Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tausayawa yace.
"Muyi haƙuri Ameenu, kada rasuwar Maryam yasa imaninmu gushewa, tabbas duk wani me rai mamaci ne, mutuwa bata barin wani dan wani, da ace tana bari kuwa da ta barmana Maryam, kayi haƙuri ka tuna da wasiyan da ta barmaka, kacika mata wasiyarta, katashi muje asallace ta, kasata acikin kabarinta kamar yanda ta buƙata."
Zaleeha dake durƙushe tana kuka, duk abun dake faruwa akan idanunta, hakanne yasa ta ƙara gigicewa, kuka take jikinta na tsuma, ko ina na jikinta rawa yake.
Ya Ahmad dake kuka sosai idanunsa gaba ɗaya sun kunbura sunyi suntum, shi ya riƙo Ya Ameenu, Haka duk jama'an dake cikin falon suka mimmiƙe, Zaleeha dake durƙushe bakin ƙofa ganin za a fita da gawan Adda Maryam ɗin yasa,ta sakin wani irin gigitaccen ƙara me ɗauke da kuka, zubewa tayi awajen takama ƙafan Yaya Fahad, da kuma na Yaya Sudais, wato ƙannen Ya Ameenu kenan, wanda suke ɗauke da gawan, sai kuma wasu abokan Baba Malam na kusa, cikin fusata Ya Fahad da Sudais suka ƙwace ƙafafunsu, dan kuwa gaba ɗaya family'n cike suke da baƙin cikin ta, haka tanaji tana gani suka fita da gawan Adda Maryam, Wani kukan kuma ta sake wanda yafi kowanne zafi, haka Baba Malam da kuma sauran jama'an dake cikin falon suka tsallake Zaleeha suka wuce, Ya Ahmad ne yayi fitan ƙarshe, cikin matsanancin kuka Zaleeha ta kama ƙafan Ya Ahmad ɗin tana wani irin kuka, cikin matsanancin kukan da yake cinsa ya ƙwace ƙafarsa, tare da wucewa ko waiwayenta baiyi ba. Wannan dalilin yasa ta soma buga kanta ajikin bango tana kuka, mai ɗauke da fitar hayyaci.

Acan waje kuwa ana fita da gawan nata, jama'a suka soma kimtsawa, Baba Malam shikansa ya shiga mamakin irin yawan mutanen da sukazo sallan jana'izar Maryam ɗin, saboda mutanene da yawa kamar ƙasa, ga wanda baisani ba ma zai iya cewa wani babban malami ko kuwa babban ɗan siyasa ne ya rasu, dan jama'an sun zarce tunaninsa, daga gidan su Saifuddeen kuwa babu wanda baizo ba, kama daga kan Saifudeeen, Ahmad, Dr Adnan, Bappa Ali Malam Ashiru Hayatuddeen, Harma dasu Wareesu abokan Saifudeen gaba ɗaya sunzo, ga Ishaq ma da Babansa Dirankadi da ƙananinsa Imran duk sunzo.
Haka akayiwa Maryam Sallah, nan aka ɗauketa aka sata acikin motan gawa, Dayawansu kuka suke me tsuma zuciya, haka dai waƴanda zasu rakata zuwa maƙabarta suka shiga cikin motocin da zasu tafi, ciki kuwa harda Ahmad da Dr Adnan da kuma Hayatuddeen, Saifuddeen kuwa anan ƙofar gidan suka zauna, saboda shi bazai samu zuwa maƙabartan ba, saboda larurarsa.

Acan cikin gida kuwa, Zaleeha har yanzu na zaune anan bakin ƙofar falon na Baba Malam, tana wani irin kuka, tariga da ta zauce, gaba ɗaya ta shiɗe bata wani cikin hayyacinta, wani irin kuka take wanda duk wani wanda ke cikin hayyacinsa dole ya tausaya mata, tun muryarta na fita har ya zamana kukan kawai takeyi, idanunta sunyi wani irin kumbura, fuskarta tayi jajur, cikin haka numfashinta ya soma ƙoƙarin ɗaukewa, duhu ne ya soma rufe ganinta, take kuwa ta sulele ƙasa daga durƙushen da take, lokaci guda numfashinta ya ɗauke, haka dai takejin kanta kamar ba aduniya take ba.

Sama da mintuna 20 ta ɗauka batare datasan inda hankalinta yake ba, harzuwa wannan lokacin kuwa babu wanda yazo yabi ta kanta, zafin ranan dake dukan jikinta shine abunda yasanya taɗan buɗe idanunta wanda suka wani irin ƙanƙancewa, hawayene suka kwaranyo daga cikin idanun nata, ahankali ta tashi inda ta jingina bayanta da jikin ƙofan falon, kuka ta fashe dashi tare da dafe saitin ƙirjinta wanda keyi mata zafi.
Aunty Lubna da tazo wucewa ne taga Zaleehan ahaka, ɗan tsayawa tayi tana meyi mata kallon mamaki, ganin Aunty Lubna yasa tasoma yunƙurin tashi dan zuwa ga Aunty Lubna'n, cikin sauri Aunty Lubna taja baya, hawayen dake cikin idanunta ta share, ɗauke kanta tayi daga kallon Zaleehan taci gaba da tafiyanta.
Abun daya ƙara sautin kukan Zaleehan kenan, nan ta zube akan guiwowinta tana kuka, gaba ɗaya aduniya babu inda zata shiga taji sanyi, kowa fushi yake da ita, gaba ɗaya danginta sun ƙita, harma da wanda take tunanin zasuji tausayinta, sun nuna mata fushi alokacin da take tsananin buƙatarsu.

Acan maƙabarta kuwa, Baba Malam da Ya Ameenu ne suka sanya Adda Maryam cikin ramin ƙabarinta, shikuwa Ya Ameenu zuwa yanzu gaba ɗaya hawayensa sun kafe, idan kuwa ya maka kallo ɗaya bazaka so ya ƙara ba, saboda gaba ɗaya idanunsa sun rune, sun zama jajur kamar wanda aka watsa masa garin barkono, zuwa yanzu yadaina tunanin komai, haka ya zama kaman mutum mutumi wato, statue, hatta da buɗe bakinsa baya iyawa, lokaci ɗaya yazama wani iri dashi, cikin rana ɗaya yayi wani irin muguwar rama, suna gama bunneta suka soma ƙoƙarin barin maƙabartan, amma me Ya Ameenu zama yayi anan bakin kabarin nata, da ƙyar su Malam Adam da Dirankadi suka lallashesa, Ya Ahmad dake wani irin kuka ne ya kama hannun Ya Ameenun suka fito daga maƙabarta'n, dan kuwa Ameenun yazama kamar wani ƙaramin yaro, ba ya um baya um um saidai shiru kawai, harkuwa suka shiga cikin mota bai daina kallon kabarin Maryam ɗin ba.
Dahaka suka nufo gida. Suna ƙarasowa ƙofar gida kuwa suka samu ankakkafa manyan runfuna, nan suka zauna ko cikin gida basu shiga ba, dan amsar gaisuwa, Baba Malam wanda da taimakon addu'o'in da yakeyi, yaji zuciyarsa ta ɗan samu salama, duban Zakariyya, dake zaune abayansa yayi, cikin muryarsa dake nuna tsananin ɓacin rai yace. "Zakariyya kaje kacewa Zaleeha ta fice min daga gida, bana buƙatarta, kome kama da da ita bana buƙata, matuƙar bata fitamin daga gida, nan da mintuna goma ba, Allah Ya isa bazan taɓa yafe mata ba." Hankalin Zakariyya ne ya tashi, take yaji wani kuka ya taso masa, shikenan zai rasa ƴan uwansa har guda biyu alokaci ɗaya, amma ya sani kome ya faru da Zaleeha ita ta jama kanta.
Nan ya miƙe cikin sanyin jiki, ya nufi cikin gidan.
Haryanzu tana nan adurƙushe kaman yanda suka fita suka barta tun da farko, kuka take harda majina, kaman ranta zai fita, fuskarta gaba ɗaya tayi jawur.
Ƙarasowa inda take Zakariyya yayi, muryarsa asanyaye ya ƙira sunanta.
Ɗago kanta tayi ta kalleshi, da idanunta wanda ko gani sosai basayi, kai Zakariyya ya girgiza tare da kawar da kansa gefe, cikin shanye kukansa yace.
"Baba Malam yace kifita masa daga gidansa, idan kika kara wasu mintuna sama da mintuna 10 acikin gidannan yace. Allah Ya isa baiyafe ba."
Cikin matsanancin tashin hankali Zaleehan ta riƙo hannun Zakariyya, cikin muryarta wanda ta dashe saboda kuka tace.
"Nashiga Uku, Zakariyya ya zanyi, ina zanje? nima Zakariyya mutuwa zanyi, bazan iya jure wannan baƙin cikin ba, kowa guduna yake kowa baya sona, waƴanda nake tunanin zasuji ƙaina, sunyi watsi dani, Adda Maryam ta rasu ta barni, Zakariyya bansan inda zanje ba, bani da kowa sama daku aduniya!.."
Taƙare maganar tana tsananta kukanta, kai Zakariyya ya girgiza mata hawaye na fita daga idanunsa yace.
"Kina dasu mana Adda Zaleeha, kina da wasu bayan mu mana, dan da ace kinsa azuciyarki cewa baki da wasu bayan mu, da baki gudu kin bar Mahaifinmu da mu kanmu acikin baƙinciki ba, ki koma inda kika fito, ki koma cikin arna'n da kika zaɓesu sama damu."
kanta ta shiga girgizawa, cikin kuka tace.
"Bazan iya jurewa ba Zakariyya, inama mutuwa tazo ta ɗaukeni, inama da ace mutuwa ni ta ɗauka ba Adda Maryam ba, kamar yanda Baba Malam ya faɗa, wayyo Allah na, ya Allah ka ka kawo min ɗauki a rayuwa ta!!!."
tafaɗi maganar tana wani irin kuka, Zakariyya ma fashewa da kuka yayi, dan kuwa yana matuƙar jin tausayin Yayartasa, saidai kuma laifin da ta aikata kowa ya sani me girma ne.
Dai-dai lokacin Malam Adam ya shigo cikin gidan, bayansa wasu baƙine, wanda zai sauƙesu anan falon na Baba Malam, ganin Malam Adam yasa ta rarrafa, ta faɗi agabansa, cikin kuka tace. "Dan Allah Daddy kataimakeni, (Daddy shine sunan da suke ƙiran Malam Adam ɗin dashi.) Baba Malam yayi fushi dani ya koreni, dan Allah kabashi haƙuri!!."

Fuska Malam Adam ya haɗe, cikin cushewar murya yace.
"Babu abun da zan iya miki, ba haƙurin kuma da zan bashi, abun da kika shuka shikike girba."
Daga haka yasa kai ya wuce cikin falon, baƙin nasa suka rufa masa baya.
Cikin kuka Zaleeha ta miƙe tsaye, duban Zakariyya tayi, sai kawai ta faɗa jikinsa ta saki wani irin fitinannen kuka, shima Zakariyyan kuka ya saka, tare da rungume ta, jin tausayinta yake kamar zai fasa masa zuciya.
Saida tayi kuka sosai kafun Zakariyya ya janyeta daga jikinsa, cikin sheshsheƙan kuka yace.
"Lokaci yana daɗa ƙurewa ki tafi kawai."
Juyawa yayi cikin sauri yana kuka ya nufi boys guater.
Cikin kuka haka ta nufi ƙofar fita daga gidan, kasancewar wajen gidan cike yake da jama'a, hakan yasa tabi ta ƙofar baya, tana cire ƙafanta daga cikin gidan tasaki wani irin kuka, haka ta miƙi titi, ta fiya take tana gauraya hanya, hawaye kuwa wani na koran wani akan fuskarta, gaba ɗaya ta fita hayyacinta, tayi wani wujiga-wujiga da ita, batasan inda zataje ba, bata da kowa aduniya bayansu da Adda Maryam na raye nema tasan ko duk zasu tsaneta ita bazata tsaneta ba, kuma tasan ko Ya Ameenu baya so zata bata mafaka kuma da Adda Maryam ta roƙa mata gafara wurin mahaifinsu, sukaɗaine gatan ta, gefe guda kuwa ga ƙafanta wanda taji ciwo har ta ɗan kumbura, ga wani busashshen jini da ya zauna akan fatarta.
Tafiya kawai take batare da ta san inda ta dosa ba, Jin an riƙe hijabinta ta baya yasanyata juyowa, Zakariyya ta gani hakan yasa ta fashe masa da wani sabon kuka, hannunta Zakariyya'n ya kama, suka ci gaba da tafiya, kasancewar unguwar tasu ta masu kuɗi ce, hakan yasa ko masu abun hawa irin na hayan nan basu cika shigowa sosai ba, sun ɗanyi tafiya, kafun Zakariyya ya hango wani mai adai-dai-ta sahu, wanda ya kawo wata mata, hannu Zakariyya yasa ya tare mai adai-dai-ta sahun, mai adai-dai-ta sahun na ƙarasowa gabansu, Zakariyya ya shiga cikin napep ɗin, tare da jawota itama ta shigo, har zuwa lokacin kuka take, sannan kuma yana riƙe da hannunta, duban me napep ɗin Zakariyya yayi asanyaye yace.
"Malam Shango estate zaka kaimu."
Kai me napep ɗin ya jinjina, sannan ya tada keken suka tafi. Ɗaura kanta akan kafaɗan Zakariyyan tayi, tare da sanya hannu ta dafe ƙirjinta dake mata zafi, nunfashinta nata ƙoƙarin yankewa saboda kukan da tayi har ta godewa Allah.
Koda suka ƙarasa Shango Estate ɗin anan ƙofar haɗaɗɗen sabon gidan Hajja Inna aka sauƙesu, Zakariyya ne ya ciro kuɗi ya bawa me napep ɗin, yana riƙe da hannun Zaleeha ya tura ƙofar gate ɗin gidan ya shiga, jin motsin buɗe ƙofa yasa me gadi dake kishingiɗe ya taso da sauri, ganin Zakariyya ne yasashi sakin numfashi ya koma ya zauna, Zakariyya kuwa yana riƙe da hannun Zaleehan har zuwa jikin bakin ƙofar da zata sadasu da babban falon gidan, key yaciro daga cikin aljihunsa ya buɗe ƙofar, sannan yaja Zaleehan suka shiga ciki. Akan kujera ya zaunar da ita, tare da ƙarasawa gaban fridge, goran ruwa me sanyi ya ɗauko sannan yazo ya aje mata agabanta, dubanta yayi cikin sanyi yace.
"Ki zauna anan, tunda Hajja Inna batanan tana can gida, wata ƙila gobe idan kika koma Baba Malam zaiyi haƙuri ya yafe miki".
Kuka ta fashe dashi tare da faɗawa jikin Zakariyya'n, cikin kuka tace.
"Na cuci kaina Zakariyya, nadasawa ƴan uwana baƙin ciki da ɓacin rai, nayi nesa da ku gashi har Adda Maryam tarasu batare da mun sake ganawa ba, lokacin dana tafi taƙira wayana, yafi sau 20 amma ban taɓa ɗagawa ba, kowa yaƙini sai bayan nayi wata biyu a can na fara amsa kiranta Zakariyya kai kaɗaine kaji tausayina, ya zanyi Zakariyya idan Baba Malam be yafemin ba, ya zanyi?".
Kukane yaci ƙarfinta sosai.
Zakariyya ma kukan yake. Zamewa yayi ya zauna tare da ɗaura kanta akan cinyarsa, ganin haka yasa ta takure jikinta waje ɗaya, nan tashiga rera sabon kuka, ita tanayi Zakariyya nayi, an rasa me rarrashin wani acikinsu, tayi kuka kam bana wasa ba, ita kanta bazata iya faɗin yaushe ne kuma tayaya ne, bacci ya ɗauketa ba, haka tayi bacci kanta nakan cinyan Zakariyya, yin baccin nata kuwa bairasa nasaba da irin kukan da tasha ta ƙoshiba, saboda yawan kuka nasanya mutum bacci, batare daya shiryawa hakan ba.
Ganin tayi bacci yasa Zakariyya zame jikinsa, pillown kujera ya ɗauka ya ɗora mata kanta akai, dubanta yayi, bacci take amma kuma sheshsheƙan kuka take tayi, hawayen da suka zubo daga cikin idanunsa ya goge, sannan ya tashi ya fita daga falon, kaitsaye ya koma gida.

Ita kuwa Zaleeha ko mintuna 20 batayi tana baccin ba, azabure tatashi, ganin bataga Zakariyyan ba, yasata dasa wani sabon kukan.
Tayi kukan tayi kukan harsaida taji kamar ma ba aduniya ta ke ba, ciwon kai kuwa ba'a magana, domin saboda tsabar ciwon da kanta keyi mata, har wani dishi dishi take gani

Haka dai ta zauna agidan idan tayi shiru yanzu anjima kuwa tayi kuka, da ƙyar ma ta iya tashi tayi sallah.
Tana nan tana kuka har dare ya rufa, yanda taga rana kuwa haka taga dare, ko lumshewa idanunta batayi ba, balle bacci ya ɗauketa, batun ciwon kai kuwa sai abun da yayi gaba, dan kuwa zuwa yanzu harwani ji take kaman kannata ya kumbura, saboda tsabar ciwo da yakeyi mata.
Haka ta kwana azaune tana karatu qur'an da kuka har gari yayi haske.
Nan dai daga falon babu inda ta gusa, banda toilet da ta shiga ta ɗauro alwala, tana nan zaune Zakariyya ya buɗe kofar falon ya shigo, ganin yanda idanunta suka kumbura kana sukai jajur yasa shi ɗan zaro idanunsa, cikin sauri ya ƙaraso cikin falon, agabanta ya zauna tare da aje ƴar ƙaramar kulan dake hannunsa, hankalinsa amatuƙar tashe yace.
"Kwana kikayi kina kuka ko?."
Yafaɗa yana me sanya hannunsa ya share mata hawayen dake kan fuskarta, kulan da ya shigo dashi ya buɗe, soyayyen dankali da ƙwai ne, sai sauce ɗin egg, turo mata kulan gabanta yayi, cikin tausayawa yace.
"Waima rabonki da abinci tun yaushe ne Adda Zaleeha? kici wannan abincin kinji." Kanta ta girgiza masa, cikin da shashshiyar muryarta tace.
"Banajin zan iyacin wani abu Zakariyya, bana buƙatar komai yanzu a duniya sai yafiyan Baba Malam, tayaya kake tunanin zan iya sakawa cikina abinci a airin wannan halin da nake ciki? bazan iya ba, ka kaini kawai naje nasake bawa Baba Malam haƙuri, hakanne kaɗai zaisa naji sanyi araina."
Hawayen tausayinta ya share, sannan ya kamo hannunta, cikin sanyin murya yace.
"Taso muje." Nan ta miƙe yana riƙe da hannunta yazama kaman shine yayanta ita kuma ƙanwarsa, haka suka fita daga gidan, tafiya kaɗan sukayi suka samu napep.

Aƙofar gidan ta baya Zakariyya yace da me napep ɗin ya sauƙesu, duban Zaleehan Zakariyya yayi, cikin sanyi yace.
"Kije Baba Malam shida su Mamy suna falonsa, nikam zan shiga ta babban ƙofa kar agane tare muke dake, nasan fushin da Baba Malam keyi dake zai iya shafana."
Kanta ta jinjina tana me share hawayenta, nan ta nufi cikin gidan, shikuwa Zakariyya ya sallami me napep ɗin ya tafi. Jikinta amatuƙar sanyaye haka ta shiga cikin gidan nasu, dayawan familynsu na cikin gida, na zaune a compund ɗin gidan, ganinta yasa gaba ɗaya duk suka tsaya kallonta, kanta aƙasa tana me zubar da ƙwalla haka ta nufi sashin Baba Malam,
jikinta asanyaye ta kai hannunta jikin ƙofar falon ta buɗe, Baba Malam, Malam Adam, Ya Ameenu, Ya Habu, Mamy, Ya Ahmad, da kuma Mama sai Goggo Maryama, sune zaune afalon, sunyi jigum, gefe kuwa wani babban abokin Baba Malam ne wanda yazo tundaga Kaduna, dan yi musu ta'aziyya, Ganin Zaleehan yasa Baba Malam rumtse idanunsa, Itakuwa Zaleeha ƙarasowa tsakiyar falon tayi, nan ta zube akan guiwowinta, tare da sakin wani irin fitinannen kuka, cikin kukan ta soma rarrafawa, dan ƙarasawa wajen Baban nata, cikin sauri Baba Malam ya ɗaga mata hannu, ransa amatuƙar ɓace yace.
"Idan kika sake kika taɓani banyafe miki ba, banason ganinki kifitamin daga gida!" Yafaɗi maganar yana me yi mata nuni da ƙofar fita. Hankalinta ne yasake tashi, take taji komai ya dawo mata sabo, cikin wani irin matsanancin kuka, ta rarrafa zuwa gaban su Mamy, azauce take matuƙa, cikin matsanancin kuka ta kamo hannun Mamy dana Goggo Maryama, amatuƙar gigice cikin tsananin kuka murya na rawa tace.
"Dan Allah Mamy Goggo Maryama ku bawa Baba Malam haƙuri, wallahi aduniya bani da kowa sama daku, Mamy dan Allah kibasa haƙuri na tuba ku yafe min." Hawayene suka zubo daga idanun Mamy na tausayin Zaleehan to amma itama, bata da ikon buɗan baki tace da Baba Malam ɗin yayi haƙuri, Goggo Maryama kuwa ma ɗauke kanta tayi gaba ɗaya, ganin haka yasa Zaleeha rarrafawa ta nufi wajen Ya Ahmad, cikin sauri Ya Ahmad ɗin natama ya miƙe batare daya bari ta iso wajen ba, ya nufi can cikin ɗakin Baba Malam ɗin, Allah yasani shi zuciyarsa me rauni ce akan Zaleeha, ko a jiya kukanta daya ganine yaƙara masa nasa kukan, sannan kuma awannan karan shi kansa baida wani hurumin bawa Baba Malam haƙuri akan ya yafe mata, ganin Ya Ahmad ɗin ya tashi, yasa Zaleeha sakin firgitaccen kuka, Mama ma kukan take sosai, wanda gaba ɗaya zuciyarta nadama da dana sanine ne ya cinye, dan har kunyan haɗa idanu dasu Baba Malam ɗin takeyi.
Kallon Ya Habu Baba Malam yayi, cikin ɓacin rai yace.
"Habu fitarmin da ita daga falo na da gida na baki ɗaya."
Tsam kuwa Ya Habu ya miƙe, hannunsa yakai ya damƙi hannun Zaleeha'n, haka ya jata yana ƙoƙarin fitar da ita daga falon, kuka take sosai har numfashinta na sarƙewa, sam Ya Habu baiji tausayinta acikin ransa ba, saboda har yanzu bai manta da irin baƙincikin da ta shayar dasu ba, asanadin ɓacin ranta, har Baba Malam saida ya kwanta jinya, shine yanzu zata zo da wani kuka tace a yafe mata.
Zakariyya kuwa ganin an fito da Zaleeha'n, kamar wata wanda ba ƴar gidan ba, yasashi fashewa da kuka, nan ya lallaɓa ya fita, dan zuwa ya sameta, Ya Habu kuwa ƙofa ya buɗe, ya turata waje, sannan ya jawo ƙofar gidan ya rufe, sulalewa tayi ajikin ƙofar tare da sakin wani irin marayan kuka, dai-dai lokacin Zakariyya ya ƙaraso, hannunta ya kamo, tare da jawota jikinsa ya rungumeta, ahankali yake ɗan bubbuga bayanta, shiɗin ma kuka yake sosai.
Cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Bani da inda zanje Zakariyya, Baba Malam ya tsaneni, yasa Ya Habu ya koreni kamar karya, ko ganina bayason yi, wayyo Allah ni Zaleeha ina zansakana kai da rayuwata! Wa zan samu ya tayani bawa Baba Malam haƙuri,tunda kowa yaƙi ya saurareni"
Cikin kuka Zakariyya yace.
"Mafita ɗayace Adda Zaleeha,."
Cikin tsananin kuka murya a disashe tace.
"Menene mafitan me zanyi in samu Baba Malam ya yafe min ne
Zakariyya?".
Hawayenshi ya share tare da cewa.
"Mafitar kuwa itace baki da wajen zuwa wanda ya wuce gidan su Hayatuddeen, wallahi na tabbata mutum ɗayane zai roƙi Baba Malam akan ya yafe miki, kuma ya aminta ya yafe miki ɗin a sauƙaƙe."
Cikin disashewar murya tace.
"Waye ne?."
Gyara tsayuwanshi yayi tare da cewa.
"Bakowa bane kuwa wannan mutumin face HAMMA SAIFUDDEEN, na tabbata idan kikazo da Hamma SAIFUDDEEN to Baba Malam zai yarda ya yafe miki."
Cikin kukan ta shiga jinjina kanta.
Murya na rawa tace. "Nayarda zanje koma inane, matuƙar Baba Malam zai yafemin, zanje shima in bashi haƙuri dan Allah Zakariyya ka kaini gidan su Hamma Saif ɗin kaji."
Kai Zakariyya ya girgiza, cikin tausayinta yace.
"Bazan iya zuwa ba.
Sam bazan iya kaikiba Adda Zaleeha, saboda bansan da wani idon zan kallesu nace nadawo musu dake ba, ke kikayi amanki saboda haka ke zaki lashe abunki ke ɗayanki, ke kaɗanki kika gudu kuma ke kaɗanki zaki koma da ƙafarki zakije ki shiga gidan dai da kika gujewan ki kwashi kayan kunyanki".
Yana gama faɗin haka ya tara mata wani mai adai-dai-ta sahu, sam bata fahimci ma me yake cewa ba, ita dai burinta kawai shine ta samu me baiwa Baba Malam haƙuri.
Zakariyya ne ya faɗawa mai napep ɗin inda zai kaita, tare da zaro kuɗinsa ya basa.
Ko acikin napep ɗin kuka take sosai, batasan cewa girman fushin da ƴan uwan nata sukayi da ita har yakai haka ba.

Koda mai napep ɗin ya sauƙeta a bakin gate ɗin gidan Saifuddeen, ido ta zubawa gidan da data gujewa kusan shekara ɗaya kenan.
Toma me matsayinta a gidan? Me sunanta? Matar gidan ko baƙuwar gidan? Da waɗanne idanun zata kallesu? Me zata cewa Ummi dottijiyar mata mai tarin mutunci da kima a idonta, me zata ce mata meyasa ta gudu? tace mata bata son ɗanta na cikinta ne ko meye? Ina zata ce musu taje? Da izinin wa ta fita? Zasu saurareta ma kuwa? Gaba ɗaya tsoro da fargaba da kunya da ƙuncin zuciya da rayuwa da nadama da danasani sun rufeta, fuskar nan tayi tib-tib tayi jazir idanun duk sun ƙanƙance, a hankali take jan ƙafarta har ta isa baki ƙofa, hannu tasa ta ƙonƙosa,
Da sauri mai gadinsu yazo ya buɗe mata ƙofar, ganin matar mai gidan ne dan

Please Login or Register in order to submit comment