Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Cikin Maryo ya fito sosai dan har ta shiga watan haihuwarta, cikin ba ƙaramar ƙiba ya saka ba ta yi wani irin haske ta ko'ina ta yi ƙiba. Ganin haka ya sa Fulani Zalina ta sa Saif ya dawo da ita sashenta don a cewarta bai kamata Maryo ta zauna a gidanta ba saboda gudun Naƙudar dare. Ko kaɗan Saif bai ji daɗi ba amma babu yanda ya iya haka ya haɗa mata kayanta ta koma can, sai dai tun da Maryo ta koma shima ya tare a can kodayaushe yana can don wani lokacin Fulani Zaliha har kunya take ji. Sai da ta yi da gaske ta fara fatattakarsa sai ya yi kamar ya yi kuka saboda sam baya son abin da zai nesanta shi da Matarsa.

Satin Maryo biyu a gida Allah ya sauke ta lafiya ta haifo santaleliyar Jaririyarta Mai kama da ita sak, Yarinyar babu inda ta baro Maryo a kammi sai dai ɗan duhun Mahaifinta da ta ɗauko. Farinciki wurin mutanen Masarautar Kano abun baya musaltuwa, lokacin da labarin haihuwar Maryo ya isa Masarautar Zazzau ba ƙaramin farinciki suka yi ba, saboda Murna Abu har ji ta yi kamar ta yi tsuntsuwa. Kwana biyar da haihuwa su Abu suka dira Masarautar Kano tare da kayan barka sha tara ta arziƙi. Abu saboda farinciki rungume Jaririyar ta yi kamar wani zai ƙwace mata. A lokacin da Maryo ta haihu Abu na da cikin wata uku, da daddare suna zaune su biyu a ɗaki Maryo ta dubi Abu ta ce, "Hajiyata ina ce kina kula mini da Ɗan uwa don ke dai na ga alamun yana baki kulawar da ta kamata, kin ga yanda kika zama uwar mata kuwa, don ni har gani na yi kamar da ajiyar mu a wurinki." Abu ta yi dariya ta ce, "Ƴar iska wai yaushe kika yi baki ban sani ba? Wallahi kin bani mamaki wai yau Maryo ke faɗin wannan maganar." Maryo ta kishingiɗa tana faɗin, "Sanin da kika yi mini amma yanzu kafin ki koma yarinyar sai na ƙara kintsaki yanda za ki bawa Ɗan uwana kulawa." Abu ta rafka salati tana tafa hannuwa ta ce, "A'uzubillah yasin kinfi ƙarfina bari na baki wuri, amma duk iskancin mutum sai ya yi arba'in biyu ko uku a gida." Maryo ta yi ƙasa da murya ta ce, "Wallahi da na bi mijina sahunmu a likafa mun wuce gida don an shiga haƙƙin masoya." Daidai lokacin Fulani Zaliha ta shiga ɗakin, Maryo ba ƙaramin kunya ta ji ba amma Fulani Zaliha ta yi kamar ba ta ji su ba ta kwantar da Naufal, kasancewar tun lokacin da Abu za ta yi aure ya koma wurin Maryo lokacin da cikinta ya fara girma sai Fulani Zaliha ta sa Saif ya kai mata shi.

Ranar Suna Jaririya ta ci sunan Mahaifiyar Maryo aka saka mata Rabi'atul Badawiyya, a lokacin Shukra tana goyon Ɗanta Namiji Mai sunan Sarki Muhammad Safyan, an yi shagali na ban mamaki. Mawaƙa da makaɗa sun baje kolinsu suna ta wasanni haka aka yi taron suna aka gama lafiya.

BAYAN KWANA HAMSIN

"Fulani maganar gaskiya yaron nan matarsa yake yi wa jelan nan saboda kina gani da kaɗan-kaɗan ya kwaso kayansa ya dawo gidan nan, ya yi mana zuru ya ji shiru kin ga yace idan ya dawo ai a bashi matarsa su tafi." Ina Habi wacce ta koma Fulani Habiba ta yi maganar cikin ƙasaitacciyar shiga ta alfarma. Fulani Zaliha da cikinta ya fara fitowa ta ce, "Fulani rabu da shi so nake na gyarata sosai don sai ta ƙara sati biyu nan gaba." Inna Habi ta zaro ido waje ta ce, "Sati biyu! Tabdi lallai zan kai ƙararki wurin Takawa don wallahi wannan shiga haƙƙin ba za a yi wa Ɗana ba." Fulani Zaliha ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce, "Wai don Allah da gaske yaron nan dalilin dawowarsa kenan?" Inna Habi ta saki murmushi ta ce, "Kina mamaki wallahi idan ba so kike a samo mana da cikin gida ba ki tattara matarsa ki kai masa, yau fa kwananta Hamsin da bakwai." Fulani Zaliha ta yi jim sannan ta ce, "Ai kuwa ba da ni za a yi wannan abun kunyar ba."

"To kuwa gara ki mayar masa da matarsa tun wuri." Gabaɗaya suka saka dariya.

Lamarin Fulani Maryama ya munana, duk mutum mai imani idan ya ga hakin da take ciki sai ya tausaya mata. A cikin wannan watannin gabaɗaya ta ciccizge jikinta, wasu rauninkan sun warke wasu kuwa guraren duk sun ruɓe, tsutsa duk ta fara cin ɓargonta ta rarake naman jikinta. Idan ka bi ta wurin ɗakinta ban da wari babu abin da yake tashi a wurin, lokacin da ciwon nata ya motsa da ta rasa wurin da za ta gaya ta ci, hannunta ta zura ta ƙwaƙwalo ƙwayar idonta tun bata kai ga cirowa ba ta fasa ƙara saboda azaba tana ihu, haka ta gama matagugunta babu wanda ya bi ta kanta, haka ta ci gaba da rayuwa cikin wulaƙanta da tagayyara.

A ɓangaren Jakadiya kuwa hauka take tuburan sai dai abin da yake ƙara haukata ta, tsirowar gashin kanta a duk lokacin da gashin kantabya tsiro sai wani aljani ya zo ya kafa bakinsa a kanta har sai ya zuƙe duk wani silin ga shi.

Ba a ɗauki lokaci ba Fulani Zaliha da kanta ta ƙara shirya Maryo da magungunan gyara, ba ƙaramun kyau ta yi ba jego ya amshe ita da ƴarta sun yi matuƙar kyau. Wata rana da daddare su Fulani Bilkisu suka mayar da Maryo ɗakin mijinta.

"Wai wata sabuwar kunyata kike ji?" Ta cikin mayafi Maryo ta zuro kai tana leƙensa, da sauri ya fisgo mayafin yana janyota jikinsa yana cewa, "Kunnuwana basa amsar sarewar duk wani sauti face na zinariyar macen da babu kamarta, idanuwa na yi mini gizo a duk lokacin da na buɗe su matuƙar ban sauke su a kanki ba. Jikina ya yi maraicin rashinki domin a kowanne sakan gangar jikina na ambaton sunanki, na yi matuƙar kewarki matata amma sai nake ganin kamar ba ki damu da ni. " Kashe masa ido ɗaya ta yi ta ɗora kanta a jikin kafaɗarsa tana cewa, "Harshe na furta kalmomi ne domin bayyana saƙon abin da yake cikin zuciya, sai dai tawa zuciyar na bayyanawa ƴar uwarta saƙonta ne a kodayaushe domin zuciyata da taka a haɗe suke basa taɓa rabuwa. A duk bugun numfashina yana sauka ne da ɗumbin begenka! Mai zai sa na yi rashinka bayan ni da kai abu ɗaya ne? Tabbas so daban yake haka ma ƙauna! Ina ƙaunarka mijina farincikina mai faranta zuciyata." Maryo na gama faɗa ta lumshe masa ido tana kanne masa ido ɗaya, Saif ku san mutuwar tsaye ya yi ƙaunarta na ƙara fisgarsa, rasa abin yi ya yi kawai ya janyota ita da Rabi'a (Nimra) ya rungume su cikin farinciki.


Tammat Bihamdullilah

Komai ya yi farko zai yi ƙarshe a nan na kawo ƙarshen wannan labarin, masoya ina godiya da nuna kulawarku ta hanyar siyan littafina bani da bakin gode muku, sai na ce Allah ya bar ƙauna domin yabon gwani ya zama dole. Tabbas kuɗin ƴan amana ne wallahi na yi matuƙar alfahari da ku saboda ban taɓa ganin labarin nan a kowanne group ba. Na gode da yanda kuka riƙe mini amana Allah ya bar ƙauna.❤️❤️🥰🥰

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._

Downloaded from GNOVELS.COM.NG




This Novel is downloaded from https://GNOVELS.COM.NG
to download more hausa novels visits our site at www.GNOVELS.COM.NG

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/gnovels

Twitter : https://twitter.com/gnovels

Telegram : https://t.me/gnovels


Please Login or Register in order to submit comment