Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gabaɗaya."

Ganin da gaske yake ya sa Sarki Aminullah ya aika aka fara shela, ba a ɗauki lokaci ba sai ga jama'a damƙam sun cika faɗa. Sarki Aminullah fargaba ce ta kama shi domin tsohon ya fara ba shi mamaki, Tsohon na riƙe da hannun Salman kamar wani zai ƙwace shi, can gefe suka tsaya kowa ya zo sai ya kalle su.

Bayan mutane sun hallara Sarki Aminullah ya sa aka kira masa tsohon gefen, ya dube shi da kallon nutsuwa yace, "Tabbas na lura kana tafe da muhimmiyar magana amma don Allah mene ne gaskiyar abin da ka faɗa dangane da yaron nan? Tabbas na san wacece Maryama ba za ta taɓa cin amanata ba, duk abin da nake so shi take so ko da bata ƙaunar abu idan ina so tana tayani ƙaunarsa. Amma ka zo mini da maganar da ta girmewa tunanina, don Allah idan har maganar ta shafi iyalina mai zai hana mu yi ta a sirrance." Kamar mutumin arziƙi haka Tsohon ya yi kasaƙe yana sauraron Sarkin Aminullah sannan yace, "Ba zan taɓa yin magana a sirrance ba matsawar akan abin da ya shafi ɗana ne don haka a yau zan fasa ƙwai kowa ya huta." Tsohon na gama maganar ya yi cikin fadar mutane na ganinsa suka fara matsa masa, kamar shine jagoran haka ya yi gaba, Sarki Aminullah na tafe jiki ba ƙwari shima ya shiga. Fulani Maryama tun da gari ya waye take jin ta kamar mara lafiya har kawo lokacin da sanarwa ta isa gare ta na kiran gaggawa da aka yi musu. Matan Sarki Aminullah gabaɗaya sun hallara a fadar, Fulani Maryama jikinta ban da rawa babu abin da yake yi tun da idanunta suka yi tozali da mutumin da ta jima da mantawa da babin rayuwarsa. Tun da ta sunkuyar da kai ƙasa ta kasa koda ɗagowa, Sarki Aminulla ya lura da haka amma saboda yanda ya bata yadda ɗari bisa ɗari ya sa bai kawo komai a ransa ba.

Masarautar Zazzau.

Asubar fari Abu ta ji alamun buɗe ƙofa da sauri ta tashi zaune tana mitseke idanu, hannunsa ɗauke da fitila ya shiga yana haska ɗakin, jikin Abu rawa ya ɗauka sakamakon ganin mutum sanye cikin wata ɓoyayyar shiga, hatta fuskarsa a rufe take, haskata ya yi nan take gabansa ya yi mummunan faɗuwa. Ƙura mata ido ya yi ya ga yanda take ta muzurai, tsawar da ya buga mata ce ta sata sake shiga hankalinta. Cikin wata irin Murya yace, "Ke!" Da sauri Abu ta kalle shi jiki na rawa ta ce, "Na'am Ranka ya daɗe" Tsugunnawa ya yi a gabanta yace, "Muga sarƙar wuyanki!" Jiki na rawa abu ta ɗago sarƙar wuyanta tana nuna masa, ƙarewa sarƙar kallo ya yi yace, "Wacece ke!"

"Sunana Abu!" A tsawace yace, "Ba sunanki ba daga wace masarautar kike." Cikin abu ne ya bada sautin ƙuuuuuuu don har sai ya bayyana a fili, a zuciyarta take ayyana, "Shi kenan tawa ta ƙare me wannan yake nufi." A fili kuma ta ce masa, "Ni ba yar kowacce masarauta bace Hasalima ni marainiya ce iyayena duka sun mu..." Da sauri ya ɗauke ta da mari jikinsa na rawa ya nuna ta da ɗan yatsa yace, "Ki faɗa mini wacece ke ko kuma yanzu na tura ki fadar Mai martaba.

Ganin yanayinsa da abin da ya faɗa ba ƙaramin ɗaga hankalin Abu ya yi ba jiki na rawa ta kwashe labarin abin da ta sani na tarihin rayuwarta da dalilin tahowarta har Allah ya sa, ta zo masarautar Zazzau a matsayin Baiwa." Hannu ya miƙa mata yana faɗin, "Ciro mini sarƙar wuyanki"

A firgice ta ɗago ta ce, "Don Allah kark..."

"Bana buƙatar jin komai daga gare ki." Babu yanda ta iya haka ta ciro sarƙar ta masa, yana karɓa ya juya har zai fita ya juyo yace, "Ki ta shi ki yi sallah a kowanne lokaci Mai martaba zai iya aikowa kiranki domin dole ki amsa tuhume-tuhumen da za a yi miki." Yana gama maganar ya fice daga ɗakin.

Kuncin duniya tare da fargaba ne suka mamaye zuciyar Abu, saboda tashin hankali ji ta yi yawun bakinta na neman ƙafewa, don haka ta nemi kukan ta rasa. Wato kuka ma rahama ne, sai a wannan lokacin Abu ta tabbatar da haka saboda idanunta sun bushe ko ɗigon hawaye babu. Miƙewa ta yi ta tura ƙofar ta fita ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba.

Bayan ta idar ta jima tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita, ta jima tana roƙon Allah a kan ya yafe mata kuskuren da ta yi da wanda ta aikatawa mijinta na fitowa da ta yi ba tare da izininsa ba. Kallon Naufal ta yi ta ji wani irin tausayinsa ya kamata, a fili ta furta, "Kowanne bawa da tashi irin ƙaddarar ni kuma irin tawa kenan, Ya Allah ga yarona nan ka tallafi rayuwarsa kana ganin ƙaddarar da ta fito da ni, wata ƙila ma mutanen nan kasheni za su yi, Naufal ka yafe mini bisa sabuwar rayuwar da za ka fara fuskanta. Na baro ka da Mahaifinka da danginka da gatanka ga shi na kawo mu cikin sabuwar rayuwar da bamu taɓa zata ba." Tana ƙarasa maganar ta fashe da wani irin matsanancin kuka.

Kukan da Abu take yi ne ya tashi Naufal daga bacci ya fara kuka, ɗaukansa ta yi ta rungume tana ci gaba da kuka gwanin ban tausayi. Tana nan zaune Bayin sashen Matan Sarki suka shiga tare da tafiya da ita can sashen da Matan Sarki suke. Sashen Mahaifiyar Yarima aka kaita, tana shiga ta tsugunna a bakin ƙofa, Matar zaune take cikin shiga ta alfarma ta yi kyau sosai ga ta da kwarjini, Abu na ganinta ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, tattaro ƙarfin hali ta yi ta gaishe da matar. Ba yabo babu fallasa ta amsa mata sannan ta ci gaba da jan carbin da take yi. Sai da gari ya waye sosai sannan Sarki ya aiko kiran Abu, wani sabon gumi ne ya shiga karyo mata ta ko ina. Haka ta saɓi Naufal ta fita tana share hawaye.

Masarautar Kano.

Sai da Sarki Aminullah ya yi Addu'a sannan ya gabatar da dalilin da ya tattara su a wuri, tun da Sarki Aminullah ya fara magana Ilahirin jikin Fulani Maryama yake rawa, Jakadiya da ke can gefe da tun shigarta wurin ta tabbatar da Fulani Maryama bata da gaskiya ya sa ta zuba idanu tana kallon yanda wannan lamarin zai kasance, Sarki Aminullah ne ya umarci Tsohon da ya fito ya yi jawabi.

Miƙewa ya yi ɗaya bayan ɗaya ya fara kallonsu sannan ya sauke idanunsa a kan Fulani Maryama ya fara cewa,

"Sanin sunana ba wani muhimmin abu bane da zai gamsar da ku domin ba wannan ne a gabana ba, Ina son jama'ar wudin nan su saurari abin da zan faɗa domin wataƙila zai iya yi muku amfani. Ni tantirin gawurtaccen Boka ne dana gaji tsafi a wurin Mahaifina tun kafin ya mutu, tun ina ƙarami na iya siddabaru don haka na yanke shekarun da yi zai yi matuƙar wahala. Shekarun baya Maryama na kawo mini buƙatunta akan Mijin wato Sarkinku da kuke kallo a yan..." Da sauri wani Bafade yace, "Hattara dai a gaban Sarki kake." Kallon da tsohon ya wurga masa ne ya sashi saurin tsoke bakinsa. Tsohon ya ci gaba da cewa, "Faɗin irin taimakon ban gushiri inbaka mandan da muke yi da Maryama abin ne da ba zai lisaafu ba, duk lokacin da Maryama ta kawon ziyara sai na yi mu'amala da ita domin duk abin da ta kawo mini duk wuyarsa sai na aikata mata shi..." Tun bai rufe baki ba Fulani Maryama ta yi zaraf ta ce, "Allah ya taimake ka wai me wannan mutumin yake faɗa ne, wacce Maryaman yake nufi? An ya ba mahaukaci bane?" Ga duk wanda yake wurin sai ya fahimci tsantsar rashin gaskiya a tattare da Fulani Maryama, Sarki zai yi magana Tsohon ya kalle ta yace, "Tabbas mai hali ba ya sake halinsa, a yanzu ne kika ƙara tabbatar mini da tabbas kina nan yanda na sanki Maryama."

Nan take Fulani Maryama ta hau borin kunya tana zage-zage ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya dakatar da ita ya umarci tsohon da ya ci gaba da magana.

"Tun da nake ban taɓa aure ba har kawo yanzu, Salmanu shi kaɗai ne Ɗana a duniya dana mallaka don haka lokaci ya yi da zan mayar da abuna wurin zamana don na koya masa har tsubbuna kafin mutuwa ta riskeni. Salamanu Ɗana ne kuma babu wanda ya isa ya hanani tafiya da shi."

Ƙananun maganganu ne suke ta shi a wurin, Jakadiya na daga gefe ta zubawa Fulani Maryama idanu zuciyarta fes don ta san babu ko tantama ranar da za a share hawayenta na mutuwar jikarta ɗaya tilo ya zo, da gayya ta sakarwa Fulani Maryama murmushi a fakaice ta mata, "An yanka ta tashi gasassa, Maryama sai a bi wani sarkin ba wannan ba." Sarki Aminullah ne ya yi gyaran murya yace, "Maryama kin ji abin da wannan mutumin yake iƙirari me za ki ce, "Fulani Maryama ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Karya yake ranka shi daɗe idan ina da wani mugun abu ma ai za ka fahimta." Sai suka ji ta fashe da kuka. Jakadiya da ke gefe ta yi zaraf ta ce, "Allah ya taimake ka tabbas abin da tsohon nan ya faɗa gaskiya ne domin na taɓa jin wani bokanta ya gaya mata tun shekaru sama da talatin baya da na yi mata rakiya wurin bokan nata. A gafarce Takawa amma tabbas ni kaina na aikata manyan laifika a gidan nan kuma kaso casa'in da tara duk akan buƙatun Maryama ne, na miƙa wuya Ranka ya daɗe duk hukuncin da ya dace a zartar a kaina, domin babu amfanin ƙin faɗar idan ma ban faɗa ba tabbas Maryama za ta tonani tun da nata asirin da ta jima da binnewa ya tonu." Fadar ce ta hautsine da hataniya kowa da abin da yake furtawa, bayan ɗan lokaci kowa ya yi tsit Sarki Aminullah ya dubi Fulani Maryama yace, "Me za ki ce game da Jakadiya." Da sauri Fulani Maryama ta ce, "Wallahi sai dai idan bakinsu ɗaya." Maryo da ke gefe ta saki murmushi tana kallon wannan diramar ta su.

Jakadiya ta karkata kai tana mamakin ƙarfin hali irin na Fulani Maryama ta ce, "Idan tana musu Ranka shi daɗe a bani bani Fadawa muje ɗakin Maryama na ciro wurin da take zuwa wurin boka da su. Kuma jingar da Saif ya yi tun yana ƙarami ba da ita aka haifeshi ba..." Haka ta zayyane musu duk abin da ya faru tun ranar da suka fara zuwa wurin Marduska da ɗaukan Bayin da yake yi har mutuwar Mahaifin Maryama da askin kansu da aka yi musu. Jakadiya ta yi haka ne don ta kunyata Fulani Marayama a cikin mutane kuma a hukuntata saboda ta san sarai tun da asirinta ya tonu ita ma ba za ta barta ba don haka ta tona musu asiri gabaɗaya ta san ƙarƙari baya wuce hukuncin kisa, kuma ta saj ko ba yanzu ba idan asirinta ya tonu har Sarki Aminullah ya sa ita ta kashe masa Mahaifi hukunta kisa. Lokacin da Jakadiya ta zo a makaganar sai Fulani Maryama ta fashe da kuka ta ce,

"Yanzu Jakadiya Sharrin da za ki yi mini kenan saboda na ce zan tona asirinki ke kika bawa Marigayi Mai martaba guba ya mutu." Jakadiya ta jinjina kai domin ta san za a rina... Ta kalli Fulani Maryama ta ci gaba da tonawa junansu asiri. Nan take Sarki Aminullah ya sa aka tasa ƙeyar Jakadiya har ɗakin Fulani Maryama. Duk wurin da Fulani Maryama take ajiyar kayan tsibbun ziyarar boka Marduska, Jakadiya ta sani ɗaya bayan ɗaya Fadawa suka fara fito da su sannan suka wuce can fada.

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[29/01, 14:11] Ameera Adam🌚: 70...


Masarautar Zazzau.

Tun da ta doshin Fadar gabanta yake faɗuwa amma babu yanda ta iya haka ta kutsa kai cikin fadar, bugun ƙirjinta ne ya tsananta sakamakon tozali da hamkimtaccen Sarki mai cike da kwarijini, mulki, haiba da kamala. Kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da tabbas an ajiye ƙwarya a gurbinta domin shigarsa ta alfarma ba ƙaramin amsar jiki da fuskarsa ta yi ba. Tana shiga duka idanun jama'ar da ke zaune a wurin suka dawo kanta, saboda ku san kowa ya hallara sai tsirarin mutanen da ba su fi mutum biyu zuwa uku ba, sakamakon wannan taron na gaggawa da ya tattara ya shafi iya iyalansa ne kawai.

Abu sai da ta gaishe da Sarki Muhammad Safyan Bn Abdulwahab, sannan ta koma gefe ta yi ƙuri tana satar kallon Yarima da ke gefe ya haɗe girar sama da ta ƙasa. Babban abin da ya ƙara ɗaga hankalin Abu yanda ta ga fuskokin ahalin kowa babu walwala fuskarsa a tamke. Babu wanda ya tanka mata haka ta zaune ba ta yi aune ba sai ji ta yi hawaye na zuba a fuskarta. Tana nan zaune Fulani Maimuna da Fulani Badawiyya suka ƙaraso, Fulani Zannira da Fulani Batula duka a wurin ta same su.

Sarki Muhammad Safyan ne ya yi sallama suka amsa masa gabaɗaya ban da Abu da take cike da zullimi, Sarki ya ci gaba da cewa, "Wani muhimmin labari ya same mu babu zato babu tsammani me ɗauke da sarƙaƙiya." Ya mayar da kallonsa wurin Abu ya ci gaba da jawabi, "An sanar mana daga masarautar da kike, kasancewarki sirika a gidan. Amma tabbas ba iya wannan alaƙar bace akwai wani ɓoyayyan alma'ari. Me ya sa za su aiko ki a zuwan 'yar leƙen asiri? Wace riba Aminullah zai samu bayan mun ajiye makamanmu kowa ya tafi harkar gabansa? Me ya sa zai yi mini haka, me ya sa zai cutar da ni ta hanyar da ban yi zato ba? Me ya sa zai biyo mini ta bayan gida alhalin tuni na riga da na manta da tsohuwar ƙiyayyar da ke tsakaninmu? Me ya sa zai ɗauki fansa akaina ta hanyar baƙantawa ahalina. Me ya sa za ki saka kanki a faɗan da tun kan kafin haihuwarki aka fara shi? Tabbas da kin aikata wani kuskure da kin cuci ƙuruciyarki don babu shakka ba za mu yafe miki ba." Abu shiru ta yi tana jin yanda ɗunbin tambayoyinsa suke ratsa dodon kunnenta, kamar mai gyambo a baki haka ta motsa baki ta russuna ta ce, "Allah ya taimakeka wallahi ban san duk tambayoyin da kake yi mini ba, abin da na sani shi na sanar da ku wallahi babu abin da ya kawo ni gidan nan face dalilin dana gaya muku, Allah ya kawo ni amma wallahi bani da niyyar cutar da kowa." Tun da Abu ta fara Magana Fulani Maimuna ta yi tsai da ranta tana sauraronta domin tana cikin zullumi sakamakon a daren jiya ta aika a kashe Abu amma ɗan aiken babu shi babu alamarsa har Sarki Muhammad Safyan ya haɗa taron gaggawa.

Numfasawa Yarima ya yi yace, "Allah ya taimake ka ina ganin wannan ba maganar da za ta tsaya iya masarautar nan bane, Ina ganin a rubutawa Sarkin Kano wasiƙar neman izinin zuwanmu hakan zai fi domin idan aka ce abin zai tsaya a nan ba za mu samu mafita yanda ya kamata ba. Tabbas Masarautar Kano na da masaniya akan komai domin babu ko tantama akwai wata a ƙasa tun da sun turo wakikiyarsu ta zo a matsayin Baiwa." Cike da gamsuwa Sarki ya amince da maganar Yarima sannan ya ɗora da cewar, "Mun wayi gari da samun wani mummunan labari, amma wannan shi ne muhimmi a gare mu domin wancan mai sauƙi ne. Ban san lokacin da Masarautar nan ta zama haka ba, idan wannan maganar ta fita tabbas abun Allah wadai ne a gare mu ace a masarauta nan an tura wani yaje yin kisan kai. Tabbas zamu hukunta duk wanda yake da hannu acikin wannan lamarin ba za mu laminta ba domin wannan ba ƙaramin ƙalubale bane a gare mu."

Jin haka ba ƙaramin firgita Fulani Maimuna ya yi ba, ita kanta Abu ba ƙaramin tsorata ta yi ba domin ta san ko shakka babu Fulani Maimuna ce ta aikata haka. Tana tsaka da tunani ta ji Sarki yace, "Zamu sa a rubuta wasiƙa zuwa Masarautar Kano idan Allah ya kaimu Juma'a mai zuwa za mu tafi can. A ci gaba da killace ta a maɓoyar sirri bana buƙatar jin wani labari mara daɗi a kanta daga baya.

Masarautar Kano.

Kamar wacce ruwa ya cinye haka Fulani Maryama ta yi kasaƙe kunya gabaɗaya ta dabaibayeta, sunkuyar da kai ƙasa ta yi ta fara rarrafawa wurin Takawa ta ce, "Don Allah ka yafe ni Ranka shi daɗe wallahi sharrin sheɗan ne don Allah..." Da sauri Sarki Aminullah ya katse ta da cewar, "Ya tabbata Salman ba ɗana bane kenan?" Gyaɗa masa kai Fulani Maryama ta yi ta ci gaba da cewa, "Tun lokacin na so sanar da kai sai..." A fusace Sarki Aminullah ya buga mata tsawa yana katse yace, "Bama buƙatar sake jin wata magana daga gare ki, kin cuce mu Maryama. Duk cikin matana babu wacce na bawa yarda ɗari bisa ɗari kamar ke, kin zalince mu domin kin munafurcemu kin kawo Ɗan da ba namu ba. Me muka rage ki da shi a masarautar nan? Me na yi miki da kika nemi halaka Jinina tun yana jariri." Jakadiya na jin haka ta yi farat ta ce, "Allah ya taimake ka, ka godewa wannan yarinyar." Jakadiya ta nuna Maryo da ke gefe ta ci gaba da cewa, "Ai bokan da ta sa ya yi mata aikin shi ya shaida mata baiwar da yarinyar take da ita kamar fa ƴar aljanu yarinyar duk wani siddabaru ta iya..." Sarki Aminullah ne ya dakatar da Jakadiya tuni ta kama kanta don ta lura babu alamun wasa a tattare da shi, wasa-wasa tun ana ganin Jakadiya na abu cikin hankali tana ta tona asirinsu sai abun ya fara zarce hankali domi zance take ta saki babu hankali babu fasali.

Sarki Aminullah na shirin magana kamar saukar ruwan sama sai ganin mutum suka tsidik a gabansu cikin mummunar shiga kamar goggon biri, jikinsa gabaɗaya duk gashi. Ba ƙaramin tsorata suka yi ba don har sai da wasu suka fara ja da baya, Boka Marduska ne ya bayyana da kayan tsafinsa a fusace ya nuna Fulani Maryama yace, "Kin karya sharaɗinmu da ke dama na gaya miki duk ranar da kika fito da kayan tsafinmu a idon jama'a kashinki ya bushe, rufin asirinki shine namu asararriya domin kin tozarta aljanun suke yi miki aiki a idon jama'a dole ne su ɗauki mataki a kanki ke da ƴar korarki waccen la'anniyar, hukuncinki razanarwar fatalwa har ƙarshen rayuwarki." Boka Marduska ya faɗa yana nuna Jakadiya da wani baƙin ganye, Ihu Jakadiya ta zuba ta fara tsalle tana yagar kayan jikinta tana cewa, "Wayyo! Ku taimaka mini zai kashe ni ga shi nan da wuƙa zai yanka ni wayyo!" Ganin haka ya sa Sarki Aminullah ya yi wa wasu Fadawa magana suka kama Jakadiya suka yi gidan Turu (Gidan mahaukata) da ita, Marduska ya koma wurin Fulani Maryama yace, "Ke ma na ki hukuncin zai biyo bayanki domin ba za ki ci bulus ba." Yana shirin ɓacewa Farin tsohon nan ya yi dariya yace, "Ka ɗauka kaima za ka sha a banza ne, idan maye ya manta uwar Ɗa ba za ta manta ba. Ka tuna Boka Ƙurgen tsohon Maigidanka da ka ci amanarsa a shekarun baya? Dama na ci alwashin ba zan taɓa raga maka ba kawai na baka dama ne amma tun da ka kawo kanka ka rage mini aiki." Hankalin Marduska ba ƙaramin tashi ya yi ba, yana shirin guduwa Tsohon ya hura masa wata iska yace, "Ku bishi har can makwancinsa ku hallakashi, amma ku tabbatar da kun azabtar da shi da azaba mai tsanani kafin mutuwarsa."

Tun tsohon bai gama magana ba Marduska ya fasa uwar ƙara har sai da wasu daga cikin mutanen wurin suka toshe kunnuwansu saboda rashin daɗin sautin, nan take ya ɓace daga wurin sannan Tsohon ya mayar da kallonsa wurin Sarki Aminullah yace,

"Ba zama na zo yi ba na zo tafiya da Ɗana ne tun da kuma na bayyana maka kaina da matsayina shi kenan, idan kuma kana buƙatar taimakona zan iya taimaka maka domin ka yi mino halacci ka kula mini da Ɗana yanda ya kamata." Sarki Aminullah ya sauke ajiyar zuciya yace, "Babu inda za ka tafi da shi domin tafiyarka da shi ba alkairi bane, har yanzu ina jin Salman a matsayin Ɗana saboda duk abin da ya faru ba laifinsa bane, don haka ba za ka tafi da shi ka dilmiyar da shi kamar yanda kaima ka dulmiya."Tsohon ya ƙurawa Takawa ido yace, "Ba na son mu yi rabuwar rashin daraja ina ganin girmanka karka bari na cutar da kai..."Tun bai rufe baki ba Sarki Aminullah ya katse shi da cewar,

"Babu mai cutar da wani bawa sai abin da Allah ya nufa, don haka ƙasƙantacce da kai zai iya cutar da ni ba."Nuno Sarki Aminullah ya yi da niyyar cutar da shi kamar ya sani ya yi a'uziya ya fara karatanto masa ayoyin tsari. Duk yanda Tsohon ya so cutar da Sarki ya kasa domin duk wani siddabarunsa ya kasa aiwatarwa, Salman da ke gefe a fusace ya juyo ta sokawa Tsohon ƙaho a wuya nan take Tsohon ya fara fita hayyacinsa. A fusace Sarki Aminullah ya miƙe ya wanke Salman da mari yana cewa, "Kana da hankali kuwa Salman me yake damunka?" Salman ya wurgar da ƙahon gefe yace, "Ranka shi daɗe sauran me ya rage mutumin nan idan mun barshi matsala zai zame mana musamman ni da yake so ƙarfi da yaji ya ɗauke ni, idan na barshi baƙin dajin nan zai mayar da ni." Jikin mutanen wurin ba ƙaramin sanyi ya yi hatta Fulani Maryama sai da ta ji ba daɗi domin duk lalacewar Ubansa bata taɓa tsammanin Salman zai iya kisa ba. Tsoro ne ya kamata domin gani take ita ma kamar zai dawo kanta ya hallaka ta.

Wannan abin da Salman ya yi ne ya sanyaya jikin Sarki Aminullah don haka ya sa aka ɗauke gawar Tsohon ya bada umarnin da a haƙa rami a binneshi ba tare da wanka ko sutura ba, daga ƙarshe ya warware igiyar aurensa da Fulani Maryama, Kuka ta fashe masa da shi tana dana sani da nadama domin wannan ba ƙaramin abin kunya bane a gare ta, rarrafawa ta yi wurin Fulani Zaliha ta dafa ƙafafuwanta tana cewa, "Don Allah Zaliha ki yi masa magana ya mayar dani wallahi zai ji maganarki don Allah ki yafe mini keda Saif wallahi sharrin shaiɗan ne, kuskure ne ba zan ƙara ba." Ba ƙaramin tausayi ta bawa Fulani Zaliha ba domin saki a lokacin da baka tsammace shi ba na da matuƙar zafi, Fulani Zaliha ta dafa Fulani Maryama ta ce, "Ki yi haƙuri Yaya haka Allah ya ƙaddara miki, kuma ni da Saif mun yafe miki amma kin san ba a mayar da mace a saki uku matuƙar ba wani auren ta yi ba." Kamar Mahaukayi haka ta miƙe tsaye ta ce, "Wallahi zan yi indai zai mayar da ni ko waye zan aure shi." Yanda ta ruɗe take ruwan hawaye har sai da ta ɗan karya zuciyar mutane da yawa domin kowa ya san irin soyayyar da

Please Login or Register in order to submit comment