Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tamkar nawa ngd sosai Allah yabamu Sa'a rayuwa da mutuwa.

Nan yashiga duba kayan yaga kananun kaya ne masu shegen kyau da tsada na yan gayu , sai jallabiya guda biyu da vest da gajeran wanduna masu yawa a takaice lefe ya hadama Jameel.

Gdy yamas asosai kana ya fada Toilet ya sake zabga sabon wanka ya fito ya shirya zanso kuga mahaukacin kyan da yayi ga sajen nan nashi dake kara kawata kyakyawar fuskar sa.

Da hannu Dr Abba ya nunamai wata kujera yace hau kayi bacci in ta tashi zanma magana.

Ido ya zaro yace bacci kuma? Ina jinyar matar nawa?.

Yeah bacci naga bakayiba som kar kaima na kwantar dakai oya maza yakara yana ɗaure fuska..

Murmushi yayi dan Baya da ta cewa hakan yasa shi cire rigar ya hau kujera dan danan kau bacci ya kama shi.

Acen daki kau yaran ne suka natsu akan wani karamin gado suka hau game da wayar Abul khairi.

Jannat ma wayar ta hau latsawa suna zaune sukaji an'turo kofar ana faɗin" Aymah nah i milisu ( miss u) yau som banyi bacci ba ,wai dan uban sheɗan saida yaga asuba tayi dan dai yaja Allah yakamani ya lallaɓo ya dingaman kalamai masu sanyi sai gashi najini Bangaladash sai tara na tashi shegen yayi nasara ayau amma In sha Allah bazai sake ciba har abada, Sannu .

Murmushi Jannat tayi tace" Deedee ina kwana?.

Laaa wacece ke mutum ko jinnu? a ina kika sanni baiwar Allah Deedee tace hankali tashe idon ta kamar zai faɗo akan Jannat.

Murmushi Jannat ɗin tayi tace" Dr na bani labarin ki sosai muna nishaɗi,shiyasa kina magana na gane kece.

Washe baki Deedee tayi tace laa wai ke matar Dr Abba ce , Allah sarki,nan idonta ya kai kan yaran tace kwaraiko ga macen nan Tuleliya kam tayi kama dashi,yoke maimakon kibar Namijin ya biyo ubansa saike kika gadosa.

Dariya yaran suka hau yi aguje kuma suka yo kanta suna faɗin yau munriga Daddy ganin Deedee shi.

Haɗa su tayi tace wannn haka yake Yar lukutar dadi nidai kam ga miji na nan ke kam kishi yace tafada tana ba Abulkhairi hannu suka kashe.

Kuka khairi zatasa Deedee ta jawota tana murmushi tace ke wasa nike duk kan ku I lobilu wallahi ..

Gabaki daya suka sanya dariya kana ta juyo wajen Aymah nan taga ta tashi ta bude ido sai murmushi take.

Da sassarfa ta ƙarasa wajen ta tace sannu Aymah na sannu,jiya kinbi layin tinkiyoyin likita kinsh wuka, Allah yabaki lfy sannu kinji.

Yawwa Deedee nah nayi kewar ki,ina zoɓo ina kunun aya?

Haba Aymah nayi su yanzu ai nacika yal'bura uba,bari nayi inga lafiyan ki kana,kajin kwai ma zan saya asaka ɗakin Adnan.

Murmushi tayi tace Allah ya samiki Albarka.

Ameen ta amsa kamin ta juya ga Jannat daketa murmushi ta bata hannu tace sannu Mrs Abbah.

Cikin kulawa Sosai Jannat din ta bata nata tace sannu Mrs Jameel kuna lfy ya karfin jiki Allah yasa an'maki a Sa'a.

Alhamdulillah Ameen ya rabbi sannu ku ta fad tana kirawo su Abul khairi nan suka gaidata cikin ladabi.
Cikw da aon yran da kaunr su ta hau amsawa tana dan tamhayar su abinda ya shfi karatun su sun bata amsa.

Deedee tace kai ammafa naji dadi wallahi jikin yayi kyau Aymah,jiya kau yanda kikason zaa maidaki yar mafiya haka aka dora maki karafuna a kirji da kai kai munga masifa Allah ya kara lfy

Ameen Deedee nah kowane bawa da nashi kaddara.

Eh ina fatan wannan yazama nah shine silar farin cikin kin Rayuwar ki har abada.

In sha Allah tace tare da waigawa ganin bataga Jameel bah.

Duk da kallo suka bita Deedee tace .
wai Aymah ina Jameel na dauka bayan gida ya zagaya amma har yanzu shuru ko haihuwa zaiyi ai sai haka?

Yafita shida Dr Jannat ta basu amsa tana bude kulolin ta shiga zuzzuba masu abinci , Yayin da ta hadama Aymah mai ruwa ruwa ta bata tanaci suna fira saida taga ta koshi kamin ta zauna taci .
Suna haka Aka turo kofar Jameel ya shigo.
Sanye yake cikin kananun kayanshi sai baza kamshi yake kana ganin fuskar shi kason bacci yayi.

Ido suka hada da Aymah ta kawar da kanta tana turo baki alamar tayi fushi.

Kanshi ya shafa yana fadin kiyi hakuri sweetheart laifin Dr ne shine yasani kwanciya.

Murmushi tayi tace"Au nakau godemasa cikon tekun maliya tinda har yasa ka huta Allah yabiyaka da Aljannah ka cancanta wallahi.

Ameen yace yana karasa wajen ta ya zauna gefe gadon tare da dan shashafa fuskar ta ya gyara zanan jikin nata A'hankali yace" zamu kara wankan yanzu ko sai Anjima?.


Laaa haula wala kuwati illah billa,yanzu Aymah dama lfyn ki klau har wanka kukayi tare amma kika naɗe kafa kika koma gurguwar ƙarfi da yaji kai jama'a ni Deedee shekaru na sun tashi a iska dana kasa tantance wayon ku.

Jannat ce dake dariya harda hawaye tace kai Deedee kefa kin ganema idon ki Daddy yabani labarin har suma kikai kika kasa magana , shine zakice karyane,kinson ba wanka zatayi ba so akwai bukatar ana kula da jikin nata dan taji daɗi ko kuwa?

Oho yanzu naji zance kinson su sun'waye yanzu bama tani suke ba tace afusace.

Deedee wallahi zaki fita waje kina ma matana ihu Jameel yace yana zubamata harara.

Uwaka Jameel tashi bar dakin na raba auran ku ni zanyi abinda kakeyi...

MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
PAGE 26

Dariya sosai yasa yace. "Wannan kuma baki da hurumin sa.
Atakaice haka suka zauna cikin nishaɗi da farin ciki mamaye a zukatan su.

Bayan azahar Manager yazo shida Baba Ali suka ganta da jiki suka aje masu kayan dubiya kana suka tafi..

Adnan

Wani mugun azaba sadam ke gana mai wacce tin yana da kudirin daukar fansa har ya fara sanyi yana so kawai ya samu mai taimakon sa ya dauke shi daga gidan tin kamin sadam ya kashe shi.
Fitsari kam kullum sai ya bashi so daya arana ya taushe shi dole yasha.

Wannan hali da yake ciki yasa Adnan din fara son kuntatama sadam din ta hanyar kwantar da hankali ya tiƙa uban kashi dan yaba su Sadam din aiki.

Shikam Sadam ganin haka yasa yace to ai hikenan tinda ni zakaba aiki kwara ahutar da kowa zaka rayu in da ya dace dakai..

Katon buhu suka samo suka dora Adnan din akai suka dinga jan shi har zuwa toilet din dake cikin get ɗin.
Akan shadda dake wajen suka ɗorashi babu ko wando yace to kaitayi in ka gaji ka sake wani dan buhun ubanka munafuki mu bamu fika Hatsabiban ciba.

Yasha kuka ya gaji gashi ko gusawa baya iya yi, ga masifar sauro da kwarin Toilet dake dallamai cizo tinda babu Kulawa,Sosai yashiga nadama abinda ya shirya gashi ya gina Ramun mugunta abin kuma ya rufta dashi..

Abinci kam a cikin leda suke kawo mai da ruwa guda su jefa su kama gaban su.

Wannan rashin kular ba karamin matsala tajaza mai ba, dan cikin lokaci jikin shi ya fara wani irin wari marar fasali,kafarshi kam da bata da lfy har wani ruwa ruwa take masu masifar Ɗoyi.

Awannan lokacin ne ya fara kuka da hawayen shi akan halin da yake ciki.

Ta ɓangaran Aymah kau Abin sai son barka ,Dr Abbah da matar shi sun shayar dasu mamaki ta hanyar bada dukkan kulawarsu ga Wannan ahli, Jameel ya sake tabbatar da haduwar su da Dr ba karamin Alkhairi bace,Aymah kau in'ka gansu da Jannat zaka yi tinanin dama tare suka tashi dan shakuwa.
Ta bangaran Manager kam abin sai son barka Hidima sosai yakemasu bakin rai bakin fama .

Bayan sati daya
Ya kama kwana takwas kenan da aikin Aymah..

Turo dakin yayi ya isketa zaune tana ƙoƙarin mikewa tsaye alamar ta fara samuwa.

Cike da farin ciki ya buɗe hannu yace oyoyo matana ta kusa dawowa hannun Babyn ta tarama masa wankan da yake mata.

Cike da shagwaɓa data kware da ita yanzu tace.
Nifa gaskiya A'a kai zakaitamun Bazan iyaba wash Baby kirjina zai faɗo ta fada tana dafe wajen da akai aikin.

Da sauri ya kamata yana fadin ki daina tashi ba,kinga gashi an sallamemu Jannat zatana kula dake gida tinda itama Nursing ce,Ga hutu mijinta ya bata saboda ke Har sai kin warke.

Cikin mamaki tace da gaske?

Yeah da gaske nike bara na dakko whell chair na tura yar gurguwata mu wuce ko, gasucen duka gidan ki ke kawai ake jira..

Murmushi tayi tace good dana zama gurguwar taka ba ta kowa ba.
Gida kuma ada ne yake nawa,a yanzu ni Aymah na baka wannan gidan halak malak,Banso kace komi in ba haka ba zamuyi fada bazan sake yarda kanamun wannan abunba ta faɗa tana juya kai cike da kunya...

Dariya sosai yashiga yi kamin ya sake rungumeta yace dan Allah sake faɗa naji, akwai dad'i dama kina so?..

Aa banaso tace murya ƙasa -ƙasa.

Ban yarda ba yace yana huramata iska a kunne tsawon 5mnt kuma ya daina.

Jin yayi shuru yasata dago idonta da sukayi jawur har ruwa ruwa ke kwanciya aciki ta zubamai su alamar yadai..

A kasalance shima ya zuba nashi cikin nata yace.
kikace bakyaso ga idonki nan ya fallasa sirrin zuciyar ki,Allah ya karabaki lfy Aymah, na fara kosawafa sosai wallahi yanzu burina ɗaya naji nayi ajiya a wannan wajen ya fada yana shafa cikin ta.

Cikin kasalalliyar murya datafi tashi yin low tace.
Ka manta bana haihuwa,Shekara 16 da aure fa ko ɓatan wata banba ,kai sai kasanya rai zan haihu a gidan ka?.

Sosai ya dinga sakin murmushi da kalaman ta har saida ta kai aya ya juyo ya fuskanceta tare da rike kafaɗar ta yace.

Matana ba juya bace som,Kema kin son haka,da kuma kikaga kin kai wannan lokacin karki manta wani baya Haihuwar ɗan wani,Sannan dama tin farko Allah ya rubuta zan ba Adnan aron'kine kamin na girma na bunƙasa na iya rikeki na kuma iyautata zaman takewar mu,yanzu kuwa bagashi an maidoman abata ba, Gashi duniya ta sheda zan iya Rikeki a halin yanzu,kuma kema kin sheda hakan,jinyar nan taki itace tazama shamaki a tsakanin mu,amma ni ina da tabbacin In sha Allah duk ranar da Mukai wasan dambe dake aranar zan jefa kwallo a raga in Allah yaso ya yarda ki rubuta ki aje nikaina na yarda da kaina , ko zakiga zahirine?

Da sauri ta ɓoye kanta a kafaɗar shi tana kai masa k'ananun duka akafaɗa tace.
Som yanzu bakaji,ada ba haka kake ba,ada ustaz ne kai,amma ayanzu idonka ya buɗe why?.

Masha Allah da kikason da ni ustaz ne, Ustaz fa dukkan abinda yason halaliyar sane to bazaki samai dajin nawie a wajen nan ba,in kuma abu ya zamto na saɓama Shari'a musuluncine zaki samai mai kaffa kaffa da abin saboda bin umarnin Allah,Karkiyi mamaki dan Yanzu na waye akan wasu abin nawinki fa ya hau kaina kana idona ya sake budewa da kallon Kyakyawar surar ki,ke in'ma baccin abinki Aymah waye zayyi ido huɗu da kyakyawar mace kamar ki bai gane cewa shi lfyayye bane, wallahi tin washe garin zamanki Asibiti na kara tabbatar da lfy nah,kai Alhamdulillah Allah kulli halin ya karasa yana bata wani lafiyayyan kiss a goshi. .

Zatai magana yace ina zuwa ma idata agidan ki, akan gadon mu,kanki a cinyana,hannuna a br....

Bakin shi ta daɗe da sauri dan kar ya ƙarasa.

Shikam dariya yayi ya mike da sauri yafita tare da cewa matsoraciya.

Naji! tace tana gyara zamanta Murmushi kwance a fuskarta,Kai Auran wanda keda rufin Asiri Duniya ne,yanzu ta tabbata da Adnan ne sai dai ta rub'e ta lalace bazai iya bata koda awa daya Acikin a wannin saba, gaskiya da mata zasubi shawarar ta su daina cewa sai mai manya kuɗi,su samu mai rufin asirin da zai basu lokacin su ya basu kulawa,amma wallahi mai dukiya bashi da cikakken lokacin kowa saina dukiyar sa da tinanin mi zai shiga ya fito,miye in yayi zai bada riba ba faduwa ba,kullum tinanin shi yanda zai sake yalwata canjin sa,ciwo in yakama matar shi bazai iya sashi zuwa ganinta ba sai dai ya turo kudi dan yana ganin sune maganin matsala komi ,baison kaga mutum kusa da kaiba ma kawai arzikine Babba,kai taga banbanci dari bisa dari.

Ahankali tace" gashi yaro jagab,kuruciya bai'baye dashi,ga kamala,ga iya soyayya,ga iya sarrafa mace,iya sarrafa halshe yayin furta zance,wow Jameel kayi sosai, Allah kabama wanda suka daura mana auran nan tukuici da gidan Aljannah.

Jameel kau Dr Abbas yaje ya kira ya sake dubata kana ya sallame ta ya fito da ita cike da kulawa da tarairaya mutane sai kallon su suke, yayin da wasu suke tinanin Yan uwan junane, wasu kuma suna tinanin miji da matane duba da irin tarairaya dayake bata.

Bayan sunje gaban mota ya sungumi abinshi ya kwantar da ita A'hankali tare da kwantar mata da sit din kana yaba wani ma'aikacin jinyar kujera ya mayar masu shikuma ya tada haɗaɗɗar motar suka tafi.

Cike da mamaki tace Baby wannan motar fa?.

Murmushi yayi yanajan kumatunta yace ta aroce..

Shuru kawai tayi tana dan cije baki,zuciyarta cike fall da tausayin sa, wato har yau baima mallaki koda keke na shiba amma yake rayuwarsa cikin farin ciki , Yah Allah kabani ikon bawa bawan nan naka dukkan abinda na mallaka, Allah duk quya duk daɗi karka taba bama zuciyata damar yin gori gareshi a matsayina na ya mace mai rauni, Allah ka cikaman burina Allah ka karaman son sa azuci shima ka karamasa nawa.

Ameen my wife ,in dai Jameel dinki ne karkiyi kokonta akan son da yake miki Aymah, sonki ya fara tasirine a zuciyata tin haduwar farko da mukai dake kina cikin halin jinya,Kai naga abu, a wanna fa ranar duk iya satar bacci kasa daukata yayi,abin har mamaki yake bani yanda na afka sonki baki daya lokaci daya,wallahi Aymah bayan iyayena babu wanda nike so sama dake, Sai dai bansaniba ko zaki iya zama dani a halin danike ciki,kar tafiya tayi nisa Aymah ki juyamun baya,kinson Annabi Allah ma yace kaji tausayin wanda ya saba da dukiya farat daya kuma ya tsinci kanshi cikin hali na rashi,Inaso Allah ya samaki hkr zama dani a cikin ko wane hali,kedai kin sani karama sana'a nike Aymah ba Babba ba..

Lips dinta ta dan cije tace .
Jameel!!!
Koda babu
Kafa,
Hannu
hanci
Kunne
Baki .
yatsu
A tattarr dakai nayima Alkawari tsakanina da Allah zan zauna dakai na tarairayeka kuma wnanan halin bazai iya sani in juyama baya ba.
Bana daya daga cikin matan dake gudun mazajen su dan wani abu balle kai daka zameman garkuwa kaida iyayenka,wani abun tabbas Adnan na samun sassaucin sane daga gareni sabida kai,bakai ka daɗe da sona ba nima na daɗe danaka wanda ya samo asaline tin ranar farko danaga juyawarka jameel.
bayan ka kadai fa nagani amma nakasa sukuni,wallahi ina sonka da dukkan zuciya na da ruhi.
I love you so much Ɗan Saurayina tace cikin shauki tana jan gemen sa.

Murmushi yayi yana sakarmata kiss a laɓɓa yace me too My Aymah nah

Tasha mamaki sosai lokacin da suka isa kofar gidan ta suka iske an gyareshi yasha sabon penti,bata ida mutuwar zaune ba saida aka bude masu get suka shiga falfajiyar gidan ya rasulu ya manzon Allah,kai Abin bazai faɗu ba .
Aget din su na biyu sukai parking tana ta bin gidan da kallo.

Bayan ya buɗe ya fito ya zagayo ya budemata.

Wata irin guda Haj Deedee ta saki kamar zata cire hancinta.

Gabaki dayan su kallon ta sukai sosai lokacin data zube cikin uwar ranar ta hau sujjadah shukur dan sosai tayi kewar Aymah .

Deedee nah Dan Allah kita shi karki ji zafi akwai rana nayi kewarki nima Aymah tace cike da son Dattijuwar tana bude mata hannu .

Cikin sassarfa kau Deedee ta tashi tare da sharre hawaye tayo kansu ta kama hannun su tace .
Alhamdulillah Aymah wallahi dadin danaji bazai misiltuba,dan karkuceman butulu da wallahi sauran kaɗan in kwashe kayana in gudu, yo gidan kango ya komamin saboda babu fitulun dake haskaman shi,Dole tasani fara dire kujera a tsakiyar su sadam da Baba Ali ana zantawa dani.

Dariya Aymah tayi tace ai yanzu na dawo in sha Allah babu abinda zai rabamu sai mutuwa.

Noo Baby nine nan zan rabaku,yanzu kam ai dole ta barni dake ba, tinda tason wata kusan tafi wata wanda akai abaya Allah ya amfana ya karasa yana murguda baki da jefama Deedee wani kallon dayasa su duka fashewa da dariya.

Kunnan shi ta kama sosai ta rike tace kai yanzu har ka kai minzalin da zaka fadaman magana Jamalu? To ka bini sannu dan yanzu nice komi tsab zan manta da uban komi in hanaku tarewa kai kason ni baka bukatar tini.

Murmushi yayi yana dan rungumota yace haba tawan ta gaban goshin amma fa in Baby na Toilet.

Duka ta kaimai tana fadin" Ni zaka mayar shawaraki saima ta shiga toilet kana? to ai shikenan sannu ku da zuwa .

Cikin farin ciki ta nemj yi masu jagora .
yace jeki muna zuwa.

Batace komiba tayi gaba shikuma ya sungumi Aymah bai direta ko ina ba sai bakin kofa ya kamata suka shiga.

Ashe kallo na palo..

Wasu lafiyayyun kujerune da labulaye da carpet komi na ciki gold colours ne palon yayi wani kyau na ban mamaki .

Deedee ta juya tace ya kukaga aikin manager,wallahi manager ubane harda kari bawan Allah dan dai duk yakara son goge lefin sa,duka gidan nan shine ya fitar mai da wannan kudin ya gyarashi,saima kin haura sama Aymah inda dakin ki yake nan zakisha kallo.

Wannan abu yama Aymah dadi har kukan farin ciki tayi.

Jameel mah sosai jikin shi yayi sanyi.

Wayar shi ya zaro ya shiga kiran shi.

Bayan ya dauka yace Daddy barka da kwana.

Cikin mugun farin ciki manager yace Jameel,kaine,yau da kanka kake kirana Daddy?.

Sosai kunya ta kama Jameel dan da haushi yake bashi wanda ya rasa dalili.
*nikam nace kishine kawai ya ke dawainiya da zuciyar ka*.

Kayi Hkr Daddy mun..

Karkace komi Jameel bari ganinan zuwa yau ai ance dama za'a sallameku amma banyi tinanin da ranaba anjima da la'asar ko bayan magariba in kun huta zan shigo in sha Allah.

Tom daddy mungode.

Aha bye my son ya fada yana kashe wayar muryar shi cike da farin ciki.

Sosai Aymah taji Jameel din ya burgeta mussamman dataga ya sakko.

Deedee kam abinci ta shiga saukewa gaban su tana ta rawar kafa diyarta ta dawo.

Jameel yace ina zuwa Deedee bari muyi wanka.

To sai kun sakko tace tana sake gyara zama tana kallo.

Aymah ya ɗauka cak
suka haura sama sai rigima take mai akan ya sauke ta.

Lallai kallo na sama na maganar Deedee.
Tsayawa tsara kyan palon nan bata lokacine.
Dakin Aymah yashiga inda yasha hadaddan kayan daki komi milk da maroum kamar yanda kujerun palon suka kasance maroum da milk..
Bayan ya zaunar da ita akan gadon yace yaufa tare zamuyi yafada yana fara kwaɓe kayan sa duka.

Ido ta zaro tare da neman kwallah ihu ya haye gadon tare da jawota jikin shi ya rufemata baki...

😳😳😳😳

MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
PAGE 27

Miye haka Aymah? dubafa kiga ina da wando ya fada yana tsareta da ido.

Gaskiya A'a nidai ka mayar da kayanka duka dan Allah banaso wannan ai karami ne.

To kinfiso na jikesu da minene zan koma gida? Ba wanka zan miki ba?.

Aa Nidai Ka hadaman ruwan zan iya da kaina.

Ohoo da gaske zaki iya?

Eh zanyi tace tana turo baki.

Hmm zan kamaki yace yana shigewa Toilet din..
Saida yayi wanka ya ɗauro alwallah kanan ya hadamata ruwan ya fito.
Kayanshi ya mayar sannan yace zaki iya tashi ?

Eh zanyi tace tana mikewa tare da ɗaukar babban towel dinta tayi Toilet din.

Cikin natsuwa tayi wankanta ta dauro Alwallah ta fito.

Akan gadon ta iske ya ajemata kayan ta na shan iska masu fadi .
Sallah ya kabbara yayin da ta zura rigar tayi zaune a kan kujerar dake wajen tayi sallarta daga zaune ,
Bayan sun gama ta fara hamma alamar bacci.

Kallon ta Yayi yace Sweety nah Bacci?.

Kai ta d'agamai a gajiye.

Yace zaki fara cin abinci kana ko?

Aa saina tashi ka manta ban dade da shan tea bah.

Ohk tom muje ki kwanta ya faɗa yana kamata suka koma akan gadon.

Wutar dakin ya kashe dakin yayi duhu kamin ya hau gadon yace ki bar ciwon nan ya sha iska tinda akwai nepa ya faɗa yana zame mata rigar kasa.

Bacci ke idonta sosai kasa hanashi tayi .
Shikam yana cirewa yashiga jagula jikinta tsawon lokaci kamin ya samu natsuwa ya tashi yayi wanka kana ya gyaramata kwanciyar ta ya fita dan zuwa gidan su.

A palo ya iske Deedee na zuba gyangyadi.

Fuska ya ɗaure gam kamar bashiba yace" zan tafi gida.

A furgice ta tashi tace kai kuwa kafaracin abincin mana ina Aymah take.

Bacci tayi yace yana zama tare da bude kulolin yaga waina ce da miya sai dagen naman kaji.
Ya kauji daɗin ganin wainar dan tana daya daga abincin da yake mutuwar so A rayuwar sa.

Bayan yaci yasha ya ce kin'daina kayan saidawarki ne?.

Tace mizai hana ni,Ai Aymah Na dawowa hankalin ta na fara nagaji dama da zaman banza, yanzu haka nason yan Albarka suna kan hanya ga naku nan an maku na mussamman ta ɗauki jug ta shiga tsiyayamasa..

Saida ya take cikinsa dam kana ya mata sallama ya fito.

D'akin Baba Ali ya biya suka shiga gaisawa kamar sun dade da sanin juna kamin ya samai albarka ya fito nan yaji ihun su sadam sunata chapter.

Kamar ya buɗe yafita yakuma fasa ya tura dakin da sallama ya shiga.

Hannu ya basu suka shiga gaisawa kamin ya sanya kai bedroom ɗin.

Yallabai Adnan kake nema ?sadam yace.

Eh .

Ai yana Toilet cen muka mayar dashi kashi yake muna a wando da gayya ..

Ya salam! akan mi,haba kaikuwa sadam baidaceba wallahi,ku barshi da dakon zunubin dake kansa kaɗai ma ya isheshi kunci,basai kunbi ta kanshi ba mutumin da bashi da hankali,nasiha Sosai yashiga masu batare da ya musu cin mutunci ba.

Gdy sosai suka shiga yimai kamin ya fita yabude get din yafita .

Sukam duk jikin su saida yayi sanyi hakan yasa suka tashi suka Dumfari wajen.

Wani mahaukacin wari mai azabatar da bawa suka dinga juyowa daga dosar wurin.
Gabaki dayan su saida suka dade hanci.

Sadam ne yace kunji mi nikeji ko kashi yake?.

Kai A'a wallahi bana tinanin haka wannan ba warin kashi bane kamar na gawa .

Ido suka zaro kamin Su zunduma da gudu.

Kwance suka ganshi kudaje, kwarikka nabi har cikin idonshi sai nunfashi yake sama sama.
Yanayin abin dai som babu tsari, Duk yanda yake basu haushi saida takai ga sunji tausayin sa.

Kama shi sukai suka fiddo daga toilet din da reza suka samu suka cire rigarshi zuciyan su na masifan tashi ko wane tuƙan amai yake ji.

Wanka sukai mai tare da kaishi wani karamin daki dake kusa dana Baba Ali suka aje suka zo suka dauki riga cikin kayanshi.
Koda suka samai kayan sunmai mugun yawa.

Ngd yace cikin bala'in sanyi dan ko magana sosai baya iyawa tsabar wahala.

Toilet din suka koma suka shiga aikin sa dan ya basu masifar tausayi, ga abincin da suka kawomai nan na kwana biyuma baici ba .

Saida sukasha wahala suka gama gabaki dayan su babu wanda bayyi amai ba.

Jameel kau cikin nishadi yake tafiya har ya iso kofar gidan su.

Bayan ya rufe motar ya fito yashiga ciki.

Inna su ya iske zaune da Baban su sunacin shinkafa da wake a flat daya sunayi suna labari.
Dukkan su sunji daɗin ganin shi nan suka shiga tambayar jikin Aymah yana amsama su .

Key din motar ya zaro cike da murmushi a fuskar sa yace.
Baba kusamun albarka, na fadamaku kwana ukku daya wuce dama aka fara mana aiki,to shine yau da safe Dr Abbah ya kawoman wannan motar wai da kudin ya sai man dan in rage Kudin abin hawa,in yaso yanzu sai a hadamasa nashi.

Sosai suka shiga murna Inna su harda hawaye daga baya suka masa fatan Alkhairi.

Malam habu yace to yanzu ina zaka ajeta?

Toh nidai na fara tinanin ajeta gidan su Kamal tinda basa Nan,Amma ina so na nemi alfarma mai gadin ne sai yasanar da mi gidan yanda sukayi shikenn dan ba yanzu zan hautaba sai gaba.

To to shikenan Allah ya sanya Albarka ya tsare ku,Ai mu haduwar mu da bayan Allah nan wallahi Alkhairi ne,Yanzu bama da haufi akan komi,Jibi mahaifiyar ka har tayi kiba ta sake kyau abinta,Bata jiran sisi nawa in nabata ta amsa,in banbata ba kuma tayi amfani da nata,Rashin tinani ne kesa wasu mazan hana matan su kasuwanci amma wallahi ba karamin ragema mutum hidima suke ba,Fatana ka rike Aymah da amana,shine kawai abinda zakamana ka biyamu,kaga ko lokacin da muna kalkashinta bata taba wulakantamu ba,, kullum kyautatawa ce tsakani mu,Ba ƙaramin Sa'a kayiba Jameel,Fatana da addu'a nah Allah ya kamama, ya kuma kara budama ka hanyoyin

Please Login or Register in order to submit comment