Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ka tafi ka fara damu na "
mikewa tsaye ya yi kafin ya riko hannun ta ya dan sunkuyo ya manna mata kiss saman hannun ta ya ce " Sai na dawo Gimbiya ta " ya na gama fadar haka ya saki hannun ta ya mike ya juya ya fara takawa ya fice parlourn ya bar part din

ya na fita ko Inaya ta fito da ga cikin corridor ta na fadin " Aunty RIANNA ba ki ga waya ta ba "

dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta ce " zo zauna ki ji "
ba musu Inaya ta karaso geffen ta ta zauna ta na turo dan bakin nan nata

dafa Shoulder din ta RIANNA ta yi kafin ta ce " my baby kin ga wani haske da ki ka kara , kin yi wani Fresh kamar wadda a ke yi wa barin madara "

turo dan bakin nan nata ta yi kafin ta ce " Aunty minene kuma barin madara "

yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce " idan kin je ki tambayi Amir , yanzu fada min ya ki ka baro min dan uwana , Allah ya sa dai kin kula da shi yadda ya dace "

" Shi dai ya kula da ni " ta fada cikin shagwaba
zaro dan idanun ta RIANNA ta yi kafin ta ce " da gaske ki ke ? to me ya sa ki ka baro shi yanzu ? "
" wajen Momy mu ka zo yin breakfast , shi ne na taho dan na gan ki , ni yanzu Aunty RIANNA ina waya ta pleaseeeee " ta kai karshen ta na marairaice fuska

yar karamar dariya RIANNA ta yi kafin ta ce " Tashi ki je ta na cikin Bedside drawer "
ba ta gama rufe bakin ta ba Inaya ta mike da gudu ta nufi corridor ta shiga

da kallo RIANNA ta raka ta har ta shiga sannan ta ce " oh ni RIANNA yanzu haka Amir ke fama da wannan rawan kan nata "

ta na a haka Inaya ta fito da ga cikin corridor ta na cewa " Aunty RIANNA , ina Nesrine ta shiga ne ? "

" sun tafi Honey moon Ita da mijin ta "

" Aunty ni ma ina son na tafi Honey Moon " ta fada ta na tsayawa gaban RIANNA ta na latsa wayar ta

Dan karamin murmushi RIANNA ta yi kafin ta ce " kar ki damu in sha Allah nan da Next week ni da kai na zan shirya muku Honey moon "

yar karamar dariya Inaya ta mikawa RIANNA wayar ta na cewa " Aunty saka min number din Nesi ina son na kira ta "
hannu RIANNA ta kai ta karbi wayar ta saka mata numbar Nesrine ta yi mata saving sannan ta mika mata wayar
hannu ta kai ta karbi wayar ta murmushi ta ce " Na gode Aunty , ni zan tafi garden " ta fada ta na fara takawa ta nufi hanyar fita parlourn
da sauri RIANNA ta ce mata " amma za ki dawo ko baby ? "

ba tare da ta tsaya ba ta ce " eh zan dawo an jima " ta kai karshen ta na ficewar ta
da kallo RIANNA ta rakata har ta fita sannan ta saki wani dan karamin murmushi ta shiga latsa wayar ta

Inaya kuma kai a sunkuye ta na latsa wayar ta , ta fito Part din MALIKAT INAS
kai tsaye hanyar garden ta nufa ta na tafe ta na sakin murmushi

ta na tsaka da tafiyar ta , ta ji ta bugi mutun har wayar ta , ta fadi
dan karamin kukan shagwaba ta saki ta na dago kai ta ce " dubi don Allah ki yarda min waya ta " ta kai karshen ta na sunkuyawa za ta dauki wayar ta

babu ko tausayi Hafsat ta daga kafa ta take hannun Inaya
wata yar karamar kara ta saki ta na dagowa da karfi ta ture Hafsat da hanayan ta biyu ta fadi kassa kan ta ya bugu cikin wani dutse

wata razananiyar kara Hafsat ta saki kafin dan ba karamar buguwa ta yi ba
Inaya kuma ko a jikin ta sai ma daukar wayar ta da ta yi ta fara takawa ta bar wajen ta nufi garden ta na duba wayar ta

abun kamar an shirya yanzu ma sai ji ta yi ta bugi mutun amma wayar ta ba ta fadi ba
slowly ta dago kai ta kali Rouksar ta ce mata " wai duk kun koma makafi ne ? in kun koma ku fada min na dinga sauya hanya idan na gan ku "

ba karamar fusata Rouksar ta yi ba ta daga hannu za ta wanka ma Inaya mari
cak ta taro hannu ta na kallon ta cikin ido ta ce " Kar ki kuskura ki ce za ki taba ni , wlh wlh sai na lahira ya fi ki jin dadi "

wata yar iskar dariya Rouksar ta yi kafin ta janye hannun ta , ta matso dab da fuskar Inaya har su na iya jiyo nunfashin juna murya kassa kassa ta ce mata " Ki bar ganin ki na karkashin kulawar Amir , ina iya zama mumunar mafarkin ki "

ta na gama fadar haka idanun ta su ka juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi , su ka koma kamar na maciji
sai da na ji gaba ya fadi dan ba karamar razana nayi ba , tunda na ke ban taba ganin irin wannan abun ba kenan ba banza Amir ya ce mata mai idanun maciji ko kuwa ?

abun mamaki kawai sai Inaya ta yi wata yar karamar dariya ta ce " idanun maciji ? Hmmm tsaya na gwada miki nawa "

ta na gama fadar haka ta lumshe idanun ta , ta sake bude su a hankali
Dum Rouksar ta ji zuciyar ta ta buga , ba shiri idanun ta su ka koma kamar da farko ta ja baya kadan ta na kallon Inaya da idanun ta su ka koma baki kirin ko digon fari babu

wani cool murmushi ta saki kafin ta ce " Idan wannan bai miki ba ina da wani "
ta kai karshen ta na lumshe idanun ta yanzu ma ta sake bude su a hankali
sai dai wannan karan Farare tas su ka koma ko digon baki babu

razana iya razana Rouksar kam ta razana dan har wata rawar jiki ta fara yi kamar ta ga mutuwa
( πŸ˜‘πŸ˜‘πŸ˜‘haba ni har fitsari ma sai na yi )

a hankali Inaya ta lumshe idanun ta , ta ja wani dogon nunfashi kafin ta bude idanun ta amma dai yanzu sun koma dai'dai

kallon Rouksar ta yi ta ce " lafiya ki ke rawar jiki haka me ya faru ? "
ta kai karshen ta na juyawa bayan ta kar a je wani abun tsoro ta gani , sai dai kuma ba komai
daga kafadun ta Inaya ta yi kafin ta juya ta ci gaba da tafiyar ta , ta bar Rouksar nan tsaye da allamun sumar tsaye ta yi

Tafiyar ta ta ke cikin konciyar hankali har ta karaso cikin garden , wajen runfar da Tesnim ke yawwan Zama , ta zauna saman sofa ta na latsa wayar ta

ta dauki wajen good ten minutes a haka ta na zaune cikin konciyar hankali
kamar da ga sama ta jiyo Muryar Amir ya na fadin " me ki ke yi tun dazu na ke miki sallama ba ki ji ba ? "

slowly ta dago kan ta ta kale shi ta saki wani cool murmushi ta ce " ni fa abun da na ke yi "

daga mata gera guda ya yi ya na cewa " mu ga ? " ya kai karshen ya na mika mata hannu allamun ta kawo wayar

ba musu ta aza mishi wayar saman hannun shi ta na murmushi
a hankali ya karaso geffen ta ya zauna ya na kallon screen wayar ya ce " me ki ke yi da Snap ? "
" pic zan yi " ta fada mishi cikin shagwaba

a hankali ya mika mata wayar ta , sannan ya kai hannu ya fido wayar shi da ga cikin Aljihun shi ya fara latsawa

su na a haka Azim ya shigo runfar ya na sallama ya Zube gaban Amir ya na gaishe shi cikin girmamawa sannan ya ce " ran ka shi dade a na neman ka a fada "

ba tare da ya dago kan shi ba ya ce " wa ke nema ta ? "

" ranka shi dade Sarkin Bayi ne "

dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " ka ce ba zan iya zuwa inda ya ke ba "
" an gama ranka shi dade " ya na gama fadar haka ya mike ya bar wajen da gudu

ya na barin wajen Inaya ta dago ta kali Amir ta ce " baby yaushe za mu tafi Honey moon ? "

ba tare da ya dago kai ba ya ce mata " Next month , mun tafi "
wani kyawatencen murmushi ta saki kafin ta matso da face din ta ta kai dan bakin nan nata saman kumatun shi ta manna mishi kiss
bai san lokacin da ya lumshe idanun shi ba a hankali kamar mai jin barci dan ba karamin dadi ya ji ba

a hankali ta koma ta sunkuyar da kan ta , ta ci gaba da latsa wayar ta

su na a haka Mohammed ya shigo Runfar ya na sallama Hafsat na bayan shi ta na kuka kamar karamar yarinya kan ta na zubar da jini

slowly Amir ya dago kai ya kale shi , sannan ya saki wani siririn tsaki ya kauda kai gefe ya ce " ba za ku iya ba ni lafiya ba wai " ya fada da larabci

cike da bacin rai Mohammed ya ce " Amir yaushe Yawo cikin masarautar nan ya fara zama hatsari "

" me ka ke nufi " Amir ya fada cikin sanyin murya
" Amir , Hafsat a ka ji ma ciwo duba ka gani ta na zubar da jini " ya kai karshen ya na nuna mishi Hafsat da ke bayan shi

kallon ta ya yi da kyau da ga sama har kassa kafin ya ce " To ku kai ta Asibi mana , ko an fada muku ni doctor ne ? "

" Amir , nazo wajen ka dan a biya mata hakkin ta , ta ya za a ce ta na tafiya haka kawai a ji mata ciwo ba tare da an dauki mataki ba , nan gaba sai mun fara yawo da makami kenan "

dan karamin tsaki Amir ya yi kafin ya ce " Okay wa ya ji mata ciwo "

juyawa Mohammed ya yi ya kali Hafsat ya ce " Hafsat fada mishi wa ya yi miki haka "

gyada mishi kai ta yi a hankali kafin ta dago hannu ta nuna Inaya da ta sunkuyar da kai da dan yatsar ta
[28/09 Γ  09:36] +234 806 127 3970:



❀⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❀


(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




πŸ’”πŸ₯€ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) πŸ’”πŸ₯€





πŸ‘‘β€ MALLAKIN MEERAH β€πŸ‘‘



【THE ROYALTY LOVE πŸ‘‘πŸ•ŠπŸ’–γ€‘




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊγ€‘





【 BOOK …………………… 2 ❀ πŸ‘‘γ€‘





____________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š___________________



PAGE 21 βœπŸ“š






dan zaro idanu Amir ya yi kafin ya juya ya kali Inaya da ke faman latsa wayar ta , ta na sakin murmushi

dan lumshe idanun shi ya yi a hankali kafin ya ce " Ya rahman ! " cikin zuciyar shi sannan ya bude su ya juya ya kali Hafsat ya ce " laifin me ki ka mata da har za ta ji miki ciwo haka ? "

dan zaro idanu Mohammed ya yi ya na kallon Amir
ya na shirin magana kawai ya ga Amir ya kai hannu ya murde kunnen Inaya har sai da ta saki wata yar karamar kara

da hausa ya ce mata " yi min shiru , me yarinyar nan ta yi miki da za ki ji mata ciwo haka , yaushe ki ka koyi fada Cutie "

yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ni fa ban ji mata ciwo ba , ina tafiya kawai na buge ta ban sani ba har waya ta , ta fadi sai da na ba ta hakuri sannan ya duka zan dauki waya ta "

cikin nitsuwa ya katse ta da cewa " to sai ki ji mata ciwo "

girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " A'a da na duka zan dauki waya ta , shi ne ta sa kafa ta take min hannu , ni kuma na ji zafi shi ne na dago na ture ta dan na janye hannu na , duba ka gani har ya yi ja " ta kai karshen ta na mika mishi hannun ta

a hankali ya saki kunnen ta , ya riko hannun ta nan ya ga da ga bayan hannun ta ya yi ja kamar jini na shirin fitowa

bai ce mata komai ba ya dago hannun ya kai saitin bakin shi ya manna mata kiss sannan ya ce " Shikenan , ba ya miki ciwo dai ko ? "

a hankali ta girgiza mishi kai ta na shagwabe fuska ta ce " amma kunne na na yi min ciwo dubi yadda ka murde min shi da zafi haka " ta kai karshen ta na sakin mishi kukan shagwaba ta tashi da sauri ta bar wajen

da kallo ya rakata har sai da ta dan yi nisa kafin ya juyo ya mike tsaye ya tako dab da Mohammed sannan ya juya ya kali Hafsat ya ce " Zan miki kashedi a matsayi Nawfel , ba Amir ba , duk ranar da na kama ki ki na yi wa yarinyar nan ko da kallon banza ne za ki fuskanci fushin Nawfel da kan shi ba na Amir ba "

da sauri Mohammed ya katse shi da cewa " Amir saboda wannan Sakarar yarinyar za ka yi mata irin wannan kashedin "

medo da kallon shi ya yi kan Mohammed ya na kallon shi cikin ido ya ce " ba sakarar yarinya ba , sunan ta Mrs Nawfel , she is my wife , our futur MALIKAT , ka san irin abun da za ka fada dangane da ita nan gaba idan ba haka ba ni da kai na zan kashe ka "
ya na gama fadar haka ya juya ya nufi sofar da ya taso ya dauki wayar Inaya da ta yarda

ya na barin wajen Hafsat ta ce " Daddy ka na fa jin abun da ya ce , ya na nufin yarinyar nan zai aura ? "

juyawa Mohammed ya yi ya girgiza mata kai ya ce " kar ki damu , dadiron shi ce kawai , amma Amir ba shi da wata mata bayan ke , yanzu tafi word room a miki dressing wajen "

dan karamin murmushi ta yi kafin ta ce " shikenan Daddy " ta na gama fadar haka ta juya ita ma ta bar wajen


β–ͺROUKSAR


" wai ke lafiya ki ka kiro ni , ina da aikin yi fa " Damba da ke zaune ya fada
ya na kallon Rouksar da ta bi ta susuce lokaci guda kamar ta fita cikin hayacin ta

ta na a haka Meli ya karaso wajen da sauri sauri , ya Zube gaban Damba ya na gaishe shi cikin girmamawa

bai bi ta kan gaisuwar shi ba ya kali Rouksar ya ce " ga shi ya iso , me ya faru ne "

a hankali ta lumshe idanun ta kafin ta kali Meli ta ce mishi " mike tsaye "
ba musu ya mike tsaye ya na sunkuyar da kai
takowa ta yi ta tsaya dab da shi ta sa hannu ta dago kan shi su na kallon juna cikin ido
nan take idanun ta su ka juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi su ka koma irin na maciji ta na kallon Meli cikin nashi idanun

sai da ta dauki wajen five second ta na kallon cikin idanun kafin ta janye hannun ta ta lumshe idanun ta ta sake bude su , sun koma yadda su ke da farko

juya wa ta yi ta kali Damba ta ce " ka gani ko "
dan karamin tsaki ya ja kafin ya ce " na ga me kuma , ke Medusa kin kirawo ni ne dan ki gwada min sihirin ki ne dama ? "

da sauri ta katse shi da cewa " Damba , ka fi kowa sanin duk wanda ya kali cikin idanun Medusa , statue ya ke komawa kamar dai haka " ta kai karshen ta na kallon Meli da ya yi tsaye waje guda ko motsi baya yi ba ya kifta idanun shi kamar statue

gyada mata kai ya yi kafin ya ce " eh na san da wannan me ya faru don Allah kin bar ni cikin duhu "

" Damba yarinyar nan sai da ta kali tsakiyar ido na amma ba ta koma Statue ba "

a dan razane Damba ya ce mata " no , ba zai yi yu ba "

da sauri ta katse shi da cewa " ni kai na abun ya ba ni mamaki , abun da ya fi ba ni tsoro ma ni shi ne aljanun da ke cikin ta , karfin tsafin su ya wuce namu baki daya Damba , Fararen Aljanu ne a cikin ta , kuma ka sani duk iya tsafin mu Fararen aljanu sun dame shi sun sanye "

a hankali ya mike tsaye ya na girgiza mata kai ya ce " a'a ba zai yi yu ba , wani abun ne dai daban ki ka gani Rouksar , amma irin wadanan Aljanun babu su Tun bayan karni na 970 , babu yadda za a yi yarinyar nan ta malake su "

kamar za ta yi kuka ta ce mishi " Damba , ba karya na ke maka tabass yarinyar fararen aljanu ne da ita , idan har mu ka bari ta yi tarraya da wani to fa kashin mu ya bushe dan da kallo ma kadai za ta iya kashe mu "

" mu kashe ta kafin ta fara kashe mu , wai har yanzu dafin macizan ki bai dawo dai'dai ba , ta wannan hanyar ce kadai za mu iya kashe ta tare da aljanun nata "

girgiza mishi kai ta yi kafin ta ce " ina ga sai mun zubar da jini "
" to me ki ke jira , ki zubar mana "
" Damba , ba fa jinin dabobi ba na ke nufi , jinin mutum , mutanan ma sai Mata wanda ba su fara period ba , ko kuma wanda su ka Kamala period , ba zan iya shan jinin macen da ta ke al'ada "

wani irin kukan zaki ne ya yi mara dadin ji kafin ya juya ya kai wa bishiyar bayan shi wani mugun naushi har sai da ta girgiza

juyowa ya yi ya kali Rouksar ya ce " ba zai yi yu ba shirin da na dauki tsawan shekara dari ina shirya shi ba ya baci lokaci guda saboda wannan yarinyar , tsaya ma ni wai ina Amir ya samo yarinyar nan "

" ni babban abun da na ke gudu kar Amir ya ce ya na son yarinyar nan ya aure ta , dan na ga kwana biyu su na yawwan zama a tare kamar massoya "

girgiza mata kai ya yi kafin ya ce " no , ki yi duk yadda za ki yi ki kashe yarinyar nan , ko kuma ki raba ta da Amir , in har ya ce zai aure ta , duk lokacin da ya yi tarraya da ita da ga lokacin ba za na iya yin komai a kan shi , dan aljanun ta za su kare shi ko da kuwa mutuwa ta tunkaro shi , dole mu fara kashe yarinyar nan tun kafin lokaci ya kure mana "

" Whl yarinyar nan ta fara ba ni tsoro , ban yi tunanin haka za ta kasance ba , da tun ranar da na gan ta zan kashe ta kowa ya huta "

dan karamin tsaki ya ja ya na kauda kan shi gefe ya ce " yanzu mata nawa ki ke bukata , ba na son aikin nan ya wuce Next week "

" Mata Goma , kuma ku tabbatar kun ba su dafin macizai biyar ma su hatsari sun sha ta haka ne kawai poison di na zai kashe yarinyar nan tare da aljanun ta "

gyada mata kai kawai ya yi kafin ya koma ya zauna ya nuna mata Meli da ke tsaye Statue ya ce mata " kar ki manta ki sake min shi , ko ba komai zai yi mana anfani nan gaba " ya na gama fadar haka ya bace bat a wajen

ya na bacewa Rouksar ta koma gaban Meli dab ta tsaya , ta kai bakin ta saman lips din shi ta yi mishi kiss kafin ta juya ta bace bat ita ma

ta na bacewa ko , Meli ya ja wani dogon nunfashi har wani tasowa kirjin shi ya yi kafin ya koma ya dafe saitin zuciyar shi ya na karanto kalmar shahada
sai faman muzurai ya ke ya na bin wajen da kallo ya ga shi kadai ne , da gudu ya juya shi ma ya bar wajen ya koma bakin aikin shi



β–ͺINAYA



konce ta ke saman bed din ta a part din MALIKAT INAS , ta yi Rub da ciki ta na kuka kassa kassa ta cire Alkyabar jikin ta ta tila ta nan bakin gadon
sneakers din ta ma ta cire su ta yi watsi da su cikin dakin

ta na a haka Amir ya turo kofar ya na sallama cen kassan makoshi
bai ce mata komai ya karaso cikin dakin ya sunkuya ya dauki Alkyabar ta ya ajiye saman bedside drawer sannan ya zauna bakin gadon ya kai hannu saman bayan ta ya na cewa " Cutie , ba dai kuka ki ke ba "

ba ta ce mishi komai ba ta ci gaba da kukan ta kassa kassa
a hankali ya janye hannun shi shi ma bai ce mata komai ba ya Haye saman bayan ta ya konta
da sauri ta ce mishi " yaya Zayd don Allah ka tashi wlh da zafi "
" ba ina miki magana ba kin kyale ni " ya rada mata a kunne

kara sautin kukan ta ta yi ta na cewa " don Allah ka tashi "
ba musu ya tashi a hankali ya sauka da ga saman ta ya koma gefe ya zauna ya kai hannu ya juya ta
sai da ya ji gaban shi ya fadi , fuskar ta duk ta yi jaga jaga da hawaye wasu na bin wasu har da majina

a rude ya ce mata " Cutie lafiya ki ke irin wannan kukan , ba dan na ja miki kunne ba , I'm sorry ni fa wassa ne kawai na ke miki "

komai ba ta ce mishi ba ta ci gaba da kukan ta cikin fitar hayaci
bawan Allah duk ya bi ya

Please Login or Register in order to submit comment