Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai singlet da wandon kayan kifewa yayi a k'asa take wasu hawaye masu matuk'ar k'una suka shiga tsere a saman fuskarsa,a wannan yanayin duk wanda yaganshi dole ne ya tausaya masa saboda ganin garjejen saurayi majiyin k'arfi yana kuka da hawaye dole abun ya baka mamaki game kuma da tsoro coz irin su ba komai ke sasu yin kukaba.
Damuwa ta tarun masa gami da dana sani wacce bata da amfani,a dai-dai wannan lokacin da kowa ke cikin farin ciki da wannan ranar mai cike da tarihi,amma sam a gurin BB babu wannan labarin sai yanzun ya tabbata da ya tafka kuskure game kuma da asara wacce ba zai tab'a samun hanyan da zai gyaraba.
Babu abunda yake banda wani irin haki mai ban tsoro idanunsa sun canja launi zuwa jaa mai duhu,kwanciya yayi nan k'asa dafe da k'irjinsa da yake jinsa kamar zai tarwatse saboda azabar ciwo da yake masa....

*GURIN 'DAURIN AURE.*
Bayan fitowar su KHALEEL lokacin an gama d'aurin aure,Nanfa yayi ta dubawa bai ga BB a gurinba duk yadda yaso ya ganshi abun ya faskara,ko da ya tambaya wad'anda suka ga fitarsa sun sanar masa ya jima da fita,ko da yaji haka k'ok'arin kiransa yayita yi amma wayoyin sai ringing suke ank'i d'auka,duk k'ok'arin da yayita yi babu amsa,hak'ura yayi amma kuma hankalinsa baya tare da shi,kawai dai jama'an da suka kewaye shi ne yasa bai tafi nemansa ba dan yasan ba k'aramin abu ne yasa shi barin gurinba kuma har ya hana shi d'aukan kiransa.
Haka suka wuce gurin reception daga nan,har akayi aka watse abokai da y'an uwa sunata musu Allah ya bada zaman lafiya,ana gamawa ko bai zarce ko inaba sai gidansu BB,direct d'akinsa ya nufa dan yasan can ne kad'ai zai sameshi.
Abunda ya gani ya matuk'ar bashi mamaki game da tsoro wanda baiyi tsammaniba,magana ya shiga yi masa a hankali BB dake kwance k'asa ya d'ago rinannun idanunsa ya kalleshi da sauri kuma ya maida kansa ya kwantar wanda gaba d'ayan veins na kan sun gamaa bayyana.
"Hasbunallahu wa-ni'imal wakeel....!
KHALEED lafiyar ka k'alau kuwa,me yasa kake son zama cikin damuwa? me yake damunka ne kam...?"
Banza yayi masa saima kulle idanunsa da yayi dan bai shiryawa jin maganganun KHALEEL enba yanzun da yake cikin wannan halin

Jiki a sanyaye KHALEEL ya nemi guri ya zauna,a zuciyarsa ya furta
"Ya kamata na sanar masa yanzun ko kuwa....?"
Da hanzari kuma cikin tausayi ya kalli BB yana fad'in
"Tashi za muyi magana yanzun..."
Banza ya sake masa,hannunsa dafe da kansa da yake barazanar tarwatsewa,hakan da yayi masa yasa shi sake kallonsa,duk k'ok'arinsa na ya kwantar masa da hankali yasa shi kuma magana dan ya kore masa damuwan hakan ya faskara dan Sam yak'i bashi had'in kai,wayansa ya shiga pressing cikin apps nasa ya binciko app na *MAHEER MU-AQQILIIY* sauka ne complete amma a app yake nan ya kunna tun daga fatiha suke sauraro tare a lokacin da kuma suke zaman kurame,yini guda sallah kad'ai ke tada su,itama nan suke yinta cikin d'aki babu mai fita,weeding pics da ake da amarya da ango saboda tarihi a wannan ranar kama sam amaryar KHALEEL bata sashi a idanuntaba,dan ko suna can zaman makoki shi da aminin nasa...

B'angaren AMARYA KHUBRA ko tun bayan da aka dawo da labarin an d'aura aure ta dad'a lafkewa kan bed dan ko dama tuni take fama da matsanancin ciwon kai wanda ya saukar mata da zazzab'i mai zafin gaske.
Da k'yar aka samu ta iya shiryawa shima sai da taimakon ZUHRA,tana kwance ZUHRA na gefenta labarin d'aurin aure ya riskesu,jikinta ko ya sake rikicewa,tana kwance cikin duvet amma kana hango yadda jikinta ke vibrating kamar wacce aka jonama shocking.
Duk k'ok'arin da MAMA take akan samun su KHALEEL a waya hakan ya faskara kan dole ta kira line en ABBA,shi enma dai suna tare da mutane lokacin da take kira dalili kenan daya sa bata same shiba,k'arshe dai sai magani aka bata haka da k'yar da sid'in goshi zazzab'in ya sauka sai ciwon kan da yak'i tafiya coz dama haka ciwon kai yake mata baya saurin tafiya idan ta fara.

Shirin dinner ake sai daifa har lokacin babu ANGWAYE bare kuma AMARE duk iya kaiwa ruwan da za ayi anyi akan shirya KHUBRA amma sam ta kafe akan ba inda zata,k'awayensu ASHNA da ZUHRA da su suka zama k'awayensu duka a gurin,haka suka shirya suka d'auki hanyan tafiya dinner,ZUHRA aka bari gida dan ta kafa ta tsare akan babu inda itama zata idan babu KHUBRA a wajen,har aka dawo daga dinner suna d'aki ZUHRA na kula da ita,yini guda babu wani abu da taci duk k'ok'arin da MAMA tayi akan taci wani abu amma ta gagara yin hakan kan dole suka kyaleta kowa ya sa mata ido sai sannu da take karb'a daga bakin mutane da dama.Wajen 9pm aka fara dawowa daga gurin dinner dan d'aukan amare a lokacin ne kuma MAMA ta sake shigowa gefen da su KHUBRA suke,a kan idanunta ta shirya duk jikinta a sake kamar wacce bata da laka har ta kammala,kayansu tunda aka fara biki iri d'aya da ASHNA.
Kusa da ASHNA aka zaunar da ita nan nefa ta d'ago idanunta da suke masu kama da an tsoma a man gyad'a tabi mutanen da kallo,KAKA ne zaune saman sofa sai sauran BAFFANINSU da kuma ABBA'NTA da ABBA'N BB,sai sauran y'an uwanta ZUHRA,FATAHIYYA,duk taurin kai da nunk'ufurci irin na BB da yake wannan kiran na manya ne sai daya halarta,cikin wani shigan daban sai k'amshi yake bazawa kamar sabon ango,fuska a d'aure kamar wani BOSS yake zaune gurin,ganinsa a gurin ya tabbatarmin yanzun kam da sauk'i jikin nasa sai dai har lokacin ba wani sosaiba sauk'in saboda yadda yake tafiya a hankali kuma cikin dauriya yake saboda bai son a gane halin da yake ciki.
Bayan dogon lokaci da KAKA ya d'auka yana musu nasiha mai ratsa jiki,sannan sauran iyaye suka d'ora nasu,bayan nan kuma KAKA yasa akayi addu'a wanda ya dad'a sanyaya musu jiki daga bisani kuma akayi musu fatan zaman lafiya sannan aka fita dasu kowacce sai kuka take,a haka aka dangana da kowacce d'akinta.
Amare sai muce Allah ya bada zaman lafiya...

BB ne ya mik'e zai fito daga parlor'n KAKA ya dakatar da shi ta hanyar fad'in
"To MALAM sauran kai ko naji ance ko budurwa baka da,ko dai a k'auye zan bada kai sadaka ne...?"

Murmushin k'arfin hali yayi ba tare da yayi magana ba har KAKA ya gama jansa da tsokana wanda k'arshe shima ya biye masa,daga bisani kuma KAKA yayi masa nasiha sosai,shi dai sai mamaki yake ko mene dalilin wannan nasihar ta KAKA oho,haka har ya samu KAKA ya sallameshi,yana fitowa ko KHALEEL na kiranshi babu yadda zaiyi kan dole ya d'auka saboda yanzun ba kamar da safe ba jikin da sauk'i kuma tunanin da yayi ne akan rashin dacewar abunda yakewa KHALEEL en ya rinjaye shi,dalilin kenan daya yanke shawaran sakin jikinsa d'aukan wayan yayi,KHALEEL ne ya fara magana cikin sanyin murya
"MAN! kana ina ne yanzun...?"

Shiru yayi na d'an lokaci kafin ya iya yin gyaran muya sannan a tak'aice ya furta
"Gida......"

"Ok Zaka iya rakani ko kuwa....?"

Jim ya sake yi kamar kuma bai gane mai KHALEEL en yake nufiba ya furta
"Ina kenan..?"

Cike da zolaya ko KHALEEL ya ce
"Sai da kai zanyi..."

"Uhmmm! kaima kasan na wuce haka ai"

"Banda kuri dai.."

"Haba wane irin kuri kuma kaima kasan gaskiya ai"

Sai da KHALEEL yayi dariya sannan ya furta
"Kawai dai ka shirya yanzun zan zo zaka raka ni wani waje ne mu dawo..."

"Haba MAN ina zamu kuma a wannan lokacin kai da kake da amarya bai kamata ka barta taita jiranka ba kaga dare na dad'a yi,ka bari zuwa wani lokacin ka je koma ina zaka.."

"To wai kam ina ruwan ka da maganar amarya ko kuwa shi kenan babu wani uzuri da zai taso min yanzun nayi kafin na wuce gidana...?"

Banza BB yayi masa cikin sanyin murya kuma kamar wanda bai son magana yace
"Za kayi ka bari d'an air kawai..."
Sarai KHALEEL ya jishi kawai dai baison BB en yace ya fasa rakashin ne yasa yace
"Naji...ni dai gani nan a hanya zan zo na d'aukeka.."
Yana gama fad'an abunda zai fad'a ya datse kiran ba tare da yaji amsan da BB zai bashiba,cikin k'ank'anin lokaci kuma ya k'arawa motan wuta zuwa gidan su BB en.

A harabar gidan ya tadda shi tun da suka gama waya ya kasa barin gurin har lokacin kuma yana jin chest ensa ba daidaiba duk da dai ya bawa kansa hak'uri amma kam yana jin zuciyarsa na k'aik'ayi kawai dai k'arfin hali yake.
Yana daidaita parking BB na isowa kusa da shi cikin shiga kamar ta d'azun yanzunma haka suke har mamaki BB yayi daya ga KHALEEL sanye da irin kayansa wanda suka kasance kyauta daga gurin ABBA'NSA,bai tambaye shiba ya b'oye mamakinsa ta hanyar d'auke kansa daga kan KHALEEL en ya shiga motan suka bar gurin.

Tafiyan babu wani nisa daga gidan su zuwa inda suka je en,a bakin wani gida KHALEEL ya tsaya sannan yayi horn,bud'e masa k'ofar get man en yayi nan ya danna hancin motan ciki,farfajiyan babu laifi akwai girma dan ko yanayin gurin zai tabbatar da hakan duba da yadda motoci da dama suke a parke a gurin,fita sukayi tare da kama hanyan shiga gidan KHALEEL na kan gaba sai BB dake bayansa,shi dai binsa kawai yake ba tare da yayi masa tambayan komai game da inda suka zo enba,har suka k'araso kusa da inda taron abokan nasu suke a cikin parlor.
A nan ne kuma mamakin BB ya kasa b'oyuwa duba da yadda suka tarar da wasu daga cikin abokansu ke zaune,mamakin dake kan fuskarsa ya kautar sannan suka gaisa nan ko suketa masa tsiyan basu ganshi gurin reception ba da sauri KHALEEL yace
"Ammm! da yake ai kunsan k'anwarsa ce amarya to kuma bata ji dad'i ba shiyasa ya tafi ya wakilce ni a gurin..."

"Eyyahhh! gaskiya ne aiko yayi maka babbar karafa.."
Daga haka suka yi musu fatan alkahiri sannan suka yi sallama da su ba tare da sun jira ganin amarya ba suka kama hanyan maida jama'ah zuwa gida.

Parlor'n ya rage daga KHALEEL sai BB suna zaune can BB ya kalleshi
"Ko mene ne ma'anar yin hakan da kayi...?
A nawa tunanin ba sai kamin haka zan san kana son na rako kaba,idan ka sanarmin gidanka zan rakoka zan gagara yi maka hakan ne...?"

Banza shima KHALEEL en ya masa saima dad'a nutsewa da yayi cikin cousion yana turo hulansa saman giransa,wayansa a hannu yana danne-danne,zaman kurame suka ci gaba da yi inda yake ankara da BB daya gama cika kamar zai fashe saboda haushin banzan daya masa bai bashi amsaba.

Jin gidan yayi shiru yasa KHALEEL ya mik'e tare da gyara zaman cap nasa yana fad'in
"Muje ko naji alamun babu mutane a gidan..."

K'wafa yayi sannan ya mik'e yabi bayansa,ta nan cikin parlor'n suka bi wani k'ofan daban,sai gasu a wani k'ayataccen parlor'n fiye da wanda suka baro,a nan BB ya nemi guri ya zauna KHALEEL ya juyo cikin d'an alamu na kamar yayi mantuwa ya kalli BB
"Sorry MAN d'an jirani nan nayi mantuwafa.."
Kallonsa yayi sannan yaja wani uban tsaki,KHALEEL dai bai jira jin me zai fad'a ba ya fice da sauri.
BB na zaune yaji alamun tashin mota a fili ya furta
"Lallaima GUY ennan koi d'an rainin hankali..."

Kiran KHALEEL en ya soma yana zaune har lokacin a gurin,shi kuma KHALEEL yana ganin kiran BB yayi murmushi game da k'in d'aukan kiran coz time en ya isa bakin get ko fita baiyi daga gidanba,sai da ya tabbatar da ya fice sannan ya tsaya gefen hanya ya fiddo wayansa,dai² lokacin kiran BB ya sake shigowa da sauri ya d'auka ko kafin yayi magana BB ya rigashi
"Wane irin iskanci ne wannan zaka ajiye ni ka fice...Ko kuma ka maidani mai tsaron gidanka ne...?"

Dariya sosai KHALEEL yayi iya son ransa har saida BB yaji haushinsa

"Idan ka gama gasamin maganar to ka shiga ciki matarka na jiranka..."

Yana fad'in haka ya datse kiran,cikin rashin fahimta BB yake son tambayansa,anya kuwa yaji dai² ko kuwa dai kunnensa ne yake yaudararsa,kafin yayi magana yaji an katse wayan,k'ok'arin sake kira yayi amma KHALEEL yak'i d'auka har ya gaji da kira dan kansa ya bari..

Ganin bai sake kiraba KHALEEL en ya tafa masa text kamar haka...

_Am sorry friend naso yi maka bayani tuni sai dai kak'i amincewa muyi maganar shi yasa ni kuma na yanke shawaran yi maka haka,tabbas nasan a yanzun kana cikin shock da maganar da na maka,sai daifa tabbas abunda na fad'a babu k'arya ko zolaya a ciki,dama kai na rako ba wai ni ka rakoba,ina maka fatan alkhairi kai da amaryarka *KHADIJATUL-KHUBRA*.Na barka lafiya aci amarci lafiya._

*UR'S KHALEEL.*

Dai² lokacin daya samu sak'on bayan ya gama karantawa mik'ewa yayi tsaye kamar wanda aka tsikara yana nanata sunan *KHUBRA* da ya gani rubuce...............





*COMMENT FOR MORE PAGE'S......* 💃💃💃





*~#TEAM KHUBRA-KHALEED.~*





*_®єαl $mαѕhєr._* 😉
💠💠💠💠💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹



*fαcєвσσk grσup:* https://www.facebook.com/groups/369678263526212/

*©®2018*
*26/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~__________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





5⃣4⃣





*S* till yayi a inda yake har lokaci he ain't believe abunda yaji kuma ya gani gaske ne,cap nasa yayi removing ya cilla saman cuition shi kad'ai sai kaiwa da kawowa yake cikin parlor,zuciyarsa tak'i samun nutsuwa da abunda KHALEEL en ya sanar masa,nan ko ya shiga magana a fili
"How za ace haka ya faru bayan akan kunnena naji d'aurin auren wannan kawai shirme ne na sani irin na KHALEEL babu yadda za ayi haka ya faru,am not believing any more...."
Waya ya sake dannama KHALEEL,ganin kiran BB yasan da akwai damuwa kan dole ko ya tsaya gefe still yayi yana sauraron maganganun BB da yake yinsu cikin fad'-fad'a
"Heyy! MR MAN u have to came and take me up here right now.....
Banda shirme irin naka taya za a d'aura maka aure da yarinya naji kuma akan kunnena ka maida ni wani sauna....Idan ma baza ka dawoba to zan bar maka matarka cikin gida,and ni kuma na san inda dare yamin..."

"Ka gama fad'an....?"
KHALEEL ya tambaya cikin coolness tone

"Ohhh! abunda za kacema kenan...wato ka mai dani wani tamkar ban san abunda nakeba shi ne harda cemin na gama fad'an....?
To ban gamaba kuma Allah ka ji na rantse babu abunda zai hanani tafiya,idan ka gama ka dawo ka tarar da babu kowa...."
Yana kaiwa nan ya datse wayan ko sauraron me KHALEEL en zai fad'a baiba kuma har lokacin yana tsaye sai huci yake.

KHALEEL jin da yayi BB ya kashe wayan yasa shi saurin yin tunanin ya kamata ya tura masa wani evidence da zai zauna cikin gidan kada ya bar yarinyar mutane ita d'aya a gidan,da saurinsa ko ya tura masa sak'o ta email,sannan ya jaa motansa ya k'ara gaba.

Dai² lokacin da yake sintiri tsakiyan parlor hannunsa d'aya a dunk'ule yana naushin iska sak'on ya shigo,da sauri ya isa kusa da phone en yana dubawa,email nasa ya shiga cikin sauri saboda ganin sak'on ta email yake,nan ko ya tarar da sak'on audio da kuma na video's wanda da gani babu tambaya kasan a gurin d'aurin aure ne.
Cikin hanzari ya shiga playing nasu d'aya bayan d'aya yana kuma sauraro har dai² lokacin da aka soma sanar da d'aurin auren kamar haka
_An d'aura auren *IBRAHIM KHALEEL* da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA* akan sadaki naira na gugan naira har naira dubu d'ari biyar..._

Wani uban tsaki BB yayi a dai² nan yana fad'in
"Banda d'an iska ni zai rainawa hankali kamar ba a gabana aka fad'i hakaba...."
Kafin ya sake magana yaji mai sanarwar yana fad'in
_"Afwan..! Afwan..!! Afwan..!!!_
_Y'an uwa a gafarceni nayi makuwa gurin sanar da wannan d'aurin auren,ina fatan kuma za amin afuwa dan kuwa ba *KHALEEL* zan ambataba gurin fad'amin ne aka samu sab'ani sai yanzun aka sanar dani gyaran dake cikin wannan maganar tawa,a maimakon KHALEEL dana ambata *KHALEED* ne angon,wannan auren na *KHALEED* ne da amaryarsa *KHADIJATUL-KHUBRA*_
_Sai kuma auren *IBRAHIM-KHALEEL* da amaryarsa *FATIMA-ZUHRA* akan sadaki dai-dai dana y'ar uwarta,aure na uku kuma shi ne na *ABUBAKAR-SADEEQ* da amaryarsa *ASHNA* sadakinta kwatankwacin na y'an uwanta lakadan ba ajalanba...._
Dafe baki BB yayi yana fad'in
"Ta yaya akayi haka ya faru? kenan bayan na bar gurin akayi haka ko kuwa yaushe ne hakan ya faru...?"
'Daya bayan d'aya ya dinga binsu yana playing har yazo na k'arshe,again bai hak'ura ba ya sake kiran KHALEEL,shima cikin isa ya d'auka yana fad'in
"MAN! lafiya kake kirana kuma dai² lokacin da zan shiga gidana? ko kuma har yanzun shaidan basu gama gamsar da kai bane...?"

Murmushi kawai yayi yana fad'in
"Noo! kawai dai na kasa yarda ne...!"

"To tunda baka yarda ba ai shi kenan ka jira gobe sai su ABBA su maka bayanin yadda akayi haka,ni nayi iya nawa sauran nasu..."
Yana kaiwa nan ko ya kashe wayan gaba d'aya dan yasan idan ya barta haka BB zaita damunsa da kira,dai² ya shigo parlor aiko ya juya ya kulle k'ofofi tare da addu'an neman kariya daga mahalicci...

**********

B'angaren amarya KHUBRA kuwa tun bayan da suka futo daga parlor lokacin za a sasu mota ta rik'o ZUHRA akan itafa lallai sai dai k'afarta k'afar ZUHRA zasu tafi,ganin zata jik'a musu aiki da dabara aka sata cikin mota sannan aka ce to ta matsa ZUHRA ta shigo,da yake babu wayo nan ko ta matsa aiko tana yin haka aka rufe k'ofan sannan driver'n yaja yayi gaba.
Kuka babu irin wanda bata yiba dan an taho da ita babu ZUHRA dama kuma ba wani cikakkiyar lafiya gareta ba,haka ko bayan da aka kawota da d'aya da d'aya duka suka zare jikinsu suka gudu,aka barta daga ita sai halinta,kukanta ta shak'a bayan taji gidan shiru a nan inda ta gama kukan take kwance jikinta duk ya dad'a yin zafi tana saman bed jikin ta ya ko dad'a rikicewa ....

Nan parlor yaci gaba da zama ya kasa yanke shawaran abunda ya kamata yayi,har 12am yana nan shi bai bar gurinba kuma bai daina kiran number KHALEEL ba duk kuwa da yadda wayan ke sanar masa a rufe take,wani zuciyan ne ya bashi shawaran kiran UMMI baiyi tunanin komaiba ko yaddana mata kira ba tare da yayi tunanin dare yayi ko akasin hakaba...
Cikin magana irinta mai bacci UMMI ta d'auka tana fad'in
"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"

Murmushi yayi mai k'ayatarwa ko tantama babu yanzun kam ya soma gasgata maganar KHALEEL,sai dai tambayan da yake ta damun kansa shi ne *TA YAYA HAKA YA FARU?*.
Murmushi yayi ta saki abunsa kamar ba wanda yake jinya ba d'azun,kan cuition ya kwanta had'eda kashe wayan ba tare da yayi magana ba,yana juya lamarin a ransa,lallai a yanzun kam ya tabbatar da komai hukuncin rabbi ne ba tare da dabara ko k'arfinsa ba ya bashi abunda ya jima a ransa a kuma lokacin da babu zato bare tsammani, ai kam ya tabbatar a yanzun yafi kowane d'a namiji sa'a,a duniyarsa gani yake babu wanda zaiyi dace kamar nasa.
Tunawa yayi da maganar KHALEEL ta d'azu da abokansu suke tambayan basu ganshi gurin d'aurin aureba,sannan kuma maganar UMMI ta sake fad'o masa inda take cewa
_"KHALEED SON lafiya kuwa ka kirani cikin wannan lokacin.....ina ita KHUBRA'N ko kuwa jikin nata ne ya sake rikicewa...?"_
Cikin hanzari ko ya mik'e yana bin hanyan da zai sadashi da d'akunan baccinsu cikin damuwa coz bai san halin da take cikiba a fili ya furta
"Is she ill...? Amma tun yaushe ne hakan ya faru...?"
Dai² lokacin ya iso kallon gefe da gefensa yayi coz bai san a wane room take ba,kallon doors yayi ya d'an tsaya tunani can kuma sai ya kalli wanda yake bud'e a hankali ya d'aga k'afafunsa ya nufeshi...


*GIDAN KHALEEL...*

Bayan ya gama tura masa abunda zai tura daya kashe phone ensa ya kulle k'ofifi,hanyan bedrooms en ya nufa yana fad'in
"HABIIBTIIY!!!.....Ina kika shige ne..?"

Shiru yaji babu amsa nanko ya nufi cikin bedroom enta,zaune saman bed ya hangota sai dad'a jan vail enta take tana dad'a rufe jikinta,da alama da ba gurin take zauneba,dariya yayi yana fad'in
"Ohh! kunyana kuma ake ji yau..? i think yau kam babu wannan a tsakaninmu tunda burin da muka jima da shi yanzun Allah ya nuna mana ranar da muketa jira...So ina ganin kamata yayi ace munyi godiya ga Allah daya nuna mana hakan cikin rai da lafiya gami kuma da kwanciyar hankali..."

A hankali ta d'an motsa kamar zata janye vail en sai kuma yaga sab'anin haka
"Ohhh! wato sai kin bani wahala dai kenan ko..?"

Har lokacin ZUHRA ta kasa masa magana,ta kuma k'i d'agowa ta kalleshi,saman bed en ya isa yana ajiye ledan dake hannunsa,a kusa da ita yayima kansa masauki,fuskanta ya shiga lek'awa yana fad'in
"Haba mana duk kalaman da nake GAM DA KATAR (ZEEY BUGAJE) dasu a kullum kuma yauda nake tsammanin ganinsu a zahiri bayan tsawon lokacin da muka d'auka bama tare,sai naga sab'anin haka,shi kenan tunda baki son ganina bari na koma inda na fito...Dama na had'u da wata d'azun so kinga saina tafi zance gurinta ko?"
Yana gama fad'in haka ko ya shiga k'ok'arin mik'ewa da niyyan zai fice,a zahiri kuma yana kallonta yaga wane reactions zata bayar da jin maganar tasa,alama yayi kamar zai fice,aiko nan ZUHRA ta dire k'afafu tana bugasu k'asa cikin tab'ara tana fad'in
"Ni wallahi a'a,kuma idan ka fita nima saina bika duk inda zaka..."
Dariya ya kwashe mata da,sai da yayi son ransa,ita kuma ganin yana mata dariya gashi dama tunda ta mik'e tayi cilli da mayafin,tsayawa tayi kallonsa yadda yake dariya take kallo sai taga ya k'ara mata kyau fiye da

Please Login or Register in order to submit comment