Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Abokan ƴaƴan nasa dayace muje mugan su, to kinga kau sai gdya,yanzu mota ukku na saya naki daya nawa daya na Baba daya,.

Taya ba sosai, tamasa fatan Alkhairi takuma kara ganin mutuncin Dr Abbah Sosai da karamcin sa gare su..

Yace yawwa saura ke akwai wani katon fili da aka sayar mana zan miki gidan gwona dashi da kudinki sai a zuba abinda ya dace kema kinsamu na taimakon al'umma, kana ya maganar aikin ki kina da ra'ayi koko?

Murmushi tayi tace kai nike saurara.

Yace tom shikenan in dai kinaso kiyi ,in bakyaso muzauna gida muyi soyayya,in kuma nafita ki zauna ki huta,In ina nan kibani daɗi na more.

Ido ta juya tace nazabi zaman gidan,Dan fuskar ka tafi haske Yayin da zaka fadi xabina na biyu.

Sosai kam yaji dadi nan suka koma ruwa baji ha gani waje kashe Arna.

Bayan isha su Malam Habu suka dawo gidan a palon Deedee suka hadu su duka aka shiga firar zumunci, Aymah kau sosai tajejin kunyar Maman Jameel yayin da itakuma ta saki sai ƙoƙarin jawota jiki take.
Ranar dai sunyi farin ciki Sosai , Jameel yace Baba wai kason ashe Aymah duk ita tasamaku kayan daki.

Nan fa sukayo caaa akanta da gdy cikin kunya ta mike tabar dakin yamasu sallama yashigo ta tare shi tana shagwaba da kukan danmi zaice itane,itafa bata so.
Hkr yabata daganan suka haura sama sukayi shirin bacci cikin nishadi suna Rungume da juna.

A takaice wannan family dai zuwa yanzu zukatan kowa cike yake da nishadi basa tare da fargaba komi ,Zumunci tsakanin Jameel da Dr Abbah kau abin ba'ace komai hakama Jannat da Dr Asiya.

Aymah kau sadda ta farga tana da ciki ranar rufe kanta tayi daki tayi kuka tayi Sallah gdy ga Allah, dan bata taba tinaniba,Jameel kau shiru tayi bata fadamai ba duk kau yanda yake fadin Baby su shuru ba dare ba rana ina noma amma har yanzu dif ba wani motsi ko bashi da Lfy ne.

Dariya kawai take tace komi lokacine kuma mijinta lafiyayye ne.

Sadda cikin nata yakai wata hudu ya fara motsi lokacin ne ya dan taso kaɗan mussamman in tana tsaye kafi ganin sa.

Wata laraba suna zaune palon Deedee kamar yanda suka tsara duk bayan isha acan sukecin abinci sai tara kowa ya koma dakin shi bayan anyi firar zumunci.

Deedee kina da fura yau banason abincin nan cewar Jameel yana yamutsa fuska.

Eh Aymah mikomasa.

Tamike kenan kamar yanda yasaba yabita da kallo nan yaga dan tashin da cikinta yayi,Da ido kawai yabita saikuma yayi tinanin Ko tumbine ta dan aje.

Koda suka koma kasa hkr yayi nan ya kwantar da ita akan kujera ya d'aga rigarta tare da dora hannunsa akan cikin nata dayayi tauri sosai ya tasa.
Lumshe ido kawai tayi tana murmushi.

Shikam Jameel saitin hannun nasa yaji dan motsi kadan kaɗan.

Ya Subhanallahi zanso kuga zaburar dayayi amma dai bai gasgataba saida yakai kunnan sa nanfa yaji.
mofsi sosai kamar jira dama Baby yake.

Wani irin cafka yakaima ta cikin wani zallar farin cikin da bata taba ganinsa cikin saba.

Baby dan Allah da gaske dan Allah, karki musaya tinanina akan abinda bashi bane dan Allah ki gasgataman farin cikana,da gsk yanzu nine zanzama Daddy, wallahi Azeem jininane acikin ki Tabbas naji tabbaci.

Cikin mamaki take kallon sa dan bata taba tinanin farin cikin da zayyi yakai hakaba da batama fara ɓoye masaba.

Cikin natsuwa ta mike ta zauna tanamasa kallon tausayi tace kayi hakuri Baby banyi tinanin farin cikin da zakai zai kai haka ba, Wlh da ban boyemaba,nadai bari ne kawai yakara girma yanda zan baka mamaki gashi kuma Alhamdulillah, ka tsinci kanka cikin farin cikin da Nike fatan ganin sa akoda yaushe a fuskar ka.

Wata nawa Baby yace cikin nishadi.

Tana murmushi tace cikin na biyar yake in sha Allah amma zanje dai Asibiti inga.

Fadamaku tattali da kulawar da Aymah ta samu a wannan daran bata lokacine ,dan duk abinda zai mata sannu sannu dai kar ta samu matsala ko ita ko Babyn ta.
Haka sukaita rayuwa cike da so da kauna kaf dangin sa,yanzu dokin haihuwar suke Maman Jameel dinma tagaji da kunya ta saki jiki inka gansu da Aymah kace wasu yan uwa ne shakikai gabaki daya sun rungumi so da kauna sun dora a cikin Aymah .

Deedee mah ba'a batta abayaba dan sosai take kulawa da lamarin Aymah danma cikin baya bata wahala iyakai dai abinci ne bata wasa dashi sai bacci, sai ko ɗaukin mijinta any time.

Malam habu kau angyara shago an zuba kaya yashiga cikin nasara sai fatan Allah kasa mudace.

Sadda cikin Aymah yayi wata tara yayi wani Uban girma zama dakyal tashi da kyal, komi sai an'mata any time Jameel kau na tare da ita ko agida ko a waya, wani lokacin kuma haka zai kama hannuta sudan fita su zazzagaya ta motsa jikin ta.

Wata juma'a da Asuba bayan sun gama Sallah suka koma ,cen Cikin bacci taji wani azabataccen ciwon da tinda ta leko duniya bata taba jin saba,Azabure ta mike tafara safa da marwa tanayi tana yarfe hannu,Wani irin juyi taji cikin ta yayi dakyal ta iya daga kafarta tashiga toilet,Ta bude sit da niyyar ta hau taji Abu ya fashe da kuma dannowa kan yaro lokaci daya.

Gigitaccen ihu ta kwallah daya sanya Jameel dake bacci yankowa da gudu.

Banka kofar yayi cikin azaba ciwo tace yaron mu Baby zai fado.

Azabure ya dagota cak yayo kan gado da ita yana kwantar da ita dan nafitowa baki daya ya tsanyara kuka.

Gigicewa sosai Jameel yayi aguje kuma yayi niyyar fita ta dakatar dashi tana sauke numfashi.

Inda kayan aikinta suka ta gwadamai da sauri ya dakko ta Yanke cibin tayi kwance tana numfashi sama sama.

Sannu ya hau jeramata yanayi yana kallon fuskar kyakyawar Babyn Dake masifar kama da uwarta sak ,gatanan tayi shuru sai hannu data sanya abaki.

Aymah kau Alhamdulillah taketa jerawa kamin ta dago ta kalleshi ta saki Murmushi tace" Baby yazama Dr ya karbi haihuwa mi muka samu.

Ajiyar zuciya ya sauke yace sannu Sweetheart Kinsha wahala,Ashe haka ake haihuwa saura kadan na hade zuciyana wlh, yanzu in'kira DeeDee ta taimaka miki ko, wlh kinyi jarumta da ba kowa zai iyataba?

Kai ta kadamai tana fadin kaida kayi aikin kai zaka ida .
Takarasa tana mikewa da cire rigarta da mahaifa ke ciki, leda dake kusa da ita tasamu ta sanya kana ta cira
kafarta dakyal tayi Toilet,ta hada ruwa tanajin jiri jiri tayi wanka cikin karfin hali, kamin ta duba kanta tana lumshe ido nan taji tabbacin bata samu karuwaba ta daɗa hutawa kamin ta fito akan kujera ta iske shi zaune shida Baby ya Zubamata ido fuskar shi cike da Murmushi yace .

Yace Ummu Aymah wannan wace irin jarimar uwace kika samu,kijifa gida cike da mutane amma babu wanda yaji ihunta Allah yasa kiyo halin Maman ki ya manna mata kiss agoshi soyayyar ta na ratsa lungu da sako.

Dan murmushi Aymah tayi tana zama gefen shi ta karbi Baby ta zubamata ido cike da so da kauna,Tace Baby ngd abisa karar da kaman ALLAH yasamata Albarka.
Ameen yace yana karamata sannu.

Tace ,pant da pad zaka hadaman.

Dakkowa yayi ya shiryamata komi ya bata yace wazai Ma Ummu nah wanka?

Tace ba yanzubu tukunna dai.
Kayan shafa Baby ta gwadamai ya daukomata tagoge mata jikinta tass kamin ta samata fararan kaya ta fesheta da turare ta dorata akafada.

Wani baccin wahala yayi gaba da ita shikuma ya sauke Baby ya azamata ita gefenta kana ya shiga yaye zanan gadon ya kai toilet ya wanke tass kamin ya fito ya goge gadon duk da ba ta batashi ba, dan babu jini ko digo haihuwar Aymah sai uban ruwa .

Bayan yagama ya fesa turaruka ya canzamasu zanan gado kamin ya dauke su ɗaya bayan daya yakai gefe ya zauna yana zuba Murmushi dayima Allah gdy daya basu wannan kyauta.
A fili yace zan barku ku huta sai anjima kowa ya ganku,nan yakoma gefen Baby ya kwanta Shima bacci yayi gaba dashi.

Wajen karfe 12:30 Aymah ta tashi tajita garau sai uban yunwa datakeji,wanka tayi lafiyayye da ruwa mai zafi abinka ga likita tason komi,bayan ta gama ta zuba daurin kallabi ta feshe jikinta da turare.

Babyn ta dauka ta zauna ta shayar da ita sosai tanayi tana lumshe ido saboda zafi.

Bayan ta gama ta sake gyara jikinta sosai lokacin da shima ya fito wanka suka shirya tsab yana kallonta da Murmushi yace mai haihuwar mamaki komi naki daban yake Jarumata ina sonki.

Murmushi tayi tace Ngd mijin Aymah,Baban Aymah.

Fada ki sake Matar Jameel yakarasa yana masu photo masu zafi kana ya kamo hannuta suka Sakko gwanin sha'awa yana rike da Baby a kafada.

Kai tsaye kofar suka bude suka fito sukayi part din Deedee ganin takalma cike ya basu mamaki amma sunson Deedee mai jama'a ce..

Aymah ta fara shiga fuskarta cike da annuri yana biye da ita.

Palon cike yake da mutane gaba daya attention dinsu ya dawo kansu.

Deedee data fito da tire din dake cike da lemuka ta bisu da kallo sama da kasa ,lokaci ɗaya ta saki tiran tana dafe kirji da fadin la'haula wala kuwaata, Habu,! Baraka! kuzo kuga danku yabi zamani wallahii yaje shida matar anyo masu kyankyasar yaro Ashe asabe batai karyaba datace yanzu kwai ake kyankayashewa na yara amma Jameel ka cuceni yanzu dan jikan nawa dama dan na'uwarane mai kwakwalwa saida Batter ma kila zai dingayi takarasa tana kecewa da kuka..

MATAR OGA NA
PAGE 36

Duka mutanan dake dakin saida suka ɗauki dariya.

Aymah kau batabi takansuba ta karasa wajen Deedee ta durkusa tana kama hannunta tace haba Deedee nah kallifa ga baki kinyi kina kuka,kema kinson ko jiya da daddare muna tare dake kuma da ciki a jikina,haihuwa Allah ne yakawoman ita da sauki cikin mnt na kalilan ,To kuma kinga ba laifi nason wani abun zan iya taimakama kaina matsayina na ma'aikaciyar jinya,Dan haka nida Baby muka karbi haihuwar nan shizakima gdy ga diyar ki nan a'hannu ki karɓa kisamata Albarka
.

Baki sake Deedee ke kallon su shikam Jameel hankalinsa nakan Baby sai wasa yake mata kamar zararre ko kallon Deedee da mutanan palon Baiba.

Amamatu Baba Bakigane wayan nan ba?.

Baba Ali dake gefe ya fada.

Da sauri ta kalli inda yake karaf idon ta ya sauka ga fuskar mutanan da bazata taba mantawa ba,Mutanan data fitar da ran sake sasu ido,mutanan da takejin nawie tunkurarsu da sunan Ita din yar suce saboda biyema Namiji da tayi, jikinta har rawa yake tace gwaggo, Aunty Aysha, Aunty Hadiza,,dama zan ganku.

Dukkansu kuka suke suna fadin kaico da cin amanar marigayi da mukai amma ba laifinmu bane mijinki ne sila kuma kinson zuciyar kawunku shiya hana kowa kussantar ki,Amma yanzu muna neman yafiyarki Ummu Aymah, saboda munson bamu kyautaba,baikamata mubiye halin namiji mu wofintar dake ba matsayin ki na jinin mu hannuka baya ruɓewa ka yanke ka yar,,muna rokon gafarar ki,munzo katsina nemanki yafi a kilga Amma munkasa gane gidan .
Wannan bawan Allah mijine nagari na kwarai babu abinda zamuce dashi sai gdya, Allah ya sakama mijin ki da Alkhairi shine yaje wajen mu ya nausar damu kuskuran da akayi da matsala data faru dake da Tsohon mijinki, har zuwa yanzu da yake matsayin miji gareki.

Aymah kau Jameel ta zubama ido lokaci daya ta fada jikinshi tana sakin kuka, Jameel ya gama mata komi,ya dai-daita farin cikinta ya kuma je har kasar su ya hadata da family nata,tana yawon tinanin su amma kuma tason bata da damar tunkarar su Saboda abinda ya faru,Amma dayake mijine na gari shi maisonta da tausayin ace da nashi kawai take rayuwa gashi yaje yasha wahala ya nemi nata dan dai ya hadamata gurbin farin cikinta gaba daya .

Deedee kau da sauri ta ɗauke ɗiyar dake kafardashi tana fadin nidai ban yardaba muga halittar ki in cikakkace bada battery kike amfani ba ta karasa tana zama zuciyarta fall da kaunar Baby ta cire mata kaya har pampas ta duba ko ina ta sauke ajiyar zuciya tace Alhamdulillah,ga gabantanan damdam masha Allah ba ma'adanin battery,Fatartama cuss bata ɗiyar Robaba Allah nagodema da yanzu saidai in hada kayana inyi kauye ko cikin network ɗin ne da bala'i in zauna nida Malam.

Dariya sosai yan palon suka dingayi .
Baba Ali yace duk inda kike muna biye Hajiya Deedee.

Jameel kau bayan Aymah kawai yake shafawa yana zubamata kalamai masu dadi,tsawon lokaci suna a haka kamin ta koma cikin danginta suka shiga firar yaushe gamo tana ta masu tambayoyi akan danginta .
Wasu ace suna nan wasu ace sun rassu.

Jameel kuma da Deedee sukayi sashen Su Malam Habu da Baby cike da nishaɗi a zukatan kowa.

Ba karamin mamaki suka shaba daganan aka hau bugama yan uwa da abokan arziki DeeDee kam aka fiddo katuwar tukunya aka shiga dafa ruwan zafi akashiga store aka kwaso gero aka kai unguwarsu gidan Asabe dan a masu dakan kunu.

Kiching ta koma ta hadoma aymah lafiyayyan abinci mai rai da lfy ta zauna ta tsareta tana washe baki tace wallahi AYMAH ta tafi ta kowa jarumar mace,zamanki likita baizama aikin banzaba,amma wasu katton banza likitocin kiga suna dukan mace in zata haihu sukau in zasu haihu sai an'sama munafukan kafafuwan su mari saboda ihu da kai ma bayin Allah Naushi..

Dangin Aymah kau dasukazo su biyar dariya sosai suke daganan suka kira sauran dangi suka sanar dasu haihuwar ta nan fa kowa yafara shirin zuwa Katsina.

Aymah kuma ta dauki waya ta kira Aminan arzikinta kan kace mi gida da yamma yacika sosai kawayen Deedee gasunan zube sai basu labarin jarumta Aymah take..

Zaman jego mai kyau da tsafta akai Anci an sha danginta sun taka rawar gani sosai dan hidima babu kamaf hannun yaro yinta suke.
Saura kwana biyu suna
Danginta kaf suka zo.
Sabuwar Rayuwa mai cike da walwala da farin ciki sukayi a wannan rana an tina da anyi kuka anyi Dariya..Ranar suna kau katon holl suka kama akaci akasha akayi photo tarihi kana aka watse da kyautatuka masu yawa dagani kason haihuwar an'mata tanajin nera .

Bayan wata biyu da haihuwar ta aka daura auran manager da Hajiya Asiya, bikin da Aymah da Jameel suka taka rawar gani kamar ba gobe.
Ana gama bikin kuma suka shirya zuwa kaduna wajen madina dan bikin yaranta ya tashi,sun kaimasu shatara ta arziki taimasu tarba mai kyau ta mulmuje har ta sake sabon aure ita kanga,ankai yara gidajensu masha Allah.

Suna dawowa taje ganin gida nan fa taga so da kauna ta zahiri duk abinda akai ada ya wuce yanzu kowa ya mallaki hankalinsa, satin su biyu suka dawo da tsaraba tagani ta fada.

Jameel kau shekarasu biyu da aure Allah ya karomasu budi sosai inda ya fitar da kujera ukku ta hajji.
Baba
Maman shi.
Deedee.

Sadam kuma da Abokin sa Bash kudi masu soka ya basu da kyautar filaye nan fa suka hau gdya kowa yaje ya kama sana'a.

Zanso kuga badakala da akai kamin Deedee tayi bacci ranar da aka sanar da tashin jirgin su tin dakinta tafara safa da marwa,abun ba acewa komi sai son barka.

Shekara na zagayo Shida Aymah suka cala suka bar ummu a wajen su Baban su.

Bayan sun dawo Baba Ali da Kb suka je Umara saboda yanayin jikin tsufa na Baba Ali bazai iya Hajji ba.

Bayan shekara biyu.

Ummu ce yar shekara Hudu mai masifar wayo kyau ko ba'a magana,Zaune take hannuta rike da chocolate tana tsotsa kafarta daya akan daya tana waya da Abul khairi sai cuno baki take tana fadin yaki zuwa ya dauketa sutafi gidan su.

Kuka tasa ta kashe wayar tana tillata gefe.

Jameel dake gefe yana tajema Aymah kai yace yadai Jarumata keda Yah Abul ɗin ko,miyamiki?

Cikin kuka tace wai nace yazo yazo yakiya wai sai ya gama jarabawa Daddy wlh auran shi zanyi kullum in ganshi kamar yanda kake ganin Mamy itama.

Gabaki dayan su ido suka zaro kamin su sanya dariya ya zaro waya ya kira Dr Abban bayan ya dauka yace Aminina yaufa diyar ka ta ballo ruwa wai a aura mata Abul khairi ta dinga ganinsa kullum.

Sosai yake dariya yace Ummu kinajina,?.

Cikin kuka tace inajin ka Daddy

Yawwa Ummu Abulkhairi shi kikeso ki aura?

Cikin farin ciki tace eh mana kaga kullum muna tare kamar Daddy da mamy tinda in anyi aure ana tare Kullum ko?.

To shikenan Baby nah in sha Allah baki da wanda yafi yayanki kinji, zaki dage kiyi krt sosai sai kiyi saurin girma sai Abul khairi ya aureki ko?

Ihun murna sosai taitayi aguje ta fita tana fadin Deedee aure zanyi.

Deedee dake damama Baba Ali fura ta dago kai tace kai jama'a Ummu wannan wane irin kirane zaki tsorataman miji jibi saura kadan ya fado daga kan kujera

Baki ta turo tace to ba aure zanba nace in fadamaki nama fasa fadamiki natafi wajen Inna.
aguje kuma ta juya tayi part dim kakarta nan suka shiga wasa da Kabeer daya dawo school.

Jameel kau yanaganin fitar ta sukai sallama ya ce Sweetheart kindaiji abinda yarki ke cewa ko,to wlh maza maza muje noma ko masamu rabo mai amfani,Kindaiga ita aure zatai karta barmu empty.

Murmushi tayi tace'' Baby ai saidai ka inganta lfy Babyn ka, waikai yaushe zaka dinga gane cikina ne yanzu ciki wata hudu amma ka kasa ganewa.

Aiko taga tsagwaran so da kauna akan wannan cikin nan suka haura sama sukasha soyayya kamin suyi wanka su sakko suka shiga gari.

Bayan wata biyar ta haifo yaranta yan biyu duka maza masu kama da Ummu amma basukai hasken fatarta ba na Daddy su suka ɗakko.

Sunan mahaifin AYMAH da Baban Jameel akasa amma ana cema su.

Areef da Arfaat.

Rayuwa sauyi sauyi, tafiya tayi tafiya inda Jameel ya gina masu katon gidan dayafi wanda suke ciki suka koma aka cigaba da rayuwa mai dadi sai fatan tsawon rai da samun zuria masu Albarka.

Baban Jameel kau kasuwan ci sai son barka dan yanzu yaboɗe reshi reshi na business Babu inda basuyi sunaba saboda ragowar farashi dasukafi yan kasuwa.

Tammat bi hamdulillah..

ina mika gdya ta ga Allah daya bani damar kammala shi lfy, kuskuran dake ciki Allah ya gafartamana.
Ina mika sakon gdya ga masoyan book dinnan Allah yabar zumunci.

Bazan manta dakuba Yan paid group ina sonku so mai tsanani fatan zumunci mai ɗorewa abadan Ya Allah..

Mrs Chief
Fatima kanam
Aysha adam
Maman areef
Aunty
Mrs Bash
Mame Ibrahim Nijer
Mamagee
Aisha
A Hdz Dutsamma
Maryam bako
Mommy mokhdoom
Mon asas
Ummu ilham
Ruky amarya
Kai da dai dukkan sauran mabiya da bazan iya lissafo yawonkuba ina gdya Allah yabar zumunci.

Ban manta dakeba Deedee❤️🤍❤️ takwara Hajiya Deedee mai kunun aya Allah yabar zumunci .

In sha Allah bayan sallah akwai free book na wayanda suka saba sayen book dina kawai mai suna MATAN HAMXA

Banaso daya daga cikin ku yayi missing dan an hada cakwakiya mai zafi sai in Allah ya nuna mana Ayi sallah lfy🥰

I miss You so much Wlh 🥺

Kadan daga cikin matan hamza.

.
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment