Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Arziki da walwala.

Ameen Baba ngd matuƙa kuma zanbi shawarar ka yace yana mikewa zai shiga daki Inna su tace wai baka tambayi autana ba.

Kanshi ya shafa yace na manta dashi som.

Murmushi tayi tace shikenan jeka tom baza'a faɗi inda yake ba.

Hannayen sa ya hade cike da son jin inda jinin nashin yake yace dan Allah Inna mu yana ina.

Baban su yayi dariya yace kace ka manta dashi,to sunje kauye da Mai unguwa suna hanya. In sha Allah.


Fatan dawowa lfy ya masu kana Yayi dakin shi ya kwanta.
Duk irin gajiya da baccin da yakeji kasawa yayi, juyi kawai yake,ya saba kwanciya kusa da ita,dan ko Asibiti tana yin kwana ukku yaga ta fara dawowa normal ya koma bacci bayanta haka yake jefata jikinshi suyi baccin su cike da Nishaɗi.

Ganin kwanciyar bazatai maiba ya sashi tashi yayi wanka ya masu sallama ya hau motar shi yaci gaba da zaga gari har bayan mangariba kamin ya juya kan motar zuwa gidan su Aymah,awaje ya ajeta kana yashiga da kafa.

Abakin Baranda ya iske Deedee zaune da uban kudi tana ta kilgawa Almajiranta zaune suma gefe sunacin tuwon datayi da miyar kuka tasha Namijin zakara sai kamshin man shanu take.

Bayan ya gaisheta yace" kiraba dani.

Murmushi tayi tace to tinda dakai nayi wahala ba.

Tana ina yace yana kallon kofa.

Tana ciki ni ai nariga na bar dakin nan Jameel tinda naga idonka ya bude Yanzu.

Sosa kai yayi yace amma fa inajin kina fadama innamu ta dainajin kunyarmu nikuma sai kisaman ido akan matana? Kina so a zage a nunama danki soyayya nikuma kizameman shamaki?.

Ido ta gwalo tana fadin yanzu da girmana da Mutuncina kake so kaman sharri, wallahii kaji tsoron Allah a ina na samaka ido,kawai wannan dakin na dawo dan in sakata in wahala ta nuna karamin part din dake kusa dana Aymah.
Tace kai kuma kaga saika zauna anan ka karasa jinyar tata kamin kaje ka samar maku wajen da zaku zauna.

Kanshi ya sosa yace ina sonki Deedee nah kin kawo shawara mai kyau .

Kamar gaske tace tana zuba fara'a.

Mikewa yayi yace babu karya a kalamina yakarasa yana tura kofar ya shiga.

Bata kasan hkn ya sashi haurawa sama

Zaune ya isketa palon sanye da wani gajeran wando milk wanda da kadan yafi pant,sai rigarshi data kasance mai net itama milk,Sai zani dake bayanta da gani ta ajeshi dan in wani yazo ta saura. ,.

Jameel kau da kyal ya iya yin sallama ganin halittun nan nata sunyi curko curko suna nema fasa rigar su fito.

Ido ya dan lumshe yace" Sweetheart wannan jan raine miyasa bazaki sanya manyan kaya ba kinson Any time zan iya faɗowa.


Idonta dake lumshe ta bude tare da zubamai a shagwabe kuma ta juya kai tana turo baki tare da daukar zanan ta dan yafashi akan jikin ta .

Minene? fadaman kar wani yaji kanmu, mu kashe mu binne Abin mu kinji matar so ya karasa gunta yana rike kunne.

Ohk ba kaine ka tafi ka barni ba, bazakamun ko sallama ba kuma sai yanzu ka dawo,nidai tom mu koma Asibiti tinda acen nafi ganin ka .

Kyakyawan Murmushi ya saki yace.
Naji dadin wannan maganar taki Sweetheart,kuma nason nidin na dabanne awajen ki tinda gashi har kewana kike in bana nan,sai dai Karki manta a yanzu jikin ki ya fara kyau, da son samune nan da sati daya ace kina gidana,Kinga dole kimin uzuri in fita in dinga nema mana na abinci kinji.

Zamanta ta dan gyara tana mikewa ta zauna tare da kama hannusa tace.
kamar bakaji maganar da namaba dazu Asibiti,ko bakason kyautar da nama ne,Nace na barma gidan nan halak malak,ko baka yarda dani ba ne,ko akwia abinda kake tsoro,ko kana gudun a kiraka da mijin Hajiya ne?.

Aa Aymah bana tsoron komi sai Allah,kuma kema kinson na yarda dake dari bisa dari tinda har na iya auran ki kuma ina burin mallaka miki kaina abadan, kawai hakanan,inaso nima nason yanda ake sauke nawin iyali wannan shine,kana bana tsoron aceman mijin Hajiya som, Tinda inba aceman ba mijin Alh za'aceman, A ganina daɗin zama ai shikesa ace da mijin iya Baba.

Hannuwa ta ware tana juya ido tace ohk fine in'dai har abinda kaceman hakane tom na yarda kai kuma ka karba. Dan...

Kasa bari yayi ta ida maganar tata ya tausa halshensa mai Sanyin Tomtom cikin bakinta,wani juyi da tsotsa mai rikita kwalwar Bil'adama yashiga Mata babu ko tsaitsayawa tsawon 10mnt kamin ya saketa ya jingina da kujera yana numfashi, yayin da itama ta jingina tana dora kanta saman ka faɗar shi ta lumshe ido.

Cikin sanyin jiki yace mukara Hakuri Sweety ko,kema naga kamar kinzo ending haka ne?

Aa tace tana juya kai.

Tom saka idonki a Nawa ki fadaman.

Kin yarda tayi saima mikewa da tayi tace ina zuwa.

Zai magana wayar shi ta shiga ring ya zaro yaga Manager ne.

Yana dauka yace ku sakko kasa.

Ohk Daddy yace murya kasa tare da mikewa ya gyara zaman wandon shi.
Kai ya dago da sauri idon shi ya fada cikin na Aymah data kasa shiga dakin dan jikinta ya mutu saidai ta jingina da kofa ta zubamai ido gashi ya kamata .

Cikin jin matsanan'ciyar kunya kamata da yayi tana kallon shi tafara neman tafiya kamar ta kife.

Da sassarfa ya bita ya cafko hannunta yace zo miye kike kallo?

Ni nifa bakai nike kalloba banmaga komiba cen gefe nike kallo tace a rude.

To In'fadamaki abinda kike kallo?.

Ido ta gwalo tace aa dan allah ka bari ni kanasani jin kunya wallahi wai yaushe kazama haka.

Hmm tin Ranar da aka mallaka man ke,sannan bazakije ko
soron gidana da wannan kunyar ba Aymah in sha Allah, Saboda zata cuceni,ni Babyn kine mai son lallashi mai bukatar kulawa sosai,Kuma ina da tabbaci zan sami komi daga gareki.

Murmsuhi tayi cike da kunya kai aure Akwai sirri,bata taba tinanin rayuwa da wani namiji ba inba Adnan ba ,gashi ta samu kanan kananta data ba shekara goma a matsayin miji ,shiyasa sai taɓara yake mata son rai, wani abunma yamata sai taji nawie ya kamata.

Jameel kau hijjob din sallah ta ya dakko katuwa ya samata.

Bara na fara wanka tukun sai muyi sallah.

Habarta ya dago yace yanzu har wanka ya kamaki?.

Ya salam saida taji kamar ta tona kasa tashiga wai miyasa yake mata hakane.
A rikice tace nifa banfa ceba ,wankan minene zai kamani ma?

Ok Na fadamaki yace yana tsareta da mayun idon sa dake cike da fitina ta matasan yaran zamani😜

Aa tace da sauri tare da faɗin ina zuwa.

Dariya yayi Yace'' sorry manager ne ke neman mu muje yace yana kama hannunata
Sannu sannu suka sakko idon mutanan dake palon yayi cah a kansu.

Kasa ta danyi da kanta Yayin da shikuma ya sake tamke fuska Gam, Jameel akwia dattako da kamun kai,in:kaga rawar kafarsa jikin matar shi yake.

Bayan sun sakko ya dan kallesu nan yaga su Deedee ne dasu Dr Abbah da Jannat, sai yaran su ,sai manager da wata mata da matasam samark guda ukku yam mata biyu.

Wannan ce matar Adnan din matar dake zaune tace.

Noo matar Jameel dai, a dane take matar Adnan Jameel yabata amsa idon shi kamar ya faɗo tsabar harara.

Tabɗi jan, Yanzu dama kece kika rike min miji munafuka tsawon wata ukku ba zuwa ba aike, sai Aukin karya da gaskiya da kuke shiryaman keda wannan munafukin manager, to ta Allah ba takuba abokan aikin sa sun fadaman duk munafuncin da kuka shirya dan haka yanzu kun shigo hannu shaheed ce su shigo..

Cike da rashin kunya saurayin ya tashi yana shagwaɓa da kara kwale wando kasa kasa yake faɗin wai ina Daddy nah Yake mom, kince da munzo zamu gansa kin tsaya ɓata lokacin ki akan wayan nan talakawan maciya haram.

DeeDee kam cike da masifa take lumshe idanuwan nan nata kafafunta daya akan daya ta daiki furta komi amma kai ba sai ance maka zuciyar ta tafasa take ba.

Kai dai jeka kadawo shalele matar tace.

Yana fita sai gashi da zugar sodoji sun kai mutum goma duka da bindigogi.

Aymah
Manager
Jameel
Deedee
Dr Abba
Jannat
Babu wanda fuskarshi ta bayyana wani tsoro saboda tsaro .

Ina kuka ɓoyeshi.
ɗaya daga cikin su ya fada a fusace yana ƙara bindiga akan Jameel.

Kulll wlh,Karku tabaman Miji Aymah tacw a fusace tana mikewa tsaye rai ɓace.

Kema bamu barkiba dan muna tuhumarki da rashin fadamana gaskiya da kikai saboda mugun nufi.
Kana taya zaki auri miji biyu kina mace,ko ganin wancan ya samu nakasu ne yasa kikai aure kan aure ina shi Adnan din yake.

Deedee ta dauki wayarta ta shiga lallatsawa tanayi tana kanne ido .

Sadam ne,yawwa to ku shigo da mushrikin nan,ohk tom takarasa tana kashe wayar.

Hajiya waya baki umarnin daukar waya kiyi kira bayan kina kalkashin hukuma saboda muna zarginki da zabgamana karya akan abinda kika fadama shuwagabannin mu da farko sann...

Wani wawan mari Deedee ta yankamai jikinta har rawa yake tace.
shekara 63 A duniya ba dan tsinanniyar da yaceman kaziba saikai ,nace saiki? shege da katon kirjinka kamar Allon Ƙirya,to ubankama kaje kace nace uwarsa,kai da hukuma da wanda ya kirkiro hukuma kun tile kun kwashe kan babba bura ubaku..

Sosai su AYMAH suka gilgiza da bala'in Deedee dan basu taba ganin ta cikin wannan yanayin ba ga zagi kamar wacce ta tashi tasha.

Rai ɓace yake sosa kumatin sa kamin ya dauki Bindiga yashiga nunamata tare da fadin shiga gaba.

Deedee kam a zafafe ta kwaceta ta shiga rattaɓamai ga kwalkwalinsa sai huci take,lokaci daya kuma ta cire dan kwalinta ta jefar gefe ta fara wani ihu tana kururuwa da bude hannuwa.😳

MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
Page 28


Zanso kuga yanda hankalin kowa ya tashi a palon nan, Aymah kau kuka ta fara sosai,Jameel kau hankali tashe ya doshi Dede.
Cikin wani irin ɓari da take tare da daka mai tsawa akan karyayi kuskuran zuwa wajen ta, inba hakaba sai ta kashe kowa cikin mnt biyu.

Aguje manager ya jawoshi hankalin shi in yayi dubu a tashe.
Dr Abbah kau tsawa yashiga dakama sodojin nan cikin ɓacin rai Yace'' ga abinda kukajawo muna, kuyi takanku tin kamin tazama ajalin ku dan ba lafiyayya bace kundaiga alama.

Kunson maza da tsoron jinni cikin kurin baki daya daga cikin su Ya fara matsawa yana faɗin.
" ai'dai zamu dawo, Tinda ba haka zata dawwama ba,dole mu binciketa yakarasa yan kama hannun wanda ta kwalama Bindiga aka,.
Zanso kuga yanda kanshi yayi malolo kamar an buɗe fatar an adanamishi lemom tsami ,kusan waje goma duk ya kumbura ya tashi sai kan ya koma kamar bishiyar mangoro.

Yaran Adnan kau bayan Maman su suka lafe Jikinsu duk ɓari yake xukatan su cike da tsoro.
Ita kanta matar Adnan din shuru tayi gabanta sai bugawa yake taga wadda tafita masifa.

Mtssssa aikin banxa tsinannu haihuwar shabiyu saura kwata na rana ,yo har kun'buga dani,Sharrima in yaganni guduwa yake balle kai banxa bazara da wani tsinannan kanka kamar gidauniyar silba, zaka wulakantani ka karyatani a gaban Jikokina, bayan nason na girmi uban uwarka.

Kaiiii Yaran ɗan ta Adda. ta dakama yaran Adnan tsawa.

A gigice suke kallo ta..

Ido ta zaro masu kamar zasu faɗo tace .
Naci uban ku dukkan ku,na daka tsalle na mari uwarku,na shake uwarku tayi aman haramcin da taci,zan zabgama kowannan ku mari dari dari in baku tashi kun dawo nan kasaba,tinda kujerun bana uban ku bane, shaggu kamar yaran turwa da ganin ku babu tarbiyya,kai Dan ubanka har zakazo muna mussulmai ka zazzage wando tsagar mazaunan ka abude da shegen Ƙugi bakikirin kamar bayan tukunyar gidan gandu,to zankoyama darasi kamar yanda na koyama Wancen katon banza uban naku.

Zanso kuga yanda katon nan da akallah ya kai shekara 23 ya fara kuka yana Mama bazan karaba karki dakeni.


Duk yan palon saida dariya taso kufcemasu lallai yaron nan basu samu tarbiyya ba sun sangarce da yawa.

Manager dan Allah ka ceci ran yarana Matar Adnan tace cikin tashin hankali dan itama yanzu ta karaya Ainun.

Babu ruwana Madina tinda ke ai a ganinki Amanarki zanci,bayan munyi magana dake ta fahimta akan in Aymah ta warke zamu baki address kizo gidan nan akwai magana,amma dan ki tozartamu da uwarmu da mukejin dadin zama da ita shine kika kwaso wayan nan sukazo suka mata rashin kunya,to babu abinda zan iya,cen kuda ita...

Cikin tashin hankali ta fara rarrafawa gaban Deedee tace" dan Allah mama kiyi hkr karki tabaman lfy yarana wallahi zan sallame su yanzu,magana ta gaskiya ogan nin mijina basumason xan zonan ba,Wayan nan dai sune nasamu labarin komi a wajen su bayan nama su Alkawari kudi mai tsoka akan in sun kawoni zan basu.

Shewa Deedee ta saki tace .
To maza korasu furgada su, mnt biyar suka kara wallahi saikin sani ubanwa zasuyima barazana da bindiga,nida ubanama ke zama gabana Yana hada boma bomai( KAI HAJIYA DEEDEE 🤭)

A guje kam Madina ta ɗauki wayarta ta sata Speaker tace suje bayason aikin.
Gardama daya yaso kawomata ta faramai masifa da fadin zata tona mai asiri dole yasa ya kashe wayar suna zaune sukaji tada motar su.

Zatai magana kenan aka turo kofar aka shigo su Sadam ne dauke da Adnan da suka sakemai wanka ..

Da sauri madina ta mike tayi
Wajen shi, Yayin da yaran ma sukayo wajen shi da sauri kowa na zaro ido .

Cikin wutar kishi sosai take kallon shi kallon sama da kasa,kallon da babu tausayi balle Rahma,kallo mai cike da kiyayya da nuni da ka munafunceni..

A fusace ta faramagana.

Ba shakka,ai dayake namiji kake,maci amana,Allah na godema, Allah ya kara kassaraka ya kuma kara kwashema albarka,kullum zuciyata ƙaryatawa take akan bazaka iya hadani da kowaba kamar yanda kace, Amma gashi,jibi wacce ka rayu da ita,nikuma inacen ka barni da yara Niga wahallalla,to Wallahi azeem dukiyata kaf sai kabani abina matsiyaci,Ka manta yanda na aureka,kana cikin haki na kunci,biyar baka da ita, Adnan wane gatane ke banmaba,amma sakayya farko shine zakaman kishiya,kishiyar da bantaba ji ko labarintaba daga wajen ka,Kullum nunawa kake nice ta farko ta karshe,hmm namiji kenan..


Idonta ta mayar ga ayimah ta zubamata ido tsawon lokaci kamin cike da dogon nazaro tace kai dakata!!!.

Wannan ba itace kake ceman kayi hayar taba in zaka shiga taro tana rakaka saboda ni banajin turan ci? itace dama matar taka,lallai kacika mugun makaryaci,ina fatan kuma Allah ya ɗai-ɗaita karshen ka mugu azzalumi takarasa cikin kuka sosai.

Kuka sosai yasa yace madina karkiman haka,karki furta mugayen kalmomi akaina,Madina ke kinfi kowa sanin duk wahala da nake sabodake da yaranki,sannan wallahi babu son ta ko daya a zuciyata face ɗaukar Fansa dake cike da ruhina,madina dubi halin da nike ciki.
Maimakon ki kasanceman jagora da zata tsayaman akan a kama wayan nan mugayen Azzaluman a garkame saboda abinda sukaman,kiji yanda suka barni na dawo,jin
Bi ruwan da kafana keyi mai ɗoyi wanda ni kaina damuna suke,amma ko Chemis basu taba kai niba,ko paracitimol basu taba baniba,dan Allah ku kwatar man yancina yace cikin kuka tare da faɗin yaku nan yarana yana bude masu hannu.

A yatsine suka dinga kallon shi lokaci daya kuma suka dan fara matsawa bayan uwarsu suna noke kafada Alamar bazasu ba.

Hankali tashe yake kallon su yana fadin mikenan idona ke fadaman.

Uwakace sanye da dan buje kafara gani Deedee tace tana gilgiza kafa.

Madina kau tace.
Gaskiya yarana bazasuzo wajen ka su kwashi wannan cutar ba,sannan ai akan munafurci kayi auran baka fadaman ba to babu abinda zai sani shigema gaba,batun kuma yara karka sake cewa naka dan Wallahi wallahi bazan iya bari yarona daya ya raɓeka ba da sunan zaman jinya,Kuma takarda dole kabada,sannan gida daman ai nawa ne tinda na mahaifina ne, ko sisi na uwarka ko uban ka babu banza butulu.

Madina ki fahimceni banci amanar kiba wlh, tambayeta kuncin da nasata gatanan,Madina bantaba yarda na Bata koda Cikin tsuntsuwaba saboda banason hada iri da ita , Wallahi so biyu ma na kus...

Lafiyayyan mari Jameel ya dankaramai zuciyarshi cike da bakin cikin jin mugun kalaman da yakema matarsa.

Cikin tafasar zuciya da fitowar kwallah daga idonsa yace .
Jahili kai dama baka isa ka bata ciki ba ko ka hanata, Allah dai ya isa tsakanina da kai Adnan,kana kuntataman zuciya duk sadda ka ai'banta wahala daka ba matata,kana sani kunci,kana kasheman walwala,inajin kamar in sanya wuka in daɓama ita ga zuciya ka mutu uban kowa ya huta, Wallahi wallahi kai asararre ne jahili marar hankali.
Kuma yau yau din nan sai kabar gidan nan tinda babu ko sisin tsoho da tsohuwa.

Karka sake zagina Jamilu kajirayi fansata gareka, bazaima dadiba tinda har ka iya sanya hannu kana dukana Adnan yace cikin bacin rai.

Okh fine mu zuba nidakai shege ka fasa.


Madin kam taɓe baki tayi tace" to in kama koreshi gidan wa zaije,nidai kam nayi iya wahalata dashi bazan iyaba,Saboda na sashi inuwa ya jefani rana.

Afusace Deedee tace to ai ga yaranshi nan masu siffar rakumin gwangwani su dau kai suyi gaba Man.

Ikram ce cikin damuwa tace" mom yanzu fa akace wannan shine baban mu wallahi love bazai iya aurena ba ko waleedah.

Kuka walidah tasa tace'' wallahi Nima Nason yaseer bazai iya haɗa iri da niba ace Daddy mu ke rike da mata biyu,sannan dubar safa duk ya lalace ya zama kazami mom ya daina wanka sai wari yake, dan Allah mutashi mukoma mom banason ganin sa.

Kuka sosai Adnan yasa yana taɓa hannu da fadin" karkumin haka yarana duk abinda nike kutino domin ku nayishi,karku juyaman baya bazan iya jure rashin kuba..

Manager Yace'' taya kuka haɗu Madina.

Hawaye ta share tace Adnan macucine kuma ALLAH ina da kokonto a kansa yanzu.

"Ni dai kam haifaffar garin kaduna ce,acen natashi da iyayena mu ukku ne a wajen su,yayyena biyu maza dukkan su ba anan suke ba suna legos da matayen su kasancewar suke rike damu mahaifina ba shi da karfi sosai.
Nayi Aure na auri wani Attajirin mutum harma na haifi da namiji guda daya a wajen sa,Ban dade da haihuwar ba aka sanar dani rassuwarsa bayan anyi zaman makoki na fita iddah dole tasa nadawo gaban iyayena nida yarona Bashir da aka raba gado akabani nawa da nashi ashema ba mai tsawon rai bane
.Shekarasa biyu yayi kyanda ya koma ga mahaliccin sa.

Tsawon shekara goma 10 ban sake aure ba lokacin kuma zaman gidan ya isheni duk da ina ɗan taba kasuwancin kayan mata na atamfa lace jikkuna da sauran su.

Wata rana ina yawo cikin gari mota na ta lalace a waje mai karanci mutane.

Cikin tsoro dai na fito da in dan dudduba kamar wasa naga mutum biyu sun zagayeni fuskarsu nade da rawani,hannu suka bani akan na basu key din motar da wayoyina da kudadena.

Jikina na rawa na mikamasu key din da wayar .

Cikin tsawa sukace in cire kayana ko su zabgaman wuka.

Kuka na fara ina gamasu da Allah cikin rashin tausayi daya ya yankaman mari tare da sanya wukar hannushi ya keta riga na daka sama har kasa .

Gigitaccen ihu nasa lokacn da naga na bayyana tsirara.

Dariya suka fara ba kakkautawa kamin kuma inji sun tsaya,kaina a kasa na farajin suna bada hkr.

A gigice na dago dan ganin misuke ba hkr haka nan idona yayi gamo da matashin saurayin da ke gwara kansu,kana ganin shi kason shima dan duniyar kanshine dukda na tabbata na girme masa nesa ba kusaba , zabgegiya bindiga naga ya zaro yana fadin zai kashesu.

Hkr suka hau bashi amma Saida ya masu dukan mutuwa kamin ya ansheman komi yabani ya juya zai tafi ba tare da ko kallona yayi ba.

Bawan Allah nace jikina na bari ina kankange jikina.

Kallona yayi sama da kasa kamin yace wani abu.

Dama gdy zanma dan Allah ka taimaka ka ajeni gida karsu dawo su iskeni na fada ina mikamai key din motar


Kamar bazai an'saba kuma ya karba cikin ikon Allah ya dan jajjagula motar ta tashi muka tafi.

Har gaban iyayena ya ajeni yama su bayanin abinda ya faru suka masa gdy Sosai.

Nikam farat daya naji na natsu dashi Saboda inason jarumin Namiji a rayuwata da kaina naimasa tayin kaina bayan nabashi lbr mijina daya rasu da harkokin da nike yaceman zayyi shawara.

A takaice wannan haduwa da mukai da adnan kamar wasa ya zama gaske har yanazoman fira..

Ganin haka yasa Abbah na cemasa ya turo iyayen sa.

Anan yake fadaman shi bashi da iyaye ɗan Nijer ne wanda ke rike dashimane ya koreshi shine yazo kaduna neman aiki Har muka hadu.

Sosai muka tausaya mai babu wanda yayi dogon bincike aka sanya ranar auran mu .
gida hadadde na saya nabashi ba tare da sanin kowaba har iyayena saboda son da nike mai.

Bayan bikin ne nikuma saboda son da nikemai da Tausayi na samar mishi Form din aikin soja.

Ranar yayi farin ciki sosai ya saman albarka tare da rantsuwa da Alkur'ani akan bazai tabaman kishiyaba saboda halaccin da namasa.
Naji dadi sosai kam dan ina son sa banaso ya hadani da wata.

bayan ya cike ni nayi duk hada hadar da zanyi wadda ta zama wajibin da..
Ankai shekara goma da fara aiki sannan ya samu babban mukami yayin da nikuma nike da yara biyar maza ukku mata biyu .
wata rana yake shedaman zaije yayima mai gidan sa daya koreshi Alkhairi ya nunamai yanda duniya tahi dashi.

Naji dadi nama sa fatan nasara .
To bayan ya dawo kuma yake shedaman sun daidaita harma ya bashi wani kwangila aiki da zai kawo mahaukatan kudi amma zasuyi shekaru.

Sosai na bashi goyon baya dan ina son cigaban sa.

Cikin damuwa yake shedaman bayason yin nisa dani na kwana ɗaya balle shekaru.
Sake nunamasa nayi ba komi ko karshen wata ne yazoman .
Haka dai ya dawo katsina da wannan zama yaceman yana aiki da brek ɗinsu .
Nama murna sosai akan shima ya bani Shawara da mizai hana in'bashi dukiyata ya jefata cikin kasuwan ci ya juyaman ta hanyar shigo da motoci daga kwatano zuwa kano,Na amince naji dadi na bashi duk abinda na mallaka,yacigaba da juyawa duk wata in zaizo yana bani kudi mai tsoka hakan yasa na sake sakankancewa da bashi dukkan yarda.

Wata rana yake ceman First love anaso a dinga turani manyan wuri da zamu tafi da iyalan mu dan tattaunawa da manyan mu amma ke bakyajin turanci.

Shuru nayi gabana na bugawa,Raina ya bani ko dai Aure zayyi dan yaga gaba da baya tsufa ya tasoman haikan.

Murmushi yayi yace karki taba tinanin zan hadaki da wata saidai bansaniba ko zaki amince na dauki hayar wata mata duk in haka ya kama muje da ita.

Da sauri na amince ina sauke ajiyar zuciya .

Bayan dawowar shi yan gidan mu sukazo ganina.
Yah Hashim
Da Yah Lawal

Bayan mun gaisa suke sanar dani sun samu labarin ashe gidan da muke ciki ni nasaya to bazasu hanani kyautatama.mijinaba amma dai yazama dole in basu dukkan dukiyar da nike da ita.

Nan fa rigima ta kaule tsakanin dasu aganina dan su kuntatama mijina ne suka ɓullo tanan.
Wannan rikici dai har Adnan yaji inda ya basu hkr da cewa su bashi wata daya ya ida sayar da kayan da aka Sawo zai kawomasu da kanshi.

Nan suka tafi rai ɓace ko sallama nikam ban masu ba.
Washe gari Adnan yaman sallama alan zaije ya hado koda kudin nane ya basu dan mu.zauna lfy.

Kwana ukku da maganar nan aka sanar dani kamawar da gidan mu yyi da wuta cikin dare wacce ba ason miya assasataba,Gabaki daya iyayena da Yayyena da sukazo tacinyesu.

Fadara tashin Hankali bazai faduba.
Amma Adnan ya taka rawar gani Sosai wajen dawo da walwalata fan kiri kiri hawan jini ya nemi kayar dani Allah ya tadani har naji sauki kamin ya dawo.

A takaice dai Saida akai shekaru kamin ya koma cen da zama sai yayi watanni kuma kamin yaceman zaizo ganin kasuwancin shi na nan .

Wannan shi ne tarihin mu amma a yanzu inada shakku akan ka Adnan,ina tinanin kai ka kasheman iyaye hakane??.

Kan shi ya dago idon shi jage jage da hawaye.

Gaskiya magana Ba...

Ya isa Adnan fadamata Gaskiya da bakin ka, a wannan palon ba'a karya Manager yace fuskar shi ba walwala idonshi sunyi jawur .
MATAR OGA NA
UMMY AYSHA
Page 29


Cikin matsanancin kuka yace.
Tabbas Madina ina sonki amma nafison kudi da kowa a duniya,Kuma nayi alkawarin duk wanda zai Saɓaman akansu sainaga bayan shi,ba karya kikaiba nine nan nasa aka ma gidan ku wuta, domin danace miki na tafi babu inda naje hasalima ni nayi aikin da hannuna.
Zahirin gaskiya tinda na tashi nidai kam banyi wayon sanin dadin iyaye ba saboda mugun takaucin su,duk a titi nayi rayuwa dan ganin na samu kudi amma bansamu ba, banson kowaba sai kyarar al'umma,shiyasa ban tashi da tausayi ko wani imani ba saboda

Please Login or Register in order to submit comment