Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Wuf tayi ta afka cikin d'aki tana dafe k'irjinta had'e da fad'in
"Waii Allah ya taimakeni MALAM bai kamani ina wannan sand'arba da yau kam ina da tabbacin komai zai iya faruwa"

Wata irin dariya ta tsinkayo a bayanta data sata saurin juyowa tana bin inda taji dariyan da kallo
Zaune saman gadonta na k'arfe ta hangoshi ya hard'e k'afafu kamar a fada
Tsoro ne ya cika mata zuciya,duk da tasan waye hakan bai rage mata tsoron da take cikiba.
Da k'yar take had'iyan yahu dan ta san ko me ya kawoshi a wannan lokacin,haka LADIYO ta shiga jan jiki har ta k'arasa gurinsa dan ta san bata isa ta bijireba,ko dan tsoron da take ciki,hakan ba maganin komai zai mataba.

A dai² lokacin da LADIYO suke tsaka da shek'e ayarsu da HATSABIBIN BOKA'N nasu ne shi kuma ABBA'N KHUBRA yake bacci mai cike da mafarkai da ya saba yinsu ko wane dare.

Cikin duhun dare cikin wani irin k'ungurmin daji da babu komai cikinsa face koke-koken tsun-tsaye da wasu halittun marasa dad'in ji.
Kamar daga sama ya tsinkayo muryar yarinyar tana kuka
"ABBA ka taimakeni....Wayyoo Allah ABBA zasu kashe ni....ABBA kada ka bari su cutar dani dan Allah"
Abunda ya iya jiyowa kenan shima cikin wani irin sauti da yake nuna ta gama galabaita ne take masa magana.
Yunk'uri yayi domin ya taimaka mata sai dai me ya kasa ko da taku d'aya saboda yadda yake d'aure jikin wani k'aton dutse,hannu da k'afafunsa duk suna sanye cikin ank'wa,wacce baya tunanin zai iya tsira daga gareta.

Hankalinsa a tashe saboda ganin yarinyar da yayi wasu irin mutane da baya iya hango fuskokinsu bare yasan su waye,sun rik'eta suna tunkarar wani k'aton rami da wuta ke ci a ciki da nufin jefata,ita kuma sai turjewa take tana waigowa tana kiransa kan neman taimako daga gare shi.

'Dagata sukayi da niyyan jefata,kafin su ida nufinsu suka fara jiyo gudu had'e da haniniyar dawaki,samari ne su biyu sun ratso ta cikin jejin haye bisa dawakai fuskokinsu rufe da k'yalle,iya k'arfinsu suka bud'e baki suna furta
"Laa-ilaha'illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz-zalimiiyn"
Fad'ar wannan kalmar babu b'ata lokaci yarinyar da ake k'ok'arin jefawa wuta,ta shiga maimaitawa cikin k'arfin hali da bud'e murya iyakar iyawarta.

Wutar dake ci cikin ramin tayi wani irin tasowa kamar an hurota,harshen wutan da yayiwo wajensu take ya laso su wutan ta kama jikinsu suka kama da wuta,sakinta suka yi a k'asa,sai dai abun mamaki wutan ko kad'an ita bai sametaba.
Cikin sauri d'aya daga cikin mahayan ya sauko tare da d'aukanta ya aza saman dokinsa ya haye shima.
Da gudu suka bar jejin inda take a nan shi kuma ya dena ganinsu sun b'ace b'at kamar iska.

B'acewan nasu ya dad'a jefa zuciyarsa cikin tsananin tsoro da fargaba,kamar daga sama yaji yo muryan yarinyar lokacin da take maimaita abunda taji wad'annan mahayan sun ambata.
Yunk'urin fad'a ya shiga yi shima,inda yana maimaitawa yaji ank'wan dake d'aure jikinsa ta zube k'asa,juyawa yayi ya kalli jejin gaba da baya sannan ya shiga shek'a gudu iya k'arfinsa ta hanyar da yaga sunbi,yana cikin gudun ya fara hangosu can nesa da shi,sosai yake gudun kamar wanda ya hau takalmin taya sai da ya kusa cimma mahayan duk da kasancewar suna kan abin hawa shi kuma yana k'asa,har ya fara murna kawai sai ji yayi ya daki wani irin dutse a gabansa da ya sashi fad'uwa a gurin,kansa ne ya daku da dutsen take idanunsa suka soma k'ank'ancewa saboda azaba...

A firgice ya farka jikinsa duk ya had'a zufa duk kuwa da yanda garin yake cike da iska saboda hadirin daya had'u a d'azun sai dai iska kawai ya bayar mai sanyin dad'i,amma shi gare shi duk ya jik'e da gumi.
Tunanin mafarkin da yayi ya tsaya yi,yana mamaki had'e da al'ajabin mene ne had'inshi da mafarkin?
K'wak'walwarsa ta dawo masa da maganganun yarinyar da yayi mafarki da ita,take ya tsinci kansa da fad'in
"Laa-ilaha'illa anta subhanaka inniiy kuntu minaz-zalimiiyn"
Maimaitawa yayi tayi cikin zuciyarsa,wanda k'arshe har kalmomin suka bayyana a fili.

Jiki a sanyaye ya mik'e daga gurin yayi hanyan fita daga d'akin zuciyarsa wasai babu zafi da kuma rad'ad'in da yake ji a baya.
Har ya d'auki buta zai shiga bayan gida ya dawo tare da ajiyewa a gefen randa,k'ofar d'akin LADIYO ya tunkara,kasancewar yasan su kad'ai ne a gidan ba tare da ya k'wank'wasaba ya kunna kai ciki da y'ar torchlight ensa da yake haska hanya da ita.
Mugun gamon da yayi yasa shi dafa bango saboda wani jiri da yake neman d'ibansa,cikin sauri kuma ya juya ya fice daga d'akin zuciyarsa na k'una.......

Tashin hankali kenan wanda ba a sa masa rana...

《《》》

Misalin k'arfe 1:40pm motan ta kunno kai cikin haraban gidan,har lokacin KHUBRA na lafe jikin BABA ZUWAIRA,baiwar Allah tana zaune sai kalle-kallen cikin gari take,har suka k'araso cikin gidin wanda had'uwa da tsarin gidan yasa take bin ko'ina da mamakin yadda akayi KHUBRA ta iya rayuwa a wannan k'ungurmin k'auyen nasu kuma har ta iya jurar wannan wahalar.
KHALEEL dake driven yayi parking sannan ya fita,inda BB shima ya mara masa baya yana fitowa ya ja k'ofan baya inda su KHUBRA suke,cikin taushin murya ya furta
"Bismillah"
Had'e kuma da nuna musu hanya suka fito KHUBRA rik'e da hannun BABA ZUWAIRA suka bi bayansa,KHALEEL a gaba BB biye da shi sai kuma su KHUBRA dake bi masa.

Ummi tsaye cikin kitchen tana gyara zaman warmer's en akan tire da take son fita dashi,gefe kuma basket ne shima da wasu had'ad'd'un Flak's,tana shirin fitowa sallaman su ta kawo kunnenta.
Da sauri ta fita tana fad'in
"Lale marhaban da Y'AY'ANA,gaskiyafa kunsha hanya"

Turus ta tsaya tana kallonsu ganin ba su kad'ai suke tafeba..
"A'aa da bak'i kuke tafe ashe,amma ya akayi baka sanar da niba da kayimin waya?"
Ta kalli KHALEEL cike da tuhuma,kunnensa ya d'an rik'e alaman ban hak'uri,murmushi tayi tare da fad'in
"Ai kaikam ka iya bada hak'uri idan kayiwa mutum laifi"

Kallon BB tayi da ya riga ya zauna tana k'arasawa dinning lokacin da ta ajiye tiren hannunta, sannan ta dawo cikin parlor
"Sannu SON kun sha hanya"

"Wallahi kuwa UMMI mun sha hanya,amma ai duk ga wanda ya jaa muka kawo yanzu bamu isoba,ya wani tsaya drive'n kamar d'an koyo"

"Oooo!nikam naga ranar da zaka fara drive'n a hankali,wato kaii dai kawai kafi son ayita shek'a gudu ko?"

"Yawwa UMMI ai haka shi ne magana"

"Uhmm Allah ya kyauta muku"

"Ameen UMMI'NMU"
Ya fad'a yana sakin murmushinsa mai kyau..

"Ooooo!kunga kun sani surutu daga zuwanku ko bak'in ban bawa gurin zama ba"
UMMI ta fad'a tana nufan inda su KHUBRA ke tsaye har lokacin sun kasa samun gurin zama.

"Bismillah mana kuna tsaye har yanzu"
Ta fad'a tana nuna musu sofa,k'in zama sukayi suka nemi guri nan k'asa kan rug BABA ZUWAIRA tana fad'in
"Nanma ya isa wallahi"

"Yawwa UMMI kin gane su kuwa?"
KHALEEL ya katseta lokacin tana shirin yin magana

"Yau kam kujimin yaro ta ina zan ganesu tunda ba bayani kuka yiminba"

Dariya ya tsaya yi yana fad'in
"Shi kenan UMMI tunda dai baki ganeba,amma bari ZUHRA ta dawo muga"

Shiru tayi tana kallon mutanen,haka dai suka gaisa ba tare da ta shaida mutanenba kuma bata tambayaba,kiran sallah ne ya katsesu daga maganar da suke yi kan haka ne suka tashi su kuma suka fice zuwa MASJEED ba tare da sunyi mata bayaniba.

_ AFTER FEW MINUTE'S._

ZUHRA ce a gaba sauran yaran na biye da ita bayan fitowansu daga mota lokacin da driver ya saukesu suka nufi hanyan parlor.
Da sallama suka shiga saboda hakan duk yana cikin irin warning da BB yayi musu kafin zuwansu gidan,kuma har ranar babu wanda yayi kuskuren aikata wani laifi,shi yasama duk abunda ZUHRA tayi to suma zaka samesu masu aikata hakan saboda gudun had'uwansu da shi.

KHUBRA dake zaune lokacin ta idar da sallah tana jiran BABA ZUWAIRA ta idar da salla'n ta jiyo sallama'nsu,amsawa tayi mai sallama ta shigo sannan yaran dake bayanta suka shigo suma,idanunta ne suka sauka kan KHUBRA dake zaune saman rug ai tuni cikin abunda baifi second's ba tayi cilli da jakan hannunta ta kwala wani k'ara lokacin ne kuma ta saki kuka dai² tana k'ank'ame da KHUBRA'N.

Kuka su duka biyun suke yi sun rik'e juna,dai² nan su BB suka shigo,tsayawa kallon ikon Allah sukayi kafin suka kalli juna suna kuma d'agawa juna kai da alaman tambaya a fuskokinsu
Dariya sukayi ganin yadda sukayi a lokaci guda,sannan suka k'arasa cikin parlor'n......

《《》》

Cikin hospital en ta shiga bayan ta amshi card,sannan ta jira layin ganin likita,lokacin da aka zo kanta bayan ta shiga gurin likitan,yayi mata tambayoyi tana bashi amsa.
Kallonta yayi sannan ya maida hankalinsa kan card en yayi y'an rubuce-rubucensa.
Bayan wasu y'an mintuna ya d'ago yana kallonta fuskarsa cike da wasu irin alamu.

Hankalin MA'U duk ya gama tashi tana kallonsa dan bata san mene ne zai fad'a ba a halin da ake ciki.
Cike da zak'uwa na son tasan me yake faruwa dan a lokacin kam har ta nemi ciwon ta rasa na wucin gadi

"Dan Allah likita ka sanar da ni abunda yake faruwa,wallahi duk na kasa samun nutsuwa saboda fargaban ban san me zaka ce yana damuna ba"

Dogon numfashi ya sauke sannan ya fara magana
"Ehhh!to bisa ga yadda dai kika yimin bayani,akwai abunda nake zargi game da ke,sai dai bazan tabbatar mikiba har sai kinje laboratory anyi miki gwajin jini"

Dumm!taji gabanta ya fad'i kanta ta sunkuyar k'asa,kome ta tuna kuma tayi dabaran saita kanta,sannan ta karb'i y'ar takardar dake hannunsa ta fita.

Da tambaya ta samu ta isa gurin gwajin jinin,bayan y'an mintuna data jira aka bata sakamako ta sake kamo hanyan office en likitan,tana tafe zuciyanta na tsinkewa haka har ta k'araso.
Knocking tayi daga ciki aka bata izinin shiga ta ko danna kai ciki,zaune yana ta rubuce-rubuce kan wasu file's.
Shigowanta yasa shi tattara wasu daga ciki daya gama amfani dasu ya nufi gurin wani vault ya zura,sannan ya dawo ya zauna had'e da amsan sakamakon nata.

Envelope en ya bud'e ya janyo takardar dake ciki ya shiga warwarewa,duk abunda yake yi idanun MA'U na kai tana sauraren jin me zai biyo baya.
Idonsa ya d'ago ya kalleta sannan ya sake yin rubutu saman card enta.
Muryarsa ta tsinkayo yana fad'in
"A sakamakon bincike da ya faru bayan hasashen da nayi hakan ya tabbatar mana da kina d'auke da.......................





_~Ina so nayi amfani da wannan damar gurin sanar daku fan's ba lallaine nan da kwanaki 3 kuga posting enaba saboda bikin friend ena da zamu fara,amma idan na samu sararin yin typing zaku jini in sha Allah, na gode.~_




*~#TEAM KHUBRA.~*





*_#REAL SMASHER._*
💠




*Y'AR GARUWA......*
*(ɬɧɛ mơʂɬ ɧɛąrɬ ɬơųcɧıŋɠ ʂɬơrყ).*



🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹





*©®2018*
*10/ʝųlყ,2018*



*ʂɬơrყ ąŋɖ wrıɬɛɛŋ*
*ცყ*
_HAWWA M.U {$мaѕнer}_
🕊🕊🕊🕊🕊
🌹🌹🌹🌹


_BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM..._
*~________________________~*
_Masoya ina baku hak'urin jina da kukayi shiru kwana biyu duk da dai na sanar daku dalilin faruwar hakan,amma ku k'ara hak'uri akan na da da kukayi..Na gode._
*~___________________________~*
_Wanna page en tukuici ne gareki y'ar uwata kuma k'awata,ina miki fatan alkhairi a duk inda kike na tayaki murna mara misaltuwa da wannan rana mai tarin alkhairi wacce tazo da sauyi a rayuwarki baki d'aya,ina addu'a tare da fatan wannan farin ciki ya ci gaba da tabbatuwa tare dake har k'arshen rayuwarki,ina miki murnan ganin rana mai cike da d'umbin tarihi rana da ta kasance ta aurenki tare da angonki,ina muku fatan dawwama cikin wannan farin ciki._
*SADIYA ISHAQ ISAH*
_DA_
*MUHAMMAD BILAL SHEHU*
_Allah ya baku zaman lafiya tare da hak'uri da juna.Allah kumavya kawo na y'an baya.Ameen thumma ameen._
*~___________________________~*


*DEVOTED TO:*
_BILKISU M.ADAM (Y'AR ABBA)_


*BESTOWED TO:*
_MURJA SALIS (NA'IKKE)._

*AND*

_FATIMA ABUBAKAR (FATEEY AFIRST)._





*4⃣1⃣*





*C* ikin parlor suka shigo kowanne ya nemi guri ya zauna suna jiran UMMI ta iso dan suyi mata bayanin abunda ke faruwa kan bak'in da suka zo da su.
Suna zaune suna kallon KHUBRA da ZUHRA da har lokacin sun gagara yin shiru,sai faman risgar kuka suke kamar wad'anda akawa mutuwa.
Babu wanda yayi musu magana kan kukan da suke,har sai da sukayi ya ishesu sannan kuma suka shiga kallon juna suna murmushi,lokaci d'aya suka kai hannayensu kan fuskokin juna suna goge hawayen dake fuskokin nasu,duk abunda suke yi BABA ZUWAIRA,BB,KHALEEL dama sauran yaran dake parlor'n akan idanunsu hakan ke faruwa illa UMMI kad'ai da bata nan.

"Wai YAYA ZUHRA wace wannan en da kuketa kuka ke da ita kuma me aka muku?"
FATAHIYYA tayi tambayar tana yamutsa fuskarta.

Sai da ZUHRA tayi murmushi sannan ta kalleta tace
"Baki ganeta ba ko?"

"To kema dai YAYA ZUHRA ta yayama zan santa,ni da ko ganinta ban tab'a yiba"

'Dan murmushi ZUHRA ta sake yi hannunta sak'ale cikin na KHUBRA sunata yiwa juna murmushi
"Uhmmmm!ba abun mamaki bane dan kince baki santaba ai
To ba wata bace wannan en face KHUBRA"

Mik'ewa FATAHIYYA tayi hannunta dafe da k'irjinta tana nuna KHUBRA'N,ko kafin ta kaiga yin magana UMMI ta fito tana maimaita sunan KHUBRA'N itama
"Yanzu dama doughter ke ce kika koma haka?har na kasa ganeki haka?"
Tana kallonta wanda babu komai cikinsa sai zallan tausayi da kuma ganin yadda ta koma cikin k'ank'anin lokaci duk ta yamutse kamar ba itaba.
Kusa dasu UMMI ta dawo ta kama KHUBRA'N tana kallo mamaki fal a tare da ita
"Ko tantama babu wannan KHUBRA ce,ku kuwa yaran nan a ina kuka samo mana ita?"

Parlor'n yayi shiru babu wanda yayi yunk'urin yiwa UMMI magana bare har tasa ran samun amsa daga bakinsu.

Ita ko BABA ZUWAIRA mamakinta baya wuce yadda KHUBRA'N take da y'an uwa masu sonta haka amma har ta daure tayi rayuwa tare da ita a cikin wannan k'ungurmin k'auyen,sai binsu da kallo take na sha'awa tana d'an murmushi.

"Wai SON a ina kuka ganota ne?"
UMMI ta sake yin tambayan a karo na biyu.

Sai da ya sauke dogon ajiyan zuciya kafin BB en ya d'ago daga danna wayan da yake yi.
Filla-filla ya warware mata yadda suka had'u da labarin da suka tsinta na irin rayuwar da tayi a k'auyen na ZAKIRAI har zuwa tahowarsu dasu ba tare da ya rage ko da wasaliba a maganarsa.

ZUHRA dake da rauni tun ana bada labarin take kuka kowa yana iya jin sautin kukanta a fili,yayin da ta dad'a k'ank'ame KHUBRA wacce ta sunkuyar da kanta k'asa tana saurarensu.
UMMI kam dauriya kad'ai tayi batayi kukanba amma kam zuciyarta ta gama karyewa,godiya take ta yiwa Allah da KHUBRA'N bata sanar da matar komai game da halin da take cikiba kafin b'acewar tata da asalinta ta barta akan su en family enta ne,lallai kuwa suma zasu nuna hakan har zuwa matar ta koma inda ta fito.

Jikin FATAHIYYA yayi sanyi sai kallon KHUBRA take tana goge siraran layin hawayen dake fuskarta,yau kam ta d'auki darasi cikin rayuwar KHUBRA da suka sakama k'ahon zuk'a kan ganin bayanta,a dai² lokacin ne kuma ASHNA ta fad'o mata,aifa nan ta shiga kuka sosai saboda da farko kukan nata ba mai sauti bane amma tuna y'ar uwarta ta jini da aka sace a kan idanunsu ya dad'a tada mata hankali wanda yasa lokaci guda sautin kukanta ya fito fili.
Babu wanda yayi yunk'urin hanata a cikin parlor'n saboda kowa da abunda yake ji a zuciyarsa.

*SOME MINUTE'S LEPT*

Bayan zaman alhini da sukayi na y'an mintuna sannan kuma suka soma shirin tafiya hospital,duk wani motsi da KHUBRA za tayi ZUHRA na biye da ita tamkar chewing gum haka ta zame mata,ita kam sai dai tayi murmushi idan ta kalli ZUHRA,su kansu sauran jama'an dake gidan suna mamakin wannan soyayya da shak'uwa idan aka cire BABA ZUWAIRA da bata san ainihin *GASKIYAR LAMARI'N* ba.

*AFTER 2 DAY'S*
Kimanin kwanaki biyu kenan da bayyanar KHUBRA wanda ko kad'an UMMI bata barinta ta bisu hospital duk kuwa da tsananin nacin da take yi kan bin nasu,sai yau da taga KHUBRA'N ta d'an soma washewa daga wannan azababben duhun da tayi na daud'a data manne mata a jikinta.
Haka suka kammala shiri bayan UMMI tasa KHUBRA sake yin wanka da sabulai masu kyau da k'amshi,sannan tun daga zuwanta gidan UMMI tasa ta cire tsummokaran dake jikinta wanda suka sauya mata halitta tamkar *Y'AR ALMAJIRA* bayan nan kuma suka d'unguma zuwa hospital...

《《》》

BIGGY zaune a parlor yanata tunanin maganar BEAUTY'NSA da har yau bai san takaimaman sunantaba,yau kimanin kwanaki sati guda kenan da tayi masa maganar tana son ya taimaketa ya maidata gida,kuma tun daga ranan ne bai sake komawa d'akinba sai dai ya aika a kai mata abinci.
Tunanin hanyar da zaibi ya magance duk wata damuwa dake neman kunno masa kai yake,yana nan yana tunani kiran HAJIYA LAURA ya shigo wayansa,kallon saman screen en yake ya k'ureshi da ido kamar mai son gano wani abu a jikin sunan dake lilo saman wayan,har kiran ya katse ba tare da yayi yunk'urin d'auka ba.
Yana kallo wani kiran ya sake shigowa wayan amma baiyi yunk'urin d'aukaba,haka tayi ta kira har ta gaji ta kyaleshi.

Tun safe yake gurin a zaune ba tare da yayi yunk'urin yin komaiba har misalin k'arfe 4:00pm sallah kad'ai ke fad'a shi a zaman gurin saboda duk iskancin BIGGY baya tab'a yadda sallah ta wuceshi,kamar wanda aka tsikara ya mike yana nufan hanyan bedroom en da take ciki.

Zaune take kamar kowane lokaci ta had'a kai da guiwa tana ta jan zuciya saboda kukan da ta jima tana yi.
Zama yayi a gabanta wanda yasa tayi saurin d'ago jajayen idanunta ta kalleshi tana jiran jin dame yazo yau kuma.
Kallon yanayinsa tayi duk ya wani koma silent da shi,kanta ta sunkuyar tana sauraron jin me zai ce.
Har kusan mintuna biyar ya d'iba yana zaune yayi shiru ba tare da ya iya furta komaiba,sannan yayi ajiyan zuciya cikin sanyin murya dake nuni da mai maganar yana tare da wani yanayi na damuwa a hankali ya furta
"BEAUTY dan Allah kiyi hak'uri da abunda ya faru,tun daga ranar da muka d'aukoki har zuwa yau da nake zaune a kusa dake ina son ki yafemin,tabbas shigowarki rayuwata ya sauyamin tsarina kuma ya canja ni gaba d'ayana,tun daga lokacin dana rasa mahaifana ban sake tunanin zan koma mutumin dake da tausayi a zuciyarsa ba ko dai² da d'igo d'aya amma zuwanki yana neman mai dani wani a rayuwa,zuwanki ya kawo haske cikin rayuwata,nayi alfahari da hakan ta faru,amma ina so kiyi hak'uri da abunda mukayi miki sannan".
Yayi shiru na d'an wani lokaci yana nazarin me zai fad'a kuma wanda zaisa tayi magana

Kallonsa kad'ai ta tsaya yi tana mamakin kalmomin da suke fitowa daga bakinsa,tausayinsa ne ya bijiro mata jin shi d'in marayane,wasu siraran hawaye ta goge tana d'aga masa kai ba tare da tayi magaba.

"In sha Allah daga yau babu wanda zai sake sani aikata irin wannan d'anyen aikin,rashin iyaye ba hauka bane da har wani zai dinga juyamin tunani ta har sani aikata ayyukan marasa imani"..

'Dan murmushi ASHNA ta sake yi tana sauraron maganarsa dake tafiya kai tsaye cikin zuciyarta

Tashi yayi da niyyan barin d'akin,wanda ASHNA sam bata san me yake afkuwa ba,saboda yadda take ta tunanin abubuwa da dama akansa,dai² bakin k'ofa ya dakata sannan cikin sanyi yace
"Ammm!ina ganin yanzun ya kamata kiyi shirin komawa gida,yanzun in Allah ya yarda zan maida ke"
Yana kaiwa nan a maganarsa yayi waje da sauri dan bata damar shiryawa.

Dariya game da hawayen farin ciki suka had'e mata lokaci guda,farin cikinta a wannan lokacin baya misaltuwa,cikin gaggawa ta kimtsa sannan ta fito daga d'akin rana ta farko tun bayan shiganta d'akin kenan da ta fito a hankali take bin corridor en tana wucewa har ta iso dai² stair's,sakkowa take jikinta yayi mata sanyi duk da tafi damuwa da son komawa gida,a parlor ta tarar da shi yana zaune ya d'ora hab'arsa a kan hannayensa da alama tunani yake,sai dai kuma sakkowanta yasa shi binta da kallo had'e da k'irk'irar murmushi,hakan ya tabbatar da baiyi nisa a tunaninba kenan.Mik'ewa yayi ita kuma tana binsa a baya har suka isa parking space na gidan,sai yanzun ta samu daman kallon gidan,babbane sosai ko dan da dare ne wancan ranan shi yasa bata iya tantancewaba.
A hankali ta d'age kafad'anta tana fad'in
"Ohooo ina ruwana a ciki wai kam???"
Kafin ta sake yunk'urin yin wani tunani har ya bud'e motan tare da mata nuni data shiga,babu musu ko ta shige shi kuma ya zagaya d'ayan side en ya zauna sannan yayi starting motan,cikin k'ank'anin lokaci suka fice daga gidan suka hau hanyan da zata sadasu da RIJIYAR ZAKI...

《《》》

Shirun da DR en yayi ne ya dad'a tada mata hankali to kuma me yake son sanar da ita haka,bakinta har rawa yake yi wajen son tambayarsa abunda ya gani a jikin result en nata.
"Dan Allah likita ka sanar dani abunda yake faruwa da har yasa kayi shiru kak'i sanarmin"

Wani ajiyan zuciya ya sauke sannan ya sake kallonta.
"No hajiya ba wani abu ke damunkiba kawai dai zazzab'i ne maybe kuma akwai abunda bakya amfani da shi da kika soma using nasa cikin y'an kwanakin nan,so ina ganin babu wata matsala,yanzun zan d'oraki kan magunguna idan yaso nan da wani lokaci idan bakiji sauk'iba sai ki dawo don a chanja miki da wasu"

Wani wawan ajiyan zuciya ta sauke sannan a hankali ta iya furta
"Ai ni wallahima DR har ka bani tsoro da kalamanka na farko kwata-kwata banyi tsammanin wannan ne abunda zai fito daga bakinkaba"

A kaikaice ya kalleta saboda rashin amincewa da maganar tata,shi kam baisan dalili ba da yasa yake mata wani irin kallo,saurin yin rubutu yayi ya mika mata card en sannan ya furta
"Hajiya ai babu abun tada hankali anan saboda jininki ya nuna 'NEGATIVE' da ya koma 'POSITIVE' ne zamu iya cewa akwai matsala"
Duk bayanin da yake mata ba wani gane negative da positive da tayi saboda bata san me hakan ke nufiba,murmushi tayi kawai ta amsa card en tana masa godiya sannan ta fice..

Bayan fitanta ya tsaya yana bin k'ofan da kallo,haka kad'ai

Please Login or Register in order to submit comment