Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Mubaya'ar da zai yi masa domin ya gama tabbatarwa zai raba Sarki Kusumul Birmi da mulki ta ƙarfin tsiya, dabararsa ɗaya idan ya yi wannan badaƙalar zai raba shi da duk wani abun da yake taƙama da shi. Ya san zai yi wuya Mutanen Masarautarsu su bashi haɗin kai. Idan ya zo ya bawa Sarki Buzaag haɗin kai ya bashi sirrikan masarautar dole za su taimaka masa ya farmaki waccen masarautar ya murɗe mulkin ta ƙarfin tsiya. Ko banza ya san zai zama ɗaya daga Sarkin ƙanana Masarautu, tun da ya san ko suma yake Sarki Buzaag ba zai taɓa barinsa a babban Sarki kamar yanda Sarki Kisumul Birmi yake a kan karagar mulkinsa ba.

Lokacin da Sarki ya sanarwa da Mahaifin Furzaan ba ƙaramin farinciki Aminan biyu suka yi ba sakamakon shima Furzaan ya sanarwa da Mahaifinsa abin da yake faruwa a tsakaninsa da Rayzuta. Babu ɓata lokaci aka tsayar da lokacin biki wata guda mai zuwa. Farinciki wurin Rayzuta da Furzaan baya musaltuwa soyayya suke zubawa cike da farinciki, kafin wani lokaci tuni maganar sa ranar Furzaan da Rayzuta ta karaɗe ko'ina a cikin Masarautarsu.

"Masoyina lafiya ka kirani a tsohon daren nan?" Jakadiyar Sarki Kisumul Birmi mai suna Bizmatu ta faɗa tana kallon Bulbutu. Bizmatu ta hannun daman Bulbutu ce sakamakon suna soyayya a ɓoye ya mayar da ita tamkar matarsa kuma ita take bashi sirrikan Sarki. Ajiyar zuciya ya sauke yace, "Na kiraki ne domin ki bani haɗin kai akan Uban gidanki Sarki Kisumul Birmi. Ina son ki buɗe kunne ki saurareni idan har kika bani haɗin kai ni kuma na yi miki alƙawarin aurenki a lokacin da nake a matsayin Sarkin wannan Daular." Nan take Bulbutu ya sanar da ita halin da yake ciki da manufarsa dangane da Sarki Kisumul birmi.

Murmushi ta yi ta ce, "Wannan ba abu ne mai wahala a wurina ba duk abin da kake buƙata ka min magana zan baka haɗin kai ɗari bisa ɗari." Daɗin haka ya sa ya rungomata nan suka ci gaba da masha'arsu.

(Jakadiyar Sarki Bizamatu ita ce Fulani Maryama a wancan ƙarnin na su Rayzuta. Sarki Kisumul Birmi shi ne Sarki Aminullah a wannan ƙarnin na su Maryo. Balbutu shi ne Tsohon da Salman yake zuwan wurinsa a harkar tsafi da bokanci. Inna Habi ita ce Matar Baban Rayzuta wacce aka mutu aka barwa amanarta. Fulani Zaliha ita ce Matar Bulbutu Mahaifin Zulik, Ina fatan bakwa ruɗewa)


Kafin wani lokaci tuni Ƙudan zuman nan ya addabi mutanen da ke cikin Masarautar, Lokacin da labarin zumar ya je kunnen Sarki Aminullah ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba, domin lokacin da ya leƙa da tagar fadarsa (Window) haka ya ya ga jama'a na faɗuwa jikinsu duk jinane. Waɗanda abin bai same su ba haka suka rinƙa rufe kawunansu a ɗaki. Saboda ko ɗaya idan ya yayimeka yana iya hallaka ka. Sarki Aminullah ne bada umarni da a kira masa Baushe, lokacin da Baushe ya zo shi kansa da ƙyar ya sha domin sai da jikinsa ya yi faca-faca da jini. Sarki da damuwa ɗauke a fuskarsa yace, "Baushe mun wayi gari da wata irin annoba da bansan wacce iri bace ta ƙudan zuma." Baushe ya nufasa sannan yace, "Allah ya taimake ka wanan zumar tun da Uwata ta haifeni ban taɓa cin karo da irinta ba amma ga tuarare a turara a gani idan ya magance ta za mu san wacce iri ce. Idan kuma bai magance ta ba sai mu san abin yi." Nan take Sarki Aminullah ya bada Umarni da a turara turaren a harabar Masararuta. Wuta aka hura da ita ce manya aka rinƙa zazzaga garin tuararen da Baushe ya ba yar amma wani babban tashin hankali hayaƙin na fara fita waɗansu irin Manyan ƙudan zuma suka fara fitowa daga cikin wutar suna yin kan Bayin da suka hura wutar. Bayi biyar ne a tsaye zumar na cizonsu jini ya fara fita daga jikinsu a wahale haka suka rinƙa faɗuwa nan take mutum huɗu suka rasa rayukansu. Sai guda ɗaya ce ta sha da ranta ita ma da rarrafe ta ƙarasa fada sai dai tun kafin ta je jikinta ya fara farfashewa yana ta tsartar da jini.

Salman na ganin kudan zuman ya saki murmushi don ya san abin da ya aikatawa Abu da Jaririnta ne ya sa Maryo ta fusata, har ta aikata musu haka. "Wato ya tabbata Tarihi zai maimata kansa kenan." Ya furta yana gyara tsayuwarsa. Ayarin ƙudan zumar ne suka tunkare shi ya zuba musu ido don a zatonsa babu wani abu da za su iya aiwatar masa, sai dai ga mamakinsa ya ga sun fara cizonsa ta ko ina, kuma duk inda suka ciza sai dai jini ya yi tsartuwa ya fara zuba. Wannan ba ƙaramin ɗaga masa hankali ya yi ba domin ya ɗauka zai iya bawa kansa kariya sai ga shi wankin hula na neman kaishi dare. Abu sannu-sannu tun yana tsaye har ƙudan zuman ya tasarma hallaka shi sai da ya yi da gaske sannan ya samu ya gudu can sashensa.

Baushe hankalinsa ya tashi matuƙa jakarsa ya kwance ya fara siddabarunsa na kiran aljanun da suke taimaka masa a cikin daji. Sai da suka bashi wasu magugunan sannan ya haɗa dana wurinsa yace a ƙara turarawa. Cikin damuwa Sarkin Aminullah yace, "Baushe ina fatan ba za a sake samun matsala ba?" Baushe ya rufe jakarsa yana cewa, "Allah ya taimakeka haka muke saka rai amma sai an gwada a kansan na ƙwarai."

Lokacin da Dogarai suka fita don su haɗa wuta ba ƙaramin tsorata suka yi da ganin mutane baja-baja a yaryashe cikin jini. A tsorace suka fara zuba maganin domin suma suna yi zumar tana cizonsu sun daure ne kawai domin cika umarnin Sarki Aminullah.

Fulani Maryama tana jin labarin saukar Annobar ta janyo ƙofarta ta datse, haka daga wurin Inna Habi domin ba ta san abin da yake faruwa da Abu da kuma ficewar Maryo ba. Abin da ta ayyanawa ranta ta san tun da Maryo ta tafi sashen Fulani Zaliha ba ta wuce wani wurin ba da har wannan kuɗan zumar za ta sauka a kanta.

Fulani Zaliha kuka ta fasa lokacin da Unguwar zoma ta yi wa Abu duk abin da ya dace amma ko motso bata yi, suna cikin wannan yanayin annomar kuɗan zuma ta saukar musu wannan dalilin ne ya sa ba su yi wani yanƙurin fita ba suka zubawa sarautar Allah ido.

Salman na shiga gida Kuɗan zumar suka sake yanyame shi wannan karon har faɗuwa ya yi suka rufu a kansa ta ko ina suke kai masa cizo a fusace. Tun yana iya ɗaga hannu ya kore su har ta kai ga ko ɗan yantsansa baya iya ɗagawa. Wani baƙin hayaƙinne ya turniƙe wurin bai jima ba ya ɓace tare da Saif sai ga wurin fayau sai ƙudan zuman sun farfaɗi suna motsi da ƙyar.

Baushe da kansa ya ƙarasa gaban wutar yana ƙara maganin da ya bayar a turara, yana zubawa a hankali ƙudan zumar suka fara taurawa a gabansa wuri gudan. Wannan lamarin ba ƙaramin mamaki ya bawa mutane wurin ba. Sai da suka gama taruwa tsaf sannan ya umarce su da su koma wurin da suka fito. A hankali suka fara nufar hanyar wurin da Maryo take, Baushe ya fara binsu da sauri 'yan bani na iya suka rufa masa baya. Suna zuwa suka tsaya akan Maryo da ke kwance tana sharar bacci hankali kwance. Baushe tsaye ya yi yana kallon abin mamaki domin ko tantama baya yi dama ya san ba zumar lafiya bace. Bayi da Dogaran da ke biye da shi mamaki ne ya kashe su a tsaye, babu irin tashin da bai yi wa Maryo ba amma ko gezau bata motsa ba. Yana shirin taɓa ta ya ji wata irin guɗa a tsakar kansa har sai da kansa ya sara, wani Dogari ya umarta da ya ɗaga ta yanda shima ya ji haka Dogarin ya ji. Wani garin magani ya ɗauko ya shafe hannu da jikinsa sannan ya sunkuya ya saɓa Maryo a kafaɗa yana gaba ƙudan zuma na biye a saitin kan Maryo suka kuka.


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[18/01, 19:08] Ameera Adam🌚: 64...

Tuna baya....

Bulbutu da ƙyar ya sha kan Zulik akan ya yi haƙuri ya ƙara masa lokaci, don cewa ya yi mai rabashi da datse numfashin Mahaifinsa sai Allah. Sai da ya sanar masa irin shirin da yake yi musu sannan ya haƙura. Domin ya lura da irin ci gaban da Mahaifinsa yake son kawo musu a rayuwarsu ta gaba. Haka ya ci gaba da warkajimsa cikin farinciki zuciyarsa ƙal babu damuwa. Duk wata ƙofar sirrin gidan sarautar Bulbutu ya buɗewa Sarki Buzaag ya samu ƙwarin gwiwa ne a wurin Jakadiya Bizamatu, domin duk wasu sirrikan Sarki Kisumul Birmi na fili dana ɓoye gabaɗaya ta sansu don haka ta rinƙa kwance masa su falle-falle a gaban Bulbutu shi kuma yana kaiwa Sarki Buzaag bayani a sirrin ce. Kwana uku da saka ranar Rayzuta, Bulbutu ne zaune da Jakadiya suna tattaunawa bayan sun gama suka faɗa masha'arsu. Matar Bulbutu na kawo kai ɗakin ta ci karo da abin da suke aikata, don haka ta fashe da kuka tana rufe Jakadiya da duka cikin takaici. Kallon tsana ta wurgawa mijinta tana cewa, "Duk mugun halinka da kake aikatawa na tsahon shekaru na yi maka shiru na zura maka ido, ina sane da ka haɗa kai da maƙiyan Sarki Kisumu amma hakan bai yi maka ba har sai ka sa Jakadiya ta ci amanarsa. Kai wanne irin azzalumi ne? Yanzu ka yi mini adalci da ka kawo mace har ɗakina kuke lalatarku?" Bulbutu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya sannan ya murtuke fuska yana cewa, "Tabbas zan rage miki hanya domin da alama wuyanki ya fara kauri idan na zura miki ido za ki iya sanya kwaɓata ta yi ruwa." Yana gama maganar ya janyota ya toshe mata hanci tun tana kakari harta faɗi ta matu a wurin. Kallon Bizamatu yace, "Maza ki fice nima fita zan yi don kar a gano lagona." Ku san tare suka fice sai bayan wani lokaci Bulbutu ya koma ya fasa kuka sannan ya fito yana kuturuwar neman taimako. Kafin wani lokaci tuni mutuwar Matar Baban Zulik ta ratsa cikin masarautar, ba ƙaramin jimami suka yi ba kasancewar kowa ya yi mata shaidar mutuniyar arziƙi.

Ranar da ta cika kwana uku da mutuwa ranar ne Sarauniya Rayzua ta kai gaisuwarta don fir cewa ta yi ba za ta ba, sai da Furzaan ya matsa mata sannan suka tafi tare da matar Babanta. Haka kawai ta ji gabanta ya fara faɗuwa amma ta dake ta ci gaba da harkar gabanta. Bayan sun yi gaisuwar suna ƙofar fitowa wasu baƙaƙen Dakaru suka nuna mata mazaunin keken doki. Kallosu ta yi da rashin fahimta ta ce, "Ku su waye?"

"Ba dole sai kin su waye ba, umarnine aka ba mu na tafiya da ke ta lallami ko ta tsiya."

Rayzuta tuni ta fara kiciniyar ƙwacewa da sauri Dakarun suka fara ƙoƙarin kamata, Matar Mahaifinta na ganin haka ta fasa kuka ta rungumeta tana ture hannuwansu. Dogarawan ƙofar Sarki Kisumul Birmi tuni aka haɗa baki da su a gabansu aka tafi ta Rayzuta da matar Babanta babu wani yunƙurin dakatarwa da suka yi. Farratu na rungume da Rayzuta domin ta san waɗannan mutanen ba alheri ne ya kaisu ba, da har sukai ƙoƙarin guduwa da Rayzuta. Lokacin da aka kaisu a wani ɗaki aka zuba su me duhun gaske, gabaɗaya a tsorace suke don ba su taɓa fuskantar haka a rayuwarsu ba. Bayan wani lokaci Sarki Buzaag ya sa aka fito da su, Rayzuta na zuwa ta hango Bulbutu a gefen Sarki Buzaag. Da sauri ta ƙarasa wurinsa tana fashewa da kuka, wani shu'umim murmushi ya yi ya fara shafa bayanta. Tana nan tsaye Zulik ya shigo fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Baba tun da nake baka taɓa faranta mini rai ba domin ka sa an kawo mini farincikina." Da sauri Rayzuta ta matsa tana nuna shi da hannu ta ce, "Dama da sa hannunsa aka kawo mu wurin nan?" Bulbutu ya bushe da dariya yace, "Da kina tsammanin zan zura ido a aurawa wani ke ba Ɗana ba?" Da sauri Farratu ta ƙarasa gabansa ta nuna shi da yatsa ta ce, "Tabbas ka bani mamaki kai macuci ne azaalumi maci amana..." Tun bata rife baki ba Zulik ya kifeta da mari yana cewa, "Shashashar banza uban nawa kike..." Rayzuta ce ta katsa shi ta wanke shi da zafafan mari har guda biyu sannan ta riƙo hannun Farratu tana rungumeta. Sarki Buzaag ne ya yi gyaran murya sannan yace, "Bulbutu mun cika maka naka alƙwarin saura namu." Bulbutu ya yi jinjina sannan yace, "A shirye nake ko yanzu zamu iya farmakar Sarki Kisumul Birmi." Farratu na jin haka ta yi kukan kura ta cukumi wuyan Bulbutu tana cewa, "Allah ya wadaranka dama kai ba masoyinmu bane babban maƙiyinmu ne bamu sani ba?" Bulbutu ya saki dariyar ƙeta ya nuna bakin ƙofa yace, "Ku ƙaraso daga ciki su kashe ƙwarƙwarar idonsu." Yana rufe baki Juddul Bahi (Shi ne wanda na ce muku mahaifinsa ne mai asalin sarautar Daulatul Jinnul Sahara.) da Jakadiya suka shigo. Jikin Rayzuta da Farratu har rawa yake saboda tashin hankali tabbas a wannan lokacin ne da suka tabbatar da mugu bai da kama. Suna shirin magana Sarki Buzaag ya bada umarnin tura Gwaraza su tafi Masarautar su Rayzuta domin farmakarsu kuma tun da dama Bulbutu duk ya gama siye su a sirrince. Zulik ne ya ƙarasa wurin Rayzuta yana lasar baki ya kai hannu zai taɓa ta, da sauri ta bige hannunsa tana ja da baya. Sarki Buzaag ne ya bushe da dariya yace, "Ƴan mata me kike yi haka ne? Maza ku kai masa amaryarsa idan kuma waccan tsohuwar ta hana ku datse numfashinta." Rayzuta na jin haka ta ƙanƙame Farratu ita ma ta riƙe ta gam suka saka kuka. Duk yadda Dakarun suka yi ƙoƙarin raba su abin ya gagara. Ɗaya daga cikin Dogarawan ne ya ɗauki wani ƙarfe ya bugawa Farratu a tsakiyar ka nan take jini ya fara tsartuwa ta yanke jiki ta faɗi. Kafin ta kai ga mutuwa ta kalli Rayzuta ta ce, "Da a kashe ki bayan an ci moriyar gangar gara a kashe ki kima mai kare martabarki ta 'Ya mace. Ba za su taɓa barinki ba koda kuwa kin ba shi kanki domin ba son ki yake ba gangar jikinki yake ƙauna." Tana gama maganar idanunta suka kafe nan take rai ya yi halinsa. Rayzuta durƙushewa ta yi a kan gawarta ta wani irin gursheƙen kuka, da ƙarfin tsiya Zulik ya fisgeta yana janta har cikin wani ƙayataccen ɗaki.

Kamar gawa haka aka kwantar da Maryo a fadar Sarki Aminullah, hakazalika waɗannan ƙudan zumar ba su daina kuka suna tsaye a kanta ba. Wani Bafade ne ya zuba mata ido ya ɗago da damuwa ɗauke a fuskarsa yace, "Baushe shi wannan ƙudan babu yanda za a yi a koresu daga wurin nan?" Baushe ya yi masa wani kallo sannan yace, "Samun sararin kuturu gaɗa a cikin rama. Ina wa laifin da suka daina addabar mutane? Ai ka bari na yi muku jawabi yanda ya kamata." Sarki Aminullah haka kawai ya ji ya damu da halin da Maryo take ciki, bai san me ya sa yarinyar take da babban matsayi a zuciyarsa ba. Ya san shi mutum mai tausayi ne amma yana mamakin yanda yake jin yarinyar tamkar 'yar cikinsa. Kallon Bushe ya yi fuska ɗauke da damuwa yace, "Baushe bamu bayanin abin da yake faruwa da yarinyar nan!"

Kafin Baushe ya yi magana Fadawa suka amsa da, "Baushe Mai martaba na buƙatar masaniyar lalurarta." Baushe ya russuna yace, "Allah ya taimakeka ba komai yake damunta ba face fusatar shuɗaɗɗun ruyukan wasu jinsi. Ba zan iya cewa ga jinsin ba amma abin da na sani tana cikin tsananin baƙin ciki domin wannan ƙudan zuman na taɓa cin karo da su shekara Ashirin baya a dajin Ɓaguru dake kudancin ƙasar nan. Aljanin da yake bani laƙani ya sanar da ni tarihinsu domin asalin wannan ƙudan da kuke gani ba kuɗan zuma bane, yana daga cikin ƙwarin wani jinsi amma wani binciki ya nuna a jimsin Jinnu ne wani kuma yace a jinsin ɓoyayyun dabbobi ne. Amma mafi rinjaye sun fi danganta shi da jinsin Aljanu." Sarki Aminullah ya yi tsai da tunani yana auna maganganun Baushe a mizani sannan yace, "Ina buƙatar sanin me ye alaƙarta da waɗannan ƙwari kuma a sallame su daga wurin nan."

"Daga ni har sauran masu magungunan duniya babu wanda ya isa ya kore su kuma babu wanda zai ya tashin yarinyar nan daga bacci. Taimako ɗaya ne da nake da iko kuma na yi Ranka shi daɗe. Na haɗa kawunan Ƙwarin nan wuri ɗaya ga su sun taru a kanta suna jiran umarninta. Idan har ba ita ta basu umarnin ba za su taɓe a haka har sai ranar da ta tashi daga bacci, baccin da babu mai iya tashinta sai lokacin da ta farka ko kuma wani mai irin tsarim rayuwarta. Nima na samu nasarar ɗaukanta ne sakamakom Maganin dana shafawa jikina ba don haka ba tuni sun riga sun hallaka ni."

"Haka zan tura ido suna hallaka mini talakawana? Ka san a ƙalla sama da mutum hamsin sun jikkata. An bani tabbacin mutuwar mutane ashirin da takwas har yanzu akwai waɗanda ba su san waye a kansu ba. Labari ya ishe mini ƙudajen nan sun fita har wajen masarauta suna ci gaba da farmakar Talakawa mutane sai faɗuwa suke." Bazan laminta ba!" Sarki Aminullah ya faɗa a kausashe da Babbar murya har sai da fadar ta amsa. Fadawan wurin da sauri suka ɗago suna kallonsa domin tun da suke da shi haka bata taɓa faruwa a fada ba. Wannan ne ya ba su tabbacin cewar Sarki Aminullah ya fusata da fushi mai tsanani, domin fuskarsa har haɗewa ta yi tai jawur. Ba su gama tsinkewa da mamaki ba suka riske shi ya miƙe tsaye ya fara takawa zuwa wurin da Maryo ke kwance, ba don numfashin da take yi ba za ka rantse da Allah gawa ce a wurin. Tsugunnawa ya yi a gabanta nan take Fadawa suka russunar da kansu ƙasa domin ransu gabaɗaya bai so haka ba ace Sarkin Sarakai, Sarkin da a ƙasarsa ta Najeriya (Nigeria) na alfahari da Masarauta kamar ta Kano mai cike da izzar mulki. Shugabansu da ke gefe ne ya ɗago da kai yace, "Allah ya ja ranka Ubangiji ya jiƙan Mai babban ɗaki, ina ganin a ƙara duba lamarin da maganin da za a yi mata. Muna mai roƙon alfarma ga adalin Sarki, Sarkin mai tausayin Talakawa da ya jinkirta zartar da hukun da zai gudanar yanzu.Tuba nake ranka shi daɗe idan magana ta ta yi tsauri."

Sarki Aminullah ya ɗago ya kalleshi da manyan idanuwansa masu sanyan mutum shiga nutsuwar da bai yi niyya ba yace, "Haƙƙinmu mu kula da rayuka da dukiyar al'ummarmu. Ba zan lamunci ganin yanda jinin bayin Allah yake zuba babu ƙaƙƙautawa ba. Ko a tarihin iyaye da kakanni haka bata taɓa faruwa ba, don haka zan tashe ta inma ta tashi inma na kori waɗannan azzaluman da kaina." Yana gama magana ya saka hannunsa a kan ƙafarta yana ambatar sunanta. Sai da ya yi mata kira uku sannan jikinta ya fara wata irin karkarawa. Kamar wanda aka jonawa wutar lantarki haka ya ji hannunsa ya yi wani zum! Sai kuma ƙudan zumar suka fara yanyame shi suna ƙoƙarin kai masa cizo. A hargitsa ta miƙe zaune tana buga musu wata irin gigitacciyar tsawa tana cewa, "Ku dakata!" Kamar waɗanda aka ƙamar haka ƙudan zumar suka tsaya ƙyam kowanne a inda yake a nan ya tsaya. Tafin hannunta ta buɗe lokaci ɗaya suka fara dawowa kai suna hawa kan hannunta, sai da suka gama ta ruwa tsaf a hannunta ta ce, "Na sallame ku." Da gudu suka fice buuuu! Daga cikin Fadar, hawaye ne ya fara zuba daga idanunta ta kalli Sarki Aminulla da ke tsaye gabanta ta ce, "Daraja tana ga mai babban Matsayi da girma a gare domin kai ɗin ma daban ne. Me ya sa za ka yi mini haka? Sam ban ji daɗin haka ba domin ya kai ni maƙura." Sarki Aminullah ya taka a hankali ya koma mazauninsa Fadawa suka ruɗe da cewar, "Takawarka lafiya Ɗan toron giwa! Gaba salamun baya Salamun Sikari ba kai farin banza, bangon zuma mai nason alheri kowa ya raɓe ka sai lasa. Turare kake sha ƙamshi ƙamshinka ya yi naso har ɗakunan Talakawa." Wani Bafade ne ya tashi ya je ya gyara Sarki Aminullah zaman alkyabbarsa sannan ya kalli Maryo yace, "Wanne ne shi? Ɗan gidan waye kuma mai ya aikata miki?"

"Bakin alƙami ya riga da ya bushe domin rijiyar da ke buƙatar agaji tuni da jima da ƙafewa. A baya ta nemi a gaji da tallafinka a lokacin da take ganiyar ɗaukinka amma sai ka wofantar da buƙatar hakan, alhalin bishiyar na buƙatar tallafi kafin ƙonewarta ƙurmus. Sanin wane ne shi me ya yi mini duk ba zai amfanar da mutum ɗaya daga cikin wurin nan ba domin, babu mutum ɗaya da hakanya shafa." Sai kuma ta fashe da kuka ta ci gaba da cewa. "Ka karya mini alwashina domin ba zan taɓa iya watsa maka ƙasa a ido ba domin kai ɗin mai muhimmanci ne a gare ni. Amma tabbas na ɗaukarwa kaina alwashin bai sha a banza ba." Tana gama maganar ta miƙe ta fice jiri na ɗaukanta taba tafe tana haɗa hanya kamar wacce ta aha ƙwaya. Mamaki ne ya mamaye Sarki Aminullah ya dubi Baushe yace, "Me ne ne matsalar yarinyar nan da take waɗannan maganganun marasa kan gado?"

"Babu wani abu da yake damunta sai dai maganganunta cike suke da ɗaukan fansa. A fusace take da fushi mai tsanani amma tabbas yanda ta faɗa ɗin haka ne kai mai muhimmanci ne a wurinta Allah ya ƙara maka lafiya." Baushe ya faɗa yana kallon Sarki Aminullah.

"A nema mata magani domin nan da kwanaki ƙalilan za a ɗaura mata aure. Don haka dole a san abin yi."

Baushe ya yi jim yana nazari domin yana ganin da kamar wuya gurguwa da auren nesa, don haka ya ɗago yace, "Allah ya taimakeka a iya sani da laluben magunguna na har yau Allah bai sanar da ni irin maganin da zan bata..." Tun bai rufe baki ba Fadawa suka buga masa tsawa suna cewa, "Hattara! Hattara dai Baushe." Baushe ya russunar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka a gafarce ni amma maganar yanda take haka na faɗa. Domin bansan abin da zan yi mata ta warware ba." Yana gama maganar Sarki Aminullah ya sallame shi ƙarshe ya sallami zaman fadar gabaɗaya.

Maryo na zuwa gida da sauri Inna Habi ta rungumo tana shafata jikinta da ya yi furu-furu da ƙasa tana cewa, "Maryo in ce dai babu wani abu da yake damunki wani labari ya ishe mini wai kin cen fada a kwance haka ne? Ina fatan dai ƙwarin nan ba su cutar da ke ba?" Maryo ta dafe kanta tana lumshe idanu ta ce, "Ba abin da ya same ni Inna kaina ciwo yake." Hannu Inna Habi ta kai ta dafa ta ji kanta ya yi rau saboda zafi da sauri ta kaita ɗaki tana fitowa ta samu mutane sun fara taruwa har da masu leƙe. Mamaki ne ya kamata amma bata furta musu komai ba saboda bata san abin da suke yi wa leƙe ba.

"Ka

Please Login or Register in order to submit comment