Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fara bincike a kan abun da ya faru , ina son ka kamo ko wanene ya yi harbin nan "

dan sunkuyar da kai Amir ya yi kafin ya ce " an gama ran ka shi dade , in sha Allah bayan jana'izar Malik za mu fara bincike a kai "

gyada kan shi kawai Amir ya yi ba tare da ya ce komai ba
A hankali General ya juya har ya yi taku hudu ya tsaya ya juyo a hankali ya ce " ran ka shi dade mu je ko ? "

ba tare da ya juyo ba ya ce " Za ka iya tafiya "
tsaya wa General ya yi ya kale shi ba dan lokaci kafin ya juya ya ficewar shi
ya na barin wajen Amir ya fara takawa ya nufi corridor ya shige abun shi

a haka a ka jana'izar Malik , a ka yi mishi wanka a ka kai shi gidan shi na karshe , duk wani Na cikin masarautar idan ya rasu akwai cemetery a bayan masarautar nan a ke bisine shi , haka zalika shi ma Malik
amma abun mamaki Ko hanyar Amir bai leko ba , kowa sai dai ya halarta ban da Amir

bayan Jana'izar Malik , Duk wani wanda ke cikin Fada sai da ya nufi part din Amir dan jin dalilin da ya hana shi zuwa
Amma tun da ga floor na farko a ka tsaida su , da cewa Amir ya ce kar a bar kowa ya shigo ko da MALIKAT AL'UMU ce da kan ta
😭😭😭DAMA HAKAN YA KE GUDU , GA SHI KUMA SUN RABA SHI DA MAHAIFINSHI , DOLE YA CE BA YA SON GANIN KOWA , 😭😭 NI YANZU TAMBAYAR ITA CE WA YA YI WA MALIK WANNAN AIKIN , DUK YADDA A KA YI WANDA YA YI HAKAN YA NA SANE DA TAFIYAR SU MALIK MAKKAH , DA KUMA RANAR DAWOWAR SU , DAN DA GA GANI MUTUWAR MALIK A SHIRYE TA KE TUN KAFIN SU TAFI 😭😭✌ NI DAI NA TAFI NA YI RARRASHIN AMIR DIN MU


[21/09 Γ  19:00] +234 913 527 7685:





❀⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❀


(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




πŸ’”πŸ₯€ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) πŸ’”πŸ₯€





πŸ‘‘β€ MALLAKIN MEERAH β€πŸ‘‘



【THE ROYALTY LOVE πŸ‘‘πŸ•ŠπŸ’–γ€‘




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊγ€‘





【 BOOK …………………… 2 ❀ πŸ‘‘γ€‘





____________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š___________________




PAGE 14 βœπŸ“š





bangaran Amir kuwa ya na shiga kai tsaye bedroom din shi ya wuce ya shiga Toilet ya yi Wanka ya yo Alwalla sannan ya fito ya wuce dressing room

jim kadan ya fito sanye da wata Jallabiya Fara kal mai mugun kyau ya sako wannan Smooth hair din na shi , yanzu tsawon shi ya fi na farko , ya zubo mishi saman shoulder har zuwa kirji , sai tashin kamshi ya ke yi

ya na fitowa kai tsaye ya nufi daddumar shi ya tada Sallat , ko da ya Kamala bai tashi da ga saman daddumar ba , sai da ya zauna ya dinga jero wa Malik aduo'i , sannan ya dauki alwashin ba zai zubar da kwalla daya ba har sai ya ga bayan wanda ya kashe mishi mahaifin shi , kuma ya san dole a cikin masarautar ya ke amma ba zai iya fadin wanene ba


β–ͺINAYA


bayan ta koma bedroom din ta , kai tsaye ta haye bed din ta , ko minti biyu ba ta yi ba , barci ya yi gaba da ita

ba ta farka ba , sai Wajen sallar magriba , ko da ta tashi , ta shiga toilet ta yi wanka ta yi Alwalla sannan ta fito ta shiga dressing room
jim kadan ta fito sanye da wata dankareriar Abaya Fara kal mai mugun kyau , ta yi Rowling veil din ta a kai sai tashin kamshi ta ke kamar wanda ta fito da ga cikin kwalbar perfume

ta na fitowa kai tsaye ta nufi daddumar ta , ta fara gabatar da sallar ta
ko da ta Kamala ba ta tashi ba , sai da ta tsaya karatun kur'ani har lokacin sallar isha ya zagayo ta tashi ta gabatar da ita

bayan ta Kamala ta tashi ta fito dakin
ko da shigo corridor ta tardo RIANNA zaune saman carpet ta kontar da kan ta saman Cinyar MALIKAT INAS da ke zaune saman Sofa ta jingina bayan ta a jikin sofar ta daga kai ta kurewa waje guda ido
ga busashun hawaye nan konce saman face din su baki daya

karasowa wajen Inaya ta yi ta na fadin " Aunty RIANNA me ya faru da ke haka ? " ta fada dai'dai lokacin da ta ke zama gaban ta saman carpet ita ma

a hankali RIANNA ta dago kan ta , ta riko hannun Inaya ta ce " Baby tashi ki je wajen mijin ki , zai bukaci kulawar ki a wannan lokacin , ki tsaya ki kula da shi yadda ya dace , na san yanzu ya na cikin damuwa , ganin ki zai sa ya rage radadin da ya ke ji kin ji ko ? "

gyada mata kai Inaya ta yi ta na fadin " shikenan Aunty RIANNA , amma ba ki fada min abun da ke damun ki ba , ga hawaye nan konce saman fuskar ki , Ammie ku ma ga hawaye nan saman Fuskar ku " ta fada ta na dawo da kallon ta kan MALIKAT INAS

sai a lokacin MALIKAT INAS ta dawo cikin hayacin ta , a hankali ta juyo ta kali Inaya cikin disashashiyar Muryar ta , ta ce " ba komai baby , tashi ki je wajen Mijin ki , ya fi bukatar ki fiye da mu "

da to Inaya ta amsa musu sannan ta tashi ta nufi kofar fita parlourn zuciyar duk ba dadi ganin yanayin da su RIANNA ke ciki

a haka ta fito part din ta nufi Building din Amir , duk da so guda ta taba tafiya , amma ta san hanya ta kuma san yadda za ta yi ta shiga

abun mamaki kuma ta na zuwa guards din da ke tsarin wajen ko tare ta ba su yi ba
a haka ta shiga building din , kai tsaye ta shiga lift ta nufi floor na uku zuciyar ta na duka uku uku

bakin ta dauke da sallama ta shigo parlourn
nan ta tardo Rouksar , Aysher da Hafsat duk tsaye cikin parlour , Azim ya tare musu hanyar shiga corridor

A hankali Inaya ta karaso wajen ta tsaya ta na bin su da kallo ta na so ta tambayi abun da ke faruwa amma sam ba su ba ta fuska ba
asali ma kowa ce sai kallon wulakanci ke yi wa Inaya

kallon Azim ta yi ta ce " Uncle , yaya Zayd ya na nan ? "
dan karamin murmushi Azim ya yi kafin ya gyada mata kai ya ba ta hanya Sannan ya fada mata a wane bedroom za ta same shi
a hankali ta daga kafa ta wuce ta na tafiya kamar wadda a ka zarewa lakar jiki

Aysher na ganin Inaya ta wuce ta sa hannayan ta dukka biyu ta ture Azim gefe ta na fadin " fin mu ta yi da za ka ba ta hanya ta wuce , ba abun da zai hana ni ganin Amir " ta fada ta na wucewa
da sauri Rouksar da Hafsat su ka bi bayan ta har su ka kamo Inaya su ka wuce ta , su ka nufi Bedroom din Amir

babu ko Sallama su ka fado mishi a tare

Amir kuwa ya na konce bakin gadon shi , ya sauko da kafafun shi kassa
da sauri Rouksar ta karaso tsakiyar dakin ta marairaice murya ta ce " Akhie ! "

slowly ya bude idanun shi ya mike zaune ya dan lumshe idanun shi kadan kamar mai maye , ga gashin nan na shi ya zubo mishi har saman kirji , dukkan su sai da su ka hadiye yawu ba karamin kyau ya yi musu ba

har Rouksar ta bude baki za ta yi magana ya daga mata hannu allamun ta yi shiru
ba musu ko ta yi shiru ta tsaya ta na kallon shi , ta na kara yabawa kyawo irin na Amir , ni ta ke kamar ta hadiye shi

a hankali ya yi kassa da hannun shi dai'dai lokacin da Inaya ta shigo cikin dakin ta na sallama da wannan siririyar murya ta ta

ya na jin muryar ta ya ji wani mugun sanyi lokaci guda , har sai da ya dan lumshe idanun shi ya sake bude su a hankali kafin ya juya ya kale ta , ta na ganin ya kale ta , ta sakin mishi wani cool murmushi cike da shauΖ™i

ya na juyawa ko Azim shi ma ya shigo cikin dakin da sauri , ya na yin karo da idanun ya sha jinin jikin shi

tun kafin ya yi magana Amir ya riga shi cewa " Me na fada maka ? " ya fada cikin wata murya cen kassan makoshi kamar an busa sarewa dan dadi ,
har sai da Rouksar ta dan lumshe idanun ta a hankali cikin zuciyar ta ta na fadin " Masha Allah , ya Allah na roke ka , ka sa ya zama nawa " ta kai karshen ta na bude idanun ta

jikin Azim har kerma ya fara yi , ya na fadin " ina neman Afuwa ran ka shi dade wlh sun matsa ne sai s...."

cikin nitsuwa Amir ya katse shi da cewa " ku fita ku ban waje ba na son ganin kowa " ya kai karshen ya na sunkuyar da kan shi

Inaya na jin abun da ya fada ta dan sunkuyar da kai ta juya za ta fice
kamar da ga sama ta jiyo Muryar shi ya na fadin " Cutie ban da ke " ya fada da hausa dan ya san ita kadai ke jin hausa

wani cool murmushi ta saki kafin ta juyo ta tako a hankali ta karaso geffen Rouksar ta tsaya ta na kallon shi

ta na tsayawa Azim ya ce ma su Hafsat su fita , ba musu su ka juya su ka fice kowace ta na cika ta na batsewa
riko hannun Inaya Rouksar ta yi , ta na fadin " wuce mu tafi ke kuma ya ce ba ya son ganin kowa "

ba ta kai ga rufe bakin ta ba ta jiyo Muryar shi ya na fadin " sake hannun ta ki fice min da ga nan "

dan zaro idanu Rouksar ta yi ta na sakin baki har da cewa " Amir kai fa ka ce ba ka son ganin k....."

a dubu dari ya dago kai ya daka mata wata gigitaciyar tsawa ya na fadin " I say get out , Azim duk wanda ya sake shigowa ko da parlour ne sai na Ι—aure ka da kai na "
nan take idanun shi su ka koma jazir , duk jiyojin jikin shi sai da su ka fito baro baro

ba shiri Rouksar ta saki hannun Inaya ta juya da gudu ta bar Bedroom din Azim na biye da bayan ta da gudu dan shi kan shi ya ji tsoron irin wannan tsawar da Amir

Rouksar kuma ta na baro wajen kai tsaye lift ta nufa ta shiga
kofar lift din na rufewa ta bace bat a cikin lift din

Amir kuwa ya na ganin sun bar wajen , ya kai hannu wajen bedside drawer ya dauki wata remote ya danna wasu button sannan ya ajiye ta
ya na ajiye ta , kofar dakin ta koma da kan ta ta rufe kan ta , ta saka security

sai da ya kofar ta rufe sannan ya juyo ya kali Inaya da ta yi sumar tsaye tun lokacin da ya yi tsawar nan

daga mata gera guda ya yi allamun minene ?
a hankali ta gyada mishi kai allamun ba komai ba tare da ta ce komai ba

ya na ganin hakan ya dan sunkuyar da kan shi ya dafe shi da hannu guda ya lumshe idanun shi

dan lumshe idanun ta ita ma ta yi a hankali ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bude su
a hankali ta fara takawa , ta karaso bakin gadon ta cire flat shoes din ta ta haye gadon
ta koma bayan shi ta yi kneel down , sannan ta kai hannayan ta a hankali bayan wuyan shi ta fara yi mishi Taussa dan a tunanin gajiya ce kawai ya ke fama da ita

kamar ko ta san ya na da bukatar hakan , a hankali ya fara dago da kan shi ya gyara zaman shi , ta na ci gaba da yi mishi taussar har wata ajiyar zuciya ya sauke

ta na jin ya sauke ajiyar zuciya ta saki wani dan karamin murmushi mai sauti sannan ta zagayo da hannayan ta , ta rungume shi ta baya ta kontar da kan ta saman shoulder din shi cikin shagwaba ta na fadin " baby na yi kewar ka sosai fa , shi ne ka dawo ko nema ta ba ka yi ba , ba ka yi kewa ta ba kenan "

a hankali ya sa hannayan shi ya cire nata ya juyo ya kale ta ya ce " na yi miki kama da baby ? "

turo dan bakin nan nata ta yi ta sunkuyar da kai ta riko gudan hannun Abayar ta , cike da shagwaba ta ce " ni fa ba wancen babyn ba na ke nufi , dama Aunty RIANNA ce ta ce na daina kiran ka da yaya Zayd , wai na dinga kiran ka da Baby ko sweetheart , shi ne kawai na yi " ta kai karshen ta na gyara zaman ta saman gadon ta kauda kai gefe

shi kan shi bai san abun da ya ke ji cikin zuciyar shi ba , kawai sai ya tsaya ya na kallon ta
slowly ta juyo ta kaleshi ta ce " yawwa Baby , ka san abun da ke damun Aunty RIANNA da Ammie , na ga har kuka su ka yi da na tambaye su me ya faru shi ne su ka ce min wai na taho wajen ka " ta kai karshen ta na hura kumatu ta da iska

slowly ya juya da kan shi , cen kassan makoshi ya ce mata " kar ki damu ba komai "

daga kafadun ta ta yi kafin ta mike saman guyiwowin ta , ta dawo bayan shi ta tsaya ta sa hannu ta tataro gashin kan shi dukka ta riko cikin hannun ta , ta na fadin " laaaa Baby wannan dukka gashin ka ne , Har ma ya fi nawa yawa " ta kai karshen ta na yar karamar dariya da ga haka ta Ι—aure mishi gashin a baya

sannan ta konto da kan ta saman shoulder din shi ta ce " amma baby ka sha azumi ko ? , dubi har wata kiba ka yi "

slowly ya juyo da kan shi ya kale ta , sai murmushi ta ke saki ya ce " ba ki sha Azumi ko guda ba ke ma , amma kin yi kiba , to ni ma ban sha ko guda ba , kawai dan kin yi kwana biyu ba ki gan ni ba ne " ya kai karshen ya na juya kan shi

yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " wa ya ce maka ban sha Azumi ko guda ba , har guda hudu na sha "

Ba tare da ya juyo ba ya ce " uhm , me ya sa , kuma Ammie na ganin ki ba ta ce komai ba ? za ta bari ki sha har azumi Hudu , ki shirya to gobe za ki fara ramuwar su "

shagwabe fuska ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce " yo ai ba laifi na ba ne , Aunty RIANNA ta ce wai idan mace na period ko ta yi Azumi ba ya ciki har sai ta Kamala "

a dubu dari Amir ya juyo ya kale ta ya na zaro idanu ya ce " Period ki ka fara ? "

a hankali ta gyada mishi kai ta na marairaice fuska ta ce " amma Baby da zafi , sai da Aunty RIANNA ta dinga ba ni maganin rage ciwon , sai da na ji kamar zan mutu " ta kai karshen kamar za ta yi kuka ta janye kan ta da ga saman shoulder din shi , ta koma tsakiyar gadon ta zauna ta yi irin zaman cin tuwo ta sunkuyar da kai ta na turo dan bakin nan nata

tsaya wa ya yi ya na bin ta da kallo , shi ya sa tun lokacin da ya sauke idanu saman ta ya ji duk ta sauya mishi , ashe babyn shi girma ya yi ba ya nan , ya so a ce lokacin da za ta fara period ya na tare da ita , ya bata kulawar da ta dace da ita

har ya bude bakin shi zai magana wayar shi da ke saman bedside drawer ta fara Ringing
dan lumshe idanun shi kadan ya yi kafin ya juya ya kai hannu ya dauki wayar , ya dauki kiran ya kai wayar a kunne ya na sallama cen kassan makoshi

a daya bangaran kuma amsa mishi sallamar shi Diya ya yi kafin ya ce " Amir ga mu nan ni da Aymane za mu shigo part din ka , amma sun hana mu shiga "

" Kai shi wajen RIANNA , Idan na bukaci ganin ka , zan kira ka " ya na gama fadar haka ya katse kiran , ya kashe wayar baki daya sannan ya ajiye saman bedside drawer , dan a yanzu dai ba ya da lokacin kowa sai na babyn shi

ya na ajiye wayar shi , ya juya ya kontar da kan shi saman cinyoyin ta , sannan ya ida Hayewa bed din ya lumshe idanun shi

yar karamar dariya ta yi kafin ta kai hannu ta fara shafa kan shi ta na fadin " baby ina ganin kamar akwai abun da ke damun ka haka ne ko ? " ta tambaye shi cikin shakku

girgiza mata kai ya yi ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " ba na da wata damuwa duk lokacin da ki ke tare da ni "

wani kyawatencen murmushi ta saki , kafin ta dan sunkuyo da kan ta , ta kai bakin shi saitin forehead din shi ta manna mishi kiss ta na fadin " Ina son ka sosai da sosai , ka sani ko , ya na yi kewar ka sosai , kullum in na yi sallat sai na roki Allah ya dawo min da kai cikin koshin lafya , yadda za mu tafi shan ice cream " ta kai karshen ta na yar karamar dariya

" ba sai mun tafi ba Ice cream din za ta tardo ki inda ki ke " ya fada cikin zuciyar shi ya na kara samun nitsuwa cikin zuciyar shi , ya ji dadi da MALIKAT INAS ta ce ta taho wajen shi , ba kariya ya na bukatar ta a kusa da shi fiye da komai a yanzu , Sautin muryar ta kadai ya isa ya share duk wata damuwar da ke cikin zuciyar shi

a hankali ta sunkuyo da kan ta saitin kunnen shi ta rada mishi wani abu kafin ta dago ta na kallon shi ta ce " haka nan ne ko ? "

slowly ya bude idanun shi ya na kallon ta ya gyada mata kai a hankali allamun eh
yar karamar dariya ta yi , ta na shirin magana ta ga ya mike zaune ya sauko da kafafun shi kassa ya mike tsaye ya ce mata " jira ni ina zuwa " ya na gama fadar haka ya fara takawa ya nufi toilet ya shiga ya rufo kofar

da kallo ta raka shi har sai da ya shiga toilet sannan ta juya ta jingina bayan ta a jikin forehead din gadon ta mike kafafun ta , sannan ta kai hannu ta dauko wayar shi saman bedside drawer , ta kunna ta , ta shiga neman game ta fara yi

ta dauki wajen Good 30 minutes a haka kafin Amir ya fito ya nufi dressing room ko sani ba ta yi ba
jim kadan ta fara jiyo wani qamshi mai mugun dadi dai lokacin da Amir ya fito da ga cikin Dressing room sanye da kayan barcin shi farare kal ma su mugun laushi kamar auduga

tun da ya fito ta tsare shi da idanu ba karamin kyau ya yi mata ba , har sai da ya karaso bakin gadon ya Haye shi ma ya zauna su na fuskantar juna ya kai hannu ya kwace wayar shi ya sake kashe ta sannan ya ce " Ba ki jin barci ne ? "

girgiza mishi kai ta yi cikin zolaya ta ce mishi " hira na ke da saurayi na "
daga mata gera guda ya yi ya na fadin " ina ya ke saurayin ? "
" ga shi nan a gaba na " ta fada ta na kashe mishi ido guda
maganar ta ba karamar dariya ta so ta ba shi ba , amma sai ya shanye ya bar kayan shi a zuciya

dan matso da face din ta ta yi kusan ta shi ta na kallon cikin idanun shi ta ce " baby lafiya ka na min irin wannan kallon ? kar ka cinye ni "
[22/09 Γ  11:13] MEERAH πŸͺ·πŸ©·:




❀⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❀


(LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯




πŸ’”πŸ₯€ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) πŸ’”πŸ₯€





πŸ‘‘β€ MALLAKIN MEERAH β€πŸ‘‘



【THE ROYALTY LOVE πŸ‘‘πŸ•ŠπŸ’–γ€‘




Marubuciyar littafin

【TAURIN ZUCIYA πŸ’–πŸ’πŸŒΊγ€‘





【 BOOK …………………… 2 ❀ πŸ‘‘γ€‘





____________________πŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•ŠπŸ•Š___________________





PAGE 15 βœπŸ“š






Bai ce mata komai ba , ya sa hannu ya warware veil din ta , ya kai shi wajen face din shi ya shaki qamshin turaren ta , nan take ya ji duk wata sigar jikin shi ta mike nan take wata muguwar Sha'awar ta , ta shigo shi

a hankali ya kai veil ya ajiye saman bedside drawer ya na fadin " ba ki jin zafi da wannan abun a kai "
girgiza mishi kai ta yi allamun a'a

dawo da kallon shi ya yi gare ta ya ce " matso ki ji "
ba musu ta matso da face din ta , saitin tashi ta na murmushi
a hankali ya lumshe idanun shi kamar mai jin barci , sannan ya sake bude su a kan ta kafin ya matso da face dinshi shi ma har hancin su na gogar na juna , a hankali ya kai bakin shi saman nata ya mata manna mata kiss kafin ya cabko lips din ta na kassa ya fara tsotsaya kamar ya samu

Please Login or Register in order to submit comment