Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana motsawa idan ya tayar mata kamar ba za ta yi raina ta dinga aman jini kenan. Sauƙin lamarin da suka samu da ake haɗa mata dana asibiti dukda da farko basu ɗauke shi da wani muhimmanci ba.

(Note: ku tuna shekara saba'in baya Al'ummar hausawa ba kasafai idan ciwo ya samu suke yarda da na asibiti ba. Wannan labarin a matsayin ya faru shekaru saba'in baya da suke wuce ne. 1951)

Sannu a hankali suka fahimci ci gaban da ake samu daga ciwon Maryo, kuma duk lokacin da ciwon ya tashi ana kaita asibiti bata ɗaukan kwanaki cikin ikon Allah take warwarewa. Sai dai abu ɗaya ne kullin Likitoci suke sanar musu da cewar yarinyar tana cikin matsananciyar damuwa, su dinga ƙoƙarin faranta mata. Wannan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yake ba domin gabaɗayansu babu wanda ya san ta yadda zai tunkari Maryo ya yi mata bayanin yadda za ta gane, idan ance maganar kurame za a yi mata babu idon da za ta gani ta hankalici abin da ake gaya mata. A hakan dai Me babban ɗaki take bakin ƙoƙari wajen zama kusa da ita da yi mata ɗan abin da ba a rasa ba.

A wannan yanayin ne har kwanakin auren su Salman suka zagayo. Shirye-shirye daga ɓangaren ta ko'ina sun fara kankama, Fulani Maryama sai shige da fice ake ana ta hada-hadar biki. Kamar wacce za ta aurar da ƴaƴa goma bata cen bata nan, ita ce gidan wannan Boka ita ce gidan wancen Boka. Duk wurin da za ta tafi ƙafarta ƙafar Jakadiya duk wani ƙulle-ƙulle tare suke yi. Fulani Maryama har sawa ta yi a yi wa iyayen yarinyar da Salman zai aura asiri, nan ne fa wani Boka suka je wurinsa ya kalli Fulani Maryama yace, "Buƙatar da kike nema ba za ta taɓa yuwu basaboda uwar yarinyar a shirye take fiye da tsammaninki, gara ma ki tsaya akan yarinyar wata ƙila idan kika mallake ta ki dinga samun alheri daga wurinta. Amma sam Mahaifiyar ba za ta mallaku ba." Fulani Maryama haka suka tarkato suka dawo ranar ba tare da ƙwarin gwiwa ba, amma a zuciyarta har lokacin bata jin za ta iya haƙura da ƙudurin da ke cikin zuciyarta. Daga wurin Fulani Zaliha sosai ta dage tana shirya Abu da kayan gyara kala-kala, sai dai gabaɗaya ta rame ta zabge saboda a kullin sai maganganun Inna Habi sun dawo mata tsakiyar ka. Ramar da ta yi ba ƙaramin damun Fulani Zaliha ta yi ba kullin ta tambayeta abin da yake damunta sai dai ta ce mata babu komai. Wannan dalilin ya sa Fulani Zaliha take tsammanin ko damuwar rabuwa da iyaye ce, tun yawanci duk amayar da za a yi aurenta sai ta yi wannan ramar.

Lokaci na ƙara ƙaratowa baƙin ciki na ƙara cunkushe zuciyar Inna Habi, wani abu da yake ƙara ɗaga hankalinta yadda take munanan mafarkai da Maryo. Tun abin baya damunta har tashin hankalinta ya ruɓanya, a takaice abin har ya kai ya kawo bata iya baccin kirki. Saura Sati guda Ɗaurin aure lamarin ya addabi zuciyar Inna Habi, a wata safiya ta fice daga sashen Fulani Maryama kai tsaye ta wuce fadar Sarki Aminullah. Russunawa ta yi a gabansa cikin girmamawa ta kwashi gaisuwa. Sannan ta ɗora da cewa, "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai ina neman izini akan a yarje mini tafiya Masarautar Adamawa." Kallonta ya yi ya numfasa yace, "Ko akwai dalilin zuwan?" Idanun Inna Habi ne ya kawo ƙwalla ta sa gefen mayafinta tana share ƙwallar ta ce, "Allah ya taimake ka kusan kullin ina yawan munanan mafarki da Maryo shi ya sa nake son zuwa na gano halin da take ciki." Sarki Aminullah yace, "Idan kin yi haƙuri rana ita yau tuni sun zo gidan nan biki." Ba haka ta so ba sai dai babu yadda ta iya, jiki a sanyaye ta russuna ta yi masa godiya ta koma sashensu, tana zuwa ta faɗa ɗakinta ta fara sakin kuka mara sauti gwanin tausayi.

Fulani Fahima yadda take farinciki da shirye-shiryen tafiya sai ka rantse auren Maleek na farko za a yi. Saura kwana huɗu biki ta haɗa kayanta tsaf aka haɗa mata kekunan dokuna. Zaune take a ɗakin Me babban ɗaki lokacin Maryo na kwance idonta a rufe da alama bacci take yi. Me babban ɗaki ta kalli Fulani Fahima ta ce, "Audullahi yace wai za ki tafi da yarinyar nan Ƙasar Kano, sam ban lamunce ba. Ba za ki ɗauki yarinya ki ɗaukar mata baki ba ayi ta tanka ta ana cewa lalura ta same ta ba. Idan kin je an tambayeta ki ce ita da Audulmaleek sun yi tafiya." Fulani Fahima sam bata so haka amma sai ta gyaɗa kai ta ce, "Shikenan Ranki shi daɗe yadda kika ce haka za a yi." Daga haka ta miƙe ta fice daga ɗakin, babu jimawa aka fito da kayanta ita da ƴar Autarta Zuhra suka shiga rumfar dokunan suka ɗauki hanyar Ƙasar Kano.

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[17/12/2021, 15:28] Ameera Adam🌚: 50...



Inna Habi tun da ta ji labarin zuwan su Fulani Fahima ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda murna da farincikin za ta yi tozali da Maryo. Farincikinta har ya gaza ɓuya ƴan matan Bayin har tsokanarta suke suna yi mata tsiya, saboda yawanci sun ɗauke ta kamar kakarsu. A ɓangaren Abu kuwa tun da ta ji labarin su Fulani Fahima za su zo duk ta firgice, gabanta ban da faɗuwa babu abin da yake yi tana fargabar haɗuwarsu da Maryo da irin kallon da za ta yi mata. Sai dai ta yi imani da Allah duk ma juyin da za a yi bata jin za ta iya sadaukar da soyyayar da take wa Saif. Lokacin da su Fulani Fahima suka sauka haka ta dinga gaya musu Maryo lafiyarta ƙalau sun yi tafiya da Maleek amma bayan kwana biyu za su zo su yi Allah sanya alheri. Inna Habi sam ba ta ji daɗi ba don ta sawa zuciyarta ganin Maryo da halin da take ciki, amma kuma sai ta ji damuwarta ta ragu saboda ko ba komai ta fahimci Maryo na cikin kwanciyar hankali, tun da har ta saki jikinta tana bin Mijinta suna tafiya wuraren aikinsa. Da ƙarfi ƙirjinta ya buga sakamakon tunowa da cikin jikin Maryo da ta yi, a hankali ta furta, "Amma lamarin da mamaki ace duk waɗannnan watannin da aka kwashe ace har yanzu cikin jinkinta be bayyana ba. To ko ya zube ba tare da wani ya fahimta ba." Hannu biyu ta ɗaga sama tana addu'ar cikin jikin Maryo ya zube a gefe ɗaya kuma tana fargabar mummunan laifin da ta aikata, domin a ranar Juma'ar satin da ya gabata Sarki Aminullah ya yi tunantarwa dangane da, muhimmancin aure da ladabbansa tare da albarkar auren, a cikin hakane har ya gangaro kan iyayen da suke ha'intar mazan ƴaƴansu ta hanyar kwantar da cikin da wasu daga cikin iyaye suke yi idan ƴaƴansu suka samu cikin gaba da fatiha. Ya yi tunatarwa me za fi har sai da Inna Habi ta sharce ƙwallarta har ta ci alwashin samun Sarki Aminullah ta sanar da shi babban kuskuren da ta aika ta dangane da Maryo da Abdulmaleek. A wannan lokacin duk yadda Inna Habi ta so ganawa da Sarki Aminullah abun ya faskara saboda baƙin da yake yawan karɓa, don haka ne ta ajiyewa zuciyarta ana gama bikin su Saif duk halin da ake ciki sai ta samu Sarki Aminullah da maganar in ya so sai a gyara aurensu ta hanyar tantance ta tare da sake sabon ɗaura aure. A ɓangare ɗaya ko kaɗan bata jin wani farinciki dangane da auren Abu da Saif sai dai tana ta yi mata addu'a akan Allah ya tabbatar da alheri ya kuma ba su zaman lafiya. Saboda ita uwa ce bakinta kamar kaifin wuƙa ne ko yaya ta faɗi kalma mara daɗi akanta ta tabbata ko ba daɗe ko ba jima sai ya kamata. Don haka ta fauwalawa Allah lamuranta take yi mata addu'a domin ta san komai muƙaddarine daga ubangiji.

Fulani Maryama kai ya fara ɗaukan zafi saboda baƙi daga ɓangare daban-daban take karɓa, gidan ba ƙaramin cika ya yi ba. Haka daga ɓangaren Fulani Zaliha sashenta cike yake da mutane sai dai gabaɗaya ta killace Abu a ɗakinta ta hana kowa shiga ɗakin a cewarta ba za a kalle Amarya tun kafin lokacin bikin ya zo ba. Ango Saif ba ƙaramin damuwa ya shiga ba saboda rashin ganin Abu ya jefa zuciyarsa cikin damuwa, saboda tun lokacin da aka tsayar da lokacin bikinsu Fulani Zaliha ta hana shi ganawa da Abu, duk yadda zai yi ya ganta su yi wata hira ta hana, ko da zai ganta sai dai idan yaje gaishe da Mahaifiyarsa. Ranar da aka yi kamun amarya da Ango ba ƙaramin tafiya hankalinsa ya yi akan Abu ba saboda wani irin gyaran jiki da aka yi mata. Ban da sheƙi da ƙyalli babu abin da take yi ga wankan lalle da aka yi mata haɗe ta waɗansu irin turararru masu masifar ƙamshi. Fulani Maryama haushi ne ya kamata ganin babu Salman a cikin kamun saboda Amaryarsa na masarautarsu bata kai ga ƙarasowa ba, da aka ce kuma za a yi musu kamun har shi a fusace yace baya buƙata ya fice daga gidan gabaɗaya. A daren ranar da aka yi kamu Saif ya kira Baiwa Laraba bayan ɗakin Fulani Zaliha, tana zuwa ta same shi a tsaye sai zarya yake kamar wanda ya yi wa Sarki ƙarya. Dukda duhun magriba be hana ta russunawa cikin girmamawa tana faɗin, "Allah ya taimake ka ranka shi daɗe an ce kana buƙatar gani na." Be ɗago ya kalle ta ba yace, "Ki kawo mini Zainab nan yanzu nan." Gabanta ne ya faɗi a firgice ta ɗago ta kalle shi ta ce, "Amma Ranka shi daɗe Fulani..." Ɗaga mata hannu ya yi saboda ya san ƙarashen labarin ba zai wuce a ce Mahaifiyarsa ta hana a fita da ita, don haka ya kalle ta fuska a tsuke yace, "Umarni ne na baki idan har aka kuskure mini na rantse har da Allah sai ranki ya mummunan ɓaci. Ki san dabara da za ki yi ki kawo mini ita." Baiwa laraba ta gyaɗa kai jiki na rawa ta wuce sashen Fulani Zaliha zuciyarta na zullimin ta yadda za ta kaiwa Saif Abu ba tare da asirinta ya tonu a wurin Fulani Zaliha. Tana shiga sashen Fulani Zaliha fara kame-kame da shige da fice, tana nan tsaye ta ga fitowar Abu sai dai tana shirin yi mata magana ta ga Amintacciyar Baiwar Fulani Zaliha tana biye da ita, gumi ne ya shiga keto mata kamar mara gaskiya saboda ta san Falmata amintacciyar Fulani Zaliha ce, duk wani abu bata iya ɓoyewa shugabar tasu saboda ba a taɓa haɗa kai da ita a ha'ince ta. Baiwa Laraba na tsaka da tunani ta ji Fulani Zaliha ta ƙwalawa Falmata kira, da sauri ta juya hakan ba ƙaramin faranta ran Laraba ya yi ba. Da sauri ta ja hannun Abu ɗakinsu Abu za ta yi magana Baiwa Laraba ta yi ƙasa da murya ta ce, "Allah ya taimake ki Me girma Saif yana bayan ɗaki yana jiranki don Allah ki yafa mayafin Bayi domin ɓadda kama, idan ban raka ki ba zan fuskanci mummunan ɓacin rai." Wani sanyin daɗi ne ya ratsa zuciyar Abu har sai da ta bayyana a fili, sauke wata nannauyar ajiyar zuciya ta yi ta ƙarbi mayafin me ɗauke da launin kayan Bayi ta yane kanta ta yadda ba za ka taɓa tsammanin ita bace. Har sun yi hanyar waje Laraba ta dawo da sauri ta janyo ƙauren banɗakin kamar da mutum a ciki ta rufe sannan suka tafi. Suna ƙarasawa Baiwa Laraba ta ce, "Allah ya taimake ka ya baka yawan rai a hanzarta domin Kar Fulani ta fahimci bata nan a samu matsala, amma a gafarce ni idan maganata ta yi kaushi." Kai ya gyaɗa mata yace, "Je ki zan neme ki." Tana tafiya ya ƙarasa wurin Abu da ke lulluɓe cikin mayafi sai zuba ƙamshi take, zame mayafinta ya yi zuwa wuyanta ƙamshin turaren jikinta ya ƙara dukan hancinsa. Lumshe idanunsa ya yi na ƴan sakanni sannan ya ware manyan idanunsa yana kallonta, kallon da yake mata ne ya sa ta ɗan tsargu har ta ɗago ta kalle shi, karaf idanunsu ya sarƙe da juna. Kashe mata ido ɗaya ya yi sai kuma ya shagwaɓe fuska yace, "Laifin me na yi? Me ya sa aka zaɓi haka domin azabtar tsokar da ke ɗawainiya da soyayyarki? Yau kusan tsawon wata biyu ban samu na yi tozali da kyakkyawar fuskarki ba." Abu sunkuyar da kai ƙasa ta yi tana jin bugun zuciyarta na tsananta saboda yadda kalamansa suke ratsa sassan cikin jikinta. Hannu ya sa ya ɗago haɓarta (Haramun ne) sai kuma ya janye hannun nasa da sauri saboda yadda ya ji wani irin yanayi da be taɓa jin irinsa ba. Jin ta yi shiru ya sa ya hura mata iska a fuska, cikin wani irin yanayi ta lumshe idonta Saif ya yi murmushi me sauti da sauri Abu ta ware idonta cikin jin kunya, ta shagwaɓe tana faɗin, "Ya Saif kar fa Ammi ta jini shiru." Ɗaga kafaɗarsa ya yi alamun rashin damuwa yace, "Sai ki ce mata kin je wurin mijinki." Da sauri Abu ta zaro ido ta ce, "Ammin zan gaya wa haka?" Murmushi ya yi yace, "Meye a ciki jibi ya rage ɗaurin aure fa." Juyawa ta yi za ta tafi da sauri ya sha gabanta yana ware hannuwansa, ɗan ɓata fuska ta yi haɗe da shagwaɓa ta ce, "Ya Saif Allah ka barni na tafi ni ba zan iya wannan rashin kunyar ba, idan aka ce mata an gammu ya zan yi?" Matsowa gabanta ta fara yi tana ja da baya har ta jingina ta bango ya matso gabda ita, har sai da ta kai suna jin numfashin juna yace, "Zainab!" Muryarsa ba ƙaramin kashe mata jiki ta yi ba a hankali ta ɗago ta kalle shi, shima ita yake kallo ya ci gaba da cewa, "Don Allah karki ƙara guje mini." Hannu ya ɗora a saitin zuciyarsa ya ci gaba da faɗin, "Rashin ganinki ba ƙarmin raunatar da rihina yake ba, ki yi mini alƙawarin duk daɗi duk wuya ba za ki guje mini ba domin ba zan iya jure rashinki ba." Abu ɗagowa ta yi ta kalli Saif tana jin wata irin ƙaunarsa na fisgarta, gyara tsayuwarta ta yi tana cewa, "Ya Saif! Kamar yadda jini yake da matuƙar tasiri a garkuwar jikin ɗan adam haka soyayyarka take zaga jini da tsokar jikina, ni ta ka ce bana tunanin akwai abin da zai kawo rabuwarmu idan ba mutuwa ba. Don Allah duk a halin da za mu kasance ka da ka guje ni saboda rashinka tamkar rasa numfashin da ke maƙale a gangar jikina ne. Ina neman alfarma a wurinka ban sani ba ko ina da wannan ƙimar a wurinka? Ban sani ba ko mutumci da darajata ta kai haka?" Hankali a tashe ya ɗago ya kalle ta bakin sa har rawa yake yace, "Wacce irin buƙata ce wannan faɗe ta matuƙar bata samawa mahalicci ba ni kuma na yi miki alƙawarin sai na biya miki ita." Abu ta ƙara narkewa tana narai-narai da idanu ta ce, "Don Allah ka da ka haɗa soyayyata da ta wata, ban zan iya ganinka da wata mace ba, wallahi ba zan iya jurawa ba saboda ina matsanancin kishinka bana jin zan iya jurar ganin ko da wata ta raɓi inuwarka ne " Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Wallahi ba ƙaramin faɗar mini da gaba kika yi ba, na ɗauka wani muhimmin abu za ki nema a wurina. Indai wannan ne na yi miki alƙawari babu wata ƴa mace da za ta kaiki koda da ƙwayar zarra ce a wurina." Baiwa Laraba ce ta ƙaraso wurin jiki na rawa ta ce, "Allah ya taimke ka Fulani na cen tana cigiya don Allah ayi mini rai na mayar da ita." Saif zai yi magana da sauri Abu ta wuce gaba ta ce, "Mu je Labara don bana son a samu matsala Ammi ta yi fushi da ni." Babu yadda ya iya yana ji yana gani haka suka wuce, wani irin farinciki yake ji a zuciyarsa tare da fatan Allah ya nuna masa ranar ɗaurin aurensu lafiya.

Abu na shiga soron gidan ita da Laraba suka yi dabara wuuf ta faɗa banɗaki, ba ta daɗe a ciki ba ta fito ta wuce ɗaki. Da kallon tuhuma Fulani Zaliha ta kalli Abu fuska a ɗaure ta ce, "Daga ina kike?" Abinka da mara gaskiya nan take ta fara kame-kame ganin haka ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Wurin Saif kika je ko? Labari ya isa kunnena ance mini an gan ku tare. Karki manta nan fa gidan sarauta ne ko tusa kika yi me ƙarfi ana ankare da kai. Amma tun da na ga kamar kun matsu bari na je na samu Takawa nace ya tara mutane a ɗaure auren a daren nan kawai yanzu an gangaɗa akai ki kowa ya huta." Zaro ido waje Abu ta yi idanunta na cikowa da hawaye hannu bibbiyu ta durƙushe a wurin tana faɗin, "Don Allah Ammi ki yi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba." Ganin yadda hankalin Abu ya ta shi ya sa Fulani Zaliha ta ce, "Shi ke nan je ki amma sai na yi nazari." Ƙara marairaricewa Abu ta yi ta ce, "Don Allah Ammi..." Fuska ba walwala Fulani Zaliha ta katse ta, "Ki wuce ɗaki akwai tukuɗin da na dama miki." Sum sum sum Abu ta wuce ciki jiki a sanyaye.


Ranar juma'a wanda ya yi daidai da goma ga watan Jumada-Awwal a shekara ta dubu ɗaya da ɗari uku da saba'in da uku (Juma'a 10, Jumada-Awwal, 1373) wanda a kalandar bature ya yi daidai da sha huɗu ga watan sha biyu a shekara ta dubu ɗaya da dari tara da hamsin da ɗaya. (14/12/1951) Dubbanin mutane daga garuruwa daban-daban suka shaida ɗaurin auren Salman da Safiyya sai auren Saif da Abu, farin ciki wurin Sarki Aminullah abun baya musaltiwa. Mutane daga garuruwa ne suka halarci taron auren, har da baƙin turawa suka zo taya shi murna daga Ƙasar Ingila. Babu jimawa aka shiga kaɗe-kaɗe da wasannin Al'adu na gargajiya abun sai wanda ya gani gwanin burgewa. Duk wani abu na kayan auren an haɗa wa Abu wanda dangin gidan maza suke yi. Haka kayan ɗaki da duk wasu kayan al'ada da ake yi wa Ƴa mace Sarki Aminullah ya yi wa Abu, daga bayan gidan Sarki aka zaɓawa Saif da Salman wasu gidaje guda biyi iri ɗaya, sai dai suma gidajen suna cikin masarautar, haka ita ma Safiya ba ƙaramar dukiya iyayenta suka narka mata ba. Duk wani shagali da ake yi Salman baya farinciki da shi. Hasalima idan ka dube shi da kyau za ka fahimci sam auren kamar baya gabansa.

Ranar da aka yi ɗaurin auren a ranar ne aka ɗauki amarya aka kaita ɗakin mijinta, Abu ta sha kuka sosai musamman da Mahaifiyarta take yi mata nasiha akan biyayyar aure, "Abu ki buɗe kunnenki da kyau ki ji ni, yanzu wani nauyi ya rataya a wuyanki me girman gaske. Igiyar aure ba abar wasa bace saboda matartabar da matar aure ke da ita ta ninka ta wacce bata da aure idan har ta riƙe mutumci, ƙima da martabarta. Ki sani ba soyayya kaɗai ita ce jigon aure ba, domin kar ki ɗauka yadda kuke soyayya a gida haka za a ɗore har cikin gida. A'a sam akwai bambamci saboda lokacin da ake waje neman fahimtar juna da samun kyakkyawar alaƙa a tsakani ake yi. Ya yinda aka yi aure kuma haƙuri da soyayya sune suke taka muhimmiyar rawa a zamatakewar aure. Yi na yi bari na bari ladabi da biyya sune jigo, haƙuri garkuwa ne kulawa ɗa'a ce godiya da girmamawa Tarbiyya ce. Duk abin da mijinki zai baki ki yi masa godiya zaman aure zo mu zauna zo mu saɓa ne, ba kodayaushe ake cikin farinciki ba. Wataran idan namiji ya guma miki sai ki ji duk duniya babu wanda ya tsaneki kamar shi, watarana kuma idan ya faranta miki ji za ki yi duk duniya babu wanda yake ƙaunarki fiye da shi."

(Gara dai mu dinga gayawa ƴanmatanmu gaskiya 😂😂😂 ba wai kullin ace yayi kissing da romance da wacce tsiyar ake a gidan aure ba, wallahi duk wacce take ɗaukar huɗubar ƙaryar novel tana ruwa, ban ce kowacce soyayyar novel ƙarya bace amma akwai soyayyar da ke kanki idan kika karanta kinsan wacce zata faru da akasin haka. Ko munƙi ko munso Aure ɗan haƙuri ne duk fallin da wasu ƴan matan suke yi ba su shiga bane, saboda suna karanta littafi su ji ance bayan ta yi sallar asuba bata tashi ba sai sha biyu kafin ta tashi mijin ya gama komai tana tashi sun faɗa banɗaki an yi awa uku a toilet ana harka da soyewa 😂😂 ban da yaudarar kai wacce uwar za a yi shafe sama da awa uku ana yi a toilet? Wallahi mazanmu babu wanda zai yadda ki miƙe kullin a gado ace ya gama miki komai kina miƙe sai dai ya ruƙo hannunki ku faɗa toilet. Amma idan da me ja wata ta gwada gobe ta bamu labari 😂😂😂😂 Billahi na san karon ba zai yi da daɗi ba.🤣🤣)

Abu ta ci kuka sosai haka ita ma Inna Habi har da share hawaye saboda rabuwar da za su yi da Abu. A ranar da aka kai Abu tare da wasu tsirarun ƙawayenta suka kwana saboda bisa ga al'ada hakan ake yi ga duk amaryar da aka kaita ɗakin mijin. Washegari aka yi buɗar kai tare wasu shagulgulan tsakanin ƙawayen amarya da ƴan tsirarun abokin Ango Saif saboda abokanansa biyu jal Huzaif da Haris, sune suka gayyato nasu abokan suka rufa musu baya. Washe garin buɗar kai Ango Salman ya shiga ɗakin amaryarsa Safiya haka daga ɓangaren Saif shima ya shiga ɗakin Amaryarsa tare da rakiyar abokansa. Shi kuwa Salman dama ba shi abokai shi kaɗai yake yawo kamar maye. Yana shiga ɗakin Bayin da ke zaune da Safiyya suka tashi suka fice, Salman gadan-gadan ya ƙarasa kan gadon ya janye hular alkyabbar jikin Safiyya. Dukda baya wani farinciki da auren amma ganin yadda Safiya ta sha kwalliya ba ƙaramin tafiya ta yi da shi ba, rungumota ya yi jikinsa yana shaƙar ƙamshin jikinta da aka wanketa cikin azababbun turarruka masu matuƙar ƙamshi. Ganin lamarin Salman na neman wuce gona da iri ya sa Safiya ta tattara ƙarfinta ta ɗan ture shi ta ce, "Yarima me ye haka?" Cikin kasalalliyar murya yace, "Me kika gani da idonki? Haƙƙina zan karɓa" Haushi ne ya kama ta ta ce, "Ko za ka karɓi haƙƙinka ai ka bi komai a sannu." Salman be jira cewarta ya fisge alkyabbar jikinta ya shiga neman ƙwatar haƙƙinsa.

Da sallama ɗauke a bakinsa ya shiga ɗakin, daga bakin ƙofa ya tsaya ya harɗe hannuwansa yana kallonta cikin farinciki. Jin shiru babu alamun takowar mutum ya sa ta ɗago kai karaf suka haɗa ido. A kunyace ta sunkuyar da kai ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta. A hankali ya fara takowa har ya zauna kusa da ita sannan ya zame hular alkyabbarta. Hannu ya sa ya ɗago haɓarta cikin tausasa murya yace, "Kunyar me ake ji." Abu shiru ta yi tana murmushi, goshinsu ya faɗa ya yi mata raɗa ƙasa-ƙasa sai gani nayi ta sunne kai ƙasa tana dariya, ɗago da kanta ya yi tana ƙoƙarin sunkuyarwa ta ji hannuwansa biyu ya tallafo fuskarta, yana goga hancinsu wuri ɗaya. kamar almara haka suka fara jin shassheƙar kuka daga waje Abu ce ta fara ɗagowa suka

Please Login or Register in order to submit comment