Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba za ka iya ɗiba daga gare ni ba. A wannan karon na yi alƙwarin duk wanda ya yi niyyar katange ni da ita na rantse da Allah sai na datse numfashinsa." Kamar wanda aka jefo daga sama haka ya faɗo musu ɗakin yana haki tamkar wanda ya wuni ya kwana yana tseren gudu. Fuskarsa a murtuke take babu ɗigon fara'a ya kalli Saif yana jin wata irin tsanarsa na mamaye masa zuciyarsa, sai da ya haɗiyi yawu me ɗaci sannan ya dube shi yana nuna shi da ɗan yatsa yana cewa, "A wannan karon ka kaini maƙurar bango amma zan nuna bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane, kuma ko Kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtaccen karen farauta. Na tabbata wannan karon idan aka ce ka dube ta da kallon rahama sai ka faɗi ka suma saboda irin izayar da zan wanzar maka..." A hassale Maryo ta katse shi da faɗin, "Ganin gida yake sa kare zagin Kura amma ba a daji ba. Kada ka manta kowa ya aikata son ransa zai ga ba daidai ba. Amma kuma zan ƙara tunatar da kai ko cikin tumaki rago ke zuwa fada. Ka yi yaƙi da dukkan jarumtarka ba da kaifin tsafi ba, idan baka manta ba a baya ina gaya maka kai ba me sa'a bane kuma ba za ka taɓa zama me sa'a ba." Wani malalacin murmushi Salman ya saki yace, "Zan rangwanta masa albarkacin soyayyar da kike yi masa, saboda azabtar da masoyi a gaban masoyi yana da matuƙar ciwo. Amma na yi rantsuwa na ƙara sai na nusar da ku Abubuwa da yawa suna ɓata a fada ba sai Takalmi ba." Maryo za ta sake magana Saif ya ɗaga mata hannu nan take idonta ya ciko da ƙwalla ta ce, "Don Allah a wannan karon karka dakatar da ni, ka fi kowa sanin wanene shi bana son ya ƙara nasara akanmu."Cikin sigar lallashi Saif ya dube ta ya sa hannu yana goge mata zirin hawayen da ya zubo mata sannan yace, "Wuƙar fiɗar giwa ba girma gare ta ba sai dai kaifi. Alƙawari na ɗaukarwa kaina duk rintsi ba zan bar me shirin yi mini iyaka da ke ba. Ki kwantar da hankalinki hargagin damusa baya firgita Namijin Zaki. Kamar baki san shi da hargagi ba ban son ki sawa kanki damuwa kin ji." Maryo gyaɗa masa kai ta yi tana watsawa Salman harara. Maleek da Inna Habi zama suka yi kamar mutum mutimi suna kallon ikon Allah, don yawancin wannan zaurancen nasu ba fahimta suke ba. Salman ne ya taka gaban Saif yana gyaɗa kai kamar na ƙadangare yace, "Wuya makarantar kare haka zalika wuya ita ke sa gawa sakin tusa. Amma ka sani alamar rago tana ga ɗaurin bante don haka idan kere na yawo zabo na yawo watarana za su haɗu." Yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin yana huci zuciyarsa na ƙuna. Bayan fitarsa babu jimawa Saif ya mara masa baya kowa ya yi hanyar gidansa.

Sai a lokacin Maryo ta ɗan sha jinin jikinta yadda ta ga Inna Habi ta yi laƙwas tana binta da kallo. Abu ce ta faɗo mata a rai da sauri ta kalli Inna Habi ta ce, "Inna ina Abu take?" Ras gaban Inna Habi ta buga saboda kullin da wannan tunanin take kwana tana tashi, babban damuwarta ace idan Maryo ta samu lafiya ta wace sigar za ta fara sanar mata da mijin da ƴar uwarta take aure. Jin ta yi shiru ya sa Maryo ta ƙara cewa, "Ba dai har yanzu tana sashen Fulani Zaliha ba?" Jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da gishiri ta ce, "Kin san fa ƴar uwarki ta yi aure tana gidan mijinta." Wani uban tsalle Maryo ta buga ta ɗane Inna Habi tana faɗin, "Don Allah Inna? Ina ne gidanta a rakani?" Maleek kallonta yake cikin birgewa yana mamakin wannan baiwa da ikon Allah, abu ɗaya zai rabata da Shukransa ita wannan ya lura tana da hatsaniya saɓanin Shukra da ko hira bata cika yi da mutane ba. Inna Habi ta yi mata hararar wasa ta ce, "Tun ba ki gama warware ba yau-yau fa kika samu lafiya, babu inda za ki sai kin ƙara warwarewa."

Ɗan turo baki gaba ta yi ta ce, "Don Allah Inna ki sa a raka ni na kwana biyu ban ganta ba." Maleek ne ya yi gyaran murya yace, "Maryo babu magana kuma?" Kunya ce ta kama ta don sun haɗa ido da shi ya fi a ƙirga amma da yake a cikin shauƙi take ba su gaisa ba, a ɗan kunyace ta ce, "Ina Wuni!" Gyara tsayuwa ya yi, sai da zuba hannu a aljihu yace, "Lafiya ƙalau ya jikin" Ta bashi amsa, "Da sauƙi." ya mayar da akalar kallonsa ga Inna Habi yace, "To Allah ƙara sauki Inna ni zan wuce sai an kwana biyu." Ina ta ce, "Har tafiya Audulmaleek? To a gaida gida Allah ya tsare a gaishe da Fulani da Mai Babban ɗaki." Ya amsa mata tare ta yin gaba, zunguro Maryo ta yi a hankali tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Maza rakashi ko bakin ƙofa ne." Maryo ta yi gaba taba tura baki gaba ba don ta so hakan ba. Suna zuwa bakin ƙofa a gurguwa ta yi masa sallama ta dawo wurin Inna Habi.

Waiwaye...

Rayzuta ta taso cikin kulawa da soyayyar iyaye gaba da baya, tun bayan haihuwarta da wata uku Mahaifiyarta ta fara ciwo sama-sama. Tun ana ganin abin da wasa har lamarin ya fara ba su tsoro, saboda yanzu riƙon Rayzuta ya dawo hannun Farratu da zama, ba ƙaramin tausayin yarinyar take ji ba musamman ga ƙarancin watanninta ace Mahaifiyarta babu lafiya. Haka daga wurin Mahaifinta hankalinsa ba ƙaramin ta shi ya yi ba. Lokaci ɗaya labarin rashin lafiyar Wurshil Ba'is ya karaɗe cikin wannan Daula ta masarauta me ɗauke da ɗubin Aljanun a ciki. Ba a ɗauki lokaci ba aka fantsama neman magani cikin da wajen wannan nahiya. Koyaushe a cikin haɗa mata magani ake amma kullin ciwonta kamar ƙara gaba yake yi. Sarki Kisumul Birmi tun yana sa ran warkewarta har ya fara sare wa sakamakon yadda jikin nata yake ƙara rikicewa. Farratu ita take jinyar Wurshil Ba'is domin ta ce babu wanda za ta lamuncewa ya yi jinyarta, saboda jikinta yana bata akwai lauje cikin naɗi dangane da ciwon kishiyar tata. Wannan haɗin kai na Matan Sarki Kismul Birmi ba ƙaramin daɗi yake yi masa ba, a ɓangare ɗaya yana ƙara jin ƙaunar Uwar gidansa na ƙara mamaye zuciyarsa, yana jinjina karamci da kyawun hali irin nata. Burdamu Ita ce Mahaifiyar Furzaan, amintakar mazajensu ya sa ta su ta zo ɗaya da Farratu suka ɗinke saboda kusan halinsu ɗaya, wannan ta sa zumuncin su ya ci gaba da tafiya gwanin birgewa. Furzaan da Zulik tun suna yara suka taso da abotarsu sai dai bambamcin ɗabi'u da halaye da suke da shi tun suna ƙanana.

Furzaan Yarone me nutsuwa ladabi da biyayya Uwa Uba girmama na gaba da shi, yana da saurin fahimtar abu. Yana da barkwanci sosai ta jin tausayin Mahaifiyarsa da ma sauran duk wani me buƙatar taimako. Saɓanin Zulik da ya ta so da haɗama, handama da babakere. Tun be yi wayon ba yake da hangen abin da wani yake da shi, sai dai da ya ɗora ido akanka muddin ya ga ka zarta shi da wani matsayi zai kawo hassada, ƙyashi da baƙin ciki ya ɗora akanka. Duk waɗannan ɗabi'u na Zulik Furzaan ya fahimce su saboda yana da saurin karantar yanayin da ƴan uwansa Jinsin Aljanu suke ciki. Don haka tun suna ƙanana kowa ya san halin kowa a cikinsu, saboda haka Furzaan yake cin maganin zama da Zulik don a zauna lafiya.

Lokacin da Rayzuta ta kai shekara biyar a duniya lokacin ne ciwon Mahaifiyarta ya warke wato a ranar ne ta koma ga mahalicci, Farratu ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita. Sarki Kismul Birmi sai shi ya dinga lallashinta yana bata haƙuri. Shiru ta yi ta faɗa duniyar tunanin irin wasiyar da Wurshil Ba'is ta bar mata a lokacin da take gabda da mutuwarta.

(Bari mu taɓo yarensu🤪)

"Jaskinbat minfartif basu kutminba Farratu banakul ginsatu lalbisfahu warga su minzanu kalmunsiban hurumi Rayzuta minzat falsibuhu zadigul basfu walkin."

(Haƙiƙa ke ta daban ce Farratu ban taɓa jin kishiya me karamci kamar ki ba ko a tarihi, Allah ya yi ni ba me yawancin kwana bace don haka ga amanar Rayzuta nan ki riƙe kamar ƴarki ta cikinki.)

Kuka ne ya kwacewa Farratu tana jin maganganun Wurshil Ba'is har cikin zuciyarta, share hawayenta ta yi ta ce, "Ki daina faɗin haka cuta ba mutuwa ba sai kwana ya ƙare." Murmushi Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "Wannan karon ciwon haɗe yake da ƙarar kwana. Dama Kakana ya taɓa gaya mini tun ina budurwa cewa ƙaddarata za ta kawo ni Masarautar Jinnul Sahara, ya sanar da ni komai amma ba zan iya sanar da ku ba saboda gudun tayar da tarzoma, amma abu ɗaya zan sanar miki da shi akan Rayzuta ba don tana matsayim ƴata ba, ina baki shawara ne dangen da goben Ƴar Rayzuta. Don Allah idan yadda kina ɗauke ni har zuciyarki haka nake kada ki Aurawa ɗaya daga cikin zuri'ar Bulbutu, idan kuka yi wannan kuskuren na tabbata ƙasƙantattun Bayin cikin masarautar nan sai sun fi ku ƴanci a cikin Masarautar nan." Farratu ta kalli Wurshil Ba'is da mamaki ta ce, "Me zai haɗa zuri'ar Sarki Kisumul Birmi da zuri'ar Bawa Bulbutu, karki manta Rayzuta jinin sarauta ce su kuwa dangin Bayi ne." Murmushin yake Wurshil Ba'is ta yi ta ce, "A kwana a tashi ko bayan babu raina za ki tuna da wannan maganar. Ki sanarwa da Sarki wannan huɗubar tawa na tabbata ba zai watsa miki ƙasa a ido ba. Idan kika cire wannan zuri'ar na yarje duk wanda Rayzuta ta nuna tana so matsawar ba shi da wani aibu ku aura mata shi. Amma ina fargabar abin da Kakana Bundur ya sanar da ni dangane rubtacciyar ƙaddararta, wataƙila yin hakan ya dakatar da tasirin ƙaddararta sai dai..." Bata ƙarasa maganar ba numfashinta ya ɗauke nan take rai ya yi halinsa.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya Rayzuta na hannun Farratu tana bata kulawa tamkar ita ta haifeta har Rayzuta ta fara zama budurwa, a wannan lokacin duk wasu al'amuran da ya shafi harkar Mulki Mahaifinta yana koya mata. Rayzuta nutsatssiyar yarinya ce sai dai ta taso da farin jinin duk kuwa da yadda Mahaifinta ya yi farin jini lokacin da yana matashi ta dame shi ta wannan fannin. Wata irin shaƙuwace ta shiga tsakaninta da Furzaan, a fannin iyayensu hakan ba ƙaramin daɗi ya yi musu ba. Ga wanda ya fahimci wannan alaƙa tasu zai fahimci shaƙuwar ta su ta rikiɗe zuwa soyayya. Zulik tun da Allah ya sa ya zama saurayi ya ji duk duniya babu yarinyar da yake ƙauna sama da ita. Babban burinsa ya ga an aura masa ita ya mori gangar jikinta, saboda Allah ya yi mata kyakkyawar sura cikin jinsinsu na Aljanu. Ganin hankalinta ya fi karkata ga Furzaan ya sa ya fara neman cusa soyayyarsa ƙarfi da yaji a zuciyar Rayzuta, wanda a lokacin har saɓani suka fara samu tsakaninsa da ita, don har sawa take Dogarawan ƙofa su dakatar da shi. Watarana yana zaune Mahaifinsa ya same shi a ɗaki ya ƙarewa Zulik kallo duk ya rame ya fara lalacewa, dama kuma ya daɗe da fahimtar halin da Ɗan nasa yake ciki kuma hakan ba ƙaramin daɗi ya yi masa ba. Zama ya yi a kusa da shi ya ambaci sunansa cikin wata irin murya da take tabbatar masa Mahaifin nasa yana son yin magana me muhimmanci da shi.

"Zulik na fahimci ka faɗa tarkon soyayyar Rayzuta ƴar Sarki Kisumul Barmi, amma ka sani soyayya da ita kamar dawo da wanda ya mutu ne. Na san za ka yi mamakin jin haka daga gare ni kuma wannan ba abin mamakii bane idan ka duba matsayinka da nata." Bulbutu ya dakata da maganar yana kallon yanayin da Zulik ya shiga, cikin rashin ladabi Zulik yace, "Wacece Mahaifiyata? Ka fara sanar da ni wannan in yaso duk wani bayani sai ya biyo baya." Murmushi Bulbutu ya yi yace, "Mahaifiyarka ta rasu tun bayan da ta haife ka, Mahaifiyarka ita ce Mahaifiyata. Na hallaka mijinta wato Mahaifina sannan na haike mata a wannan tarraya ta mu da ita ta samu cikinka. Ka san dalilina na yin haka?" Zulik ya dube shi da kallon tsana ya girgiza masa kai sannan Bulbutu ya ci gaba da cewa, "Laƙani aka bani na yi amfani da shi domin kasancewata Sarkin gobe a wannan masarautar. Boka na ya sanar da ni cewar matsawar na yi tarayya da Mahaifiyata za ta haifi wanda zai auri ƴar Sarki Kisumul Birmi, amma indai ban yi tarayya da ita ba har abada ni da Saruta. Bincikensa ya nuna idan muka bi da dabaru tabbas za ka aureta kuma kana aurenta Mahaifinta zai baka Sarautar ka ga sai yadda muka yi da su. Sai dai ya sanar da ni wannan yaro Ɗan wurin Waziri zai kawo maka cikas, don haka ba da gaggawa za mu bi lamarin ba. Ka yi ƙoƙari ka daina nuna jin zafinka akan Furzaan za ka ga ta fara sauraronka, kuma a yadda na lura yarinyar tana da sha'awar harbe-harbe. Don haka zan turaka horon harbi na kwari da baka in ya so idan ka dawo sai mu yaudari Sarki akan za ka dinga koya mata Harbi, a wannan lokacin za ka cusa mata soyayyarka. Kaga kana aurenta ka zama Sarki me mulkar wannan Nahiyar ta Daulatul Jinnul Sahara." Duk yadda Zulik ya kai ga jin haushin Mahaifinsa sai ya ji zuciyarsa fes baƙin cikin da ke ciki ya yaye. Kallon Mahaifin nasa ya yi yace, "A farkon labarin ji nake zuciyata na tafasa kamar na datse numfashinka, amma daga ƙarshen labarin na hango nasara da cimma buri a ciki." Daɗi Bulbutu ya ji a ranar ya shiryawa Zulik tafiya ba tare da kowa ya sani ba, ya aikata cen Nahiyar Baƙaƙe Aljanin ƙarƙashin ƙasa. (JINNUL TARABIY) Domin amsar horon Harbi yadda ya kamata.


Duk yadda Maryo ta so a raka gidan Abu Inna Habi ta ƙi yadda, a gefe ɗaya kuma tana fargabar rikicin da ka je ya zo. Suna zaune su biyu a ɗaki Inna Habi ta dubi Maryo tana cewa, "Maryo babu abin da za mu ce da Allah sai godiya. Cikin ikon Allah kina gani lokaci ɗaya idanunki da kunnuwanki sun buɗe, an ya lamarin nan babu sihiri a ciki kuwa. Ni fa ina ji a jikina tabbas akwai wani ɓoyayyen al'amari a ƙasa, amma meye haɗinki da Ɗan wurin Fulani Maryama? Sannan kuma me ya sa kika sakewa Namiji har yake iya rungumarki ke ba matarsa ba? Maryo na yi mamakin ganin haka saboda sam ban yi muku tarbiyyar son zuciya ba. Me kike tunani ga duk namiji da ya samu damar taɓa wani sashe na jikinki? Kina tsammanin zai aure ki ne?" Maryo jikinta ne ya yi sanyi ta kalli Inna Habi tana ƙarajin ƙaunar tsohuwar a zuciyarta tana faɗin, "Inna wallahi babu wani abu da yake tsakanina da Ɗanta, shi kuma Saif ba tun yanzu ba na gaya miki saurayina ne. Amma wallahi Inna ina ji a jikina shi ɗin kamar wani tsagina daga ɓangaren jikina, jikina na rayawa mini wasu al'amura musu muhimmanci dangane da rayuwata. Ciwon nan kuma yana daga Ubangiji Inna kar mu saka zargin kowa a zuciyarmu don kar a zoɓe ladan kankarar zununbin dana samu. Game da rungume ni da Saif ya yi na yi kuskure Inna amma duk hukuncin da ya dace za ki iya aiwatarwa a gare ni, na yi miki alƙwari In sha Allah hakan ba za ta sake faruwa a tsakaninmu ba. Amma wallahi ki yadda da ni Inna babu wani abu da ya taɓa haɗa ni da shi wannan ma kuskure ne." Maryo akwai iya falsafar zancen da sauke magana a inda ta dace, idan tana tsara maka magana za ka rantse da Allah wata babbar macece take yi maka magana. Inna Habi ce take mamakin yadda lokaci ɗaya kunyar Maryo ta yaye akan wannan Ɗan Sarki Saif, jiki a sanyaye ta dubi Maryo ta ce, "To ya kamata a kiyaye gaba saboda hakan baya daga tafarkin tsarin addinin musulunci." Maryo ta amsa mata cikin girmamawa, Inna Habi da har za ta tambayi Maryo game da cikin da take iƙirarin na Saif ne sai dai kuma ta fasa.

Sannu a hankali tun Bayin sashen Fulani Maryama ba su san da warkewar Maryo ba, har suka hankalta. Wasu daga cikinsu sun ta ya ta murna ya yinda wasu kuma suke tsoron magana kasancewar sun fahimci Fulani Maryama ta kafa musu ƙahon zuƙa, ko gani ta yi kanfiye mu'amala da Inna Habi sai ta kira ka ta yanka maka kashedi. Lokacin da Fulani Maryama ta samu labarin faruwar wannan lamarin ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, duk yadda ta so ganin Jakadiya a ranar abin ya faskara don Jakadiya na kwance maruru ya fito mata a hammata, tana kwance tana fama da hannu a sama don ko sauke shi ƙasa bata iya yi, saboda azabar da yake yi mata.

Lokacin da Saif ya koma gida Abu na zaune a kan gado ta jingina da fuskar gado da alama baccin ɗaukarta ya yi ba tare da ta sani ba, Saif na shiga ya hangi Baiwa Sahura tana surfe. Ƙare mata kallo ya yi har sai da ta tsargu take ganin kamar ya lura da ta zuba wani abu a ƙofar ɗakin matarsa. Amma sai ta hau muzurai tana faɗin, "Barka da shigowa Ranka shi daɗe." A taƙaice yace, "Barka!" Har ya wuce gaba ya juyo ya sake kallonta yana bin hannuwanta da kallo, wannan karon tsoronta ya bayyana a fili sai ya wuce cikin gida. Tun daga bakin ƙofar ɗakin ya fara bin hallitun da yake gani a fili, kansa ne ya sara masa lokaci ɗaya idanunsa suka rune jawur ya kalle su fuska babu wallahi yana faɗin, "Maza ku koma wurin da aka turo ku muddin kuka saɓa mini wallahi babu wanda zai tsira daga gare ni. Saƙo na baku duk wanda ya ƙara gigin taɓa mini gudan jinina tabbas uwarsa sai dai ta haifi wani." Tun be rufe baki ba ɗaya bayan ɗaya suka fata ɓacewa, Baiwa Sahura da take gefe tana kallonsa yana ta surutai cikin zuciyarta take ayyana ko dai wani zancen zucin yake yi har ya fara fitowa fili. Fuska a tamke ya juyo gare ta jikinta har tsuma yake amma ga mamakinta sa ta ga ya nuna ta da Ɗan yatsa ya bushe da dariya, sai da ya yi me isarsa sannan yace, "Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da za a baki mugun abu domin salwantar da abin da yake cikin Matata, idan ba haka ba wallahi zan baki mamaki. Kuma karna ƙara ganin ƙafarki a sashen nan." Baiwa Sahura ban da gyaɗa kai babu abin da take yi jikinta har rawa yake ta ci gaba da abin da take yi, Saif ya faɗa ɗaki ya kwanta a kan gado ya tsunduma kogin tunanin rayuwar abin da yake faruwa da shi. Sai a wannan lokacin ya tuna cewar Maryo ƴar Uwar Abu ce ji ya yi kansa ya yi wani iri. Ɗagowa ya yi ya ga yadda take bacci a wahalce, ta shi ya yi ya ƙarasa yana gyara mata kwanciya cikin tausayawa domin kwana biui kawai duk ta zabge ta rame.

Bayan kwana biyu da warkewar Maryo ta gama tabbatarwa kanta dai suna zaune ne a sashen Fulani Maryama, ko kaɗan ba ta so hakan ba saboda gabaɗaya ta tsani matar don tun da take bata taɓa jin wani mutum da ta tsane shi farat ɗaya ba kamar Fulani maryama. Kamar kullin yauma ta saka Inna Habi da magiyar zuwa gidan Abu amma sai hanya-hanya Inna Habi take yi mata, babu yadda ta iya haka ta haƙura. Misalin sha biyun rana Inna Habi ta kwanta tana jan carbi har bacci ya yi awon gaba da ita. Hamdala Maryo ta yi don haka ta ja ɗauko mayafinta a hankali ta fito harabar gidan. Baiwa Sahura ta ga ni da sauri ta ƙarasa wurinta tana ƙasa-ƙasa da murya ta ce, "Sahura don Allah ina ne gidan Yayata Abu ki raka ni?" Sahura ta gwalo ido waje saboda kashedin da Saif ya yi mata, ganin haka ya sa Maryo ta ce, "Lafiya Sahura?" Sahura ta wanyance da cewa, "Fulani Maryama ce ta sani aiki sai dai in nuna miki gidan ba zan shiga ciki ba kar na daɗe na yi laifi a wurinta." Hannu bibbiyu Maryo ta sa ta riƙo hannun Sahura ta ce, "Na gode Sahura Mu je."

Sahura tana gaba Maryo na biye da ita har suka ƙarasa ƙofar gidan su Abu, daga bakin ƙofa ta tsaya Maryo ta shiga tana rafka sallama. Tana shiga tsakar gidan haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa amma sai ta yi tsammanin ko dan ta kwana biyu ba ta yi tozali da ƴar uwar tata bane. Bayin Abu ne suka amsa mata nan take tambayarsu Abu suka nuna mata ɗaki kasancewar duk sun san Maryo ƴar uwar Abu ce ya sa basu tsaya yi mata iso ba. Maryo sai da ta yi sallama a bakin ƙofa sannan ta ji Abu ta amsa mata sama-sama, ɗaga labulen ta yi ta shiga a zaune ta hangi Abu akan filo da turtsetsen cikinta. Jin yadda Abu ta amsa mata ya sa Maryo ta ɗauka ko don bata gane ta ba, amma lokacin da ta shiga da murnar ta ƙarasa gaban ƴar uwarta tana faɗin, "Abu kece haka yeeehh na kusa Ɗaukan Ɗana na kaina." Maryo har da ɗan tsallenta kamar wata ƙaramar yarinya, Abu dukda tana jin haushin Maryo a ƙasan zuciyarta ba ƙaramin daɗin ganin Maryo ta ji ba, sai dai kishin mijinta da take ji akan Maryo ya hanata amsarta hannu bibbiyu. Ɗauke kai gefe ta yi ta ce, "Maryo ke ce?" Maryo zama ta yi a sanyaye tana mamakin sauyin halin ƴar Uwarta don ta yi tunanin za ta yi farinciki da ganinta, basarwa Maryo ta yi ta ce, "Abu ya jikin ya Yayan namu?" Ras gaban Abu ya buga wani haushi ya sake turniƙe ta, sai da ta furzar da iska me zafi ta ce, "Duk muna lafiya." Maryo ta jinjina kai da yanayin mamaki ta ce, "Abu hala cikin nan yana takura miki ko bakya jin daɗi ne?" Abu ta watsawa Maryo wani Kallo tana shafa cikin jikinta ta ce, "Cikin da Masoyina ya yi mini har zan ce yana takura mini, sai kace wacce aka yi wa dole." Wannan karon mamakin Maryo be ɓoyi ba a hankali ta miƙe jiki ba ƙwari ta ce, "Abu ni bari na wuce gida Inna ba ta san na fito ba." Abu tana daga zaune ta ce, "Ki gaishe su." Maryo ta amsa tana ɗaga labulen za ta fita suka kusa gware da Saif hannunsa ɗauke da ledar kwakwar manjar da Abu ta ce masa tana buƙata, be lura da ita ba saboda da sauri Maryo ta yi baya tana faɗin, "Subhanallah ashe da mutum a hanya." Muryarta ce ta karaɗe dodon kunnensa da sauri ya saki ledar hannunsa bakinsa na rawa yace, "Ke... ke ce?" Mamakinta ƙarara ya bayyana ta ce, "Me ka zo yi gidan Abu." Abu da ke cen gefe ta yunƙura da ƙyar ta miƙe tsaye ta ce, "Kamar ya me ya zo yi mutum da gidansa, Maryo ko baki san Wannan ne Mijina ba." A hargitse Saif ya buga mata tsawa yana faɗin, "Lafiyarki Abu?" Kafin Abu ta yi wani yunƙuri Maryo da take jin jiri-jiri na nema ɗibanta ta ce, "Wai abin da ta faɗa haka ne kaine Mijinta?" Saif ya sunkuyar da kai ƙasa Abu da gayya ta ce, "Maryo na taɓa yi miki irim wannan wasan ne, idan ba ni ce matarsa ba kin san

Please Login or Register in order to submit comment