Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

za ki yi iskancinki ki san a inda ya dace ki yi amma ki tabbatar da kin yi na farko kin yi na ƙarshe a nan. Tun ranar da kika fara zuwa wajenmu muka sanar dake dokokinmu kika amince dan haka ki kama kanki, duk abin da kika ga ya biyo bayanki sakamakonki ne." Fulani Maryama tsoro ne ya kamata dan sai a lolacin ta fahimci wautar abin da ta aikata. Cikin nadama ta russunar da kai ta ce, "Tuba nake Marduska na yi kuskure ayi mini afuwa, ka san duk wani mai rai ajizi ne." Murmushin jindaɗi ya yi ya kalli Fulani Maryama yana hura boɗareren hancinsa kamar na botorami yace, "Fulani Maryama kenan kedai zuma ce sai da wuta. Babu komai an yafe miki amma ki kiyaye gaba, Kuma ki bar murna karenki ya kama zomo billahilazi a kodayaushe komai yana iya tashi kwaɓarki na iya yin ruwa. Bar ganin yarinyar nan ta bar masarautarku ki ɗauka zaki miƙe ƙafafuwa yadda kike so a kodayaushe nayi bincike ina ganin bala'i haɗe da tashin hankali a cikin masarautarku. Na gaya miki a wannan karan me sha da rayuwarsa sai wanda Allah ya tseratar, ina tunanin tarihi ne zai ƙara maimaita kansa sai dai wannan karan abun zai fi ƙamari da muni fiye da tunanin me tunani, ina matuƙar tausayawa Sarki Aminullah domin shi mutum ne me sanyin hali amma wani dalili daban kan iya tabbatar da wani yanayi a masarautarsa. Tabbas ƙaddara dole idan har Allah ya rubuta saukarta akan mutum, guje mata kamar gujewa mutuwa ne sai dai wataƙila tazo da sauƙi ko akasin haka. Amma bana ganin wannan ƙaddarar zata iya zuwa cikin sanyin hali ba tare da ta girgiza mazauna da wajen cikin masarautar ba. Abin da yake ƙara ɗaure mini kai ta yadda na kasa ganin daga ina wannan ƙaddarar zata soma shin Zulik ne zai fara taso da ita ko Rayzuta ko kuma mai dannaniyyar zuciya Furzaan. Lamarin tattare yake da sarƙaƙiya me ɗauke da ɓacewar tunani, ina ƙara haska miki hanya ne domin ki kwana da sanin tashin hankalin ba zai zo miki da sauƙi ba, zama bai ganki ba domin su tanadi suka yi na dubbanin shekaru ke kuma daga yanzu naki tanadin zai soma. Ki yi ƙoƙari kija Zulik a jikinki asirin bil adam a yanzu baya taɓa tasiri a jikinsu sai dai ki haɗa da kissa nafi tunanin wannan ce hanya mafi sauƙi a gare ki. Ki cusa masa soyayyar mulki da zaƙin da ke cikinsa dukda shima a haukace yake ta wannan fannin, amma hakan da zaki yi zai iya sa ki samu wani matsayi a wurinsa kamar wancen karnin. Ni da kika ganni ƙarƙari na yi miki bincike na kuma sanar da ke halin da ake ciki, domin su Rayzuta sun fi ƙarfina ba zan iya ja da su ba idan kuwa na zaƙewa lamarin halaka ni a wurinsu ba abu ne mai wuya ba." Ya ƙarasa maganar yana kafe Fulani Maryama da idanu. Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba duk tayi fiƙi-fiƙi kamar sabuwar munafuka, kamar wacce take da gyambo a baki haka ta ɗaga laɓɓanta a hankali ta ce, "Marduska a duk lokacin da na ziyarce ka maimakon ka kwantar mini da hankali sai dai akasin haka, na zo ne dan ka bani mafita amma koyaushe sai dai ka dilmiyar dani cikin tashin hankali. Ka sare mini gwiwa ta yadda nake ganin ba zan iya aiwatar da komai ba dukda zuciyata tayi tsayuwar gwamin jaki. Macece mafita akan lamarin ta ina zan fara?"Marduska ya zura hannunsa cikin wutar da ke zaɓalɓalawa kamar wacce ake watsa mata makamashi, waɗansu gwarwashi ya ɗebo guda biyu ya murje su a tafin hannunsa ya ƙura musu idanu sannan ya ɗago da kai yana sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya yi tseren gudu yace, "Karki ki ji zafina ko kaɗan domin ba za ki fahimci amfanin zuwanki wurin nan ba sai gaba, idan har kin ɗauki shawarwarin da na baki na baya da wanda zan kuma baki a yanzu. Ni haska miki fitila nake wacce zata nusar da ke hanya me ɓillewa, shawara zan baki bansan yadda zaki ɗauke ta saboda kowacce ba lallai tayi miki daɗi ba, dan kowacce tana tafe da ƙalubale. Za ki iya fassara hakan da gaba kura baya damisa, ko kuma ki kira ta da gaba kura baya siyaƙi. Amma mafi muhimmanci a wurinki ki baje kunnuwanki domin ki ɗauki maganganun da zan sanar dake ɗaya bayan ɗaya. Nima fa bincike na yi sai kuma harsashe na bansani ba zai tabbata ko ba zai tabbata ba amma yana da kyau ki riƙe su, wataƙila Rayzuta ta dawo masarautarku wataƙila kuma ta tafi kenan dan ban ga yaƙinin juyowa masarauta a tattare da ita ba. Idan har ta dawo kiyi ƙoƙarin janta a jikinki, dukda nasan tsananin ƙiyayyar da ke tsakaninku. Ki kasance me ɓoye ƙiyayyarki a fili dangane da ita, idan ba haka Salman da kika haifa kina ji kina gani zai murɗe wuyanki har lahira. A haukace yake ya zauce akanta ta yadda baya ji bare gani akanta, duk wani abu da yake ƙoƙarin yi masa iyaka da ita yana iya hallakashi." Da sauri Fulani Maryama ta ce, "Ai tuni Maleek ya tafi da ita kuma lafiya ƙalau suke zaune.'Marduska ya ɗago jajayen idanunsa masu kama da gauta yace, "Wa yace miki suna zaune lafiya, Masarautar Adamawa na cikin ƙadamin da bil'adam bai isa ya dakatar da abin da yake faruwa ba a halin yanzu." Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙwaryar dake gabansa nan take sai ga hargitsin masarautar Adamawa ya sauka aciki, shafe ganinsu ya yi sannan ya ɗago yace, "Idan kina tantama bayan ki koma ki kira ɗaya daga cikin masarautar zai sanar da ke halin da ake ciki." Fulani Maryama jiki a sanyaye kamar wacce aka zarewa laka ta ce, "Wai ba garin nake nufi ba. Na ji kace Zulik na iya hallaka kowa bayan kuma Maleek ya tafi da ita babu wani abu da ya biyo baya." murmushi Marduska ya yi har sai da ƙaton wawulon bakinsa ya bayyana sannan yace, "Ai ya san ba matarsa bace. Hasalima ya san duk tsanani babu wani abu da zai taɓa haɗata da Maleek, sai dai akwai wata ɓoyayyar alaƙa a tsakaninsu da ba kowa ne ya san da ita ba, wannan alaƙa ya sa Rayzuta ba za ta bari a cutar da shi ba abu na biyu da ya sa ba zai cutar da shi ba yaron na da riƙon ibada sosai, dan haka zai yi wuya jinnu su iya cutar da shi amma ban tabbatar ba. Abu na gaba da zan shaida miki idan har Zulik ya ƙara kawo miki ƙudurin aurenta ki goya masa ba har a samu ya mallake ta, ita kuma sai ki samu ki lallashe ta da yaudara har ta amince ta aure shi. Amma kinsan duk wannan ba zai yuwau ba har sai abu ɗaya ya tabbata." Da sauri Fulani Marayama ta ce meye shi." Marduska ya ce, "Maryama kenan. Ai duk gaggawar unguwar zoma ta bari a haihuwa kuma duk gaggawar asara ta jira samu. Kawai daga ganin hadari sai ki fara wanka da kashi?" Fulani Maryama a ɗan kunyace take faɗin, "Marduska na ƙagu ne na ji, amma ai naƙuda ga me tsohon ciki ba laifi bane?" Ya mayar mata da amsa da cewar, "Idan har cikin ya isa haihuwa ba idan kuma bakwaini ne kinga wataƙila asararsa za'ayi." Shiru ta yi tana kallon sa bata tanka masa ba dan ta san idan ta biye masa sun dinga yi kenan. Marduska ganin haka yasa ya ci gaba da cewa, "Ba za ki taɓa karya ƙadarin Rayzuta ba har Furzan wato Saif ya yi aure, idan ma bakya jan sa a jiki yanzu ki fara domin ki fahimci halin da yake ciki, na ga soyayya a ƙarƙashin zuciyarsa idan har kike cire dannaniyyar soyayyar da Zulik ya binne masa ya faɗa tarkon soyyaya, ki hanzarta goya masa baya ya yi aure muddin be yi aure ba bana tunanin zaki iya tanƙwara zuciyar Rayzuta hakan ma zai iya jawo miki allura ta tono garma. Idan kika samu zulik ya aureta wataƙila ki ci gaba da cin karenki babu babbaka, wata ƙila kuma ƙaiƙayi kan iya koma kan masheƙiya. Ku ta tashi ku tafi na yi iya yi na" Fulani Maryama zata ƙara magana ya katse ta da cewar, "Babu abin da zan kuma furtawa dangane da halin da masarautarku zata iya shiga, abu ɗaya na sani zan baku magani wannan garin ya daina zuba, dama ba komai bane kashin aljanin da yake latsar kanku ne idan kuka wanke kanku da maganin har abada bazai dawo ba, na gama magana bana buƙatar tambaya ko ƙarin bayani ku ta shi ku fice." Yana gama magana ya wurga musu wani garin magni, Jakadiya sai raba ido take Fualni Maryama na gaba tana biye da ita zugwai-zugwai kamar jela har suka fice daga kogon dutsen.

Har bayan shigar Maleek ɗaki wurin Maryo bai daina jin iface-ifacen mata da ƙananan yara ba. Wata irin haniniya dokin yake me tsoratarwa wacce iskar da ke ta shi a wurin kaɗai abar tsoro ce, har lokacin jikinsa ban da rawa babu abin da yake yi musamman idan ya tuno halin da ya riski wani mutumi a ciki wanda har lokacin bai gane fuskarsa ba sakamakon yadda jini ya wanke ta. Daga bayan ɗakinsu ya ji kukan dokin kafin ya yi wani motsi yaji ya bigi katangar ɗakinsu har sai da wani sashe na daga jikin katangar ya zube. Kamar mace haka kuka ya ƙwace masa tare da furta, "Innalillahiwa'inna'ilaihirraji'un." da sauri ya faɗa kan gadon yana dukan Maryo yana kiran sunanta musamman daya tuna abin da dokin yake yi a waje yana gudun kar ya fashe ɗakin suma ya same su ya illata su. Abin da ya faru lokacin da su Maleek suka fita suna zuwa suka samu wani baƙin doki yana hauka, bakinsa ɗauke da wani mutum ya kafa masa haƙoransa ya riƙe masa gadon bayansa yana fyaɗa shi da ƙasa ban da jini babu abin da yake zuba a fuskar mutumin, wani babban tashin hankali da ban tsoro haɗe da ban ta'ajibi duk wurin da Dokin ya taka sai ƙasar wurin ta dagargaje ta tsage tana ƙoƙarin ruftawa ciki, duk waɗanda suke tafe a hanya haka ya dinga bangaje mutane suna faɗuwa a sume wasu kuma nan take kansu yake fashewa su mutu. Haka ya ci gaba da fyaɗa mutumin bakinsa da bango, ba shiri suna ganin haka kowa ya fara yi takai-takai domin neman ɓuya. Maleek cikin tashin hankali ya fara dukan Maryo yana cewa, "Shukra! Shukra wai me yake damunki wannan wanne irin bacci ne kike yi haka ki tashi mu tafi sashen Mai martaba zai fi nan saboda da alama dokin nan yana ƙoƙarin shigowa nan." Kamar gawa haka ya janyo Maryo ta yi yaraf ban da yana jin numfashinta zai iya rantsewa da Allah gawa ce a wurin, hannu ya sa da ƙarfi ya ɗan mari gefen fuskarta yana kiranta sunanta. Tun bai ɗauke hannunsa daga kan fuskarta ba jini ya fara ɗiga daga hancinta, buɗe dararan idanuwanta tayi suna haɗa ido da sauri ya wurgar da ita tare da ja baya, sakamakon ganin fuskar baƙin dokin da ya yi ƙuru-ƙuru ciki yana buɗe baki, gefen wajen da ya mareta da wajen da ya riƙeta tuni ya fara tsattsafo da jini, haka shima daga hannuwansa da gefen wajen da jikinta ya taɓa shi nan da nan ya yi burɗinɗin tare da yin taruwar jini. Yana daga gefe yana ƙoƙarin guduwa yaji ta fara magana cikin wata irin murya me amsa amo mara daɗin saurare, "Kana yawan shiga hurumin da ba naka ba, amma ina ƙara jan kunnenka da ka tsaya matsayinka. Ina ɗaga maka ƙafa ne saboda ɓoyayyar alaƙarmu banasan taɓa rayuwarka saboda gaba nima rashinka zai sani a matsala, jini na kai komo yana wucewa ta sassan jijiyoyin cikin jiki, baka kamaci zaka masoyi na gari ba idan aka duba zunzurutun soyayya da matsayinta, ka gaggauta shiga duniya wataƙila ka iya nemarwa kanka mafita amma ba wannan ba, domin mazaunin gida baya taɓa cimma nasara da muradin zuciyarsa. Ita soyyaya a duk inda take bata ɓuya karka kasance me raunatacciyar zuciyar da wata zata nuna mata jajircewa, kayi ta gudu kamar me laluben ƙarshen duniya akan nemo sahihiyar yalwatacciyar soyayyarka. Kada ka manta daraja ɗaya kake ci na ɓoyayyar alaƙarmu da tuni zancen wani ake ba kai ba. Karka ƙara dakatar da ni akan hukuncin da nake zartarwa dai dai da laifin masu aikata shi idan ba haka ba kaima ina iya bi ta kanka." Tana gama faɗa ta kuma yanke jiki ta koma bacci tare ta sauke ajiyar zuciyar kamar wacce tayi tseren gudu, wanda haka ya yi dai-dai da hankaɗe katangar ɗakin da Dokin ya yi ya kutso cikin ɗakin yana ɗaga ƙafafuwa sama tare da ci gaba da haniniya mara daɗin sauraro.


Ga mu a wannan yanayin lamari dai ya ɗauki hazo, Masarautar Adamawa na cikin yanayi, ina fatana kalaman wannan shafin bai rikitar da ku ba🤣🤣


_LITTAFIN ANYA BAIWA CE? NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[02/12/2021, 18:01] Ameera Adam🌚: 39....


Maleek kusan mutuwar tsaye ya yi ban da karkarwa babu abin da jikinsa yake yi, runtse idonsa ya yi ya miƙa wuya ya saddaƙar da sai dai wani ya ƙara numfashi ba shi ba. Dokin bai saurara ba ya buga wata haniniya tare da buga ƙafafuwansa na gaba a ƙasa da ƙarfi, nan take komai da ke cikin ɗakin ya tsalle kamar waɗanda ake yi wa girgizar ƙasa. A cikin abubuwan da suka yi tsalle sama har da Maleek wanda tuni ya sarewa rayuwa, yana gabda faɗowa sama dokin ya cafe shi da bakinsa ya ci gaba da wata irin haniniya. Maleek jikinsa ne ya saki wanda yake nufi da ɗaukewar numfashinsa a take ya sume bai ƙara sanin abin da yake faruwa ba. Dokin na ganin haka ya yi wurgi da shi cen gefe sannan ya juya a haukace ya ci gaba da banke masu ƙararrarun kwana, waɗanda suke da rabon shan wahala kuma suna kwance kamar gawarwarki cikin jini, wasu ko numfashin kirki basa iya yi. A haukaci ya nufi sashen Mai martaba bugu ɗaya ya kaiwa katangar ɗakin ta rushe, sai ga haske rana ta dallare cikin turakarsa wace take a kusan cike ta maɓoye daga ƴaƴansa bayinsa harda dogarawansa da sauran mutanen cikin gida. Suna ganin dokin gabaɗaya jikinsu ya fara tsuma shiru suka yi kamar waɗanda ruwa ya cinye su, masu sakin fitsari na yi masu zawo a wando suna yi. Kafe su ya yi da idanuwa yana zaro harshe kamar zalamamman maye da ke gabda haɗiyar bil'adama, waige-waige ya dinga kamar me neman abu sai kuma ya fara takawa a hankali har gaban su Sarki Abdallah, miƙa kai ya dinga yi yana shinshimasu ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda dokin ya kai kansa sai ya yi kamar zai mutu saboda tashin hankali. Sarki Abdallah tuni ya janyo rawanin har saman fuskarsa ya mayar da shi kamar hijabi. Dokin na zuwa kan wani Dogarin Sarki ya gatsawa kansa haƙora yana fisgoshi, ya fyaɗa shi da bango nan take ya faɗi ko shurawa bai ƙara yi ba, nan take ɗakin ya hautsine da hayaniya ban da ihun yara da manya babu abin da yake tashi a ɗakin, dan gabaɗaya sun saddaƙar da ƙara samun zuƙar iskar duniya. Suna tsaka da ihun ya sake fisgo wata baiwa dake rakuɓe acen gefe har ya ɗaga zai fyaɗa da ƙasa kamar daga sama suka jiyo muryar Maryo tana cewa. "Dakata! Ba mutuwa zai yi ba. A bashi wahala." Tun bata rufe baki ba dokin ya fara tumurmusar baiwar ban da ihu da ƙaraji babu abin da take yi, gabaɗaya hankulan mutanen wurin a tashe yake a lokacin da za a tsaga jikinsu wataƙila ba za a samu jini a jiki ba. Yana gama tumurmusa ta ya ƙarasa wurin Maryo da ke tsaye kyam tana ƙare musu kallo, russunar da kai ya yi a gaban ta cikin girmamawa yana jirana umarninta. Hannu ta sa ta fara shafa kansa tana murmushi sannan ta ɗago da kai ta kalli wurin ayarin mutanen, ta fara takawa a hankali cikin ƙasaita. Tana ƙarasawa ta fara kurɗawa cikin mutanen ban da zare idanu babu abin da suke yi.Hannu biyu ta sa ta riƙo Jakadiyar Sarki Abdallah ta ɗago ta, jikin Jakadiya sai rawa yake kamar mazari haka ta tsayar da ita tana ƙoƙarin faɗuwa saboda ƙafafuwanta sun ga za ɗaukarta. Kallon ta ta yi tana murmushi ta ce, "Alƙawarin da na ɗauka miki na cika miko shi tabbas wannan hukun da na yi musu bai kai azabtarwar da suka yi mana ba, amma ko babu komai sun ɗanɗana kuɗarsu." Ita dai Jakadiya tana tsaye kamar gunki sai raba ido take kamar shege a rabon gado. Hawaye ne ya ɗan zubo mata ta sa gefen hannunta ta goge sannan ta ci gaba da cewa, "Amma har gobe zuciyata ta gagara yafe musu bana tunanin zan iya manta abin da aka aiwatar gare mu." Jakadiya kamar fitar tusa haka ta tsinci bakinta yana faɗin, "Ita yafiya alama ce ta tsarkakkakiyar zuciya. Yafewa macuci ba aibu bane duba da muma muna yiwa Ubangijin da ya hallice mu laifi, kuma idan muka roƙe shi yana yafe mana, ki tausasa zuciyarki laifin wani baya shafar wani." Gyaɗa kai Maryo ta yi ta ce, "Saboda ke zan yi, saboda darajar bakinki amma ina neman yafiyar ki, amma tabbas sai ha hukunta Fulani Halimatu. Ta cutar da baiwar Allah na tsawon shekaru, ta yi tsammanin asirinta ba zai tonu ba wanda hakan ba ƙaramin kuskure bane. Ita ta killace Mai babban ɗaki a kogon bokanta sai ni na ɗauko ta, a shekarun baya kun wayi gari da gawar Mai babban ɗaki wanda sam ba ita bace rufa ido suka yi muku ita da bokanta, kuma billahillazi sai ta girbi abin da ta shuka. Kinsan darajarwa tasa na taimake Mai babban ɗaki?" Jakadiya kasa magana ta yi Maryo ta ci gaba da cewa, "Saboda Maleek ne! Akwai ɓoyayyar alaƙar da ke tsakaninmu. Ba za ku taɓa fahimta ba sai nan gaba. Na taimaka mata ne saboda duk cikin jikokinta ta fi ƙaunarsa, ta bashi kulawar da babu wani jika da ya samu haka." ɗaga kai ta yi ta kalli Sarki Abdallah ta ce, "Ka gaggauta mayar da ita ɗakinta domin Mai babban ɗaki ta fi ƙarfin zama a ɗakin baya, Uwa uwa ce babu na biyunta idan har kana san gamawa da mulkinka lafiya, kuma ka fara hukunta matarka kafin ta aminshi nawa hukuncin." Tana gama faɗa ta kalli Jakadiya cikin tausasa murya ta ce, "Ya Mahaifiyata zaman ki a nan ba dace ba ko za ki biyo ni mu tafi?" Da sauru Jakadiya ta fara girgiza kai ta ce, "A'a zan zauna a nan Allah ya yi miki albarka." Murmushi Maryo ta yi mata ta ce, "Ba zan takura miki ba. Amma idan akwai abin da kike buƙata ki sanar da ni." Jakadiya ta gaɗa kai, Maryo ta juya ta kama dokin ta kamar tsuntsuwa haka ta ɗafe kansa suka fice daga ɗakin.

Idanu ya zuba mata har sai da ta fara tsarguwa ta sunkuyar da idonta ƙada tana murnushi, daga cen nesa Uwar bayi ce tafe tana kallonsu cikin takaici. Ji take kamar ta ƙarasa wurin da suke zaune ta damƙi wuyan yarinyar ta shaƙe kowa ya huta, hannunta na dama ta kalla wanda yake ɗauke da ƙwaryar fura da nono wanda yaji garin magani, amma idan ba a gabanka aka saka ba, ba za ka san da wani magani a ciki ba. Tana ƙarasawa wurinsu ta faɗaɗa fara'arta cikin girmamawa ta yi sallama tana faɗin, "Barkanku da hutawa ranka shi daɗe." Saif ya ɗago idanu ya kalleta yana cewa, "Barka dai Baba." Miƙa masa ƙwaryar furar hanunta ta ta yi ta ce, "Ga fura Bintu ta damo maka ta ce a kawo maka jikin nata ya ƙara warwarewa." Faɗaɗa fara'arsa ya yi yace, "Na gode Babah ita kuma Allah ya ƙara mata lafiya." Mayar da kallon sa ya yi wurin Abuh yace, "Kema za ki sha ko?" Gyaɗa masa kai ta yi sannan ya tura mata ƙwaryar yace, "Ga shi sha ki rage mini." Hankali a tashe Uwar bayi ta karaf ta ce, "Amma ai kai na kawowa." Kallon ta ya yi yace, "Ni da Abuh kusan ɗaya ne." Uwar bayi haɗiye mugun yawu ta yi dan bata so asirinta ya tonu yasa ta ce, "To shi ke nan amma ka tabbatar da ka sha fa." Kallonta ya yi yana nazartar maganar ganin haka yasa ta wayance da cewar, "Na ga idan baka sha ba Bintu ba za ta ji daɗi ba." Gyaɗa mata kai kawai ya yi bai kalleta ba yace, "Uwar bayi a bamu wuri." Sumi sumi ta tashi tana faɗin, "Na barku lafiya." Kallon Abuh ya yi yace, "Ba ni furar nan!" Abuh ta ɗan kwaɓe fuska ta ce, "Sha fa zan yi." Ya ɗan tsuke fuska yace, "Na ce ki bani." Miƙa masa ta yi ta wurga masa tambaya, "Dama Bintu har abinci take aiko maka?" ta tambaya tana kafeshi da idonta. Ɗagowa ya yi da manyan idanuwansa ya kalleta sai kuma ta ji ba za ta iya ci gaba da jurewa kallonsa ba, sunkuyar da kai ta yi ƙasa ta ce, "Amma kawai na yi mamaki ne." murmushi ya yi yace, "To me ya sa kika tambaya? Ko bakya son haka?" Bata san lokacin da ta gyaɗa masa kai ba, ya saki lallausan murmushi yace, "Saboda me?" Ta yi karaf ta ce, "Idan kana so ka bani na dinga yi maka." Kallonta ya yi yana jin wani irin farinciki cikin zuciyarsa yake tunanin, "Shin ko itama ta farajin abin da nake ji a zuciya ta?" kallonta ya yi yace, "Shi ke nan! Kin san Bintu ta yi wani irin ciwo me ban tausayi shi yasa nake tausayin yarinyar, amma yanzu ta warware. Ina tunanin sabon da muka yi yasa lokaci-lokaci take aiko mini da fura." Kallonsa ta yi sai dai a ƙasan zuciyarta bata ji daɗin abin ba. Gabanta ne ya yu mummunan faɗuwa da ta ayyana meye na ta na jin babu daɗi dangane da haka, tunowa ta yi da Maryo sai ta ji tausayin ƴar uwarta ya kamata. Ina ma yadda Saif yake sakar mata fuska haka zai yi wa Maryo. Tafa hannunsa ya yi a saitin fuskarsa yace, "Tunanin me kike yi?" Idonta ne ya kawo ƙwallah ta ce, "Ƴar Uwata Maryo." Tsuke fuska ya yi yana jan guntun tsaki, Abuh ta fara girgiza kai tana faɗin, "Me ya sa baka ƙaunar ƴar uwata alhalin ta fini kyawawan halaye." Fuska ɗaure ya kalle ta yace, "Na ce miki bata da kyawawan halaye ne? Ba na san damuwa fa." Daga haka bai ƙara tanka mata ba ya fara ƙoƙarin ta shi, da sauri ita ma ta miƙe tana faɗin, "Dan Allah ka yi haƙuri." Gyaɗa mata kai ya yi ya wuce kamar za ta yi kuka haka ta bi bayansa kamar jela.

"Maryama lafiya na ga kwana biyu kina ɗari-ɗari da ni ko wani abu yana damun ki ne?" Sarki Aminullah ya faɗa yana ƙare mata kallo dan ba haka ta saba zuwa turakarsa ba ko da babu wani abu da yake haɗa su amma tana nuna masa kulawa. Murmushi ta yi tana kallonsa amma a ƙasa zuciyarta, ji take ƙirjinta na dukan uku-uku. Tattaro jarumta ta yi dukda a lokacin jikinta ya kusa jiƙewa da gumi ta ce, "Babu komai Ranka shi daɗe kaine dai ka ga haka." Sarki Aminullah yace, "Na sai wani sha mini ƙamshi ake ina jin sai na ƙara ƙwarƙwara." Fulani Maryama dukda ta san a yanzu Sarki Aminulla babu amfani da zai ƙara yi wa

Please Login or Register in order to submit comment