Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaitsaya wa .

Gabaki daya ido suka zaro dan tinda sukaga tana wannan kafirar dariya sunson ba karamin balai ta shiryama Adnan ba.

Ya rasulu ya manzon Allah. Dan Allah Deedee nah karkije ki tabomuna inda za'a hallakamu Kinga sai sojane.

Cak ta tsaya da dariya tace in kaga wani Abu ya faru daga Allah ne , Dan haka karka wani damu.

Adnan.

Kullum in ya fita baya sake dawowa gidan sai dare,Gidan bude yake amma ya zuba matakan tsaron da in tayi yunkurun guduwa zaisa a cafketa.

Ranar daya cika wata ukku cif yayi Shirin komawa aiki dan ya fahimci komi ya kammala dan da niyyar sa wata daya zayyi ya koma, Amma saida ya tsaya ya siyar da Asibitin Aymah da wasu filayenta kamin ya wuce...

Garin kwaki mai yawa ya ajiye mata yakai tiyya biyar da uban yaji dakakke sai manja.

Baimata sallamaba yasanya Key ya rufeta ya kama gaban shi.


Bata taba gane abinda ya shiryamata ba saida taji kwana biyu tsit din tayi yawa anan taga ko kujera dake dakin shi an ɗauketa ga Dakin yayi datti.

Tsaki tayi ta koma D'akin ta ta kwanta ƙasa tare da tada kai da jikkunan ta da sune kawai ta tsira dasu Amma ko pilo bai barmata Ba.

Yunwa taji tanaji ta tashi ta shiga kiching dan samun abinda zataci dan yanzu har ta saba da maneji .
Indomie kau har tasanya zafi ya tasomata saboda cinta da take yawanyi.
Cikin natsuwa ta fara tafasa ruwan zafi kenan gas din ya kare ya salam tace tana dawowa ta zauna palo to ta ina zata samu abunda zatai Amfani dashi.

Idonta ne ya sauka ga ledar garin Kwakin nan anan ta tashi ta buɗe tayi murmushi dan harga Allah taji daɗi, Dan sadda tana mkrt in taga an'kawoma Ƙawayenta suka Haɗashi har rokonsu take.

Manja ta diba ta kaishi ga rana tare da jefa tafarnuwa guda biyu kana ta dawo ta ɗiba ta Jiƙashi.

Ya salam tace sadda taga tana kwadashi yawunta na tsinkewa.

Sadda tagama taci ta koshi tasha ruwa kamin ta tashi tayi Alwallah ta dawo ta ɗauki Alkur'anita da yazama abokin zamanta ta fara karatu.

A haka Aymah keta rayuwa cikin kunci tin tanajin dadin abincinta na yanxu har ta dainaci dan Ta fahimci tsab ya tsanemata Ruwan jiki Sai dai shan Ruwa ,Ace Rogo ne da safe dare rana abin Yayi yawa tayi kuka har ta gode Allah ta hakura..

Jameel kau masha Allah jiki yayi sauki kullum kagan shi kwance daki yayi shuru, wani lokacin kuma yana sakin murmushi da kama pilo .
In kuma ya tino wani abun sai yaji shi cikin fargaba da Kunci.

Kwana shi Hamsin yaso komawa su Inna suka hana shi da Alkawarin sai Yayi wata biyu.

Ranar daya cika wata biyu kam da kuzari sosai yatashi yana fatan zuwa ya ganta cikim aminci.
Bayan ya gama shirin shi tsaf Deedee ta kama hannushi ta rike sosai tace.
Allah yamaka Albarka , nayi istakhara nagano muna da nasara.
Dan haka kaima kaji tsoron akkah karka cuci kowa karkuma ka keta mutuncin matar Aure ta hanyar yawaita fira da ita,in akwai rabo tsakanin ku duk wuya duk dadi zata zama taka,ka kama kanka ka iya takonka kar in'ƙara ganin wannan rawar jikin naka.


Murmushi yayi yana dan rungumeta yace ngode Kakar da babu ya ita,Nifa bance Sonta nike ba,Aa kawai ina tausayin ta ne..

Dariya tayi tace haka yake wannan karatun.
To Amma in ba so mike kawo Tausayi?.

Shuru Yayi yana ɗan sosa kai kamin ya mata Bankwana ya fito .

Gaisawa sukai da mahaifin shi dake Tsince Tattasai dan yanzu dole tasa shi kasa cefane kofar gida yana siyarwa kuma ba laifi Allah yasama abun Albarka Yana samun Na cefane,dan Basu da Matsala kayan Abinci Babu Abinda Dr nan Bai ajemasu ba.

Jameel kau bayan sunmai addu'a ya fita ya tsaya ya ɗauki wayar shi tare da kiran Alh Adnan.

A mutum ce ya ɗauka dan dama kamar jira yake.
Bayan sun'gaisa yace .
ka warke ko ?zaka iya dawowa bakin aiki dan dama inaso a duba gidan nan aga ya labarin Dabbobin dana bari.

Ido jameel ya dan zaro yana tinanin to wace Dabbba Ya aje? Kar yaje ya barshi ya shiga wajen abinda bai saba dasu ba.

No in kaje kagani karka damu yanzu turomun account number ka zan sama kudin aikin ka 50k.

Sai kuma in sama na abincin dabbobin 10k kayi manege kullum Dari biyu da Hansin zaka kashe in ka kashesu kamin wannan lokacin wallahii nidakai ne.

Tsaki Yayi yana Harara wayar kamin yace .
OGA bafa xai yiyu kanamin ihu ba karka manta jinya nayi ba sannu ba komi Sai faɗa!in baka bukatana saina tafi ka samu wani Dama ai ka kori Iyayen na ni zaman mi zanma?

Shuru yyi kamin yace ina jiran account number xan lissafama komi ya kashe wayar.

Minti biyu tsakani yaji alart.
Da kuma list din kayan abinci kamar haka.

Garin kwaki
Manja.
Barkono
Gishiri.

Dariya Jameel yayi sosai yace
mugu yanzu bayama iya sammasu abincin gidan kwara amasu Wannan Haɗin Bala'in dan shi duk tinanin shi Karnuka ne.

Bayan ya isa gidan wani mutum yayi parking da Machine kusa dashi ya buɗe gidan kamin ya Mikama Jameel din yace .
Gashi inji oga in zaka tafi wani wuri kaje dashi kaima muna biye dakai.

Cikin mamaki yace biye dani danayi mi?

Shuru mutumin yayi tare da tada Machine Yayi gaba.

Ganin ba sarki sai Allah ya buɗe gidan yashiga duk compound din yayi kura ,Gashi duk motocin Gidan Basanan.

A'Hankali yafara kalle kalle wata Zuciyar nace mai ko harda Aymah yatafi wanna karan dan baiga alamar akwai mutane agidan ba.

Karnukan ma bai gansuba ko Haushin su Baiji ba..

Aymah kau tin sadda ya bude ya shigo ta dawo bakin kofa ta bude ta fito barandarvta dan damabkofar a bude take.

Ido yajiyo jin motsin abu.
karaf kau suka hada ido.

Gabaki daya wani mugun zaro ido yayi ganin yanda tayi mugun duhu ga wata uwar rama datayi kamar ba Aymah ba dagani ba wadataccen abinci.

Hankalin shi tashe cikin sassarfa ya nufeta yace miye haka jinya kikai.

Batace komi ba ta kawar dakai.

Wata kafurar tsawa ya bugamata kamar wanda ya girmemata yace .
Ba magana nike mikiba mike damunki?...

Kuka sosai tasa dake cin ranta kamin ta fara magana cikin rawar murya

"Nagaji! Nagaji Wallahi da rayuwar nan, Ya rabbi ka ɗauki ra....


Wani uban tsalle ya daka yana matse bakin ta idon shi yayi bala'in ja cikin rawar murya yace.
Da kaddara Allah zakiyi jayayye,shin kenan bazaki gode Allah da Ni'ima dayamiki ba ta barinki da rai,Mike faruwa dake? Miyasa ba zaki godema jarabawar da Allah ya nufe ki da shi..


Cikinta ta nunamai tace .
yunwa nikeji sosai,nagaji da abinda ya barmun,Cikina kullum yanamin ciwo,Ga jiri dake matsaman.

Miyabarmiki yace yana janyeta daga jikin shi..

Palon taje ta ɗakkomi shi ledar ta gwadamai.
Anan ya gane abinda Alh Adnan ke nufi.
Wa'iyazubullah Tir da Hakin sa dayake kiran matarshi da dabba ashe kam babu babban dabba kamar shi..


A
Cikin Lallami da Kwantar da hankali yace .
kiyi shuru kiyi Hakuri Allah na tare da mai hakuri ina zuwa.

Dan Allah karka tafi tace cikin rauni da kuka.


Bazan jimaba zandawo yace cikin Alhini ganin duk Yanda ta dawo kamar Yarinya
.
Kuka ta sanya sosai tana dafe cikin ta dan ta Tabbata shima guduwa zayyi ya barta.

Jameel kau yana fita kai tsaye kudin yaje ya cire ya shiga kasuwa ya raba kudin shi biyu Dan bama Iyayen shi Rabi kamin ya fara mata sayayya kayan tea irin su indomie ƙaramin gas da Aka samai shi ga Buhu da kayan baki daya harda su biscuits da yan kayan maƙula shi.

Kayan Abinci ma saida yamata aune aunan duk abinda yakamta wanda zataci .
10k dinta ya ɗauka yamata cefa ne da nama kana ya doshi gidan da uban buhu a bayan Napep.

Koda ya sauka ya bude ya shiga.

Ajesu Yayi baranda inda ya barta yace ga shinan kiyi girki kici binda kikeso in sha Allah xan nemo miki duk Abinda kikeso...


Wani maɗaukakin farin ciki ya bayyana ga kyakyawar fuskar ta data sanya Ran bankwana Dashi.
Ya Salam!,Wani girma mutunci taji yaron nan ya karamata a ido, Lallai yacika Jinin Baraka dan Ta tabbata sunson karamci Yaro ƙarami Da Hankakin Manya.

Sassanya murmushi tayi tace wayabaka Kuɗi? kana miyasa ka zabi kashemun?

Shima murmsuin yayi yana dan shafa sajensa yace HAL JAZA'U IHSAN ILAL IHSAN...


Kai ta dagamai cikin murmushi tare da fara kwararo Masa Addu'a Budi Na Alkhairi dan Tabbas tajishi Har cikin Jinin Jikinta Ashe dama Za'a Samu Namiji mai tausayi A wannan Lokacin..

Ameen yace ya koma ya xauna yayi shuru.

Itakam cikin Sassarfa ta cire Hijjob dinta ta fara aiki baji ba gani wani Mugun dadi takeji ga magi da komi irin wanda Maman shi ke amfani dashi ya siyomata.

Cikin awa daya tagama abincinta shinkafa Da miya lafiyayya da salat, gefe kuma naman kajine ta soya su sosai ta masu peper chicken Ta ɗora akai.

Tana gamawa ta dauki lemun daya sai mata guda biyar wanda harda kankara aciki ..

Tire ta samu ta shirya abincin mai rai da lafiya ta dora cokali da ruwa da lemo ta fito waje yana nan inda yake ya jingina da bango.

Gashi nagama tace cikin fara'a da murmushi.

Kai ya gilgiza yace Laaa Bafa dani zakiyiba ke kadai zakina abincin ki dan ya daɗe miki,zan karɓa na yau amma dan Allah gobe basai kinyi dani ba.

Wata shagwaɓa ta kwacemata tace .
to ko gani kake ban iyaba ta karasa tana turo baki da Dire kafa.

Kai ya Gilgizamata yana murmushi kamin ya dauka ya motsa da Bissimillah ya kai bakin shi Dan tabbas Ya biyemata zata iya sawa Ya zare Area wajen shagala da Kallon ta.

Ido ya lumshe sosai yana wani kadasu kamin yace gaskiya Alhamdulillah MATAR OGA NA Ta iya abinci sosai. masha Allah.


Fuska ta kwaɓa kamin ta tashi tayi ciki dan tsaf zata iya kuka yana cemata matar oga.

Komawar Jameel gidan Aymah ba karamin sauyi ya kawomata ba cikin ikon Allah,dan iya bakin kokarin shi yanayi wajen ganin ya wadata ta da abinci mai dadi mai gina jiki,cikin ikon Allah kuma ta dawo hayyacin ta tayi kyau ,Hasken ta ya dawo bata da damuwar komi dan Jameel ya tsayamata.

Jameel kau Sosai yake cikin farin cikin ganin ta dawo cikin walwala sai yaji inama.zai iya tafiya ya barta ya kara neman wata sana'a dan ya wadatata da duk abinda take nema. Amma ina Yanzu tsoro ma yakeji dan tini suka dawo gidan kwana shida kabir anan dakin masu gadin farko suke kwana dan yanaganin kamar za'a iya kawomata farmaki kowane lokaci dan Tini yagama gano Manufar Alh Adnan akanta.

Yammacin wata Alhamis ne Jameel na xaune bakin get da wata takarda yana zane zanen gidaje yaji motoci na tsayuwa bakin get din,kamin ya an'kare har An fara Ƙaƙaniyar buɗe get.

Fuskar manya sodojine suka bayyana kamin yaji sun fara Ɗurrowa ciki.

Da ido ya bisu har suka shiga basu jimaba kuma suka fito gabaki dayan
su suka ficce dan dama ba wanda aka bari.

Adnan daya aje uban tumbi ya doso wajen da murmushi yace.
kayi daidai Jameelu daka kasa ka tsare zakuma ka raka
wanna ma ya tabbatar man da rikon amanar ka dan Haka zanje dakai dan nason Zaka iya .

Murmushi kawai yayi kamin yace tinda ka samu dawowa zanje gida

Ohk ka rufe kofar in kafita..


Wata harara Jameel ya watsamai cikin ɓacin rai da kishin abinda yace kamin ya juya ya tafi Yana sakin Tsaki zuciyar sa nata Hararomai Abubun da zai Faru wai Ya rufe gidan Allah kasanya Karta Saurareka Shashasha.

Koda yaje gida dakyal ya fadama Deedee dawowar Adnan amma bai fadamata dalilin bacin ran nashi ba data Tambata yace dai yana tsoron ya mata wani abu.

Dariya ta zuba tace bar shege,Ni yanzumafa bari inje gidan Adawiyya mu gaisa kwana biyu tana fama da baseer mai tsiro.


Adawo lfy sukaimata ta tashi ta yafa mayafi ta fita.

10mnt ba adauka ba Deedee ta shigo gidan tana rizkar kuka da fadin.

shikenan Asirina ya toni Adawiyya ta rassu jama'a kutayani jaje nayi rashin aminiya,Alkah sarki Rabi wayyo ni Hansatu.

Gabaki daya sunshiga tashin hankali Malam Habu yace.
Ina ake zaman Makokin An kaita ne?.

Ido ta zaro kamin ta sake fashewa da kuka tace.
wai ashe amma tafi da ita kauyen funtuwa dan asamu Aimata aikin gida Ashe acen rai yayi halinsa, yanzu haka kudin Likkafani ne ya gagara wai canjin nasu bashi da yawa kai jama'a yanzu abinma da zaa rufe tsiraicin Mamaci sai ya Gagareka Ga yaron duk sun kwasa mazan sunyi cen Kauyen yanzu motace kawai da za'a je masu gaisuwa.


Sauran canjin 2k din dake hannun Jameel ya zaro ya bata cikin tausayi yace .
Deedee to gashi kije ki basu.


Toto tace tare da karɓa daya tace.
kaima ka rike ɗaya kaji , Ni yanzu bari in'Bisu muje arufe kawata dani kamin lokacinmu yayi.

Malam Habu ya mike tsaye yace bari in maki rakiya tasha ...


Ido ta zaro tace nace mafa ga mota cen bakin Layi nicemafa na tsaidasu sai nadawo kawai tace tana shiga dakinta ta dauki kayan ta
Guda daya ta fito da Zungureriyar Cazbaha da Kwalli sai Powder ( Hoke Dede Yar gayu gidan Mutuwar ake kwalliya kenan😄)


Dariya ta sheke dashi kamin ta shiga shagon Iliya mai Likafani ta yanki yadi hudu akamata doguwar riga har kasa da wata kalar hijjob mai madauri.

Killace abinta tayi ta sallamai tafara tafiya.

Abakin kofar gidan Aymah tayi tsaye dan tagan shi rufe

Iyakarfinta tasa ta fara dukan gidan amma ina Ba abude ba.
cen taji takon tafiya ana cewa waye?
Da sauri ta buya.

Adnan yazo ya bude ya Duddu ba baiga kowa ba.

Haka Deedee taitayimai yana fitowa yana dubawa baya ganin kowa Itakam tana cikin shukoki baya ganin ta.

Ranshi ɓace ya fara
Tafiya dan son ganin ko wane shegene dake bugomai gida Yana ɓoyewa Bayan Layi.


Da gudun tsiya kamar ba tsohuwaba ta fada gidan sai uban nishi take.

A palo ta iske Aymah nata kuka .

Inane dakin da baya shiga Deedee tace cikin sauri.

Arikice Aymah ta mike tana nunamata dakin su na kasa tace gashinan kaka lfy.

Deedee tace in ya fita nafito ta shige da sauri tare da dan nama kofar key ta barshi ciki.

Akasa ta zube dan dama agyara yake ta hau sauke numfashi.

A'Hankali tace. zakaci ubanka Ɗan Yau.
wallahi badai mutum ba Sai dai Allah.
Ja dabaya ga rago ba Tsoro bane. Ah toh munga jiya munga yau sai fatan ganin gobe,Yo ashema haka mijin yake ɗan kwat kamar kwandon tsane salat,Sai uban ciki kamar na Akuyar Yan Caina,Ga kai kwal kamar madubi anya wannan ba ɗan uwan su sheɗan bane dan bala'in kama suke da Wanda Na taɓa Gani Cikin Shara wata Rana kauye.

(DEEDEE INA KIKAGA SHEƊAN😄)

Adnan kau rai ɓace ya dawo ya fara kiran layin Jameel amma basa zuwa.

Kafa ya haɗe yana jijjige jijjige tare da fadin bazaki fadaman wanda ya baki wanna gas dinba?

Kulolina nasa aka saida aka saiman bana da murhun da zanyi girki hasakima ban iyaba.

Oh fine har kina da kaddara da zaki saida kiyi abu to suma bazaki sake sasu ido ba ya karasa yana daga waya ya fara kiran wani layi.

Cikin lokaci katti nan sukazo suka sake kwashe komi aka fitar tare da kawo icce da murhu aka aje.


Da Hannu ya nunata yace ga sauyi nan na gero da dawa in shi kike so gasunan kison yanda zakiyi ya ƙarasa yana wucewa dakin shi ya kira manager dan Jin kudaden dayacemai akwai matsala shigar su account ko sun shiga.

Aymah kau dakin da Deedee take ta isa ta ɗan fara bugawa kasa kasa tace kaka nice.

Deedee ta taso ta bude tana mayarwa ta rufe tare da zama kusa da Aymah tace Anan yake kwana ko waje.

Da hannu Aymah ta mata nunu da sama tace anan sama yake.

Dariya tayi tace maza ɗakkoman Kulki ko Taɓarya Yar nan.

Ido Aymah ta zaro cikin Raɗa tace mizakiyi.

Oho nace ki dakko Deedee tace tana zaro mata ido.

Aymah ta kawomata Deedee ta karɓa tace maza jeki anjima munyi magana.

Fita Aymah tayi inda ta dauki sauran garin dake gareta tun na farko ta jika ta diba ta akwoma Deedee sauran.


Jameel kau zazzabi sosai ya rufeshi komawar shi kuma ba komi bane sanadi sai rufe kofar da akace yayi ya barsu sosai zuciyar sa ke zafi da tafasa ga tunani barkatai da yake,Zazzaɓin daya rufeshi yasashi kashe wayar sa yayi kwanciyar shi.


Adnan kau suna zaune da mangariba aka kawomai abinci Lafiyayye yaji naman kaji sai kamshi yake ga uban lemo da ruwa.

Saida ya gama Yayi net kamin ya danyi aikin shi ya haura sama Yana mika.

Dakin shi ya shiga ya hau kujera da aka kawomai dawowar sa ya kwanta Ya fara baza munshari.


Tsaye take gaban mirron toilet ɗin cikin shigar farar rigarta.

Fuskar ta ta sha farar powder kwarmin idon kau cike yake da Bakin kwalli.

Farin gashinta ta turo gaba sosai.kamin ta sanya wannan hijjob mai mazugai ta daure tare da kallon kanta a madubin toilet din nan.

Ita kanta ta razana Da yanayin nata dan ba Shegen Daya isa yace ba fatalwa bace.

Katuwar Taɓaryar ta ta dauka cikin sanɗa kamin Ta fito.

Matakan benan ta fara hawa sulu sulu Kamar hawainiya.

Dakin farko ta tura ta ganshi ba komi sai kaya kasa da jikkuna wannan ya tabbatar mata dana Aymah ne.

Na karshe ta bude A'hankali Tun palon Ta farajin Munshari kamar kukan giwa.

Murmushi ta saki tana gyaran zaman tabarya kamin ta tura kofar A'Hankali ta shiga.


Tsaye tayi akan shi tana karemai kallo kamin kuma ta dan fara bubbugamai taɓarya dake hannuta a kumatu A'hankali.

Sosai yake juya kai kamin kuma ya ɗan Budesu a hankali.

Toch light din hannuta mai bala'in Haske tasa ta kashemai Yan idanuwa.

Azabure ya mike yana fadin kai waye Anan.

Hannuwan ta ta ware akan katuwar fuskar shi ji kake tass Tass tass har so ukku kamin ta fara jijjiga jiki cikin wata murya ta tsahhi sosai datayi Kasa tace AMANAR DA MUKA BAKA KENAN ,ADNANNNNN...

Ihu ya kurma sadda ya dawo hayyacin shi wanda tagwayen marin nan ya rasashi.

Minaimaku dan Allah.

Ku kunnomai Haske ya ganemu Deedee tace da ƙarfi cikin basaja.kuma ta kai ma glop ɗin dakin duka da taharya hannuta saiga Haske ya gauraye palon.

La hauka wala kuwati illah billah adnan yace yanajin numfashin sa na neman tsayawa sadda Yayi ido hudu da ita sak taimai kama da mahaifin Aymah.

Deedee kau matsawa taitayi gare shi tana wani murmushi tana kusantar shi taɓarya ɓoye abayanta...


Alhamdulillah mungama free page

Maiso ya biya ɗari ukkun sa ya karanta cikim Aminci.

Kamin magana ta Whatsapp number nah sai nabaka account ɗin da zakasa.07038423451

❤️MATAR OGA❤️
UMMY AYSHA

PAGE 11


*Dan Allah dukkan wanda yaman magana yaga ban bashi reply ba Yamun uzuri wayata ce ta samu matsala ba girman kai bane ba kuma izgilanci bane aa kawai Tsautsayi yafaɗa kantane nikaina hakuri Nike Allah kasa ku fahimceni masujin Haushina kuma ku yafeman*.


***Ido ya hau sake gwalewa amma dayake mahaifintane aranshi tsaf ta koma mai shi.

"Yaro ina buƙatar samun kusan ci dakai a makwancina Deedee tace tana daga taɓarya nan ta kwaɗama Makunnun hasken ɗakin ya sake yin duhu.
Wani Gigitaccen ihu yasa yana ƙoƙarin mikewa ya sake faɗuwa awajen.
Yayin da ta Daka tsalle tayi kanshi ta hau yakushi da cizo cikin wata makirar murya mai wani kuka kuka mai tada hankali take fadin sai Yabita kushewar su ya girbi abinda ya shuka.

Adnan kau tashin hankalin da yake ciki a daidai wannan lokacin bamai kirguwaba ne, Dan gabaki ɗaya lakkoki jikinsa sunyi mugun week baya ko iya daga Yatsunshi dan Yariga' ya tsadaƙas kawai fatalwar ubanta ne .
Deedee ta daga hannu da niyyar sake kwashe shi da mari taji ta cikin ruwa mai bala'in zauri wanda ko ba'a fadamata ba tason fitsarine ya sakomata ranta kau ya kara ɓaci dan Deedee ta tsani zauri kona Gishirin Ƙunci kuwa.
Kanshi ta cafka ta dinga kalangu dashi shikam yakasa komi sai wani gurnani yake kamar tsohon rakumi.

Saida ta gaji dan kanta ta sake kunna hasken dakin a fakaice tana zubamai ido da sakin wannan murmushin dayake sanya barin jikin shi aiki.

"Ya makomar Auran yata take gare ka ?tace tana juya kai da ido.

"Fabu Aule na akanta na taketa taki ukku yace cikin mawuyacin hali dan bakin shi ya riga da ya karkace..
(BABU AURENA AKANTA NA RIGA NA SAKETA SAKI UKKU)

Wata Sassanya guɗa Deedee ta saki kamin ta dinga juyi firrr cikin ɗakin kamar tantabara ita da likkafanin ta.
A idon Adnan kau gani yake kamar tashi zatai sama.

Cen kuma ta juyo ta dakamai tsawa tace dukiyar yata?
Dukiyar kace daka kwace kai na tarawa?
Miye nufinka a kanta?

Shuru Yayi sai Ya'u dake dilalomai.

Saida tasake juyi kamar sabuwar fanka kamin tass ta kwashe katuwar fuskar shi da mari tace.
magana nikema.

Cikin wahala yace .

Inatan dukiya ! ta balmani ,Alhati kai akuli tan Allah ka kaini atibiti Ɓalin jikina ya tanye.

(Inason Dukiya! Alh kai Hakuri dan Allah ka kaini Asibiti Ɓarin jikina ya shanye)

Dakyal Didi ta rike dariyar ta jin cikin awanni kaɗan ya koma maganar yara .


"Au mu Asibiti mukezuwa? muda muka riga mukai wafati .
Babban Asibitin da zaka shine kushewata zan kaika acen ne zakai bacci ka huta harda saleɓa badai takamar ka zalinci ba,Adnan minaima,Miyasa na cancanci haka Wajen ka?


Kuka ya fara kamin Deedee ta dakamai tsawa tace rufe ido .

Ruff kau ya rufe cikin sakan daya ta ɓaccema ganin shi.


Ya rasulu ya manzon Allah yace Cikin ranshi. lokacin dayaga walam kamar an yi walkiya an ɗauke Babu Alh Abdulkarim Mai Dala a ɗakin.

DeeDee kau tana sauka kasa ta cire kayan jikinta ta fada dakinta tana sauke numfashi.

Wata mahaukaciyar dariya ta hauyi tana tino yanda ya dinga magana da yanda yake zare ido Kamar sabon Angon dake neman Hanya.
Cikin dariya tace honi Deedee,In nasa kaina sodojima mantawa suke da matsayin su,Yo mantawa mana ke da ace a siffar jinnu najemai ai da tini yasanya bindiga ya karni amma najemai a siffar da uban kowa ke tsoro wato fatalwa,Gashi yanzu na gano kan gaskiya.

Saura Aymah ina so naji wacece ita ya matsayin mahaifin ta da Alh Adnan yake miye Alaƙar su.

Allah sarki jamalun Deedee ashe da matarka kake ta samun kusanci shiyasa kaƙi natsuwa, in sha Allah sai nayi tsayuwar daka An daura maku aure kaida Aymah mai kyau in ga yan yaranku tagwai tagwai.
Sai kuma ta buga ta gumi tace.
To amma ya za'ayi Ɗan shekar Ashirin da shidda ya auri yar shekara 36 ohni Deedee to taya zai iya da ita kar aje asake cutarta a karo na biyu ta karasa tana mikewa tsaye ta fada wanka danjinta take kamar toilet sai zauri take ..

Bayan ta gama ta ɗauro Alwallah ta fito ta hau kan sallaya ta dinga nafila da Nenan zabin Allah akan rayuwar da Aymah zata fuskanta dan suma ba wani karfine da suba.

Washe gari Aymah ce ta bugo sakko ta fado dakin DeeDee Ta isketa zaune akan sallaya.
Bayan sun gaisa tace Kaka yau mizakici naga garin ya kare kuma ni ban iya Amfani da wannan geron da yakawo ba.

Murmushi Deedee tayi tace karki damu yar nan ina zuwa amma kamin nan kije ki fara duba mijinki ki dawo ina da magana dake.

Aymah ta dan bata fuska tace.
babu ruwana dashi kaka kwara na tsaya matsayin daya ajeni.

Deedee ta sake murmushi tace .
A'a kije dai,kwara ke ki sauke hakkin shi dake kanki kinji Yar Albarka.
maza jeki gaishe shi , inma kinga bacci yake ba sai na fitaba muyi aikin tinda baison da zuwana ba.


To ! tace ta tashi ta fita ta nufi ɗakin shi dan itama yunwa takeji .
Fatanta Allah yasa bacci yake Deedee ta gwadamata yanda zatai amfani dasu.

Tin palo takejin mugun wari kamar na mushe ga zarni.

Cikin sassarfa ta karasa cikin dakin tana toshe hanci da tambyar ko lfy.

Tana tura Kofar sukai ido hudu dashi yanata hawaye ga wayar shi cen nesa dashi tanata haske alamar kira ake.


Aymah ta kalleshi tace. lfy ka cika daki da wari haka ?kiye haka?ko gudawa kake?.

"Kati nayi yace cikin gwamutsatsar hausar shi.

(Kashi nayi)

Ido ta sake zarowa dan yanzu ta tabbatar da kaddara shanyewar ɓarin jiki ya kama shi.

Sake zubamai ido tayi taga yanda hannushi ya sandare da kafa guda.

Adnan matsala ka samu garin ya , faɗuwa kayi ta karasa cikin rauni tana zaro ido.

"Ma'aifinkine cila,cine ya jaman,Fatalwa yaman,yakuma taukeni yaje dani kucewalci kaca ta maceni ya karasa yana ɓarkewa da kuka .
(Mahaifinki ne sila! Shine yajaman,Fatalwa yaman,Yakuma ɗaukeni yaje dani kushewar shi kasa ta matseni).


Duk yanda Aymah taso ta daure kasawa tayi nan ta shiga wata irin dariya idonta jage jage da hawaye, dariya da tasa har faduwa take tana tashi amma ina

Please Login or Register in order to submit comment