Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

har lokacin tace
"Kaje kace masa Bismillah! zai iya shigowa"
Da sauri ya fita don isar da sak'on da aka bashi.
Har bayan fitansa MAMA bata koma dai² ba saboda firgicin da take ciki wanda ya hanata magana.

Da sallama ya shigo cikin shiga ta kamala wanda idan har wanda ya sanshi ya ganshi a cikin wannan kayan zai iya tsammanin ba shi bane wani ne daban,sosai kyaunsa ya dad'a bayyana ga wani classy da ya k'ara,har k'asa ya sunkuya ya gaidasu sannan ya zauna a kan rug,k'afafunsa a tank'washe kamar mai d'aukan darasi,wanda bai sanshiba idan ya kalleshi a wannan shigan zai iya tsammanin dama can haka yake.
Shiru cikin parlor'n na wani lokaci,su kuma suna masa kallon rashin sani dan babu wanda ya tab'a ganinsa cikinsu bare ya shaida shi.
MAMA ce taga shirun yayi yawa ta fara magana da fad'in
"Samari daga ina haka mu nan babu wanda ya shaidaka cikinmu"

Kansa ya d'an sosa yana d'an inda-inda dan bai san ta ina zai fara maganaba,kansa a k'asa yana shirin yin magana su BB suka shigo shi da KHALEEL
"Da farko dai HAJIYA ni suna na *SADEEQ* wanda wasu daga cikin mutane ke kirana da *BIGGY* na zone domin baku hak'uri tare kuma da neman gafararku bisa abubuwan da suka faru a y'an watanni sannan kuma zuwa wasu satittika da suka shud'e"

Kallon mamaki duka suka bishi da shi,inda su KHALEEL suka nemi guri suka zauna don jin abunda zai biyo bayan zancen da yake yi.

"A da HAJIYA ni ban kasance cikin mutane masu tausayiba bare imani....."

"Subhanallah!" UMMI ta furta
"Kai kuwa wane irin mutum ne da har kake furta baka da imani,ka san kuwa ma'anar wanda aka ce bashi da imani?
A duk lokacin da aka cewa mutum bashi da imani to tabbas wannan mutumin baya cikin jerin mutane masu imani,saboda ko me ka aikata ka rok'i yafiya daga gurin mahaliccinmu sannan ka nemi yafiyar wad'anda ka zalunta,tabbas ubangiji zai gafarta maka dukkan zunubanka,ina fatan ka gane ko?"

Kai ya kad'a mata sannan idanunsa na fidda hawaye kamar mace yace
"HAJIYA sam abunda na aikata ba shi da alak'a da abunda kike magana,kamar dai yadda kikaji na ambata ni na kasance ina yin aiki na marasa imani,kamar kuma yadda na kasance cikin marasa tausayi had'e kuma da aiki ga mutane marasa imani"

Wani kallo gaba d'aya mutane hud'un dake cikin parlor'n ke masa mai wuyar fassara,gaba d'aya hankulansu na kansa basu da burin daya wuce jin cikakken labarin wannan SARK'AK'IYA.

Dad'a duk'ar da kansa yayi k'asa ya goge fuskarsa sannan yaci gaba
"HAJIYA ni da kuke gani a da na kasance cikin mutanen da suke yin *GARKUWA* da mutane domin neman wani abu ko kuma asasu sace wasu sannan mutane su yasar wani yanki daban
Idan baku mantaba a watannin baya kun nemi y'arku kun rasa wacce kuka jima kuna nema ba tare da kun gantaba
Sannan a weeks da suka shud'e kuka sake neman wata kuka rasa,wanda ita kuma ta dawo gida kimanin sati kenan da samunta"

"Kaii da Allah dakata kada dai kace mana kai ne k'asurgumin b'arawon da ka sacesu duka"

Ba tare da ya kallesuba ya kad'a kai,yin hakan babu b'ata lokaci KHALEEL ya kalli BB daya ke kallon wannan bawan Allah mai matuk'ar k'arfin hali.
"Ammafa kayi k'ok'ari kuma ya zama wajibi a jinjina maka saboda bajintar da kayi,a saboda haka ni kuma nayi tunanin karramaka ta hanyar baka lambar yabo..."

Da sauri KHALEEL ya kalli BB cikin fad'a yana fad'in
"Haba MAN wane irin bajinta kuma?.........wane irin kuma karramawa kake magana ga azzulumi irin wannan?wanda makomarsa bata wuce gidan sark'aba,irin wad'annan mutanen makomarsu ma yaci ace tafi haka muni saboda ayyukansu......"

"Ya isa haka SON,me yasa zaka katse shi daga bayanin da yake yi bayan d'umbin nadama da yayi wanda har ya masa jagora akan yazo neman afuwarmu,ina ganin idan har ba dagaske yake ba babu abunda zai kawo shi gurinmu,mu bashi dama muji dame yazo tukuna kafin a yanke masa hukunci....."
Maganar da UMMI tayi ita tasa su yin shiru kowanne sai huci yake burinsu bai wuce a kyalesu su sab'a masa halittaba ko samu sassauci,idanun BB sun gama rinewa da b'acin rai ga tarin bak'in cikin dakatar da shi da akayi gurin hukunta wannan k'asurgumin mai laifin dake gabansa,kunnuwansa yasa hannu ya toshe duk dan kada yaji abunda ake fad'a idanunsa a lumshe kamar mai bacci haka ya jingina bayansa a jikin sofa...

Kallon matasan samarin BIGGY yayi da suke cike da zafin kai wanda a ganinsu idan har aka barsu da BIGGY to babu abunda zai yi saura a jikinsa..
Sai daya sake kallon mutanen parlor'n sannan yaci gaba
"Bisa wannan kuskure dana aikata a rayuwata kuma bisa ga dalilin had'uwata da d'aya daga cikin y'an matan dana sata zuciyata ta kasa nutsuwa wanda har tayi min jagora zuwa alkhairi,itace ta kawo haske cikin rayuwata wanda yayi sanadiyyar dana yanke shawarar dena aikata duk wani laifi dana ke tawa akan hakane na yanke shawarar dawo da ita gida....."
Daga nan ya kwashe duk yanda suka yi da ASHNA tun bayan daya sace ta da irin damuwar da ta shiga,har kuma yanda yayi nadama kan aikin nasa ya kuma dawo da ita a ranar da sukaje asibiti shi ne lokacin da suka tarar da MAMA'N ta samu sauk'i,sannan ya k'ara da yadda ya tafi ya bar asibitin wanda a ranar babu wanda ya kula dashi
acikin d'akin saboda yadda hankalinsu ya koma kan MAMA...
Shiru yayi bayan ya kai nan a zancensa yana jiran ganin matakin da zasu d'auka akansa.

"Alhamdulillah!da har haka ya faru kuma muna godiya ga Allah daya sa ka shiryu daga mugun aikin da kake aikatawa,abun farin cikine ace wani ya shiryu ta sanadinmu,wannanma kad'ai ya ishemu alfahari da har haka ta faru
Y'anzun shin kana da wata sana'a ne da za kayi bayan dena waccan mummunar sana'ar taka?"

"A'a HAJIYA amma dai zan ci gaba da k'ok'arin nema ko dan ganin ban koma wancan sana'ar dana bariba"

"To Alhamdulillah da haka ya kasance lallai wannan ya tabbatar mana da cewa da gaske kake yi ka tuba daga wannan d'anyen aiki,abunda zan maka albishir da shi shine idan har ka dena abunda kake gaba d'aya ka kuma yi min alk'awarin bazaka sakeba
Ni kuma in sha Allah nayi alk'awarin nema maka aiki,amma abunda nake son ji daga gareka.....shin kayi makaranta ne?"

Sai da yayi murmushin jin dad'i sannan ya furta
"Ehhhh!HAJIYA nayi karatu rashin aiki ne tun farko da kuma sharrin matar mahaifina ta d'orani a wannan hanyan tun bayan dana rasa mahaifana"

"Asshha! Allah ya kiyaye ashema ba hakanan ka fara wannan mummunar sana'ar ba,Allah ya tseratar damu daga sharrin masu sharri amma abu baiyi kyauba
Abun da nake so da kai yanzu shine ina so ka kawo min copy na takardunka nan da sati guda kaji ko,sannan kuma kasa a ranka gaba d'ayanmu mun yafe maka abunda kayi mana,Allah kuma ya yafe mana baki d'ayanmu...."

"Haba UMMI ta yaya zaki saurin amincewa da maganarsa daga fad'an magana har kin yarda,irin wad'annan mutanen wallahi munafukai ne akwai wani mugun nufi da suke zuwa da shi a zuk'atansu,sai su fake da neman yafiya nan ko wani abu suka hango shi yasa suka lallab'o da sun samu nasara zaki neme su ki rasa...."
KHALEEL ya k'are maganar had'e da zabga masa wata uwar harara,wacce shi kam BIGGY baima san yana yiba dan ko kansa a k'asa yake.

Hararar shima ya samu daga gurin UMMI sannan ta masa dak'uwa tana fad'in
"Ungo naka SON wato kai gaka sarkin fitsararru ko?da nace a bar maganar kai ne bazaka iya yin shiru ba kenan,kana gani d'an uwanka yayi shiru amma kai saboda futsara shi ne zaka ci gaba da magana ko?to Allah yasa na sake jin ka furta wata magana wallahi saina sab'a maka kaji dai na fad'a maka..."

Kame bakinsa yayi bai sake yin maganaba duk maganar da UMMI ke yi da BIGGY babu wanda ya kuma ko da tari a cikinsu,har suka kammala maganar da suke,godiya sosai BIGGY yayi musu sannan ya mik'e yayi musu sallama da niyyan komawa,babu wanda ya kulashi tsakanin BB da KHALEEL duk kuwa da yanda ya mik'a musu hannu da zai fita,haka ya fice jiki a salub'e dan sam bai ji dad'in yadda KHALEEL en yake aika masa da kallon tsanaba.....

Dai² bakin parlor yana shirin fitowa ta taho a guje tana waiwaye tana ihu da alama akwai wanda ta tsokano karo tayi dashi da sauri ta maida kanta dan ganin mene ta buga haka,idanunsa na kanta duk da lokacin da ya fito zuciyarsa babu dad'i amma yanzun kam da ya ganta yaji dad'i sosai wanda baya misaltuwa,a hankali ya furta
"BEAUTY......."
Saurin kallonsa tayi dan tunanin inda tasan mai wannan kamannin take sai dai ta kasa ganewa yanzun kam da yayi magana ta rigada ta gama gane ko waye shi en,da sauri ta mik'e daga jikinsa tana fad'in
"Kaiii ne?.......me kuma ya kawoka gidanmu?"

Dariyama tambayanta ta bashi a hankali kuma ya karkatar da kansa gefe cikin wani irin yanayi yake fad'in
"Neman yafiya nazo gurin family enki dama ke kanki"

Idanunta ta sake bud'ewa tana k'are masa kallo saboda yadda ya mata kwarjini a yau,kallon sama ba sosai take iyawaba,kanta a kasa zuciyanta na skipping,ga wani feelings da take ji tattare da shi a lokacin,maganar daya mata ne wancan ranar ya fad'o mata a zuciyanta ta furta
"Kenan dama maganar dayamin kan zai daina abunda yake yi gaske ne?........To amma wane azzalumi ne yasa shi aikata mana wannan rashin imanin.......?"

Duk maganar da ASHNA ke yi batayi tsammanin a fili take yintaba sai da taji ya bata amsa
"K'warai kuwa BEAUTY da gaske ne babu k'arya a ciki....Kina son ki san wanda yasani aikata hakan ne?"
Yayi tambayan yana kallonta
"A'a kawai dai nayi maganar ne amma ba haka nake nufiba"

'Dan murmushi ya sake yi sannan ya furta a hankali
"Noo!BEAUTY nasan kina son sani kawai dai kinamin alkunyane ko?"

Bata ce komaiba taci gaba da murza ring en dake yatsanta,shi dai BIGGY (SADEEQ) yana ta kallonta duk wani abu da za tayi ji yake tana k'ara burgeshi,musammama wannan y'ar kunya da take nuna masa.

"Shin kin san wata mata mai suna HAJIYA LAURA?"
Tambayar ta daki kunnen ASHNA wacce bata yi tsammanin jin hakanba,a firgice ta d'ago kanta tana kallonsa,idanunta ne suka cicciko da hawaye cikin rud'ewa tana inda-inda take shirin tambayarsa,ko kafin tayi magana har ya rigata ta hanyar fad'in
"To itace bak'ar azzalumar data sa muka sace y'ar uwarki wacce muka yar a k'auyen garin ZAKIRAI,sannan kuma ita ce wacce tasa muka sace ki akan wani buri nata da mu bamu saniba....."
Kafin ya kai k'arshen maganarsa tuni ASHNA har tayi fitar burgu ta fad'a cikin parlor tana rusa kuka mai ban tausayi.
Shi ko BIGGY dake tsaye ganin hakan da tayi yasa jikinsa dad'a yin sanyi,a hankali ya juya ya bar gidan,yana tafe yana tunanin halin da BEAUTY ke ciki...

Fad'awa'nta parlor tana gunjin kuka shi yasa BB bud'e idonsa d'aya yana kallonta,ko kafin yayi magana har sun tsinto maganar ASHNA cikin kuka tana bada labarin abunda BIGGY ya shaida mata yanzun.
Da sauri MAMA ta mik'e tana zunduma wani gawurtaccen zagi wanda gaba d'ayansu basu tab'a tsammanin jinsa daga bakinta ba,jikinta sai karkarwa yake kamar wacce ake kad'awa mazari haka ta hau sababi
"Lallai HAJIYA LAURA yau kam kin riga da kin gama janyowa kanki k'arshen bala'i,yau ni HAJIYA MURJA zan nuna miki k'arshen colour ena,saina bar miki darasi a rayuwa wanda ko sunana kika ji an ambata zai sa ki dinga gudu dan neman mafaka......ba dai ni kika tab'a ba shi kenan mu zuba mu gani shege ka fasa yau zaki tabbatar da kin tab'o ......... dodo
Maza ki shirya yau ga maza nan bisa kanki"

Gaba d'aya mutanen parlor'n sun shiga shock idan aka d'auke BB da ya sake maida eyes yayi closing,mamakinsu ya kasa b'oyuwa saboda kowa yasan yadda suke da HAJIYA LAURA duk wani tak'ama da take yi da bazar HAJIYA MURJA take taka rawa,lallai ko yau kam HAJIYA LAURA kin d'ebo ruwan dafa kanki......

《《》》

Tun bayan da MALAM BUBA ya gama kora mata jawabi take tsaye a nan inda ya barta k'afafunta duk sun mata nauyi wanda ta gagara d'agasu,a gurin ta zube hannunta a ka ta shiga rera kuka babu ji bare gani...

Haka MALAM BUBA ya shige d'akinsa nan ko ya shiga jero nafilfili yana dad'a rok'on Allah yafiya bisa kuskuren da ya tafka a baya,sai da dare yayi nisa sosai sannan yayi addu'a ya kuma kwanta yana mai dad'a yin tasbihi ga ubangijin sammai da k'assai.


Kwanaki sun dad'a jaa inda a kullum tashin hankalin LADIYO yake dad'a k'aruwa daga lokacin da aka ce mata dare ya kawo kai,zuwa yau kuma babu wani labari dangane da MA'U bare ita kanta KHUBRA da ABBA'NTA yasa LADIYO ta dawo masa da d'iyarsa kamar yadda ya bata umarni.

《《》》

Tun daga ranar da BIGGY yazo gidan har zuwa yau bai sake dawowa ba,wanda zuwa yau an kwashi kwanaki da dama ba tare da ya sake waiwayar gidan ba.

A b'angaren ASHNA kuwa ko wane dare da tunani da kuma mafarkin BIGGY take kwana kuma take tashi,ko wane motsawar second ji take kamar za tayi hauka saboda yanda zuciyarta ta damu da shi fiye da tunaninta,tun bata yarda da cewa sonsa take ba har ya kaiga yanzun ta amincewa zuciyarta da son da take masa..

Tafiya tayi nisa a b'angaren zaman KHUBRA a gidansu KHALEEL a yayin da itama ZUHRA tayi tsalle ta dire kan itafa sam bata amince da a sake rabasu ba,nan ta tsaya kai da fata akan sai dai UMMI ta tafi dasu duka,nan ko UMMI tace taji ta gani kuma tana sonsu duka dan haka ta kwashesu duka suka koma gidanta.
Kulawa ta musamman suke samu daga gurin UMMI inda ta mai dasu y'ay'a tamkar ita ta haifesu da cikinta,d'aki guda tasa aka ware musu had'e da tsara shi da kayan k'awa wanda idanu bazasu iya tantace ainihin yadda suke ba,bare baki ko hannu su samu damar shaidawa masu sauraro.
Rayuwarsu a gidan UMMI kusan za a iya cewa a yanzun sunfi sakewa duba da yadda UMMI ta maidasu kamar wasu k'awayenta,shi yasa suma basa tab'a b'oye mata wani abu daya shige masu duhu,idan ko unguwa zata je zaka tarar dasu tare da ita duk inda ta cire k'afarta to ko nan zasu maida tasu.
Zuwa yanzun KHUBRA har ta dad'a washewa ba kamar yadda ta dawo daga garin ZAKIRAI ba,ta k'ara cikowa fatar nan tad'an yi fresh daga muguwar yamutsewar da tayi.....


Nema kam kusufa-kusufa akewa HAJIYA LAURA tun daga ranar da HAJIYA MURJA ta samu labarin itace shaid'aniyar data sa aka d'auke mata gudan jininta,wannan dalilin yasa HAJIYA'N cin *ALWASHI* (UMMI AISHA) gurin ganin bayanta...

Wannan kenan..........





*~#TEAM KHUBRA.~*





*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠



*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹





*©®2018*
*13/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*4⃣4⃣*




*T* un bayan da su KHUBRA suka bar gidan dukkanin wata walwala ta k'are a tare da BB zaman gidanma sam baya masa dad'i bayaga hakama babu wani abinci mai dad'i da suke samu a gidan dama-dama da ace d'aya cikinsu na nan to tabbas da sun samu abinci mai gina jiki musamman ma ace MR'S KHUBRA.
A duk lokacin da yaji bazai iyaba sai dai ya shirya tare da ficewa ranan ko gidan UMMI zai nufa a nan zai cika tumbinsa ba shi zai dawo ba sai dare shima sai dai kwanciyan bacci ne zai dawo da shi.
Tunda ya san sauran yaran babu abunda suka iya,ko da kuwa ace dafa lipton ne,sam basu san yaya tafasan sa yake ba,wannan lokacin ne kuma da dalilin yasa MAMA ta yanke shawaran ganin ta gyara musu rayuwansu gudun kada a zageta nan gaba (kun jifa fan's).
Sosai MAMA ta dage gurin yak'i da son jikinta ta kuma zage damtse gurin ganin hak'anta ya cimma ruwa tare da taimakawar BABA ZUWAIRA da har lokacin take zaune a gidan,dan MAMA sunyi ruwa sunyi tsaki akan baza ta komaba za taci gaba da zama da su har k'arshen rayuwa,duk lokacin da suka taso daga makaranta babu sauran zama a gurinsu gaba d'aya take tusasu a gaba su shiga kitchen bata tab'a rabuwa da su su huta sai dai ko idan akace lokacin sallah yayi ko cin abunci wannan kad'ai ke sawa ta d'aga musu leg.

《《》》

Sanye cikin brown en shirt da black trouser sai wani k'aton Timberland shoe brown colour dake k'afansa,idanunsa sakaye cikin black sun glasses ya ci mazuu,tafiya yake cike da k'asaita kamar kowane lokaci,yana tafiya yana kad'a car keys en dake hannunsa har ya k'araso bakin motan,a hankali ya bud'e sannan ya shige kamar wanda akawa wani abu ya fizgi motan a guje tun kafin ya isa bakin get en yaketa faman doka horn,a guje BABA ya bud'e masa tun kafin ya k'araso,a 220 ya bar wajen wanda ya bar BABA da mamakin irin wannan tuk'i da KHALEED ke yi a yau.
Fitansa daga gidan bai zame ko inaba sai gidansu KHALEEL wanda yanzun ya koma YAYA'N KHUBRA da ZUHRA.

Motansa na kunna kai cikin farfajiyan gidan idanunsa suka sauka akansu sunata guje-guje,sanye da k'ananan kaya kowacce ta had'e cikin colour en da ranta ke so,k'wallo suke bi a guje suna ihu.
Parking yayi a gefe yana kallonsu wanda su sam hankalinsu bai kawo kansa ba,ihun da KHUBRA tayi ne yasa shi dad'a maida hankalinsa kansu,gani yayi ta tsaya tana ta faman dira k'afafu da alama a koi abunda ya faru tsakaninsu,a hankali yayi k'asa da glass en dake side nasa,cikin murya kamar ta mai shirin yin kuka take magana
"Allah ban yardaba tun d'azun sai rinto kikemin dan kinga ban iyaba ko...."

Dariya sosai ZUHRA ta tsaya tana mata,kallonta KHUBRA tayi ta b'ata fuska had'e da fara matsar idanu tana shirin yin kuka,da gudu ZUHRA ta saki boll en ta nufo inda take,ganin haka yasa KHUBRA felle k'afafunta da gudu ta d'auke kwallon sai jin ihunta ZUHRA tayi tana ta faman doka tsalle kan itama ta ci..
Tsayawa ZUHRA tayi kafin ta juyo tana fad'in
"Allah nima ban yardaba ai ojoro kikamin,kuma Allah sai an sake ai ba cin tsakani da Allah bane kikayi"

Tsalle KHUBRA taci gaba da yi abunta tanawa ZUHRA gwalo,duk tsallen da take bata san yana kallontaba,waya ya ciro da niyyan kiran KHALEEL,idanunsa kuma har lokacin na kanta a hankali ya danna kiran had'e da d'orata a kunnensa,ring na farko ya d'auka
"Ya akayi ne MAN?"

"Gani na iso ka fito ina mota...."

"Lallai amma kai anyi d'an air gidan surukanka kazo ne da saina fito na maka jagora sannan zaka shiga?"

Ya tsina fuska yayi kafin ya bashi amsa
"Wa ya sani ne abu a duhu......MALAM idan zaka fito to idan kuma baza ka fitoba na k'ara gaba"

"To jarababbe gani nan fitowa kada kayimin masifa ni....."
K'it yaji tun kafin ya k'arasa maganan,a hankali ya kalli screen en sannan ya kad'a kansa,shi kad'ai yayi murmushi yana fad'in
"Naga ranan da zaka fara yiwa mutane magana da sanyin murya"
Da sauri kuma ya fice dan yafi kowa sanin halin mutumin nasa baya son jira.
A mota ya same shi ya k'ure volume yana ta faman jin 9ja music da suke playing one bye one daga gurin mawak'a daban-daban.
Bud'e motan yayi ya shiga,bayan ya zauna ne ya mik'a masa hannu suka yi musabiha,KHALEEL ne ya katse masa kallonta da yake ta cikin glasses en,juyawa yayi ya kalleshi sannan kuma a hankali ya zare glass en daga idaonsa
"MAN lafiya kuwa kake naga idanunka sun sauya colour,anya kuwa ba wani abu ke damunka ba ko jarabar ce ta motsa?"
KHALEEL ya tambaya yana kuma dad'a k'ure BB da ido duk dan ya gano damuwar tasa,murmushi yayi masa ta gefe d'aya
"Noopp!wani abu ka gani?"

"A'a babu komai kawai na ga ka canja ne kamar kana tare da damuwa"
Yana magana yana kuma kallonsa duk dan ya gasgata abunda yake damunsan,sai da ya kalli side ensa inda suke ta tsalle-tsallensu sannan ya kalli KHALEEL ya kuma yin wani murmushin
"No babu komai......kawai dai ina son......."
Sai kuma ya sake yin shiru
"Kana son me kuma?"
"Uhmmm!nothing.....Kawaifa maganar da mukayi da kai ne kan neman UNCLE a waya da mukayi akan zamu tuntub'e shi ko ya san inda ABBA yake"

"Ohhh!kaga kumafa ni wallahi har na mantama da maganar amma in sha Allah kam ya kamata ace tun kafin lokaci ya k'ure mu tuntub'eshi muji me zai ce mana ko....?"

"Yeahh!dama dai hakan yafi kamata muyi,amma.....yaushe kake ganin zamu same shi a wayan idan mun kira?......ina nufin wane time ne yake free babu hayaniyan aiki a tare da shi?"

"Emmm!ina ganin yanzunma yana gida........yanzunma ya kamata mu jarraba kiran nasa muji"

"Okk ka kira mana shi muji ko"

Wayan ya jima yana ring ba'a d'aukaba,kamar yadda suka jima suna kira har na wani tsayin lokaci,rashin sa'an samun sane yasa suka hak'ura akan zasu gwada wani lokacin.
Shiru dukansu sukayi kamar kurame can kuma KHALEEL ya kalli BB fuskansa da matsanancin farin ciki
"MAN ka san wani abu kuwa?"
Ba tare da ya jira ya amsa masaba yace "Ko da yakema muje gurin UMMI kawai akwai maganar da nake so muyi da ita kuma sai kana gurin zan iya mata magana"
Wani kallo BB yayi masa na rashin fahimta kafin ya bud'e motan ya fita,a baya shima ya bishi suna tafiya dai² zasu shiga parlor KHUBRA ta fello da gudu hannun KHALEEL ta rik'e tana fad'in
"YAH KHALEEL dan Allah kayi mana alk'alanci"

Tsayawa dukaninsu sukayi da sauri BB ya d'auke kansa daga kallonsu,sai dai yana sauraron abunda suke yi
"Haba k'anwata alk'alanci kuma nida ba school of law nayi ba,ina ni ina yin shari'a?"

Shagwab'e fuska tayi kamar za tayi kuka cikin muryan tab'ara take fad'in
"Shi kenan tunda kaima

Please Login or Register in order to submit comment