Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya kaimu washe gari........


Rayuwa ta mik'awa KHUBRA cikin wannan gida,wanda iya wannan lokacin babu wani abu dake shiga tsakaninta da y'ay'an gidan,ta kame kanta had'e da rik'e matsayinta na y'ar takala,duk wani aikinta tana gama shi take barin cikinsu ta koma guarding tai zamanta,mafi yawancin lokaci nan ne gurin da ke d'ebe mata kewa,musamman idan ta tuna ABBANTA ko MAMANTA da bata tashi tayi rayuwa da ita ba...

Cikin sauri² ta fito zata shiga cikin gidan,karo suka kusa yi da ZAHRA,da saurinta kuma ta tsaya tana kallonta duk sai murna take uwa wacce akama wata gagarumar kyauta,kallonta ta tsaya yi...
Da sauri ZAHRA ta rik'eta tana jan hannunta suka nufi kitchen,aikinta ta fara suna ta hira,duka yau tana kula da yanayin ZAHRA wani murna take tayi ita kuma tak'i tambayan dalilin,suna ta aikin su,can ZAHRA ta d'ago tana kallon KHUBRA...
''Wai kam sis kin san wani abu?''
Kai kad'ai ta kad'a mata kafin ta bud'e baki tayi magana ZAHRA ta katse ta da fad 'in
''Cikin month ennan YAYANMU zai dawo fa''
''Eeyyahh!Allah dawo da shi lafiya,yasa ya samo abunda yaje nema''
''Ameen dear,aiko zai sha labarinki duk ranan da mukayi waya''
Ita dai KHUBRA bata sake magana ba,ta ci gaba da aikinta,ZAHRA kuwa nan taita bata labarin YAYAN nasu,wanda har zuwa yau bata tab'a tsintar sunansa ba..

Har suka kammala,ZAHRA nata mata surutu,ita ko sai dai tayi murmushi yanayin yanda suke rayuwa da yadda ZAHRA take bata labarin irin rayuwarsu abun sosai yake bata sha'awa,har wani lokaci ma ta kanji inama itama tana da d'an uwa,duk lokacin da ta tuna haka takan yi kuka sosai...

*SOME WEEKS LEAP.*

Da sanyin safiya ta tashi,bata b'ata lokaci ba ta shiga kitchen,tunanin irin girkin da za tayi ta hau yi,dan kam tun jiya HAJIYA MURJA ta sanar da ita suna da babban bak'o,saboda haka tana son tayi girke² kaloli da yawa had'e da drinks na gargajiya,coz ta san bak'on baya son tamalli da kayan gwangwani...

Tana cikin tunanintan ZAHRA ta shigo da saurinta,sis bafa muga ta zama ba,kinga tunda ke kad'aice barin fasa binsu airport,muyi abunda ya kamata,nan ko suka hau aiki ba ji bare gani,suna yi suna hiransu...

Tsawon awanni da dama suna ta aikin kafin suka kammala,ficewa suka yi bayan sun gama shirya table kafin kowa ya kama hanyarsa...

*SOME HOURS LATER...*

Wani bak'in PRADO ne ya Parker a haraban gidan,cikin k'asaita aka bud'e k'ofan ko kafin ya bud'e ya fito sai da ya d'auki lokaci kafin ya ziro k'afarsa ya fito,cikin k'ana nan kaya wanda suka matuk'ar amsarsa uwa bature,gashinsa ya d'an yi tudu ta gaba sai shek'i yake da gani kasan yana shan gyara,idanunsa saye cikin sunglasses bak'i na GUCCI,komai yayi kyau yake masa,cikin takun k'asaita ya soma tafiya,har cikin parlor da ya sha gyara.A baya suka bishi har cikin parlorn sai rawar kai ASHNA da FATAHIYYA suke zubawa,shi kam yana gaba bai ko kula ta kansu ba,a zaune suka tarar da HAJIYAN sai wani dare baki take tana dariya had'e da fad'in
''Oyoyo my son''

Fuskarsa d'auke da murmushi da ya dad'a k'awatar da ita,ya amsa yana zama cikin sofa..
Cike da ladabi uwa ba wanda ya fito daga k'asar turawaba ya gaidata,tana amsawa fuskarta da fara'a wacce ban tab'a zaton tana da ita ba...

'Dakinsa ya nufa cike da gajiya,yana shiga wani sanyayyen k'amshi ya doki hancinsa,take kowace gab'a ta jikinsa ta amsa,jinsa yake uwa an masa duka,da k'yar ya k'arasa kan bed,aiko ya zube saman bed yana dad'a shak'an k'amshin turaren kasala na dad'a saukar masa a jiki,jin abun zai masa yawa yasa ya mik'e da k'yar ya iya nufar toilet,ya jima ciki kafin ya fito,ko minti biyar bai ba ya shirya cikin singlet fari da boxer,ai ko ya haye saman bed take baccin gajiya ya kwashe shi...

Tun bayan da suka gama aikin suka k'ule a guarding sai fira suke suna dariya abunsu uwa ya da k'anwa duk da baza su wuce sa'annin juna ba...
Sam basu ji shigowar motor ensu ASHNA ba,sai shewansu suke KHUBRA na bata labarin k'auyensu,ita ko ZAHRA sai kwasar dariya take...

Three hours ya d'auka yana baccin gajiya kafin ya farka,jin cikinsa fayau yasa cikin sauri² ya sake watsawa jikinsa ruwa,jallabiyya ya zura,sai da yayi sallah sannan ya fito,suna zaune cikin parlorn su HANEEF duk sun cika gurin da hayaniya,ganin fitowansa yasa take suka shiga hankalinsu ba tare da ya furta ko a ba,k'ala bai ceba amma gaba d'ayansu kowa ya k'ame kamar doll...

''MAMA ni kam ina Sis ena?''
Tab'e baki tayi kafin cikin b'acin rai ta iya furta
''Tana can tare da wannan shashashar yarinyar''

''Wace wannan kuma?''
Yayi maganar yana yamutsa fuska...

Saboda tasan halinsa na rashin son magana yasa tace
''Wata ce''
Daga haka ko ta bar maganar ba tare da ta sake furta komai ba ta ja bakinta tayi shiru...

*******
''Laaa!sis kinga lokaci ya tafi nasanma yanzu haka BB ya dawo,taso muje dan Allah''

''A'a y'ar uwa ki je yanzun zan biyoki daga baya ''

''Ba wani nan nasan ba zuwa za kiyi ba''

Murmushi kad'ai tayi,ita kuma tayi saurin barin gurin tana fad'in

''Sai na ganki duk da ba yarda nayi akan za kizo ba''
Tana tafe da d'an gudunta ta shiga parlorn,idanunta na sauka kansa ta fasa wani ihu da gudu kuma ta fad'a jikinsa....

Jin an fad'o jikinsa yasa ya kalleta,sai murmushi take dokawa,shi ko ya had'e fuska yana fad'in
''Matsamin a nan,ai ke kam fushi nake da ke''

''Wayyoo YAYANAH dan Allah kayi sorry kar kayi fushi da ni,kasan duk duniya bana k'aunar naga kayi fushi da ni,ko so kake nayi kuka?''
Ta fad'a tana narke fuska za ta masa kuka

''Haba mana sis ina kika b'oye?ko kije tarona kuma na dawoma ban saki a idona ba why?''

''Ammm!YAYANAH Allah ko aiki mukayi shi yasa kaga banje taroka ba,kaima kasan ba haka kad'ai zan k'i zuwa ba,aiiii dai ka hak'ura ko?''
Tana d'an murmushi had'e da lek'en fuskansa da ya kawar da ita gefe...

Murmushin shima yayi mata,yana kad'a mata kai...

''Yeeehhhh!thnks BB na''

''Laaa!YAYANAH taso kaga abunda muka maka''
Ta kama hannunsa tana jaa zuwa dinning,a hankali ya bita har gurin tarin warmers en ya kallah yana tab'e baki,yasan dai wannan kam sai dai ko idan y'an aiki suka yi amma ba MAMAN ba bare kuma wad'ancan sangartattun biyu...

''Nikam sis kyale ni da wannan shirman masu aikin''

''Laaaa!YAYA fa mu mukayi,zauna kaga Allah yayi sweet sosai,kuma favourite naka mukayi''

Ta jaa masa kujeran tana turashi har sai da ya zauna,shi sam baya jin zai tab'a iya cin abincin masu aiki duk k'azamai dasu su maka wani abinci kuma mutum ya ci,k'amshin da ya ziyarceshi shi ya dakatar da shi daga maganar da yake yabi warmers en da kallo...
Drink en da take tsiyayawa a cup shi yabi da kallo sai k'amshi yake,murmushi yayi mata ganin yadda take ta rawar k'afa a kansa ya juya parlor ya kallesu duk sun zuba musu ido suna jiran ganin abunda zai faru,juyowa yayi ya sake kallonta yanda take masa yasa ya k'udirce a ransa ba zai bata kunya ba,ko da zai ci ya haras da shi zai gwada...

Cup en da ta cika da sob'o ta mik'a masa tana fad'in
''YAH bismillah!''

Karb'a yayi ya d'an d'osana cup en a bakinsa har da runtse ido,duk da yadda yake k'amshi bai gama tabbatarwa a ransa zaiyi dad'i ba sai da ya sha,aiko take ya shanye cup en hannunsa zuciyarsa cike da tunanin waye yayi wannan drink en haka?

Cup en ya mik'a mata,zuciyansa ta lula duniyar tunani.....

《《》》

Tun bayan da ZAHRA ta bar gurin itama ko zaman ya isheta,bata wani jima ba ta bar gurin,inda ta k'ule cikin d'aki tana aikin kuka da ya zame mata abokin rayuwa duk lokacin da ta tuna MAMANTA....

Ta jima a haka kafin da k'yar ta tsaida kukan,ta hanyar d'auro alwala ta tada sallah......



*_~#TEAM KHUBRA~_*



*_REAL SMASHER. 🤞🏻😘_*

💠💠💠💠💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹






*©®2018*
*4/ʍɑվ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹

_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*~________________________~*
_íղɑ ʍɑԵմҡ'ɑɾ ցօժíվɑ ՏօՏɑí ʍɑՏօվɑ,Տɑҡ'օղҡմ ɑ ҡմӀӀմʍ վɑղɑ ɾíՏҡɑԵɑ,ղɑ ցօժҽ ɑժժմ'օ'íղҡմ,ɑӀӀɑհ վɑ ҍɑɾ ҡ'ɑմղɑ.._ *ɾҽɑӀӀվ ӀմѵՏ մ ʍվ ԹҽԹՏ..💓💓*
*~________________________~*
_Tabbas ba dan bak'ar addu'ah babu kyaubaa da babu abunda zai hanani kwana yi miki addu'ar da sai kin gwammace baki zo duniyarba, amma kam tabbas mun barki da Allah shi kad'ai zai nuna miki ishara, Allah ya isar mana....._

*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*2⃣1⃣*






*T*un kafin ta idar ko bacci ya fara fisganta,da sauri tayi sallama da rarrafe ta haye kan katifan ko addu'anma idanunta a kulle suke kan bacci haka tayi addu'an kwanciya bacci,ko ninke abun sallan bata yiba bare hijab en da ta cillar a k'asa...
Cikakken mintuna uku sun yi mata yawa take bacci mai nauyi ya d'auketa......

《《》》

Zuba masa ta sake yi,shi ko sai dad'a kafa kai yake yana shanyewa a haka har sai da ya sha rabin jug en,sam bai sani ba yana can duniyar tunani,dariyan da ta saka ne ya dawo da shi diniyarsa yana mai binta da kallo,hannunsa ya sake sauke idanunsa har lokacin cup en na mak'ale a hannunsa,d'an murmushi yayi yana shafa kansa...

''YAH me zan sa maka?''
Tambayanta ya katse mishi tunani

''Anything ma sis''

Murmurshi tayi tana jin dad'in yadda yake nuna kulawa kan komai da take yi...
Wani warmer ta bud'e take ko ta zaro faifan sinasir,aiko yana gani ya hau murmushi coz yana sonsa sosai MAMA ce dai da yake ba wani iya girkin gargajiya tayi ba,ko da yake na zamaninma dai da sauk'i,(auu kada ta jiyo ni) ☺.......
Ai ko take ya dakatar da ita ta hanyar fad'in
''Sisnah bar shi haka ai kin gamamin komai tunda kikamin favourite nawa,sauran ki kyauta idan na gama abunda nake''

Sosai ya dage yaci sinasir en da miyan agusi,sukam su ASHNA suna cikin parlor duk abunda ke faruwa tsakanin ZAHRA da YAYAN NASU sun zuba ido ne suga ya zasu k'arke shi da ba cin abincin masu aiki yake ba,sai dai kuma kash abunda suka zata bai faruba,duk kuwa da sun san suna shiri sosai da ZAHRA a kan abuncin masu aiki komai zai iya faruwa hatta kuwa ita kanta ZAHRAN,sosai ya basu mamaki,sai da yaji uwa bazai iya tashiba sannan ya hak'ura tas ya shanye sob'on,fuskansa d'auke da fara'a ya kalli ZAHRA yana fad'in
''Thnks Lil sis''

Murmushin itama ta mayar masa kafin suka koma parlor da yake tsit uwa ba mutane...
Tabbatarwa da sukayi ya gama MAMA da muk'arrabanta suka dira a dinning en,har suna rige² gurin bud'e warmer en sinasir aiko dai² lokacin ya juya ya kallesu a hankali ya furta
''Lil sis maza ki adanamin sinasir ennan,coz da safe shi nake son ci''

''Laaaaa!BB ya maka ne?''

Kai ya kad'a mata

''To ai muna da garin,da safen sai ayi maka sabo''

Bai ce komaiba zuwa wani lokaci kuma ya soma tambayanta
''Lilly a ina kika koyi girki ne?''

''Laaaa!BB bafa ni nayiba,kawai dai ina taimaka mata,kuma ina ganin yadda take yi''

''Kin kyauta sosai da kike koyo kin fi wancan sakarkarun''
Har yayi shiru kuma sai ya tuna maganarta da take cewa ''ba ita tayi ba'',kenan waye yayi?
Yama kansa tambayan,aiko take ya d'ago yana kallonta
''Waye ne yayi lil sis?''

''Uhmmm YAYA wata ce''

''Aiko ta burgeni sosai da ta iya kalolin abunda nake so''

''Da gaske YAH?''
Kai ya sake kad'a mata,aiko sai murna take tace
''Ai kam kama tunamin ta ce zata zo maka sannu da dawowa,amma har yanzun shiru''

Shi dai yana saurarenta sai firan take masa tana ta bashi labarin irin kirkinta sai dai har lokacin bata ambaci sunanta ba,tunda suke bata tab'a masa maganar wani ba sai yau,har ta soma jin bacci,k'arshe kam sallama sukama sauran har bakin k'ofan d'akinta ya rakara ya mata sai da safe,sannan ya wuce nasa room en....

Bai jima da shigaba ko shima yabi lafiyan bed dama gajiyan bawai ya gama sakinsa bane aiko bacci ya d'aukesa babu b'ata lokaci......

《《》》

Duk duniyar a yau kam haushin kowa take ji,haka ta wuni ranan takaici duk ya cika mata zuciya....

Ko da dare yayi,tana shiga d'akinta ta ganshi zaune kan gadonta ita kam ma har tsoro abun ya bata dan kam ta san bata bar kowa ciki ba,taya zata ga mutum kuma zaune yanzun...

Har ta juya zata kwasa da gudu, ya dakatar da ita ta hanyar nuni zuwa k'afafunta,take ko tajita uwa wacce aka d'aure,bakinta har rawa yake gurin magana,sai dai ta kasa furta ko (A)....
Ta kowa yayi har gabanta ganinsa ne yasa jikinta ya dad'a yin sanyi,danko tasan zasu maimaita jiya ne....

Bata gama tunanitanba ya shek'e da wata irin dariya da ta cika d'akin ita kam jikinta duk ya saki,daga nan kuma labari ya chanza salo......

Kamar waccan ranar ba shi ya k'yaleta ba sai gabanin b'illowar alfijr......
Haka ya tafi ya barta duk bak'in ciki ya dabaibayeta,tana tunane tunanenta bacci yayi gaba d ita....

《《》》

Tun da ta farka ta d'auro alwala tana kan abun sallah har aka kira sallah,sannan ta saurara tayi sallan subh,tana zaune tana lazimi,garin ya soma haske ci gaba tayi har gari ya gama yin haske tukun ta mik'e..
Wanka tayi ta shirya cikin dogon riga cikin irin kayan da ZAHRA ke bata,ta zura hijab en sallahnta ta fice....

Karafniyarta a kitchen ZAHRA ta jiyo,aiko itama ta kamo hanya ta fito,after sun gaisa ZAHRA ta kalli KHUBRA ta fad'in

''Shi ne kika cemun zaki zo amma naji ki shiru ko?''

'Dan murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da aikinta
''Aiko sis ban baki labari ba,wollah jiya BB ya ban mamaki,kin san ba abincin kowa yake ciba,kuma wallahi ciki har da na MAMA,in fad'a miki sob'on da kika had'a fa tas ya shanye bai rage komai ba''

'Yar dariyanta ta sake yi,tana shirin d'ora gyad'anta a wuta dan yau kam kunun gyad'a ta tashi da niyyan yi.....

''Laaaaa!sis ban fad'a miki ba,wallahi BB cewa yayi na ajiye masa sinasir en jiya ni kuma nace mishi ya bari a yi masa wani da safe''
Ta tak'aice maganar tana kallon KHUBRA tana kuma sauraron taji me za tace,dafe kanta KHUBRA tayi kafin ta kalleta
''Kin san kuwa sauran garin kenan jiya mukayi amfani da shi?''

Zaro ido ZAHRA tayi tana dafe kai
''Wayyo Allah na,yanzun gashi na bari sun ciye masa,da na sani na adana masa,amma yanzun mene abunyi sis?''
Fuskanta uwa za tayi kuka take kallon KHUBRA,d'an murmushi tayi na k'arfafa mata guiwa

''Hak'uri za ki bashi,amma kam baki kyauta ba''

''Wallahi sis sam na manta sauran garin kenan,shi yasa na ce za ayi masa wani''

''Shi kenan ki bar damuwa,yanzun kawai muyi FUNKASO in yaso sai ki kai masa shi,ki kumayi masa bayanin abunda ya faru,in ba jaka ba zai d'aukeki a mak'aryaciya idan har kika jira ya fara tambaya''

''To sis na gode sosai''
Jikinta a salub'e haka suka ci gaba da aikinsu''

Juya baya KHUBRA tayi ta ci gaba da aikin kwab'in funkasonta....


Tun da ya tashi wanka kad'ai yayi ya zura jallabiya milk colour,silifas en wanka ya zura ya fito,a hankali yake tafiya ko wata macen baza ta gaya masa tafiya a nutse ba...
K'amshin girkin ya biyo,har kusa da kitchen en,nan ne ya soma jin magana k'asa²,a bakin k'ofan ya tsaya yana kallon yadda suka zage suna aiki,ya dai ga ZAHRA kam da yake tana gefe sai surutu take zubawa...
Ita ko d'ayar sam baya iya hango fuskanta,saboda haka bai wani damu da sanin wace ba...

Juywa yayi zai bar gurin dai² ZAHRA ta d'an waigo ai ko ta ganshi,da suri ta biyo shi parlor tana fad'in
''YAYANAH barka da safiya''

Fuskarsa da y'ar fara'a ya kalleta yana amsata,nan kuma tayi shiru kafin cikin d'an tsoro² ta ce
''YAYANAH idan na fad'a maka wata magana baza kaji haushi ba?''

''No princess bazan ji ba,ai bakya laifi a gurina''

''Ammmm!dama ko YAH garin shinkafan da za muyi maka sinasir ne ya k'are,na manta jiya nace maka akwai,amma dan Allah kayi hak'uri kaji''

''Nooo!Princess kar ki damu,babu komai maza jeki ku ci gaba da aikin''

''To YAYANAH na gode sosai''
Murmushi ya mata kafin da d'an gudunta ta bar gurin ta nufi kitchen en.....

Tana shiga ta tarar da KHUBRA har ta gama kwab'in,tana juya kununta da ta dama,da y'ar murnanta ta juyo ta kalleta
''Wato ko sis ina fad'a miki kin san baimin fad'a ba kuma Allah bai damu ba''

''Ai na fad'a miki dama gara da kika fad'a masa yanzun kafin ya tambayeki,da shi ya riga tambaya Allah sai ya ji haushinki''

''Ai kuwa dai wallahi yanzun dad'i nake ji da na fad'a masa kuma bai nunamin damuwa ba''

Ita kam sai murmushi take tana aikinta,haka har ta k'are komai tana k'ok'arin soma suyan funkason,mutiyar tana gefe zaune kan stool tana mata fira...

Sai da suka gama gyara komai na kitchen en kafin KHUBRA ta zari hijab enta dake kan k'ofa inda ta sak'ale shi

''Yawwa sis muje ku gaisa da BB kinga sai ki masa barka da dawowa tunda jiya baki zo ba''
Tana gama fad'in hakan ta hau jaan hannun KHUBRA,ita kam kanta ta saukar k'asa a haka suka fita cikin parlorn,suna tafiya duk jinta take wani iri uwa wacce aka yiwa duka,sai dad'a sinne kai take yi......

《《》》

Tun bayan fitar 'DAN LADI take nan kwance duk idanunta sun gagara komawa ainihin kalarsu...

Haka ta yini ita kad'ai a cikin gidan sam ta kasa tab'uka komai,tana tsaka da tunanin mafita Ogan d'an ladi ya fad'o gidan
Mad'aurin............. a hannunsa ya shigo d'akin,ko sallama babu ya k'arasa har gaban MA'U dake kwance idanunta rufe,sam ta kasa bud'e idanunta bare ta ga waye ya shigo,dan ba buk'atarta kenan ba....
Jin mutum tayi kawai yana juyata,cikin kasala ta d'an soma bud'e idanuntan a hankali hoton face ensa suka yi arba da k'wayar idanta,take ta maidasu ta rufe,aiko nan take suka fad'a harka wacce bata da tsayayyen lokacin da za su daina sai lokacin da suka yi ra'ayi......


Sam a yanzu MA'U ta manta da babin wata halitta mai kama da KHUBRA wacce iya tsawon watanni hud'u (4) kenan bata sake bi ta kan kud'in aikin KHUBRAN ba,dan ko itama tana kan samun nata na k'ashin kanta,dan ko dama can fatara ce tasa take damuwa da samun su,to yanzun nata k'ofofin samun sun bud'e shi yasa sam ta manta da ita.....

《《》》

A tsakiyar parlorn suka ja burki sai dai babu kowa cikin parlorn,waige² ZAHRA take yi amma tabbas idanunta ba k'arya suke mata ba baya nan..

Har lokacin ko idanun KHUBRA na k'asa bata d'agoba bare tasan halin da ake ciki...
Zaunar da ita ZAHRA tayi tana fad'in
''Sis zauna nan ina dawowa,barin kirashi ku gaisa''
Tana gama fad'a tayi hanyan corridor da zai sada ta da bedroom ensa...

A hankali ta d'ago kanta ta kalli cikin parlorn sai da ta tabbatar ZAHRA tayi nisa sannan ta mik'e cikin sand'a ta fice daga parlorn,ganinta a waje tayiwa Allah godiya,take ko ta kwasa a guje,ba ita ta dakata ba sai da ta tsinci kanta cikin d'akinta sannan ta mai da k'ofan tayi locking nata,ta shiga mai da uwa wacce ta shiga gasar there ta duniya............




*_~TEAM KHUBRA~_*



*_REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹



*Viawattpad@realsmasher01.*



*©®2018*
*6/ʍɑվ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹
_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._

*~________________________~*
*հҽհҽհҽհҽհҽ!!*
_ժɑɾíվɑɾ ɾɑíղíղ աɑվօ ҡҽղɑղ,ցɑ աɑղժɑ վɑ ԵՏɑɾցմ..._

_íղɑ ʍíҡ'օ ցɑíՏմաɑ վ'ɑղ ɑʍɑղɑ ʍմԵaղҽղɑ,abօҡan tsoҡana,sarɑkan riҡici.աղղ Տհí ղҽ Եɑҡҽղҡմ._
*DURLING SIS MY HUBBEEY*
*MY LEEMA*
*AUNTY MAIMOUNATH (O.G)*
*AUNTY MEELAT*
*HASEENA OGANNIYA ND D REST...*
_Aɾɑժմ íղɑ վíղҡմ íɾíղ ҍɑՀɑ ɑ ɾɑҍմҍɑ ҽղղɑղ AӀӀɑհ վɑ ҍɑɾ Հմʍմղcí ժɑ ҡ'ɑմղɑ,վɑ ҡմʍɑ ҡɑɾҽʍմ Տհɑɾɾíղ ʍɑՏմ Տհɑɾɾí..._
*~________________________~*
_íղɑ ʍɑԵմҡ'ɑɾ ցօժíվɑ ՏօՏɑí ժմɾӀíղց ҍɾօԵհҽɾ ժɑ ցվɑɾɑղ ժɑ ҡɑʍíղ,AӀӀɑհ վɑ ҍɑɾ Հմʍմղcí.._
_ցɑíՏմաɑ ժɑ faԵan ɑӀҡհɑíɾí ցɑɾҽҡɑ *Տɑժҽҽզ ɑʍíղմ վɑհվɑ (ԹíӀօԵ)* աօӀӀɑհ ɑղɑ ʍմցմղ Եɑɾҽ ʍվ ҍɾօ.._
*~________________________~*
_Aradu sai dai idon mak'iya ya fad'o k'asa,ka sha gabansu,ka wuce gaban kwatance duk mak'iyinka sai dai ya sadda kansa k'asa idan akace ga kanan,OUR SURUKI ka wuce da saninsu,yara baza su jaa da kaiba dan ko kafi k'arfinsu......Yeahhhh kai kad'ai nake nufi *(HASSAN ATK)* Allah ya bar zumunci ya maka nisan kwana mai amfani,mu da kai mutu ka raba (takalmin kaza) k'aryar mak'iya su shiga tsakaninmu,na jinjina maka OUR SURUKI,Allah jaa da ranka...._
*~________________________~*

*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*2⃣2⃣*


*Nɑվí ʍíՏԵɑҡҽ աɑյҽղ sunan ZUHRA íղɑ ʍɑí ժɑՏհí ZAHRA, Տօ ZUHRA ղҽ վղՀղ ҍɑ ZAHRA ҍɑ,ɑʍíղ ɑƒմաɑ,ԵհղҡՏ ҍɾօԵհҽɾ ƒօɾ cօɾɾҽcԵíօղ..*



*C*hest enta ta dafe saboda yadda take jin zuciyanta na skipping uwa zai faso ya fito,duk ta gama tsorata kanta,da k'yar ta ja k'afafunta ta zauna bakin katifanta,hijab en dake jikinta ta cire duk ta had'a gumi uwa wacce tayi gudun kilometer's....
Kumatunta ta tallafe tana faman mai da numfashi,a fili ta shiga magana ita d'aya


Please Login or Register in order to submit comment