Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka RIANNA ta fito da ga cikin corridor din a hankali ta karaso ta tsaya a bayan shi cikin sanyin murya ta ce " Akhie tasso mu je ka gani "

girgiza mata kai ya yi a hankali ya na cewa " I can't , Ukhtie please kill me , ki kashe ni na tarda ta tun kafin ta yi min nisa , wlh ba zan iya rayuwa babu ita ba , I love her more than you think , ya zan yi yanzu da rayuwa ta , na kashe wadda na ke so da kai na "

wani cool murmushi ta saki kafin ta dan sunkuyo ta riko hannun shi ta na cewa " Akhie please tasso mu je ka gani "

a hankali ya mike tsaye ya fara takawa ya na rike da hannun ta , ya na taku kamar jiri ya debe shi
a haka har su ka karaso bedroom din , RIANNA ta turo kofar su ka shiga sannan ta nuna mishi Inaya ta ce " duba ka gani "

slowly ya dago kan shi ya kale ta , da karfi ya zaro idanun shi ya na kallon ta zuciyar shi na duka uku uku

konce ta ke , ta na rufe da Duvet din su fara kal , ta na kallon Ceiling ta na kiftawa a hankali

a hankali ya zame hannun shi da ga cikin na RIANNA ya daga kafa ya tako bakin gadon murya har kerma ta ke ya ce " Cu.....Cut.....Cutie ? "

a hankali ta bude baki ta ce " na'am "
dum ya ji zuciyar shi ta buga , mafarki ya ke ko kuwa
da sauri ya juya ya kali RIANNA irin kallon nan na ban gane ba
kamar ko ta sani sai ta ce mishi " ni ma a haka na tardo ta "

a hankali ya juyo ya kali Inaya ta karaso bakin gadon ya zauna cike da shakku ya ce mata " Cutie da gaske ke ce ? "

yar karamar dariya ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa ta ce " baby in ba ni ba ce wacece to ? "

wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke a dubu dari ya fada jikin ta ya rungume ta ya na fadin " ba ki san irin tsoron da na ji ba , na zata kin tafi kin bar ni har abada , I'm sorry i promise ba zan sake ba , ba zan iya jure rashin ki ba My Cutie I really love you more than my own life "

cikin rudu Inaya ta dan bubuga bayan shi ta ce " Baby wai maganar me ka ke yi haka ? "
slowly ya dago da ga jikin ta , ya na shirin magana RIANNA ta riga shi cewa " tunda ba ku bukata ta zan iya tafiya ? "

da sauri Malik ya tashi ya nufe ya rungume ta a kunne ya rada mata " I really love you my Sister , na gode da ki ka dawo min da ita "

cikin rada ita ma ta katse shi da cewa " Akhie ni fa ba abun da na yi , yadda ka tardo haka na tardo ta ko taba ta ban yi ba da na ga idanun ta a bude shi ne na koma na kira ka "

slowly ya dago da ga jikin ta ya na zaro idanu cike da rudu " what do you mean ? "
" Akhie ka tabbata da ta mutu , kar a je suma kawai ta yi ba ka gane ba "

a hankali ya girgiza mata kai kafin ya ce " no sai da na duba zuciyar ta na ji ta daina bugawa , kuma har ruwa na zuba mata amma ba ta tashi ba "

slowly RIANNA ta dan juya da kan ta , ta kali Inaya da ke konce ta na kallon Ceiling cikin konciyar hankali
sannan ta juyo ta kali Malik ta ce " je ka kula da matar ka , gobe mun yi magana " ta na gama fadar haka ta juya ta fice musu bedroom

ta na fita ya juya a hankali ya nufi Inaya ya Zube saman guyiwowin shi bakin gadon ya kai hannu saman kumatun ta ya ce " My Cutie ! "

wani cool murmushi ta saki kafin ta juyo ta kaleshi ta ce " hmm Malik ne da kan shi na ke gani saman guyiwowin shi ? "

maganar ta ba karamar dariya ta so ta ba shi ba amma sai ya shanye anya ma ta san mi Malik ya ke nufi

a hankali ya mike ya juya ya fara takawa ya nufi toilet ya shige
da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta lumshe idanun ta

ta na a haka ta ji ya fito da ga cikin toilet din ya nufi bed din ya sa hannayan shi dukka biyu ya dauke ta cak kamar baby har da duvet din da ta ke rufe da shi , dan ba zai jure sake ganin barnar da ya yi ba
ta na jin shi amma ba ta bude idanun ta ba
kai tsaye toilet ya koma da ita , bai dire ta ko ina ba sai cikin bath da ya tara ruwan zafi a ciki dan ya gasa mata jiki

ya na dire ta ko ta saki kara ta na neman ta gudu
da sauri ya sa hannu ya janye duvet din ya tila gefe sannan ya meda ta cikin ruwan ya na fadin " please Cutie calm down "

kamar za ta mishi kuka ta ce " baby ruwan nan zafi gare su "
" na sani amma ki yi hakuri , zafin da ki ji yanzu kadan ne saman wanda za ki ji da ga baya "

a hankali ta sakin mishi kuka ta na murkuso cikin ruwan ta na neman ta tashi
cikin sigar rarrashi ya ce " i'm sorry Cutie , zan saya miki chocolate "
cak ta tsaya ta na kallon shi ta turo dan bakin nan nata ta ce " da gaske baby ? "

a hankali ya kai dan bakin shi saman nata ya manna mata kiss , ya ce " yeah , da gaske na ke "
wani cool murmushi ta saki kafin ta koma cikin ruwan ta lumshe idanun ta , ta na jin shi har ya yi mata wanka ya saka mata Bathrobe sannan ya dauko ta kamar baby ya dawo da ita cikin bedroom ya kontar da ita saman Sofa
ya nufi bed din su ya zame bedsheet din su da ta koma jazir da jininta ya koma toilet da ita

jim kadan ya fito sanye da bathrobe shi ma , ya na rike da sabuwar bedsheet da duvet , bai bi ta kan Inaya ba ya nufi bed din su ya saka ya kyara shi

sannan ya juya ya nufi Inaya da barci ya dauke saman sofar , ya sa hannu ya dauke ta ya koma wajen gadon ya kontar da ita ya janyo duvet ya rufe ta har zuwa kirji sannan ya juya zai bar wajen

cak ta riko hannun shi ba tare da ta bude idanun ta ba ta ce " baby kar ka tafi "

a hankali ya juyo ya kale ta , bai ce mata komai ba ya dawo ya konta geffen ta , ya kai hannu ya kashe lamps din dakin ya kunna bedside lamps

ta na jin ya kashe wutar dakin ta matso kussan shi , ta kontar da kan ta saman chest din shi ta na sauke ajiyar zuciya

ajiyar zuciya shi ma sauke ya kai saman bayan ta murya cen kassan makoshi ya ce mata " konta ki yi barci , ba ki ga dare ya yi ba "

shiru ta yi ba ta ce mishi komai ba kamar mai barci
a hankali shi ma ya lumshe idanun shi , ya rasa tunanin da zai yi , na kashe ta da ya yi kokarin yi ko kuma Yadda a ka yi ba ta mutu ba



β–ͺWASHE GARI ( Misalin karfe 4 na safe )



a hankali ya ware idanun shi ya na karanto adu'ar tashi da ga barci , duk da ba wani barcin ba ya yi
slowly ya juyo da kan shi ya kale ta , sai barcin ta , ta ke cikin konciyar hankali har wani cool murmushi ta saki da allamun barcin ya yi mata dadi ba kadan ba

bai ce mata komai ba ya juya ya sauko da kafafun shi kassa ya mike tsaye ya fara takawa a hankali ya nufi toilet dan ya yi wanka

jim kadan ya fito daure da towel a kugunshi ya nufi Dressing room ya shige , ta cikin dressing room din ya shirya cikin wata farar jallabiya mai mugun kyau ya bi ta hanyar sirri ya tafi mosque din da ke cikin masarautar

misalin karfe 7 ya dawo cikin bedroom din
inda ya bar ta ko motsi ba ta yi ba
a hankali shi ma ya karaso bakin gadon ya zauna ya zuba mata idanu , wani irin shauki ya ke ji cikin zuciyar shi , har ga Allah ba ya tunanin zai iya rayuwa babu ita , da yanzu a ce ta mutu ba ya tunanin zai ci gaba da rayuwa da shi ma sai ya kashe kan shi ya tarda ta , amma kuma in ya tuno irin dadin da ya sha cikin daren , kamar ya sake afka mata dan har yanzu a hannu ya ke , dadin ta bai gama sakin shi ba

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi kawai sai ji ya yi ta kontar da kan ta saman cinyar shi
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya sauko da kan shi ya kale ta
wani cool murmushi ta sakin murmushi cikin sanyin murya ta ce mishi " Good morning ranka shi dade mai girma Malik "

a hankali ya sunkuyo da kan shi ya manna mata kiss a saman forehead din ta ya ce " Good morning My MALIKAT "

wata yar karamar dariya ta yi har sai da dimple din ta ya lotsa
a hankali ya dago hannun shi ya saka yatsar shi cikin yar hudar dimple din ta ya ce " tashi mu je ki wanka "

shagwabe fuska ta yi kafin ta ce " baby ni breakfast zan fara yi , ni da baby na yunwa mu ke ji "

dan zaro idanu ya yi ya na kallon ta ya ce " wane babyn kuma ? "

" wanda ke cikin ciki na mana " ta kai karshen ta na kashe mishi ido guda

mikewa tsaye ya yi sannan ya sa hannu ya dauke ta cak ya nufi toilet da ita ya na fadin " ke da samun baby sai a lahira in a na samu " ya kai karshen ya na shiga cikin toilet da ita

sai da ya share wajen good one hour a cikin toilet din kafin ya fito da ga cikin toilet din ya na dauke da ita , su na sanye da bathrobe dukkan su

kai tsaye Dressing room ya wuce da ita
jim kadan ya fito sanye da manyan kayan shi da Alkyaba , da allamun Fada zai tafi
ya na dauke da ita kamar baby , ta na sanye da wata gown pink colour mai mugun an yi mata zanen flowers da wani zare mai launin gold

kai tsaye bedroom din ya baro tare da ita , ya fito parlour ya nufi dining ya janyo chair ya zaunar da ita sannan ya janyo ta geffen ta ya zauna

sai faman hura kumatu da iska ta ke wai ita ta ba ta jin dadin daukar nan da ya ke mata shi kuma ya ki hakura ba ya son ya bar ta , ta taka ko da nan da cen ne

" My Cutie , me ya faru ? " ya tambayeta kamar bai san abun da ke faruwa ba

turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " yaya Zayd ka kyale ni , na ce maka zan iya tafiya da kai na amma ka ki yarda "

" shikenan tashi ki yi taku biyu mu gani , amma in ki ka ji zafi kar ki ce ban fada miki ba "

ba musu ta tashi ta yi taku biyu cikin nitsuwa har juyawa ta dinga yi ta na ce mishi " ka gani ko ? sai da na ce maka ina ina iya tafiya amma ka ki yarda "

kallon ta ya ke cike da mamaki , wai cikin mafarki ya yi dis virgin din ta ko ya ne wannan abun , shi ya san aikin da ya yi mata cikin daren nan ba zai yi yu ba a ce ta na takawa haka har da juyawa
gaskiya akwai ayar tambaya a nan , shi da kan shi ya duba ya ga eh ta mutu , to ya a ka yi ta tashi lokaci guda ko 30 minutes ba a yi ba , ga shi kuma yanzu ta na tafiyar ta cikin konciyar hankali , shi sai yanzu ma ya tuno yadda ya ga vagina din ta da su ka shiga wanka kamar bai yi dis virgin din ta ba , gaskiya ya kamata mu gano abun da ya faru bayan fitowar shi bedroom din , dan duk abun da ya faru da ya na cikin dakin a lokacin da zai ga komai , amma ba laifi akwai camera ko ina cikin part din , na bedrooms ne kadai ba wanda ya san da su sai shi dole ya duba su dan ya samo amsoshin tambayoyin shi


a hankali ya mika mata hannu ya na fadin " shikenan i'm sorry , yanzu zo zauna ki yi breakfast ba kin ce yunwa ki ke ji ba ? "

gyada mishi kai ta yi ta na murmushi ta karaso ta riko hannun shi sannan ta zauna saman chair din ta , su ka fara yin breakfast a tare , ita dai fruits kawai ta ke sha dan ta fi jin dadin yin breakfast da su
shi kuma tea kadai ya sha
bayan ya Kamala ya mike ya yi mata kiss saman forehead din ta sannan ya ce " Ki kula da kan ki , idan ki na bukatar wani abu akwai Maid a kitchen ki yi musu magana "

ya na gama fadar haka ya juya zai bar wajen
da sauri ta riko hannun shi ta marairaice fuska ta ce " baby ba za ka jima ba ko ? "
gyada mata kai ya yi a hankali allamun eh
wani cool murmushi ta saki kafin ta saki hannun shi ta na yi mishi a dawo lafya sannan ta juya ta ci gaba da shan fruits din ta

a hankali ya juya ya fara takawa ya nufi lift , sai da ya shiga lift din ya juyo ya daga mata hannu dai'dai lokacin da kofar lift din ta rufe ya sauko floor na uku

ya na shigowa parlourn ya tardo Diya zaune
cen kassan makoshi ya yi mishi sallama ya na karasowa cikin parlourn
dan karamin tsaki Diya ya yi kafin ya mike ya na fadin " gaskiya Malik ba ka da kirki , tun karfe 8 ka ce na zo , amma yanzu dubi karfe nawa , ka san da baby na ba ta da lafiya na tashi na baro ta kawai dan ka na nema ta "

" Nesrine ba ta da lafiya me ya same ta ? " Malik ya fada cikin sanyin murya

mikewa tsaye Diya ya yi ya karaso gaban shi ya tsaya ya ce " i don't know "
cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " ka tabbata ba yarinyar mutane ka yi wa ciki ba ? " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi lift

dariya sosai Diya ya yi ya na bin bayan shi sai da su ka shiga cikin lift din sannan ya ce mishi " Malik yarinyar mutanan da ka ke cewa matata ce , kuma in na yi mata ciki ba ruwan ka a ciki "

" ni na fada ne kawai dan mu fara shirye kayan baby kar mu samu surprise "

" kar ka damu , duk lokacin da na ji qamshin shi kai ne na farko da zai sani , but she is not Pregnant for the moment "

gyada kan shi Malik ya yi a hankali kafin ya ce " okay , ya kamata ka sa doctor ta je te duba ta da wuri "

ya na gama fadar haka kofar lift din ta bude ya daga kafa ya fito building din
ya na fitowa sai saman wasu bakaken motoci guda uku zagaye da sojoji kowane rike da gun
su na ganin shi su ka shiga Sara mishi sannan daya da ga cikin su ya yi sauri ya bude mishi gidan bayan motar ta tsakiya
[05/10 Γ  08:06] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:


❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸ”₯









_________________________β€»β€»β€»β€»β€»___________________________





BOOK ________2 βœπŸ“šπŸ”₯







P A G E 2 7 πŸ₯€ ❀





cikin nitsuwa ya shiga cikin motar tare da Diya , sannan sojan ya rufe
duk su ka shige cikin motocin su , su ka bar wajen
ba su yi tafiyar two minutes ba su ka iso Prison din da ke cikin masarautar , cen bayan masarautar

su na isa sojojin nan su ka sauko da sauri su ka bude mishi kofa
ya sa kafa a hankali ya sauko , Diya ya na bayan shi
Cikin nitsuwa Diya ya ce ma sojojin nan " ku jire mu a nan " ya kai karshen ya na bin bayan Malik su ka shiga cikin Prison din

ya na shiga wani Sojan ya tarbe shi cikin girmamawa ya gaishe shi sannan ya yi mishi iso wajen cell din saurayin nan da ya ce a rufe

duk inda ya wuce Sai sojoji sun sara mishi cikin girmamawa
mai ce musu komai ba ya na tafiyar shi cikin nitsuwa har su ka karaso wajen cell din in da wasu sojojin biyu ke tsaron ta

su na ganin shi su ka sara mishi cikin girmamawa Sannan dayan ya bude mishi cell din ya daga kafa ya shiga
wajen duk duhu ne da kyair ya iya ganin saurayin cen karshen cell din zaune , ga handcuffs a hanayan shi

ya na shiga ya ce ma Diya " Please ina son na yi magana da shi "
ba musu Diya ya juya ya bar cell din , sojojin nan su ka bi bayan shi su ka dan yi nisa kadan

a hankali Malik ya daga kafa ya karasa cikin cell din ya zauna saman dan gadon cell din ya rike hannayan shi ya na kallon saurayin ba tare da ya ce mishi komai ba

sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce mishi " barci ka ke yi ? "

a razane Saurayin nan ya bude idanun shi , zuciyar shi na duka uku uku ba karamar tsorata ya yi ba ganin Malik da kan shi zaune cikin cell din shi har wani baya ya ke yi

cikin nitsuwa Malik ya ce mishi " kontar da hankalin ka "

wasu yawu saurayin nan ya hadiye murya har kerma ta ke ya ce " ran ka shi dade ? "

dan lumshe idanun shi ya yi a hankali ya sake bude su a kan shi ya ce " a yanzu ba Malik ne ba a gaban ka , Nawfel Hicham bin Jaabar ne wanda ka kashewa mahaifi "

shiru saurayin nan ya yi bai ce komai ba , gaskiya ba karamin kwarjini Malik ya yi mishi ba

ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya ce " zan so ka kontar da hankalin ka , ba abun da zan yi maka , na zo ne dan na yi maka wasu tambayoyi , dan na tabbatar da gaskiyar ka , zuciya ta ba yarda da kai kashe Malik haka kawai , za ka ba ni amsar da na ke so ? "

a hankali saurayin nan ya gyada mishi kai allamun eh

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Da farko zan so na san sunan ka "

a hankali Saurayin nan ya bude baki shi cikin wata disashashiyar Muryar shi ya ce " Abdoul Hakim Jafar " a takaice

gyada kan shi Malik ya yi sannan ya ce " a ina ka ke zaune "

" Maroco , a cen na ke zaune tare da family na kuma a cen na ke aiki a ciki Army "

" okay Hakim , zan so na san dalilin ka na baro Maroco ka zo har Saudiya kawai dan ka kashe min mahaifi na "

wani cool murmushi Hakim ya saki kafin ya ce " ranka shi dade , kar ka ce na yi ba dai'dai ba , amma zan so na san wani abu saman ka "

gyada mishi kai kawai Malik ya yi allamun ya na sauraron shi
" ranka shi dade me za ka iya yi a kan soyayya , a kan macen da ka ke so fiye da rayuwar ka ? "

shiru Malik ya yi bai ce mishi komai ba kawai ya tsare shi da wadanan hazel eyes din nashi

sai da ya dauki wajen good ten minutes kafin ya bude baki a hankali ya ce " ba me zan iya ba , me zan yi a kan ta , dan babu abun da zai gagare ni a kan ta Zan iya ba ta rayuwa ta , kuma zan bada rayuwar duk wanda ya yi kokarin cutar min da ita "

wani cool murmushi Hakim ya saki kafin ya sunkuyar da kan shi ya ce " haka zalika ran ka shi dade zan iya yin komai a kan matata , ko da sadaukar da rayuwa ta ne , na san ka na kaunar MALIKAT din ka da ga jin kallaman ka , duk abun da na yi , na yi shi ne saboda soyayyar matata "

cikin rudu Malik ya ce mishi " kenan ita ta ce maka ka kashe Malik "

cikin nitsuwa hakim ya girgiza mishi kai sannan ya dago shi
nan Malik ya ga idanun shi sun ciko da ruwa

" Hakim please tell me , kar ka ji tsoro , na yi maka alkawari zan yi maka adalci , Idan kuma wani ya saka ka yin hakan zan so ka fada min wanene , in ku..... "

bai kai karshen maganar shi Ba Hakim ya katse shi da cewa " ka yi hakuri ran ka shi dade , ba a son rai na na yi hakan ba , na san zafin rashin uba saboda ban tasso da nawa uban ba , ba zan so wani ya ji irin wannan radadin saboda ni , amma ba yadda zan yi , Najoua ita kadai ta rage min , ba zan iya jure rashin ta " ya kai karshen hawaye na zubo mishi

" Who is Najoua ? " Malik ya tambaye shi cikin sanyin murya

wani cool murmushi Hakim ya saki kafin ya ce " My wife , ita kadai ce abun da na mallaka a duniya , saboda ita na ke rayuwa kuma saboda ita zan iya yin komai , murmushin ta kadai ke sa na ji duk wata damuwa ta ta gushe , Ita ce farin ciki na kuma ina alfahari da ita a

Please Login or Register in order to submit comment