Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bayan ya dawo daga Masallaci ya bi gefenta ya kwanta. Juye-juye yake saboda yanayin da yake ciki amma ganin irin wahallan baccin da take yi, ya sa akan dole ya haƙura, ga jikinta ya ɗauki wani irin za fi da alama zazzaɓi ne ya rufe ta ruf.

Bayan gari ya yi haske da kansa ya tashi ya ɗumama musu sauran farfesunsu sai da ya kammala komai, sannan ya tashi Maryo tana ta shi ta fara yatsina fuska. Kallonta ya yi ya miƙa mata hannu ta sauko tana takawa da ƙyar, saitin kunnenta ya je ya raɗa mata, "Yarinyar nan kin fiya langwai an ya ba zamu koma na baki magani da kaina ba." Kamar jira take ai kuwa ta rushe da kuka tana maka masa fulo, ban da dariya babu abin da yake yi mata.

Sai da suka yi wanka sannan suka zauna cin abinci, da kansa ya rinƙa bata abinci a baki tun tana sunne kai har ta zage ta rinƙa ci hankali kwance, daga daren ranar zuwa safiyar wata irin soyayya ake bugawa tsakanin Maryo da Saif. Lamarin Saif tun yana bata kunya har ya tuƙe ta saboda bata taɓa tsammanin Saif ya ƙware a fannin soyayya kamar haka ba. Abinci kala-kala Fulani Zaliha ta aiko musu wannan karon babu wanda ya tura wata wakiliya don bincikar yanda amarcin su Maryo ya kasance.

Abu kamar wasa tun warin yana iya sashen Fulani Maryama har ya kai ga ya fara kaiwa gidajen da ke Maƙotaka da ita, a wannan karon Sarki Aminullah tura Fadawa ya yi tare da basu umarnin ɓalle ƙofa matuƙar suka yi magana bata buɗe musu ba. Kamar Takawa na da masaniya tun da Fadawan suka je suke yi wa Fulani Maryama magana amma sai ta rinƙa zaginsu ɗaya bayan ɗaya. Ganin haka ya sa jagoransu ya basu umarnin karya ƙofar. Tun ba su kai ga cire ƙauren ba wani irin wari ya doko hancinsu, da sauri suka ja baya aka fara tunanin wanda zai fara shiga amma duk wanda aka ce ya shiga sai ya noƙe. Mafi yawa daga ciki ba don sun ji muryarta ba ɗauka za su yi mutuwa ta yi gawarta ta fara wari.

Ana cikin haka wani daga cikin Fadawan ya yi ta maza ya tura kansa ciki. Ganin haka ya sa sauran ma suka rufa masa baya, sai dai shigar su ba ƙaramin ɗaga musu hankali ya yi ba. A tsorace suka ja da baya kowa yana neman hanyar guduwa sakamakon abin da suka riski Fulani Maryama tana shukawa. Suna gudu tana biye da su a baya sai a lokacin jama'ar wurin suka farga da waɗansu irin manyan tsutsotsi da suke yawo a harabar wurin.

Da gudu suka faɗa cikin faɗar, Fulani Maryama tana biye da su zawo na zuba, a bakin ƙofar wasu Fadawa suka tare ta don a yanayin da take ba za su taɓa barinta ta shiga Fadar Sarki Aminullah ba. Suna shiga Fadawan da suke cikin fadar suka fara cewa, "Hattara dai! Hattara." Mutumin da ya fara shiga sashen Fulani Maryama ne ya fara magana, "Allah ya taimakeka babu lafiya Salman ne Salman..." Ban da sauke numfashi babu abin da yake yi da ƙyar ya samu ya ci gaba da cewa, "Fulani! Fulani ta kashe shi ga shi can tana cin namansa. Gabaɗaya al'aurarsa ta tsige a hannunta muka same ta." Hankali a tashe Sarki Aminullah ya kalli Bafaden yana shirin magana ya ji Fulani Maryama tana cewa, "Kun ga laifina Ɗana ne fa yazo zai haike mini don na cire al'aurarsa na yi laifi. Wa zai taimaka mini ya dakatar mini da ita? Gudawa ce nake yau sati guda kenan ta ƙi tsayawa. Ku barni na je wurin Takawa an ce shine shugaban masu zuƙe gudawa, gara ya zuƙe mini ita na huta ko kun ga laifina don na zo ma'aikatar zuƙe gudawa?" Da kansa Sarki Aminullah ya miƙe ya tako zuwa bakin ƙofa don ganin halin da Fulani Maryama take ciki, don tun da ta zo ƙofar fadar wurin ya turniƙe da wani irin wari.

Ba ƙaramin sanyi jikin Sarki Aminullah ya yi ba, lokaci ɗaya tsoron duniya da ruɗinta ya shige shi. Hawaye ne ya fara zubo masa ganin Maryama ƴar gayu mai ji da ƙwalisa tsaye a cikin jama'a, zawayi na bin jikinta kuɗaje suna yi mata gaɗa a kai. Fulani Maryama na hango Takawa ta buga tsalle tana ƙoƙarin kwaye zanin jikinta ta ce, "Wallahi kaine ko kaffara bana yi an ce kaine Shugaban masu zuƙe gudawa. Gudawa nake ta ƙi tsayawa amma Marduska yace na baka ka zuƙe ta, ka san me Salman ya yi? Shi fa ba Ɗanka bane wai ina Mahaifiyarsa ya zo zai haike mini ni kuwa na sa hannu na tsige abar, amma wallahi kaima idan na kamaka sai na tsige ta saboda ni ce na yi maka asiri baka iya taɓuka komai game da iyalanka, nima sai nake nuna na damu don kar a zargeni duk fa na yi ne don karka ƙara haihuwa, kuma dama Marduska ya faɗa kai da haihuwa sai a lahira." Fulani Maryama na gama magana sai ji suka yi tsuuuu! Wata gudawar na ƙara zirarowa ta gefen ƙafafuwanta. Hannuwa biyu ta sa ta fara kwasa tana turawa baki tana cinyewa ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya bada umarnin a wuce da ita turu.(Gidan Mahaukata)

Kafin wani lokaci tuni labarin abin da ya faru ya baza ciki da wajen Masarautar Kano wannan lamarin ba ƙaramin taɓa zuciyar mutane da yawa ya yi ba.

Ɗaki guda aka ware aka saka Fulani Maryama a ciki, tun da aka kaita ban da gudawa babu abin da take yi. Idan ta yi abarta ta cinye kayarta tun tana cin iya zallar gudawa har ta fara yagar naman jikinta tana ci. Haka wasu daga cikin sassan jikinta suka fara ruɓewa suna wari daga ƙarshe da masifar abin ya taso mata haka ta saka baki ta rinƙa cizgar Nononta har sai da cire guda ɗaya. Hatta abinci ta daina ci koda an zura mata ta window bana ci sai dai ya lalace a haka, akwai ranar da Mai zuba musu abinci ta zura mata abinci ta window bata san Fulani Maryama na laɓe ba, sai ji da yi ta kafawa hannunta cizo har sai da ta cire mata Ɗan yatsa ɗaya. Tun daga ranar suke zuba mata abinci a leda suna wurga mata, tun da ta ji daɗin naman jikinta ta daina bi ta kan kowanne irin abinci.

Duk wanda ya ga gawar Salman sai da ya zubda ƙwalla sakamakon irin kisan wukaƙancin da Mahaifiyarsa ta yi masa, saboda ya jima a mace jikinsa har ya kumbura ban da wari babu abin da yake yi. A haka aka sallace shi a ka kai shi makwancinsa aka binne shi domin jikinsa ya yi lalacewar da ba za a iya wanke shi ba.

Bayan kwana biyar.

Fulani Fahima, Maleek, Shukra, Mai babban ɗaki, da Sarki Abdallah sune suka dira a Masarautar Kano. Murna wurin Maleek kamar ya fi Shukra farin ciki da bayyanar iyayensu, babbar tarba aka yi musu sai da suka ci suka sha sannan aka fara mayar da labari. A nan suke jin labarin abin da ya faru da Fulani Maryama, duk irin mugun abun da ta aikata sai da suka ji tausayinta Fulani Zaliha da ke gefe har da hawayenta. Duk budurin da ake Maryo ba ta ji labarin zuwansu ba don Saif cewa ya yi sai sun zo zai sanar da ita. Tun da aka kai Maryo Abu take ta matsantawa Saif akan ya bata takardarta ya so ya riƙe su duka biyun a matsayin matansa amma fir Abu ta shafawa idonta toka, babu yanda ya iya a ranar da suke da kwana uku da aure ya aika mata takardarta ba tare da Maryo ta sani ba. Sosai Maryo ta zage take nunawa mijinta kulawa da soyayya, a cikin kwanakin har wani canjawa ta yi ta ƙara haske saboda kwanciyar hankali.

Kamar daga sama haka Maryo ta ji sallamar su Shukra, tana fitowa ta hango ƴar uwarta. Wani uban tsalle ta buga ta ɗane Shukra tana yi musu barka da zuwa. Maleek da ke gefe ya yi gyaran murya yace, "Ki yi dai a hankali don ba ita kaɗai ba ce." Kunya ce ta kama Maryo ta ja ƴar uwarta suka wuce ɗaki. Bayan shigarsu ba daɗewa Fulani Fahima da Mai babban ɗaki suka shiga nan fa aka baje da hira. Mai babban ɗaki na maƙale da Maryo kamar wani zai ƙwace ta nan aka jajanta abin jajantawa, a ka yi san barka ga abin murna da farinciki.

Kwanansu ɗaya a Masarautar Kano gabaɗaya suka ɗunguma zuwa ƙasar Zazzau, don tun a ranar da su Maleek suka dira Sarki Muhammad Safyan ya aiko da masu tarba haɗe da kekunan Dawakai waɗanda za su tafi da su gabaɗaya zuwa Masarautar Zazzau.

Lokacin da suka sauka a wani babban falo aka tarbe su, falon cike yake da iyalan Sarkin Zazzau yara da manya Maza da mata. Tun da suka shiga Fulani Badawiyya take bin su da kallom sha'awa lolaci ɗaya ta ji yaran sun kwanta mata. A ɓangare ɗaya kuma tana kallon kamaninsu kamar ta san mai yanayin fuskarsu.



_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[15/02, 18:03] Ameera Adam🌚: 75...


🔚🔚

ƘARSHE

Gabaɗaya iyalan Sarki Muhammad Safyan kansu a ɗaure yake da wannan sabon yanayin da Mahaifinsu ya ɓullo musu da shi, ban da Yarima da babu wani mamaki a tattare da shi don ya san maƙsudin zaman. Abin da ya ƙara ɗaure musu kai shi ne saukar da a ka yi wa Sarkin Kano da tawagarsa, saɓanin baya da ko sunan Masarautar Kano ba a cika ambata a Masarautar Zazzau ba. Hankalin kowa a kwance yake ban da na Fulani Maimuna da tun tuni jikinta yake bata akwai wani abu a ƙasa, ga shi yanda ta lura kwana biyu Takawa baya bata fuska ko turakarsa ta je zai ce ta fita ta ba shi wuri. Daga ƙarshe ma idan ta aika neman iso baya bata izini, dukda ta san an kama ɗan aikenta amma tana da yaƙinin a irin kashedin da ta yi masa ba zai taɓa tona mata asiri ba. A ɓangare ɗaya kuma tana ganin koda ya tona mata asiri a yanda take da Takawa ba zai taɓa amincewa da maganarsa ba, kuma duk hanyar da za ta bi don ganin ta wanke kanta sai ta bi ta don haka fargabarta ta ragu. Amma haka kawai ta ji zuciyarta bata aminta da waɗannan tagwayen da ta gani ba hasalima ji ta yi duk duniya bata ƙaunar buɗe ido ta gansu a gabanta.

Tun da suka zauna idon Saif yana kan Maryo motsi ɗaya biyu sai sun haɗa ido, suna haɗa ido zai sakar mata murmushi sai dai ta yi masa murmushi ta ɗauke kanta don da alama shi ya manta a wurin da suke zaune. Ta shi ta yi ta fita aka nuna mata makewayi don yin fitsari, tana fita Saif ya bi bayanta Fulani Zaliha har sai da kunya ta kamata don lamarin na Saif ƙara gaba yake yi. Tana fitowa daga banɗaki sai ji ta yi, ta yi karo da mutum a tsorace ta ja da baya za ta faɗi ta ji ya rungumota jikinsa yana dariya. Shagwaɓe murya ta yi tana kai masa dukan wasa ta ce, "Wallahi ka bani tsoro ban san kana wurin nan ba." Hannuwansa biyu ya sa ya zagayo da su ta bayanta yana jin bugun zuciyarta har cikin ƙirjinsa, kumatunta ya sumbata yace, "Na yi kewar Matata tun jiya aka nesanta ni da ita na gaza daurewa shi ya sa na biyo a bata." Hararar wasa ta wurga masa ta ce, "Ai kuwa ni da Kano sai na yi wata biyar don sai na sha Nono na ƙoshi." Kansa ya zura wuyanta yana ɗan hura mata iska yace, "Ai kuwa da na zauna sai a bamu ɗaki idan lokacin komawar ya yi sai mu tafi tare kin ga sai ki samo mana ɗan Zazzau." Da sauri ta hau kiciniyar ƙwacewa tana cewa, "Wallahi Habibi sam baka jin kunyar faɗa magana, sake ni na tafi kar wani ya ganni."

Riƙe ta ya yi tsam sannan yace, "Ai gaskiya na faɗa! Da gaske idan aka ce za a riƙe mini matata sai dai a riƙemu tare." Suna na tsaye Maleek ya ƙaraso yana faɗin, "Laila Majnun idan kun gama ku ake jira." Maryo ba ƙaramar kunya ta ji ba tana shirin ƙwacewa ta ji Saif yace, "Kai kuma Ɗan sa ido ba sai ka tsaya daga baya ka isar da saƙon ba?" Maleek ya juya yana cewa, "Lallai Yaro wuyanka ya yi kauri bari na sanar da su Takawa abin da na gani ƙila su..." Da sauri Maryo ta yi gaba tana cewa, "Don Allah Ya Maleek kar mu yi haka da kai." Suka wuce gabaɗaya suna dariya.

Sai da suka ci suka yi ƙat sannan aka shigo da wani mutum jikinsa jina-jina da ƙyar yake iya takawa a kan ƙafafuwans. Tsuggunar da shi a ka yi a gaban Sarki Muhammad Safyan sannan aka shiga da wata Tsohuwa, ita ma zama ta yi saitin wurin da Mutumin yake. Suna shiga wani Uban gumi ya jiƙe ta da sauri Fulani Maimuna ta sunne kai za ta fita, Sarki Muhammad Safyan ya dakatar da ita. Tun da ta yi tozali da Dillaliya hantar cikinta ta hau kaɗawa, ilahirin jikinta ban da rawa babu abin da yake.

Bafaden da ke gefen daman Sarki Muhammad Safyan yana shirin magana, Takawa ya dakatar da shi ta hanyar ɗaga hannu sannan ya dubi mutumin da ke tsugunne, sai da ya buɗe taron da Addu'a sannan ya ci gaba daji cewa,

"A wannan lokacin ina zaune a gabanku ne a matsayin Mahaifi ba Sarki ba, maƙasudin haka ya samo asaline ta wasu ɓoyayyayen al'amari, wanda zai bayyana a ta bakin wannan bawan Allahn. Kai yaro me ye sunanka muna son ka maimata abin da ka faɗa a kwanakin baya."

A firgice Fulani Maimuna ta ɗago gumi na ci gaba da yanko mata, jikinta tamkar mazari haka yake kaɗawa da sauri-sauri. Mutumin ya sauke wahallalan numfashi sannan ya fara da cewa,

"Da farko sunana Duna na shafe shakara da shekaru ina yi wa Fulani Maimuna aiki a sirrance, hasali dai ni tsohon Saurayinta ne..." Tun bai rufe baki ba Fulani Maimuna ta katse shi da cewa, "Ƙarya kake baƙin munafiki ko kalarka ban taɓa gani ba." Sarki Muhammad Safyan ya saki murmushi don ya san za a rina duk wani alamaun rashin gaskiya ya bayyana ga Fulani Maimuna, Duna bai kulata ba ya ci gaba cewa, "Fulani Maimuna ta sakani ayyuka da dama a gidan nan daga ciki har akwai Kisan Jakadiya Tine da satar tagwayen da Fulani Badawiyya ta haifa." Fulani Badawiyya da ke gefe ji ta yi kanta ya sara a firgice ta kalli Fulani Maimuna da sunne kai ƙasa, ba ta san lokacin da ta rushe da kuka ba ta dubi Fulani Maimuna ta ce,

"Sakayyar da za ki yi mini kenan Maimuna bayan rufin asirin da na yi miki ashe ni za ki tura rana, ki manta lokacin da duniya ta juya miki baya ni na baki sutura? Kowacce mace na da kishi amma haka na danne kishin mijina na sashi ya aure ki amma kika aikata mini haka? Me na tsare miki." Ganin haka ya sa Sarki Muhammad Safyan ya dakatar da Fulani Badawiyya ta hanyar rarrashinta, sai da ta yi shiru mutumin ya ci gaba da cewa, "Ba ni kaɗai na gabatar da aikin ba domin a lokacin asirina zai iya tonuwa saboda satar yara biyu ba wasa ba. Dillaliya Kaltume ita ta taimaka mini muka sace Jariran a ranar da suka cika kwana uku cif da haihuwa, mun samu nasarar sace su cikin tsakiyar dare. Kaltume ita ta ɗauki Hasana ni na ɗauki Usaina, muna fita daga Masarautar Zazzau kowa ya yi nasa wurin ni na jefar na Usaina a ƙasar Shanono ita kuma Dillaliya ta nufi ƙasar Ƙatsina da ita." Mun yi wannan dabarar ne domin kar asirimun ya tonu don a lokacin na yi niyyar murɗe wuyan Usaina na kashe ta sai tausayin yarinyar ya saukar mini. Ita dama Dillaliya tashin farko ta ce ba za ta iya kashe Jariri ba dama guba za a bata za ta iya zuba mata. Amma don mu amshi ladanmu sai muka cewa Fulani za mu aiwatar da abin da ta umarcemu. Sanin bana bata matsala a aiki ya sa ba ta damu ba ta sallam mu da dukiya mai yawa ta kuma gargaɗi Dillaliya da ko da wasa ta dawo Masarautar Zazzau sai ta sa an hallakata. Nima ta yarje mini zamana ne saboda tana bani ayyuka kuma ina zartar mata. In taƙaice muku labari ba tun yau ta ba ni kwangilar kisan Yarima ba amma kullin na tunkare shi da niyyar kisa sai inji ya yi mini kwarjini, haka kawai na kasa zartar da ƙudurina a kansa.

Sanadiyyar haka har sai da muka samu matsala da Fulani sai daga baya muka sasanta. Daga ƙarshe ta sanar da ni ta samu wacce za ta kashe shi idan ta kashe shi ni kuma sai na kashe ta. Ana haka har ranar da ta umarce ni da na kashe wata baiwa mai suna Abu daga nan asirina ya tonu. Amma don Allah a yi mini rai wallahi tsautsayi ne." Yana gama maganar Falon ya yi tsit ban da sautin kukan Fulani Badawiyya babu abin da yake tashi. Gabaɗaya jikinsu ya yi sanyi Maryo da Shukra sai hawaye suke kamar haɗin baki suka miƙe lokaci ɗaya suka ƙarasa wurin Mahaifiyarsu suka rungumota suna fashewa da kuka.

Babu wanda ya hanasu sai da suka yi mai isarsu sannan Fulani ta ɗago ta kalle su da kallon tuhuma, cikin kuka Maryo ta gyaɗa kai tana cewa, "Mune Ammi" Da sauri ta waiga wurin Sarki Muhammad Safyan suna haɗa ido ya gyaɗa mata kai yana cewa, "Mun ɓoye miki ne ni da Ɗanki saboda na san ki da rikici sai ki ɗaga mana hankali kafin zuwansu."

Fulani Badawiyya ta rungumo su tana godewa da Allah ya bayyana mata Tagwayenta, lokaci ɗaya farinciki ya mamaye zuƙatan ahalin Fulani Maimuna ta fashe da kuka ta rarrafa gaban Mahaifiyarsu Maryo tana neman yafiya. Sarki Muhammad Safyan da kansa ya miƙe ya ƙarasa wurinta. Hannu ya sa ya riƙota sai da ya kaita har bakin ƙofa sannan yace, "Ki fice mini daga ƙasata na sake ki saki Uku. Umarnin gaggawa na baki duk wanda ya ƙara ganin ƙafarta a ƙasarta a kawo mini ita hukuncinta zaman gidan ajiya da gyaran hali na dindindin." Yana gama maganar ya janyo ƙofa ya rufe, sanin halin Zafin Sarkin Zazzau ya sa ba ta yi wata-wata ba ta fice daga Masarautar yara na binta da dutse suna jifanta.

Dillaliya cikinta ne ya kaɗa don ita bata san irin hukuncin da Sarki zai sa a yi mata ba, tana cikin tunani Sarki ya bada Umarni aka fitar da ita tare da tsula mata bulala hamsin. Shi kuwa Duna sakamakon ya yi kashen-kashen rayuka Sarki ya sa aka tura shi gidan yari ɗaurin rai da rai.

Bayan an gama jimami nan ƴan uwa da abokan arziƙi suka shiga nunawa su Maryo kulawa da soyayya, nan aka shiga nuna musu dangi na kusa dana nesa.

Matan Sarkin Zazzau huɗu, Mahaifiyar su Maryo ita ce Uwar gida sai bayan aurenta da shekara biyar da Haifi Yarima Kaleed tana cikin goyonsa Maimuna ta je ta same ta da buƙatar ta taimaka mata akan Sarki ya aureta saboda wasu ƴan Fashi sun yi mata fyaɗe lokacin da suke hanyar tafiya zuwa garinsu da ke Ƙasar Zamfara. Da ƙyar Mahaifiyarsu Maryo ta shawo kan Sarkin Zazzau ya amincewa auren Fulani Maimuna, an yi aurenta da shekara shida ta haifo ƴan biyunta duka mata.

Mahaifiyarsu Maryo da Mahaifinsu Ɗan wa da Ƴar ƙanine dukkansu gadon jinin Sarauta ne na Masarautar Zazzau, su Maryo suna da Ƙanne biyu Mace da Namiji, Nurain da Nu'aima. Gabaɗaya ƴaƴan Sarki Muhammad Safyan goma sha huɗu maza bakwai mata biyar.

Farincikin wurin ahalin Sarki Muhammad Safyna ba zai musaltu ba ririta su Maryo ake kamar tsoka ɗaya a miya, attajirai, ƴan kasuwa, ƴan uwa da abokan arziƙi sai dafifi ake yi wurin zuwa taya Sarkin Zazzau bayyanar Ƴaƴansa.

BAYAN WATA BIYAR

"Lafiya kike ta ɓata fuska waya taɓa mini ke Fulani na?" Sarki Aminullah ya faɗa cikin zolaya don da alama gimbiyar ta shi rikici take ji. Fulani Zaliha ta dube shi hawaye na ziraro mata ta ce, "Don Allah yanzu me ya fi wannan abin kunya? A ce Sirikata na da ciki ni ina laulayi." Kamar wanda aka yi wa busahara haka Sarki Aminullah ya washe baki cikin farinciki yana faɗin, "Da gaske kike?"

"Duk wasu alamu sun gama bayyana yau wata biyu kenan rabona da baƙon wata ga alamomin cikine sun bayyana a jikina." Sarki Aminullah ya ɗaga hannuwa biyu yana godewa Ubangiji, tagumi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Amma kuma idan baka manta ba Maryama ta ce Boka yace ba za ka sake haihuwa ba an ya kuwa ma cikin ne?" Takawa ya ɗan ɓata fuska yace, "Kina nufin kema kin fara gasgata maganar Boka kenan, boka fa ba Allah bane da zai san gaibu. Aiki suke da aljanu suna tura su sama domin sato maganganun da Ubangiji yake yi da Mala'iku. Zancen boka zancan gaibu ne Allah shi kaɗai ya san abin da gaba za ta haifar. Kika sani duk haihuwa ku rinƙa jerawa da Matar Saif kina sauke mini tagwaye." Ai kuwa kamar ƙaramar yarinya haka Fulani Zaliha ta fashe da kuka tana girgiza kai.

Sarki Aminullah yace, "Saƙo ya same na auren yarinyar nan Safiyya (Matar Salman) Ance mini Ɗan Sarkin Nufe shi zai aureta cikin wata mai kamawa." Fulani Zaliha ta faɗaɗa murmushinta tana faɗin, "Allah sanya alheri ikon Allah ka ga lamarin Ubangiji kenan."

Tuni Abu ta riga ta gama iddarta har Yarima Kaleed ya yi maganar aurenta, da Farko ƙin amincewa ta yi sai daga baya ta amince aka ɗaura musu aure, lamarin ba ƙaramin daɗi ya yi wa Maryo ba haka ta tasa Abu tana yi mata shakiyanci kala-kala. Can Ƙasar Zazzau aka kaita cikin Masarautar Zazzau, ba ƙaramar kulawa take samu a wurin Fulani Badawiyya ta ɗauke tamkar ƴarta ta cikinta. Ba ƙaramin karamci Ina Habi take samu daga wurin Mahaifi da Mahaifiyar Maryo ba har ma da al'ummar Masarautar Zazzau bakiɗaya. Sun zama tamkar ƴan uwa sanadin ruƙon amanar da ta yi wa ƴarsu.

Watan Abu biyu da aure aka ɗaura auren Sarki Aminullah da Inna Habi, da farko fir Inna Habi ƙin amincewa ta yi don har da kukanta akan maganar aurenta da Sarki Aminullah, sai da Fulani Zaliha ta yi mata nasiha da nuna mata muhimmancin auren a yanayin shekarunta tun da ba wuce auren ta yi ba, sannan ta amince. Babu wani lokaci da aka ɗauka aka ɗaura musu aure. Fulani Zaliha da kanta ta kai Inna Habi turakar Sarki Aminullah, lokacin da ta kaita sai da ta yi musu tsiya sannan ta fice ta basu wuri. Rayuwa suke cikin farinciki, zama suke na tsakani da Allah kamar ba kishiyoyi ba don dama Fulani Maryama ita kaɗai ce mai tsananin kishi duk cikin matan Sarki Aminullah.



Please Login or Register in order to submit comment