Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi da babu alamar kwanciya har lokacin kyam yake tsaye kamar falwaya.

Tsaki yyi tare da sakeyin kwafa akaro na ba adadi kamin ya ɗauki wayar shi ya kira Driver shi dan su dan fita dan bazai iya tuki ba amma yaji wayar duk kashe.

Kanshi ya dafe yana tino magana da yace dasu kowa zai iya kashe wayar shi yaje ya samu dogon hutu na tsawon wata daya kamin su koma bakin aiki ashe kanshi yayiwa tsiya.

Babba riga ya zuba tare da fitowa palo yana sake bubbuɗata dan rufama kanshi Asiri.

Baraka kawai ya iske tana goge kayan kallo har kasa ta gaidashi ya amsa cikin isa yana niyyar yin waje kuma ya dan juyo yace "Ko mijin ki ya iya tukin mota?

Juyowa tayi dan ta tabbatar da da ita yake koya .

Kai ya jinjinamata Alamar tabbatar wa.

Cikin ladabi tace.
" gaskiya aa yallabai som Bai iyaba gadi dai ne yake yi Asibitin Hajiya amma akwai Babban Yaron mu ya iya dan da yana tuka motar makwabcin mu sunayi jigila Dutsama zuwa Katsina Kamin kuma Allah ya.Kawo sanadi mai Abun yayi accident ya rasu aka kuma rasa motar ya dawo gida da xama.

Fuska ya yamutsa yace akiraman shi yanzu na bada 30mnt.

To tace tana ajiye Kyallen hannuta tare da zaro wayar ta da Aymah ta saimata ta fara neman layin da aka yi save da Wannan Yaron(Alkunya mutanan da wa yaran su na fari)

Bayan an ɗauka tace .
Wannan Yaron kazo yanzu maza dan Allah nan gidan da nike aiki,eh bayan mu nan,to shikenan ina jira Allah yayi albarka ta karasa tana datse wayar tare da kallen gefen Alhaji Adnan da yaketa mutsu mutsu yanajin kamar an samai maciji cikin wando duk ya kasa sukuni sai uban faɗi yake karama Babba rigar shi.

Alhaji yana hanya cikin izinin Allah tace tana mikewa tayi kiching.

Kai ya jinjinamata yana auno hukuncin da zaiwa Aymah gashi ta hanashi aikin shi ta kuma ki aminta da shi.

Wani tinani yafara wanda kuma cikin lokaci ya aminta dashi ,Tabbas ya aminta dashi dan Babu makawa fitar da tayi jiya wani taje ya kwanta da ita.
Ranshi ne ya sake ɓaci yaji matukar zafi a zuciyar shi dan shikan shi ya son yana son Aymah kwarai amma shi bayason matsawa yana bama aikin sa lokacin sa kwarai baya so kamai kutse cikin lamarin Aiki yanzu ka zame masa matsala .

Baraka da har ta koma kiching ta sake fitowa har kasa tace ''Alhaji ya iso yana cen wajen get din farko.

Fita ki shigo dashi yace batare da ya kalleta ba.

Tashi tayi ta fita ba ajimaba suka dawo da wani Matashin saurayi mai tsananin kyau da haiba, Chocolate colour ne irin mai hasken nan wato sirkin madara da milo amma a idon wani zasu iya cemasa fari ma,Yana da doguwar fuska mai dauke da manyan idanuwa masu yalwar Gashi girar shi ciccike ,sumar kanshi kau ya mata wani aski mai masifar kyau sai sheki take da ganin ta kason ta fulanine dan wani kwarya kwara takeyi tsabar kyau da gyara,Ga
Wani shegen saje ya adana a kan fuskar tashi daya zagaye suut mai matukar kyau daya kara haskashi,Lips din shi na kasa light pink ne sosai saina saman mai dan duhu kaɗan,Masha Allah zanso kuga wannan haɗaddan matashin da a shekaru baifi 25 ba,Riga da wando ne yan kanti a jikin shi duk da ba sabbi bane amma kuma basu sha wahala ba,A wanke suke tass a goge Sai kamshi yake .

Baraka tace wannan yaron ina rokon Allah yasa Alkhairi ne ya kawoka gidan nan.

Ameen Inna yace cikin Daddaɗar muryar sa.

Sallama tayi ta shiga palon Yayin da Alhaji Adnan ya amsa .
Tace gashinan tsaye bakin kofa.

Ohk shigo dashi yace yana zubama kofar ido.

Fita tayi suka dawo tare da sallama suka shigo su duka suka samu kasa suka zauna cikin sanyin muryar sa mai nuni da natsuwar sa da tarbiyyar sa yace. Yallabai barka da rana .

Alh Adnan yace Lfy ka iya mota?

Kai ya daga mishi kawai dan in dai isa ce yafi Alhaji Adnan ɗin ma .

Key ya bashi yace gashi na daukeka aiki duk wata zan baka dubu hamsin yayima ?, Dan ko bana nan ina so ka dingamun wani aiki ne da saina tafi xan barma shi .


Tom Allah ya bani ikon yi yace babu yabo ba fallasa dan ya kula Alhajin ɗan rainin wayone gani yake dan zai bashi kudi ihun murna zaitayi yana .masa doddofa ai aikin wahala zai mai dan haka ba wani murna da zai zage yanayi zayyi godiya ga Allah dan yason shine mai tsara komi kawai...

Key ya bashi yace gashi muje ka kaini wajen da zan huta.

Karɓa yayi kamin ya juya ga mahaifiyar shi da gabanta ke faduwa ta manta batajamasa kunne ba tason halinsa sarai.

Gwiwar kafarta ya dafa cikin sanyi da wani so dake tsakanin uwa Ɗa.
Yace Inna mu ki samin Albarka ki kumayimin fatan Alkhairi ga abinda Allah ya zabaman kinji?.

Kai ta jinjina kamin tace" In sha Allah Wannan yaron zaka hadu da rahma Allah a duk inda kake , Allah ya tsareka ya baka kariya yasa Albarka a cikin abinda zaka fara kaji, tashi maza kuma karka manta da addu'a duk sadda zaka hau abin hawa.

In sha Allah yace yana mikewa.

Alh Adnan dai baki ya taɓe yana ganin yaushe xaka tsaya kaita rattafa zance haka kamar tsohon Aku,Kai kanama talakka ai kuka ya dace kaitayi kullum kana tinanin yazaka samu manyan kudi suzo amma ka tsaya doguwar magana wannan ke nuni da cewa bakama nazarin zuwan su(Nidai kam nace Dattijo mai kan kwakwa ka manta Allah ne ke tsara komi😄)

Fita sukai inda ya fara xazzagayawa dashi cikin gari shikam ya hakimce tare da sakin rafkeken cikin shi da ya zamema halin da yake ciki Garkuwa.
Sun daɗe Yana zaga gari har ya gaji gabaki ɗaya fuskar shi bayyane take da ɓacin rai saboda shidai yaji an'ce wajen shakatawa amma ya tambaye shi pack zasu yace a'a yayita tafiya dai sallah kawai sukeyi su cigaba sai cen yamma suka dawo.

Ya sunan ka? ya tambayi Saurayin.

Sunana Jameel.

Ohk koda bazamu fitaba ina bukatar karfe takwas ta dingama anan gidan ,in ka saɓa lokaci zakaji a kudin ka.

Jameel tace'' tom yallabai banki na nakaba amma ina da ka'ida nima.
Bana tashi bacci in nakoma bayan Asuba sai ƙarfe goma,Tashina kamin lokacin dana tsara Tamkar rusa rayuwata ne,dan haka ka zafcare farashin awanni da zanyi daga naira daya har zuwa abinda kace zakabani bazan damuba ya faɗa cikin gaskiya da gaskiya ba tsoro ko shakka a tattare dashi.

Ido Alh Adnan ya gwalo dan tinda yake babu wanda ya tabamai wannan musun.

Ya buda baki zaimai.magama Jameel din ya watsamai manyan idanuwan shi dake nuni da ranshi ya fara ɓaci da maganganun Alhajin nan.

Wani irin kwarjini yama Alh Adnan din hakan ya sashi faɗin.
Zan shawara ya karɓi key din ya shige ciki yana tinanin wannan ɗan ubanwa ye dayake da isa kamar ba talakka ba .


Mtssss Jameel din ya tsaki saki yana gyara zaman wandon shi Ya fara tafiya cikin sassarfa jikin shi ko ina murde yake dam-dam da gani yana bama motsa jiki lokacin sa da kuma ɗaukar Abu mai nawie dayasa Damtsen Hannun sa murɗewa.

Wajen pampon daya gani ya isa ya fara wanke fuskar shi kamin yayi Alwallah ganin mangariba ta gabato kamin ya fita daga gidan.

Bari mu waiwayo Aymah

Tin kwanciyar da tayi bacci mai ƙarfi ya fizgeta bata sake sanin duniyar da take cikiba sai wajen shidda na yamma ta motsa a furgi ce dan batai sallah azahar da laasar ba ga mangariba ta doso kai.

Toilet ta shiga cikin hanzari dan gabatar da wanka da kuma Alwallah.

Saidai tana shiga ta gane cewa period Yazo mata, ajiyar ajiyar zuciya ta sauke tana mai godiya da Allah dan batason lokacin sallah na shigewa bata gabatar ba.

Bayan ta ɓata lokacinta tayi wanka mai kyau ta ɗauki pad ta lika ga pant dinta ta zuge window da niyyar yada Takardar daidai lokacin da ya rufe pompon ya fara tafiya cikin mugun sassarfa.

Dum Dum Dum
Gabanta ya shiga lugude da batason na miye ba.

Kara leƙawa tayi daidai lokacin daya kulema ganinta.

Subhanallahi waye wannan tace cikin wani yanayi na mamaki.

Som ta manta da abinda ya faru tsakaninta da Adnan riga kawai ta zuro aguje ta fito daga dakin nata tayi nashi ta Banka kofar da karfi tare da fadin .
Yallaɓai waye ya fita daga gidan nan yanzu?waye shi? miyazoyi? kason da zuwan sa ne? wajen wa yazo ta jeromai tambayoyin lokaci ɗaya.


Yallabai kau dayake gaban madubi cikin takaici yana kallon yanda yayi mugun amalala cikin wandon shadda jikin shi ya juyo a fusace ranshi ɓace ya kaima wuyanta mugun cafka,Tsabar masifa naman fuskar shi har rawa yake wajen cewa ubanwa kika kauracewa?

Ido ta zaro dan sai lokacin ta tino ma abinda ya faru amma yanzu ba Wannan ne gabanta ba waye yazo.

Cikin wuya da neman wullawa lahira tace.
Am.. sa..keni sai nama bayani amma fadaman waye wancen.

Kara maƙureta yayi ranshi ɓace ya bugamata tsawa yace .
"ubankine,nace ubanki ne shegiya kwartuwar banza kwartuwar wofi daga ganin shi har yawunki ya Tsinke ko,Nace har yawunki ya Tsinke ko,dama ina sane da duk abinda kike ido na zubamiki to yau kinzo hannu ya karasa yana ware hannuwan sa ya kwashe farar fuskarta da mari.


Wani wulll tagani na wucin gadi kamin ganinta da jinta ya dawo na dan lokaci.

Karfinta tasa gabaki ɗaya ta daddage ta zabgama hannuwan sa cizo iya karfinta.

Taurin rai na soja da bakin hali baiko motsa ba sai ma canza hannu da yayi daga rikon wuyanta da yayi daga hannun dama zuwa hannun hagu.


Ganin numfashin ta ya fara barazana barin rayuwata yasata kallon saitin wandonshi bata tsaya shawara ba takai hannu tamai mugun riko tare da mai wata makirar matsa data nemi cizgemai makaman yaki.

Ihu ya kwallah yana sakinta kamin ya zube kasa warwas yana faɗin" shikenan ta kasheni ta ciremin mafitsara innalillahi wa inna ilaihi Raji'un.

Aymah kau aguje ta fita daga dakin tana numfashi sama sama,ta waje ta rufeshi tabar key ɗin jiki,kamin ta shiga dakin ta ta faɗa Toilet ta dinga shan ruwan pampo ta fito tana layi ta fara kwasar wasu kayayyakin ta a gulguje ta fito, kiching ta iske Baraka cikin tashin hankali da rawar jiki tace Baraka muje muje in saukeki karya fito .

Waye ?

Baraka ta fada a rikice.

General ne yana so ya kasheni ne ta fada tana nunamata sashen wuyanta da yayi mugun ja...

Gas baraka ta kashe kan kace mi ta watsa dagudu waje gabanta na faduwa Aymah ta rufamata.baya.

Tare suka fita Aymah taja kofar Kamin cikin tashin hankali ta kunna motar ta ta bata wuta aguje suka fita daga gidan bayan masu gadin sun wangale masu get.

Saida sukaje kwanar su Baraka ta tsaya kamin ta fashe da kuka tana fadin har anzo lokacin duka Baraka nashiga ukku rayuwata ta fara lalacewa ta karasa tana kwantar da kanta akan sitiyarin motar.
Baraka daketa raba ido tace kiyi hakuri Hajiya amma Miyayi zafi haka da ake zancen kisa harda wannan shaƙar haka?.


Aymah ta ɗago da niyyar bata amsa numfashinta ya tsaya cak jini ya fara fitowa ta hancinta.

Ihu Baraka ta kwallah dakyal ta iya bude motar cikin tashin hankali ta fada tsakar gidan su tana fadin "Wannan yaron! Halima! Kabeer! kuna ina zata mutu.


Waye zai mutu? Jameel da shigowar shi kenan daga masallaci ya tsinci sauran kalmarta.

Ai kamar jira suke gaba daya suka fito daga daki da alama sallah suke.

Baraka tace Hajiya da nikema aiki ce takarasa tana nuna musu waje.

Gabaki dayan su suka fita da sauri jameel ya fara buɗe mazaunin Driver Aymah tayi luu ta faɗo akan shi yayin da yayi saurin dukewa kasa gabaki dayanta ta fafo akan shi.


500 ne kacal ba yawa kimin magana ta Number Nah 07038423451

Humra sirri.
Maganin mata na mussamman
Ga kai buka chart me Harkar ta manyan mata ne in kinson baki shiryaba karmu ɓatama juna lokaci wannan nike.haɗa abina da kaina ba tallah nikewa kowaba tawace kashin kaina kunson kuma bazan siyar da akuya ta dawo tana cikin dangaba aheee😜


❤️ *MATAR OGA NA* ❤️
*MALLAKI*
*UMMY AYSHA*

*PAGE FOUR*

Aslm Alaikum masoyana ina maku fatan Alkhairi da nuna so da kulawa akan duk labarin da zanzo muku dashi.
Da fari dai ina so na baku hakuri a dakatar da rashin *Mijin zee* danayi na dasa wannan, saboda wannan din yafi wancen amfani ga rayuwar da mu mata muke fuskan ta.

Abu na biyu kuma an samu kura kurai misali wajen sunan Yaron Baraka wato A/K wanda namayar dashi jameel yanzu, Nabeel kuma na mayar dashi kabir,Saboda na daɗe da fara littafin aka fara azumi na dakata sai yanzu naga dacewar cigaba to kuma ban samu page one nd two ba saidaga baya so kawai zamuje da sunan jameel din ne nagode ina fatan kun fahimce ni.


***
Innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un wannan yaron karfa ace ni na kasheta kason abin fada bayayin wahala wa mutane.

Jameel da yaketa kallon sashen wuyanta da yayi sawun riko alamar shaka ya dago jajayen idanun sa ya zubama mahaifiyar tashi tare da faɗin" Inna banson mizamuyimata ba, amma mafita daya akaita Asibiti kawai.

Yawwa hakan yayi akaita Asibitin ta kawai tace cikin sauri.

Halima ta kama mai kafafuwan ta suka sanyata bayan mota ya shiga mazaunin Driver Inna su ta shiga gefe yayin da sukace da kabeer ya shiga ya kula da gida suka ɗauki hanya.

Basu wani jimaba suka iso mahaifin shi malam Habu na zaune kan Benci da redio yana jim labarai ya tashi da fara'a ya buɗe get din Asibitin yana fadin" Hajiya barka da shigowa.

Jameel ne ya dan leko yace barka Baba sannu da aiki.

Cikin mamaki mahaifin nashi ya sake kallon motar da kuma kara dalla shi da fitila duk da hasken fitulun dake harabar wajen kamin cikin mamaki yace , kaine da Mota Hajiya?

Kai ya dagamai kamin ya shiga yayi parking Baban su ya rufe kofar da sauri yayo kanshi daidai sadda Baraka ta fito daga motar.

Wani irin sauri Malam Habu ya kara ganin matar tashi da gaggawa ya cimmasu yana mai sanya hannu wansa ya kama na Baraka.
Kamar jira take ta fashe da kuka tana fadin "Baban su Hajiya ce gatanan kwance babu lfy tana aman jini ai maza a kirawo ma'aikatan jinya dan Allah su duba ta.

Jin hakan yasa shi fadin" innalillahi wa Inna ilaihi Raji'un. Tare da sakin Baraka da sassarfa ya fara kiran nus din cikin lokaci suka fito da whell chair dan sunson bai wuce majin yaci aka kawo ba yake neman kashe masu Dodon kunne...

Waye babu lfy malam Habu ka bude baki kanata watsamuna kira haka? Haba da Allah ka dinga daukar rayuwa da sauki.
Cewar wata Yar tsamurmura dake sanye da fararan kaya kamar sabuwar gawa sai karairaya take ala dole ita ma'aikaciya ce.


Jameel kau dake tsaye ranshi yayi matukar ɓaci cikin bala'in saurin maganar dayakeyi mai haɗe da in ina duk sadda ranshi yakai matukar baci ya nunata da yatsa yace.

Ke kikama kanki..ɗi..yar Yara ko in wanke miki fuska da mari, maza kwasheta ku shiga da ita ko in'baki mamaki Ya karasa idon shi rufe cikin muguwar tsawar data sanya jikin su ɓari.

Malam Habu ya matsa ya rikemai hannu yana faɗin Kayi shuru kaji yaron kirki,Kyaleta Allah ya tausashi zuciyar Jameelu na,Kuma Jamalun Deedee .

Shiru yayi baiko motsa ba kuma bai bude idon saba.

Ke kuma Ramatu Hajiya ce ke bata lafiya shiyasa kikaji ina kiran ki da ƙarfi amma kiyi hakuri.

Jin haka yasa da sauri suka karaso motar suka fiddota har lokacin kadan kadan jini na zubomata ta bakinta da kuma hancinta.

Shikau jameel A'Hankali ya fara bude idon shi da sukayi wani mugun ja, Duk da duhun dake saman sararin samaniya amma kana ganin yanda hasken fitulu suka tona Asirin hawayen dake kwance a cikin kyawawan idanun nashi.

Wacce aka kira da Ramatu Kallon shi tayi sadda zasu wuce da Aymah tanajin wani bala'in tsoro da shakkar shi ,ga wani kwarjini da yamata, a wani sashen kuma na zuciyar ta ya bala'in burgeta mussamman sadda yake magana nan Cikin sauri da sauri gashi in inarsa ta motsa saidai ya rufe ido kamin ya samu magana tayi daidai Ya buɗe..

Yana ganin wucewar su yayi tsaki yana kallon Baban nasu.

Malam Habu yaja hannusu su duka suka koma gefe dan yason dokar Asibiti ba A bari ka tsaya wajen majin yaci yayin da DOCTOR ke duba shi.


Bayan sun zauna nan Baraka ta shiga koramasu bayanin abinda ya faru .

Jameel na jin su baice komi ba Amma har cikin ranshi yaji mugu mugun tsanar Alh Adnan dama shi bai maiba tin farko.


Baba habu ya gilgiza kai cikin rauni da salon iya magana na Dattijon Arziki yace.
" Kai Maman su Allah ya ganar da wasu mazan,hakika wasu mazan na jahiltar zaman Aure,suna ganin duk sadda suka nemi mace suka samu aka basu ita tayi sallama ta shigo gidan su to daga ranar ta zame masu baiwa,ta zamemusu takalmi duk inda suke so zasu taka da ita,Suna ganinta kamar baiwa babu mu'amullah mai kyau da zasu iya yi da ita,nikam aganina daga sadda iyayen ka suka baka mace ka kulle kofa da ita Maman su ai angama maka komi ko? , Sannan matan mu marufin sirrin mune,duk sadda muka kasance masuyin rayuwa mai dadi da matan mu wallahi azeem sai munfijin dadin rayuwa koda ba ko sisi,Ke Baraka banason Allah yabani arzikin da zan gujewa iyalina kwara na zamana cikin rufin Asiri nafi samun lokacin da zan sauke hakkin ku dake kaina,Ta yanda zan karɓi sakamakona da hannu dama a gobe kiyama..

Hawaye Baraka ta sake sharewa tace.
" Wallahi Baban su na sani, Kuma ina mai kyautata maka zato,Bazan ce bama faɗaba saboda tsakanin halshe da hakorima ana sabawa ɓalle mutum da mutum,Amma tabbas samun ka a wannan lokacin Babba rabone saboda irin ku kunyi karan ci.

Wannan yaron dan Allah kuyi koyi da halin mahaifinku dan Allah, Duk wacce Allah zai baku kumata irin rikon da mahaifin ku kemun ,kunga dai yanda muke rayuwa dashi da daɗi ba daɗi amma babu abunda ya dakushe daga fannin kulawar da yakemun,Bana tinanin tin tashin ku kuntaɓa ganin muna faɗa dashi yace nace,To munayi.
Amma adaki,sannan ba ihu yakemun ba,Yana mun nasiha ne ta yanda zan fahimta amatsayina na mace mai karancin tinani,Ina ƙara godiya a gareka Ranka ya dade ta karasa tana haɗe hannayenta waje daya tare da sakin yalwataccen murmushin daya sasu duka darawa.

Kai kawai Jameel ya gilgiza dan yason duk Abinda ta fada gaskiyane, kuma shi kanshi baya fatan ace ya zauna da mace dan ya kuntata mata ,Yafiso ya zauna da wacce zata soshi domin Allah, yabata kulawa ta bashi, Ya tarairayeta ya bata lokacin sa itama ta bashi nashi.

Suna nan Nursing ɗin nan ta fito tana yanga tana gwatso da neman karewa tace" Dr Aymah na kiran Baraka.

Tsaki kawai Jameel yayi jin yanda ake kiran sunan mahaifiyar sa gatsau kawai dan batada kuɗi ,gashi wannan yar shilar har tasamu bakin Kiran sunan uwar su kai tsaye.


Da sauri Baraka ta tashi tace da malam habu tana zuwa ya dagamata kai yana fadin .
"Kiyi dai a sannu wajen a kwai sulɓi sosai tafi a hankali Kinji.

Murmushin gefen baki kawai Jameel yayi soyayyar iyayen nasu na tsananin burgeshi da bashi sha'awa, bakaramin taka tsantsan mahaifin su keyi da mahaifiyar suba bayaso ko ruwan sama na dukan ta( *WAYYO SOYAYYA DAƊI WLH ,ALLAH KA BARMU DA MASOYAN MU NA GASKIYA MASU GIRMAN KAI KAU DAN KAR IYALIN SU SU RAINASU ALLAH YA TSINE MUSU YAN KUTUMAR BURA'UBA*😎)

Koda ta mata jagora har dakin da take ta juya Baraka kuma ta rufe Kofar tare da ƙara sawa da sallama tace sannu Hajiya.

Aymah da hannuta ke sargafe da karin ruwa tace.
yawwa Baraka sannu,Waya kawoni nan?..

Dan Murmushi tayi tace ki gafarceni Hajiya yaro ne nasa ya kawomu da motar ki ganin ki cikin wani mawuyacin Hali.

Ido ta lumshe hawaye na zubomata tace.
" Baraka wai duk namijin da zai daga hannu ya dokeki yana sonki kuwa,Anya Adnan baya shaye shaye kuwa?..

Shuru tayi kamin cen ta nisa tace.
"Kiyi hakuri dai Hajiya aita gayama Allah, Allah zai kawo mafita.

Baki Aymah ta cije tana kallon ruwan hannun ta kamin kuma ta tashi ranta ɓace ta cizgeshi ta diro daga kan gadon.

Duk yanda Baraka ke mata magiya akan ta tsaya karta tashi amma ina zuciya ya ciyota(A kiyayi ƙure mai hakuri) .

Fitowa sukai tana ta sauri kanta hula ce kawai babu ko mayafi sai doguwar rigar data zuba data fito wanka dan ma Allah yasa dare ne ba kowa zai gane ba.

Kai tsaye motar ta ta shiga da hanzari Baraka ta buɗe gefe ta shiga kamin a karo na farko ta riko hannuwan ta tace.
*Ummu Aymanah*.

Da sauri Aymah ta kalleta dan Tinda Iyayen ta suka rassu babu wanda ya taɓa kiranta da sahihin sunanta cikakke kamar yau, batataɓama sanin tason sunan taba dan kullum Hajiya take cemata.

Kai Baraka ta gilgiza cikin dattako da girma tace .

Duk abinda hakuri baiba Aymanah rashin sa bazai ba,sannan babu abinda ke ɗorewa sai ikon Allah,fushi ba naki bane , Domin ke macace mai rauni ,Aikin mi kike da kika bar damuwa ta shiga ranki,ina Alkur'ani ki?Ina ilim ki da bazakiyi amfani da koyar wa annabi Muhammad sallalahu alaihi wassalam ba ki magance damurmwar ki,Ayma nason ban haifekiba amma kuma inajin ki kamar kanwata,Shawara daya ki kara dagewa wajen kyautata alakar ki da Allah,kana karkiyi zalinci,kina nan zaune zakiga sakayya daga mai sama,ki yawaita sadaka tana magance masifa ko wace irice,Ina mai baki hakuri da baki shawara da karki yarda kije wani wuri a halin da kike ciki yanzu kiyi hakuri ki koma ki zauna daki da safe sai ki koma kibashi hakuri, tana gama fadin haka ta bude motar ta fita tare da zagayowa ta budema Aymah ta kamota kamar jaririya haka suka koma ciki,Kai tsaye office dinta ta nufa Baraka na rike da ita ganin yanda take rangaji kamar wadda tasha giya.

Nasiha Baraka ta sakemata kamin tamata sallama tace zasuje gida.

Harta sanya hannu zata bude Aymah ta dago jajayen idanunwa ta kalleta tanajin wani girma da mutuncin matar na ratsa ta lungu da sakon ta, akaro na farko taji ya kamata ta girmamata ta daina fadin sunanta gatsau kamar yanda ta saba,Ko ba komi yau ta mata abinda iyaye ne kawai zasuma shi..
Kanta ta mayar a kasa tace nagode Baba Baraka Allah yasaka da Alkhairi,kana kicewa Baba ya rufe get din kuje tare da Asuba ya dawo.


Madallah Nagode Baraka tace tafita tanajin tausayin Aymah a ranta , Duk da batacemata ga abunda ke faruwaba amma tana tare da ita tanaganin yanda shakkar mijinta ke hanata sukuni in dai yana nan, ya riga ya samata tsoron shi cikin rai(Nikam nace gidan miji ba barikin sodoji bane Adnanu mai kan kwakwa)

Koda Baraka ta fita ta faɗama Baba gida suka wuce sunata tattauna maganar Akan Aymah da Alkawarin sata cikin addu'a su dan ta masu halacci yanzu sular tace suke samun ci dasha har so ukku arana.

Jameel dai baice komi ba dan shi dama miskiline na bugawa a jarida magana hamsin zakayi muddum baka sashi ba baya tankawa.

*Alhaji Adnan*

Tinda ya zube kasa yake ihu yanajin kamar ranshi zai fita,Ya daɗe a wannan yanayin kamin ya samu sukuni yatashi yana kokarin bude kofar amma ta rufe ta waje.

Mai gadin gidan ya kira yazo ya bude shi kamin ya samu fitowa yana sakin numfashi sama-sama.

Dakinta ya tura ya shiga wayam. Dama Yayi tinanin haka dan sama sama yaji tashin motar ta, kenan nufinta ta hallaka banza , aiko zai maganinta yason duk inda taje zata dawo tinda bata da gidan daya wuce nashi .

A daddafe yayi wanka, Bayan ya gama ya fito dakyal yake tafiya,Zaman palon ya fara yaji ya gaji ya koma daki da niyyar fara aiki amma ya kasa gaba daya ta lalatamai wannan ranar yanaji yanagani ga xafin da yakeji kamar zai hallaka shi.

Karfe goma da rabi na dare yaji kamar zai mutu ko wando bai iya sawa dole tasashi lalubo number jameel.

Saida yamai kira ukku kamin ya dauka yayi shuru.

Maza kazo dan Allah ka kaini Asibiti Alh Adnan yace cikin sanyi da murya dake nuni da yanajin jiki.


Jameel din yayi shuru kamin kuma yace" to ya ajiye wayar ya tashi ya sanya kayan shi ya fito ya iske Inna su da Baban su waje sunata firar su abin su cikin nishaɗi, gefen su gyaɗa ce Baban su na

Please Login or Register in order to submit comment