Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watarana "

shagwabe fuska ta yi ta ce mishi " ta ya zan iya kashe ka , ni ka ban nono na sha ko na yi maka kuka "

matse gera ya yi ya ce mata " Cutie ni wai tsaren wassan ki ne , na ga kwana biyu kin fara raina ni "

murguna mishi baki ta yi kafin ta tashi da ga saman cinyar shi ba ta ce mishi komai ba ta nufi lift za ta barin wajen maganar shi ba karamin bata mata rai ba ya yi , da ga ta na yi mishi wassa

a dubu dari ya mike da ga saman chair din shi taku biyar kadai ya yi ya damko kugun ta ta baya
ya na riko ta , ta saki kuka ta na neman kwatar kan ta ta na cewa " yaya Zayd ka kyale ni na tafi , wajen mama zan je "

a hankali ya juyo ta su na fuskantar juna ya ce mata " Cutie yaji za ki yi min ? "

cikin kukan nata ta ke ce mishi " yaya Zayd ka kyale ni na tafi don Allah "

shiru ya yi ya na kallon ta sai kuka ta ke hawaye na zubo mata bibiyu
cikin sanyin murya ya ce mata " i'm sorry my Cutie " ya kai karshen ya na sakin ta
ya na sakin ta ta juya da gudu ta shiga cikin lift
ya na kallon ta har ta shiga dai'dai kofar za ta rufe ta fudo tongue ta yi mishi kwalo

shi dai bai ce mata komai ba , sai da kofar ta rufe sannan ya juya ya koma cikin corridor ya shiga bedroom din shi

bangaran Inaya kuma ta na baro part din kai tsaye ta nufi part din MALIKAT HOUDA kamar ta san hanya

bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA
nan ta tardo Muntaz zaune tare da MALIKAT HOUDA
cikin girmamawa Inaya ta karasa wajen MALIKAT HOUDA ta tsuguna ta gaishe ta
da fara'a a fuskar ta ta amsawa Inaya gaisuwar ta har da zolayar ta irin wassan nan na sirikai sannan ta ce mata ta shiga mamar ta na ciki
ba musu Inaya ta tashi ta nufi corridor ta shiga bedroom din Mama

tun da ta shigo parlourn Muntaz ke yi mata wani kallon kaskanci kamar ba ta san ita ce MALIKAT din Saudiya ba a yanzu

sarai MALIKAT HOUDA ta lura da Muntaz shi ya sa ta ce ma Inaya ta tashi ta je
sai da ta bari ta shiga bedroom din mama sannan MALIKAT HOUDA ta ce Muntaz " kin san ko wacece yarinyar nan a yanzu ki daina yi mata irin wannan kallon banzan "

cikin bacin rai Muntaz ta ce " yanzu Mamie ki na ji ki na gani za ku bar Malik ya auri yarinyar da ya yi biyun shekarun ta , kuma har ta hau kujerar MALIKAT "

" Muntaz Malik ya na son yarinyar nan dan idanun shi kadai za ka kala ka san ya na matsanincin son yarinyar nan , da kin tsaya kin ga abun da ya faru a ciki fadar lokacin da za a nadda ta MALIKAT , bai bawa kowa damar yin jayaya da shi ba , kin sani wanda ya nadda Malik shi ke nadda MALIKAT , amma wannan da hannayan shi Malik ya nadda ta , kin ga ko ba damar yin jayaya "

kamar za ta yi kuka ta ce " yanzu shikenan mamie ta raba ni da shi "

dan karamin tsaki MALIKAT HOUDA ta yi kafin ta ce " Dama a tare ku ke ne ? dama a ce shi ma ya na son ki ne da farko da sai ki ce ta raba ku amma a sani na ko hira ba ta taba shiga tsakanin ku da Malik dan haka ki bawa kan ki lafiya sakara kawai "
ta na gama fadar haka ta mike ta shiga corridor ta koma bedroom din ta

ta bar Muntaz nan sai faman cika da batsewa ta ke sai ita ta ji haushi
Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment