Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai tambaya,Kai dai nacema da dama Jameel ba hikenanba, nidai ban haneka zuwa ba iyalinkace amma dai akiyaye dan Allah saboda budewar kirjin.

Ai batama rufe bakiba ya tashi ya zura takalmanshi sauri sauri ya fada motar shi yayi gidan Aymah kamar zai tashi sama.

Inna su kau itama a ɗan rude tace Deedee bata da lfy ne Aymah?.

Oho rawar kai dai zai fara na takamai burki kinson yaran zamani.

Shuru tayi tana sauke ajiyar zuciya tare da dan satar kallom malam Habu ya sakarmata murmushi ta dauke kai kunya fal idonta.

Malam Habu kau ledar Viva bakace dake hannushi ya zazzage duka yace kin zo asa'a Deedee,kinga duk wahala da muka dingayi akan a sai gonarnan akaki,to gashi aiki yabiyo ta kanta anaso a fitar da service aka kiramu aka bamu wannan million goma ce cifcif.
Da kuma katon fili dake cikin shagari low-cost.

Hadadda guda Deedee ta rangada tace kai Alhamdulillah, Sa'a ta kawoni kam,kai amma fa naji dadin da baki bazai iya furtawaba, kaga binda mukaitafama abamu ko 500k ne dan ama jamilu aiki aka ki shine aka bamu wanna makudan kai Alhamdulillah nayi farin ciki arziki ya taho in sha Allah.

Murmushi yayi yace in sha Allah.

Tace toh Alhamdulillah yanzu dai wannan gona zamu iya cewa taka ce Habu, tinda gadon mahaifinka ne,nikuma abinda akabani kaga shine nabayar akasai wannan gidan ko,to yanzu dai dukiya takace ka sarrafata abisa tsari da koyarwa mussulun ci.

Murmushi yayi yace Deedee ina dake saina tsaya tsara abu,ai tinda Allah dai ya bamu kawai kifadi abinda kike so ayi.

Ido ta kanne tsawon lokaci kamin tace masha Allah Alhamdulillah na samo dabara.

Mizai hana wannan dan gidan a rushe shi ku sai wani , Wannan kuma amaidamaka shi babban shago asamaka kayan tireda tinda dai ba wani zurfi gareka a karatu ba.

Shawaraki tayi Deedee nah yace cikin farin ciki


Tacw yawwa Alhamdulillah hakan za'ayi, zanje gidan yarancen naga dai sauri yake nabashi waje yasha iska
Ba.


Cikin kunya Inna su tace anjima Baban su kabari muje gidan mukara ganin mai jiki ko.

Sosai Baraka yanda kikace yafada cikin sauri.

Murmushi Deedee tayi tace.
Abu nagaba kaji zancen da yaran na su manja suka shigo dashi ko?,nifa abun som baiman dadiba ai yakamata in an'girma ason an'girma koko.

Murmushi yayi yana sunkuyar da kanshi yace.
kiyi hkr ni kaina da suka tunkare ni da maganar da ban amince ba amma daga baya naga fa'idar haka,saboda taimakon da zakiyi.

Baki ta tabe tace ku kuka sani ta mike tamasu sallama ta fita,tana fita tace yan banta uba nimafa ina son sa,ina kuma tausayi sa,akan hanyarta ne ta biya tasai zogala da ƙuli masu kyau tayi gida.

Jameel kau Allah ne yakaishi lfy kai kace wata doguwar tafiya zaiyyi da yake xabga gudu.

Bakin get din farko ya aje motar cikin sauri ya ƙarasa ciki ,bata palon kasa bata na sama a bedroom din da yabar tarihi ya tura yashiga da sallama.

Kwance ya ganta tana bacci daga ita sai have vest da wani wando da dukkan mazaunanta bude suke, ta wani kife alamar baccin yamata dadi,.

Wani yawun wahala ya hade kamin ya karasa wajen ya zauna akan gadon yana burkitoto dan gyaramata kwanciyarta.

Ahankali ta fara bude ido ta sauke shi akanshi yayim da shiman nashi ke cikin nata.
Saitin raunin nata yasanya hannusa masu taushi ya hau murzawa da tofa addu'a.
Murmushi tamai tana mikamai hannu da fadin ina kwana ya kake.

Amsamata yayi yana tambayar lfyn ta.

Badai ciwo ko.

Kai kawai ta dagamai suka danyi fira yamata sallama akan zaije yadawo.

Rakiya zatamai ya hanata tare da fita da sauri kamar zai fadi ta bishi da kallon tausayi dan tason shigartane ta ruɗashi,

Abakin kofa sukayi kicibus da Deedee tace kaiko baka da mutunci yanzu kwara in daɓo sayyada daka kawoni bisa wannan motar taka mai siffar agwagwa..

Kiyi hkr yace yana shafata ya wuce ya fada mota.

Ya dade zaune a cikin mota kanshi akan sitiyari jin wani fitinannan felling.

Yadade kamin ya wuce gida yayi wanka yayi wajen Dr Abba.

Aymah kau wanka tayi ta sakko kasa nan taga Deedee na kwada zogala suna ta fira abinsu har tagama ta zubamata ta mike zata kaima Baba ali aka Turo kofar da sallama.

Wani irin ihu Aymah tayi aguje kuma tayi bakin kofar tana faɗin Hajiya Asiya.

Da sauri suka rungume juna lokaci daya kuma suka fara kuka baji ba gani ..

Nidai dan Allah ku saki juna haba wannan ai iskancine nidai miji nason ana rungumewa amma ke Aymah dan wulakanci na hanaki Rungume mijinki dan lfyn ki shine zaki rungume wata salom kirjinki ya ɗaya ace nazama babba banza cewar Deedee a fusace tana dakko iccen mopa...

Ayi hkr b yawa

MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
PAGE 34

Da sauri suka saki juna suna fashewa da dariya yayin da itama tasa dariya tace'' sunga icce sun watse matsorata.
Hajiya asiya ta juyo tana dariya sosai ta Rungume Deedee tace.
ga Deedee mu da labarinta kullum ke jemun kullum son ganin ki nike amma sai yanzu.

Zama Deedee tayi suka gaisa kamin tace tana zuwa.
Tana fita suka sake rungume juna kamin su zauna idon kowa akan juna cike da kewa.

Aymah tace haj Asiya dama rai kanga rai, ashe kina nan amma baki taba nemana ba nayi fushi.

Hmm Aymah kenan ke kinson kina makale araina, kawai wannan tsarin manager ne ganin yanda Adnan ya tsaurara tsaro akanki da Dukiyar ki shiyasa muka bi komi cikin siyasa,amma bagashiba cikin ikon Allah komi ya shide,ga babba tsaraba nayomaki ta karkace tana bude katuwar ledar daketa tashin kamshi.
Manyan kwalaben humra sirri ne daketa tashin sihirtaccen kamshi tace gashinan daga wajen mutuniyar muke ummy Aysha, ga kayanan iya kaya,qannan kuma kwalbar kwalacca ne itama zakiga yanda namiji zai koma miki,wannan kuma turaran tsugunni ne zakiji yanda zaki matse ko yatsanki biyu bazai iya wucewa ba,wannan kuma akan mararki zaki shafa yayin kaima oga ziyara,ga kwallin sirri bayan ke babu wata azuciyar mai gida,ke wlh ko mace goma zayyi sonki saiya babbanta dana sauran,gashi dama mijinki saurayine kyakyawa ajin farko Aymah dole kiyi duk abinda zkaiyi wajen sake jawoshi jikinki,ki saki jiki dashi daganin sa kamili ne,kibashi hakkin sa in so goma ya zo nema saboda daganin sa jajurtaccen namiji ne,karkimai rowar kanki daidai da rana daya dan in baki bashiba zai fara zuba idonsa a kallan matan banza,Ni inaji ajikina Allah ne yakawo shi rayuwarki dan yamaki maganin matsalar ki dama cen baki dace da wannan Adnan ɗin ba,ga maltina mata nan kisha zakibani labari,wannan kuma dan la'asar ne zakisha shabiyar duk sadda za'ayi,ga wani ruwan magani nan kafi budurwa ukku ki tatse leda daya ki hada tea ki juye aciki kisha na kwana ukku Aymah wallahi azeem kin wuce da kwalwar yaro sai dai baban yaro dan mata na iske gidan suna neman sa,kinga ,tashin hankali masifa ta da namiji saidai kiji wani wajen anayi amma kekam sai gani sai hange zaki zamemai ƙadan garan bakin tulu a zuciyar sa.

Rungumeta sosai Aymah tayi tace ngd aminiyar arzikin da babu kamarta ina alfahari dake,shiyasa nayi kewarki matuka,to amma kinson bana da lfy kuma wlh kamar yafi karfina nason ni mabukaciyar macace Asiya amma ƙarawa daya jarumin nan ya kaini kas har yau jinike kamar baniba .

Shekeke ta kalleta tace.
To tashi tsaye zakiyi da neman magunguna masu inganci saboda irin su saisu raunata ka,Yanzu kifara shan galan din nan na maganin sanyi in yaso kisha sauran magungunan daga baya, wlh sai dai kukai juna kasa ,Amma dama taya za'ayi kibashi dama batare da kingyara kankiba ai dole ki jigata,Zancen jinya kuma banason iskanci ke bakinson in kin warke ba ko baki warkeba,ina dai fatan yabarki bayan kun gama Amarci ki dawo bakin aiki.


Dariya tayi tace kumafa hakane,to yanda dai yace .

Zatai magana Jannat ta turo kofa ta shigo nan suka rungume juna suka zaune cike da wayewa suka shiga fira itama ta bude jikka ta debo Turarukan wutar UMSAD INCENSE Masu masifaffan kamshi da kama gida tace gashi to nawa gudunmuwar fatan mu ayi zaman lfy mai dorewa(in dai kamshi kuke nema wlh nagida to ku neme ta)

Sosai tamata gdy Haj Asiya tace tsaya kiga bari in hadamata abubuwa naganta abun akwai sanya.

Nan tashiga kiching ta dauki tea spoon ta zuba rabin maganin data zo dashi saboda karfinsa ta ba Aymah ta sake hada wani taba Jannat.

Karba sukai suka sha Aymah tace Ya banga kin hada naki ba.

Murmushi tayi tace to ba mai aure keshan magani mataba sadda nasha nasha.

Cup din Aymah ta aje cikin furgici tace bangane ba.

Murmushin takaici tayi hawaye suka zubomata tace Aymah naga butulcin maza,tini mijina ya sakeni amma nakusa Aure.

Innalillahi wa inna ilaihi Raji'un miya hadaku Asiya.

Hmm akan zai kara Aure yarinya tace bata bukatar zama da kishiya shine yabani takadda da saki har biyu yanzu kuma yana bukatar na koma saboda an'fasa bashi sunce tinda ya iya sakina yar suma zai saketa to nikuma namai nisa yarane kuma Allah ya shiryasu duk inda suke, gasu maza dama duk inda nike sun iskeni.

Sosai sukaji ba dadi daga karshe suka hau lallashinta suka shiga fira.

Deedee kam koda takai ma Baba Ali kwad'an ta zauna sukai fira nan yake shedamata gobene fa.

Dariya tayi tace kai kam dai malam baka gajiya,sai kace wasu yara sai rawar kafa kake.

Dariya yayi yace mai Sa'a ai shine zai sameki Hajiya Deedee ,dan mi bazanyi rawar kafaba nason ko bayan raina za'aman tsarkakakiyar takaba.

Hmm malam kenan Allah ne kawai yason gawar fari ka daina wannan magana banaso tafaɗa tana tashi tayi tafiyarta ta fara aikin tsumin Aymah.


Bayan tagama ta aje yasha iska tayi wanka tayi kwanciyarta dan ta huta.

Da yamma tashiga wajen Aymah ta bata galan din da cup tace susha.

Nan fa duk wanda yashashi cikin su saida ya gilgiza dan lokaci daya suka farajin yanayi ,Asiya kam sosai tashigama Aymah balai dan ita tace ta dandana taji gashi ita ba miji b balle tasanya ran samun relief in sun gaisa.

Dariya Aymah tamata duk da yanda takejin marar ta ta daure gam.


A takaice nan suka yini Sai mangariba Asiya ta wuce da Jannat da niyyar zasu dawo bayan kwana biyu .

Sallama sukai suka shiga waje Deedee daganan suka wuce kamar sunsaba da juna sai fira suke cike da wayewa..

Bayan isha Jameel ya shigo gidan hannusa dauke da manyan ledoji ya ajema Aymah gabanta tare da bude wata karama mai kyau ya zaro kwalin wayar iphone mai kyau ya mikamata yace ga tukuicin Farin cikin da kika sani, sannan inaso muyi magana dake kuma inaso ki fahimceni dan Allah.

Murna tayi sosai tare da jeromai Addu'a karin budi na Alkhairi.

Ameen .

Aymah inaso musai wannan gidan naki bansaniba ko zaki saidaman, inaso na haɗe family nah waje guda ba ace ni ina gidan kiba iyayena suna wani wurin,bama da yawa kamar yanda kema babu wani naki a kusa dake,Idon kau muka hada kanmu zamuji dadi fiye da tinanin ki,ko yaran mu suka taso gasu ga kakannin su,ga kuma kema Deedee ki a kusa dake,

Ido ta zaro tana aje mai wayar shi gabanshi fuska daure tace yanzu Baby bazaka dai iya karba kyautana ba ko, saidai in na siyar ma .

Aa amfanin siyarwa anan shine...

Nan yabata labarin abinda yafaru dan gane da gonar su da hukuncin da Deedee ta yanke na rushe gidan su aginama mahaifin su daga karshe yace.
Dr Abba da Daddy ne suka bani wannan shawarar ke kuma Aymah sai abaki kudin abaki wancen filin in yaso kina iya yin abinda zai zama sadakatu jariya wa iyayen ki,ko kigina masallaci,ko kiyi islamiya duk dai wanda kike so.

Cikin gamsuwa da kalamansa tace to shikenan na yarda da hakan.

Rungumeta yayi yana shakar daddana kamshin kwalacca ta yace ina sonki .

Murmushi tayi tace nima haka..

Sallama su manager ne da Deedee ta katse masu hanzari nan suka zauna aka gaisa manager yace Aymah kinki shawarar da muka bayar ko,ina ganin hakan shine daidai tinda wannan gidan dai babban gidane,kuma in yana wajen Jameel kamar yana wajen kine tinda gidan mahaifinki ne,kana natsuwarku kuduka ku hade waje daya kuzama tuwona maina,ni dai matsayina na mahaifi gareki na amince.

Daddy nima na amince .

Yawwaa madallah Allah yamaki albarka.
Yanzu mikikafiso ayi islamiya ko makaranta.

Kanta a kasa tace in zai yiyu duka ayi in akwai wani filin akusa asaya sai in bayar da kudin sa a hade kawai.

Aaa Aymah wancen filin babba ne ya isa ayi makaranta da Islamiya baki daya.

To tace Jameel yace nikuma zangina maki shi yanda kike so in sha Allah ,ai iyayenki nawane sun gama min komi da suka haifa man ke.

Ido ta tsura mai tace wayabaka kudi to?

Murmushi yayi yace kanki na sayar.
Dariya duka yan dakin sukai nan suka tashi suka tafi.

Washegari aka daura auran Deedee da Baba Ali,Zanso kuga lefen da aka kawo kamar na budurwa kauye abun sai son barka.
Su Aymah kau da sukaji labari sunyi farin ciki ranar ta kashe kudi kamar mi, an'daki kwarya kamar yanda DeeDee tace anci ansha kawayen Deedee sunmata kara sosai.

Bayan isha Angon ya shiga dakin amaryar sa da katuwar ledar kaza sai fatan mutuwa ta raba.


Bayan wata daya.

Aymah ce tsaye part din da su Baba zasu dawo tasa an'samasu hadaddun kayan daki batare da sanin kowaba daga ita sai kawarta Hajiya Asiya suke harkarsu Dan wani filine data taɓa saye batare da sanin kowaba tasa aka sayar aka subamasu kaya na more rayuwa a part din da Adnan yayi jinya Kabeer kuma aka gyaramasa dakin da Baba Ali ya tashi.
Saida ta Tabbatar komi yayi yanda take so kamin su turare wajen su fito.
Daganin yanda take tafiyar kason tagaji sosai.

A palon ta suka zube Hajiya Asiya ta bita da kallo sosai kallo na kurullah tace anya matar nan klau kike kuwa?.

Fuska ta yamutsa tace kalau nike kawai nagaji ne wlh ..

Murmushi tayi tace ina Angon naki .

Ido ta lumshe tace yau satina biyu da kwana ukku bansashi ido ba, nayi kewar sa sosai, basanan shida Dr Abbah sunyi tafiya.

Ohk Allah ya maidoshi lfy.

Ameen tace tanayin shuru kan kace mi kuma bacci yayi gaba da ita.

Dariya Hajiya Asiya tayi tana daga hannu sama tace .
Alhamdulillah naji dadi Allah ka inganta, Allah kuma ka kawomata da sauki,Mahakurci mawadaci,ashe kema zakiga naki .

Suna zaune Deedee ta shigo da sallama Haj Asiya ta amsa tana fadin Deedee Sannu.

Yawwa au bacci take? wannan bacci na Aymah yanzu yana damuna,ko fira kuke sai bacci kamar kasa,Ba mamaki shawarace ke damun ta dole inje nemo maki magani anjima in sha Allah bari malam ya tashi bacci.

Murmushi Haj Asiya tayi tana Dawowa kusa da Deedee ta rike hannuta.
Tace Deedee Aymah fa ba shawara bane, tanada shigar ciki amma ita kanta bata saniba,kawai tana ganin gajiya ne.

Ido ta gwalo tare da tura kanta cikin filon kujera ta saki guda da zubewa kasa tace Alhamdulillah,lokaci daya kuma ta mike ta fara rawa abin gwanin dariya itanan duk murna ne.

Dariya sosai Haj Asiya keyi.

DeeDee tace ke mijinta k
Na hanya dan Allah akirawo mana mai lalle ta zanemata kafar tass dan dole in mikata wajen mijinta ɓargon ɗan su ya ida bunkasa kalkashin kulawar iyayen su .

Baki da matsala Hajiya Deedee tace tana daukar wayarta tashiga kiran kawarta akan ta basu mai lallan ta, nan tabasu address din gidan .

To gatanan zuwa suka wayar.

Bayan mnt na kadan ta tashi tana yamutsa fuska da binsu da kallo ganin suduka kallonta suke.

Fuska ta yamutsa tace Deedee yunwa nikeji kamar banci komi ba.

Baki a washe Deedee tace angama mizakici Aymah nah.

Komima amma mai yaji tace tana mikewa dan wanke bakinta da fuskarta.

Kamin ta dawo Deedee ta ajemata dambun shinkafar da tayi yaji kayan lambu sai peper chicken akai.

Nan ta zauna ta karamasa yaji sosai tahau ci tana lumshe ido dan yamata yanda take so.

Kantagama sukaji sallama mai lallan nan ta bisu da kallo.

Hajiya Asiya tace lalle nikeso aman biki gareni.

Da sauri tace inaso dan Allah afaraman .

To shikenan gama Amaki sai amun.


Sauri sauri ta cinye daidai sadda wayarta tayi ring,ganin Jameel ne yasa tayi dakin da DeeDee ta taba zama nan kasa tafada akan karamin gadon tana lumshe ido da fadin.

Baby nayi kewarka sosai wallahi ,inason jinka kusa dani takarasa tanamasa shashekar kukan dake cike da shagwaba dan da gaske take, kwana biyu kewar sa take har mamaki take yanda takejin masifaffan feeling akan sa ,sai dai ta danganta hakan akan maganin da ta dinga sha.

Jameel kau a kasala ta saukar mai lokaci daya,cikin low voice dinsa.
Yace'' Sweetheart baki kaini ba wlh ,dakyal nike bacci,duk abinda zanyi ina rike da tinanin ki,gashi bana da natsuwa saboda dandanonki da kika lasaman yana hana zuciyana sukuuni,inaso nazo na ganki sai dai banso hakurina yakai karshe,bana tinanin a wannan karan zan iya samaki ido ,shiyasama na yanke shawarar sake ko wata biyu ne kamin ki warke duka ko..

Kuka sosai tasa mai tana fadin nifa wlh na warke dama Deedee ne ke abinta amma ni ai na warke dan Allah kazo nayi kewarka, gasu Inna mu yau zasu dawo, kaxo mu tarbesu tare kaji b
Babyyyy.

A yanda taja sunan saida yaji kamar ya saki sitiyarin motar z dakyal ya taka burki yana sauke ajiyar zuciya.
To in nazo zaki barni na gaisa dake.

Da sauri tace mizai hana duk abinda kakeso zanma kaji da gaske zaka zo.

To mizaki ajeman in zanzo kuma wane tarba zakiman.

A kagare tace dan Allah Baby kace zakazo din nikuma wallahi zanbaka mamaki dan nayi kewarka sosai.

To shikenan in sha Allah zanshigo yau ..

Ihu ta fasamai har saida ya dauke wayar yana dariya yace Sai nazo Sweetyy nah.

Lafiyayyen kiss tamasa kamin sukayi bankwana.

Da sauri ta fito palon tana rungume Deedee tace

Ga beby nan zuwa Deedee.

Baki Deedee ta washe tace haba Aymah ai sai yakara sa
Watanni nan gaba, ashe Kema kin fahimta dayake likitocine kai wllahi naji dadi.

Cikin rashin fahimta inda kalamanta ya dosa tace minene na fahimta.

Da sauri Hajiya Asiya dake dariya sosai tace tana nufin ga Maigidanta nan zuwa fa DeeDee.

Laa ah toh Aymah naji tace Beby.
Yawwaa nikam magungunan nan dana baki zaki bani saura in akwai dan zuwa yanzu sunyi enfiya ( expired) cewar Deedee cikin sabon turanci.

Dariya suka fashe dashi tace ai bana da komi duka na shanye.

Hannu ta dora akai ta kwallah ihu tace Aymah lfyn ki kuwaz yanzu har galan biyu nan kinshanye.

Baki ta turo tace to ni daɗin sha yakeman kikaroman ma ina son bauri baurin sa.

Tureta tayi tace wallahi har abada sai shekara mai zuwa, Allah ka dubeni da idon rahma karta haifoman ɗa mai ganye aka.
cewar Deedee cikin damuwa.

Haj Asiya tace haba ba damuwa Deedee mu.

Zama Aymah tayi aka shinfidamata lalale hadadde tana gamawa ta dakko kayan dilka da Asiya tasaimata wajen ummy Aysha ta shafe jikinta da shi bayan awa daya tayi wanka da sabulun dilka mahadin man dilken.

Zanso kuga hatsabibin Kyan da tayi.

Mai lallan dake zaune tanacin abinci ta bita da kallo ganin ta fito ciki sha'awa tace.
Aunty dan Allah ki zauna na maki make up ,ga kayan kwalliya nan dama wata mai jego zanje namawa sai nafaramaki.

Murmushi Aymah tayi tace ngd kanwata nan ta zauna aka bata lokaci akan gyaran ta,zanso kuga kyan da baiwar Allah nan tayi cikin shigar shadda mai masifar kyau Red colour gashinan ya sha gyara yayi luf luf abin sai son Barka..

Zafafan photo akaimata masu masifar kyau da ɗaukar Hankali a wayarta ita kanta tason ta hadu..

Karfe biyar suka farajin ana bude get din gidan motoci suka fara shigowa ajere Har guda ukku.

Da sauri Aymah ta zubama window ido ganin wane bakine sukai.

Idonta ya sauka akan jarumin nata dayayi wani masifffan kyau, yana sanye cikin wata farar shadda kan nan yasha hula ga wani fitinanna glass baki ya kwama kamar kullum fuskar nan tashi tamke gam..

MATAR OGA NA
PAGE 35

Cikin mamaki sosai take kallon shi ganin canjin dayayi ga wani masifaffan haske dayayi kamar mai bleaching,kana ganin Jameel kason hutu yazo kudi ya zauna dan fatar shi ta murje sosai kamar wanda akama wankan inji.

Key din hannun mutanan ya karɓa sukai magana saida yaga sun juya kamin ya doso ciki Kabeer biye dashi.

Kasa daurewa tayi aguje tafita kamar yarinya tana fdin Babyyyy.

Yana ganinta ya waro ido Cikin farin ciki tare da bude mata hannu takau fada kirjinsa tayi lamo jin sassanyan kamshin da yake mai tsananin dadi
.

Jameel kau kiss ya manna mata agoshi yana tattaɓa bayanta cikin tsananin kewa, Cikin shaƙaƙa muryarsa data disashe Saboda jin kamshin fitinaniyar Humra ta dake dukan Hancin sa yace.
Kinyi kyau matuka Sweety ko haka kika tsaya kin gamamin komi, nayi missing naki sosai sana na samu tarba da nike so,Nason bani kadai nayi kewar kiba gashi kema kin fiddo da taki zahiri.

Cikin kewa da farin ciki ta dago kanta tasa ya tsanta babban ta lakace hancinsa tace nine ke kewarka jibi yanda na rame akan tinaninka kaikam kaje ka huta ka xama kato jibi teɓa da kai.

Sosai yake dariya yace dakau ban yafema kaina ba akace nayi teɓa dan nasan ke xancuta xan karamiki nawie yakara she yana kashe mata ido daya.

Murmushi Tayi ta kama hannun sa da fadin sannu da zuwa Baby ya gajiya.

Yawwa Sannu ki ina yan gidan.

Deedee dake bayansu tana ba Baba Ali abinci abaki tace gamu a kusa, wata kuson tafi wata ,yau nima mijin nawa yatashi da gudawa jikin ba ƙarfi,Ya kuke ka kadawo Lfy ina Dr Abbah.

Subhanallahi sukace suna karasa wajen, Kabeer yace Aunty Ina wuni.

Ido Aymah ta zaro sai kuma kunya takamata Ashe yana tare da Jameel amma bata gansa ba.

Cikin matukar nawie tace Alhamdulillah kanena ya kake.

Lfy klau yace yana ajemata jikkar Jameel din yace bari inje mukarasa aikin gida .

Tace ohk munanan muna baza ido.

Dariya yayi yafita yana yaba kirkinta.

Bayan sunma Baba sannu Jameel yace tin yaushe bayajin dadi.

DeeDee tace yau da safe.

Aymah tace kuma Deedee baki fadaba akaishi Asibiti?.

Tace kai bafa komi kawaii mu tattalin mijine damu, duka fa so biyu yashiga toilet din,to amma mu kunson mutanan da dana yanzu ba dayaba nan jinike kamar yayi shekara bayajin dadi shiyasa nima bana da sukuni takarasa tana tsaki.

Dariya duka suka sanya Jameel ya mike Aymah ta dauki akwatinsa suka masu Allah yasawaka sukayi ciki.

Suna shiga palon a zafafe yawani juyota cike da kewa ya tausa halshansa anata yashiga sarrafawa cike da kwarewa dakuma zallar kewa,tsawon lokaci tsayuwa ta gagare su dan ita kanta zagewa tayi tana mayar masa da martani dan ba karya a kame take.

Ido rufe ko gani sosai basayi suka zube akan lallausan carpet din wajen, Daga nan wasan ya canza,ba karya sun murji juna kuma kowa yaji dadi ,Farin ciki sosai bayyane ga fuskar su,bayan sunyi wanka sun dawo palon ya zubama carpet din ido kamin ya dago ya kalli Aymah cikin nishadi yace Sweetheart amalala kikamana a palo.

Kallon wajen tayi lokaci daya ta sunkuyar da kanta tana fadin koma miye kaine sila kakai jarumine da dole abinda yafi Haka nayi,Duk banson wannan abunba sai awajen ka,Banson yanda zanji dadiba sai awajen ka,Ina da bukata amma banyi tinanin daɗin da akeji zai iya kai wannan ba .

Rungumeta yayi yana fadin naji daɗin wannan yabon,nakuma gode Allah da akaina kika san komi,nasha fadamiki dama matana ne aka Arama Adnan,gashi yanzu ai tadawo gareni, dan zaki ya girma,yanzu rufe ido.

Gam kau ta rufe tana murmushi ya buda tafin hannuta ya damkamata wani karamin kwali dakuma abu kamar key yace xaki iya budewa.

Tana budewa taga kyautar key ne na mota sai kuma zabban gwal masu masifar kyau manya dasu daganinsu basai ance komiba wajen tsada.

Cikin farin ciki tace Baby wannan fa ko kana nufin nawane?

Eh kyautàr dadin da kika banine.

Gdy sosai tashiga mai kamin tace Baby dan Allah kayi hkr akan magana da zanma,inaga hakkina ne nason sana'a ka ko,inaji ajikina ba iya Driver kawai kake ba. Dan bazai baka wannan kudin ba.

Murmushi yayi yana jawota jikin shi ya shiga labartamata komi yace dama bari nayi sai na sallami duk mai bina bashi kinga yanzu Dr Abbah daya bani kudin naba shi , Yanzu dukiyar da uwar tawane babu abinda zance dashi sai gdy shida family nasa,ina kara gdya ga Allah daya hadani da Abba, wlh Abbah mutumin kirkine Aymah,bilhakki yake sona,yanzu tafiyar nan da mukai karkiso kiga yanda abubuwa suka bude masha Allah, munsamu mun hadu da manyan mutane Abokan Huɗa,ga aikin safa ya aje tsawon wannan lokacin dandai duk ya hadani

Please Login or Register in order to submit comment