Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakin baki ta yi tana kallon Fulani Zaliha don Allah ya sani tun da take da ita sai da irga adadin murmushin da ta taɓa gani a saman fuskar Fulani Zaliha, hasalima tun da take bata taɓa daɗewa a sashenta kamar daɗewar da ta yi yau ba. A zuciyarta ta fara godia don ta tabbata tun da ta samu arziƙin sakin fuska, ba ƙaramar kyauta za ta samu ba. Wannan ya bata damar yashe baki ta ci gaba da bambaɗanci har Fulani Zaliha ta sallame ta. Jakadiya na fita bata zarce ko ina ba sai sashen Fulani Maryama, kanta tsaye ta yi sallama ta shiga. Tun daga tsakar gida Jakadiya ta fara rangaɗa guda, tana juyi a tsakar gida. Inna Habi dake ɗaura lalle daga ɗakinta tana hangota ta girgiza kai, don gabaɗaya ta gama fahimtar Jakadiya munfuka ce ajin farko. Kasancewar Fulani Maryama na cikin farin ciki yasa ta bawa Bayin ta damar kowa ya tafi sabgar gabansa na tsawon wunin. Jakadiya na shiga ta tsugunna nan ma ta fara bambaɗanci kamar yadda ta yi wurin Fulani Zaliha, sai da ta gama ta gyara zama ta ce, "Allah ya taimake ki wai ni kam don Allah wace tsiya ce ta ƙarewa Zaliha da Ɗanta, su rasa wacce zai aura sai ƴantacciyar Baiwa. Kai wallahi ni kam ba ƙaramin takaici na ji ba wannan ai salon ya ja wa Masarautar nan zagi ne saboda Allah, duk ƴaƴan Sarakunan ƙasar nan amma ya rasa wa zai so sai waccen figaggiyar ƴar Fulanin." Fulani Maryama da tun shigar Jakadiya Murmushi ne kwance a saman fuskar, ta kuma washe baki tana dariya me sauti ta ce, "Im muguwar kaza ta fara shiga akurki duk wacce ta zo sai ta tare ta. Don haka ni fes a gareni." Jakadiya ta yi murmushi ta ce, "Fulani Maryama kenan. Ba a sanin murnar karen da bashi da wutsiya." Fulani Maryama ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin izza da isa ta ce, "Jakadiya duk Karen da bashi da wutsiya dube shi da kyau ƙwayar idonsa za ta gaya miki amsar halin da yake ciki." Jakadiya ta saki shewa ta ce, "Amma kin fi kowa sanin Zaliha Miskila ce cikin mata ba kamar sauran kishiyoyinku take ba, na tabbata wannan karen kallon ƙwayar idonsa za yi miki wahala." Fulani Maryama ta buɗe hannuwa alamar rashin damuwa ta ce, "Jakadiya kin manta da ko anci birnin Kura ba a ba kare dillanci, Maryama nake ginshiƙin dutse kowa karo da ni za shi ƙasa. Sam ban damu da wacce Saif zai aura ba ko da kuwa mahaukaciya ce burina na dai kawai ya yi aure shi da Salman, idan na fara cimma wannan matsayar sai na san yadda zan ɓullowa sauran lamura, domin shan tabar kwaɗo da baki da hanci yake." Jakadiya ta kalli Fulani Maryama tana jinjina kai ta saki murmushi ta ce, "Maryama ƙarfin gwiwarki da izzar ki yana matuƙar birge ni, ba kowa yake gane murmushin jaki ba wani idan ya gani ɗauka zai kuka yake wani kuma ya yi tsammanin cizo zai kai." Fulani Maryama ta gyaɗa kai kamar ƙadangaruwa ta ce, "Tabbas kuwa, domin kwana a gado daban da sabon kabari." Jakadiya ta sauya fuska zuwa yanayin jimami ta ce, "Oh! Sabon kabari me sa a tuna Allah. Maryama yaushe za mu tuba ne?" Fulani Maryama ta ce, "Lokacin da na gama biyan buƙatar rayuwata." Jakadiya ta kalleta a kaikace ta ce, "Ai kuwa buƙatar me rai bata cika sai kwana ya ƙare." Ɗaure fuska Fulani Maryama ta yi ta ce, "Wani me ran ya kan cika buƙatunsa sai kuma rai ya yi halinsa. Jakadiya idan muna raha ki bar sako mini zancen mutuwa." Jakadiya cikin zuciyarta take mamakin baƙi hali irin na Fulani Maryama da bushewar zuciya, da mamaki ƙarara asaman fuskarta ta ce, "Sarautar Allah kare a bakin kura. Maryama wacce irin zuciya gare ki." Kai tsaye Fulani Maryama ta bata amsa, "Wacce aka ciro daga jikinki aka liƙa mini." Jakadiya ta shi ta yi ta ce, "To Allah ya ƙwato ki don na lura kin yi nisa bakya jin kira." Fulani Maryama ba ta tanka mata ba, saboda ta lura idan ta biyewa Jakadiya sai ta ɓata mata rai alhalin tana cikin farin ciki. Jakadiya na fita bata zame ko ina ba sai ɗakin Inna Habi. Rangaɗa uwar sallama ta yi Inna Habi ta amsa mata ba yabo ba fallasa. Zama ta yi a gefe dokin ƙofa ta ce, "Uwar amarya sai kuma nake jin abun alheri." Inna Habi ta ɗauka murnar Salman take yi mata, murmushi ta yi ta ce, "Eh wallahi Yarima ya kusa girma, Allah ya nuna mana lokacin." Ganin kamar Inna Habi bata fahimci inda zancen ya dosa ba Jakadiya ta ce, "Ban da abin ki Habi na san dai Abu ai ba ta fari bace a wurinki, to karar me za ki yi?" Inna Habi ta yi murmushi ta ce, "Jakadiya karar me zan yi kuma?" Jakadiya ta ce, "Yooo na ga ina yi miki Allah sanya alherin Abu kina kaucewa, Allah na tuba ai farinciki za kiyi Namiji kamar Saif me nasaba da tushe har aka yi masa baiko da Abu ai abin nunawa duniya ne." Cikin rashin Fahimta Inna Habi ta ce, "Wace Abun aka yi wa baiko da Saif?" Jakadiya gulma na cinta ta ce, "Abuh ƴar wurinka mana ai duk tare aka yi musu baiko da Salman. Kuma ance yana mutuwar son Abuh ita ma tana ƙaunarsa, wai ke baki sani bane." Inna Habi ta fahimci bugun cikinta Jakadiya take don haka ta ce, "Na yi mamaki da Abuh ta zaɓi Saif ne, mun yi magana da ita ta ce akwai wani Yaro da suke taɗi. Kin san yaran yanzu baka gane alƙibilarsu." Jakadiya sam ba haka ta so ba ta miƙe tsaye tana faɗin, "Yooo ke kuwa ga wurin da za a haɗu da babban rabo, ko ba komai ai ta auri jinin Aminullahi."tana gama faɗa ta fice daga gidan.


Al'ummar da ke zaune a masarautar Adamawa ba ƙaramin mamakin mugun halin Fulani Babba suka yi ba, saboda su dai a iya zamansu da ita basu taɓa kawo za ta aikata makamancin abin da ta furta da bakinta ba. A iya saninsu dai ita mace ce me son girma da son shugabanci, amma ba su yi zatan son matsayin nata har ya kai ga haka ba. Wunin ranar haka kowa ya wuni da ta'ajibinta, wasu na tsine mata wasu kuma suna ganin kuskurene da kowanne ɗan Adam yake iya aikatawa. Amma mafi yawa daga ciki sun fi danganta hakan da son zuciya, zalinci da rashin imani. Maryo na komawa ɗaki ta zauna ita kaɗai a ɗaki ta haɗa kai da gwiwa tana zubda wani irin hawaye me ƙuna, zuciyarta za fi take ga wani irin raɗaɗin ƙaunar Saif da yake ƙara nuƙurƙusar zuciyarta. Hannu ta sa ta dafe saitin zuciyarta ta kuma fashewa da kuka, nan take wani irin tari ya turniƙeta tun tana yi daga zaune har ta fara galabaita tana dafa bango tana ƙoƙarin miƙewa, feshin jini bakinta yake yi har ta fara fita daga hayyacinta. Dafa bango ta fara yi tana tafe tana labuben hanya hannunta ɗaya na kan ƙirjinta, hannu ɗaya tana laluben ƙofar fita. Tana zuwa bakin ƙofa ƙarfinta ya ƙare nan ta yanke jiki ta faɗi hancinta da bakinta na zubar da Jini. Lokacin da fadar ta watse jiki babu ƙwari Maleek ya miƙe kallon Mahaifinsa ya yi yana jin tausayinsa na mamaye zuciyarsa, musamman yadda ya ga har zuwa wannan lokacin yana rungume da Mahaifiyarsa yana zubda hawaye, ita ma hawayen take yi tana shafa kansa da rawanin kansa yake ƙoƙarin zamewa. Ganin hakan ne yasa Dogarawa suka sallami kowa harda su suka fita zuwa bakin ƙofa, ya zama ɗakin daga Sarki Abdallah, Me babban ɗaki sai ƴaƴansa maza guda Uku. Maleek ga ni ya yi ba zai iya ci gaba da gani ba don zuciyarsa ta fara karyewa, don kukan da Muhsin yake ba na farinciki bane. Yana kukan halin da Mahaifiyarsa take ciki da abin da ta aikata, don gabaɗaya ji yake ya tsani kansa yana kunyar fita ya haɗa ido da sauran al'umma. Lokacin da Maleek ya nufi sashensu gabansa ne ya ci gaba da faɗuwa don be san abin da zai je ya tarar, jiki babu ƙwari ya kamar marar laka a jiki haka ya fara takawa har zuwa bakin ƙofa, sama-sama yake jiyo nishinta tsoro ne ya fara kamashi don gani yake idan ya leƙa kamar zai iya ganin abin da zai kuma sumar da shi, kamar marar gaskiya haka ya fara tafiya saɗaf-saɗaf har ya zura kansa ya leƙa don ganin abin da yake faruwa. Zaro ido waje ya yi lokacin da ya yi tozali da halin da take ciki, da sauri ya ƙarasa hankali a tashe ya fara ƙwala mata kira amma bata iya buɗe idonta ba bare ya sa ran za ta kula shi ba. Hankali tashe ya ɗauke ta yana ƙwalawa Bayin da ke harabar sashen amma sakamakon abin da ya faru babu kowa a wurin, da sauri ya fice daga wurin ya nufi sashen Mahaifiyarsa da ita. Yana shiga ya same su jigun-jigun sam hankalinsa be kai ga yanayin da suke ciki ba, cikin damuwa yake faɗin. "Ummi! Shukra don Allah karta mutu aman jini take yi." Hankalinta ne ya tashi da sauri ta aika aka kira baushe nan take ɗan aiken ya dawo tare da Baushe. Kwantar da Maryo aka yi tana numfashi sama-sama, ƙura mata ido ya yi sanann ya jiƙa wani garin magani ya shafa mata a jiki ya ɗura mata sauran a bakinta. Numfashinta ne ya ci gaba da kaiwa da kawowa yana sama yana ƙasa, tarin ne ya ƙara rufeta ta fara yi babu ƙaƙƙautawa. Baushe ba ƙaramin tsorata ya yi ba, don be taɓa ganin ciwo irin wannan ba. A hankali Maryo ta buɗe idanunta da suka rune jawur, kallonsu take ɗaya bayan ɗaya hawaye na ƙwarara daga idanunta ta fara motsa bakinta a hankali tana cewa, " kowanne lokaci kowanne ɗan adam yana tafiya da yadda ƙaddararsa ta faro tun daga tsiron nufashinsa, ni tawa rubutacciyar ƙaddarar kenan. Allah ya ƙaddara ba zan sake cika burinmu na kasancewa ababen farantawa zuƙata ba, tafiyar ƙaddarata tafe yake da sauran ƙalubalen baya. Wataƙila tarayyata da shi bata da alheri shi yasa inuwar junanmu take ƙara nesa da juna." Tari ta ƙara yi jini na bin gefen bakinta ta ɗago ta kalli Maleek da ke gefe yana zubda ƙwallah, ta sakar masa murmushi ta ce, "Tabbas na aminta da yadda ka jiɓanci wani tsagi na daga sashena, haka tamu ƙaddarar take samun muradin abokin rayuwarmu na tafe da ƙalubale. Ka riƙe maganar da nake gaya maka har kullin, ni ba Shukra bace ka yi ta gudu me yawa kamar wanda yake laluben bangon duniya, tabbas za ka cinma muradinka idan har ka kasance baka wuri ɗaya a zaune. A duk lokacin da ka haɗu da Shukra ka bata wannan zoben na hannuna, wataƙila zata fahimci zanen ƙaddarata wanda yake tattare da ƙalubale." Hannu ta ɗaga da kyar jikin ta na karkarwa ta damƙi hannunsa da ɗan yatsenta yake ɗauke da wata azurfa, kuka na neman cin ƙarfinta ta ce, "Don Allah zan baka saƙo ka kaiwa Saif!" Hannu ta sa ta dafe zuciyarta da take barzanar faso ƙirjinta hawaye na zuba ta ci gaba da cewa, "Ka gaya masa ina ƙaunarsa fiye da tunanin ne tunani kuma ba zan fasa ƙaunarsa domin ƙaddararsa tafe take da tawa ƙaddara. Ka gaya masa na ci albarkar ƙaunar da nake masa ya sakawa ƴarsa sunana, sai ƴar uwa ta Abuh ka gaya mata ta tayani kishinsa saboda ta san yadda nake mutuwar sonsa, da zan iya da na shawarci ta zame masa mata sai dai banajin zan iya haɗiye wannan ƙaddarar. A dacen ma ban juri ganinsa da wata mace ba bare yanzu, ka isar da saƙona gare su na fatan aleri. Sai Inna Habi..." nan take tari ya sarƙe ta amai ya ci gaba da zuba daga bakinta. Numfashinta ne ya shiga yin sama da ƙasa ta fara wata irin shaƙuwa, da sauri Maleek ya ɗau ruwa ya fara ƙoƙarin bata amma sai ji ya yi numfashinta ya ɗauke, jikinta ya yi wani irin nauyi kanta ya langaɓe gefe ɗaya. Cikin tashin hankali ya fara ƙwallah mata kira amma babu alamun numfashi a tattare da ita, Fulani Fahima da sauran mutanen da ke wurin jikinsu ba ƙaramin sanyi ya yi ba, ban da hawaye babu abin da suke yi. Fulani Fahima zani ta janyo ta janye Maleek da ƙyar ta rufa mata, sannan ta aika aka sanarwa da Sarki Abdallah rasuwarta.

R I P MARYO😭

A lokacin da zanen ƙaddarar wasu take ƙarewa a lokacin wasu suke farawa, ita ƙaddara kamar inuwa ce baka taɓa guje mata. Wani ƙaddararsa haɗe take da kasada ƙarshenma kasa, haka wani yake rayuwa ba tare da cimma burinsa na duniya ba. Bakowanne buri ne ake iya cika shi ba, wani duk yadda ya kai ga cimma burinsa zanen ƙaddararsa na katange burukansa.

ALLAH SA KANKU BE KULLE DA YAWA BA😂😂😂😂😂😂 TO GAMU A WANI YANAYI ME DAƊI NE KO MARAR DAƊI CI GABAN LABARIN SHI ZAI IDAR DA HAKA, AMMA FA SAI DAI KU YI HAƘURI DA YADDA TSARIN LABARIN YAKE SABODA TAFE YAKE DA BAN TAUSAYI NA RASHIN CIKAR MURADI.

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[11/12/2021, 19:14] Ameera Adam🌚: 46...


Inna Habi zuciyarta sai harbawa take jikinta ya yi wani irin sanyi, zantukan Jakadiya ne suke yi mata yawo a zuciya. Duk lokacin da ta kai aya a mamaita maganar Jakadiya sai ta ji ƙirjinta ya buga, janye masakin lallen ta yi gefe jiki a mace don yadda take ji da ace bata gama saka lallen ba babu yadda za a yi ta ci gaba da zama a wurin.

Abu na cikin ɗaki haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa musamman da ta tuna da Mahaifiyarta, zaro ido waje ta yi tana dafe ƙirji a fili ta ce, "Na shiga uku na! Wallahi Idan Inna ta sani na san kashe ni za ta yi. Na shiga uku." Nan take jikinta ya hau karkarwa tsoro na ci gaba da mamaye zuciyarta, ilahirin jikinta gumi yake tana fargabar haɗuwarsu da Mahaifiyarta don ta san ta aikata babban laifi domin ko da wasa bata taɓa yi mata hirar Saif ba. Ta ina ma za ta fara tun da bata manta yadda aka ƙarke da Maryo ba. Wani irin bugu ƙirjinta ya ƙara yi wanda har sai da ta yi saurin dafe zuciyarta tana jingina da bango, tunowa ta yi da cikin da ke jikin Maryo wanda take ta iƙirarin na Saif ne. Wani ƙulun baƙin ciki ne ya kamata ta a zuciyarta ta ayyana, " Kenan Saif ya taɓa sanin Maryo?" Nan take hawaye ya fara gangarowa daga idanunta, a gefe ɗaya tana jin haushin Saif da Maryo amma Maryo ta fi mugun bata haushi.

Inna Habi jikinta har rawa yake tana gama wanke lallen ta fice daga gidan ko neman izinin Fulani Maryama bata yi bi, tana shiga sashen Fulani Zaliha ta nemi iso wurin Fulani Zaliha, ba a ɗauki lokaci ba suka yi mata iso tana shiga ta same ta a zaune cikin shiga ta alfarma. Russunawa ta yi ta gaida Fulani Zaliha, ta mayar mata da murmushi tana faɗin, "Barkanki da zuwa Inna Habiba ya aiki, ya bayan saduwa?" Inna Habi da kwarjinin baiwar Allahr ya mamaye zuciyarta ta tattaro jarumta ta ce, "Ranki shi daɗe sai alheri." Fulani Zaliha ta yi mata murmushi don lokaci ɗaya ta ji matar ta kwanta mata a rai. Ɗan jim Inna Habi ta yi Fulani Zaliha ta lura da yanayin da Inna Habi take ciki kamar tana cikin damuwa, gyara zaman ta tayi ta ce, "Inna Habiba ga dai abin alheri ya haɗamu." Inna Habi gabanta ya faɗi tana addu'ar Allah a samu saɓanin magana akan abin da Jakadiya ta sanar mata da shi. Jiki a sanyaye ta ce, "Ki gafarce ni ranki shi daɗe na yi jinkirin yi miki Allah sanya alheri." Fulani Zaliha murmushi ta yi mata ta ce, "Karki damu Inna wannan ba wani abu bane, na yi matuƙar farinciki da Abu za ta kasance matar Ɗana, Allah ya biya ki da gidan Aljanna sakamakon tarbiyyar da kika bata." Idanun Inna Habi ne ya ciko da ƙwalla gabanta na ci gaba da faɗuwa ta ce, "Amin Ranki shi daɗe." Abu da ke ɗaki jin muryar Innarta ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tana ta zarya a ɗaki ta ji Fulani Zaliha ta aika da akira ta.

Kamar mara gaskiya tun kafin baiwar ta shiga kiranta ta yi zaraf ta fito, ɗakin ta shiga tana sunne kai ƙasa tana zura ƙafarta ta ji ƙirjinta na bugawa. Murmushin yaƙe ta yi ta ƙarasa gefen Inna Habi tana raba ido ta ce, "Barka da zuwa Inna ran...amm... dama..." Haka ta fara inda-inda Inna ta yi murmushi ta ce, "Ba komai kawai dama na ce zan zo na yi wa Fulani Allah sanya alheri ne."

Inna Habi ta miƙe ta kuma rassunawa ta ce, "A huta lafiya ranki shi daɗe." Fulani Zaliha ta amsa mata sannan ta ce, "Abu ki tashi ki yi mata rakiya mana." Kamar wacce aka zarewa laka a jiki Abu ta miƙe ta bi bayan Inna Habi tana raba idanu, tana zuwa soro Inna Habi ta juyo ta kife ta mari kafin ta ɗago ta kuma kife ta da mari sai kuma ta rufe ta da duka tana fashewa da wani irin kuka me tsuma zuciya.

Sarki Abdallah wata tsawa ya bugawa Dogarin da ya same shi da mutuwar Maryo ya yi yana faɗin, "Yarinyar da ta bar waurin nan yanzu ita za ka ce mini ta mutu kana hauka ne?" Dogarin sunkuyar da kai ƙasa ya yi ya fara motsa baki don be san da wane yanayi zai gamsar da Sarki Abdallah ba. Ɗagowa ya yi zai yi magana Maleek ya shiga a haukace kamar mahaukaci sabon kamu, yana zuwa ya durƙushe gaban Sarki Aminullah yana kuka yana faɗin, "Wai shukra ta mutu yanzu nan fa ta fita daga wurin nan. Don Allah Ranka shi daɗe muje ka tashe ta, wallahi ba zan iya rayuwa babu ita ba." Jikin Sarki Abdallah ne ya yi sanyi don yadda ya ga Maleek tabbas babu ko tantama maganar da Dogari ya faɗa haka ne. Dafa kafaɗar Maleek ya yi yace, "Ka yi haƙuri Maleek amma duk wanda ka ga ya mutu kwanansa ne ya ƙare." Maleek ya ɗago da hawaye shaɓe-shaɓe yace, "Kwananta be ƙare ba wallahi idan muka je da kai za ka iya tashin ta." Da sauri Sarki Abdallah ya kife Maleek da mari, sai lokacin ya saita nutsuwarsa ya fasa wani irin kuka me tsuma zuciya, dan duk wanda yake cikin gidan ya san irin zallar soyayyar da yake yi wa Shukransa. Me babban ɗaki da tun shigowar Dogari tana jin saƙonsa ta fashe da kuka hankalinta na daɗa tashi. Sarki Abdallah tattaro jarunmta ya yi yana jin zuciyarsa na rauni ya kalli Dogarin yace, "A je a sanarwa da Jakadiya ta je su yi mata sutura."

Jakadiya na shiga gidan gabanta ya faɗi, fuskarta ɗauke da hawaye ya ɗaga labulen ɗakin da Maryo take kwance. A hankali ta zame zanin bayan an kawo mata ruwan da za ta wanke Maryo da shi, idanunta na sauka kan Maryo ta zaro ido cikin tashin hankali. Waɗansu irin manyan tururuwai ne suka zagaye ta masu yawan gaske, daga cikin kunnenta jini ne yake ɗiga kaɗan. A hankali tururuwar ta fara zaizaiyar ƙasar wurin da maryo take a kwance, A hankali Jakadiya ta ɗora hannunta akan hannun Maryo ta ji shi sanyi ƙalau, wata tururuwa ce ta hau saman hannun Jakadiya cikin azaba ta fasa ƙalla ta fice daga ɗakin tana kururuwan neman taimako.

A tsorace mutanen wurin kowa ya ɗiba da gudu don a tunaninsu Gawa ce ta riƙe ta, Jakadiya ban da juyi babu abin da take a tsakar gidan da ƙyar ta samu ta fisge Tururuwar da ƙarfin tsiya, sai ga shi ta haɗa da fatar wurin da ta ciza, jini ne ya fara gangarowa daga hannun Jakadiya yana ɗiga. Duk inda Jinin ya ɗiga da sauri Tururuwar za ta bi ta fara zuƙa.

BARKA DA HUTUN ƘARSHEN MAKO🥰


_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA'A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR,0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
[12/12/2021, 19:34] Ameera Adam🌚: 47....


Jakadiya tsaye ta yi cikin tsoro tana kallon ikon Allah saboda abu ne da bata taɓa ganin irinsa ba. Ganin Jakadiya a tsaitsaye yasa Sauran matan Sarki Abdallah leƙowa suna ganin abin da yake faruwa, ɗaya bayan ɗaya haka suka fara fitowa suna kalon hannunta da yake ɗigar da Jini, sannu suka fara yi mata suna tambayar ba a sin abin da yake faruwa. Nuna musu turuwar ta yi cikin haki ta ce, "Turuwa ce ta zagaye gawar, kinga wannan ita ta maƙale mini a hannu dubbi yadda hannun ya yi." Dafe ƙirji suka yi cikin ta'ajibi kowa tsoro ya kama shi. Fulani Fahima ce ta yi namijin ƙoƙarin cewa, "Jakadiya mu shiga mu gani mu biyu ko zamu iya sai a sauyawa gawar wurin kwanciya." Jakadiya ta yi tsalle gefe ta ce, "Allah ya taimakeki ni dai tun da muke da ke ban taɓa yi miki musu ba amma maganar gaskiya ba zan iya tunkarar gawar nan ba, don ni kaɗai na san halin da na shiga lokacin da Tururuwar nan ta hau kan hannuna." Fulani Fahima bata tankawa Jakadiya ta kalli wasu Bayinta mata biyu ta buga musu tsawa tana nuna musu ɗakin, jikinsu banda rawa babu abin da yake yi, haka suka ɗafa labulen ɗakin suka fara tozali da wannan tururuwar don ta yanzu har ta fi ta lokacin da Jakadiya ta shi ga rawa. Fulani Fahima dakatar da su sannan ta umarci da ɗauko fiya-fiya. Tana nan tsaye suka dawo da fiya-fiyan ta karɓa ta fara yarfawa, Maryo ce ta ɗago da hannunta wanda Furzaan ya taɓa saka mata zobe ta fara girgizawa alamar a'a. Da sauri duk suka ja ba Fulani Faliha saki kwalbar kalanzir ɗin ta faɗi ƙasa, a zabure Maryo ta ɗago da kai idanunta a rufe hanci da bakinta na ɗigar da Jini cikin ƙaraji ta ce, "Na gaya muku ku bari." Kalanzir ɗin na fara taɓa Tururuwar ta fara tashi sama kamar fari tana yo wa kan su Fulani Fahima."

Cikin tashin hankali suka fice daga ɗakin a fice, kafin futarsu Wata turuwa ta maƙalewa Fulani Fahima a ƙafa, fara kuka ta yi saboda azaba Bayinta tuni suka fice a guje Jakadiya ta faɗa Turakar Sarki Abdallah ba tare da ta sani ba. Da ƙyar Fulani Fahima ta fisge Turuwar ta ɗauki kujera ƴar tsugunno ta makawa Tururuwar amma wani abun mamaki sai ji ta yi kamar ta makawa Dutse, Kamar mutum haka Tururuwar ta juya tana kallonta sannan ta koma ɗakin ta Maryo take.

Fulani Fahima ɗingisawa ta yi ta fice daga sashen tana fita harabar gidan babu kowa sai wani Dogari, aikensa ta yi wurin Sarki Abdallah ta sanar da shi ya gaya masa duk abin da yake faruwa. Lokacin da saƙon ya isa kunnen Sarki Abdallah da sauri ya fito ya nufo sashen yana tafe Me babban ɗaki da Maleek na biye da shi, ganin Sarki Abdallah kamar baya saurin da ya kamata ya sa yasa Maleek zubawa a guje ya shige ciki.

Maleek na shiga be tsaya tambaya ba ya faɗa ɗakin, kwance ya samu Maryo kamar gawa babu alamar

Please Login or Register in order to submit comment