Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda bana so." Maryo na maganar hawaye na zuba.

"Ƙarya kike!" Da sauri Maryo ta ɗago ta kalleta Avu ta ci gaba da cewa,

"Kalmanki sun furta akasin abin da yake zuciyarki, kin manta cece Abu kin san na fi kowa karantarki da halin da kike ciki me ya sa za ki cuci kanki? Babu komai idan kun san wata ba ku san wata ba." Da sauri Maryo ta kalli Abu ta ce, "Me za ki yi?" Kai tsaye Abu ta ce, "Abin da ta dace!"

"Don Allah..." Da sauri Abu ta katse ta, "Mu bar maganar tun da dai ba za ki aure shi ba shi kenan" Jikin Maryo ne ya yi sanyi don ta san Abu sarai ta san akwai abin da ta ƙulla. Kukan da Jaririn yake tsalawa ne ya sa Fulani Zaliha ta yi musu magana, a kunyace Abu ta karɓe shi ta fara bashi Mama. Maryo ta guntse dariyarta suna haɗa ido Abu ta ɗaɗa mata duka ta ce, "Munafuka faɗi abin da yake bakinki!" Maryo ta fashe da dariya don dama a cike take da ita, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce, "Oh! Ni 'Ya su Abu wai kunya ta kike ji." Abu ta basar don ta san halin Maryo sarai idan ta gano lagonka ka shiga uku ta ce, "Kunyar uwar mai sai ka ce wata sirikita ke ni ko Fulani ba na jin kunyarta bare ke." Maryo ta riƙe baki ta ce, "Allah ya shiryeki na san za ki aikata abin fa ya fi haka." Abu daɗi ta ji har ciki ranta yanda ta ga ƴar uwarta ta saki jiki suna wasa da dariya a gefe ɗaya kuma ta ji haushin kanta domin da bata auru Saif ba babu wani abu da zai shiga tsakaninsu yanzu da tuni Ɗan Maryo ne a hannunta.

Suna na zaune suna hira Jaririn ya tsanyare da wani irin matsanancin kuka jikinsa na wani karkarwa, a zabure Maryo ta miƙe tsaye ta karɓi Jaririn ta zuba masa ido sai kawai ta sake shi a ƙasa ya faɗi, bata bi ta kansa ba ta fice daga ɗakin.

Sorry 4 the errors ban yi editing ba

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[13/01, 16:13] Ameera Adam🌚: 62...


Da sauri Fulani Zaliha ta faɗo ɗakin domim kukan da Jaririn yake sam bana lafiya bane, Abu tana tsaye jikinta na karkarwa da sauri Fulani Zaliha ta ɗauke shi tana buga mata tsawa, "Wannan wanne irin sakarci ne kuke yi haka za ku yarda yaro kuna kuna tsaye kina kallonsa me yake damunki ne?" Abu kasa furta komai ta yi sai kawai ta fashe da kuka don yanayin da ta ga 'yar uwarta a ciki ya tabbatar mata da tabbas akwai abin da yake faruwa. Fulani Zaliha ce ta miƙa mata Jaririn a faɗace tana cewa, "Maza kaɓe shi ki ba shi ya sha." Shiru Abu ta yi kamar kurma sai da Fulani Zaliha ta maimata mata maganar sannan Abu ta sunkuyar da kai ƙasa ta amshi Jariri da ya ƙura mata ido ƙir (Waɗanda suka karanta littafina na Jariri ne kaɗai za su fahimci yanayin🤣) har sai da Abu ta tsargu tsoro ya ɗan kamata. Fulani Zaliha ta ce, "Abu wai ko wani abu na daminki ina yi magana kina ji na?" Abu ta sunkuyar da kai ƙasa cikin sanyim murya ta ce, "Ki gafarceni Ranki ya daɗe amma bana jin Maryo ta yi kuskure domin ba za ta yarda shi a banza ba, na tabbata tana da dalilin yin haka. Ina ji a jiki a kwai wani ɓoyayan al'amari a dangen da jariri..." Da sauri Fulani Zaliha ta katse ta a fusace, "Ba na son sakarci kina hauka ne? Karki sake ki furta kalma mara daɗi a kan jikana."

A kan dole Fulani Zaliha ta tursasa Abu ta bawa Jaririn Mama, tana zama rai a ɓace ta fara bashi ya fara sha kawai sai gani ta yi Abu ta fara sanƙame wa idanunta suna niyyar kafewa. Wani babban tashin hankali sai ga jini ya ɓalle mata ya zuba kamar an buɗe famfo. Tuni Fulani Zaliha ta cire Jaririn da yake ta zuƙarta ta ajiye shi a gefe ta fita kururwar neman taimakon mutane. A daidai lokacin Saif ya shiga ya samu Mahaifiyarsa cikin tashin hankali, ba ƙaramin tsorata ya yi da ganin jinin da yake zuba daga jikinta ba. Dunƙule hannunsa ya yi yana ɗan girgiza kansa sai ya ɗora a saman kanta nan take ta sandare numfashi ya yi ƙaura daga gangar jikinta. Wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kansa, sai ya mayar da kallonsa ga Jaririn da yake kwance ya saki wani irin murmushi domin shi lamarin Salman ya fara ba shi dariya. A zuciyarsa yake ayyana, "Tabbas yaƙin ba iya a kan Maryo bane, saboda da a kanta ne ba zai yi mini haka ba. Tun da ya kwana da sanin ba da ni a ka saka mata rana ba. Amma wannan karon shi ne na farko kuma na ƙarshe." A gaggauce ya tashi ya je fita Mahaifiyarsa ta shiga ita da Jakadiya da Unguwar zoma. Bai saurare su ba ya yi gaba har ya kusa fita ya juyo ya ce, "Ammi Maryo ta shigo wurin nan ne?" Fulani Zaliha ta ce, "Eh yanzun nan ta fita."

"Tana ɗakin abin nan ya faruwa?"

"A'a ita ta yarda Jaririn dai a ƙasa sannan ta fice." Fulani Zaliha ta ba shi amsa.

"Kar ku taɓa Abu ba za ta tashi yanzu ba Ammi." Yana gama maganar ya fice a gaggauce. Sororo suka yi suna mamakin furucinsa, Fulani Zaliha ta ce, "Unguwar zoma maza mu je ki duba ta ko wani abin za ki jiƙa mata idan kuma turare ne a samo garwashi." Unguwar zoma ta zurawa Abu ido ba don tana tsoron furta abin da ta gani ba da ta gaya musu gaskiya amma babu yanda ta iya haka ta yi gaba suna biye da ita a baya.

Maryo tana fita babu in da ta tsaya sai fadar Sarki Aminullah ta shiga ko kyakkyawar sallama ba ta yi musu ba, ba ƙaramin mamaki suka yi ba domin ko hijabi babu a jikinta ƙafarta babu takalmi. Tana shiga bata tsaya a ko'ina ba sai ba gaban Sarki Aminullah, a tsaye take ƙerere sai ɗan russunar da kanta ƙasa da ta yi bata furta koda kalma ɗaya ba. Bafadawan da suke fadar suka fara buga mata tsawa, "Gyara dai hattara yarinya a yi biyayya." Kanta na sunkuye ta juyo ta kalle su Goge mai maganu da ke gefe suna haɗa ido gabansa ya faɗi. Mayar da kallon ta ta yi ta sake russunar da kai ƙasa ta ce, "Ka sa mini albarka." Mamaki ya kama Sarki Aminullah sai kuma ya saai murmushi domin lamarim Yarinyar a kodayaushe mamaki yake bata, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu yana mamakin an ya jinnu ba su samu wurin zama a jikinta ba. Domim idan bai manta ba ita ce Baiwar aka tura ta kashe shi, sannan ita ce baiwar da yake a gani tana taimaka masa a mafarkinsa duk lokacin da ya ga Salman na yunƙurin cutar da shi. Kallonta ya yi yanayin ba ƙaramin mamaki ya bata ba ya saki murmushi yana cewa Fadawa, "Ku ƙyale ta"

Mayar da kallonsa ya yi kanta yace, "Me za ki aiwatar da zan saka miki albarka?" Bata ɗago ta kalle shi ba ta ce, "Ka sa mini albarka, zan aiwatar da mihimmin abu amma na tabbata ba zai yi maka daɗi ba."

"Mene ne shi?"

"Ba buƙatar ka sani ka dafa kaina kawai nake buƙata..." A hassale Fadawan suka furta, "Yarinya Hattara..." Wara hannuwa ta yi tana nuna su kamar mai yin daƙuwa (Daƙuwa ta zagi) nan take bakinsu ya ɓame suka kasa furta koda kalma ɗaya sai wani irin yunƙuri suke yi. Sarki Aminullah mamaki ne ya kamashi yake ayyana, "Yaushe tsafi ya samu wurin zama a masarautar nan?" A gaggauce Maryo ta dube shi ta ce, "Lokaci yana ƙure mini ka dafa kaina." Shiru ne ya biyo baya, ganin haka ya sa Maryo ta fisgi hannun Sarki Aminullah ta ɗora a kanta tana runtse ido. Miƙewa ta yi ta fice daga fadar hat bayan fitarta bakin Fadawa nan bai buɗe ba.

Sarki Aminullah ya kalli Goge, Goge ya sunkuyar da kai ƙasa don ya fahimci abin da Takawa yake nufi ya russunar da kai ƙasa yace, "Allah ya taimake ka babu abin da zan iya aiwatar dangane da ciwon Fulani, hasalima ita wannan yarinyar ita take da maganin ciwon nata domin tana da masaniya dangane da lalurar tata. Allah ya baka yawan rai ka riƙe ta hannu bibbiyu domin za ta taimaka maka fiye da yadda kake tsammani..." Sarki Aminullah ya katse da cewar, "Kana nufin ita ta cutar da Fulani? Idan haka ne meye makomar lalurarta me ta yi mata. Wane irin taimako za ta yi mana sannan ta ya za mu gasgata abin da ka furta?" Goje ya russunar da kai ƙasa ya ce, "Waɗannan amsoshin suna tattare da ita, abin da na sani dangane da ita ne kawai na sanar da kai amma idan kana shakku za ta iya tuntuɓarta." Fadawan da suka koɓa bebaye ne suka fara wanin gurnani suna son su yi magana amma harshansu ya naɗe. Sai a lokacin Sarki Aminullah ya fara gasgata abin da Goje ya faɗa domin biri ya yi kama da mutum amma saboda ya ƙara gasgatawa ya dube su yace,

"Abdurrahman me kuke yi haka?" Bafade da aka kira da Abdurrahman ya fara yunƙurin yin magana sai ya kasa kawai sai ya fashe da matsanancin kuka. Wannan lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalin Sarki Aminullah ya yi ba, jim ya yi kawai sai ya sallami kowa tare da sanar da su zai tsayar da lokacin da za a yi zaman gaggawa a cikin fada.

"Ka fara yin galaba a kansu tun da mun fara taɓa matarsa da Ɗan da yake rawar kai an haifa masa. Amma mene ne ya sa dalilin da ya sa kaƙi haƙura da lamarin yaron nan Saif? Ina ce a kan yarinyar cen ne kuma ba shi zai aureta ba. Me ya sa ba za ka uzzurawa mai neman aurenta ba, tun da yanzu auren ma kwanaki ya rage." Farin Tsohon ya watso masa tarin tambayayi kala-kala. Salman ya saki dariyar ƙeta yace, "Ƙiyayyarasa a jinin jikina take ban taɓa jin ɗigon sonsa a zuciyata ba, tun yana nakasasshe har ya san wanene shi. Alwashi na ɗaukarwa kaina sai na ga bayansa tun da ka cw mini idan baan hau Karagar mulki ba zai iya ɗarewa. Wanda zai aure ta akwai dalilin da ya baya gabana domin duk yadda ya kai ƙunarsa na taɓa zuba masa wani haki a ruwan wanka ya bi jikinsa tun wancen tafiyar da ya yi da ita. Koda ya aureta zai gaji don kansa ya sake ta ko ka taɓa jin an yi zaman aure babu mu'amala?

(Wannan ne dalilin da ya sa idan Maleek ya taɓa Maryo jini yake kwanciya a jikinta har jikinsu ya dinga raɗaɗi)

"Lallai Bahaushe ya y gaskiya da yace gado ba karanbani ba. Barewa ta taɓa gudu ɗan da ya yi rarrafe ba. Tabbas ko yanzu mutuwa taa riskine zan yi alfahari da baya na na aiwatar da abin da fara." Dattijon ya yi magana cikin nishaɗi.

Salman bai fahimci maganar tsohon ba ya ci gana da cewa, "Na san zamansu ba zai je ko ina ba shi ya sa ban tashi hankali na a kan haka ba.Na makantar da ita na kuma kurumtar da ita ne sakamakon ta fara ƙoƙarin yanke wata shawara, shi ya sa na dakusar da ita har zuwa lokacin da waccen kwantaccen ya a gano shiri na. Ka san dalilin da ya sa bata iya taɓukawa kanta komai ba?"

"Saboda sharaɗi ne na gindaya mata na halakarwar da zan yi wa Al'ummar ƙasar Adamawa, zan yi musu kisa mai tsananin azaba domin saboda da farko shiga na yi jikin Dokin da yake mara mata baya, na dinga take mutane suna faɗuwa suna mutuwa sai da ta amince mini na fice daga jikinsa. Buƙata ta a nan gaba ta wancan tsohon ne dole ya mutu ya bani Sarautar saboda na gaji da jiran ya mutu don haka zan ƙarasashi." Ya yi maganar cikin ƙunan rai.

"Ba za ka iya kashe shi ba muddin baka kawar da ɗaya daga cikinsu ba domin dukkansu suna ba shi kariya don kowannensu a cikinsu Mahaifinsa ne. Amma ka san wacece za ta taimaka maka dangane da cimma burinka a kanta."

Da sauri Salman ya fara girgiza kai, Wani farin allon ƙarfe tsohon ya watsawa ruwa nan take hoton wata matashiyar mace ya fito raɗau a kan allon. Da mamaki Salman yace, "Ta yaya mai zai sa sai ita bayan ka san ba za ta taɓa bani goyon baya ba." Tsohon ya saki murmushi yace, "Ban san yadda aka yi jinin Maryama ya fi tasiri a jikinka ba, tabbas garaje da gaggawarku bata da maraba da juna. Sai tin kunnensa ya samu ya raɗa masa magana da sauri Salman ya ɗago yana zaro ido yace, "Tabbas a cikin gawurtattun bokaye kai na daban ne." Kyaklyawan tsohon mai mummunar zuciya ya saki murmushi yace, "Ni kaina ina tsoron kaina don ina gudun kar wata rama na yi wa kaina illa"

"A ina zan ganta?" Tambayar da Salman ya jefa masa.

"Tana gabda shiga Masarautarku, amma ina mai jan hankalinka karka bari ta shiga domin shigarta Masarautarku daidai yake da kwaɓewar al'amuranka."

Kamar zai yi kuka Salman yace, "Ta zan san lokacin da za ta shigo?"

"Maryo ce za ta baka tabbacin haka! Wannan aikin ya rage maka amma za ta samu wani sauyi daga yanayi har zuwa magana ta haka za ka gane. Idan kuma an riga da an yi aurenta da Maleek ka je bakin ƙofar fadarku ka ɗaga kanka sama za ka ga bishiyar hagu da ke bakin ƙofar ta bushe. Wannan shi zai baka tabbacin tana gabda shigowa wato tana nan harabar masarautarku. Duk ranar da ta shigo za a wayi gari da samun hargitsi da hayaniya tsakanin Inna Habi da Maryama. Don haka sai ka saka idanu ta shi ka bani wuri." Tsohon ya faɗa yana tattara kayan tsafinsa.

Maryo na fita ta bata tsaya ko ina ba sai sashan Salman in da yake zauna da Matarsa Safiya. Tafiya take kamar za ta tashi sama duk inda ta wuce bayi da Dogarai sai sun bita da kallo, har ta ƙarasa soron gidan. Tsayawa ta yi a daidai kusurwar bango ta runtse idonta tana cewar,

"Bimanatu ku fito gabaɗaya." Tana gama faɗan haka sai ga rukunin jerin 'yan mata sun suna fitowa sahu-sahu suka fito rairas babu adadi. Da hannu ta yi musu nuni da ɗakin Safiyya sai ga shi nan take sun fara tikiɗa zuwa siffar Safiyya kowaccen su na ɗauke da tsohon ciki. Tana gaba suna biye da ita har suka ƙarasa ƙofar ɗakin Safiyya. Da wata irin murya Maryo ta ɗaga labulen ta ce, "Safiyya!" Safiya da ke zaune a kan gado da sauri ta amsa don kiran ba ƙaramin razanata ya yi ba. Ta ɗago kai gabanta ya yi mummunan faɗuwa ganin Mata a tsaye masu fasalinta sak, wani irin ihu ta kwalla nan take ta yanke jiki ta faɗi sumammiya. Ɗaya daga ciki Maryo ta umarta da ta ɗauke ta nan take ta ɗaukota kamar jarirya sai kuma ta ɓace da ita daga wurin. Nuna musu ɗakin Safiyya ta yi suka fara shiga ɗaya bayan ɗaya sannan suka haɗe wuri ɗaya ta nuna musu wurin da Safiyya take a zaune suka zauna sannan ta ɗauki tafin hannunta ta ɗora akan fuskarta sai ta kalle ta kyau ta ce,

"Bimanatu bana son a samu matsala kowacce iri ce saboda tafiyar mai nisa ce don haka ki kiyaye." Cikin girmamawa ta russunar da kai ta ce, "An gama ya shugabata" Daga haka Maryo ta fito daga gidan kamar wacce ake ƙarawa iska haka take tafe da sauri-sauri.


Daulatul Jinnul Shaha...

Zulik na barin Lambun Sarki Kasumul Birmi bai zar ce ko ina ba sai sashen Mahaifinsa, yana zuwa ya zauna yana huci kamar kumurcin maciji. Mahaifinsa Bulbutu ya dube shi yace, "Mai nema baya gaggawa domin shi jinkiri ga mai manufofi tamkar taki ne da ake zubawa tsirrai." Zulik ya kalli Mahaifinsa yace, "Tuni na isar da saƙona yanzu naka aikin ya rage. Da farko na ɗauka soyayyar ƙarya nake mata sai daha baya na tabbatar. Dole ka san abin yo domin na gama haukacewa a kan ƙaunarta komai zai iya faruwa." Hankalin Mahaifinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba domin ya tuna tunatarwa da Bokansa yake yi masa da yake ce masa, muddin ya fara kuskura ya yi masa tsarki da ruwan maganinsa to zai matukar haukacewa a kanta, ta yadda a koyaushe zai rinƙa ƙoƙarin haike mata. Idan har kuwa a ka nemi hanashi ita to babu makawa tura zata kai bango har sai ya haike mata. Shi kuwa ruwan maganin da ya yi masa tsarki da shi da shi ne zai yi wanka duk ranar da Sarki Kisumul Birmi ya mutu.

Kallon Ɗansa ya yi kai tsaye yace, "Me kake so a yi." Zulik ya sake tamke fuska cikin rashin ladabi yace, "Aurenta nake son yi a kwana kusa domin idan aka ja lokaci ba zan iya riƙe kaina ba."

"Ka same ta ka gama. Ka ba ni nan da mako biyu na yi maka alƙawarin idan baka aureta ba ka datse kaina." Da sauri ya kalli Mahaifinsa sai ya tafi da gudu ya rungumeshi yace, "Na ji daɗi ƙwarai da wannan kalaman naka. Amma ka sani muddin wannan lokacin ya wuce baka aura mini ita ba to tabbas zan datse kanka kamar yadda ka buƙata." Bulbutu kansa tsaye yace, "Zan ta ya ka datse kaina da hannuna muddin ban aura maka ita ba."

Rayzuta fusata ta yi bayan fitar Zulik ta fisge hannunta tana cewa, "Ka ga irin abin da nake gudu ko? Ni na san dalilin da ya sa sam bana buƙatar ya kunsanto kusa da ni." Gyara tsayuwa ya yi yana kwaikwaiyar muryarta yace, "Ki manta da shi kin san ya fiye shirme."

"Shirme? Kana tunanin Zulik ya yi haka da wasa ne? Ina tunanin idan baka zama mutum na ɗaya wanda zai bayar fa labarinsa ba, ba za ka zama na biyi ba." Riƙo hannunta ya yi yace, "Na ji amma a bar maganar haka." Bin bayansa ta yi cikin shagwaɓa ta ce, "Kai dai baka son laifin Abokinka." suka fice cikin so da ƙaunar juna. Sai da ya raka ta har sashenta sannan ya wuce sashen Mahaifansa. Tun daga wannan ranar wata irin soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakaninsu, yanda suke zama su yi ta hira a bin zai birge ka saboda soyayya suke mai tsafta. Tun ranar da Rurzaan ya riƙe mata hannu bai ƙara kuskuren haka ba. Sai dai duk wannan abin da yake faruwa Mahaifinta Sarki KIsumul Birmi bai san wainar da suke toyawa ba. Shi dai abin da ya sani Furzaan na zuwa biyawa Rayzuta karatun ƙur'ani bayan haka ya san 'Yarsa ƙawar Furzaan ce kuma sun yo matuƙar shaƙuwa.

(Kun san suma kamar mutane fa suke yadda muke bautawa Allah suma haka suke yi.)

Maryo na tafe suka haɗu da Saif, wuce za ta yi da sauri ya matsa sha gabanta yana haɗa hannuwa biyu alamar godiya yace, "Na gode da taimako Abu da Jaririnta."

"Me ya sa za ka yi mini godiya bayan tun tuni na gaya maka wannan faɗan nawa ne? Kada ka manta Abu 'yar uwata ce abin da ta haifa Ɗana ne don haka ba buƙatar a godewa Uwa don ta kula da Ɗanta." Maryo ta ƙarasa maganar tana yin gaba abinta. Shiru ya yi kamar ruwa ya shanye shi, ya ji daɗin kalamanta don ko babu komai ta danganta Ɗansa da cewar Ɗanta.

Cikin daji-daji da ke cikin Masarautar ta fara kutsawa bata tsaya ko ina ba sai bakin wata ƙatuwar bishiyar tsamiya. Zama ta yi ta sunkuyar da kanta ƙasa a hankali ta sa hannu ta fara ƙwaƙwular ƙasa sannu a hankali waɗansu irin manyan ƙudan zuma sula fara fitowa suna nufar hanyar Masarautar. Haka suka rinƙa fitowa babu adadi suna tafiya tun a hanya suka fara cin karo da Waziri.

(Idan kun tuna akwai wani mutum mai zuwa wurin Fulani Maryama da daddare, wanda take kira da Ɓoyayyar fuska😷 )

Duk ƙudan zuma ɗaya idan ya ciji Waziri wurin fashewa yake jini ya fara tsiyaya. Kafin wani lokaci tuni Zumar da fara karaɗe cikin masarautar, ku san dul wanda ta faɗawa sai dai ya hau kururuwa yana kartar jiki jini ya yi ta fita daga wurin. Maryo na gama haƙar ƙasar wurin ta ɗauko dutse ta ɗora a kan ramin ta ɗebi ƙasar ta mayar ta rufe ramin sannan ta kalli sauran ƙudan zuman ta ce, "Idan ba wannan ramin ba ban lamimce muku mutuwa a kowanne wuri ba." Tana gama maganar ta kishingiɗa nan take bacci ya yi awon gaba da ita.


*Maryo kam an yi taƙadiriyar muguwa*😂🤣

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[15/01, 19:21] Ameera Adam🌚: 63...


Waiwaye...

Lokacin da Mahaifin Zulik ya samu Sarki Kasumul Birmi da maganar auren Rayzuta da Ɗansa Zulik ba ƙaramin mamaki Sarki ya yi ba tare da fadawansa. Amma Sarki bai nunawa Bulbutu ba sai yace zai tuntuɓi Rayzuta domin ya ji ta bakinta. Bayan Fada ta tashi Sarki ya samu Rayzuta ya gaya mata, ranta ba ƙaramin ɓaci ya yi ba a nan take ta sanar masa da bata son Zulik, kuma a wannan lokacin ta gaya masa wane ne zaɓinta. Sarki ba ƙaramin daɗi ya ji ba domin hankali da nutsuwar Furzaan ba ƙarmin burgeshi yake ba. Daɗin-daɗawa zumincinsa da Mahaifin Furzaan zai ƙara ƙarfi. Washegari Sarki Kisumul Birmi ya aika aka kira masa Bulbutu bayan ya gaida shi Sarki ya sanar masa da saƙon 'Yarsa. Bulbutu bai wani damu domin dama ya san da haka za ta faru saboda ko makaho ya shafa zamantakewar Rayzuta da Zulik ya san babu kyakkyawar alaƙa bare kuma soyayya ta shiga a tsakaninsa. Ya faɗawa Sarki Kisumul Birmi ne saboda wannan ya zame masa hujjar da zai kafa idan ya je yi wa Maƙiyan Sarki Kisumul Birmi mubaya'a.

Daga cikin fadar bai zame ko'ina ba sai fadar Sarki Buzaag, Duk Fadar Sarki Kisumul Birmi kowa ya san irin tsananin ƙiyayyar da ke tsakanin Sarki Buzaag da Sarki Kisumul Birmi. Daɗaɗɗiyar ƙiyayya ce ta sahon shekaru, Sarki Buzaag mutum ne azzalumi mai tsananin son kansa tare da burin mallakar yankuna mabambamta. Wannan buri na shi, ya sa ya rinƙa farmakar ƙananan dauloli babu yanda suka iya haka suka rinƙa yi masa mubaya'a. A wannan lokacin ya kaiwa Sarki Ƙisumul birmi ta yi amma ƙarfin mulki ta tsananin jarumtar Masarautar da Jaruman cikinta ya sa suka gagari Sarki Buzaag. Wannan ya sa babu wata kyakkyawar alaƙa a tsakaninsu, kowanne ɓangare yana ƙullace da juna. Bulbuta na zuwa a ka sanarawa da Sarki Buzaag zuwansa, da farko wasu daga cikin Dakarun Sarki Buzaag sun so tasar masa sai wani Badakare ya dakatar da shi domin ya tabbatar ba zai yi zuwan banza ba. Bulbutu na zuwa ya sanarwa da Sarki Buzaag dalilin zuwansa

Please Login or Register in order to submit comment