Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ya kama hanya cikin sauri don tsayar da ita tun kafin ta b'acewa ganinsu.

Cikin sauri yake bin bayanta wanda da k'yar ya samu ya isa bayanta a dai² lokacin da take k'ok'arin karkatawa ta shiga hanyan da zai sadata da cikin gari.
Sallama yayi mata yana daga bayanta dan yasan hakan dai shi ne kad'ai abunda zaisa ta tsaya.
Cikin sa'a kuwa ya samu ya tsaya tare da juyowa don ganin waye ne mai maganar duk da tasan hanyan babu mutane sosai,duba da yanayin da aka tashi da shi a garin.

Idanu KHUBRA ta bud'e sosai ganin fuskar dake tsaye gabanta,tunani ta d'an tsaya yi kanta d'age a sama tana son tuna inda tasan fuskansa.

Magana yake yi wanda sam ta kasa bashi amsa saboda yadda ta lula duniyar tunani,har sai da yayi magana da d'an k'arfi sannan tayi firigigit da dawo duniyar da take tare da fad'in
"Ammm!kace mene?"

Shiru yayi yad'an tsaya yana binta da kallon mamaki da kuma tunanin inda yasan mai wannan muryan,kallo sosai ya k'ureta da shi sai dai bai gano komai kan fuskartaba,dalilin daya katse shi kenan daga tunanin da yake.
Yana shirin yin magana BB ya iso gurin yana fad'in
"MAN lafiya ka zo ka zauna ka wani shanyani a jeji bayan kana ganin yadda garin yake"
Shiru yayi lokacin da ya k'araso ya gansu tsaye suna kallon-kallo tsakanin su.
Kallonsu yayi sun kafe juna da ido,a hankali KHUBRA ta maida kallonta kan BB da isowarsa gurin kenan,dad'a fiddo idonta waje tayi da sauri kuma ta maida kanta k'asa had'e da dafe chest enta jin yadda zuciyanta keta skipping kamar zai fito waje.

Tun daga sama har zuwa k'asa BB yake kallonta a zuciyarsa yake magana
"Ina nasan mai wannan kamannin?anya ko itance ko kuwa mafarkine nake yi?"
Sake kallonta yayi da yadda take tsaye jikinta na vibrating da gani kasan akwai abunda ya bata tsoro wanda yasa ta shiga yanayi irin na rashin gaskiya haka,da sauri ya katse shirun ta hanyar magana da ya sasu kallonsa
"Ammm!baiwar Allah taimako muke buk'ata"

Ba tare da ta kalleshiba ta furta
"Taimako akan me kenan?"

Sake kallonta yayi yanzun kam ya samu shaida ta biyu da take bayyana masa hasashen da yake yi akanta,abu d'aya yake nema don tabbatar da gaskiyar lamarin.
"Muna buk'atar ruwane zamu sa a mota,mun d'an samu matsala ne so motan yana can kan hanya"
Har lokacin duk maganar da yake yi yana yine idanunsa na kanta,yayin da ita kuma duk take jinta a takure saboda yadda take jin idanunsu a kanta.

KHALEEL ya koma kamar wani idol yayi shiru yana sauraren muryanta dake masa yawo cikin kansa,so yake ya tuna inda yasan wannan muryan,yayin da a b'angaren BB shima hakan take dan shi kam gani yake a yanzun yana da yak'inin itance da kashi 50%,babban abunda yasa bai gama amincewa da itanceba ganin yadda wannan take b'aka,ga yanayin suturan dake jikinta sannan ya tsinceta cikin yanayin da baya tunanin KHUBRA zata shiga.

Duk sunyi shiru har sai da yayi k'arfin hali tare da danne zuciyarsa kan lallaifa wannan ba waccan KHUBRA'N da suke tsammani bace,kawai dai yanayin halittane da kuma su d'in da suke cikin yanayi na rud'u yasa suke ganin kamar itan ce da gaske.
Kautar da tunanin yayi tare da fad'in
"Amm!ina fatan dai ba zaki damuba dan da d'an tafiya tsakanin nan da gurin da mukayi parking"

"A'a babu komai,muje kawai"
Ta fad'a tana juya akalar kuran nata da niyyan komawa bayan garin inda suka bar motan nasu.

A baya suka shiga binta tana tura kuran nata,duk wani motsi nata akan idanunsa hakan yake yana ankare da ita,suna tsaka da tafiyan ne wata matashiya ta taho kanta d'auke da robber yellow da alama daga rafi take ta gansu suna tafiya,kallon mamaki tabisu da shi kafin tayi magana
"A'a KHUBRA ina kuma zaki nufa haka bayan kin d'ebo ruwan kike k'ok'arin komawa"

Cak!KHUBRA ta tsaya a gurin kamar anyi pausing enta ba tare da ta k'ara one step forward ba.
"Shi kenan HAFSAT kin tonamin asiri,wayyyo Allah ka kawomin d'auki"
Abunda ta furta kenan k'asa-k'asa idanunta a runtse ba tare da tayi tsammanin wani cikinsu zaiji me ta fad'aba.

A hankali ya furta
"ALHAMDULILLAH ALAA KULLI HALIN!
ALHAMDULILLAHIL-LAZIIY BI NI'IMATIHI TATIMMUS-SALIHAT!!!"
Yanzun kam ya gama samun shaidan da ya bayyana masa itan ce dai wacce yake hasashe d'ari bisa d'ari yanzun ya tabbatar da hakan.
"Amma to ya akayi ta koma haka ne kam?"
Yayima kansa tambayan ba tare da tunanin samun amsa daga gare shiba.
Matsawa yayi a hankali ya d'auke hat en dake kanta tare da sake k'ureta da kallo,ko tantama baya yi yanzun kam daya ga fuskarta ya gama yin amanna akan yak'ininsa gaskiya ne.

"Why KHUBRA zaki nuna baki ganemuba a yanzun?me yasa?me yasa za kiyi haka??"
Cike da tsawa ya k'arashe maganar tasa.

Kuka ne ya kufce mata wanda daga ji kasan mai yinsa cike yake da fargaba da kuma tsoron halin da take ciki,ta jima tana kukan wanda su dake tsaye gurin suka kasa magana sai kallonta kawai da suke yi,ganin bata da niyyan dainawane yasa KHALEEL yin magana
"Ina tunanin yanzu kam ba kuka ne abunda ya kamata kiyi ba,godiya ya kamata kiyiwa Allah da yayi sanadiyyar had'uwarmu,kafin mu wuce gida kuma"

"A'aaaa!! babu inda zani........ni kam babu inda zani........bazan biku ko inaba.........kawai kuyi tafiyanku ku k'yaleni a nan.........bazan biku ba!"
Ta fad'a lokacin da kukanta ya dad'a tsananta,tana ta kuka mai tsuma zuciya.

HAFSAT dake tsaye har lokacin duk abunda ya faru akan idonta,duk wani furucinsu da maganganunsu ya tabbatar mata da akwai wata alak'a tsakanin wad'annan samari da *KHUBRA Y'AR GARUWA* ,cillli tayi da robber dake kanta take ta felle k'afafunta ta yanki hanya sai cikin gari,gudu take shek'awa wanda ba ita ta tsaya ba sai gaban BABA ZUWAIRA dake ta hada-hadar sallamar customer's,cike da haki take maganaa
"BABA kiyi sauri ga KHUBRA can a bayan gari da wasu samari sai kuka take yi kuma"

Ambaton sunan KHUBRA da tayi shi ya dakatar da ita daga abunda take yi ta mik'e tsaye cikin firgici dafe chest enta
"Y'ar nan maza sanar da ni inda kika ganta tun kafin wani abu ya sameta"
Cike da rud'ewa take musamman jin ance KHUBRA'N tana kuka shi ne babban tashin hankalinta saboda tunanin BABA ZUWAIRA a wannan halin samarin tareta sukayi zasu mata "FYA'DE".

HAFSAT a gaba BABA ZUWAIRA a bayanta yayinda tayi k'wallo da kayan abincin ta marawa HAFSA'N baya sunata faman fakaka sauri kamar wad'anda zasu tashi sama..

Kukanta take tuk'uru yayin da ta kuma jajirce kai da fata ba inda zata bisu itakam,suna tsaka da wannan tak'addamar su BABA ZUWAIRA suka iso gurin,har kuma lokacin ta kasa yin shiru daga kukan da take yi.

"Y'ar nan ina fatan kina lafiya"
BABA ZUWAIRA ta fad'a tana shafa jikin KHUBRA'N dake tsaye.

Da sauri KHUBRA ta k'ank'ameta tana sake sakin kuka
"Ni bazan bisuba,a nan zan ci gaba da zama gurinki"

Maganarta ta d'aurewa BABA ZUWAIRA kai cike da mamaki ta d'agota suna kallon juna ta kuma furta
"Yi shiru ki sanar da ni,ina ne baza ki bisu ba?"

"Gida zasu maida ni,ni kuma ba zan bisu ba,ni gaskiya a nan zan ci gaba da zama gurinki"


Kallonsu tayi d'aya bayan d'aya,sai yanzun ta soma d'aukan haske game da lamarin nasu da kuma inda maganar KHUBRAN ta nufa,cike da jin dad'in Allah ya kawowa y'ar tata k'arshen wannan rayuwar k'uncin take fad'in
"ALHAMDULILLAH!Lallai Allah shi ne abun godiya a kowane irin yanayi,Allah ya amshi rok'onmu da addu'o'inmu da muka jima munayi,Allah mun gode maka"
Idanunta d'auke da k'wallar farin ciki take ta magana,kafin talli KHUBRA
"Bai kamata muci gaba da tsaiwa a nanba,muje gida tukun sai muyi magana ina ganin hakan zaifi"
Fuskarta d'auke da wani irin expression da ba zai fassaruba suka mik'i hanya da niyyan komawa cikin gari,inda KHALEEL yayi saurin zuba ruwa a motan ya biyo bayansu dan su kam har sunyi gaba basu tsaya jiran shiga motaba....

《《》》

Shigowanta gidan kenan daga hospital,shima daga dukkan alamu ta dawone dan yin wasu uzurorin kafin ta koma.
Wayanta ne ya shiga kuka a parlor saboda nan ta ajiye hand bag en da ta shigo da shi yanzun,tana shirin shiga kitchen kasancewar gidan babu kowa duk yaran sun tafi skul saboda yau en ta kama monday ne shi yasa take ta komai cikin sauri duk dan ta kammala kafin dawowarsu.

Kukan wayan da ta jiyo shi ya fito da ita daga kitchen en cikin sauri ta d'auka dai² lokacin da kiran ya zama missed,d'an janye key en tayi sannan ta duba number da aka kiratan da shi,kafin tayi wani yunk'uri wani kiran ya sake shigowa cikin sauri ta d'auka
"Assalamu alaikum!SON mutanen DUTSE ince dai ba cewa za kayi kuna hanya ba ko?"

Sai da yayi wani murmushi mai cike da sauti wanda yake nuna yana tattare sa tsantsar farin ciki sannan ya amsa mata
"UMMINAH barka da safiya da fatan duk kuna lafiya"

"Lafiya k'alau muke SON ya mutanen gidan?"

"Wallahi suna lafiya UMMI duk suna gaidaku"

"Muna amsawa kun samesu lafiya dai ko?"

"Ehh!to lafiya k'alau dai za ace,amma dai kam UMMI KAKA ba shi da lafiya kuma ya jima cikin ciwon,ya jikin MAMA?"

"Too HAJIYA MURJA dai kam da sauk'i za ace,ammafa har yanzun tana nan kamar yadda kuka tafi kuka barta,bata san waye akanta ba ni kam wannan ciwo nata yana bani mamaki wollahi,yanzun jiran dawowarku nake muji yanda za ayi gaskiya ciwonta baya buk'atar a zuba ido hakanan,tunda nan en babu wani ci baba da ake samu"

"To UMMI in sha Allah muma muna nan kan hanya nan da anjima kad'an,yanzunma akwai wani abu ne mai muhimmanci da ya tsaidamu,amma idan mun k'araso za kiji labarin koma mene ne wannan abun"

Sai da tayi murmushi sannan ta ce
"To SON Allah ya kawo ku lafiya kuma Allah yasa muga Alkhairi"

Su duka sukayi dariya sannan ya amsa da "Ameen" yayi mata sallama akan sai sun k'araso...

《《》》

Yau tun da ta tashi jikinta yayi zafi saboda zazzafan zazzab'i data tashi da shi,kusan sati uku kenan tana fama amma ta kasa fita taje asibiti ko dan samawa kanta sauk'in ciwon dake damunta..

Shigowar babban mutumin kenan ya shiga cire kayansa kamar ko wane lokaci da hakan ya zame masa d'abi'a,da duk inda yaje ya dawo tofa yana shigowa zai hau tub'ewa kamar wani k'aramin yaro dake son mahaifiyarsa tayi masa wanka.
Saman gadon ya shiga haurowa yana shafata kafin ya d'age gefen duvet en data rufu da shi,cikin jikinta ya shiga k'ok'arin shigewa,ita kuma sai dad'a matsawa baya take saboda a yanzun kam bata jin zata iya tab'uka komai a rayuwanta,sosai ya manna jikinsu da juna duk uban zafin da jikinta yayi hakan bai hana shi fara abunda ransa ke soba,cikin wahalalliyar murya ta bud'e baki iya k'arfinta
"Dan Allah ka k'yaleni yau kam bana jin dad'i gaba d'ayafa kana jin yadda jikina yayi zafi ko wanka na kasa yi saboda rashin k'wari da jikina ke fama da"

Duk maganarta hakan baisa ya saurara mataba,saima shinshinata da yake yana wani fiddo da harshensa kamar kare tare da sakin wani irin numfashi.
"Kinsan dai a yanzu kam yadda nakai wannan matakin ba zan iya jurewaba,babu wani hak'uri da zan iya yi a halin yanzu,kawai dai kiyi hak'uri ki bani had'in kai mu ragewa juna zafi"

Ko d'aya cikin maganganunsa babu ko guda d'aya wanda ta iya ganewa saboda ta kai mak'ura gurin wahala,shi kuma duk da haka bai d'aga mata k'afa ya kyaleta ba,saima dad'a k'ok'ari tare da himma da yake gurin ganin ya cimma burinshi na biyan buk'atarsa.

Ba shi ya kyaletaba sai bayan da ya tabbatar da he is well satisfied,sannan ya sauka a kanta had'e da cilla mata damin kud'i
"Ga shinan kije kiga likita,ni fita zanyi idan kin dawo muyi waya"

Daga haka bai jira jin komai daga bakinta ba ya shige toilet en hotel en,har ya gama shirinsa ya fice MA'U na kwance ta kasa tab'uka komai kuma bata d'aga kai ta kalle shiba,da k'yar ta iya lallab'awa ta yi wanka shima jikinta sai kyarma yake haka dai ta shirya ta fice tare da kulle k'ofan ta nufi hospital...

《《》》

Lokacin da ya gama waya da UMMI yayi dai² da isowarsu k'ofar gidan,yana kallonsu suka bud'e gidan suka shiga,hakan ne yasa shi fitowa shima ya kulle motan sannan yabi bayansu.
A tsakar gidan ya tarar da su suna zaune kan tamarma sunyi jigum-jigum.
Guri ya samu ya zauna,sannan suka gaisa da BABA ZUWAIRA wacce KHUBRA ta kanainaye kamar wani yace zai tafi da ita duk ta hanata sukuni.

"Samari duk da dai ganinku nayi sama ta ka,hakan ba zaisa nayi saurin yanke hukunci ba,nasan dai duk inda akaje aka dawo kuna da alak'a da KHUBRA kuma alak'a mai k'arfi,duba da ganin yadda kuke kama da juna"

Kallon-kallo akayi tsakaninsu su uku kowa na burin gano abunda BABA ZUWAIRA ke fad'a a tare da d'an uwansa hatta da kuwa ita kanta KHUBRA dake kwance sai da ta d'ago tabi su KHALEEL da kallo.

"Tabbas ku en y'an uwane na hak'ik'a ko ban tambayaba nasan ku yayunta ne"
Tana magana da fara'a akan fuskarta tana kuma binsu da kallo,tun kafin BB yayi magana KHALEEL yayi tsalle ya dire da fad'in
"K'warai kuwa mu yayunta ne,tun bayan b'acewarta da muka yi neman bamu sametaba wanda ya had'a da jami'an tsaro a ciki,kaf cikin gari sai da aka dubata amma ba a ganta ba,ashema tana kusa-kusa damu kawai dai Allah ya nufa hakan dai sai ya faru"
Yayi shiru yana kallon BB daya kafe shi da kallo,ita kuwa KHUBRA kanta ta sauke k'asa tana sauraron maganganunsu.

"To ALHANDULILLAH tunda dai yau Allah ya nunamin wani naki KHUBRA kuma in sha Allah a yau ba sai gobe ba zaki bi danginki ku koma gida,saboda dama zamanki tare da ni ba shi ne mafi a'ala ba,ki zauna tare da danginki shi ne babban kwanciyar hankali kuma kema da su duk zakufi samun nutsuwa saboda kuna tare da juna.
Ni da kike tare da ni Allah ne ya had'amu kuma ina fatan Allah ya sake sadamu cikin amincinsa da alkhairinsa,yanzu zan baku labarin yadda akayi na samu KHUBRA da kuka ganmu tare"
Take ta shiga labarta musu yadda akayi suka had'u da zamansu tare tun daga ranar da ta fara ganinta kawo yanzun da suke zaune suna sauraronta ba tare da ta b'oye musu koda wasali ko harafi ba.
Jikinsu duk yayi sanyi kan irin wahalar da ta sha da irin rayuwar da tayi duk da kuwa sun ganta kan sana'ar tata,kallon tausayi had'e da al'ajabin yadda ta juri wahalar sana'ar suke binta da shi kafin daga bisani suka sako maganar tafiya da KHUBRA'N.

Haka BABA ZUWAIRA ta shiga d'aki ta had'a kayan duk data san na KHUBRA'N ne ta fito,tana d'an matse idonta da k'walla ta tarun mata.
Mik'ewa sukayi cikin shirin barin gidan,nanfa KHUBRA da BABA ZUWAIRA da suka ga dai tabbas tafiyar nan zasu yi,suka k'ank'ame juna suna kukan rabuwa da juna a lokacin da d'ayansu bai tab'a tsammanin faruwar hakanba.

KHALEEL ne ya ja BB gefe yana fad'in
"MAN baka jiba"

'Dan matsawa BB yayi jikin KHALEEL tare da kallonsa yana d'aga masa kai

"Gaskiya a shawarana ina ganin rabasu yanzun akwai damuwa duba da yadda suka shak'u da juna,ina ganin me zai hana mu tafi da su duka kaga ta wani b'angarenma BABA'N zata mana amfanifa ko kuwa me kake gani?"

Shiru BB yayi yana hasashen maganar KHALEEL en sannan kuma ya d'an daki kafad'ansa
"Yeahhh!ka kawo shawara mai kyau kawai muyi hakan"

Komawa gurin da su KHUBRA suke tsaye sukayi har lokacin suna manne da juna,KHALEEL yana y'ar dariya yace
"Ina ganin BABA da kun daina kukan nan haka nan,saboda mun yanke shawaran tafiya dakune duka"

Da sauri KHUBRA ta d'ago kanta ta kalleshi,shi kuma ya kad'a mata kai dan ya fuskanci so take ta tabbatar da abunda ya fad'a.
Aiko da sauri ta shiga gogewa BABA ZUWAIRA hawayenta itama ta goge nata tana dariya,cikin sauri ta shiga d'akin ta d'ebowa BABA ZUWAIRA kaya sannan suka d'unguma suka fice daga gidan,sai da ta shiga mak'otanta tayi musu sallama,tukun ta dawo inda ta barsu a k'ofar gidan jikin mota,daga nan suka shige tare da d'aukan hanya sai cikin gari wato cikin k'waryar KANON DABO.......................





*~#TEAM KHUBRA.~*





*_#REAL SMASHER._*
💠💠💠💠💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹





*©®2018*
*4/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*4⃣0⃣*






*"B* EAUTY me ya sameki kike kuka?wani abu yana damunki ne?"
BIGGY ne yake wannan maganar cikin rud'ewa yana tambayar ASHNA dake sunkuye ta had'a kai da guiwa sai risgar kuka take kamar wacce aka aiko mata da sak'on MAMA ta rasu.
Kukan da take yine ta kuma k'i bashi amsa yasa ya ajiye package en hannunsa,kusa da k'afafunta ya nemi guri ya zauna had'e da lank'washe k'afafunsa,fuskarsa cikin wani irin yanayi yake kallonta
"Please BEAUTY kiyi shiru hakanan ki daina wannan kukan kinji,yanzun fad'amin duk abunda kike so ayi kinji?"
Da sauri ta d'ago fuskarta da tayi kacha-kacha da hawaye tana kallonsa,kai ya d'aga mata alamar da gaske yake.
"Da gaske nake miki BEAUTY amma sai kin daina kukan nanfa kinji?"
Da sauri ta shiga goge fuskarta ta sake kallonsa had'e da d'anyin murmushi,aifa BIGGY wannan murmushin da ASHNA tayi masa ba k'aramin tafiya yayi da shiba take kuwa ya kafeta da idanu har bai sanma tana magana ba sai da tayi clapping a dai² fuskansa,sannan yayi saurin dawowa hayyacinsa yana fad'in
"Ammmm!BEAUTY me kika cene?"

Da d'an mamaki ta kalleshi wato dukma maganar da tayi bai san tana yiba kenan ko mene yake nufi?
Daurewa tayi ta fara magana cike da shagwab'a kamar tana gaban MAMA.
"Ni gurin MAMANA nake son zuwa.....Dan Allah ka maidani gida...Ina son na san halinda MAMATA take ciki...Please kaji"
Yanayin yanda take magana duk ta wani narke ita a dole y'ar lelen MAMA.

Ga BIGGY kuwa wani yanayi yake tsintan kansa aciki duk lokacin da tayi magana to shi kuma nan zaiyi da nasa kan dan duk inda ta lank'wasa kanta yana biye da nasa kan,yana faman zuba murmushi.

Tsuke fuska ASHNA tayi tana kallonsa da mugun haushi d'auke cikin idanunta kan yadda taga duk ya wani kafeta da ido.
"MALAM lafiya kake min irin wannan kallon?
Nifa kaga banson irin wannan kallon k'urillan haka kawai duk ka gano munin mutum,to gaskiya ya isheka haka"
Cike da tsiwa take maganar tana zabga masa wata uwar harara,dariya yayi mata wanda yasa farare tas en hak'oransa suka bayyana,dariyan da yayi shi ya bawa beauty point dake gefen kumatunsa lotsawa,take kuwa ASHNA ta saki baki tana kallon ikon Allah
"Ammafa GUY en ba laifi,duk da kasancewarsa bak'i,da wad'annan jajayen idanun nasa amma ai yana da hanci ga beauty point,wow inama ba cikin mugayen nan yake ba,kuma kyau ace yayi boko,omg ya zai kasance?"
Kanta ta d'an d'age tana son tuna ya wannan GUY en zai kasance,sai dai tayi murmushi had'e da fad'in
"Kaiiiii ammafa wollahi da ba k'aramin HANDSOME za ayiba"
Gintse fuska ta dad'a yi ganin yadda yake sake kallonta
"MALAM nafa ce maka ka denamin irin wannan kallon ko? har da wani yimin murmushi,ka rik'e abunka bance maka ina soba ai
Yanzu kawai ka fad'amin zaka mai dani gidanmu?"

"A'a BEAUTY bazan iya mai daki ba yanzu"

"Da Allah ni ka dena wani cemin BEAUTY tunda ba maidani za kayiba,kawai ka tashi ka bani guri"

Ko rufe bakinta bata yiba taga ya mik'e yana shirin barin d'akin,baki ta dad'a b'arewa tasa masa kuka.
Daf da bakin k'ofan ya tsaya had'e da rufe idanunsa lokacin da take kukan,da sauri kuma ya fice daga d'akin tare da rufe d'akin...

Fitowansa daga d'akin ya tsaya nan cikin corridor en,number HAJIYA LAURA ya shiga kira,bayan ta d'auka ya shiga labarta mata abunda suka yi ASHNA yanzun.

Ko gama rufe bakinsa baiba HAJIYA LAURA cikin tsawa ta dakatar da shi
"Nooo!BIGGY kadama ka kuskura ka tafka wannan d'anyen aikin,taya zaka biyewa wannan y'ar mitsitsiyar yarinyar
Baka gudun abunda zai je ya dawo ne hala idan ka maidata gida?
Ko kuwa baka tunanin gane fuskarka da tayi zai jawo mu fad'a hannun hukuma to gaskiya tun wurima ka kama kanka da wannan maganar
Sam hakan ba mai yiwuwa bane ina fatan ka gane"

Jiki a sanyaye yayi mata sallama ya kashe,nanfa BIGGY ya jingina jikin ginin gurin ya rufe idanunsa yana tuna irin yadda yarinyar ke nuna damuwarta da son ta koma gida ko don sanin halin da mahaifiyarta ke ciki.
Tambayoyi ya shiga yima kansa
"Shin mema yasa muke irin wannan aikin ga wasu mutanen da babu tausayi a zuk'atansu?ko don na rasa iyayena ne tun ina yaro shi yasa na biyewa irin wad'an nan mutanen suna sani aiki irin wannan,shin bana gudun ranar da Allah zai tashi kamani? Dame zanje masa wanda zan kare kaina a gurinsa?
Gaskiya ya kamata na nutsu.....Ina buk'atar shawara daga gurin wani......Ina buk'atar canja halayena.....To amma wa zan tunkara da wannan maganar?

Shi kad'ai yana ta magana da zuciyarsa,rashin samun maka yasa shi saita kansa sannan ya bar gurin jikinsa duk yayi sanyi saboda tunanin da yayi.

《《》》

Shigowar dattijon gidan kenan da sallama sai dai babu kowa tsakar gidan,hakan ne yasa shi tunkaran d'akinsa ya sanya d'an k'aramin key en ya murza tare da bud'e k'ofar yana mai kunna kai cikin d'aki.
Kan y'ar lank'wamammiyar katifan ya kwanta duk abun duniya ya dame shi,zuciyarsa duk babu dad'i haka yake jinta,haka dai ya juya ya kwanta cike da damuwa da ya rasa ta mene ne.

Lek'e ta shiga yi ta saman dangar karan dake kewaye da gidan duk burinta bai wuce ta hango cikin gidanba,k'ofar d'akin MALAM en ta hango a bud'e da alama ya dawo kenan.
A hankali cikin sand'a ta shigo gidan,wuf tayi ta shige d'akinta da ganin yadda take tafiya kasan babu gaskiya wai akace "awo a d'aka".


Please Login or Register in order to submit comment