Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gadan- gadan.
Kan ta an'kare sai dai tafarajin dakuwar hakoransa kaf kaf kaf kamar zai taune halshen sa.

Kallonsa tayi a tsanake ganin kamar ya fara fita hayyacinsa a razane tace.
" Jameel miye?.

Kanshi ya ɗago duhun wajen bai hanata ganin yanda kwallah ke rige rigen saukar masa ba, da yanda bakinsa ke ɓari.

Cikin mabayyani tashin Hankali tace'' miye haka dan Allah ka tashi mutafi Jameel na hakura wallahii na barwa Allah miye haka kake kayi man magana Please.

Magana yakeso yamata akan ta natsu amma bazai iyaba, "wannan masifa tayi yawa wai waye Adnan din nan ne? ina iyayen sa ne da ya zama kamar Arne som bashi da imani, iyayen matar ka zakasa a kashe?Wai miye manufarsa ne akanta.

Aymah kau da sauri ta tashi tana kalle kalle dan ta samu abinda zata taimakamasa amma ina ba komi .
Aguje tayi gidan su saigata dasu sadam suka kamashi aka shiga dashi nan wajen Deedee har lokacin da zazzabi jikinsa sosai sai layi yake.

Sosai Hankalin Deedee ya tashi cikin kuka ta ce" wai dama baka rabu da wannan masifar ba Jameel."AYMAH wani abu akamasa ne ko wani abu ya faru dashi Jameelu ka zama kamar mace abu kadan ya kayar dakai kai jama'a.

Aymah dake kallon yanda yake haɗewa waje guda ta share hawaye tace" Deedee kawai na faɗamasa ne cewa Adnan ne silar kashe iyaye na.

Ido Deedee ta zaro kamin itama ta nemi wajenta zauna tace" nasani, wallahii nason za'a rina,Ai dama na fadamaku amma bantaɓa tinanin da gaske wannan matsiyacin zai iya kisan kaiba, Wai Aymah bakison abinda ya haɗasu bane Har yanzu?.

Hawaye ta share tana zama kusa da jameel tace" Tukunma dai! Yanzu dai video abun ne muka gano muna kan binciken dalilin daya kawo haka ta karasa tana shafa Bakin Jameel dake karkarwa..

Deedee ma gefe ta matsa ta fara rera kuka tana jama Adnan Allah ya isa da fadin sai ta sake tashi ta nema ta kwatoma Aymah Hakkin ta..

Aymah kau ganin tsananin da jikin nasa yake yasa ta tashi cikin dauriya tanajin kanta kamar zai fashe ta shiga kiching ta debo ruwa a roba.

Haurawa sama tayi ta ɗakko towel mai kyau tazo dashi gaban shi ta ɗan jika ta mikawa Deedee tace "gashi ki dan gogemasa jikin sa.

Cikin kuka Deedee tace" kyaleshi dan uban sa ban gogewa,Kai shikenan da kaji abu ba'a jaje dakai sai kayi Raɓe Raɓe ka baje, To bazanma ba dan ubanka Tacigaba da kukan ta .


Aymah tace Deedee wallahii ba laifinsa bane.
Halittace kowa da kalar tashi.
Suna da raunin zuciyane, Shiyasa kuma irinsu sunfi tausayi da iya kulawa da abinda suke so.
Karkiga laifinsa alhinine yake tayani,wannan ma yakarama Jameel martaba da kuma girma a idona .

Hawaye ta share tare da mikewa tace'' kyaleshi yagaji ya tashi tayi waje kai tsaye dakin Adnan ta nufa a fusace.

Aymah kau ganinta ta maido kanshi cikin tausayi to taya zata iya masa abu shiba muharraminta ba?
Wata zuciyar ta shedamata cewa ai tana da damar taimakon duk wanda yake da bukatar hakan kasancewar ta ma'aikaciyar lfy .

Ido ta lumshe kamin ta rintse ido hannunta har rawa yake ta sa ta dan d'aga rigar sa sama.

Farar vest din shi dake fara sol sai kam shi take tabi da kallo a sace. kamin itama ta dagata tana juya kai zuwa bakin kofar...
Sake tsoma abun tayi ta sakeyobkan fatar tashi data kasance fara sol.

Cikin mamaki tace ashe jikinshi tass tass yake har wani Yellow Yellow fatar keyi ga masifar taushi kamar mai ma fatar Dilka .
Gashin dayama kirjin nasa k'awanya kadai ya isa ya burge lfyayya mace.

Ido ta ɗago da Sauri ta kalleshi taga idon shi a lumshe yake amma ya daina wannan rawan sanyi.

Hannunta tasa guda ta rufe idon ta kamin taci gaba da dan gogamasa yanda ya dace .
Saida ta tabbatar jikin ya ɗan rage zafi kamin ta mayar masa da vest din ta sake jika abun tayi kan kyakyawar fuskarshi da yaune kawai ta taɓa kureshi da kallo Haka.
Masha Allah ta faɗa abayyane tana dan gogamasa akan fuskar tashi har zuwa kan sajen sa dake kwance luff luff...
Rayuwa Aymah na bala'in son Namiji me saje amma Adnan kullum fuskar shi kamar bayan fai-fai ba komi,Kanshi uwa gidauniyar sulba sol waishi soja.

Sadda tagama ta kalle shi fuskar tayi fess sai sheki yake kamar wanda akama wanka.

Murmushi tayi tana matsawa da Hancinta akan nashi ta dan goga nata akan Tsinin nasa tare da fadin kana da Sahihin kyau tamkar mace.

"A jiyar zuciya yaje a kasalance yace .
Namafi macen kyau ya faɗa yana bude idonsa da d'agamata gira guda.

Ya Subhanallahi tace tana neman mikewa tsabar bala'in kunya, bata taɓa tinanin idonsa biyu ba.

Karfinsa yasa ya cafko hannuta tare da mayar da ita ya zauna shima ya tashi ya zauna ya gyara zama yace " Akan mi zaki gudu bayan baki ida aikin ladar kiba? Gaskiya Allah ya biyaki ya miki Albarka.
Tabbas ke din mai albarkace , jini yau ɗaya daga kin dora lallausan hannuki akan gangar jikin dake cike da rauni da cuta farat daya ciwo ya ɗauke, Ngd Allah ya sakamiki da Alkhairi ya baki tukuicin gidan Aljannah.
Aymah ina mai baki hakuri da kuma sake tausar zuciyarki akan abinda ya faru.
Tabbas Adnan ya zalinceki zalinci mafi muni.
Saidai karki manta duk abinda zai faru dama tsare yake cikin kundun kaddara bawa.
Allah shine ke kashewa ya kuma Raya saidai ɗan Adam ya zama sanadi.
Adnan ya zama sanadin iyayenki tabbas wannan yayi Kuskure mafi girma wanda in kika zubamai ido muna nan zakiga D'aid'aicewar da zayyi Ya lalace ,Tun yanzuma kinfara gani dai,Gashi nan ba baki ba kafa kuma babu wanda Allah yasa ma tausayin ya taimaka masa saboda mugun Halin sa..
A shawarar da zanbaki ki tsaya iya tsayawar ki karki yarda akai maganar nan court.
Kibarwa Allah domin kuwa ya isar miki.
Shikuma wanda yake iƙrarin sai anje ki nusar dashi mahimmancin Hakuri da juriya Akan Jarabar da Allah ya kaddara maki.
Wallahii wallahi mai hakuri baya lalace Aymah .
Sai dai nasabar shi har kullum tayi sama Aymah.
Kana Allah zaikawo mafita a rayuwarki ya ɗaga darajarki ta inda baki tinani...

Jikin shi ta fada ta sanya kuka tace" na yarda Jameel maganar ka haka take kuma in sha Allah zan tsaya akan bakana na ganin maganar nan bata fitaba dan yanzu tin duniya Allah ke hukunta azzaluman bayinsa.
Hakkin rayukan daya ɗauka kadai bazai barshi yaji dadi ba.

Bayanta ya dan bubbuga yace masha Allah Dakika fahimta.
sorry Kinji my Dear wata rana sai labari.

Kai ta jinjinamai tana dan Murmushi tace" ka warke Yanzu?.

Kai ya dagamata yace "yeah.
Likitan zuciyana ta bani magani tini ciwo yayi gidan sa sai fatan Allah kabama iyayenmu aljannah fiddausi.

Ameen tace cikin jin daɗin kalaman sa wa iyayen ta.

Kallonta ya sake ido cikin ido Yace" Aymah zaki iya aurena ?

Ido ta waro tare da neman tashi tabar wajen ya mike ya cafko kafaɗunta ido cikin ido fuskar shi na canzawa yace" A karo na biyu na Roke ki kuma Inaso kiman magana ɗaya dan in'san inda kika ajeni Aymah, kar naita aikin banza kullum sonki na huda jinin jikina yawo yakeman a dukkan sassan da kika sani, nema yake yaci ɓargona shin so kike ya karni ? Dan Allah ki tausayaman ki tausayama zuciyar data daɗe tana dakon sonki, in kau har kince bakyasona to tabbas cikin dayan biyu.
Na farko
Kina ganina talakka kaskantacce Mahaifina da mahaifiyata sunyi zama kalkashin ki sunci sun'sha.
Na biyu namiki Yaro kina ganin bazan taɓa wadataki da abinda ya shafi Rayuwar Aure ba.
Amma karki manta matar Annabi Muhammad SAW Nana khadija ta girmema Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam.
Amma kiji yanda Sukai Aure suka kuma raya sunna Babu tawaya aciki.

Zanbaki dama Aymah daganan Har tsawon wata daya wallahi inason sanin matsayina a wajen ki.

In kinbani muhalli acikin rayuwarki zanfi kowa farin ciki.

Haka zalika idan kikaga zaki cutu kika nuna bakyayina zanyiwa Allah gdy dan nason shiya tsaraman hakan kuma hakan shine Alkhairi na a Rayuwa. Wallahi azeem bazanga laifin kiba som,sana duk abinda nason zan miki kiji dadi wallahi zanmaki da iya iyawata in sha Allah Saboda kin riga kin zama jinin jikina..

Shuru tayi shikuma ganin haka ya shafata zai wuce zuciyarsa ba dadi dan yagaza gane ma'ana shurun nan nata wallahi ba karamin tayar mai da Hankali yake ba..


Yasa hannu sai bude kofar tace Jameel.

Bai juyiba amma ya dakata da fitar .

Ganin haka yasa tace. Jameel bakajin tsoron ace da kananun shekarunka ka auri mace kamarni? baka gudun Abokan ka suma dariya ace kana auran wacce ta girmeka Jameel? zaka iya jerawa dani kacema duniya nice matarka bazakaji komi ba?

Dan juyowa yayi yana sakin murmushin takaici yace" AYMAH basai kinmin jurwaye mai kamar wanka ba.
Nasan so kawai kike kiceman Kinajin kunya duniya taga nine mijinki ina talakka iyayena sunyi bauta a Kalkashin ki, kakata na kalk.....

Kaiman shuru Jameel tace da karfi cikin kuka.

"Ya kake magana haka Jameel,miyasa kakeson muna samun matsala,kai kuma taka salon soyayya haka take,Duk sadda zaka fadaman haka inaji . Kamar kana lumamin wukane a ciki ,Koba soyayyarka a zuciyata iyayenka iyayena ne ballema ina sonka ina sonka ta fada da ƙarfi tana cakumo wuyanshi da fashewa da kuka dan harga Allah ta tsani yanuna shidin kaskantaccene a wajenta ita mai mutunci ce tason kuma mutuncin duk wanda take tare dashi balle su dasukamata halacci.

Shikam wani bala'in dadi da farin ciki ya ziyarci zuciyar shi.
Kafadarta ya rike ya hau juyi da ita cikin tsananin farin ciki.

Habarta ya kama ya ɗago tare da goge hawayenta yace "really kin amince ban tursasaki ba.

Harara ta watsamai kamin tayi sama abinta tanajin zuciyarta wasai da ta amayar da abinda ke damunta .
Shike Ƙaskantar da kanshi awajen ta amma shidin mai matsayine sosai a rayuwarta som batajin dadin abinda yake cewa game da shi da family nashi da suka zame mata garkuwa,Ita kanta da baya zata dawo gaba ai bazata taɓa yarda mahaifiyar shi tayi aiki a kalkashin ta ba,Dan abin namata ciwo duk sadda ta tina.
***
Deedee kam cikin kuka ta fita kai tsaye dakin da Adnan yake ta nufa .

Su sadam na zaune palo sun sanya tvn su da suka dakko gaba suna kallo da abokan su.

Gaidata sukai ta amsa tayi ciki.

Kwance ta ganshi yana bacci iya karfinta tasa ta yankamai mari sai gashi ya tashi yana neman Hanya.

Cikin kuka sosai ta zauna gaban shi tace" kai asararran mutum ne wahalalle fajiri marar amana butulu kawai, takarasa tana tofa mai yawu.

""Yanzu dama kaine ka kashema Aymah iyaye ko? to mungano komi kuma zaka girbi abinda ka shuka da kanka dan Uban Baban ka da wannan Wukar zan kasheka matsiyaci ta nunamai sabuwar wukar dake kyalli hannunta...



❤️MATAR OGA NA ❤️
MALLAKI
❤️UMMY AYSHA ❤️
Page 18

Paid book
MAISO CHART ME.....07038423451


""" Gabaki d'aya yanayin sa saida ya sauya ,wata irin rawa da jijjiga yafara yana zaro ido da kad'a kai tashin hankali bayyane akan bak'ar fuskar shi.

Mari ta kwasamai tace." Da ubanka nayi kama ko da tsinaniyar uwar data kawoka duniya ne da kake kallona? ko nima kashenin zakai?

Ido yaci gaba da zubamata cikin mugun tsanarta data ke hangowa abayya ne ga fuskar shi.

Hannu ta shiga taɓawa tace "Yanzu kai Babu alamar saduda a lamarin ka,Aiko yau sai kaci ubanka tashiga kwalama su Sadam kira,aguje suka shigo ta fashe da kuka da fadin" ina zamu samu wanzami yanzu cikin daran nan wannan mahaukacin na iske da Hakkin tsintsiyar laushi yana kwal-kwale kwal-kwale yana ganina maimakon ya zaro sai ya turata cikin jikinshi ina da tabbacin ta daɗe magudanar Bawalin sa dan alylah akirashi ya dan yimasa gyaran shayin sa.

Gabaki daya suka fashe da dariya suna tafawa kamin cikin mugunta sadam yace "Shege gashi a lankwashe amma ya iya iskanci, to ai hikenan muna zuwa ya karasa suna tafawa da abokansa suka fita suna kwasar sariya..
Abokin sadam din ne mai suna Bash ya fashe da dariya cikin mugunta yace "kai wallahii Isa Abba zamu kira kason bashi da mutunci ko awajen Jariri ne kau, Dan haka dole ayi dogon bincike agano inda yakai wannan hakkin suka fashe da dariya Sadam yace "shegen yana cikin wannan halin ma shiga Ayu sai yayi ciyayya.
Dakyal suka samo Isa Abbah ya hado duka kayan aikin shi suna sake fadamai yanda abin ya kasance sai kada kai yake yana Fadin ai aikin sune ,Mutum ko shekara arba'in yakai sai yamai kaciya balle wanda tishi ne kawai.

Koda suka isa gidan Deedee dai-dai lokacin da Jameel ya fito baibi ta kansu ba farin ciki yasa ya bude gidan yayi tafiyarsa zuciyar sa fara tass yanajin sa cikin mugun nishaɗi yayi gida.

Da sallama suka shiga har lokacin Deedee na tsaye tana mashi masifa shikam sai gurnani yake mai nuni da faɗane kawai yake ba la'asar jikinsa yayi ba.

Da sallama suka shiga inda Dede ta sake saka kuka tace" ni tindama nike na taɓa ganin wannan abu yar ɓula da ba wani abuba amma ka saka abu baka gudun ka toshe wata jijiyar taka kai Allah kabama marar Hankali lfy.

Dariya Isa Abba yayi yace." kar kidamu mudama mukema maguzawa shayi da girmansu balle shi wannan da aikine kawai za'amasa sai anga abun yayi yawa sai aɗan raba mazakutar tasa biyu a fidda cutar.

Ɓererererrrrr!!!!

Adnan ya fara haushi yana neman mikewa.

Deedee kam cewa take wayyo sannu sannu dole kaji zafi,yo ba haka aka taɓa sama Ashiru mai faci robar fitsariba sai gashi ta mayar dashi Mai Yoyon fitsari ba, ko dariya yayi sai ya canza sabon tsarki dan fitsari ke zubomai wannan yar ɓula ai batason bako kamar ido take.
Shiyasa ma bance muje cenba nason aikin arziki ai saiga wanzamai tinda su sunfi kowa sanin abinda wajen keso da wanda bayaso sannu Isa Abba Ɗan gado kunfi ƙarfin Haye.

Cikin jin daɗi Isa Abba yace" cau-cau kakus fada ki sake fada kanki tsaye, kai ku budeman sutura tashi ku rike man hannusa abani fitila mai haske dan in'ƙara ƙarfin ganina..

Dariya suka sanya Deedee tace to bari in'jiraku falo aibana kallai ba Harka duk ta masu Alkalami ce ta koma palo tayi zamanta tana kaɗa kafa da kashe ido daya tana tinanin Rayuwar Aymah mai Cike da riski da Kalubale.

Shikam da karfi yasa aka tale Adnan dake ta ihu ya gwalemasa cinya tare da cafkar Jikin nashi dayayi mugun yaushi tamkar Tsohon Allayyahu .
Afusace yace dan ubanka kadan tashi dan mussan inda zamu samo abun, Kaman kwance kamar ruwa kaɗan kumbura nace ma'ana ka mike ba tsayeba saita abun naka ka mike shege da mace ka gani ai da tini ka zama Pencil ɗin yaran boko.


Su Sadam kau misuke inba dariya ba harda sakin Adnan dan bil hakki Isa Abba ya fusata.

A fusace Isan yace wallahi ko kuyi aikin ku ko in mayar daku mata maza ku dukkan ku kananun Yan iska...

Da sauri suka natsu suka sake banƙare mai Adnan.

Adnan Kau kai ya shiga gilgizawa hawaye na zubomai.
Isa Abba kau afusace ya ɗakko wata katuwar kibiya mai lankwasa kamar kwarashin saka ya danna cikin ɓula yana jujjuyawa da faɗin" dole ayi saka awajen nan indai ana a samo abinda a keso shegen gaban kamar na tsuntsu ance ku dinga gyara amma bakwayi.

Ihu sosai Adnan keyi yana gwaranci danshi kaɗai yason azabar da yakeji adai dai wannan lokacin.
Iya bincike Isa Abba yayi baiga komiba ya dauki yar askar su yace bari adan maka tishi muga.

Daga palo Deedee tace" A'a barshi In baku ganshiba kar ya isheni da wari, in kuna da magani bashi kawai shiyasani kamar ba taimakonsa za'ayiba banza kamar yaro sai iskanci yake barshi ya kume masa a ciki.

Afusace isa Abbah ya wankamai mari yana nishi yace" Shege duk ya bani wahala dole a dafamaka Dauri abaka kasha in dai anason ganin dai-dai..

Tashi sukai Deedee ta zaro 1k tabashi da mashi godiya suka rakashi ya tafi suka dawo.
Sallama ta masu ta koma daki inda da iske Aymah na sama alamar ta kwanta .

Dakin dake ƙasa tashiga tayi Alwallah tayi Isha dan tama makara a ƙallah goma saura duk tana wajen wancen dan iskan.
Bayan tagama tayi shafai tare da addua bacci dan dama sai ta tashi cikin dare take wuti ri.
Som bacci kasa zomata yayi tausayin Aymah cike da zuciyar ta wai ace wanda ke tare da kai amma shine sanadin iyayen ka wannan wace Irin rayuwace.

Washe gari Asubar fari ta tashi tashiga ta haɗamasu kalacin kunun tsamiya da ƙosai mai zafi ta zubamasu ita da Aymah takaima su Sadam sauran da fadin su dibarwa Adnan a ciki.
To sukace sukaje suka cinye suka fita waje suka siyomai garin kwaki na talatin sugar Ashirin suka hadamai suka bashi ba yanda ya iya haka yasha.

Aymah ce ta sakko cikin shirin riga da siket na atamfa sunyi tsam ajikinta katon mayafine akanta da alama fita zatai.
Bayan sun gaisa da DeeDee tayi shiru.

Deedee tace "Aymah ina zuwa hala naga kamar kinyi shirin fita?...

Kanta ta dan shafa tace" zanje wani wurine Deedee kimin Addu'a nasara.

Tom Aymah ak6kah ya tsareki ya baki saa akan dukkan abinda kika sanya gaba.

Ameen tace tana mika hannu ta dauki ƙosai daya taci.

Deedee ta zaro ido tace ke badai kina nufin bazakiciba zaki fita.

Eh Deedee nah saina dawo bazan jimaba in sha Allah zan dawo .

Ohk tom adawo lfy tace tana tashi tanufi kiching dan samata nata a kula.

Aymah kau tana fita wata mota na parking kofar gidan nasu cikin natsuwa ta bude tashiga aguje akaja motar sukabar layin.

Tafiya mai nisa suka isa wani ɗan kauyen dake da ragowar al'umma .

Bakin hanya suka ajiye motor suka fara kutsawa ciki saida sukai tafiya mai bala'in nisa kamin suka iso wata tsohuwar bukka .

Wanda suke tare da ita ya juyo cikin gajiya yana warware rawanin fuskar shi.
Ido nazaro ganin Manager ne wato wanda Adnan yaba ajiyar dukiyar Aymah ma'ana manager sa.

Sallama sukai bakin bukkar wani ɗan farin dattijo ya fito da sanda a hannusa yana dogarawa ya tsufa sosai Dagani yana cikin wahala Rayuwa.

Ido ya zubamasu kamin ya saukesu kan Aymah yace "Amamatu Baba.

Itama isyon ta zubamai cikin balain nasari wanda ke cemata Amamatu Baba.

Amamatu Baba baki ganeniba?

Ido ta zaro kamin kuma ta nuna shi da yatsa bakinta na rawa Tace" Baba Ali dama kaine,Baba akace ka mutu tinma Abba nada rai Baba da Allah kaine takarasa a rukice Idonta na kawo ruwa.

Dan murmushi Yayi yana nunamasu wata tabarma kaba dake ƙalƙashin bishiya yace su zauna.

Gabaki ɗaya suka zauna harda shi.

Ido ya sake zubama Aymah cikin lokaci kuma hawaye suka sakko mai yace Allah Sarki Amamatu duk yanda naso na kare mahaifin ki daga sharrin Black driver amma abu bai yiyuba Amamatu ki yafemun dan Allah...


Cikin kuka sosai tace Baba dan Allah kayiman bayani yanda zan gane miya faru wane sharri ke tsakanin Adnan da mahaifina da har ya iya sanya masu Babba mota bin takansu?

Hawaye ya share yace.
Aymah kinson dai ni Amintaccen mai gadin mahaifinki ne tsawon shekaru, kinson harkar mahaifinki harkace ta bukatar taimakon al'umma dan mutum daya bazai iyaba kinson harkar fito dai.
Mahaifinki na da dribobi da dama da suke masa tukin mota in sun dawo zaima kowa sallama ta kirki wanna dalilin ne ya karama shi farin jini kowa nason yayi aiki a kalkashin sa.
Yanada wani aboki Alh Hamza ɗan sanata babban aminin sane kuma duka harka ɗaya suke saidai an'fison kayam mahaifinki sosai saboda ragowar farashin da yake dashi...
Hamza baya Kaunar mahaifinki ko kadan amma bai taba yarda ya bayyanaba ko afuska hasalima kullum goyan baya yake samu daga mahaifin naki.

Wata rana muna zaune gidan dawakan mahaifinki saiga Alh Hamza da wani yaro kaca kaca yaron yasha wahala Daganin shi a tagayyare yake ashekaru baifi 25 ba.

Bayan sun gaisa yakecewa da mahaifinki Alh ga yaro nan na kawo kason ni yanzu harkata ta farayin ƙasa bama da empty motar da zanbashi ka taimakamasa yana bukatar taimako saboda ya kula da mahaifiyar shi.

Abban ki mutum mai tausayi cikin lokaci yaji yaron ya bashi tausayi .
In takaicemaki aranar ya bashi sabuwar motar gwarama dakuma kayan abinci yace yakaima iyayensa.
Yaron na har kuka saida yayi daganan fa shima ya dage ya rike amana yazo ya sharce dukkan sauran dribobi kokari gashi kaifi daya kuma baya zalinci da wasu keyi sana duk abinda akai zai kawoma mahaifinki bayacin ko sisin sa, ke ko mota ta lalace baya faɗa sai dai yasa kudin sa ya gyara wannan fa shine yakarama mahaifinki soyayyar yaron nan mai suna Adnan da Dribobi yan uwan sa ke cemai Black driver ya jawoshi jiki ke saida ya mayar dashi tamkar ƙanan sa wanda suke uwa daya uba daya babu inda zaishiga bakiga Adnan a bayansa ba,Uwa uba inda ya ida saye Baban ki wajen son da yake maki da baki kulawa duk inda yaje yadawo tsarabar ki daban...

Sun samu shekara takai biyar suna cikin wannan jin dadin rayuwar kwatsam wata rana Adnan din yazoma mahaifinki da son Ya aramishi kuɗi tsabar 100ml.
Mahaifini kuma lokacin ya kwashe yawancin kudadansa wajen turomasa da wasu sabbin kayan da basu riga sukayi magana da Adnan dinba ya bashi hakuri da nunamai ya Bari sai komi ya kammala zai bashi Yanzu ga ƙudirin sa.

Wannan abufa yama Adnan zafi ganin lokacin da suka ɗauka amma ya kasamai Alfarma kawai yasha alwashi sai yabar aiki kalkashin sa tinda amfani kana tare da mutum ya taimakama ranar da kake da buƙata.

Bayan kwana biyu yazo da kanshi muna zaune bakin get din gidanku ya cillama mahaifinki key tare da mai munana kalamai ta hanyar nunamai shiɗin mutum ne mai masifar son abin duniya uzirin sa kawai yasani baison na kowa ba Allah ya hada kowa da rabon sa.

Iya wuya mahaifinki yashiga tashin Hankali yin duniya Adnan ya tsaya yaji uzurinsa amma yaki daga baya ya nuna mai shi ya hakura da nashi uzirin yazo yabashi amma yaron nan ya shure kafa ya tafi cikin zafin zuciya dan dama bakar zuciyane dashi som Abokan aikin suma basu son shi gashi dama Mahaifinki yafi sonsa dasu akwai wannan kishin A ransu.

Amamatu wallahii Alh Abdulkarim kuka yasa sosai yana faɗin" Dan Allah kuce yazo wallahi zanbashi banaso wannan abun yashiga tsakanina da yaron nan Baba Ali banaso kowa yaga baƙina kar Adnan ya daukeni maison kai kamar yanda yace.

Ban'cemai komiba illah tashi dana yi cikin sassarfa nabi bayan as
Adnan dan in samo in lallaso shi ..
Daga nesa nike hangosa banyi tinanin kwala mai kiraba illah binshi danacigaba dayi har muka fara shiga cikin gona ki inda cak ya tsaya kalkashin wata bishiya tare da zaro sigari yasa a bakin shi ya ɗauki waya ya fara latsawa.
Koda aka dakko wayar cikin muryar sa ta yan daba da bamuson yana da itaba yace" Yahajj komi yazo kwana ɗan iskanan fa yashiga tashin hankali ya kake gani akarɓa koko abar shi da Alhini,aini dama wallahi ba wani sonsa nikeba nutum ana tare dakai muke wahala amma arziki nakane kullum jinike kamar in karshe shi wallahi shida ɗiyar nan tasa mai ciman kudi har cikin raina in nasaimata Abun biyar shikam yayita washe baki dan ubansa yanajin dadi zasuzo Hannu ai...


Jikina ɓari ya kama tashin hankali mabayyani ya bayyana agare ni da jin furucin wanda banyi tsammaniba .
Jin yacigaba da waya yasani dade bakina nayi kasa cikin ciyayi inajin yana fadin.
Yo dayason halacci ko Billion nace zai bani ai zai girmama bukatuna amma ba komi nayi alƙawarin Sai naga bayan shi ,sai nayi gutsun gutsun da naman jikin shi ,wanna Yar tashi kuwa sai na lalata rayuwarta badai ita yakema wannan ɓata lokacin ba, Wallahi wallahi yau ko gobe saina watsamata rayuwa nayi mata daga daga na keta mutuncin ta shikuma bazai sake sani idoba sai bayan shekaru zanzomai ta sigar da baitaɓa tinaniba.

Kuka ya kufceman da karfi wanda yasa shi juyowa a razane nan mukai ido hudu dashi jikina ya fara bari na fara ja da baya yana biyoni da fadi" kai Ali tsohon banza dama laɓe kakeman aiko daga kaina ka gama yasa hannu ya zaro wata katuwar wuka yayo kaina .
Dan ceton rayuwata na juya na fara gudu yana bina sai dai sabon jini da tsohon jini sunsha banban ganin zanbashi wahala yasa shi jefoman wannan Wukar takau saman anan ya gwadamasu wajen wuyan shi kamin yace ganin nafaɗi ciki jini ya biyoni ya haye ruwan cikina yace tinda kaji sirrina nida Hamza sai kabar duniya ,Zan kuma datse hannuka guda saboda

Please Login or Register in order to submit comment