Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Subahanallahi Ameena me ya samu idanunki haka naga sunyi ja?". Ɗan sadda kai ƙasa Ameenan tayi, murya aɗan sanyaye tace. "Babu komai Ummi, kawai dai mura ne keta damuna jiya kusan kwana nayi banyi bacci ba, saboda tari da atishawa."
Kai Ummi ta girgiza cikin tausayawa haɗi da kulawa tace.
"Allah sarki, sannu kinsha magani kuwa?" Kaita jinjina alaman "Eh" Hayatuddeen ne yace. "Ayya Aunty Ameena sannu ko."
Ɗan murmushi tayi masa tare da jinjina kanta, Saifuddeen kuwa idanu ya zuba mata, yana me mamakin ƙaryar da ta zabga, yanayin yanda yaga fuskarta yasa shi gane cewa kwana tayi batayi bacci ba, shikam yarasa irin kishin Ameena, dan kishine da takeyinsa babu wani dalili. Zaleeha dake tsaye nan kan dinning area, jin cewar Ameenan bata da lafiya ne yasata ɗan ɗago kanta, cikin sakin fuska tace.
"Ummu'n Adeel barka da safiya, ya jikin?" Jin muryan Zaleehan yasa ta ɗago dakai ta kalli inda taji muryar Zaleehan na fitowa, wani irin bugawa kirjinta yayi, take taji wani irin masifaffen kishi ya sake rufeta, musamman ma ganin yanda Zaleehan tayi kyau cikin doguwar rigan jikinta, haushi da takaicin Zaleehan ne suka turnuƙe mata zuciya, gudun kada su Ummi su zargi wani abu, yasa ta ɗan danne zuciyarta, murmushin yaƙe, wanda yafi kuka ciwo ta saki, can ƙasan maƙoshi tace.
"Yauwa barka, jiki Alhmdlh."
Kai Zaleeha ta jinjina cikin sanyin da ta dawo ɗabi'arta tace.
"Masha Allah, Allah Yaƙara sauƙi."
Kasa amsa mata tayi, dan kuwa wani abune yazo yayi mata tsaye acikin rai, jin muryar Zaleehan acikin kunnuwanta yasa taji kaman ta kurma ihu, ƙasa-ƙasa ta watsawa Zaleehan harara, cikin zuciyarta tace.
"Shegen iyayi, koma menene ai duk sanadinki nasamu kaina ahaka, wallahi da ace ina da yanda zanyi Saifuddeen ya daina ganinki acikin gidan nan da nayi, lokacin da bakyanan ai hankali akwance yake, yanzu kuma da dawowarki da shegen farar fuska kaman mayya duk kin wargaza min nitsuwa ta."
Ta ƙare maganar tana me sakarwa Zaleehan harara ƙasa-ƙasa, Zaleehan, ko zataji sanyi aranta.
Ummi kuwa ganin su Zaleehan sun gama shirya break fast ɗinne yasa tace.
"Dukansu su tashi suje suci abinci." Anan kan dinning suka zauna, yauma kamar kullum Zaleeha ne tayi seving ɗinsu, inda take komai nata acikin nutsuwa. Saifuddeen kuwa gaba ɗaya yau yakasa ɗauke idanunsa akan matan nasa Zaleeha'n, tayi matuƙar kyau, ga fresh skin ɗinta dake ta shinning,
Ameena kuwa tausayinta yakeji da yanada hali da ya yaye mata wannan kishin ta huta, ahankali yake tauna abincin bakinsa, yana wani irin lumshe ido, sosai yakejin daɗin abincin Zaleeha'n, dan zai iya cewa agidan bayan Umminsa babu wanda yakai Zaleeha iya girki duk da yasan Ameena ma ba tayar bayaba bace. Ameena kuwa gaba ɗaya ko daɗin abincin ma bataji abakinta, cuccusawa kawai take, komai bayayi mata daɗi, saboda zafin kishin da ta sawa kanta, ɗan ɗagowa tayi ta kalli gefen Saifuddeen, dan tun da suka zauna bata ɗago kai ta kalleshi ba, kasancewar har yanzu fushi take dashi. Ganin yanda yake sakin murmushi da kuma yanda ya ke kallon Zaleeha wanda take tauna abincin bakinta cikin nutsuwa, yasa taji gaba ɗaya ranta ya ɓaci, wani irin maƙaƙi ne ya zo maƙoshinta, hakan yasa batasan lokacin da ta ƙware ba, take kuwa tasoma tari, kumburarrun idanunta suka kaɗa sukayi ja.
Hankalin Ummi a tashe tace. "Subahanallahi Ameena tarin ne?".
Kai ta jinjina alaman "Eh." tana me riƙe ƙirjinta dake mata zafi. Saifuddeen kuwa hannunsa yasa yana ɗan bubbuga bayanta cikin kulawa.
Zaleeha da Raleeya kuwa atare suka haɗa baki wajen cewa. "Sannu."
kasa amsa musu tayi saboda matsanancin kishi da kuma ɓacin ran dake cinta, Hayatuddeen cikin kulawa yace.
"Ayya Aunty Ameena sannu, kisha ruwa kinji." Yafaɗi maganar yana me miƙo mata goran ruwan faro me sanyi. Babu musu ta amsa tasha, saida tasha sosai kafun take kifa kanta ajikin dinning ɗin tana meda numfashi. Ahankali Saifuddeen ya aje spoon ɗin dake hannunsa, tare da ɗanjan kujeransa baya, ƙoƙarin barin dinning area ɗin yake, Ummi tace.
"Inakuma zaka ana tsaka dacin abinci?" Ɗan shagwaɓe fuska yayi, tare da sanya hannu ya shafi lafaffen cikinsa alaman ya ƙoshine. Kai kawai Ummi ta girgiza tare da maida hankali ta cigaba da cin abincinta, shikuwa Saifuddeen kai tsaye yafice daga cikin falon. Koda ya fita compound ɗin gidan, nan inda motar Ameena take ya nufa, yana zuwa kuwa yayi sa'a batayi locked motar ba, buɗe murfin motar yayi yashiga, anan ɓangaren me zaman banza ya zauna, tare da jawo ƙofar motar ya rufe. Ameena kuwa jin ta soma dawowa cikin hayyacinta, yasa ta miƙewa tsam, dan batajin za'a iya ƙare cin abincin da ita, tsayuwarta awajen kuwa dai-dai yake da hawan jini ya kamata. Ummi tayiwa saita dawo, tare da ɗansa hannu taja kumatun Adeel dake jikin Ummi'n, dan idan za'aci abinci kullum Ummin ne ke karɓan Adeel ɗin ta ɗaurasa acinyarta. Adawo lafiya Ummi tayi mata, haka ma su Zaleeha, al'barkacin Ummi yasa ta amsa musu fuska asake, jakarta ta ɗauka sannan ta fice daga cikin falon, sukuwa ci gaba sukayi da cin abincinsu. Haka ta fito compound ɗin gidan sam fuskarta babu alaman walwala, kaitsaye wajen motarta ta nufa, tana zuwa kuwa ta buɗe tashiga, ƙoƙarin ajiye jakar hannunta takeyi, idanunta ne suka sauƙa akan Saifuddeen wanda ya zuba mata kyawawan idanunsa, wanda ke masifar tafiya da duk wani tunaninta. Sosai ta ɗan tsorata da ganinsa, amma tunawa cewar fushi takeyi dashi yasa ta shiga ta dake tare da kawar da kanta gefe, can ƙasan maƙoshinta tace.
"Lafiya?." Gane abun da tace yasashi girgiza kansa, kana ya gyara zamanshi da kyau yadda zasu fuskanci juna, dubanta yayi da kyau cikin body language dinsa yace. "Wannan itace sabuwar gaisuwar da kika koyo?." Sake haɗe fuska tayi, tare da ɗaura hannunta akan steering motar, ganinsa akusa da ita, da kuma tunowa da irin kallon da yake jifan Zaleehan ɗazu, da tayi yasa taji gaba ɗaya ma haushinsa takeji. Ganin haka yasashi ɗan lumshe idanunsa tare da kamo hannunta ya rumtseshi cikin nashi hannayen, sam baisan menene damuwar mata ba, akan Ameena kuwa bayaso ace ya sani, kwata-kwata baya ƙaunar abun da zai kawo masa matsala arayuwarsa, tabbas ya fahimci cewa tunanin Ameena ƙaramine, dole saiya nusar da ita kuma ya bita a hankali yasan zata gane zata kuma fahimceshi.
gyara zamansa yayi akasalance cikin body language ɗinsa yace. "Azamana dake ina iya ƙoƙarina wajen ganin na sauƙe haƙƙin ki dake kaina, bansani ba Ameena, bansan mekikewa fushi ba, bansan me namiki ba, ban kuma san dalilin dayasa kika ɗauki kishi da zafi har haka ba, azamana dake bana cutar dake, ba kuma na musguna miki, kinsani na sani Zaleeha matatace kamar yanda kema kike matata, to menene aibuna dan nashiga wajenta na jima? kada ki manta ba haƙƙinki na ɗauka na kai mata ba, saboda ba ranan girkin ki bane nata ne, ashe kenan banyi haka dan na cutar dake ba, meyasa dole kikeson sawa rai da zuciyarki damuwa? ko kusa banason Ummi ta zargeni da rashin yi muku adalci ku biyun, bana kuma fatan ranan da zanyi rashin adalci atsakanin ku, amma saidai naga kaman haƙurin ki naneman gazawa, akullum ƙoƙarin bayyanar da kishinki afili kike, meyasa Ameena? meyasa bazaki daure zuciyarki ba? tunjiya kike fushi dani batare da wani dalili ba, me nayi miki? faɗamin ina jinki laifin me nayi miki?. " Gaba ɗaya jikinta ne yayi sanyi, hakan yasa ta sadda kanta ƙasa, lokaci guda kuwa saiga hawaye sun kwaranyo daga cikin idanunta, tabbas ita kanta tasani fushin da takeyi dashi bashi da dalili, saboda ba laifi yayi mata ba, bai kyareta ba, bai kuma zageta ba, babu abun da yayi mata asalima ya ninka kulawarshi a kanta ne ita kanta tasan baya son damuwarta, kawai dai zallan kishi ne ke ɗawainiya da ita, har yasa take ganin kaman yayi mata rashin adalci. Ɗago kanta tayi da idanunta wanda sukayi luhu luhu, cikin sanyin murya irin ta rashin gaskiya tace.
"Kayi haƙuri, nima bansan me yasa nakejin hakan ba."
Ta ƙarashi mgnar tare da manna kanta a ƙirjinshi. Idanunsa yaɗan lumshe tare da cije laɓɓansa, asanyaye cikin body language yace. "Banason irin wannan halin, ina dalilin ta kura kanki da kikayi? kinsa kanki cikin ƙunci, sannan kin kwana kuka, kin tashi kuma kina fushi dani, bayan ban tauye ɗaya daga cikin haƙƙoƙinki dake kaina ba, banason Ummi tafara tunanin cewa ina tauye miki haƙƙi, idan wani abu nayi miki ki faɗamin, kinsa kanki aɗaki kin kwana kuka, saboda kina yarda da abun da zuciyarki da shaiɗan ke raya miki, sannan sun tambayeki kince musu mura ne ke damunki, su mahaukata ne da bazasu gane cewar kuka kikayi ba, ki dubi fuskarki, ki dubi yanda idanunki suka bayyana alamun kuka, meyasa ba zaki nutsu ki maida hankalin ki ba? Meyasa kike haka?". Hawayen da suka zubo daga cikin idanunta ta sharce, murya na rawa tace.
"Dan Allah kayi haƙuri."
Kansa yaɗan jinjina mata alaman yaji, sannan kuma ta kiyaye, dan abun da tayi ɗin ya sosa ransa, bai kamata ace tana fushi batare da ƙwaƙƙwaran dalili ba, Allah Ma yasani yana iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin bai tauye mata haƙƙinta ba.
Buɗe murfin motar yayi ya fice, kaitsaye part ɗinsa ya nufa, dan yanaso yaje yaɗan huta. Itakuwa Ameena gaba ɗaya jikinta amace yake, dan tasan bata da gaskiya, gefe guda kuwa ga wani irin soyayyarsa dake ratsa ta, ita har ga Allah tasan Zaleeha batayi mata komaiba kuma itama bawai tsanar Zaleeha takeyi ba, sai dai tana jin kishinta, haka tayiwa motar key, asanyaye ta fice daga cikin gida. Ta tafi tasan in taje wurin aiki ƙawarta Samira zata ƙara kwantar mata da hankali, ita kanta tasan Samira ƙawace ta gari.

Acan falon Ummi kuwa cikin nutsuwa suka kammala break fast ɗin, Zaleeha da Raleeya ne suka kimtsa dinning area'n, inda Raleeya ta zuba kwanukan da suka ɓata acikin injin wanke wanke, nan falon Ummi suka zauna suna ɗan taɓa hira. Ganin lokaci na ɗan jane, yasa suka sake komawa kitchine ɗin, lunch suka ɗaura, basu wani yi girki me wahala ba, hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka kammala, Raleeya ne ta haye sama dan agajiye take jinta sosai, itama Zaleeha part ɗinta ta nufa, Adeel ɗauke akan kafaɗanta, koda ta isa ɗakinta, akan gado ta aje Adeel ɗin sannan ta jefa masa ɗan ƙaramin pillow dan yayi wasa dashi, kayan jikinta ta rage, sannan ta shiga wanka, koda ta fito wata ƴar riga marar nauyi tasanya, sannan ta haye saman gadon, jawo Adeel jikinta tayi tare da ɗaurasa akan cikinta, ahankali take shafa bayansa, ahaka har bacci ya ɗaukesu. Ahankali yaɗan buɗe idanunsa, wanda suka ɗanyi ja, saboda baccin da yayi, wayarsa dake ɗaure kan bedside ya ɗauka, ganin ƙarfe 12:15 pm yasashi tashi zaune, wheelchair ɗinsa ya jawo tare da hawa kai, kaitsaye toilet ya wuce, wanka yayi ya fito sanye da rigar wanka ajikinsa, ɗan ƙaramin towel ne ahannunsa, yana tsane gashin kansa, koda ya kammala body lotion me daɗin ƙamshi ya shafa ajikinsa, wasu riga da wandon shadda na getzner ya sanya wanda sukai masa masifar kyau, tsab yagama shirya kansa tare da fesa turare, wayarsa da kuma laptop ɗinsa ya ɗauka sannan ya fice daga cikin ɗakin.
Kaitsaye part ɗin Ummi ya nufa.
Babu kowa a falon Ummin, ko ina shiru, dan tun 11 Hayatuddeen ya tafi school, Raleeya da Ummi kuwa kowa na ɗakinsa.
A falon ya ɗan tsaya jim ya ɗanyi dan yasan a irin wannan lokacin Ummi ma bacci takeyi,
A hankali ya juya ya fita, a harabar gidan ya ɗan tsaya kamar zai wuce wurinsu Sule sai kuma ya juya ya nufi side ɗinshi da matanshi ƙofar falon Zaleeha ya buɗe ya shiga a hankali yake sarrafa keken nashi, shiru falon nata sai sautin AC da kuma karatun ƙur'an da ta saka wanda yake tashi a hankali,
kamar zai juya ya fita kuma sai yaji zuciyarshi nayi mishi jagora zuwa cikin ɗakin nata,
a hankali ya tura ƙofan,
tare da sarrafa kekenshi cikin nitsuwa ya isa tsakiyar ɗakin, ido ya zuba mata ganin yadda take konce ruggume da Adeel,
idonshi ya lumshe tare da fidda sassanyan numfashi, a ranshi yace.
"Uhumm to wannan konciya a bakin gado ai juyi ɗaya zakiyi ki yarmin da yaro ƙasa ki fasa min kanshi."
dan gaba ɗaya ƙarfin konciyar nata a bakin gadon ne, sarrafa kekenshin yayi a hankali ya iso bakin gadon, cikin nitsuwa yasa hannu ya tallafi Adeel tare da ɗauke shi daga kan ƙirjinta,
ya ɗan roggofo da niyar kontar da Adeel ɗin bayanta kenan,
cikin bacci taji kamar yaron zai faɗo ba tare data buɗe ido taɓa tayi maza ta ruggumeshi,
madadin ta ruggumi ɗan sai ta ruggumi uban,
da sauri ya kontar da Adeel daketa bacci sai, ido ya ɗan zaro jin yadda ta ruggumeshi gam a jikinta,
idon ya zuba mata, yana mai maganar zuci.
"Wayyo Allah zata lalata min al'wala".
Ita kuwa Zaleeha cikin baccin ta fahimci wannan ba Adeel ta rugguma ba, da sauri ta buɗe idanunta tare dayi sauri ta sakeshi, ido ta zazzaro kana ta mirgina baya,
da sauri ya riko hannunta ganin zata mirgina kan Adeel,
cikin mayen bacci tace.
"Bacci zanyi".
Ido ya tsura mata tare da jujjuya mata su kana ya mata mgna da yarensu na kurame.
"To na hanaki baccin ne, daga zuwana kin shaƙoni kin ruggume."
Ya ƙare kwatance dayi mata nuni da rugguma,
baki ta ɗan tura tare da cewa.
"Ni ai Adeel nake son rugguma ba kaiba".
Sake hannunta yayi tare da mata alamun.
"Karya kikeyi".
ita dai gefe ta koma ta konta tasa Adeel a gaba,
shi kuwa juyawa yayi ya fita dan baison worwore al'walanshi.

Yana fita ta maida ajiyan zuciya tare da shafa kan Adeel kana sukaci gaba da bacci su.

Shi kuwa suna fita shida Sule kasuwa suka wuce,
Nan ya zazzagaya shagunanshi dan duba hada-hadarsu dan sun kusa suyi zaman lissafin cinikin shekara da ribar da suka shigar da sanin zakkar daya dace su fidda,
Sai da ya gama zagayawa shida Ahmad da Mudassir kana da Warisu.
Sannan ya wuce, ya gaggaida su Alhaji Yawale, Ba miskila, Alhakin Isha, Alhaji kabiru, uban gidansu na dilan leda Alhaji Aliyu, domin baya mance duk matakin da yake ciki a rayuwa sanadin pure water da leda dasu magine ya kai wannan matsayin.

Daga kasuwa ofishin su na Jonapwd ya wuce,
yana shiga ciki ana ƙoƙarin shiga sallan azahar, nan ya shiga jam'i akayi salla.
Bayan an idar ne ya wuce ofishin Ishaq, tare da jagoranci Sani,
cikin yadda suka saba mgna yake mishi bayanin Malam Ishaq yana cikin G.S.U sai dai yanzu zai dawo,
aiko suna nan zaune Ishaq ya shigo,
Murmushi yayi tare dabin gefen table ɗinshi ya matso kusa da kujerar da yasan nan Saifuddeen ke zama hannu ya bashi tare da cewa.
"Ango mai mata biyu, sai yau aka tuno mu?".
Hannunshi Saifuddeen ya kama tare da rubuta mishi,
"Kai Isha banda sharri last week mafa nazo dani akayi mitin".
Murmushi Ishaq yayi lakacin daji saƙon aminin nashi, gyara zama yayi kana yace.
"Eh ai yanzu zuwanka sati-sati ne."
Murmushi sukayi baki ɗaya kana sukaci gaba da hira,
A nanne Saifuddeen ke cewa Ishaq ya kamata fa ya tsaida batun aure duk abokansu sunyi aure sai shida Mudassir suka rage,
a nan Ishaq ke ce mishi su shirya shima nashi nan tafe dan sun gama dai-dai tawa da Rashida ƙawar Zaleeha,
sosai Saifuddeen yaji daɗin haka dan yasan Rashida tanada mutumci da kima,
nan dai sukayi tashan hirarsu ta abokai.

Sai da yamma ya baro wurin Ishaq kana, ya nufi gida.


A gidan kuwa tuni Zaleeha da Raliya sun gama aikin abincin dare.
Amina ma ta dawo wurin aikinta

Duk suna zaune a falon Ummi sunata ɗan taɓa hira.
Duk da Ameena najin zuciyarta babu daɗi dan har yanzu data dawo dataje ɗakinta saida taji ƙamshin turaren Zaleeha a jikin rigar Adeel amman ta danne.

Shi kuwa Saifuddeen kai tsaye side ɗinsu ya wuce ganin magrib ta gabato, ruwa ya ɗan watsa kana ya zura jallabiya ya fito ya nufi masallaci,
Hayatuddeen na biye dashi a baya,
a bakin gate suka samu Ahmad ma nayin al'wala daga nan suka wuce masallaci.
Sune basu dawo gidaba saida akayi sallan isha.

Suna dawowa suka zauna duk sukaci abinci,
daga nan Ahmad ya haura sama dan a matuƙar gajiye yake, in ya ɗanyi bacci kafin Raliya ta gama hiranta ta dawo zaiji dama-dama ya samu raya daren


Hira suke ɗanyi yayinda Zaleeha ke zaune ƙasa kan carpet, tasa Adeel a kan cinya tana yanke mishi farce.

Ameena kuwa ta zuba musu ido,har ranta tasan ba soyayyar ganin ido Zaleeha keyiwa ɗanta ba,
to amman ita ta kasa jin ta dena kishin Zaleeha a ranta, ganin yadda tayi zugum tayi tagumine yasa Ummi ta kalleta cikin kulawa da nitsuwa tace.
"Ameena zo".
Tana faɗin haka ta wuce tayi cikin ɗakin ta.
Cikin sanyi Ameena ta miƙe tabi bayanta,
a bakin gado ta samu Ummi na zaune, cikin yin ƙasa da kai ta ƙaraso cikin ɗakin,inda Ummi ta nuna mata nan ta zauna sunkuyar da kanta tayi a hankali tace.
"Ummi gani".
ido Ummi ta zuba mata sai kuma ta gyara zama cikin kulawa da son gane matsalar Ameena tace.
"Ameena meke damunki?".
A hankali ta jujjuya kai alamun babu.
Cikin kula Ummi tace.
"Kinga Ameena kada kiyi min haka,kinji ni matsayin ƴa na ɗauke ku,muddin kinada matsala ki gaya min, in inada damar yaye miki ita zan yaye miki ita in kuma bani da dama, zan tayaki da addu'a da shawarwari, dan haka gaya min meke damunki yadda bazan so Ahmad ya tozarta Raliya ba bazanso Saifuddeen ya tozar takuba, gaya min me yayi miki,ni nasan na isa dashi".
Cikin rauni da sanyin murya tace.
"Babu abin da yamin Ummi,wlh Hamma bai min komaiba".
cikin gamsuwa Ummi tace to menene matsalarki meke damunki?".
Kai ta ɗan rausayar tare da cewa.
"Ba komai Ummi wlh Hamma bai min komaiba."
Cikin kula Ummi tace.
"To Alhamdulillah dan ni shi na zarga, tunda kuma kince bai miki komaiba, shikenan, amman ki saki ranki ki dena sa damuwa a ranki, bana son ganin kina tagumi kinji ko tashi kije kuyi hiranku da ƴan uwanki".
Cikin jin daɗi da ganin daraja da kimar Ummi da mijinta ta miƙe ta fita tana mai yin mgnar zuciya.
"Ameena ki sassauta wa kanki kishi bayin Allah nan basu rageki da komaiba wacce kikeyi dominta ma bata saniba".
A hankali ta fito falon gefen Zaleeha ta zauna, cikin kula Zaleeha ta kalleta tare da cewa.
"Ummu Adeel bashi yasha nono naga yanata mutsu-mutsu".
Murmushi ta ɗanyi kana ta ɗauke shi ta bashi nono.
Shikuwa Saifuddeen ido ya zuba musu a yadda suke jeren,
hamdala yakeyi da godewa Allah daya azirtashi da matan da ko wacce da nasabarta,
murmushi yayiwa Ameena tare da jinjina mata kai alamun tayi kyau.
kauda idonta tayi dan sai take ga kamar ba'a yayi mata ya za'ayi yace tayi kyau bayan ga Zaleeha kusa da ita bata san cewa kowa da irin sirrin kyanta ba.
ganin yadda ta tsuke fuskane ya sashi jin ba daɗi.
"To wai me nayi mata,ko dai ta daina so nane yasa duk abinda nai mata sai ta juyashi marar daɗi".
Yana cikin mgnar zucin yaga ta miƙawa Zaleeha Adeel ta miƙe ta fita,
da ido ya bita,
Raleya ce ta kalleta cikin kula tace.
"Aunty Ameena har zaki shiga?".
Kai ta gyaɗa mata, jin Hayatuddeen yace.
"To saida safe Aunty Ameena".
Yasa ta ɗan juyo tare da cewa.
"To auta Allah ya bamu al'khairi".
Baki ya tura tare da cewa.
"Wai auta nida har inada yara sai kuyi ta cemin auta yanzu in Adeel ya fara mgna shima ba sai yabi bakinku yace min autanba".
Murmushi tayi ta fice,
Zaleeha kuwa dariya ta ɗanyi tare da cewa.
"Ya isa ya cema auta ai kai Appinshi ne".
miƙa yayi tare da konciya bisa kujerar da yake.

Amina kuwa tana shiga ɗakinta bakin gado ta zauna tanajin tana son danne zazzafan kishinta kenan yanzu yauma a ɗakin Zaleeha zai kwana,
kwanciya tayi tare da kife kanta bisa pillow ta saki nannauyan numfashi.
Ita dai ALLAH ya sani da Saifuddeen zai saki Zaleeha wlh da tanaso da kuma tafi kowa jin daɗi.
ɗago kanta tayi ta ɗauki woyarta jin alamun saƙo ya shigo mata.
buɗe saƙon tayi ganin sunan Abban Adeel hannu tasa ta share hawayenta lokacin data karanta abinda ya turo mata.
"Kin tafi kinje kin fara kukan ko?."
Da sauri ta tura mishi amsa.
"A a wonkafa zanyi".
ajiyan zuciya ta sauƙe sanda taga saƙonshi.
"Kin tabbata ba kuka kikeyi ba?".
Da sauri tace.
"Eh."
"Yauwa Ummu Adeel haka nake son ji,kinji ko kada in sake ganin kina min kukan da babu dalili,in laifi nayi miki ki gaya min banfi ƙarfin in baki haƙuri ba".
Wannan text ɗin yayi masifar sata jin daɗin, sai kuma shaiɗan ya kisa mata.
"Ke sokuwa kika san me yake gaya mata ita kuma?".
Take ta kife kanta taci gaba tubka da worwora

Please Login or Register in order to submit comment