Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ƙarfi ya shiga hura mata iska a bakin tun tana cikin hayyacinta har ta fita daga hayyacinta idanunta suka fara lumshewa. Sannan ya ɗauke bakinsa daga nata, kamar saukar ruwan sama haka ta fara kwara wani irin baƙin amai kamar za ta amayar da hanjin cikinta. Da sauri Maryo ta ƙaraso ta riƙe ta a ɗan fusace ta ce, "Me kake yi haka ne Saif?" Ido ya zuba mata sannan yace, "Hakan shi ne mafita idan na barta da gudar da ya zuba mata tabbas zai cutar da ita da abin da yake cikinta." Idonta ne ya ci gaba da zubda ƙwalla ta sunkuyar da kai ƙasa bata furta komai ba sai kuma ta yi gaba, da sauri Saif ya riƙo hannunta don ya fahimci abin da za ta aikata, juyowa ta yi a zafafe amma kallon yake yi mata ya saukar mata da kasala, hakan ya sa ta sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Don Allah ka sake ni!" Shiru ya yi mata bai tanka mata.

Salman da ke gefe ya saki dariya me sauti yana tafi da hannunsa yace, "Ka bar murna karenka ya kama Kura." Saif ya ɗaga masa gira ɗaya yace, "Ka san ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Maryo ta nuna shi da ɗan yatsa fuska babu walwala ta ce, "Duk a kaina kake wannan haukan ko? Ka ɗauka zan ƙaunace ka ne bayan kana barazanar halakar da ƴar uwata. Ka buɗe kunnenka ka saurareni da kyau ka ji, wallahi baka ci bulus ba na rantse da Allah sai na baƙanta maka da baƙin ciki me tsanani. Idan ma saboda Saif kake yi wannan haukan daga kai har shi babu wanda zan aura, na faɗa na ƙara wallahi babu mutum ɗaya daga cikinku da zan aura. Ka taɓa mini 'Yar uwata ni kuma na ɗaura ɗambar taɓaka tun daga yau har ƙarshen rayuwata." Abu ce ta jiyo ta kalli Maryo tana miƙa mata hannu, a hankali Maryo ta ƙarasa ta riƙe hannunta tana sunkuyar da kai ƙasa ta fara cewa,

"Don Allah ki gafarce ni ƴar uwata ba ni na cutar da ke ba, kuma ba ni da burin cutar da ke daidai da ƙwayar zarra a zuciyata, duk wannan abin ya faru da ke ta sanadina ne don Allah ki yafe mini." Maryo ta faɗa tana kallon ƙwayar idon Abu, Saif ne ya taimaka mata ta tashi daga gadon da take kai zuwa wani gadon ya nannaɗe zanin gadon da ya ɓaci, a hankali Maryo ta bi ta kan sabon gadon ta sake zuba mata idanu don jin amsar da Abu za ta bata.

Abu ce ta kalli Saif da ke hidima da kayan wurin ta ce, "Ba zan taɓa yafe miki ba har sai Saif ya yi mini alƙawarin duk abin da na buƙata a wurinsa zai aiwatar mini." Gaban Maryo ne ya yi mummuna faɗuwa, Saif ya tsaya cak sannan ya waigo ya zubawa Abu ido yana juya maganganunta. Gyaɗa masa kai ta yi, a hankali Saif ya furta, "In dai za ki yafe mata na yi miki alƙwarin biya miki buƙatarki matuƙar bata saɓawa addinin musulunci ba." Abu ta gyara kwanciyarta tana cewa, "Don girman Allah ka sauwaƙe mini ka auri 'yar uwata Maryo, wallahi ko baka sauwaƙe mini ba na yi alƙawarin ba zan koma gidanka ba." Jin maganarta ya yi dum! ya zuba mata idanu ya kasa furta koda kalma ɗaya ce. Da ƙarfi Maryo ta daki gadon da Abu take kai ta ce, "Yaushe kika fara hauka Abu ban sani ba? Kina cikin hayyacinki kuwa?" Abu ta saki murmushi ta ce, "Tun da muke baki taɓa gaya mini magana ta rashin girmamawa irin wannan ba, me ya sa don na faɗi abin da yake raina zamu fara haka da ke.?" Idanun Maryo ya kaɗa jawur ta ce, "Wa muke bautawa?" Abu ta ce, "Allah!" Maryo ta jinjina kai ta ce, "Na rantse da girmansa idan har Saif ya sake ki saboda wannan buƙatar taki babu ni babu ke, kin sanni farin sani idan ba bar abu na bar shi har abada kar ki janyo abin da zai rabani da ke. Karki manta komai rubutacce ne a wurin Ubangiji, kina tunanin bawa zai iya gujewa rubutacciyar ƙaddararsa? Kenan Allah ba zai jarabcemu ba ko mun fi Ubangiji sanin abin da ya kama? Ko kina gidan Saif ko bakya gidansa wallahi ba zan aure shi ba don haka idan kina son na ci gaba da ɗaukanki kamar yadda muke da ki bar wannan maganar."

Abu ta lumshe ido ta ce, "Ina burin ganin farincikinki Maryo amma ki sani wannan ciwon nawa ba na tashi bane don Allah ki bari na ga aurenki da Saif kar sai lokacin da ƙasa ta rufe mini ido a yi babu ni, domin ina ji a jikin wannan cikin abokin tafiyata ne..." Da sauri Saif ya rufe mata baki idanunsa sun yi jawur saboda tashin hankali, Maryo jikinta na rawa ta ƙarasa wurim Abu ta ce, "Ya isa ki bari ki samu lafiya duk abin da kike so haka za a yi ba dai so kike na aure shi ba. To Allah ya baki lafiya." Kamar me shirin ta shi sama haka Salman ya fice fuuuu daga cikin ɗakin. Gabaɗaya suka bi shi da kallo babu wanda ya tanka masa.

Abu ta ce, "Maryo meye alaƙarki da Likitan can har kuke musayar yawu." Nan take Saif ya sanar da ita abin da yake faruwa, Maryo ta kora mata bayanin burin Saif a kanta. Ganin ta shiga damuwa ya sa suka kwantar mata da hankali da nuna mata hanyoyin da za su shawo kan matsara. Maryo ta sanar da Abu za ta auri Saif ne domin ta lura idan ta biye mata sai jikinta ya sake rikicewa fiye da na baya, don ta lura da nadamar aurensa da ƴar uwar tata ta yi.

Fulani Maryama ta gana tabbatarwa da kanta hannunta ya riga da ya shanye, ba a ɗauki lokaci ba ta sanarwa da Takawa duk abin da yake faruwa, lokacin da take yi masa bayani kuka ne a fuskarta shaɓe-shaɓe. Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, amma abin da ya fi daminsa da ta ce Maryo ce ta shanye mata hannu sai dai an tabbatar da cewar tun da aka tafi da Abu asibiti babu wanda ya ga gilmawar Maryo, ganin yadda ta rikice ya sa Sarki Aminullah ya tabbatar da cewar tabbas aljanu ne suka shafe ta domin babu yadda za a yi ace mutum ɗan uwanka ya shanye maka hannu. A ranar ya aika ka fara gayyato masu magungunan gargajiya domin sun bata magani ko hannun ya miƙe. Kafin wani lokaci tuni shanyewar hannun Fulani Maryama ya karaɗe cikin Masarautar, wannan gayawa wancan gayawa wancan. Sauran kishiyoyinta sam maganar bata yi musu daɗi ba haka daga ɓangaren Jakadiya lokacin da labarin ya je mata sai da ta shiga banɗaki sau biyu sannan ta lallaɓa ta nufi sashen Fulani Maryama domin tabbatar da abin da kunnuwanta suka jiye mata dukda ita ma ba maruru na ci gaba da rarake hammatarta.

Abu satinta Biyu a asibiti aka sallamota jikinta ya yi kyau sosai ta warware, cikinta ya ƙara tsufa da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wannan dalilin ya sa Fulani Zaliha ta dakatar da komen Abu ta umarci a mayar da ita sashenta domin ta ci gaba da bata kulawar da Uwa take bawa ƴarta. Inna Habi na jin daɗin yadda Fulani Zaliha take ƙaunar Abu, Maryo ku san kullin tana wurin Abu domin idan damuwa ta yi mata yawa in taje can tana samun sauƙin halin da take ciki. Hakan yana yi wa Inna Habi daɗi domin damuwar da Maryo take shiga na raguwa, ana cikin haka Maleek ya kawo mata ƙoƙon barar soyayyarsa. Da farko ta so ta bijire masa amma sai ta yi tunani idan ba amince masa ta yi ba ba zata samu kwanciyar hankali a wurin Saif da Salman ba, domin ta san ita kanta Abu ta yi mata shiru amma ta jadadda mata baza ta koma gidan Saif ba ya fi a irga. Wannan labari ba ƙaramin daɗi ya yi wa Inna Habi ba dama kuma duk wanda ya ga yadda Maleek yake yi wa Maryo zai tabbatar da irin ƙaunar da yake yi mata.

Ba a ɗauko lokaci ba Manya suka suka shiga magana, Mahaifin Maleek ya zo Masarautar Kano ya nemar Ɗansa auren Maryo a wurin Sarki Aminullah. Takawa sai da ya ji ta bakin Maryo domin yace wannan karan sai an ji daga gare ta, a kunyace ta amsa dukda za ta auri Maleek ne ba don tana sonsa ba sai don kyawun halinsa da kulawar da yake bata. Nan take Sarki Aminullah ya sanya musu rana wata biyu masu zuwa. Lokacin da Saif da Salman suka samu wannan labarin ba ƙaramin girgiza su ya yi ba, amma ga mamakin Maryo sai ta ga Salman bai nuna wata damuwa ba sai dai Saif da ya rikice mata yana nuna mata tsananin damuwarsa.

BAYAN SATI UKU

Ranar Laraba da daddare naƙuda ta kama Abu tun tana ɓoyewa har ta ji ciwon ya tsananta ta fara sintiri a ɗaki, Fulani Zaliha ce ta farka saboda jin motsin Abu da ta yi. Ku san kwana ta yi tana abu ɗaya sai bayan Asuba Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santalelan Ɗanta namiji kyakkyawa kamarsa ɗaya sak da Saif. Fulani Zaliha ba ƙaramin farinciki ta yi bata jima tana kallon yaron sai take tuna lokacin da haifi Saif, rumgume shi ta yi tana godiya ga Allah bisa wannan kyautar da ya yi musu.

Da kanta ta gyara Mai jego ta da jariri sannan ta mayar da su kan shimfiɗa Abu ta rungume Ɗanta suka koma bacci, sai a lokacin Fulani Zaliha ta aika Bayi da ta kira Unguwar zoma, nan take ta ƙaraso ta gyara wurin sannan aka fara sanarwa da mutanen kyakkyawan albishir.


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._


[12/01, 18:55] Ameera Adam🌚: 61...

Waiwaye...

Duk yadda Zulik zai yi ya janyo hankalin Rayzuta ya yi amma sam abin ya faskara, hasali ma 'yar gaisuwar mutumcin da suke yi ma ta yanke ta don ko ya zo cikin fadarsu idan tana zaune, ko ta tashi ko ta nemi wani uzurin da zai tashe ta daga wurin, abin sam baya yi wa Furzaan daɗi sakamakon Zulik abokinsa ne makusanci ba shi da na biyunsa. Hasali shi ba mai sha'awar tara abokai bane, wannan dalilin ya sa kodayaushe yana cikin masarauta idan baya sashen su to yana wurin ƙawarsa wacce ta rikiɗe zuwa masoyiyarsa. Wata ranar Juma'a suna zaune cikin lambum Mahaifinta suna hira Furzaan ya zuba mata ido lokacin da take ba shi labarin mafarkin da ta yi,

Bari mu ɗan taɓa yaren nasu🌚

"Wurbankis guna bila kalbistu kinmansu walbisu fatgurin zakbistu..."

(Ka bani goron albishir na baka labarin mafarkin da na yi, ka san mai ya faru...)

Sai kuma ta katse maganar bakinta tana zuba masa ido har ta sa hannu a saitim fuskarsa, har sai da ta ɗan tafa hannunta a kan fuskarsa sannan ta ɗan ɓata fuska ta ce, "Wai dama ba saurarena kake yi ba."

Shagwaɓe fuska ya yi yace, "A kodayaushe sauraron muryarki na sanya ni faɗawa cikin wani yanayi, har yanzu gani nake ina ta bilayi ban sani ba ko waiwayen da nake yi za a fahimci ƙishirwata. Sai dai a koyaushe idan na yi tuno da giwa ta yi wa barewa nauyi na kan ji karaya a zuciyata, sai dai bana jin zan iya jure kishirwar da nake ji ba tare da na kawar da ita ba." sai kuma ya marairaice murya kamar mai shirin yin kuka ya ci gaba da cewa, "Ba ta yi mini adalci ba kuma da zan iya tozali da na hukuntata da hukunci mai tsanani saboda bata shawarce ni ba. Na faɗa kogin soyayya ba tare da shiri ba sai dai bana jin zan samu gurbi domin bakin rijiya ba wurin wasa makaho bane. Wannan dalilin ya sa nake karaya..."

"Karaya ga gawurtaccen jarumin maza sam bai dace da kai ba. Bana buƙatar saka jin kalmar daga bakinka domin sam bata dace da kai ba. Ta dace da gurbin zama shi ya sa ta samu sukunin zama a cikin zuciyarka. Kada ka taɓa tsammanin bata yi maka adalci ba domin ta ɗora ƙwarya a gurbinta. Ya za a yi ka hukuntata alhalin ta yi abin da ya dace domin duk abin da kake muradi yana tare da kai. Ka daina kewaye-kewaye domin ba zai haifar da Ɗa mai ido ba." Rayzuta ta faɗa tana kashe masa ido ɗaya. Mayar mata da martanin murmushi ya yi ya ruƙu hannunta, wannan ne karo na farko da haka ya fara faruwa a tsakaninsu, wani irin yaar ta ji a jikinta ta ɗago da idanunta karaf suka haɗa ido, rana ta farko kenan da ta gagara jurewa kallonsa a hankali ta sauke kanta ƙasa, tana cikin wannan yanayin ta riski muryarsa na cewa, "A yau zan bayyana miki abin da ya daɗe yana yi mini yawo a cikin zuciyata, Rayzuta!" Ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa. Ɗagowa ta yi ta kalle shi sannan ta sunkuyar da ka ƙasa ya ci gaba da cewa, "Koda za ki sa a hukunta ni sai na furta domin barin kashi a ciki baya maganin yunwa. Na san ba zan samu matsayin da za ki amshi ta yi na ba domin bambamcin tsakanin ruwa da jini a bayyane yake. Rayzuta ina ƙaunarki tun ranar dana fara tozali da ke! Ina sonki fiye da tunanin mai tunani. Sai dai bana jin zan iya mallakarki a matsayin matar..."

"Wa ya gaya maka?" Rayzuta ta yi maganar tana harɗe hannuwa a ƙirji sai ta ci gaba da cewa, "Na zura maka ido ne dama domin na ga iya gudun ruwanka. Furzaan! Na jima da dakon ƙauna da soyayarka, sai dai na yi kawaici ne domin mace da kunya aka santa. Duk wasu alamu na soyayya ina nuna maka amma kai sai ka nuna kamar baka gane ba shi ya sa na kame baki na." Farinciki ne ya lulluɓe masa zuciya lokaci ɗaya ya rungumota jikinsa ita ma ta kwantar da kanta tana jin wani irin farinciki a zuciyarta. Ɗago da ita ya yi yace, "Faɗa mini mafarkin da kika yi."

Ta ku biyu ta ƙara sannan ta juyo ta kalleshi ta ce, "Na yi mafarkin ana ɗaura mana aure sai wani irin duhu ya mamayr wurin daga baya kuma sai na Takawa ya fara zubar da jini."

Hankali a tashe ya furta, "Jini kuma?" Kanta tsaye Rayzuta ta ce, "Eh mene ne?" Murmushin yaƙe ya yi yace, "A'a babu komai!" Sauya fuska ta yi ta ce, "Amma sai na ga kamar baka yi farinciki ba." Hancin ta ya riƙe yana cewa,"Ke dai bakinki baya shiru." Ita da shi suka saki dariya lokaci ɗaya.

Suna cikin wannan yanayin Zulik ya faɗa wurin hannunsa riƙe da kwari da baka, yana ganinsu a wannan yanayin ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Haɗiye yawu mai ɗaci ya yi ya ƙirƙiro murmushin yaƙe ya ɗora a fuskarsa ya ƙarasa yana cewa, "Barkanku da hutawa." Rayzuta na tamke fuska ta yi ta fara haramar wucewa, da sauri Zulik ya sha gabanta yana cewa, "Yau ba za ki bar wurin nan ba har sai kin sanar mini me na yi miki?" Da mamaki ta juyo ta kalleshi fuska a tamke ta ce, "Zan tunasar da kai kada harshenka ya yi gangancin furta abin da zai kaika ga mummunan hukunci, ka tuna wace ce a gabanka." Fuzaan ya tausasa murya yana cewa, "Rayzuta! Ki tsaya don Allah ki saurare shi."

"Me kake so?" Ta tambaye shi a gajarce.

Wani shu'umin murmushi Zulik ya yi domin ya san haƙƙansa ya kusa cimma ruwa, saboda duk maganganun da su Furzaan suka yi tun daga farko har ƙarshe yana laɓe yana jin su. Juyawa ya yi wurin Furzaan yace, "Duk cikin gidan nan ka fi kowa kusanci da Gimbiya kai ne babban abokinta don Allah ka roƙar mini alfarma a wurinta, ta taimaka ta amshi soyayyata duk duniya babu wacce nake so nake ƙauna sama da ita." Jin maganganunsa yake kamar saukar aradu, ido ya zura masa yana jin maganganunsa na yi masa yawo a tsakiyar ka. Yana shirin yin magaga Rayzuta ta ce, "Karka wahalar da yawun bakinka domin wannan buƙatar taka daidai take ta ɓillar ƙaho a tsakiyar kan ɗan tsako. Na riga da na samu masoyi na haƙiƙa domin na gwada shi ta hanyoyi mabambamta. Don Allah ina roƙonka ka bar wahalar fa kanka domin wannan ba abu bane mai faruwa. Tana gama faɗa ta yi gaba kafin ta fita ya sha gabanta da sauri ya sha gabanta ya saki murmushi yana cewa, "Wallahi sai na aureki kin ji na gaya miki bar ganin ina lallaɓaki amma sai na nuna miki idan na nemi abu dole sai na same shi babu ruwana da matsayinki abin da na sani..." Bai rufe baki ba ta ɗauke shi da mari. Ta nuna shi da ɗan yatsa tana cewa, "Ina ganin mutumcinka ne saboda kai abokin Masoyina ne, amma kana neman ka kaini magaryar tuƙewa idan ka sake yi mini makaman..." Bata yi aune ga ta ji ya rumgomata da sauri Furzaan ya janyota jikinsa ya ture Zulik cikin fushi yana cewa, "Ya isa haka karka fara ƙoƙarin wuce gona da iri. Tun da ta ce bata ƙaunarka ana dole ne?" Zulik ya saki murmushi sannan ya nuna su yana cewa, "Allah ko? To mu zuba mu gani ni da ku shege ka fasa. Wallahi sai na cimma ƙuɗurina a kanki." Yana gama maganar ya fice daga lambun.

Wannan shi ne mafarin rashin jituwar Zulik da Furzaan...

Kafin wani lokaci tuni labarin haihuwar Abu ta karaɗe ciki da wajen masarautar Kano, wannan labari ba ƙaramin faranta ran su Inna Habi ya yi ba. Saɓanij Fulani Maryama da wannan saƙo ya zame mata mummunan albishir, wannan saƙo ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba dukda ta san wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma sam bata ji daɗin haka ba, amma a wannan karon tana shakar ziyarta ɗaya daga cikin Bokayenta saboda hannun da take fama da shi har gobe babu wani ci gaba da a ke samu. Masu magungunan gargajiya kala-kala sun zo kowa ya gwada basirarsa amma babu wani sauƙi ko canji. Canji ɗaya take lura da shi wato ta lura hannun nata ya fara tsotsewa yana ƙanƙancewa.

Jakadiya maruru ya yi mata sauƙi har ya fara saɓa, da safiyar ranar da Abu ta haihu ta leƙa wurin Fualani Maryama bayan sun gaisa Jakadiya ta yi ƙasa da murya ta ce, "Fulani ashe mummunan mafarkin da na yi a daren jiya ba banza ba? Wacce yarinyar ashe haihiwa za ta yi? Ya a ka yi muka yi sake har wannan lamarin ya auku? Maryama kina me har ta haife cikin nan ba tare da an ɓarar da shi ba." Fulani Maryama fuska ɗauke da damuwa ta janyo shanyayen hannunta tana nunawa Jakadiya, da sauri Jakadiya ta yi baya tana zaro ido waje ta ce, "Na taɓa ki da alheri Maryama meye wannan nake gani ido biyu da farar safiyar nan?"

"Jakadiya babu wanda zai yarda da abin da zan faɗa idan bake ba. Yarinyar nan Maryo ita ta tsotse mini hannuna."

"Kamar ya Fulani kina nufin ture ta yi miki?" Jakadiya ta tambaya hankali a tashe. Fulani Maryama ta rausayar da kai ta ce, "Turen Ƙadangare na yi wa Sirikar Zaliha shi ne ta diro mini yadda na ganta ido biyu in ga Annabi, amma yaran nan kowacce sai cewa ta yi bata ganta ba. Wallahi yarinyar ba mutum ba aljana ce, idan ba aljan ba waye zai aikata haka matsa hannuna fa ta yi amma ji na yi kamar ta tura shi cikin wuta. Tun daga lokacin shi kenan bana jin komai." Jakadiya jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba ta ce, "Maganar gaskiya Maryama ya kamata mu samawa ranmu salama akan yarinyar nan, ni fa ba tun yau lamarinta yake bani tsoro ba. Mu kawo ido mu zuba wanda muka yi a baya ma Allah ya yafe mana." Wani murmushi Fulani Maryama ta yi ta ce, "Jakadiya kina matuƙar ba ni mamaki, me ya sa kike saurun karaya ne?" Tsoro ƙarara ya bayyana fuskar Jakadiya a take ta miƙe tana cewa, "Maryama kin daina ba ni mamaki yanzu lamarinki tsoro yake bani, ni bari ki ga wucewata Allah ya baki lafiya amma duk yanda hannunki yake tsotsewa kamar an tsotse rake baki daddara ba." Wannan karan ko kyakkyawar sallama ba su ba Jakadiya ta fice ta faɗa sashen Fulani Zaliha. A cen ma bata daɗe ba saboda bata samu fuska ba, tana fita dagan sashen ta wuce sashen sauran Matan Sarki sannan ta koma sashensu.

Inna Habi lokacin da aka sanar da ita ba ƙaramin farin ciki ta yi amma fir ta ƙi zuwa ganin Abu da Jaririnta (Saboda tsananin kunya irin ta mutanen da) Maryo ko bari a gama sanar da saƙon ba ta yi ba ta fice da gudu ko takalmi babu. Tana zuwa ko a gurguje ta gaishe da Fulani Zaliha, murmushi ɗauke a fuskar Fulani Zaliha ta ce, "Ai fa ba zama an ɗaurawa karya aure. Su Maryo an yi ɗa da alama ko takalma baki taho da su ba." Maryo na shirin bata amsa ta ji kukan Jaririn Abu da gudu ta faɗa ɗakin tana zuwa ta haye kan gadon ƙarfen ta karɓe Jaririn da ke ta mutsu-mutsi yana saka hannu a baki." Cak Maryo ta tsaya tana zuba masa ido sakamakon tsananin kamar da ta ga yana yi da Saif, wani irin farinciki ne ya kamata a zuciyarta take ayyana,

"Tabbas ko ban auri Saif ba wannan ya zame mini abin farinciki. Yau Ɗan Saif ne a hannuna jininsa ne mallakinsa. Wannan shi ne murna biyu ga shi Ɗan 'yar uwata mahaifinsa kuma masoyi na." Ba ta san lokacin da ta rungume shi tsam a jikinta ba sai kuma ta faraa yi masa kissis cikin so da ƙauna.

Wata irin kunyarta Abu take ji, kamar ta san abin da yake zuciyar Maryo. Ta ɗora hannunta a kan Maryo tana sunkuyar da kai ƙasa ta ce, "Bawa baya taɓa gujewa ƙaddaras sai dai wannan ƙaddarar ba ta zo mini ta sigar da nake buƙata ba. Ta yi mini yankan ƙauna domin tana neman yin katanga ga a tsakanin masoya. Maryo!" Abu ta kira sunanta cikin wata irin murya ta ci gaba da cewa, "Wannan yaron da yake hannunki Ɗanki ne halak malak ina raye da bana raye na mallaka miki shi koda mahaifinsa bai amince ba ni na mallaka miki tun da ni na san zafin naƙudar shi." Idon Maryo ne ya ciko da ƙwallah ta kalli Abu ta ce, "Tun da na zo duniya babu kyautar da na taɓa farinciki da ita irin wannan haƙiƙa ke ƴar uwace ta daban." Abu ta yi murmushi tana cewa, "Abu na gaba ina son ki janye maganar aurenki da Maleek idan har ina da matsayi a wurinki. Karki damu da ni na sha gaya miki zamana da Saif yanzo ƙarshe amma kina ɗaukar lamarin kamar wasa, wallahi ba zan koma gidansa ba..." Da sauri Maryo dakatar da ita tana cewa, "Don Allah ina tsaka da farinciki kada ki ruje mini shi. Na gaya miki ina ƙaunarsa ne da za ki tursasani aurensa. Me ya sa bakwason farincikina ne? Na samu mijin da zai bani kulawa miji mai ƙaunata ya kike so ki sa ni auren

Please Login or Register in order to submit comment