Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

din ya lumshe idanun shi

kamar da ga sama ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " Al-Malik Nawfel bin Jaabar "

dan karamin tsaki Ya yi kafin ya bude idanun shi ya kali Diya da ke zaune geffen rawanin shi ya ce " lafiya ka biyo ni ? "

yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " ba komai Amir , oh Sorry ina nufin Malik "

tsaki Malik ya yi ya na kauda kai gefe
" yawwa na ce , wai me ya sa ka ce a kai yaron nan prison ba ka yanke mishi hukuncin kai tsaye ba , bayan bincike ya nuna shi ya kashe Uncle ? "

dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " Gaskiya ba na ji a jiki na yaron nan zai iya kashe mutum haka kawai "

" ka na nufin cilas ta mishi a ka yi ? "

a hankali Malik ya gyada mishi kai kafin ya ce " shi ya sa na ce a rufe min shi , gobe zan je da kai na , na tambaye shi , Idan ma cilas ta mishi a ka yi zan gano da kai na "

" okay , yanzu tashi mu tafi wajen wallimar da a ka shirya maka "

lumshe idanun shi Malik ya yi murya cen kassan makoshi ya ce mishi " tashi ka tafi ni babu inda zan je "

yar karamar dariya Diya ya yi kafin ya ce " Why ? , kai fa a ka shirya wa , bai kamata a ce ba ka wajen "

" please Diya let me , ba na bukatar ganin kowa a yanzu "

" ko da kuwa MALIKAT Inaya ce ? " Diya ya fada ya na dan lekon face din Malik

Shiru ya yi bai ce mishi komai ba , dan duk duniya ita kadai ce yanzu ya ke son gani , tun bayan da ta Kamala period din ta yanzu wajen kwana biyar bai sake saka ta a idanun shi ba sai yau , yau din ma ba wani gani kirki ya yi mata ba , ga shi ta yi wani fresh ta kara haske , ta samu kula da ga wajen MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU , fatar jikin ta ta yi wani laushi kamar ta baby , hannun ta kadai da ya taba ya ji wata muguwar sha'awar ta ta taso mishi dalilin da ya sa ma ya baro fadar ba shiri , dan kar mutanan wajen su lura ya na cikin sha'awa

ya yi nisa cikin tunanin shi kawai ya jiyo Muryar Diya ya bushe da dariya
dan karamin tsaki ya yi kafin ya ce mishi " wai minene abun da dariya , kai ba ka da aiki sai dai dariya "

tsagaita dariyar shi Diya ya yi kafin ya ce " ba dole na yi dariya ba , Bari zan je na fadawa Ammie a kawo maka matar ka tun yanzu ba sai dare ya yi ba , ko kuma na sa a kawo maka lemun tsami ? "

bai ce mishi komai ba ya mike cikin nitsuwa ya nufi corridor ya shige
da kallo Diya ya raka shi har sai da ya shiga sannan ya sake bushewa da dariya har da dafe ciki kafin ya tashi ya sauko Floor na farko , dan a nan ne a ka shirya wallimar



β–ͺROUKSAR


tsaye ta ke gaban Damba , da ke faman Dariya har wasu hawaye na zubo mishi
cike da bacin rai ta ce mishi " Damba don Allah ka daina wannan dariyar mu san abun yi "

tsagaita dariyar shi ya yi ya ce mata " Sai da na fada miki ki kashe yarinyar nan , amma ki ka tsaya wai sai an yi nadin Malik , dan ki na da tambacin ke zai nada a matsayin MALIKAT , to yanzu wa gari ya waya ? dan haka ki bar ni na yi dariya "

dan karamin tsaki Rouksar ta yi kafin ta ce " Damba , a sani na kai ma cewa ka yi kai ne Malik zai nada a matsayin na hannun daman shi , amma mi ya faru yanzu "

" Diya ya nadda a matsayin na hannun daman shi , amma kar ki manta wassan Mulkin Saudiya yanzu ya fara , ko shekara dubu zai dauka mulkin Saudiya sai ya dawo a tafin hannu na "

" yanzu Damba ya ka ke so mu yi , dan gaskiya ba zan iya kallon yarinyar nan ta zauna saman kujerar MALIKAT ba , yanzu kennan aura mishi ita za a yi ? "

wani murmushi mai dan sauti Damba ya yi kafin ya ce " wa ya sani may be matar shi ce tun farko , dalilin da ya sa ta ke makale mishi kennan "

a hankali Rouksar ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " ko ba komai da sauki tunda ba wacen Hafsat a ka aura mishi ba , yar iskar yarinya tun kafin a yi auren ta dame ni da MALIKAT Hafsat , MALIKAT Hafsat , za ki ci uban ki ba MALIKAT Hafsat ba "

" kar ki manta , kin kashe maciji ne ba ki dare kan shi ba , ita wadda a ka nadda a matsayin MALIKAT ta fi karfin mu , idan har ki ka bari a ka kai ta part din Malik cikin daren nan , to tabass da ga ita har Malik sai dai kallo ba abun da za mu yi musu , cikin daren nan ki tabbatar kin kashe ta da poison din ki , Idan kuma mu ka yi sa'a Malik bai taba ta ba cikin daren nan , har yanzu da sauran damar mu "

wani makirin murmushi Rouksar ta saki kafin ta lumshe idanun ta , ta fara motsa lips kamar ta na magana

nan take duk jelar gashin ta ta koma green , duk ya koma kamar fatar maciji
a hankali fatar jikin ta ita ma ta fara komawa green wasu scale irin na maciji su ka fara fito mata saman Fuska
daya bayan daya jelar gashin ta , ta fara komawa manya manyan macizai , sai murkuso su ke yi su na fido harshen su waje su na wata kara abun ban tsoro

a dubu dari Rouksar ta bude idanun ta , sun koma idanun maciji sai da na ji gaba na ya fadi

wani mugun murmushi ta saki nan take fuskar ta ta koma kamar ta maciji , ta na fido harshen ta irin na maciji shi ma

cikin wata murya mara dadin ji ta ce mishi " Ssssssssssssss , sai na gggggaa bbbbbbbayyyyyyan ta , tunnnnnnn cennn wasssssssssa nnnnna ke mata "

wata shegiyar dariya Damba ya yi kafin ya ce " ya isa haka Medusa , ni fa wannan halitar taki ba son ganin ta na ke ba , specially wannan maganar ta ki ta macizai "

A hankali Rouksar ta lumshe idanun ta ,
sannu sannu jelar gashin ta ta fara komawa dai'dai tare da Skin ta
Slowly ta bude idanun ta da su ka koma dai'dai ta yi wata shegiyar dariya ta ce " Idan sun san wata ba su san wata ba , yanzu Mulkin Medusa zai fara , har shi kan shi Malik ba zan raga mishi ba " ta na gama fadar haka ta bace bat a wajen ta bar Damba
ta na barin wajen shi ma Damba ya bace bat



β–ͺINAYA


a tare da RIANNA su ka nufi part din MALIKAT AL'UMU Tesnim da Nesrine ba biye da su
bakin su da sallama su ka shigo parlourn MALIKAT AL'UMU , ta na zaune saman sofa one seater
ta na ganin Inaya sanye da Alkyabar ta , ta saki wani kyawatencen murmushi ta mike tsaye ta nufi Inaya

da sauri Inaya ta kwace hannun ta da ga cikin na RIANNA ta nufi MALIKAT AL'UMU da dan sauri ta fada jikin ta , ta rungume ta

wata yar karamar dariya MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta ce " MALIKAT Inaya sai a sake ni ko kin karaya min baya "

yar karamar dariya ita ma Inaya ta yi kafin ta saki MALIKAT AL'UMU ta na fadin " Sorry Momy "

hannun ta MALIKAT AL'UMU ta riko , ta kali RIANNA ta ce " ku bar ta a waje na zuwa dare sai ki zo ki kai ta , tun da ni ba zan iya zuwa ba "

gyada mata kai RIANNA ta yi kafin ta ce " amma momy , ki na ganin zai yarda ta koma part din shi baki daya ? , ko yanzu wajen nadda ta MALIKAT sai da mu ka fuskanci sa'insa "

wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " kar ki damu , ai shi da kan shi ya ba ta matsayin MALIKAT , kawai ki dawo ki kai ta part din shi idan lokaci ya yi "

ta na gama fadar haka ta juya ta kali Inaya ta ce " MALIKAT mu je na shirya miki wani abu na musaman "

" Da gaske momy " ta fada cike da zumudi
gyada mata kai kawai MALIKAT AL'UMU ta yi kafin ta nufi corridor ta shige
a hankali ita ma Tesnim ta bi bayan su ta nufi bedroom din ta

juyawa RIANNA ta yi ta kali Nesrine ta ce " mu tafi ko ? "
" Aunty RIANNA , ina so na ga mama " Nesrine ta fada cikin sanyin murya

da to kawai RIANNA ta amsa mata kafin su baro part din , a tare su ka nufi part din MALIKAT HOUDA

tun a cikin parlourn su ka tardo mama zaune saman sofa , ta yi zugum waje guda da allamun yau ta tuno malam dan ga hawaye nan konce cikin idanun ta

da gudu Nesrine ta fada jikin ta ta rungume ta ta na fadin " mama na yi kewar ki sosai da sosai "

wani cool murmushi mama ta saki ba karamin sanyi ta ji cikin zuciyar ta ba a hankali ta zagayo da hannayan ta ita ma ta rungume Nesrine ta na fadin " Amarya sai yau a ka tuno da ni ko ? "

wata yar karamar dariya Nesrine ta yi kafin ta raba jikin ta da mama ta koma gefe ta zauna ta na fadin " mama ai ni kullum ina tune da ke kuma ai kin san ba na cikin gidan nan yau din nan mu ka dawo "

" shikenan ya mijin naki ya ke "

dan sunkuyar da kai Nesrine ta yi wai ita kunya ta ce " ya na nan lafya "

ta na gama fadar haka Muntaz ta fito da ga cikin corridor ta na kuka kamar baby MALIKAT HOUDA na biye da bayan ta , tare da Gimbiya Manisha

da sauri RIANNA ta taro ta ta na fadin " Muntaz lafiya ki ke irin wannan kuka haka "

cikin bacin rai Muntaz ta sa hannu ta tura RIANNA baya ta na fadin " ki kyale ni , shikenan yanzu kun raba ni da Amir , kun fi kowa sanin tun ina karama na ke fama da son shi cikin zuciya ta , saboda shi tambayar aure nawa naki karba , kawai saboda irin son da na ke mishi yanzu kuma an aura mishi wacen Hafsat da ko kyau ba ta da "

wani cool murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce " to ai ita ma bai aure ta ba "

cikin rudu Muntaz ta daina kukan ta ta ce ma RIANNA " bai aure ta ba ? "

a hankali RIANNA ta gyada mata kai allamun eh

wani kyawatencen murmushi ne Manisha ta saki kafin ta karaso geffen Muntaz ta dafa shoulder din ta ta ce " kin ga sai da na fada miki Amir ba zai auri Hafsat ba saboda ba ya son ta , kuma na san shi ma ke ya ke so , zan wa mahaifin ki magana a aura auren ku ke da Amir..... "

cikin nitsuwa RIANNA ta katse ta da cewa " Malik ya ke a yanzu , kuma Muntaz zan fada miki gwara ki hakura da shi saboda ya nadda wadda ya ke so a matsayin MALIKAT "

" ban gane ba RIANNA me ki ke nufi , ki ka ce bai auri Hafsat ba to wacece MALIKAT " Manisha ta tambaye ta

wani cool murmushi RIANNA ta saki kafin ta ce " MALIKAT Inaya , matar shi wadda ya ke so kuma ya ke kauna , saboda ita a bai auri Hafsat ba , ba dan ya na son ki ba Muntaz dan haka gwara ki cire son shi da ga cikin zuciyar ki zai fiye miki al'heri "
ta na gama fadar haka ta juya ta fice parlourn ta bar part din baki daya

ta na fita ko Muntaz ta sake fashewa da sabon kuka ta na fadin " ni wlh sai an aura min Amir ko kuma na kashe kai na "

ba ta gama rufe bakin ta ba ta ji saukar mari Tasss a saman kumatun ta har sai da ta shanye kukan ta ba ta shirya ba

cikin bacin rai MALIKAT HOUDA ke ce mata " ki kashe kan ki sai me ? saboda mutumin da ba ya son ki , kin yi assara wlh Muntaz , tun wuri gwara ki cire son shi da ga cikin zuciyar ki , ke ko kunya ba ki ji ba , dube ki da kyawon ki da komai ki tsaya ki na yi wa namiji kuka , sai me idan bai aure ki ba mutuwa za ki yi , ko kuma shi kadai ne namiji a duniya , ni don Allah idan kukan ki za ki yi ki fice min a part kar ki cika mik kunnuwa "

ta na gama fadar haka ta nufi corridor ta shige ita dama ta gaji da rashin kunyar Muntaz duk cikin jikokin ta ita kadai ce mai taurin kai , ga shi kuma Manisha ta sangarta ta , ba dan Hussein na tsawata mata ba da abun ya fi haka

cike da bacin rai Muntaz ta nufi kofar fita part din ta fice Manisha na biye da bayan ta , ta na bata hakuri

duk abun da ya faru mama da Nesrine su na zaune su na kallon su dama dama Nesrine ta gane wani abu da ga cikin maganar su kuwa , mama ko rass ta ke jin su dan ita ma ta iya larabci

sai da parlourn ya rage da ita sai Nesrine sannan ta juya ta kale ta ta ce " Nesi wai me ya faru ne na ji su na maganar Inaya "

nan Nesrine ta shiga ba ta labarin abun da ya faru da ga farko har karshe
wani cool murmushi mama ta saki har sai da ta lumshe idanun ta , gaskiya ta na son ta ga Zayd din su amma ba hali dan rabon ta da shi tun bayan dawowar shi da ga Makkah ya zo ganin MALIKAT HOUDA ta hanyar sirri ta yi katari ta gan shi har su ka gaisa



β–ͺABDOUL
[02/10 Γ  21:23] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:





❀⚘ EXILED PRINCE ⚘❀
(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯





( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




STORY & WRITTEN BY : MEERAH πŸ‘‘πŸ”₯







_________________________β€»β€»β€»β€»β€»___________________________




BOOK ________2 βœπŸ“šπŸ”₯





πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯πŸ‘‘β€πŸ”₯




P A G E 2 5 πŸ‘‘ ❀ πŸ”₯





β–ͺABDOUL



tafiya ya ke yi da dan sauri kai a sunkuye ya na latsa wayar shi ko gaban shi ba ya kallo
ya na tsaka da tafiyar shi kawai ya bugi mutun da karfi har wayar shi ta fadi kassa
wata yar karamar kara Tesnim ta saki ta yi fuuu baya za ta fadi
cikin zafin nama Abdoul ya kai hannu ya damko kugun ga ya janyo ta , ta fado jikin shi ya na kallon face din ta ya ce " I'm sorry ba ki dai ji ciwo ba ko ? "

slowly ta bude idanun ta , sai cikin nashi ko nan take kawai idanun su su ka sarkafe cikin na juna

wani cool murmushi ya sakin mata ya ce " lafiya ki ke min irin wannan kallon ? "

a razane ta dawo cikin hayacin ta , ta janye idanun ta da ga cikin nashi ta yi kokarin raba jikin ta da nashi
ba musu ya saki kugun ta , ya sunkuya ya dauki wayar shi ya na dubawa ko ta samu matsala ba sannan ya dago kai ya kali Tesnim ya ce " ke ma kin koma makafniya ne na samo miki dan jagora ? "

wani dan karamin tsaki ta ja kafin ta ce " na ga kai ma ba ka kallon gaban ka "

murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya dan sunkuyar da kai ya ce " a yi min afuwa ranki shi dade "

wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " Shikenan ya isa haka "

" okay , za iya miki dan jagora dan na ga kin fara...... "
bai kai karshen maganar shi ba ta kai hannu ta buge shi a damtse ta na tsuke fuska
yar karamar dariya ya yi kafin ya ce " shikenan ban hanya na wuce yanzu "

ba musu ta matsa geffen ta ba shi hanya
" na gode , amma ki yi dan murmushi "
" why ? " ta fada a takaice

" murmushi ya na yi miki kyau over " ya kai karshen ya na daga mata gera guda
wani cool murmushi ta saki ta na sunkuyar da kan ta
shi ma murmushi mai dan sauti ya yi kafin ya fara takawa ya yi gaba abun sa

ta na jin ya fara takawa ta dago kai a hankali ta kale shi , kawai sai tsaya wa ta yi ta na bin shi da kallo
har sai da ya yi nisa sannan ta saki wani kyawatencen murmushi ta juya ta ci gaba da tafiyar ta ita ma
duk abun da ya faru Malik na kallon su ta cikin part din shi



β–ͺAFTER SOME HOURS


β–ͺMALIK


zaune ya ke saman chair din shi ta Gold ya daga kai sama ya lumshe idanun shi
ya na sanye da kayan barcin shi white color ma su mugun kyau sun zauna mishi a jiki sosai , sai tashin qamshi ya ke da ga gani ya na cikin nitsuwa

ya na a haka kawai ya yi wani fitinannan qamshi ya dake shi a hanci har sai da ya sauke ajiyar zuciya

slowly ya bude idanun shi sai Inaya da ke takowa a hankali kai a sunkuye ta na sanye da wata gown white color mai mugun kyau ta sha stone har da wasu sarkokin da ga tsakiyar ta , ta daura Alkyabar MALIKAT AL'UMU wadda ya aza mata da safe , ta saka hular Alkyabar ta saki gashin ta ya zubo mata saman shoulder sai tashin qamshi ta ke kamar ka sace ta ka gudu

tun da ta shigo ya tsare ta da idanu babu ko kiftawa har sai da ta karaso gaban shi ta tsaya kai a sunkuye ba tare da ta kale shi ba
a hankali ta Zube saman guyiwowin ta a gaban shi ba tare da ta dago kai ba

shi dai da ido kawai ya ke bin ta dan ba shi da bakin magana
cen kuma ya bude baki a hankali kamar mai rada ya ce mata " ke kadai ki ke tafe ? "

a hankali ta girgiza mishi kai kafin ta ce " ni da Aunty RIANNA , amma ita ta tsaya a floor na biyu , ta kuma ce na gaishe ka "

gyada kan shi kawai ya yi kafin ya Meda idanun shi ya lumshe , ya san da MALIKAT AL'UMU ta na iya fitowa da ita za ta kawo Inaya part din shi , amma kuma ita RIANNA wani dalilin ya saka ta tsayawa tun a floor na biyu bayan ta san a floor na uku ya ke zaune ?

" za ki sha Fruits ? " ya tambaye ta ba tare da ya bude idanun shi ba
cikin nitsuwa ta ce mishi " a'a ranka shi dade "

ba shiri ya bude idanun shi ya na kallon ta , yanayin da ta yi mishi maganar ji ya yi kamar ba Cutie din shi ba ce , ga shi ta yi maganar cike da nitsuwa abun ba karamin sanyi ya yi mishi cikin zuciyar shi ba bai taba jin ta yi magana cike da nitsuwa kamar yanzu

a hankali ya ce mata " stand up ! "

ba musu ta mike a hankali kai a sunkuye ta na kallon kassa
ta na mikewa ya riko hannun ta a hankali ya janyo ta ya zaunar da ita saman cinyar shi , ya kai hannu saman habar ta ya dago kan ta

wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta janye kan ta a hankali ta meda ta sunkuyar da shi

a hankali ya zame hannun shi da ga saman habar ta ya riko nata ya na fadin " yaushe ki ka fara jin kunya ta ne haka ? "

turo dan bakin nan nata ta yi cikin shagwaba ta ce mishi " baby ni fa ba na jin kunyar ka , kawai Aunty RIANNA ce ta ce min na dinga yi maka magana cikin nitsuwa "

" Shikenan , tashi ki je ki yi wanka , I've a Surprise for you "

wani kyawatencen murmushi ta saki ta dago kai ta kaleshi kafin ta ce wani abu ya daura dan yatsar shi saman bakin ta ya ce " shiiiiiiiiii , za ki fara cika ni da surutu ko ? , tashi kawai ki je ki yi wanka na ce ki zo ina jiran ki " ya kai karshen ya na janye yatsar shi

turo dan bakin nan nata ta yi ba dan ta so ba ta mike simi simi ta nufi corridor ta shige bedroom din shi , da kallo ya rakata har sai da ta shiga corridor din sannan ya lumshe idanun shi ya na sauke ajiyar zuciya

sai da ya share wajen good one hour zaune a nan ya na faman jiran ta , ko me ta tsaya yi oho ?

ya na a haka ya jiyo wani dadaden qamshi na tashi da ga cikin corridor
slowly ya bude idanun shi ya juya ya kali corridor din
a hankali ta ke takowa , ta na sanye da wasu kananan kayan barcin ta pink color ma su mugun kyau da allamun ko underwear ba ta saka ba dan duk taku daya in ta yi breast din ta ya girgiza
nan take duk ta tafi da imanin shi , kawai ya tsare ta da kallo har ta karaso geffen shi ta tsaya ta na mishi magana bai lura ba

ya yi nisa cikin duniyar tunanin shi kawai ya ji saukar hannun ta saman shoulder din shi
a hankali ya ja wani dogon nunfashi ya lumshe idanun shi a hankali kamar mai jin barci ya ce " What happening ? "

ba ta ce mishi komai ba ta zauna saman cinyar shi ta kontar da kan ta saman chest din shi ta ce " Baby wai tunanin me ka ke yi tun

Please Login or Register in order to submit comment