ki zage kimin abin sa nike so shi zai sa babu wata ya macen da zata burgeni ko kinaso namiki kishiya?.

Da sauri ta buɗe idon ta ta watsamai harara tace.
gaskiya karka sake cewa zaka kalli wasu ashe zaka iya haɗa sona dana wata ? Zaka iya shearing dina da wata da har kake tinanin min kishiya Baby?

Dariya yayi kadan ya matsa wajen ta yace" bagashiba nasa kin bude kinyi kyau sosai ,Ina mai miki Alkawari da yar dar Allah kece kawai a birnin zuciyana,Koda Allah ya tsaraman zanyi fiye da ɗoya to namiki Alkawari bazata kaiki ba balle ma bana da wannan ƙarfin na rike mace har biyu..

Ido ta lumshe tana murmushi tace Allah yasa da gaske, Allah kuma ya dorar da son da kakeman har abada.
Nayi missing Deedee nah sosai fa ina kewar ta .

Ameen sweetheart.
Hmm kibar Tsohuwar nan nikam babu kewarta danayi dan yanzu Deedee tana ta samun rikicin tsufa,nan yashiga bata labarin abunda tamai jiya.

Murmushi sosai ta dingayi wanda da tana da lfy sai tasha dariya.

DeeDee nah kenan Allah ya karamata lfy da nisan kwana..

Ameen Sweetheart mizakici?mikuma kike so na miki.

Mifa zan bukata ina tare da kai,duk wani abun da nike so kamin,bana buƙatar komi Baby.

Tom naje nayi wanka kin yarda?

Kai ta jinjinamai tace kaje saika fito.

Kiss ya mannama ta a goshi yace *zaki rama wanda nake miki in kika warke fa ki sani bashi ne kike ci,in so goma na miki in har kinji sauki tom sai kin min so goma kin yarda?.

Ido ta rufe cike da kunya shikuma yayi murmushi kamin ya mike yashiga toilet din.

Sadda ya fito tayi bacci hakan yasa shi bude kofar ya fito dan son zuwa gida ya ɗakko mata abinda take so.

Ahanya suka hadu da Dr Abba da da matar shi sai yaron su guda biyu ɗaya namiji sai mace hannusu rike da basket.

Ango ango yashiga zaulayar sa tare da faɗin.
munbarku ba komi Sorry fah madam ce ba lfy sosai shiyasama muka fito yanzu..

Bkm Dr barka da kwana ya fada yana mikamai hannu,Baya sun gaisa ya juya suka gaisa da matar .

Ango ya mai jiki? .

Alhamdulillah da sauki sosai yafada yana bama yaron hannu suka gaisa.

Ya sunan ka ya tambayi Yaron.

Sunana Abul khairi,
Nikuma sunana
Ummul khiri inji macen tana turo baki.

Dariya yasa cike da sha'awar yaran yace khairi, kin san ni?

Aa ban s@n kaba Daddy ne yace muzo muga Friend nasa da Aunty bata lfy.

Cike da son yaron har cikin ranshi yace hakane to muje sai kuga Aunty kumata ya jiki ba.

Da to suka amsa yamasu jagora suka shiga har dakin Aymah.

Bayan ya ɗan duba wasu magungunan nata yace .

Jannat ki zauna da ita zan dan ganshi muna zuwa Dr Abba yace.

Ohk my Love sai ka dawo ta fada tana aje ledar hannuta kusa da gadon.

Hannun Jameel ya kama suka fita kai tsaye office din shi suka nufa suka mayar suka rufe.

Kula ya jawo ya shiga zuba masu felfesun yan ciki daketa tashin kamshi kana ya aje ledar Bread kusa da su ya tsiyayamasu Black tea mai kayan kamshi.

Abokina muci wannan na tabbata baka ci komi ba.

Murmushi Jameel yayi yace naci mana.

Tom naji wannan na daban ne.

Nan suka wanke hannu sukaci suka koshi bayan sungama yaba Jameel katuwar ledar daya sawomashi kaya sunkai kala goma yace" ga gudun muwa ta nan bayawa,sauran na wajen tela.

Baki Jameel din ya sak kamin a raunace kuma yace wai miyasa kakeman hidima haka ne,jibi fa abinda kamana dan Allah,.

Kafi karfin komi Jameel awajena bakason yanda na daukeka bane, Jameel an yaudareni anci amanata abokin dana yarda dashi ya rusa rayuwata,shi nike ba sirrina yayin da ya daukan sakarai daga karshe ya nemi lalata da matata Jameel daga lokacin na kasa samun Aboki ko guda saboda na tsorata,kai kam na yaba da halaccinka na yaba da kirkinka da rike takonka Jameel, som baka da rawar kan matasan zamani,nakara sonka ne tun sadda naji Deedee nama faɗa akan baka tarayya da kowa shiyasa na kutsa kaina awaje ka har nasamu ka aminta dani,Dan hala nike da gdy ,ga matana nan Jameel ina so ka hadasu zumunci da matarka ina fatan Allah ya dorar da zumuncin mu har abada,albishir da zanma anan shine yau an'hadama motarka in sha Allah, da Daddare zasu fita gobe su dawo Allah muke roko yasanya albarka da buɗi acikin kasuwar nan.

Cikin farin ciki yabrungume shi yace* wallahi ni nai sa'a, kuma in sha Allah zaka sameni mai amana Abbah zan ruke iyalin ka

Please Login or Register in order to submit comment