Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹





*©®2018*
*21/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*4⃣8⃣*





*K'* atuwar motar da tayi parking a k'ofar gidan nasa yake bi da kallo game da tsantsan mamaki a zuciyarsa yake fad'in
"Wannan kam sunyi makuwa da alama gidan mai gari suke nema....."
Bai gama tunaninba mutanen ciki suka shiga fitowa d'aya bayan d'aya,har lokacin ABBA'N KHUBRA mamaki ne shimfid'e a saman fuskarsa saboda rashin sani wanda ake cewa ''yafi dare duhu''.

KHUBRA da take kusan ta k'arshen fitowa daga motan,idanunta suka sauka kan mahaifinta da ako wane lokaci shi ne farin cikinta,nan ko ta kwasa a guje bata tsaya wata-wataba ta ruk'unk'umeshi,kukantane ya bayyana inda shi kuma ABBA ganin wannan al'amari yasa shi fad'in
"Y'ar nan yi maza ki sake ni kada ki jawomin abunda za a jefeni....kina yiwa Allah ki sakeni tun kafin labari ya isa kunnen mai gari...."
Idanunta da suka gama jik'ewa da ruwan hawaye ta d'ago tana kallonsa har lokacin kuma wasu na ci gaba da sakkowa
"Alhamdulillahil-laziiy bii ni'imatihi tatimmus-salihaat!!!...."
Abunda bakin ABBA'N nata yaketa furtawa kenan har lokacin kuma ya gagara sakinta saima dad'a k'ank'ameta da yayi kamar wanda akace za a rabasu har abada.
"UWATA ke ce ko kuwa gizo kikemin kamar yadda kika saba zuwamin...?"
ABBA'N nata ya tambaya cike da rashin gasgatawa,saboda a ganinsa a ko wane irin lokaci zata iya b'acewa daga gurin.

"ABBA nice ba gizo bane..."

Godiya kawai yakewa Allah daya bayyana masa y'ar tasa kwaya d'aya tal.

ABBA'N BB ne ya matso kusa dasu hannunsa na nuna MALAM BUBA da shi sam ma bai kula ta kansuba y'arsa ce kad'ai abunda idanuwansa ke hango masa,da k'yar ABBA ya harhad'a kalmomin yana fad'in
"M.A....L..A..M......BU....BU...BUBA....."

A d'an firgice ABBA'N KHUBRA ya d'ago kansa yana kallon inda aka ambaci sunansa,kallonsa yake like no other yana son tuno inda ya sanshi,amma sam k'wak'walwarsa ta gagara tunawa da abunda yake son ganewar tattare da wannan d'an gayun mutumin.

"Nasan da wuya ka iya shaidani amma da zaka kalleni sosai tabbas zaka iya tuna fuskata..."
ABBA ya fad'a yana murmushi,aiko kamar wanda aka bawa wani gagarumin aiki ya k'ure shi da idanu duk da ya kasa tunawar hakan baisa ya hak'ura ya daina kallon ABBA'N BB ba..
"A gaskiya ALHAJI ban shaidakaba,sai dai ko kamin k'arin bayani la-Allah sai na iya tunawa"

Sai da ya saki wani k'ayataccen murmushi wanda ke bayyana kyau da kuma zallan hutu da wannan bawan Allah ke ciki sannan ya furta
"Ehhh! to ina ganin mu zauna tukun dan maganar tamu bata buk'atar muyita a haka..."

LADIYO na gefe rakub'e a zaure tana lek'e dan tun bayan da ta samu MALAM en ya saketa tayi zaraf ta shige had'eda lab'ewa tana lek'en wad'annan turawan bak'in.
Duru-duru MALAM en ya shiga yi na neman abun da zai shimfid'a musu su zauna,kafin yayi yunk'urin yin wani abu LADIYO tayi zaraf ta fito tana fad'in
"MALAM ai da ka kaisu cikin gidan ko dan nan yayi kan hanya..."
Wata uwar harara ya sake aika mata wacce take nuni da 'idan kika sakemin shishshigi zanyi maganinki,a fusace ya wuceta dan shi kam gare shi ya tsani ko da ganinta bare har wata magana ta shiga tsakaninsu.
K'atuwar tabarma ya shimfid'a musu sannan ya shiga fad'in
"Bismillah...!!!"
Gaba d'aya ko suka nemi guri suka zauna,LADIYO da MALAM ya barta tsaye da sakakken jiki ta nemi guri daga can gefe ta rakab'e,a inda kuma tayiwa kunnuwanta matsuguni a tsakiyar mutanen da takewa kallon daga wata k'asar suka zo,musamman y'an matan da har yanzu babu wacce ta shaida hatta kuwa da KHUBRA dake kusa da ABBA'NTA ta jingina dashi,idan ta kalleshi sai tayi murmushi a zuciyarta take fad'in
"Yau nima na samu y'anci gani kusa da mahaifina...."
Abu d'aya zai iya sawa kayi saurin gano b'acewar annurin dake kan fuskarta a wannan lokacin,ba komai bane kuwa face tunanin MAHAIFIYARTA da bata tab'a ganiba.
Muryoyinsu ne suka katse mata tunani inda suke ta faman gaishe-gaishe da tambayan juna iyali,bayan nan kuma gurin yayi d'an shiru na wucin gadi kafin ABBA'N KHALEEL yayi addu'ah.
Nan kuma aka koma kan ainihin maganar da ta shigo dasu,ABBA ya sake kallon MALAM BUBA da yake jiran k'arin bayani daga bakinsa,kamar yadda suma sauran jama'ar gurin suke sauraron jin me zai biyo baya.

"Nasan gaba d'ayanku kunyi mamaki musamman dana nuna nasan MALAM BUBA ko?......"

Nan suka hau amsawa da "Hakane....!"

"To Alhamdulillah! yanzun zaku ji yadda akayi na sanshi duk da dai shi bai shaidaniba..."
Kallonsu ya sake yi d'aya da d'aya,KHUBRA kuwa murna take yi jin ABBA'NSU ZUHRA yasan ABBA'NTA,fuskarta sai annuri ke fita

"Ni dai dai farko suna na SAFWAN kuma ni haifaffen garin DUTSE ne ta nan jihar JIGAWA"

Kallonsa sosai MALAM ya sakeyi jin sunan daya ambata,kamaninsa ya shiga hangowa ko tantama ba yayi shi ne dai wanda ya sani shekara da shekaru da suka gabata..

"Tabbas wallahi shi ne!....Shi ne....SAFWAN...."
Sai kuma ABBA'N KHUBRA ya fashe da kuka da alama akwai wani abu da yake damunsa wanda ya tuna a dai² lokacin.

Da k'yar suka lallasheshi yayi shiru,inda gaba d'aya sauran jama'ar gurin suke kallonsu,saboda yadda suka sasu a duhu
"Tabbas sai yanzu na shaidaka...."
Sabuwar gaisuwa suka sake da tambayar bayan rabuwa.

ABBA'N KHALEEL ya kalli ALHAJI SAFWAN yana fad'in
"To ALHAJI mu kam kun samu a duhu,bamu fahimci abunda kuke nufiba.....dama kun san juna ne kam ko yaya abun yake....?"

Kai ABBA ya girgiza masa kafin yayi magana MALAM BUBA har ya rigashi
"K'warai kuwa mun jima da sanin juna...kamar dai yadda kuka gani yanzun zan yi muku bayanin alak'ar dake tsakanina da SAFWAN....
Ni dai da farko suna na ABUBAKAR SA'ADU wanda mafi yawancin jama'a suka sani da MALAM BUBA kamar yadda na taso da wannan suna....alak'ar dake tsakaninmu kuwa ita ce.......

《《》》

Ciwo ne ya soma cin k'arfinta tun bayan zuwanta asibiti da likita ya sanar mata komai lafiya bata sake yunk'urin komawaba,jikinta duk babu kuzari a yanayin yadda take jinsa babban dalili kenan da yasa yau d'in ta shiga shiri babu ji bare gani na ganin ta koma asibitin tunda ciwon yaci k'arfinta..
Tafiya kawai take amma da tayi tayi sai ta huta,saboda rashin kuzari duba da yadda kwanakin take fama da amai da gudawa.
Layin karb'an kati tabi bayan jira da tayi na wani lokaci sannan aka sallameta,hannunta rik'e da katin ta nufi office en likitanta na wancan lokacin.

Shiganta office en ta nemi guri ta zauna kan kujera,katin ya amsa idanunsa sanye da glasses ya kalleta yana mata tambayoyin abunda ke damunta..
A hankali take motsa bakinta saboda ina ganin kamar bakin natama ya tafi yajin aiki had'e da sauran gangan jikinta..
Idanunsa na kanta har ta k'are bayaninta sannan yayi y'an rubuce-rubuce,bayan y'an mintuna kuma ya sake d'agowa yana mata bayanin za taje tayi test a yau ta kawo masa,amsa tayi ta fice daga office en kamar wancan lokacin,bata zame ko inaba sai laboratory na asibitin.Bayan an d'ibi jininta ta zauna jiran fitowan sakamako a nan.
Mintuna sun sake shud'ewa inda wata nurse ta hau kiran sunanta aiko nan MA'U ta mik'e da k'yar tana nufarta
Wani kallo nurse en ta mata sannan ta mik'o mata sakamakon gwajin tana yatsina fuska,haka ta karb'a sannan ta kamo hanyan dawowa gurin likita danjin me kuma sakamakon nata zai nuna a karo na biyu.

Shigowarta office en ta tarar da shi yana waya kan dole ta tsaya jiransa har ya gama,sannan ya amshi takardar dake hannunta,zaro farar takardar yayi da take ninke a cikin envelope ya warware,abunda idanunsa suka fara tozali da shi shine yanda gwajin jininta ya koma *POSITIVE* maimakon *NEGATIVE* wannan shi ne abunda ya tabbatar masa da matar na d'auke da cutar da yake hasashe,ajiyan zuciya yayi sannan ya maida takardar ma'adaninta,cikin sanyin murya ya shiga yi mata nasiha kan yarda da *K'ADDARA* da kuma karb'arta ta kowane fuska tazo maka mai kyau ne ko akasin haka,ita dai MA'U ido ne nata babu baki,sam ta kasa gane inda wannan tatsuniya ta likita ke tafiya duk ta kafeshi da idanu
"Likita nifa har yanzun ban gane ma'anar wannan wa'azin nakaba ,kawai idan zaka sanarmin abunda ke faruwa to,idan kuma bazaka fad'a ba to ka sallameni dan na gaji da zaman gurin nan"

Kallonta kawai yayi jin yadda take magana cikin kaushin murya a ransa ya furta
"Lallai wato bata san meke faruwa ba amma takemin irin wannan maganar....aiko zaki san ni kikewa magana haka"
Yayi niyyan sanar da ita cikin ruwan sanyi amma maganarta tasa shi had'e giran sama dana k'asa ya shiga fad'in
"HAJIYA sakamakon gwajin da aka miki ya tabbatar mana da kina d'auke da cuta me karya garkuwa'n jiki wato *HIV* kenan kamar yadda muke kiranta a turance,wanda a hausa kuma muke kiranta da *K'ANJAMAUU*......."


《《》》

Hannunsa d'auke da envelope yana tafiya yana kare fuskarsa saboda zafin rana dake damunsa,ci gaba da kallon hanya yake saboda hangen abun hawa da zai d'auke shi a lokacin,da k'yar ya samu NAPEP ya fad'a masa inda zashi,tafiyar mintuna k'alilan ta kawosu bakin k'aton get en,kud'i ya fiddo ya sallami mai NAPEP en sannan ya tura get en ya shiga.
Tun daga harabar gidan nake kallon gurin kamar na sanshi haka wani lokaci daya gabata,cikin sauri ya shige k'ofar da zata sadashi da babban parlor na k'asa,shigowarsa ya tarar dasu sun baje kayan shaye-shaye wasu da kwalabe wasu kuma sai had'awa sama hazo suke.
"Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un!!"
Abunda ya fara fitowa daga bakinsa kenan,cikin fushi ya isa gurin baiyi wata-wataba ya shiga fashe kwalaben a k'asa cikin fad'a yake fad'in
"Ban fad'a muku kada wanda ya sake yimin shaye-shaye a gida ba?.....ko kuwa so kuke ayimin cunen y'an drugs?
To wallahi yau kam kunyi na k'arshe dan dukanku sai kun barmin gida...gara kusan inda dare yayi muku,nima na samu Hutu da nutsuwar zuciya.."

"SO.....SO...SORRY OGAAA...."
Wani yaronsa daya sha yayi mankas ya fad'a idanunsa na rufewa da bud'ewa
"In...sh...sh...sha....Allahu ba zaka sake kamamu da wannan laifinba.."
Tsaki yayi ya wuce hanyan stairs a ransa yake fad'in
"Ya zama dole akaina ko dai ku chanja hali ko kuma dukanku dole na rabu daku"
Kafin ya k'arasa haurawa saman wayansa dake aljihu ta soma k'ara da sauri ko ya zarota ganin bak'uwar number har zai fasa d'auka wata zuciyar tace
"Ina kai ina k'in d'aukan bak'uwar number,ai kawai ka d'auka wata kila ko cikin guraren da ka kai takardunkane aka dace ka samu aikin da kake nema...."
Bai ka'arasa tunaninba yayi saurin d'auka had'eda karata a kunne,cikin harshen nasara daga gefen da aka kira shi ake fad'in
"Ko kaine SADEEQ MUHAMMAD?"
Cikin hanzari har yana had'awa da girgiza kai BIGGY ya amsa da eh shi ne..

"Muna nemanka ranar monday a ma'aikatar revenue ta nan kano a branch enmu dake bomphai..."

Ai BIGGY kam ji yayi kamar zai gangaro daga saman stairs en saboda dacen da yayi bak'aramin dad'i yajiba,dan dama ranar da UMMI tace ya kai mata takardunsa ya amsane kawai amma a ransa ya k'udurce shifa ba zai koma gidanba har sai bayan ya samu aiki wanda yayi k'ok'arin hakan a k'ashin kansa,wannan shi kad'ai zai sa su ganshi da k'ima..
Godiya yayiwa Allah,sannan ya kuma tabbatarwa da kansa lallai duk wanda yake laifi ya tuba ubangiji yana karb'an tubansa,kansa ya d'aga sama hawayen farin ciki suna sakko masa a hankali ya furta
"Lallai ne ubangiji shi kad'ai yafi cancanta da a bautawa...Allah na gode maka da ka nufeni da tuba tun lokaci bai k'ureminba..."





*~#TEAM KHUBRA.*~




*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹





*©®2018*
*22/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*4⃣9⃣*




*"A* lak'ar data had'amu da SAFWAN itace auratayya inda na auri k'anwarsa mai suna FALMATA"
A nan ABBA'N KHUBRA ya dakata saboda wani tunanin daya bijiro masa wanda sam baiji dad'in hakanba,sai yanzu yake nadama da dana sanin abunda ya aikata,ciki kuwa harda saurin yanke hukunci,wanda Annabi (S.A.W) ya hanemu da mu yanke hukunci cikin fushi.
LADIYO ya kalla da rinannun idanunsa da babu komai cikinsu face zallar b'acin rai wanda kana kallonsa zaka tabbatar had'e kuma da gano abunda ke k'unshe k'asan zuciyarsa.
Muryarsa a shak'e ya kalli mutanen gurin ya kuma kallon LADIYO data sha jinin jikinta,sai da yayi gyaran murya sannan ya fara da fad'in
"Da farko dai zan fara da yiwa wannan matsiyaciyar matar Allah ya isa,sannan kuma in shaida muku ina son ku zama shaida ni ABUBAKAR SA'ADU (MALAM BUBA) na saki LADIYO saki uku babu ni babu ita,daga yau ina son ta tattara kayanta tabarmun gidana na sallameta......"

Innalillahi wa-inna ilaihi raji'un...
Abunda mutanen gurin keta maimaitawa kenan kamar sa ari baki,ABBA'N KHALEEL ne ya fara magana
"Haba MALAM ya zaka yanke irin wannan hukunci haka,bayan ka sani cewa ubangiji da kansa yana k'yamar saki irin wannan,sam bai dace kayi hukunci irin wannan ba koda kuwa wane irin laifi ta aikata maka,idan ka kyaleta da mahaliccinmu zai hukuntata komai girman laifinta kuwa..."
Bai kai k'arsheba MALAMA BUBA ya dakatar da shi ta hanyar fad'in
"Haba ALHAJI yanzu ita wannan matar da kake magana akanta kasan girman laifukanta kuwa?ko kuwa ni kasan meta aikatamin?kasan tsahon loacin data d'auka tana cutata?to ku saurareni yanzun zaku ji irin cutarwa da azabtarwar da wannan munafukar tayimin ni da iyalina...."

*19 YEAR'S BACK......*

"Shekaru sha tara 19 baya,na kasance malamin makarantar islamiyyane kamar yadda kuka ji suna na ABUBAKAR SA'ADU wanda akafi sani da MALAM BUBA,kaf garin nan idan ka tambaya tun daga kan manya da yara babu wanda bai sanniba saboda baiwa da Allah yayimin ta ilimin islama,ta wannan baiwar ne har na samu nake koyar da mutane da dama cikin garin nan namu,a lolacin ina da mata d'aya wacce itace LADIYO,muna zaune da ita lafiya tun bayan aurenmu wanda yake tun na saurayi da budurwa,tsahon rayuwar da mukayi da ita a wannan lokacin Allah baisa tana da rabon haihuwa ba,har muka kai kimanin shekaru goma Allah baisa ko da b'atan wata ta tab'a yiba,a kwana a tashi maganganu sunata yawo a gari kan matata bata tab'a haihuwaba,kai in tak'aice mukuma wasu har samuna suke sunamin magana kan idan na amince zasu bani auren k'annensu wasu suce y'ay'a ga mutanen da suka manyata kenan a wannan gari,gidanmu kuwa wajen mahaifana suma ba a kyale suba da wannan maganar,sai dai na basu hak'uri tare da godiya saboda karramawa da girmamani da sukayi wanda har ya jawo sunamin kyauta mai girma amma ni kuma ban karb'a ba,kwanci tashi asarar mai rai a shekara ta sha d'aya da aurenmu sai nayi wata tafiya zuwa garin DUTSE inda za a gudanar da wata *SEMINER* ta addini,cikin hukuncin Allah bayan zuwana garin duk yinin duniya idan muka gama abunda za muyi a gurin seminer sai mu fita don zaga gari.A wata ranar *LITININ* wacce bana jin zan iya mantawa da ita a iya tsahon rayuwata,kamar kullum mun fito muna zaga gari muka had'u da wata y'ar matashiyar budurwa kyakykyawa da ita,wacce ko ni idan aka bani abun zane ba lallaine na iya zana wacce ta kaitaba bare kuma wacce ta fita saboda kyau da Allah yayi mata sam bata da makusa ta kowane b'angare,nan dai maganganu iri-iri sukaita fitowa daga bakunan abokan tafiyata kan yaba kyau irin nata,jin abun da sukeyi yasa ni dai nayi shiru ban furta komaiba muka ci gaba da tafiya,wani ikon Allah yarinyar tana tafiya a gaba garemu mu kuma muna bayanta kusan duk hanyar data bi to ko muma ita muke bi daga dukkan alamu kuma aikenta akayi,mun biyo wata hanya ne kuma muka ga yarinyar na k'ok'arin shiga gida inda a nan wani mutum daya fara manyanta daga dukkan alamu kuma mahaifintane ya dakatar da ita,babban abun burgewa a tare da ita lokacin data tarar da shi a zaune tun daga nesa da shi kad'an ta cire takalmanta,sannan ta durk'usa ta gaida shi,bayan nan ta shige gida..
Tun daga wannan lokacin naji zuciyata ta kwad'aita da yanayin tarbiyya irin ta wannan baiwar Allah wacce ko sunanta ban saniba bare na tabbatar da nan ne gidansu ko a'a.
Tun daga wannan ranar bamu sake biyo hanyar ba sai da muka kwana uku,sannan a yammaci na hud'u na shirya cikin shiga ta kamala kamar ko wane lokaci na d'auko hanya,ban zame ko inaba sai hanyar da muka gamu da wannan baiwar Allah,ina tafiya ina kuma duba gine-gine da yanayin unguwan har Allah yasa na kawo dai-dai wannan k'ofar gida data shiga,nan ko na samu guri na tsaya ina kuma k'arewa unguwar kallo,layin shiru babu mutane sosai zuwa wani lokaci sai wani yaro daga mak'otansu ya fito nan dai zuciyata ta rayamin na tambayi yaron ko Allah zaisa ya santa,banyi wani dogon tunaniba ko na kira yaron na tambayeshi ko yasan wata a gidan nan?,nan na siffanta masa ita da yanayuita,bud'ar bakin yaro ya furta eh yasanta sunanta *FALMATA* na masa dai y'an tambayoyi wanda bazasu gagara yaro ya amsaba ya bani amsa dai² da saninsa,sannan na zaro murtala na dank'a masa had'e da yi masa godiya,a guje yaron yabar gurin yana murna.Na jima tsaye a gurin kafin na bar unguwar.Tun daga wannan ranar ya zamemin d'abi'a kusan kullum saina je unguwar amma haka zan dawo ba tare da nayi magana da itaba.
Bayan sati uku da faruwar wannan lamari ne kuma muka kammala abunda ya kaimu garin,nan muka shiga shirye-shiryen komawa gida,to kuma a cikin wannan lokacin ne na yanke shawaran tunkarar gidansu da magana ko nasamu nasara ko akasin haka,nan na shirya na ko kama hanyar gidansu,cikin sa'a ina zuwa unguwar tun daga nesa na hango wannan dattijo na ranar farko zaune a k'ofar gida,da sallama na tarar da shi bayan mun gaisa ban tsaya k'wauron bakiba nayi masa bayanin abunda ke tafe dani,nan dai yayi dariya shima mutumin sannan yayimin albishir d'in cewa shi ne mahaifinta,kuma yaji dad'in abunda nayi,sannan ya d'ora da fad'in zai samu yarinyar zasuyi magana idan har ta nuna ta amince to idan kuwa ta nuna akasin haka tofa sai dai nayi hak'uri dan shi kam ba zai mata doleba duk abunda take so shima shi yake so kuma shi zai bata,bayan nan yamin tambayoyi akan inda nake da sana'ata,ban b'oye komaiba na daga abunda ya shafeni na shaida masa,daga k'arshe kuma nayi masa sallama gami da godiya na kama hanyar komawa inda na fito.
Kamar yadda yayimin alk'awarin bayan kwanaki na dawo dan jin yadda sukayi,kuwa na sake shiryawa daga garinmu dan a lokacin mun riga da mun koma gidajenmu,bayan naje mun gaisa da shi ya sanarmin da yadda sukayi,daga nan kuma ya shiga gidan da kansa ya kirawota,mun gaisa da ita bayan nan kuma tayi shiru saboda kunya da take da ko kallona bata iyayi a wannan lokaci,ban b'ata lokaciba na gabatar da kaina a gurinta a matsayin d'an takara na neman aurenta.
In tak'aita muku labari haka soyayya gami da shak'uwa suka k'ullu a tsakaninmu da FALMATA,wanda ba'a d'auki lokaciba mahaifina kafin ya rasu sukaje nemamin auranta,kun dai san yadda ake sa rana a k'auye ba'a d'aukan lokaci kamar na birni su sukan sa lokaci tak'aitacce ne,sun yanke ranar aure watanni biyu masu zuwa,inda kowane b'angare aka shiga shiri,da farko LADIYO bata nuna damuwarta kan auren da zanyi ba ganin yadda mahaifiyata take sonta,bayan auren kuma sai wasu halayya na banza suka fara sako kai cikin al'amuranta wanda da gani kasan zuga ce take aiki a kanta.
Muna zaune da FALMATA lafiya k'alau tun bayan aurenmu da ita da yake ita ba mai magana bace komai nata cikin sanyi take yinsa,wannan yasa ko da ake zugo LADIYO idan ta takaleta da fad'ama bata biye mata sai dai tayi shigewarta d'aki ta barta nan,haka itama zata k'araci masifar fad'anta ta bar gurin,ganin babu nasara sai ta canja salo inda a hankali ta soma jan FALMATA a jiki a gaban kowa tana nuna mata soyayya amma a zuciyarta babu wannan,ganin haka sai mutane suke sha'awar yadda suke zaune da juna,har wasuma suke fad'in ai MALAM BUBA yayi dacen mata na gari babu fad'a tsakaninsu.
Kwanci tashi har muka shafe tsahon shekara aurena da FALMATA amma shiru babu wani labari ganin haka sai hankalin LADIYO ya dad'a kwanciya,ta sake sakankancewa babu su babu haihuwa tunda ga wata nanma na aura amma shiru itama babu labari,haka dai akaita tsegumi da gutsiri tsoma akan nine bana haihuwa,wani hukinci da iko sai ubangiji a cikin shekara ta biyu da aurenmu da FALMATA sai Allah ya azurtata da samun juna biyu wanda babu wani ko wata da ya ankara da hakan da yake babu wani laulayi da tayi,har cikinta ya kai kimanin wata shida,ita dai ajikinta taji chanji wanda mafi yawancin lokaci takan sanarmin amma sai nace mata kada ta damu babu komai,a lokacin data sake sanarmin tanajin abu na mata motsi a ciki sai nake fad'awa iya cewa ga abunda ta fad'a min,bud'ar bakin iya sai tacemin micijin ciki ke damunta,nan ta had'oni da jik'e-jik'en magunguna na gargajiya na kawo mata..."
Nan MALAM BUBA ya dakata yana kallonsu da murmushi a fuskarsa sannan ya d'ora da fad'in
"Kun san wani abun al'abi a cikin wannan labarin?"
Babu wanda yayi magana cikinsu sai dai wasu cikinsu sun kad'a masa kai
"To ku saurara kuji.....Abun da zai baku mamaki shi ne,har cikinta yakai wata tara babu wanda ya gane sai dai ita da kanta ta fuskanci akwai wani bak'on al'amari a tare da ita wanda ganin hakan kuma da tayi baisa ta sanar da kowaba, a lokacin ni kuma nakanje fatauci daga wannan gari zuwa wannan kuma nakan kwashi watanni uku-biyar ban waiwayo gida ba,to kunji dalili kenan daya sa babu wanda ya gane tana d'auke da juna biyu

Please Login or Register in order to submit comment