Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ki je gida."


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[22/12/2021, 18:29] Ameera Adam🌚: 55...



"Maryama ko sama da ƙasa za ta haɗe wallahi sai na tafi da gudan jinina, don nima ɗan Adam ne kamar kowa ina buƙatar me tsaya mini tun da girma ya fara kamani. Idan na yi miki na miki idan ma waɗannan shekarun da aka kwashe ban yi miki ba ba damuwa ta bace. Na yi miki hallaci amma kika sak mini da butulci, dama wannan ranar nake jira domin na ci alwashin sai na tozarta ki. Amma kin ji na yi rantsuwa wallahi sai na tafi Saif, ba zan zauna kura da shan bugu Gardi da kwace kuɗi ba, ni da haihuwar yaro wani banza cen yana mora." Fulani Maryama ta zube bisa kan ƙafafuwanta tana faɗin, "Don Allah Ɗan magori ka taimakeni ka rufa mini asiri wallahi idan asiri na ya tonu na kaɗe har hanjina, duk duniya mutane biyu ne kawai suka san Saif ba Ɗan Sarki Aminullah bane. Daga kai sai Jakadiya..." Maryo ta katse mata maganarta da faɗin, "Sai kuma ni!" Hankali a tashe ta ɗago ta kalli Maryo a zabure ta miƙe tsaye tana nuna ta da ɗan yatsanta bakin ta na rawa ta ce, "Yanzu ma ke ce?" Maryo ta fashe da dariya ta gyaɗa mata kai cikin ƙwarin gwiwa ta ce, "Kina mamaki ne? Kin ɗauka za ki sha da wannan baƙin zalincin na ki? Kin yaudari kanki domin rana dubu ta ɓarawo rana ɗaya tak ta me kaya." Ɗan Magori ya hango Saif yana ƙarasowa ya damƙi hannunsa yace, "Wannan surutan banza ku ya dama amma tun da na ɗauki ɗana ku je cen ku ƙara." Saif ne ya ɗan fara turjewa Ɗan Magori ya kalle shi yanan murmushi ya nuna Maryo da ɗan yatsansa yace, "In dai kana son mallakar wannan ka biyo ni ni kuma na yi maka alƙawarin taimaka maka har sai ka mallaketa." Saif haka ya bi Ɗan magori kamar raƙumi da akala. Fulani Maryama ban da kuka babu abin da take yi. Maryo dariya ta fara sheƙa mata tun tana yi a hankali har dariyarta ta fara tsoratar Fulani Maryama.

Firgigit ta farka daga mummunan mafarkin da take yawan yi a ƴan tsirarun kwanakin nan, gumi ta haɗa sharkaf jikinta har wannan lokacin be daina rawa ba. Ba ƙaramin tsorata ta yi da mafarkin wannan ranar ba, babban tashin hankalinta da duk mafarkin da za ta yi Ɗan magori take gani raɗau a cikin mafarkinta ga shi kuma na wannan ranar har da Maryo a ciki. Ɗan tsoron Maryo ne ya ɗarsu a zuciyarta sai dai kuma lokacin da ta tuna da lalaurar da ke jikinta sai hankalinta ya ɗan kwanta. A fili ta furta, "Ɗan Magori me ye dalilin bibiyar da kake yi mini a cikin mafarkina bayan ka shafe sama da shekaru masu yawa, me yake shirin faruwa da ni ne an ya ba wani abu ne yake shirin faruwa da ni ba?" Wani tsagi daga cikin zuciyarta yana nuna mata da tayi watsi da wannan mafarkin domin shirmen Mafarki ne. Baccin da Fulani Maryama ta gagara kowa haka ta zauna tana saƙa da warwarar yadda za ta ɓullowa waɗannan munanan mafarkan masu neman rikitar da ita lokaci ɗaya.

Bayan kwana biyu Inna Habi na zaune tana yankewa Maryo farce, tana yi tana jin babu daɗi a zuciyarta saboda kusan kullin da kalar masu maganin da suke duba Maryo suna bata magunguna, wasu daga ciko har da turare. Sai dai duk ranar da aka yi mata turare kwana suke babu daɗi ba ƙaramin jiki take ji ba, haka Inna Habi take kwana akanta tana tofa mata addu'o'i sai a hankali jikin yake ɗan yi mata sauƙi. A ɓangare ɗaya kuma Salman ya tsira shigo musu ɗaki haka kawai bata yi aune ba sai ta riski ya faɗo musu ɗaki babu sallama, haka zai sa Maryo a gaba yana zabga dariya son ransa. Wani lokacin idan tana kwance har hannu yake sakawa ya tayar da ita zaune ya dinga leƙa fuskarta yana dariya. A wannan lokacin tana lura da yadda Maryo take fusata tana ƙoƙarin fisge jikinta, daga baya kuma sai ta fashe da kuka haka za ta wuni ta kwananda ɓacin rai. Wani abu da yake ɗaurewa Inna Habi kai ko da Salman be taɓa Maryo ba indai zai shiga ɗakin to ranar haka za ta wuni ta kwana tana kuka. Ranar da abin ya ishi Inna Habi Salman na shigowa ta ɗaure fuska ta ce, "Yarima maganar gaskiya abin da kake yi mini bana jin daɗi yau Maryo ko ɗan mutum ta kashe maka sai haka, da me yarinya za ta ji da lauluar jikinta ko da wannan dariyar da kake yi mata mara tushe?"

Wata dariyar ya kuma saki yana nuna Inna Habi yace, "Ki iya bakinki idan ba haka ba wallahi sai na mayar da ke abar tausayi fiya da kike ganinta a wannan halin." Yawun bakin Inna Habi ne ya kusa ƙafewa nan take ta ɗora zargin ciwon Maryo akansa saboda furucin da ya yi da kuma yadda yake zuwa yana sheƙa mata dariya. Inna Habi ba ta ƙara tanka masa ba har ya gama abin da zai yi ya fice. Yana fita ta je ta rungume Maryo kusan lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kuka.

Malam Liman Abdurrahman bn Safyan ne ya jagoranci yaɗa da'awa a ƙananan ƙauyukan da ke cikin birnin kano, ƙauyukan da suka kai wannan jihadin ga maguzawa a ƙarƙashin birnin Kano suke, irin su Doguwa, Zangon Dakata, Dawakin Tofa da sauransu. Cikin ikon Allah, suka nasara musuluntar da dubban Maguzawa da tsirarun kiristoci a ciki. Kasancewar boren da ƴan uwan waɗannan mutanen suka yi musu saboda karɓar addinin Musuluci ya sa suka taho da su cikin masarauta, kasancewar Sarki shi ne Uban kowa matsawar shi yake jagorantar wannan al'ummar.

Yawan wannan mutane ya sa Sarki Aminullah ya umarci da a fara fitar da sabbabin gine-gine, domin rage cukoson Bayi a cikin ɗakuna. Saboda kafin zuwan waɗannan baƙin ana samu Bayi biyar har shida a ɗaki ɗaya. Wannan dalili ya sa aka shiga sare bishiyoyi da ƙananan sukoki aka shiga fitar da ɗakuna tare da faɗaɗa girman Masallaci, saboda samun wadatuwar gabatar da ibada yadda ya kamata.

Tsugunne yake a gaban Mahaifiyarsa bayan sun gaisa take tambayarsa Abu da jikinta, a kunyace yake amsa mata daga haka suka shiga hirar duniya. Bayan ya yi mata sallama miƙewa ya yi zai tafi kawai sai gani ta yi ya yanke jiki ya faɗi. Hankali a tashe ta faɗa kansa tana ambatar sunansa, "Saif me yake faruwa be? Saif lafiyarka kuwa?" Wani irin gumi ne ya rufe shi na ƴan sakanni sai kuma jikinsa ya fara wani irin karkarwa. Duk abin da yake faruwa Saif be san Mahaifiyarsa na yi ba har sai da ya ji zafin na raguwa daga jikinsa, a hankali ya ɗago ya kalli Mahaifiyarsa yace, "Ammina!" Yana gama faɗa ya yunƙura zai ta shi ta taimaka masa ya tashi sai yace, "Ammi jiri nake ji." Fulani Zaliha bata amsa masa ba ta ci gana da tofa masa addu'o'in bakinta, ruwa ta miƙa masa ya sha sannan ta kalle shi ta ce, "Saif kana yawan yin azkar kuwa?" Murmushi ya yi saboda wani irin farinciki da ya ji yana ziyartar zuciyarsa, miƙawa ya ƙara yi yace, "Wallahi ina yi Ammi yauma tsautsayi ne." Duk yadda ta so hana shi fita be haƙura ba. Sallama ya yi mata ya wuce gida yana jin zuciyarsa fes.

"Ke Sahura kalle ni da kyau, wannan garin maganin da na baki barbaɗa mata za yi a abinci ko ruwa, wallahi idan kika wuce yau sai na ɓatar da ke. Ki bani hankalinki nan idan kika bari asirinki ya tonu kece a ciki." Sahura da ta yi fiƙi-fiƙi da idanu ta ce, "Ba za a samu matsala ba ya shugaba ta." Fulani Maryama ta ci gaba da cewa, "Ki tabbatar kin ga ta fara naƙuda kafin ki fito, don babu yadda za ayi ta riga matar Saif haihuwa yana matsayin Yarima. Amma kika kuskura aka samu matsala ranki sai ya yi mummunan ɓaci." Jiki na rawa Sahura ta soke ƙullin maganin da bakin zaninta sannan ta fice daga gidan.


Saif na zuwa gida ya faɗa kan gado yana lumshe ido, Abu kallonsa ta yi ta ce, "Abu Nouf an ya kana lafiya?" Kallonta ya yi sai ya sunkuyar da kai ƙasa yace, "Bani da sukuni sam saboda ina kewarta, ban san a wanne yanayi take ba amma jikina yana bani tana cikin damuwa." Cikin Abu ne ya kaɗa har sai da ɗan cikinta ya juya, mamaki ɗauke a fuskarsa yace, "Akan wa kake magana?" Kamar yana jiran tambayarta ya sake marairaice fuska yace, "Rayzuta! Na san wanda ya cutar da ita amma wannan karan dole na ɗau mataki akansa. Ita ce rabin rayuwata bana jin zan iya rayuwa da wata macen bayan ita, ba zan iya ci gaba da jin yadda take rayuwar ƙasƙanci ba, na rantse da girman Allah idan na har ya yi gangancin ciken jikinta ya samu matsala sai na datse rayuwarsa." Abu jijiga Saif ta yi hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba ta ce, "Saif ni kake ambatar sunan wata a gabana shin wace ce wannan da ta asirce ka lokaci ɗaya? Me na yi mata da za ta raba ni da kai? Wacece wannan da soyayyarta ta rufe maka ido har ka gagara shakkata kake begenta a gabana."

Hannuwa biyu ya sa ya tallafo fuskarta idanunsa ya zuba a kanta yana faɗin, "Ita ɗin rayuwata ce! Farincikana ce. Maryo ce wacce a duk bugun numfashina yana sauka ne da zallar soyayyarta." Abu dishi-dishi ta fara gani da ƙyar ta jingina da bango tana jin wani irin zafi a cikin zuciyarta, lokaci ɗaya kuma sai ta saki wani irin kuka me tsuma zuciya.

Amun afuwa da errors ban tace shi ba.


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[25/12/2021, 19:30] Ameera Adam🌚: 56...



TUNA BAYA...

*SHEKARA DUBU UKU BAYA*

DAULATUL JINNUL SAHARA

A wancen zamanin a cikin wannan Daular akwai wata gawurtaciyyar Masarautar Aljanu wacce take cike da tsantsar izza irin ta sarauta, Mulki irin na waɗanda suka gada iyaye da kakanni ba taka haye ba. Kamusul Birmi shine ainihin cikakken sunan wannan Sarkin na wannan Masarautar, ya gaji mahaifinsa ne bayan rasuwar Mahaifinsa. Asalinsu sun fito daga zuriyar Fararen fulanin Aljanun doron ƙasa, yawancin su Aljanu ne marasa haƙuri da sauri fushi sai Uba Uwa sun kasance masu matsanancin faɗa. Sai dai suna da matuƙar tausayi da tausasawa wanda yake da buƙatar taimako wala Aljani ɗan uwansu ko a cikin Mutane. Sarki Kimusul Birmi mafaɗacin gaske ne sai dai yana da saurin fahimta saɓanin ƴan uwansa. Mahaifinsa Birmil Ƙasi ya ga ji sarautar ne daga hannun Wan mahafinsa sakamakon Juddul Bahi yana da ƙaracin shekaru. Juddul Bahi ɗa ɗaya ne tulo a wurin Sarkin wancen nahiyar, ƙanƙantar shekaru da rashin ƙwarewa a mulki ya sa aka naɗa Mahaifin Kimusul Birmi.

(Ku fahima da kyau kar gaba kanku ya kulle, Ai nihin sarauta ta gidan su Juddul Bahi ce wato Sarki Garzukul Juddu da ya mutu sai aka bawa Ɗan ƙaninsa Birmul Ƙasi. Da ya mutu aka bawa ɗansa na Fari Kimusul Birmi.)

Kimusul Birmi yana da mata biyu Farratul Janwasu ita ce matarsa uwar gida tun auren saurayi da budurwa, Da mahaifinta da Mahafiyar Sarki Kisumul Birmi ƴaƴan mata suke auren gida aka yi musu. Sun shafe sheƙara sama da Talatin da aure babu wani labarin ciki daga wurin Farratul Janwasu, wannan lamari ba ƙaramin ɗaga hankalinsa ya yi ba yana ta taraddadin kar ya mutu be samu magaji ko magajiya ba. Ana haka har ya haɗu da Wurshil Ba'is ƴar Sarkin Buzayen Aljanun wancen lokacin. Lokaci ɗaya ya ji ya kamu da ƙaunarta ba a ɗauki lokaci ba aka ɗaura musu aure. Kasancewar Farratu Macece me sanin ya kamata ya sa babu wani abu da ya dame ta domin ta san haihuwa lokaci ce kuma Allah shi yake bayar da ita. Da auren su ko shekara biyu ba a rufa ba Wurshil Ba'is ta Haife kyakkyawar ƴarta, gwanin birgewa da ban sha'awa. A lokacin Masoyansa da dama ne suka nuna farin cikinsu ya yinda masu baƙin cikin suma ssuka shiga sahun masu nuna farinciki amma zuciyarau baƙiƙƙirin take kamar gawayi. Kisumul Birmi da kansa ya tambayi Farratu ta za ɓi sunan da ta ga ya dace a sakawa Jaririyar, sakamakon karamcin kulawar da take bawa amaryarsa saboda ya san son so fusabillahi take yi mata ba za ta cutar da ita ba. Farratu ba ƙaramin daɗi ta ji ba ganin irin wannan girmamawar da aka bata har da ƙwallarta sanan ta ce a saka mata suna RAYZUTA sunan ya matuƙar dacewa da ita, don haka aka shiga shagulgunan suna na ban mamaki tare da gayyatar manyan masaratun Aljanu na ko ina a faɗin duniya.

Waziri Mardil Kibsan ɗaya ne daga cikin Masu himtawa Masarautar Sarki Kimusul Birmi, kuma babban aminin Sarki. Sun ta so tun suna yara tare suka yi komai har aure kusan lokaci ɗaya suka yi, amintarsu ta dabance shi ya sa duk cikin masarautar babu wanda Sarki Kisumul Birmi ya yadda da shi sama da Mardil Kibsan saboda duk rintsi baya taɓa fitar masa da sirrinsa. Yana da ƴaƴa biyu Mace da na miji Babban Ɗansa me suna FURZAAN sai me bin sa HIDRAT. Lokacin da aka haifi Rayzuta Furzaan na da sheka goma sha biyu a duniya, ya yinda ƙanwarsa take da shekara ɗaya rak a duniya.

Balbutu shine shugaban bayin da suke hidima a ƙarƙashin Masarautar Daulatul Jinnul Sahara, Aljani ne kwaɗayayye me son zuciya da zalintar na ƙasa da shi a fakaice kuma ya kasance me mara kyakkyawar ɗabi'a. Duk wani mugun abu da miyagun halaye yana da su sai dai da yake ya iya takunsa babu wanda zai fahimci tsantsar halayyarsa. Yana da ɗa ɗaya tal a duniya me suna ZULIK sai dai kafin Zulik ya haifi ƴaƴa da yawa suna mutuwa. Bincike ya bayyana Bulbutu ya yi wa Mahaifiyarsa Fyaɗa har ta samu ciki shine ta haifi Zulik, bayan haihuwarsa baƙin ciki ya sa zuciyarta ta buga ta mutu.

Wannan kenan!

Duk in da nutsuwa da kwanciyar hankali suke sun yi baram-baram a cikin gidan Abu da Saif saboda baƙon al'amarin da Saif ya shigar masu da shi cikin gidan aurensu ba tare da Abu ta tsammace shi ba. Lokaci ɗaya ta zabge ta faɗa kamar wacce ta kwana biyu tana jinya saboda ko lokacin da ta yi laulauyi bata yi ramar da ta yi a wannan lokacin ba, ta rasa gane masa ba shi da magana sai ta Maryo, hatta doguwar hira baya iya yi da Abu wannan ya ƙara jefa ta cikin kogin tashin hankali. Za fi biyu ne ya haɗar mata na farko masoyinta annurin zuciyarta ya juya mata baya, na biyu kuma babu inda take zuwa bare ta samu sukunin sanar da Mahaifiyarta halin da take ciki. Lokaci ɗaya ta fara saka ɗan zargi akan Maryo take ganin kamar asiri ta yi wa Saif shi ya sa har ta fake da ciwon makantar ƙarya.

Da daddare bayan sallar Isha'i Abu na zaune tana jiran shigowar Saif saboda tun safe da ya fice daga gidan be ƙara waiwayo ta ba. Tana jin motsinsa zumbur ta miƙe ta ɗaga labule tana murmushi amma ga mamakinta sai ta hangoshi ya nufi hanyar banɗakinsu yana zuwa bakin bishiyar Ɗorawar ya samu wuri ya zauna a wurin, shi kaɗai ya fara murmushi sakamakon tuna waɗansu irin abubuwan baya da ya yi. A hankali ya buɗe baki yana faɗin, "Ina ji a jikina kina kusa da ni, wannan ɓoyan da kike yi sam ba zai fisshe ki ba domin indan kika shiga hannuna sai na baki mamaki yarinya." Sai kuma ya marairaice murya yana faɗin, "Amma dai kin san azabatar da zuciyata kike yi, ni na san kina tare da ni amma duk ina kika na yi alƙawarin zan nemo ki domin kece farincikina." Abu ce a tsaye tana hawaye ta ce, "Saif!" Ɗagowa ya yi yana kallonta ta ci gaba da zubda hawaye tana faɗin. "An ya Maryo ba asiri ta yi maka ba? Da wannan daren za ka zo nan kana surutai. Ni kam indai asiri ne gaskiya Allah ya isa tsakanina da ita." Huci ya fara yi saboda yadda maganganun Abu suka yi masa zafi a zuciya, nuna ta ya yi da ɗan yatsa yana huci yana faɗin, "Ki gyara kalamanki akanta saboda ita ta musamman ce idan kika sake faɗa mata makamanciyar wannan maganar za ki gane baki da wayo, sakarai shashasha. Yana gama faɗa ya fice fuuu daga gidan.

Abu durƙushewa ta yi a wurin tana fashewa da wani irin matsanancin kuka me tsuma zuciya, tana komawa ɗaki ta fara haɗa kaya tana cin alwashin zaman ta da Saif ya zo ƙarshe.

Saif na fita sashen Mahaifinsa ya nufa, daga ɗan nesa ya hango Salman na tahowa fuska a murtuke. Saif ya yi niyyar yi masa magana ya ga hakan ba shi da fa'ida. Salman ne ya sha gabansa yana nuna shi da yatsa yace, "Na ga alamar ka samu kanka amma har yanzu da sauran rina a kaba." Murmushi Saif ya yi yace, "Idan ka ji mutum na tsoron dare ba a ɗaure shi ya kwance bane. Mu zuba ni da kai mu gani shege ka fasa. Wallahi idan baka yi wasa ba wannan karan sai dai gyatuma ta haifi wani." Wucewa ya yi ta gefensa ya wuce saboda zuciyarsa da ransa duka a ɓace suke. Salman ya yi saki wata dariyar ƙeta yana cewa, "Tarayya ke sa Zomo ya auri sarauniyar giwa. Amma baƙar wahala ita ke sa Shege ya nemi Ubansa." Ya sake waigawa yana kallon Saif yana sakin murmushi.


Abu na tsaka da haɗa kaya Baiwa Tine ta shiga da sallama cikin girmamawa ta miƙawa Abu akushin da Fulani Zaliha ta aikota da shi wanda ta saba aika mata da abinci, karɓa ta yi ta ajiye a gefe sai kuma ta ji jikinta ya yi sanyi, musamman da ta tuna yadda Mahaifiyar Saif take ɗawainiya da ita. Wannan dalili ya sa ta fasa tafiya gida.

Washegari Kamar daga sama Inna Habi ta ji Sallamar Maleek, bayan ya gaishe da Fulani Maryama ya ƙarasa wurin Inna Habi, sam Fulani Maryama bata so haka ba amma ta barwa kanta sai ya ta fi zata cancarewa Inna Habi. Gaisuwar mutumci suka yi da Inna Habi haka kawai ta ji tana ƙaunar Maleek saboda yadda yake bawa Maryo kulawa. Ido ya zubawa Maryo da bata san da zuwansa ba yana ji a zuciyarsa ina ma za ta iya ganinsa har ta buɗe baki ta yi masa magana. Ya jima suna hira da Inna Habi sannan ya tashi ya nufi sashen sauran Matan Sarki Aminullah. Sashen Fulani Zaliha ne ƙarshe ita ma sun jima suna hira sannan ya miƙe ya yi mata sallama. A soron tsakiya suka haɗu da Saif bayan sun gaisa Saif yace, "Ɗan uwa lallai ka miƙe da zumunci ina jin ko wata biyu ba ka yi ba rabonka da nan ya su Ummi." Maleek ya yi murmushi yace, "Kai kuwa ina da mara lafiya ai dole na zo dubiya." A ɗan hanzarce ya kalle shi yace, "Waye ba lafiya a nan?" Da mamaki Maleek ya kalle shi yace, "Maryo mana yarinyar da take kama da matata Shukra." Sunan Maryo ne ya yi masa wata irin kuɗa a kunne har sai da ɗan runtsa idanu, sai kuma ya damƙe hannun Maleek da ƙarfi yana faɗin, "Tana ina?" Maleek be yi mamaki ba ya ɗauka Saif na ta ya shi jimami ne kansa tsaye yace, "Mu ƙarasa na yi musu sallama tana wurin Babarta Inna Habi." A hankali Saif ya maimata, "Inna Habi dai Mahaifiyar Abu?" Maleek sam be ji shi ba sakamakon tuni ya yi gaba yana son ya yi musu sallama don daga nan Garin Zazzau zai wuce.

Tun shigarsu gidan gaban Saif yake faɗuwa yana jin wani iri a jikinsa, a gaggauce ya gaishe da Fulani Maryama sannan suka wuce Ɗakin Inna Habi Maryo na kwance jikin Inna Habi tana tsefe mata kai. Maleek ne ya fara shiga Saif na biye da shi. Tun shigar Saif gidan a zabure Maryo ta miƙe tana lalube-lakube tana buɗe baki alamar tana son yin magana amma ta kasa, kawai sai ta fashe da wani irin tana ci gaba da lalubawa. Hankalin Inna Habi ba ƙaramin tashi ya yi ba tana ƙoƙarin kama Maryo amma tana kwacewa. Saif na arba ta ita da sauri ya ƙarasa wurinta cikin wani irin yanayi ya sa hannu biyu rungumeta a jikinsa, Maryo na jin haka ta sauke wata irin nannanuyar ajiyar zuciya sai dai ko kaɗan bata yi yunƙurin hanashi ba. Ɗago da kanta ya yi ya hurawa idanunta iska, ya sa bakinsa a daidai kunnenta ya hura iskar da ƙarfi nan take jikinta ya fara wata irin karkarwa. Ja da baya ta fara yi tana murza idonta sai kuma ta waiga wurin Inna Habi da take tsaye kamar gunki sakamakon tozali da abin da mijin ƴarta ya yi akan idonta. Da gudu ta tafi ta rungumeta tana faɗin, "Inna kece a gabana nake ganinki." Saif ya ƙarasa ga hanyo Maryo tana faɗawa Jikinsa yace, "Ni ba ki yi maraba da ni ba?"

BILLAHI AKWAI ƘURA GIDAN SARKI AMINULLAH YA KUSA KAMAWA DA WUTA😂


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI_
[30/12/2021, 17:38] Ameera Adam🌚: 57....


A kunyace Maryo ta sunne kai ƙasa don sai yanzu take jin nauyin abin da ta yi a gaban Inna Habi, kiciniyar kwace kanta take Saif ya haɗa goshinsu wuri ɗaya har yana jin yadda sautin ƙirjinta yake bugawa da sauri-sauri, kamar me yi mata raɗa a kunne haka muryarsa ta fara sauka tana ratsa sassan jikinta yana faɗin, "Ba dai guduwa za ki yi ba?" Kallon gefen da Inna Habi take ta yi ta mayar masa da amsa cikin sigar da ya yi mata magana, "Inna tana kallonmu fa." Sassauta riƙon da ya yi mata ya yi ai kuwa kamar me jira da sauri ta ƙwace kanta tana murmushi ta koma cen bayan Inna Habi ta rungomata ta baya tana ɗora kanta a gefen kafaɗarta. Ilahirin jikin Inna Habi ya yi sanyi saboda abu ne da bata taɓa tsammaninsa ba, a yadda ta lura babu wata damuwa a tattare da Maryo sai ma ta lura shauƙin da suke nuna juya kamar mata da mijin da suka yi shekaru ba tare da juna ba. Maleek da ke gefe gabaɓaya annurinsa ya ɗauke sai furzar da iska yake me zafi yana wurgawa Saif mugun kallo, takawa ya fara yi a hankali zai ƙarasa wurin Maryo a hargitse Maleek ya buga masa wata uwar tsawa yana faɗin, "Dakata! Wane irin shirme kake yi haka?" Nan take annurin da ke fuskar Maryo da Saif ya ɗauke kamar waɗanda aka isar musu da saƙon mutuwa. Saif ne ya zuba masa idanu sai da ya lumshe su ya sake buɗewa sannan ya kuma watsa masa manyan idanuwansa da suka fara sauya launi, da wata irin murya ya kalle shi yana faɗin, "Ina matukar ganin mutumcinka Ɗan uwa karka bari ya zube, domin na tabbata idan ya ɓare ko ƙwayar zarra

Please Login or Register in order to submit comment