Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dai babu yadda za a yi Namiji kamarsa ya shigo mini ɗaki." A hankali Maryo ta fara jan kafarta ba tare ta lura da inda take jefa ta ba ta fita, da sauri Saif ya sha gabanta yana faɗin, "Don Allah ki tsaya ki ji yadda lamarin ya kasance wallahi..." Hannu ta ɗaga masa tana dubansa da rinannun idanunta ta sai kuma ta saki murmushin yaƙe da ya fi kuka ciwo ta ce, "Ba sai ka ce mini komai ba, don Allah ka bani hanya na wuce saboda ina yi maka kallon Yayana ba zan iya yi maka ranshin kunya ba kamar yadda bana taɓa yi wa Adda Abu." Tana kaiwa nan ta fice daga ɗakin tana tafe wani abu na dunƙule a zuciyarta hatta ƙafarta bata san inda take jefa ta ba.


Yau na san Abu ta shiga uku🥺🥺


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[07/01, 19:39] Ameera Adam🌚: 58...


Lokacin da ta koma Inna Habi bacci take hankali kwance bata tashi ba, Maryo na shiga ta zube a ƙasa tana sakin kuka me tsuma zuciya. Sama-sama Inna Habi ta fara jiyo kukan Maryo a firgice ta tashi tana tambayarta abin da yake faruwa, Maryo ban da kuka babu abin da take yi hatta magana ta kasa iya furtawa. Inna Habi jikinta na rawa ta miƙe ta fita daga ɗakin tana dube-dube sai dai tsakar gidan shiru ma yake babu Bayin da ta bari suna aiki kafin ta kwanta bacci. Komawa ta yi ta zauna ta zubawa Maryo idanu don bata san me za ta yi ba, tun da ta yi mata tambayar duniya amma amsa ɗaya ce kukan da take rusawa. Sai da ta ci kuka ta gode Allah fuskarta jawur sannan Inna Habi ta sake tambayarta tana ƙasa da murya kamar me raɗa, "Maryo me aka yi miki? Ko yaron nan Ɗan wurin Maryama ne ya yi miki wani abu?" Maryo girgiza mata kai ta yi ta ce, "A'a ba shi bane." Kanta ne ya ci gaba da sara mata saboda tsananin ciwon kai ko idanunta bata iya ɗagawa, a hankali jini ya fara ɗiga daga hancinta tana shirin gogewa Inna Habi ta ruƙota cikin tashin hankali tana faɗin, "Me aka yi miki Maryo haka da har yake neman tayar miki da ciwonki?" Sai a lokacin Maryo ta iya faɗawa jikin Inna Habi ta fashe da wani irin kuka me tsuma zuciya. Inna Habi jin kukan Maryo take har cikin ranta tana ayyana wannan karan ta kai maƙurar tiƙiwa, ba Salman ba ko Fulani Maryama ce ba za ta iya ci gaba da ɗauka ba.

Bayan fitar Maryo a hassale Saif ya ƙarasa wurin Abu ya fisgota da iya ƙarfinsa, gani ya yi ta kafe shi da idanu sai kuma ta bushe da wata irin dariya. Sunkuyar da kai ƙasa ya yi saboda baƙin ciki ya rasa wanne irin hukunci zai yi mata. Be ƙarasa tunanin da yake yi ba ya riski muryar da bata zame masa baƙuwa ba a cikin dodon kunnensa ana faɗin, "Wannan shi ne karonmu na farko da kai a taƙaice za mu iya kiran wannan da wasa farin girki." Yana gama maganar Abu ta sulale ta faɗi ta rubda ciki. A zabure Saif ya yi kanta yana kiransa sunanta, daga saman kansa ya sake jin bushewa da dariya yana ana faɗin, "Wannan karon za ka tashi biyu babu." Be saurara masa ba ya fara jijjiga Abu da lokacin tuni jini ya fara zuba daga jikinta. Ganin wannan ba zai kai shi ba ya sa shi fita da sauri gudu-gudu, kai tsaye ya wuce sashen Mahaifiyarsa. Da gudu ya faɗa ɗakinsa yana ƙwala mata kira, kai da ka ji irin kiran da yake yi mata za ka tabbatar ba na lafiya bane, kamar yadda sauran Bayi suka riski shigowarsa cikin tashin hankali." Hankali tashe Fulani Zaliha ta tare shi tana tambayarsa, ban da haki babu abin da yake saukewa yana faɗin, "Abu ce ta faɗi har ta fara zubar da jini." Ba ƙaramin tashin hankali Fulani Zaliha ta shiga ba da sauri ta aika aka kira mata Uwar Bayi da Uwar tuwo. Lokacin da suka ƙarasa gidan Abu ta fara fita daga hayyacinta, Saif sai kaiwa da kawowa yake yi yana nazarin irin hukuncin da ya dace ya ɗauka akan Salman. Kafin wani lokacin tuni unguwar zoman da aka kira ta ƙarasa ta fara duba Abu sannan ta jiƙa magani da turare aka bata na sha da shafawa sannan ka turara turare. Jikinsa ne ya bashi akwai abin da yake faruwa a ɗaki wurin da Abu take kwance yana shiga akin Uwar Bayi ta miƙe zumbur tana faɗin, "Ranka shi daɗe wannan ciwon mata ne ka fita duk abin da ya dace za mu yi..." Tun bata rufe baki ba ya ɗaga hannu ya maka mata a fuska Unguwar zoma na ganin haka jikinta ya fara karkarwa tun bata gama haɗa kayan magungunanta ta ɗauki jakarta ta fice daga ɗakin.

Shaƙar wuyanta Saif ya yi da ƙarfin tsiya yana huci kamanninsa sun fara canja launi idanunsa sun fito sun yi jawur gashin jikinsa ya miƙe yana huci yace, "Ka kasar mini matata ko na illata ka, wallahi daga ita har abin cikinta idan ya samu matsala sai na kassara rayuwarka." Salman dake ɗauke da siffar Uwar bayi ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yace, "Na yi tsammanin kanka baya ja ashe yana ɗaukan al'amura. Na gaya maka wallahi ba za ka iya ja da ni ba, sai na kashe ka da ranka kana kallo. A tashin farko ka ga na rabaka da Masoyiyarka na tabbata babu yadda za a yi ta ci gaba da ƙaunarka bayan tana muku kallon maciya amana kai da matarka. Sannan ka kwantar da hankalinka ba zan halaka matarka ba domin idan na halaka ta zan baku damar da za ku iya ɗinkewa har maganar aure ta shiga tsakani. Sai kuma abin cikinta bana tsammanin za ku same shi a yadda kuke da buƙata. Zan iya baka zaɓi idan ita ka zaɓa ko Mahaifiyarka, Mahaifinka, Matarka da abin da yake cikinta fansarta ne duk zan hallaka ku ɗaya bayan ɗaya. Idan kuma ka bar mini da ita za ka ci gaba da rayuwa da waɗannan mutanen dana lissafa maka. Dabara ta ragewa me shiga rijiya." Saif na jin haka sai kawai ya bushe da wata irin dariya yace, "Ai ban san irin wannan wasan kake so mu yi ba, amma tun da ka bani dama zan baka mamaki. Indan haka ne kaje nina san ta wurin da zan ɓullo maka. Amma ka rubuta ka ajiye na rantse da girman Allah duk abin da ya shafi waɗannan mutanen zan baka mamaki." Yana gama faɗa ya fyaɗa Saif da ke cikin siffar Uwar bayi da ƙasa ya sa ƙafa ya murje wuyansa har sai da ya buga wata uwar ƙara da ƙarfi sannan ya tashi da gudu ya fice daga ɗakin.

A sace Bulbutu ya kai Zulik horon harbi ba tare da kowa ya sani ba, sai dai duk wanda ya tambaye shi yace ya kai shi dangin Mahaifiyarsa ziyara, sakamakon lokacin da cikin cikin Mahaifiyarsa ya fara bayyana ya sace ta kaita tsohon kogon Mirzu ya ɓoye ta a cen har ta haihu. Baƙin cikin ganin Ɗanta kuma Jikanta ya sa ta kwashe musu albarka daga Zulik har Bulbutu a take a wurin ta haɗiyi zuciya ta mutu. Lokacin da ya shiga masarautar da Zuliki yana jariri kowa bin sa ya dinga yi da kallo, kowa na san sanin wane yarona a hannunsa amma suna gundun irin fassarar da za a yi mishi. Ganin suna bin sa da kallon tuhuma ya sa ya ɗauki Zulik ya wuce Fadar Kamusul Birmi, yana zuwa ya zube ya yi gaisuwa sannan ya fashe da kuka. Babu wanda ya tanka masa sai da ya sha kuka me isar sa sannan Sarki ya dube da kulawa saboda a iya saninsa Bulbutu gawurtaccen sadaukin namiji ne, kamar ya san me yake zuciyar Sarki sai ya ɗago Zulik ya nuna masa ya sake fashewa da kuka. Fadawa tsawa suka buga masa sakamakon a gaban Sarki Kasumul Birmi ba kowanne sakarci ake iya yi ba. Hannu Sarki ya ɗaga musu jiki a sanyeye kamar kazar da aka jefa da kishiri yace, "Ku ƙyale shi! Ku amso mini yaron ku kawo shi." Tun be rufe baki ba suka cika umarninsa, wannan karan ma sai da ya jima yana kuka sannan ya ɗago ya fara wassafo karya kamar ba shi ya sha kuka ba.

"Sarki me cikakken iko me maɗaukakiyar izza da babu irinta duk faɗin nahiyar nan, me ɗauke da tausayin talakawansa. A wannan karan na yi kuskure me girma ban san ta wacce siga za ka hukunta ni ba." Jin wannan bayanin nasa ya sa suka tattara hankulansu wuri ɗaya suna sauraronsa, ya goge hawaye ya ci gaba da cewa, "Na yi aure tun shekaru biyar da suka gabata a cen Daular Bahi da ke ƙarƙashin Jinnul Nariy, yarinyar da na aura ashe bata da lafiya basu sanar da ni ba har aka yi auren. Lokacin da na yi niyyar tahowa da Matata sai ciwonta ya tashi, haka na barwa zuciyata lamarin kuma na bar Matata a cen suna jinyarta, sai dai lokaci-lokaci ina ziyartarta amma ko kaɗan bata san wanda yake kanta ba. Ana haka bayan shekara uku da aurenmu sai ta sami lafiya ta dawo cikin hankalinta. Amma fa a nan take iyayenta suka ƙi amincewa da na taho da ifa sai dai kawai muka ci gaba da mu'amalar aure. Katsam sai ta samu ciki a ranar da ta haihu a ranar ciwonta ya tashi, nan take ta faɗi ta mutu." Bulbutu na zuwa nan a zancensa ya rushe da kuka, Bafadawa ne suka fara bashi baki yana gyaɗa kai, nan take ran Sarki Kisumul Birmi ya ɓaci ya dubi Bulbutu da kausashiyar murya yace, "A wane yanki wannan nahiyar take na aika fadawa a ɗebo iyayenta domin hukunta su, ba su barka ka ji da mutuwar matarka ba za su baka yaro ƙarami ka taho da shi." Cikin Bulbutu ne ya kaɗa yana ganin saura ƙiris asirinsa ya tonu don haka ya sake marairaice murya yace, "Sarki me adalci ba haka lamarin yake ba, kasancewar Kakar yarinyar ta taɓa bani labari cewar ita ma ta samu wannan ciwon ne sakamakon tana jaririya, shi ya sa na tsorata na ce su ba ni shi na kaiwa me ɗakina za ta ba shi kulawa. Da farko sun so hanani sai daga baya na yi musu jan ido sannan suka amince, mun yi magana da su akan duk bayan wani lokaci zan dinga kai shi wurinsu ina dawo da shi." Ajiyar zuciya Sarki ya sauke sannan ya tausasheshi da kalamai masu daɗi, da farko Sarki ya so yace ya bar masa yaron a wurinsa amma gudun shiga haƙƙi ya sa ya miƙa masa Zulik yana tambayarsa, "Bulbutu ka yi masa suna ne?" Bulbutu ya ci alwashin saka masa sunan da Bokansa ya sanar da shi ya san idan yace be yi ba wataƙila Sarki ya raɗa masa, don haka yace, "Kafin Mahaifiyarsa ta rasu ta bar wasiyyar a raɗa masa suna Zulik." Sarki Kisumul Birmi ya ɗan yatsina fuska don sunan sam ba na masu kyawawan ɗabi'a bane, sunan wani Shuɗaɗɗen aljani ne da Kakanin kakaninsu suke basu labarin zalincinsa, amma gudun kar ya yi shisshiga kuma ya ji ance wasiyya ce shi ya sa ya sa masa albarka.

Tun daga ranar riƙon Zulik ya koma wurin uwar gidansa, da farko ta so bijire masa amma sanin halin mijin nata ya sa babu yadda ta iya ta amshe shi ta riƙe ba don ta so ba, sai don gudun kar ya ɓatar da ita.

Zulik ya shafe kwana da kwanaki sannan ya dawo, Mahaifinsa ba ƙaramin daɗin ganinsa ya yi ba. Idan Zulik ya riƙe kwari da baka ya yi harbi Tsintsuwa duk nisan ta sai kibiyar da huda jikinta ta faɗo, sannu a hankali Zulik ya fara gwada basirarsa a cikin Bayi. Kafin kace wani abu tuni zance ya yaɗu a ko ina a cikin masarautar. Furzaan ba ƙaramim daɗi ya ji ba kasancewar Babban amininsa ya ƙware a fannin da babu Aljani ɗaya daya iya.

Ban da ajiyar zuciya babu abin da Maryo take yi, a zuciyarta take ayyana me za ta iya gayawa Inna Habi bayan ta san Abu Ƴarta ce halak malak. Shin za ta ce mata ta je gidan Abu ta ga Saif ne mijinta ko kume. Inna Habi gabaɗaya jikinta ya yi sanyi kamar kazar da aka jefa da gishiri, bata yi aune ba ta ji Maryo na faɗin, "Me ya sa za ki yi mini haka?" Da sauri Inna Habi ta ce, "Maryo wace ce gaya mini me ta yi miki." Kallon Inna Habi ta yi cikin tausayawa don bata taɓa tsammanin zancen zucinta ya fito fili ba, ta hau girgiza kai sannan ta ce, "Inna wani Mafarki na yi da wata mata." Da mamaki Inna Habi ta furta, "Mafarki kuma Maryo?" Maryo ta gyaɗa mata kai, Inna Habi ta yi mata kallon tsaf tana nazartarta yanayin da take ciki. Girgiza kai ta yi cikin wata irin dakakkiyar murya ta fara cewa, "Maryo ni ce Mahaifiyarku kina da wacce za ki gayawa damuwarki bayan ni, tun kuna ƙanana na san halin kowa Maryo yaushe kika fara ɓoye mini damuwarki?" Maryo hawaye ne ya ci gaba da ziraro mata ta ƙara kwanciya a jikin Inna Habi ta ce, "Inna don Allah ki yi haƙuri amma babu wani abu da yake damuna." Inna Habi ta gyaɗa kai tana faɗin, "Shi ke nan duk lokacin da kika so sanar da ni za ki yi mini bayani amma ki sani ba zan lamunci ganinki cikin damuwa ba." Maryo ta ce, "Shi ke nan Inna ba za ki sake gani ba Insha Allah." Inna Habi ta ce, "Ta shi kije ki wanke fuskarki bana son ganin wannan haɓon na zuba." Maryo ta tashi ta fice daga ɗakin cikin damuwa.

"Ya kai wannan Boka me karamci yanzu babu wani taimako da za ka iya tallafa mini da shi akan wannan Hallitar, na zautu ta yadda bana iya kallon kowacce mace a matsayi kyakkyawar hallita. Tun muna samun matsala da Matata har ta haƙura ta zuba mini ido, ka yi wani abu akai idan kuwa ka ce ba zan iya mallakarta ba na yi rantsuwa da girman Allah sai na kasheta sai dai kowa ya rasa. Na gwammaci na aiwatar da abin da ya faru a shekarun da suka shuɗe, domin muddin ban cika muradina ba, ba zan taɓa bari Saif ya mallake ta ba." Mutumin Tsoho ne tukuf me ɗauke da farin gashi a sassan jikinsa, kallo ɗaya za ka yi wa fuskarsa ka tabbatar da rashin tsoron Allah ya samu mutsuguni a kan fuskarsa. Kyakkyawan ne ajin farko ga duk wanda ya yi masa kallon kitse... dole zai ɗauka mutumin arziƙi ne. Murmushi ya yi yana kallon Salman da yake cikin damuwa yace, "Na gaya maka muddin tana cikin hankalinta babu yadda za a yi ta amincewa aurenka. Kiyayyarka daga jinin jikinta take ba za ka taɓa samun gurbi a zuciyarta ba, sai dai akwai mafita!" Da sauri Salman yace, "Gaya mini wacce iri ce duk girma da hatsarinta zan bi domin ganin na mallake ta. Na yi rantsuwa da girman Allah ba don bani da ikon sace ta da ƙarfin tsiya ba da babu yadda za a yi na zuba mata ido ina wahalar da kai." Murtuke fuska tsohon ya yi yace, "Karka ƙara ambatar sunan Allah a wurin nan domin nan wurin zaman ɓatattu ne, kamar yadda na baka wancen laƙanin ka binne masa haka wannan karon zan baka wani laƙanin amma wannan ya fi wancen hatsari. Amma zan ƙara tunasar da kai gabaɗaya ku ukun nan Filsifi ne, tasirin sihiri baya wanzuwa a jikinku har sai da haɗin kan ɗaya daga cikin jinsinku. Ina mu'amala da ɗaya daga cikin Bafaden Mahafin yarinyar nan don haka akwai wani taimako da zai yi mini wanda babu wani Bil'adam da zai iya aiwatar da shi." Salman ya kwantar da murya yana faɗin, "Tuba nake Bokan bokayen duniya, ina sauraron duk abin da kake faɗa kuma ko ta halin ƙaƙa zan aiwatar da abin da za ka umarceni."

Wani tafasasshen jini ya ɗauko a cikin wata ƙwarya ya ɗaga sama sai da ya yi surutan tsafinsa sannan ya juya ya kalli Salman yace, "Me kake gani?" Salman ya zura kai yana kallon jinin nan take ya ji kansa ya sara har sai da ya sa hannu biyu ya dafe kansa sannan ya ɗago da kai idanunsa sun yi jawur yace, "Jini ne sai dai na kasa tantance ko na mene ne." Murmushi tsohon ya sake yi yana janye kwaryar ya mayar da ita gefe sai a lokacin kan Salman ya rage sara masa, Tsohon ya dube shi da kyau sannan ya ci gaba da cewa, "Ina taimaka maka ne kawai saboda akwai wani ɓoyayyen al'amari a tsakanimu, na san kai baka sani ba amma wataƙila nan gaba za ka fahimta. Wannan wani sirrinmu ne ni da mahaifiyarka da muka binne na tsahon shekaru, amma nan bada jimawa ba akwai lokacin da Ya za ta ɗakin Ƙanwa." Da mamaki Salman yace, "Mahaifiyata kuma? Kana nufin Mahaifiya ta san ka ko ta taɓa ziyartar ka?" Al'adar tsohon kenan koyaushe cikin murmushi yake sai dai baƙin halin da ke ƙunshe a zuciyarsa ya wuce abin a kwatanta. Murmushi ya kuma yi yace, "Mu ajiye wannan batun a gefe ka bari ka cimma burinka tukunna sai ka zo na yi maka cikakken bayani. Da farko dai laƙanin da zan haɗa maka magani da shi yana tare da kai wato da magani a gonar yaro..." Salman jikinsa har rawa yake ya miƙe tsaye yana faɗin, "Gaya mini ko mene ne na aiwatar maka da shi idan wanda zan ɗauko maka ne yanzu na kawo maka shi."

Farin Tsohon ya saki dariya me sauti sannan yace, "Tabbas ko makaho ya shafa ka sai ya tabbatar da Barewa ba za ta yi gudu Ɗanta ya yi rarrafe ba, ko a ina jinin Maryama yake sai ya bayyanar alaƙarsu tabbas jini ba wasa ba na ƙara tabbatarwa da kai Jinin Maryama ne. Amma kuma duk gaggawar Ango ya bari a kai Amarya ɗaki, haka zalika duk gaggawar Unguwar zoma ta bari a haihu. Saurin me kake yi Salmanu." A hankali Salman ya koma ya zauna sannan tsohon ya ci gaba da cewa, "Matarka tana da Ɗauke da cikin Ƴa mace. Daidai lokacin da cikinta ya cika wata Bakwai nake son Jaririyar zan yi amfani da jininta, ita kuma uwar da jinin Biƙinta zan haɗa dole ita ma Maryo ka samo mini jinin jikinta kowanne iri ne. Idan ka kawo mini waɗannan zan haɗe su wuri ɗaya na zuba a cikin wancen ƙwaryar. Jinin ƙwaryar can da kake gani jininku ne na shuɗaɗɗun shekaru lokacin da aka yi ambaliyar Jini a daularku, shi ya sa kanka ya sara lokacin sa nuna maka, haɗakar Jananenku ne ku ukun. idan ka kawo mini zan haɗe su a cikin wannan shi ke nan burinka ya cika har abada Maryo ba za ta taɓa dawowa hayyacinta ba, amma da sharaɗi dole ka haɗo da jinin Saif daidai da ƙwayar zarra domin shi ɗin kamar inuwarta ne dole sai an haɗa jininsa idan ba haka ba ya dinga farmakarka kenan. Ni kuma a koyaushe na fi son ka kasance Me nasara."

Farin ciki ƙarara ne ya bayyana a fuskar Salman lokaci ɗaya kuma damuwa ta sauka a fuskarta ya dubi Dattijon cikin damuwa yace, "Amma akwai ƴar damuwa!" Dattijon ya ɓata fuska kamar wanda aka isarwa da saƙon mutuwa yace, "Bana son ka dinga jin shakku a ranka domin abokin karawarka ya fi ka ƙwarin gwiwa, dukda ka fi shi kafar samun nasara be taɓa jin gazawa ko karaya a zuciyarsa ba." Salman ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Ba ina karaya bane sai dai duk ta sigar dana bijiro masa sai ya gane ni. Na bi ta siffar jikin Matarsa ya gano ni. Na yi siffar Unguwar zoma shima ban yi nasara ba. Idan zan ɗebi jinin jikinsu ta wacce sigar zan bi?" Tsohon ya ɗebi gasasshiyar wata hallita me ban tsoro ya watsa a baki yana tauna sannan ya fara magana, "Ka ci gaba da jarrabawa idan baka yi nasara yau ba za ka yi gobe. Sai dai ka ajiye a ranka shima ba zai taɓa zama haka ba. Karka manta cikin matarka watansa Shiga Ita kuwa Matarsa cikinta ya tafi wata tara. Ka yi ƙoƙarin ganin ka kula da Matarka ta yadda ba za a samu matsala da cikin jikinta ba, domin dole sai da jininka dana abin da za a haifa maka za mu yi aiki da shi. Bana buƙatar jin tambaya ko neman ƙarin bayani na gama magana ka ta shi ka wuce." Salman babu yadda ya iya haka ya miƙe a sanyaye kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki ya fice daga kogon dutsen.

Bayan ficewar Salman daga ɗakin Abu kamar zautacce haka Saif ya ɗauki Abu da bata san abin da yake faruwa ba. Kamar matacciya haka kanta, ƙafafuwanta da hannuwansa suke raito, gudu-gudu sauri-sauri haka ya fice da ita daga ɗakin ya wuce sashen Mahaifiyarsa da ita hankali a tashe. Fulani Zaliha ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba ganin halin da Abu take ciki, har lokacin jinin jikinta be daina zuba ba. Hankali a tashe ta aika aka sanarwa da Takawa halin da Abu take ciki. Ba shiri ya bayar da Umarnin akai Abu Asubiti don ceto rayuwarta. Dole ƙanwar naƙi. Don dole aka sanarwa da Inna Habi halin da Abu take ciki, daga ita har Maryo tashin hankali ne ya bayyana ƙarara a fuskarsu, ba a ɗauki lokaci ba aka wuce da ita Asibiti rai a hannun Allah. Maryo da Inna Habi sai Uwar Bayi ne suka tafi asibitin sai sai wasu Dogarawa biyu da Sarki Aminullah ya umarce su da tafiya asibitin.

"Maigida yau kuma ni kake yi wa barka da gida?" Murmushi ya yi yace, "To meye don na miki sannu da ɗinma da bana yi kuskure ne yanzu kuwa na gyara kuskure na." Ba ƙaramin daɗi Safiyya ta ji ba don a duniya tana son ta ga mijinta na bata kulawa musamman da Allah jarrabeta da mutuwar ƙaunar Salman, wani lokacin idan ya yi mata wulaƙanci har zama take ta ci kukanta ta godewa Allah, don haka take jin ta cikin farinciki da annushuwa. Salf da ke ɗauke da siffar Salman ya ƙurawa cikin jikinta ido lokaci ɗaya kuma sai ya ji tausayin Safiyya ya kama shi, don yadda ya ga tana ta murna da sannun da ya yi mata ya fahimci bata jin daɗin zama da Saif ko kaɗan. Tunanin irin halin da za ta shiga ya yake yi musamman da ya tuno da halin da Matarsa take ciki. Jikinsa ne ya yi sanyi ta dube shi tana cewa, "Maigida lafiya na ga kayi shiru." Murmushi ya saki yana cewa, "Mantuwa na yi a waje amma karki damu zan fita an jima." Safiyya ta saki murmushi tana faɗin, "Au ho ni kam na yi mamaki na ga tunanin ya yi yawa. Wai yau wani abu ne ya same ka na lura kana cikin farinciki." Ido ya sake zuba mata saboda ya san waye Saif zai iya azabtar da ita saboda soyayyar da yake wa Maryo, wannan karonma tausayi ta bashi don yana gabda shafar cikin jikinta amma jikinsa ne ya yi sanyi ya kasa aiwatar da abin da ya yi niyyar yi. Be kalleta ba ya juya ya fice yana cewa, "Ina zuwa."

Yana fita ya koma siffarsa ta

Please Login or Register in order to submit comment