Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Ko amsa mata bai yi ba ya ci gaba da tafiyar shi
Sai da ya bar wajen sannan ta juyo ta kali MALIK ta ce " Abbi don Allah ku janye maganar nan ta AMIR ya hau mulki wlh ba ya so "

Daga mata hannu MALIK ya yi ya katse ta kafin ya ce mata " RIANNA ke da NAWFEL na ga bakin ku daya , idan bai hau mulki baya na ba wa zai hawa , ku nai sheda shi kadai ne yarima da na mallaka , ya tafi ya hura miki kunne ko , ya zuba miki shagwabar da ya saba ko "

Marairaice fuska RIANNA ta yi ta na fadin " please Daddy , ku ba shi damar ya zabi abun da ya ke son yi , kar ku condemend din shi saman abun da bai da ra a yi , wlh Abbi tun da ya nuna ba ya son Mulkin nan wlh ko ya hau ba zai tsaya ya kula da saudiya kamar yadda ku ke yi "

" RIANNA tashi fice min da ga gani sai ki bi bayan shi dama ke ce ke darme mishi gindi ya na abun da ya ga dama , to sai ki je ki rarrashe shi , ki kuma fada mishi gobe ya shirya bi na Fada "

" Abbi ......... "
Da sauri Malik ya daga mata hannu ba tare da ya ce komai ba
Tashi ta yi ta na dan kananan magaganun ta bi bayan AMIR ita ma ta bar wajen
Su dai Malikat kallon shi kawai su ke dan sun san halin Malik idan ya yanke shawara to babu wanda ya isa ya sa shi ya sauya shawarar nan dama haka nan ya ke da magana guda a ka san shi , duk irin halin da zai tsinci kan shi , shawarar kan shi kawai ya ke dauka , bai taba neman shawarar wani ba , Idan kuma abu ya shige mishi duhu shawarar Matan shi kawai ya ke nema


Bayan RIANNA ta baro dining room din su kai tsaye wani kyawatencen parlour ta nufa nan ta isko AMIR zaune saman chair din Malik ta gold zalla ya daura kafa daya bisa daya ya kurawa Tv ido

Dan zaro idanu RIANNA ta yi ta na kallon shi da sauri ta nufe shi ta na fadin " kai AMIR kujerar Malik za ka hau haka , maza sauka tun bai gan ka ba , ka fi kowa sanin bayan shi babu wanda ya isa ya hau wannan kujerar "

Slowly AMIR ya juyo da kan shi ya kali RIANNA ya na dan lumshe idanun shi kamar mai jin barci , cike da izza ya ce mata " da ga yau ta zama tawa " ya kai karshen ya na meda kallon shi kan Tv

Dan zaro idanu RIANNA ta yi ta na kallon shi baki sake , tun da ta ke da AMIR ba ta taba ganin ya yi mata kwarjini kamar na yau ba
Ta na shirin magana ta jiyo Muryar Malik a bayan ta ya na fadin " yanzu sai ka tashi me ita ya zo "

Dum ta ji gaban ta ya buga da sauri ta juya ta na kallon shi ta na dan zazzaro idanu
Shi dai AMIR ko motsi bai yi ba asali ma ko kallon inda Malik ya ke bai yi ba ya ci gaba da kallon Tv ................... ( ku tsaya na dubo abun da ke cikin Tv din nan gaskia )
Ba komai ba ne face masarautar ya ke kallo ta cikin kananan camera da a ka boye ta ko ina cikin masarautar , shi dai kawai ya na kallon abun da ke faruwa a cikin masarautar ne amma hankalin shi na nesa

Har sai da Malik ya karaso gaban shi ya tsaya ya na yi mishi magana bai sani ba
Kawai sai ji ya yi an buge mishi kafar shi ta sama ta fadi kassa ,
Slowly ya lumshe idanun shi kafin ya bude su ya na kallon Malik ido cikin ido kafin ya ce " What ? " a takaice

Ba Malik kadai ba har RIANNA da ke tsaye a bayan shi sai da ta zaro idanu ta na kallon AMIR
" NAWFEL sauka da ga saman kujera ta " Malik ya fada cikin nuna isa

Shiru AMIR ya yi na dan mintina kafin ya meda kallon shi kan Tv din ba tare da ya ce komai ba
" Akhie ............ "
Kut maganar ta yanke sakamakon daga mata hannu da Malik ya yi
" Idan ka na son zama saman wannan kujerar , dole sai ka yarda ka amshi sunan ka na yarima mai jiran gado ka fara bi na Fada domin ganin yadda a ke kula da masarautar nan sannan za ka iya zama saman wannan kujerar "


Slowly AMIR ya mike tsaye ya fara takawa a hankali ya karaso gaban Malik ya tsaya ya na kallon shi cikin ido ya ce " kujera ce dai sai na hau ta , sannan ni ba zan je Fada ba , ba na bukatar shawarar kowa ba na kuma bukatar sannin yadda a ke kula da masarautar , duk ranar da a ka nada ni a matsayin Malik tsari na kadai zan bi dan haka ka daina min zancen wata fada ni babu inda zan je " ya na gama fadar haka ya juya ya koma saman kujerar nan ya zauna ya daura kafa daya saman daya ya ci gaba da kallon Tv din gaban shi


Shi dai Malik sumar tsaye su ka yi shi da RIANNA
Sai ya kare mishi kallo da kyau sannan ya ce ma RIANNA ta ba su waje
Ba musu ta juya ta bar parlour dama part din Malik ne su ke ciki sai ta bar part din baki daya dama su Malikat su riga ta tafiya TESNIM kuma ta tafi yawon birididin da ta saba , ba ta wannan part ba ta wacen duk in da ta kama ta tafiya ta ke yi


A hankali Malik ya nufi wata Sofa da ke daman kujerar da AMIR ke zaune a kai shi ma ya zauna ya na kallon AMIR

Kamar ko ya san kallon shi ya ke yi ya ce mishi " lafiya ka na kallo na haka "
Girgiza kan shi Malik ya yi ya na murmushi ya ce " Mulki ya na kama ka AMIR why kullum ka ke abu kamar mace , sai dan karan shagwaba , ko takobi sai da RIANNA ta matsa sannan ka fara koyo , da ba hakan ba yanzu ko makiyi ya zo maka ba za ka iya kare kan ka ba "

Shiru AMIR ya yi bai ce mishi komai ba
Dariya Malik ya yi kafin ya dauki wani pillow saman sofar ya tila wa AMIR
da sauri AMIR ya kauce pillow din bai same shi ba
Dan karamin murmushin geffen fuska ya yi ya ce " Abbi , ni fa fada ne da makami ba ya burge ni , na fi son fada da hannu "

" hmmm , hakan ba shi ba ne mafita ba , ya kamata a ce duk wani makami a duniya ka iya fada da shi , ba ka san ta yadda makiyin ka zai zo maka ba , bare kai da ka ke cikin gidan sarauta "

Cikin nitsuwa AMIR ya katse shi da cewa " Idan kuma makiyin ya zo maka ta baya ? "
Shiru Malik ya yi ya rasa amsar da zai ba shi
Jin ya yi shiru ya sa AMIR juyo da kan shi ya kali Malik
Dan karamin murmushi ya saki kafin ya ce " ba ka san ta yadda makiyin ka zai zo maka ba , amma na san wani abu , duk mai sanin ganin bayan ka , ba zai soke ka ta gaba , dole ta bayan idon ka zai soke ka , saboda ya san ka fi karfin shi ta gaba "

" wait ! Maganar me ka ke yi min haka " Malik ya fada dan shi bai san abun da AMIR ke fada ba

Meda kallon shi AMIR ya yi kan Tv sai da ya dan dauki lokaci kafin ya ce " ba komai kawai ina nufin ka zama me tsare bayan ka a kodayaushe saboda ba ka san ta inda makiyin ka zai zo maka ba , Idan kan ce ka za kare gaban ka kadai , to ta bayan ka zai zowa , dan haka ka zama mai kare gaba da bayan ka , saboda ba ka san da wa ka ke tare da shi ba , Makiyin ka zai zo ma ka da sufar aboki , aboki kuma da sufar makiyi "


Dariya sosai Malik ya yi kafin ya ce " shi ya sa ban yarda da kowa cikin masarautar nan , ko a fada ba shawarar kowa ba ke doka ba "

" Duk da hakan , yanzu idan na tambaye ka cikin fadar nan wanda ke zaune da kai da zuciya daya za ka iya fido min su "

Shiru Malik dan ba kariya ya fada ba
" Shi ya sa na ce ka zama mai tsare gaba da bayan ka , ba ka san wanda ka ke tare da shi ba , ko da ya na zaune da kai da zuciya daya , wata rana zai iya juya maka baya "

Dogon nunfashi Malik ya ja kafin ya ce " kai ni fa hirar nan ta ka mara ma'ana ta fara isa ta "

Murmushi kadan AMIR ya yi kafin ya ce " ban rike ka ba tashi ka tafi "
" ban son shirme , part di na ne ka ke ciki "
Dariya AMIR ya yi ya na fadin " ba wajen matar ka ba za ka kwana , tashi ka je ni a nan zan kwana "

" kai eh fa haka ne ka ma tuno min , bari na tashi na tafi wajen baby na " ya kai karshen ya na mikewa tsaye

Da sauri AMIR ya taro shi ya na fadin " Wait, Abbi wa ka ke kira da baby "
Hararrar wassa Malik ya yi mishi kafin ya ce " Mummyn ka mana " ya kai karshen ya na kashe mishi ido guda

Dariya sosai AMIR ya yi har da dafe ciki idanun shi na kawo ruwa
Shi ma dai Malik yar dariya ya yi kafin ya tako kusa da AMIR ya dan sunkuyar da kai
Ya rage sautin Muryar shi kamar mai rada ya ce " Ka na ji na ko , ita fa mace yar shagwaba ce ka bar ganin dan ta haifi zankadeden saurayi kamar ka , kullum ta na son a dinga ririta ta , a na shagwaba ta kamar baby , dan ba ka da matar ne shi ya sa ba za ka gane ba "

" ba ni ma son na gane " AMIR ya fada ya na yar dariya

" hmmm AMIR ina guje maka ranar da so zai maka mugun kamu , wlh sai ka yi kuka "

Dan matsowa AMIR ya yi kusa da face din Malik murya kassa kassa ya ce " Har yanzu ba a yi macen da za ta Mallaki zuciyar AL-AMIR NAWFEL BIN JAABAR d'a tilo ga MALIK HICHAM BIN JAABAR jikan MALIK ABDOUL LATIF BIN SAUD , Har yanzu ba ta shigo duniya ba "

Jinjina kan shi Malik ya yi kafin ya ce " Gaskia ne kam , izza a jinin ka ta ke , amma ka sani , mace ce ta haife ka , kamar yadda ta haife ka haka zalika , za ta haifi wadda za ta malake zuciyar ka , duk wannan izzar da ka ke nuna wa sai ta zube a gaban ta , ka jira ka gani "

" Abbi , dubi wuce ka tafi wajen babyn ka , ni kyale ni film zan kala "
Yar karamar dariya Malik ya yi kafin ya kai bakin shi ya sumbaci forehead din AMIR sannan ya ce " ai kai ma baby na , I love you "

Dan murmushi AMIR ya yi kafin ya ce " I LOVE YOU dad "
Jinjina mishi kai Malik ya yi kafin ya mike ya juya ya fara takawa
Har ya yi nisa ya jiyo Muryar AMIR ya na fadin " ka yi min magana da Azim "
Jinjina mishi kai kawai Malik ya yi ba tare da ya ce komai ba har ya ficewar shi ya bar AMIR shi kadai

Bai yi five minutes da fita ba wani mutumin ya shigo parlourn ya na sallama
Ya sha ruwan mamaki ganin AMIR zaune saman kujerar da Malik ke zama , a sanin shi bayan Malik ba wanda ya taba zama saman ta sai yau ga AMIR zaune sama

Karasowa gaban AMIR ya yi ya Zube saman guyiwowin shi ya sunkuyar da kai ya na fadin " Allah ya ja zamanin yarima , dan sarki jikan Sarki , ina mika gaisuwa na ga Adalin shugaba na , Umarnin kadai na ke jira "

Daga mishi hannu AMIR ya yi kafin ya ce " ya isa haka Azim wani aiki na ke son ka yi min , kuma zan so ya tsaya a tsakanin mu "

" umarnin kadai na ke jira ya shugaba na , yadda ka so haka za a yi "

" ina son ka je part di na , Bedroom na farko ba wanda na ke barci ciki ba , ka duba cikin bedside drawer , akwai passport di na , da Visa , duk ka dauko su , sannan ka shiga ka duba cikin closet , ka dauko jakar cumputer di ta ka saka su a ciki ka kawo min ina jiran ka "

Da sauri Azim ya ce " An gama shugaba na " ya na gama fadar hakan ya tashi da sauri ya fice parlourn
[16/09 à 09:57] M.N.M:


❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤


(LOVE MEETS POWER ) 👑🔥




( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny )




⚘🕊 MALLAKIN MEERAH 🕊⚘



【 THE ROYALTY LOVE ✌👑🌹】




Marubuciyar littafin :【 TAURIN ZUCIYA 💖💍🌺 】




YOU CAN FOLLOW MY WHATSAPP CHANEL
👇👇👇👇👇👇👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaGhJCqKmCPUvpvIJ80i





BOOK .............. 2 🌹👑







________________🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊________________





{PAGE 3 ❤🔥}






Ya na fita AMIR ya mike tsaye ya nufi glass din da ke bayan shi dan duk ginin na glass ne
Ya tsaya ya na kallon masarautar ya na nade hanayan shi a baya

Ya dauki wajen good ten minutes a hakan kafin Azim ya dawo cikin parlourn ya na sallama
Ba tare da ya juyo ba ya amsa mishi sannan shi cen kassa kassa
Geffen shi Azim ya karaso ya Zube saman guyiwowin shi ya na fadin " An gama ya shugaba na , ga abun da ku ka bukata "

" Ajiye saman Sofa ka zo ina son magana da kai "
Ba musu Azim ya tashi ya koma cikin parlourn ya ajiye jakar saman sofa kafin ya komo geffen AMIR ya Zube saman guyiwowin shi

Cikin nitsuwa AMIR ya ce mishi " mike tsaye Azim , ka san fa ka girme ni a shekaru "

Mikewa tsaye Azim ya yi ya dan ja baya kadan ya tsaya ya na sunkuyar da kan shi sannan ya ce " ya shugaba na , tabass na girme ka da shekaru , amma ai matsayin ka sama da nawa ya ke "

Dan karamin murmushi AMIR ya yi kafin ya ce " Azim duk wannan matsayin ba komai ba ne , a wajen Allah duk daya mu ke , zan tambaye ka wani abu Azim kuma ka fada min gaskia "

" in sha Allah shugaba na idan na sani zan fada maka "

Gyada kan shi kadan AMIR ya yi kafin ya ce " ina son ka fada min , a ganin ka zan iya yin mulkin saudiya kamar na Malik "

Dan karamin murmushi Azim ya yi cikin girmamawa ya ce " Ba zan yi maka kariya ba Shugaba na "

Da sauri AMIR ya katse shi da cewa "ka kira ni da suna na "
Kara fadada murmushin shi Azim ya yi kafin ya ce " ba zan yi maka kariya AMIR amma ina ji a jiki na ba za ka yi mulki irin na Malik ba , no ! Na ka na musaman ne , da sabon salo zai zowa , na san za ka zama Adalin shugaba , Za ka yi Mulki kamar na MALIK AL SAUD dan mulkin shi har yanzu tarihi ne , ka na da zuciya mai kyau ya shugaba na , ina fatan za ka mulke mu da wannan kyakyawar zuciyar ta ka "


Dan karamin murmushi AMIR ya yi kafin ya ce " yanzu a ce ba na nan "

Da sauri Azim ya ce " ba na fatan hakan AMIR domin duk cikin yaran shi Malik ya fi kaunar ka , wannan kowa ya shaide shi cikin masarautar nan , na san ba zai iya jure rashin ka ba "

Shiru AMIR ya yi na dan mintina kafin ya ce " na gode Azim za ka iya tafiya "
Dan sunkuyar da kai Azim ya yi kafin ya ce " na gode ya shugaba na , Sai da Safe " ya fada kafin ya juya ya fice parlourn

Sai da Amir ya dauki wajen good 30 minutes ya na kallon cikin masarautar , ya na kallon yadda jami'an tsaro ke kai kawo
Kafin ya daga kafa slowly ya juyo ya nufi wannan bakar Jakar da Azim ya ajiye saman Sofa ya dauke ta kafin ya juya ya nufi wani corridor da ke fuskantar sofar

Sai da ya wuce kofa uku sannan ya iso ta hudun ya daura yatsar shi saman finger print
Nan take kofar ta bude kan ta har da fadin sunnan shi
A hankali ya shiga cikin dakin yanzu na sallama kassa kassa
Wani tanpasheshen bedroom ne da ga gani ka san na Malik din ne da kan shi dan dakin ya kai girman parlourn da ya fito

bai tsaya wani dube dube ba ya nufi bedside drawer da ke cen da ga cikin dakin
Ya zauna bakin gadon , ya kai hannu ya bude box na farko
Nan ya ga bandir bandir din kudi dirham shakke a wajen
Jakar hannun shi ya bude ya sa hannu ya fara jidar kudin nan ya na saka wa a cikin jakar nan
Sai da ya debi rabin kudin sannan ya meda box din ya bude na kassa
Nan wajen kuma bandir din Dollar ne , cike a wajen
Nan ma sai da ya debi wajen rabin kudin ya saka a cikin yar jakar nan sannan ya hakura ya meda box din ya like , jakar har ta yi yauni ta cika kamar za ta fashe

Rufe zip din jakar ya yi sannan ya ajiye ta geffen shi kafin ya tashi ya nufi wata door
Ya na isa ta bude kan ta ya shiga ciki
Ya na shiga kofar ta meda ta kan ta

After some minutes ya fito daure da towel a kugunshi allamun wanka ya yi
Ya na fitowa ya nufi wata door ita ma dan nesa kadan da ta toilet
Ya na isa wannan karan ma ta bude kan ta

Bai yi five minutes ba ya fito sanye da wasu kayan barcin farare kal ma su mugun kyau kamar yanzu a ka ciro su da ga cikin leda , ya saki wannan lalawsan Darck black smooth hair din na shi ya zubo mishi har saman shoulder , sai tashin fitinannan kamshi ya ke
( kaiiiii , kudi duniya ne gaskia 🤣 amma na halak 🤣🤣🤣 )

Kai tsaye wannan royal bed ya nufa ya Haye ya konta ya lumshe idanun shi ya na karanto adu'ar barci
Ba jimawa barci ya yi gaba da shi


* MISALIN KARFE 2 NA DARE


Ya na tsaka da barcin shi a hankali ya fara jiyo kamar warin kuna
A dubu dari ya ware idanun shi , nan ya ga uban hayakin da ke tashi cikin bedroom din nan take ya fara tari ya na toshe hancin shi idanun shi su ka koma jazir

Kafin ya yi yunkurin tashi duk hayaki ya gawraye dakin ba ka iya ganin komai
Amma a hakan ya mike ya laluba jakar shi , ya rataya ta , sannan ya sauko da ga saman gadon ya na uban tari dan hayakin ya fara yi mishi yawa ya nufi dressing room ya shigo

Kamar wutar jira ta ke ko , ya na shiga kofar shigowa dakin ta ba da wata razananiyar kara kamar ta watsewar glass , ta fadi kassa , finger print din kuma ya watse nan take wuta ta gawraye bedroom din komai sai da ya kone a ciki
( bari dai mu ga da ga wajen kuma )

Duk mutanan masarautar su na tsaye gaban Building din , dan wajen hawa uku gare shi
Duk hawa ukun sun kama da wuta wajen ya koma jazir
Azim da wasu mutanan biyu su na rike da Malik sai kiran sunan AMIR ya ke ya na a bar shi ya ceci ran yaron shi kar ya mutu

MALIKAT AL'UMU ma haka zalika sai da MALIKAT INAS da MALIKAT DJAOUDATT da MALIKAT HOUDA su ka ririke ta
TESNIM da RIANNA kuma sai kuka su ke yi , su na kiran sunan AMIR
Su na a haka RIANNA ta saki wata razananiyar kara da ga haka ta dauke ta fadi a kassa sumamiya

Da karfi MALIKAT INAS ta kira sunan ta , ta saki MALIKAT AL'UMU ta nufi diyar ta , ta na kiran sunan ta

Ganin abun da ke faruwa ya sa Malik Zubewa kassa saman guyiwowin shi ya dafe kan shi da hannu guda ya na fadin " wai me ya ke shirin faruwa ne haka , Azim me ku ke jira har yanzu ba ku kashe wutar nan ba "

Bai gama rufe bakin shi ba duk glass din ginin su ka tarwatse su na bada wani razanannan sauti su ka fado musu kassa da sauri kowa ya juyo bayan shi wasu har guduwa su ke

Dan zaro idanu ta MALIKAT AL'UMU ta yi ta fadi sunan AMIR da karfi har Muryar ta na sarkewa , ta na gama fadar hakan ta dauke lokaci guda ta na neman zubewa da sauri MALIKAT DJAOUDATT da MALIKAT HOUDA su ka taro ta a tare

Da sauri Malik ya mike tsaye ya na fadin " ku kawo min ruwa tun da ku ba za ku iya kashe wutar nan ba , AMIR di na ya na ciki , NAWFEL ka na ji na , kar ka ji tsoro yanzu na zo na fitar da kai " ya kai karshen hawaye na zubo mishi ya nufi ginin da gudu ya na taka glass din da ya zube a wajen duk kafafun shi su ka fashe

Da gudu Azim da wasu dogarai su ka bi bayan shi su ka taro

Please Login or Register in order to submit comment