Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne kawai saboda ina gudun zalincin da zaki aiwatarwa talakawa na, ko kaza bana fatan ƙara rashinta bare bil Adam." Yana gana faɗa ya miƙe tsaye yana gyara zaman rawaninsa sannan ya wuce, da sauri Maryo ta yi gaba fuuuuu har mamakin saurinta suke yi saboda wata irin tafiya take yi kamar za ta tashi sama. Lokacin da suka shiga Fulani Babba na tsaye ƙiƙam kamar gunki ko motsin kirki ta kasa yi, Me Babban ɗaki tana kishingiɗe a jikin lallausan daddumai. Mazauninsa ya je ya zauna ga mamakinsa sai ya ga mutane na ta hankaɗowa cikin fadar wasu har bakin ƙofa. Maryo ce ta miƙe tsaye ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya, sannan ta juya ta kalli Fulani Babba ta nunata da ɗan yatsa sai a lokacin Fulani ta motsa tana sauke ajiyar zuciya kamar wacce ta yi tseren gudu. Kallon mutanen wurin ta yi ta ce, "Ke baƙar munafuka maza ki buɗe baki ki gaya musu mugun halinki da mugun abin da kika aikatawa waccen baiwar Allahr da bata ji ba bata gani ba." Fulani Babba ta durƙushe a wurin ta ce, "Don Allah ki rufa mini asiri" Tun bata rufe baki ba Maryo ta sa hannu ta matse bakinta nan take ta fasa ƙara sai ga haƙoran Fulani Babba suna faɗowa ɗaya bayan ɗaya kamar tsabar masara.

"Allah ya taimake ka ya baka yawon rai, lafiya me yake faruwa ka nemi magana da ni kuma na ga duk kayi wani iri." Damuwarsa ce ta bayyana a fili ƙarara ya kalleta fuska ba walwala yace, "Masarauta Adamawa ce babu lafiya wani abun almara wai Me Babban ɗaki ta dawo." A razane ta kalle shi nan ya zayyane mata abin da yake faruwa, suka haɗu suna jajantawa. Sun jima suna wannan hirarar sannan Sarki Aminullah ya dube ta yace, "Zaliha na kira ki ne dangane da yaran nan." Da sauri ta juyo gabanta na faɗuwa ta ce, "Ina fatan ba wani laifi ya aikata ba?" Murmushin gefen baki ya yi yace, "Ba zamu yi muku maganarsa ba sai idan laifi ya yi?" Fulani Zaliha sai ta ji duk bata kyauta ba ta ce, "Tuba nake ranka shi daɗe" Sarki Aminullah ya ci gaba da cewa, "Lokaci ya yi da ya dace su fito da matan aure su yi aure. Saboda shekarunsu sun fara ja nima ina buƙatar ganin jika na na wurin ƴaƴana maza." Murmushi Fulani Zaliha ba ƙaramin daɗi ta ji ba ta ce, "Gaskiya na ji daɗin wannan maganar Ranka shi daɗe. Kuma dama kwana biyun nan ina zargin akwai yarinyar da ya faɗa soyayya da ita, amma in sha Allah zan tuntuɓe shi a daren yau ba sai gobe ba." Murmushi Sarki Aminullah ya yi yace, "Zaliha yaushe kika bar kunyar ki ta fulani ne? Kamar ba ke ce wacce ko kallona bakya iya yi, amma yanzu na ga sam kin canza." Murmushi ta yi ba don karta waiwayo da abin da ya wuce ba da ta bashi amsa, saboda tun lokacin da kowa ya yi watsi da su ita da Saif tun yana ƙarami ta cire kunyar idonta bata yi wa kowa kara akan Saif. Murmushi ta ƙara yi sannan ta ce, "Haba dai Ranka shi daɗe kawai dai haka ka gani." Daga haka suka ci gaba da hira cikin farinciki.

"Saif Mahaifinku ya same ni wata magana." Kallon mahaifiyarsa ya yi cikin nutsuwa ya gyaɗa mata kai, ta ci gaba da cewa, "Yace kai da ɗan uwanka ya kamata ku fito da matan aure, idan kuma akwai wacce kake so sai ka sanar da ni ko ka sanarwa da mahaifinka." Murmushi ya yi ya fara yi wa mahaifiyarsa bayani kai tsaye saboda ya mayar da ita kamar abokiyar shawararsa, ya numfasa yana faɗin, "Ammi wallahi ni dai babu wacce nake so sai ƴar Abuh amma bansani ba ko za ta amince da ni." Farinciki ne ya lulluɓe zuciyar Fulani Zaliha ta ce, "In sha Allah za ta ma amince da kai, amma idan haka ta faru na fi kowa farinciki."

MEYE HARSASHEN KU KO ABUH ZA TA AMINCE DA AUREN MASOYIN MARYO? 😢

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[09/12/2021, 14:24] Ameera Adam🌚: 44...



Murmushi Saif ya yi don ko ba komai Mahaifiyarsa ta ƙara masa ƙwarin gwiwa kuma za ta ƙaunace ta don ya hangi zallar ƙaunarta a idanun mahaifiyarsa. Miƙewa ya yi yana murmushi sai kuma ya ji duk kunya ta kamashi, da sauri-sauri ya miƙe ya fice daga ɗakin. Mahaifiyarsa ta kalle shi tana dariya a zuciyarta tana mamakin wai yau Saif ita yake jin kunya. Saif yana fita ya wuce ɗakinsa yana jin wani irin farinciki a zuciyarsa, wata irin ƙaunar Abuh ce take yunƙuro masa da shi kansa be san lokacin, da ya tsunduma cikin kogin sonta ba lumshe ido ya yi kamar a mafarki sai gani ya yi fuska Maryo raɗau a cikin ƙwayar idonsa. Da sauri ya buɗe idonsa yana sai yake jin kansa na juya masa, wata iska ya furzar me zafi yana jin ransa yana masa wani irin suya. Kwanciya ya yi yana jin ransa babu daɗi a hankali tunanin Maryo ya fara yi masa kai komo, ta shi ya yi zaune yasa hannu biyu ya rafka uban tagumi.

Gabaɗaya mutanen wurin ido suka zuba mata hankali a tashe, tsit wurin ya ɗauka ban da ihun Fulani Babba babu abin da yake tashi a wurin. Sarki Abdallah ne ya kalli Maryo ya buga mata tsawa cikin fusata, "Ke! Wanne irin abu kike yi haka ne?" Maryo bata saurare shi ba ta kalli Fulani Babba da take cikin galabaita ta ce, "Muna sauraronki " Fulani Babba ta kalli Me babban ɗaki da ke zaune a gefe ta ce, "Don Allah ki gafarce ni Ranki shi daɗe ki yafe mini amma don Allah karku tona mini asiri." Muhsin a maza shi ne babban ɗan Fulani Babba, shekararsa Ashirin da biyar. Shigowarsa kenan fadar ya ga halin da mahaifiyarsa take ciki, wata razanannniyar tsawa ya bugawa Maryo da har sai da wasu daga cikin mutanen Fadar suka tsorata, a hassala ya ƙarasa ciki yana cewa, "Ke me kike yi haka ne baki da hankali ne?" Maryo bata juyo ta kalle shi ba kuma bata fasa abin da take yi ba. Kallon Fulani Babba ta yi fuska a haɗe, tun kafin ta fara magana Fulani babba jiki na rawa ta fara magana, "Don Allah ku gafarce ni amma tabbas na yi kuskure, wallahi tsautsayi ne da sharrin sheɗan." Me babban ɗaki ta ɗago ta kalli Fulani Baba ta ce, "Na tabbata ba ni ba hatta sheɗan ɗin sai an yi muku hisabi da shi saboda sharrin da kika yi masa, munafuka algunguma." Muhsin shiru ya yi yana mamakin wannan lamari Maryo ta kuma kallon Fulani babba tana gyaɗa mata kai, da sauri Fulani Babba ta haɗa hannuwa cikin tashin hankali tana roƙonta, "Don Allan ki yi haƙuri karki azabtar da ni wallahi zan faɗa." Maryo murmushi ta yi ta fara takawa a hankali a nemi wuri ta zauna, ta ɗebo manyan idanuwanta ta zubawa Fulani babba wanda da alama ta yi haka ne domin ta fara sauraron abin da za ta faɗa. Fulani Babba kallon mutanen fadar ta yi ta sunkuyar da kai cikin nadama, don ta rayawa zuciyarta gwara ta faɗi abin da ta aikata ko ta huta, don waccen azabar ma da ta yi mata bata gama sakinta ba. Ɗagowa ta yi ta kalli Sarki Abdallah idanunta suka ciko da ƙwallah, don ta san ƙarshen zamanta ya zo da shi ta fara da cewa



"Shekaru talatin da biyar da suka gabata Sarki Abdallah ya kasance sarki a masarautar Adamawa, kuma ya gaji mahaifinsa ne wanda ya yi sarauta kafin shi, bayan rasuwarsa aka naɗa shi sakamakon shine ɗansa ɗaya tilu namiji. A lokacin da aka naɗa shi sarauta mu biyu ne kaɗai matansa ni ce uwar gida Fulani Maimuna amarya, a lokacin ƴaƴana uku duk mata ƴaƴan Fulani Maimuna biyu amma haihuwarta uku namijin ya rasu. bayan shekara biyar da hawansa karagar mulki sai ya auro Fulani Fahima ita ma da aurenta ko shekara ba ayi ba wan mahaifiyarsa ya bashi ƴarsa wato Fulani Sadiya. A haka dai idan ka ga zamanmu zaka rantse da Allah lafiya ƙalau muke zaune, amma a baɗini ba haka bane ta ciki na ciki ne, babban abin da ya fi ɗaga mini hankali yadda duka amaren da aka yi mana ba su jima ba kowacce tana ɗauke da juna biyu, kuma har lokacin babu wanda ya haifi ɗa namiji da ni da Fulani Maimuna. A da kafin ƙarin auren Sarki Abdallah ba ma zaman daɗi da Maimuna amma da ya yi aure sai na janyo Maimuna jiki muka haɗewa Fahima kai, tun Fulani Maimuna na ɗari-ɗari dani har ta saki jikinta muka ɗinke kamar babu wani da ya taɓa shiga tsakaninmu. A kwana a tashi har Allah ya sauki Fahima lafiya sai ga shi ta haifo ɗan ta namiji wato Abdulmaleek, a lokacin saboda baƙin ciki har ji nake kamar zan mutu, amma sai na danne na fara neman hanyar da zan halaka shi ta ruwan sanyi ba tare da wani ya zarge ni ba. Me babban ɗaki su biyu ta haifa daga Sarki Abdallah sai ƴar uwarsa Zakiya, a lokacin Me babban ɗaki haka ta shiga nannan da Maleek ita ce yi masa wanka da sauransa, tun ranar da aka haife shi ta ɗaga shi sama tana yi masa kirarin magajin sarki, wannan ba ƙaramin baƙantamin rai ya yi ba. Haka nima na sake aka ci gaba da nuna farinciki har da ni kamar babu abin da yake raina, har Maleek ya cika wata uku a lokacin ne kuma Fulani Sadiya ita ma haifo ɗan ta namiji kamar haɗin baki, a lokacin ne nida Maimuna muka shiga fafutukar neman yadda za mu kashe yaran amma duk inda muka je wurin bokaye sai ace mana Me babban ɗaki na jiƙa sanwa da sauran magunguna tsari tana wanke su da shi, don haka babu wani abu da za su iya yi akai, idan ma mutum ya matsa mugun abin da ya yi zai iya komawa kansa. Wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga mana hankali ya yi ba, daga ƙarshe sai Maimuna ta same ni ta ce ita kam ta fauwalawa Allah lamuranta amma ta tuba ta daina harkar biye-biyen malamai da bokaye, gudun karta zarge ni ko wata rana ta tona mini asiri yasa nima na sauya yanayi na cikin damuwa, na nuna mata tabbas mun aikata kuskure amma mu watsar da komai mu fauwalawa Allah buƙatunmu, wanda sam a zuciyata ba haka bane. Haka na ci gaba da biye-biye na a sirrance wani kuma na tura Larai baiwata ta je mini, a haka har wata rana na je wurin wani boka wanda yace tabbas zai yi mini aiki amma da sharaɗi, ban damu da sharaɗin da ya gindaya mini ba nan take na amince, wata laya ya ciro daga bakin wani zomo da ke tsugunne a gabansa ya miko mini yace ina shiga gida karna kula kowa na wuce sashen Me babban ɗaki, ko na shiga karna yi mata magana kawai na damƙi hannunta na saka mata layar a ciki nan take ni da ita zamu ɓace daga wurin. Kamar ƙiftawar ido haka muka ɓace daga wurin sai gamu a ƙogon dutsen da boka yake, da mamaki Me babban ɗaki ta kalle ni ta ce, "Lafiya ina ne nan kika kawo ni?" tun kafin na bata amsa Boka ya ja hannunta ya zaunar da ita akan wani farin dutse, kallo na ya yi yace, buƙatarki za ta ci gaba da biya matsawar tsohuwar nan za ta rayu a cikin kogon nan, amma muddin kika bari ta koma masarautarku kashinki ya bushe. Ban damu da abin da ya faɗa ba na bushe da dariya na ce, " Wanene ya isa ya mayar da ita idan ba ni ba? n Ni kuwa ko a mafarki ba na jin zan aikata wannan saɓon." Boka yace mini, "Ba za ta taɓa komawa ba, amma ba za mu kashe ta ba. Sai dai za ta zama matacciya a cen masarautarku, yanzu kina komawa za ki ga me siffarta a mace muddin ba ke kika bada ƙofar da za a fahimci wani abu ba babu wanda zai gane ba ita bace." Murmushin jindaɗi na yi masa na juya zan tafi Me babban ɗaki ta fashe da kuka ta ce, "Don Allah karki yi mini haka..." na katse ta da murmushi sannan na yi ficewa ta, abin da ban sani ba ashe duk wannan lamarin da nake nima ina ɗauke da ƙaramin cikin wata uku, kuma ina dawowa na samu ana ta rusar kuka ina zuwa ɗakin Me babban ɗaki na ganta yashe a kwance har sai da na ja baya na razana, ina fargabar kar asirina ya tonu. Ga duk wanda ya ga halin da na shiga zai ɗauka kiɗimewar mutuwa ce ta sani haka, nan kuwa ba haka bane ina fargabar kar a wayi gari Me babban ɗaki ta dawo, Kuma a washegari ne ɗan wajen Fulani Sadiya shima ya mutu, Fulami Maimuna da take da ciki wata bakwai shima ta haifeshi babu rai, ashe cikin ɗa namiji gare ta, Maleek kuma ya kwanta jinya. Haka na ci gaba da kaiwa Boka ziyara Me babban ɗaki tana cikin kogon dutsen tun tana yi mini kuka da magiya har ta daina, tsuntsaye da namun dajin da Boka yake kamowa shi yake gasa musu suna ci ita shi, a haka aka ci gaba da rayuwa har Allah ya sauke ni lafiya na haifi ɗana namiji. Yadda na ɗauka Sarki Abdallah zai yi zumuɗi sai na ga sam ba haka bane, amma ban damu ba tun da nima na haifi namiji, idan aka cire Maleek duk wacce za ta haifi namiji a bayan nawa yake. A kwana a ta shi har yara suka girma duk bokaye na sun gagara kashe Maleek, sai na lura da Takawa yana jan Maleek a jiki har yana koya masa wasu al'amuran dangane da harkar mulki, nan take na sa boka ya yi aiki akansa don ya ja ra'ayinsa a harar karatun nasara to na san muddin ya karkata ana ko da nan gaba ne bayan mutuwar Sarki Abdallah, jagororin da za su yi naɗin sarauta ba za su naɗa shi ba za su ce ya fi karka da ilimin nasara be san abin da ya shafi sha'anin mulki ba. Wani tashin hankali dana shiga da boka ya sanar da ni akwai yarinyar da Maleek zai auro wacce za ta zame mini ciwon ido nan gaba, yace wai tana daga cikin FILSIFI, shi yasa ko da Maleek ya auro Shukra na fi kowa tsamari wurin kafa mata ƙahon zuƙa dukda dama kowa ba ƙaunarta yake ba. Duk ƙulle-ƙullen da na yi har ta bar gidan nan ashe ban tsira ba sai ga shi yanzu ta ƙara dawowa kuma ta bankaɗo abin da na ɓoye shekara da shekaru." Kamar haɗin baki haka Fadar gabaɗaya suka ɗauki salati cikin al'ajabi, Sarki Abdallah idanunsa ne suka yi jawur saboda ɓacin rai, a hankali hawaye ya fara gangarowa daga idanunsa. Tsam ya tashi ya ƙarasa wurin mahaifiyarsa ya rungumeta ya fashe da kuka, Dogarawan Sarki sunkuyar da kansu suka yi zuciyarsu babu daɗi, Muhsin wani irin abu ne ya turniƙe shi yana jin kalaman Mahaifiyarsa na maimaita kansu a cikin ƙwaƙwalwarsa. Maleek da ke gefe shiru ya yi ya kafe Fulani Babba da idanu, dan har lokacin mamakin abin ta faɗa yake yi gani yake kamar a mafarki ne, ɗan yatsansa ya tura baki ya ɗan gantsa cizo, jin zafin haƙoransa a hannunsa yasa ya tabbatar da gaskiya ne abin da yake faruwa. Maryo murmushi ta yi ta kalli Fulani ta ce, "Wanne hukunci kike so na yi miki? Kuma ki gyara bakinki ni ba shukra bace wataƙila wata filsifin ce ba ni ba." Fulani Babba ta ce, "Don Allah ayi mini afuwa, ki gafarce ni Shukra akan cutarwar da na yi miki." Maryo bata saurareta ba ta miƙe ta fara tsalleke mutane tana murmushi ta fice, tana fita Fulani babba ta zunduma ihu tana yage-yage haɗe da kaiwa mutane wawura. Haƙwaranta na ƙasa ta fara tsinta tana haɗiyewa tana gama cinye su ta danne wani Dogari tun kafin a yi wani yunƙuri, ta naushi bakinsa ta tura hannunta ta ƙwaƙulo haƙoransa ta fara wurga su baki ɗaya bayan ɗaya tana haɗiyewa. Da ƙyar aka ƙwaci dogarin fuskarsa har ta fara kumbura, da sauri Muhsin ya ƙarasa yana mata magana ta janyo shi za ta kai masa duka a baki, da kyar aka ƙwace shi ba a ɗau lokaci ba Sarki Abdallah ya bada umarni da akaita turu (Gidan mahauka) a cen ɗinma yace a ware mata ɗaki ita kaɗai don karta illata sauran.

Cikin zumuɗi Fulani Maryama ta sanarwa da Sarki Aminullah yadda suka yi da Salman, shi ma ba ƙaramin daɗi ya ji ba. A nan yake sanar mata da Saif shima yana da wacce yake so daidaitawa kawai ya rage su yi, murna ta nuna a fili dan ita tana murnar ne saboda buƙatar kanta, da nishaɗi ta dube shi ta ce, "Allah ya taimake ka sai dai wani hanzari ba gudu ba, ka san fa Salman be cika kule-kule ba don yace ka nemo ɗaya daga cikin ƴaƴan abokanka in yaso sa daidaita." Sarki Aminullah ya ɗan yi jim har sai da gaban Fulani Maryama ya faɗi tana fargabar kar ya ƙi amincewa, ta ga ya kalle ta yace, "Eh to sai dai na yi wa Sarkin Gaya ko Sarkin Ƙaraye magana na san suna da ƴaƴa mata ko kuma Sarkin Rano." da sauri Fulani Maryama ta ce, "Allah ya taimake ka Sarkin Gumel ma kamar yana da ƴaƴa ƴan mata, na ce ko a cen za mu nemi iri don yaran suna da tarbiyya." jinjina kai Sarki Aminullah ya yi yace, "Babu damuwa zan duba na gani." Satar kallonsa ta yi tana addu'ar Allah sa haƙƙonsu ya cimma ruwa don idan Salman ya auri ƴar Sarkin Gumel kakarsu ta yanke saƙa. Kallon tsaf ya yi mata yace, "Maryama na aika a zo da Sarkin Wanzamai a sirrance ya baki magani don gaskiya na damu da ganin kanki haka babu gashi, wannan ba ƙaramar matsala bace ace haka kawai ka wayi gari babu gashi ko silli ɗaya, ko ma'askin dare fa ba haka yake yi ba." Fulani Maryama yaƙe ta yi ta amsa masa don kada ta yi gardama ta tonawa kanta asiri ana zaune ƙalau, gara ta zuba ido masu maganin su zo su gama abin da za su yi su tafi. Ta tabbata makarin komai yana hannun Marduska don Marduska ya wuce tunanin me tunani.

Salman ya yi mamakin yadda ya sanarwa da Abuh amma babu ko ɗigon farinciki a tattare da fuskarta, amma kafin wannan lokacin ya tabbata ko mahaukaci ya san Abuh ta fara ƙaunarsa, be tursasa mata ba sai ma nuna mata ya yi da be fahimci abin da take nufi ba. Don haka ko da ya ga ta yi shiru ya kau da kai gefe don ƴan muskilancin ne akansa yace mata, "Zainab ki yi nazari akan abin da na sanar da ke amma ba zan tilasta miki ba, ina sauraronki zuwa nan da kwana biyu." Yana gama faɗa ya wuce, Abuh zama ta yi sai ga hawaye na bin fuskarta wannan shi ake kira da gaba kura baya siyaƙi. Idan har ta ce bata ƙaunar Saif ta yi ƙarya hasalima da shi take kwana take tashi a ranta, amma ta san hakan ba me yuwu bane. Ya za ayi ta auri mutumin da ƴar uwarta take begen shi babu dare babu rana. Girgiza kai ta fara yi tana faɗin, "Inaa sam wannan ba zai taɓa yuwuwa ba." Miƙewa ta yi da niyyar shiga sashen Fulani Maryama don ta sanar da mahaifiyarta halin da ake ciki amma tana gabda shiga ƙofa wasu dogarawa suka dakatar da ita, da mamaki ta kalle su da niyyar buɗe baki ta yi magana taji ɗaya yace, "Umarni ne daga Fulani Maryama ta ce kar a ƙara barinki ki shiga sashenta." Babu yadda Abuh ta iya haka ta juya tana jin zuciyarta babu daɗi, sashen su ta nifa zuciyarta da tunane-tunane, ta ɗaga labulen ɗakinta ta ji Fulani Zaliha ta ƙwala mata kira wanda ya yi daidai da faɗuwar gabanta, kamar mara jini a jiki haka ta juya jiki a sanyaye ta nufi turakar Fulani Zaliha ta russuna cikin girmamawa ta gaishe ta, "Barka da hutawa ranki shi daɗe" Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Barka dai ƴata ya ganki duk wani iri me yake damunki?" Abuh da sauri ta ɗago sai kuma ta ga sam ba za ta iya sanar mata da halin da take ciki ba don ta tabbata uwa uwa ce dole idon ta ce bata son Saif dole ba za ta ji daɗi. Don haka ta sunkuyar da kai ta ce, "Na je ganin Inna ta ne Dogarawa suka hanani shiga." Fulani Zaliha ta ce, "Kamar ya? Waye ya isa ya hanaki shiga ko Maryaman ce ta bada umarni?" A hankali ta gyaɗa mata kai. Ajiyar zuciya ta sauke ta ce, "Wannan ba hurumi na bane amma zan yi wa Takawa magana." Da sauri Abuh ta ce, "A'a don Allah karki gaya masa kar na yi wa Fulani Laifi." Murmushi Fulani Zaliha ta yi ta ce, "Zainab me ya sa kin fiye tsoro ne, yauwa ɗazu mun yi magana da Saif. Takawa yace su fito da matan aure shi dai yace kece zaɓinsa, ba ƙaramin daɗi na ji ba saboda ƴar gida za muyi amma ban sani ba za ki amince da shi?" Gabaɗaya Abuh dabaibayewa ta yi gumi ya fara tsattsafo mata, shiru ta yi ta faɗa duniyar tunani a duniya dai ta san Fulani Zaliha tana matuƙar ƙaunarta, bata taɓa ƙyamarta ba tana yi mata abin da uwa za ta yi wa ƴar ta. Jin shirun ne yasa Fulani Zaliha ta dafa kafaɗarta wanda shi ne silar dawowarta daga duniyar tunanin da ta faɗa, ɗagowa ta yi suka haɗa ido ta sauke kanta ƙasa, Fulani Zaliha ta ce, "Zainba! Na ɗauke ki tamkar ƴata idon bakya son Saif ki gaya mini ba zan miki dole ba, sai na sashi ya nemi wata." A hankali Abu ta ce, "Ba haka bane Ranki shi daɗe na amince." murmushin jindaɗi Fulani Zaliha ta ce, "Masha Allah, Tashi ki je Allah ya tabbatar da Alheri." Abuh bata iya amsawa ba ta miƙe a kunyace ta fice ta nufi ɗakinta, tana shiga ta fara zarya har lokacin gumi ne yake karyo mata.


SHA BIYAR GA WATAN SATUMBA A SHERAR DUBU ƊAYA DARI TARA DA HAMSIN DA ƊAYA
(15/09/1951)

Wanda ya yi daidai da ranar Laraba a ranar ne Sarki Aminullah da Abokinsa Sarkin Gumel, suka sanya ranar auren Salman Aminullah Muhammad da Safiyya Yusuf Kabir sai Saifullah Aminullah Muhammad da Zainab Ya'u Me Nagge. An saka ranar aure wata uku farinciki wurin waɗanan iyalan abin ya ƙi misaltuwa.

MARYO NA CEN AN YI WUFF DA MASOYINTA😢
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[10/12/2021, 19:46] Ameera Adam🌚: 45...



Lokacin da labarin sanya aurensu ya isa kunnuwan Abuh haka kawai ta ji gabanta ya yanke ya faɗi, tana daga ɗakinta a kwance ta ji Jakadiya tana ta zabga bambaɗanci da fadanci. Kasancewar Fulani Zaliha na cikin farinciki yasa ta kalli Jakadiya da murmushi ɗauke a saman fuskarta ta ce, "Jakadiya anjima a aiko a karɓi tukwici." Jakadiya

Please Login or Register in order to submit comment