Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ahmad a cewanta mai sunan yayanta ne dan Yaya ma take kiranshi tun tana gaidashi yana amsawa a yatsine har dai ya fara ɗan sasaautawa.

Har yau kuma a woje take kwana cikin gardin,
wannan abun shine yasa Ahmad yake matuƙar jin baƙin cikinta,
shi kuwa Saifuddeen  da fari baisan bata kwana a ɗakintaba dan baya shiga kuma da safe yana ganinta a wurin Umminshi,
To tun shekaran jiya daya dare ya ankara da bata ɗakin, ya dudduba ko ina na cikin part ɗin nata babu ita ba dalilinta, falonshi ya koma wayarshi ya ɗauka tare da yin mgnar zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana yau kwana biyu kenan bata kwana a nan."
Kanshi ya ɗan jingina da jikin kujerarsa tare daci gaba da mgnar zuci.
"To waya sanima ko ta daɗe da barin kwana a nan."
sai kuma yayi ajiyan zuciya tare da cewa.
"ko dai part ɗin Ummi take kwana? kai Anya kuwa Ummi zata barta ta kwana a side ɗinta,
to ko dai part ɗin Raliya take kwana."
Text ya rubutawa Ahmad,
"Kayi bacci ne?."
Ahmad da ke zaune a falo shida Raliyya suna mgnar Zaleeha dan hango wucewarta da sukayi,
murya a sanyaye Raliya tace.
"To wai ko dai Hamma Saifuddeen bai san bata kwana a ɗakinba?."
Ajiyan zuciya Ahmad ya sauƙe tare da cewa,
"Ina zaton bai saniba, kinfa san shi da miskilanci, in kuwa yasan bata kwana a cikin to yasan inda take kwanan shiyasa bai kulataba ai jiki magayi."
da sauri ya ɗago wayarshi ganin saƙon Saifuddeen ne ya sashi cewa.
"To ina ga dai bai san bata kwana cikiba sai yanzu dan ga text ɗinshi wai nayi bacci ne."
ido Raliya ta zuba fuskar wayarshi tana ganin amsar da yake rubuta mishi.
"A a banyi bacci ba, lfy dai ko?."
jim kaɗan sai ga wani saƙon.
"To lafiya dai zance,amman Zaleeha na wurinku ne?."
murmushi Ahmad yayi tare da cewa Raliya,
"Hmmm zanyi mgnin yarinyar nan."
sai kuma ya rubuta mishi amsa.
"A a Zaleeha kuwa, bata nan."
a take sai ga wani saƙon.
"Kasa Raliya ta dudduba nan wurinku, taje Side ɗin Ummi ma ta duba ko tana can."
yana gama karan tawa yace.
"Lafiya dai kam ko?."
tsaki Saifuddeen ya ɗan ja kana ya rubuta mishi,
"Nima ban saniba lafiya ko ba lfy ba, ina dai zargin yarinyar bata kwana a gidan nan, dan tun shekaran jiya na lura babu motsinta, sannan yanzu na dudduba ko ina bata ciki side ɗin."
cikin nuna fargaba Ahmad yace.
"Innalillahi, to ina take zuwa ta kwana, gani nan fitowa."
sai ya kuma miƙe ya kalli Raliya tare da cewa,
"Maza kije side ɗin Ummi ki gaya mata, ana neman Zaleeha ki kuma ce karta nuna tasan inda take kwana zanyi mgninta."
to tace tare da juyawa ta nufi side ɗin Ummi,
kana shi kuma Ahmad ya nufi ƙofar falon Zaleehan nan yayi kicibis da Saifuddeen daya fito,
"To wai ina ta shigane, mufa mun dudduba wurinmu babu ita."
kai ya jujjuya mishi alamun shimafa ya dudduba wurinsu babu ita.
dai-dai lokacin kuma Ummi da Raliya suka iso, nan fa suka haɗu suka nuna basu san inda takeba.
ita kuwa Zaleeha tun fitowan su Ahmad ta buɗe ido,
jin ita ake nema yasa ta zame a hankali ta konta a ƙasan kujerar fulawi ke zagaye da ita.
Ahmad kuwa yana hangota hakan ya sashi cewa.
"Hmmmm zaki gane kurenki."
wayarshi ya zaro lallatsata yayi ya nemo number Ya Aminu,
ya kirashi kana ya kara wayar a kunnenshi.

Can cikin bacci Ya Ameenu yaji wayarshi nata suwa,
a hankali ya ɗan zare Maryam daga jikinshi,
hannu yasa ya ɗauki wayar time ya duba ƙarfe ɗaya na dare.
"Ahmad kuma a daren nan lfy kuwa?."
sosai yaji fargaba ,kar dai Zaleeha nacan na tarfa musu rashin ɗa'a, jiki na rawa ya amsa kiran cikin sauri yace.
"Salamu alaikum ,Ahmad lfy kuwa?."
cikin nuna tashin hankali yace.
"Ya Ameenu Zaleeha ce bamu ganiba mun nemata ko ina a gidan babu ita ba dalilinta,
kuma Saifuddeen yace tun shekaran jiya bata kwana a side ɗinsu,
to sai yayi tunanin wai ko side ɗinmu take shigowa ta ɓuya ko na Ummi,
to shine yanzu ya sanarmana zatonsho tana wurinmu,mun duba kab gidan bata, nan shine nace bari in kiraka ko ta dawo gidane?."
cikin kaɗuwa Ya Ameenu ya miƙe tare da cewa.
"Zaleehan to ina take zuwa?."
a taƙaice Ahmad yace.
"To ko tana gida ne?." rai a ɓace Ameenu yace.
"Kai anya kuwa sam bata gida, to ina take zuwa ta kwana, yi haƙuri bari in kira Baba malam."
to Ahmad yace kana ya katse kiran sannan ya gaya.musu yadda sukayi da Yayanta Ameenu,
kana yace su shiga ciki kafin Ameenun ya kirashi.

Shi kuwa Ya Ameenu wani irin tashin hankali ne da ɓacin raine mai tsanani ya rufeshi to ina Zaleeha take zuwa ta kwana ina take tafiya ta bar ɗakin mijinta me haka yake nufi?
kiran Baba Malam yayi bawan Allah yana zaune bisa sallaya yana karatun qur'an kiran Ameenu ya shigo wayarshi,
har wayar ta katse bai ɗaukaba duk da yaga Aminune so yake yaje ƙarshen surar Arrahaman da yake karantawa,
yayinda wani fargaba ya rufeshi lfy kuwa kira da tsakiyar daren nan.
Yana zuwa ƙarshen surar kira na uku na shiga wayar, da hamzari ya amsa kiran,
"Barka da dare Baba Malam kayi haƙuri na tada kai daga bacci."
Ameenu ya faɗa a ladabce,
murya a ɗan harɗe Baba Malam yace.
"Ameenu lfy kuwa meke faruwa?."
cikin sanyi Ya Ameenu yayi mishi bayanin da Ahmaɗ yayi mishi, ya ƙara da cewa.
"Ko dai ta taho gida ne?."
lumshe ido Baba Malam yayi yana jin wani irin suya da zuciyarshi keyi me Zaleeha ke nufi zubda mishi mutunci da kima  a idanun mutane ko?
a hankali ya cewa Ameenu.
"Ameenu bana zaton tana cikin gidana ,bazata zo nanba, amman dai bari in bincika."
to Aminun yace kana y katse kiran.
shi kuwa Baba Malam fitowa yayi da kanshi yayi tabin luggu da saƙo na gidan ya duba ko ina kab babu ita, koda ya titse Mama da tambayar ina Zaleeha ke zuwa ta kwana,
rantse-rantse tayi ta mishi akan ita bata san ina Zaleeha ke zuwa ta kwanaba.
a daren Ameenu ya kira goggonsu Maryama da duk inda suke zaton zataje ko ina sai ace musu bata zoba.

Wannan abu yayi matuƙar tada hankalin Baba Malam ya Ameenu kuwa ji yake in yaga Zaleeha zai kusan karta,
dole ya kira Ahmad yace,
wlh bata wurinsu amman tunda da safe tana dawowa zai zo ya sameta, har ɗakinta.

Da  wannan kowa ya koma ɗakinshi, Ahmad kuwa ranshi ƙal yasan Zaleeha zata gane kurenta.

Washe gari kamar yadda ta saba, suna tafiya masallaci ta koma ɗakinta wonka tayi da ruwan ɗumi wai ko tsamin cizon sauro da  jikinta keyi zai ragu, wanka da al'wala tayi,
kana ta fito tazo tayi salla koda ta idar  azkar tayi sanan ta miƙe ta kimtsa jikinta cikin wata doguwar rigar mai ɗan karen.kyau wanda duk na kayan aurene, da mayafinshi ta yane kanta ,kana ta nufi sashin Ummi.
a falo ta samesu, dukansu, cikin nitsuwa ta isa gaban Ummi dake mata murmushi tare da cewa.
"Gari ya waye ko ɗiyata?."
murmushi tayi tare da rusunawa gaban Ummi cikin ladabi da sanyin lafazi tace.
"Ummi Ina kwana?."
cikin kula Ummi tace.
"Lafiya lau ya  baƙunta?."
kai a sunkuye tace,
"Alhamdulillahi."
"Masha Allah." cewar Ummi kenan
Hayatuddeen ne ya gaidata ta amsa fuska a sake, kana ta kalli,
Ahmad dake zaune kusa da Saifuddeen bisa alamu lissafi sukeyi,
cikin sanyin sauti tace.
"Yaya ina kwana?."
a taƙaice yace.
"Lafiya lau." daga nan kuma sai ta miƙe tare da cewa Ummi .
"Raliya na kitchen  ko?."
cikin jin daɗi Ummi tace.
"A a tana sashinta yau wai kanta ke ciwo."
a hankali tace,
"Ayyah ban saniba Allah ya bata lfy."
Amin Amin Ummi tace,
Kana sai ta ɗan rusuno tare da cewa,
"To Ummi bari in shiga kitchen, me zan  haɗa  mana breakfast?."
sosai Ummi take jin daɗin yadda take sakewa da Raliya su shiga kitchen tare, gashi yanzu har tana shiga ita ɗaya ma tayi musu girki.
cikin kula Ummi tace.
"Bari inzo mushiga tare to."
da sauri tace .
"A a Ummi ki bari zan iya ki huta."
sai kuma ta kalli Hayatuddeen daketa murmushi tace,
"Zo muje kitchen ka tayani hira."
da sauri ya miƙe yabi bayanta, yana cewa.
"Yauwa muje ki min dege-dege."
da ido Ummi ta bisu har suka shiga kitchen ɗin.

koda suka ƙarasa cikin kitchine ɗin, hayewa kan wata kujera Hayatuddeen yayi ya zauna, wayarsa ya fiddo daga aljihunsa tare da soma latsawa, ita kuwa Zaleeha, direct wajen fridge ta nufa, buɗe cikin firjin dake shaƙe da kayayyakin abinci tayi, nan ta zaɓo manya manyan kaji guda biyu,  sake wankesu tayi sannan ta ɗaura akan wuta tare dasa kayayyakin ƙamshi dana danɗano.
nan ta ɗibo irish patatoe tasoma ƙoƙarin ferewa,  Hayatuddeen ne ya taso tare da soma taya ta,  haka suka cigaba da firan, yana ta zuba mata surutu,    mayafin dake jikinta ta ajiye, tare da soma yin aikinta cikin nutsuwa, yayinda Hayatuddeen gaba ɗaya ya sakota gaba da surutunsa,  cikin abun da bai wuce awa ɗaya da rabi ba, ta kammala haɗa barbecued chicken da kuma patotoe balls,  sai kuma bread Pizza, wanda gaba ɗaya ƙamshinsa ya cika kitchine ɗin, Hayatuddeen dake zaune agefe sai haɗiye miyau yake, dan har ya tsara irin cin da zaiyiwa bread pizza ɗin, da ƙamshinsa ya cika masa hanci, spearmint tea ta haɗa, sannan ta juyesa acikin flask, nan ta kimtsa gaba ɗaya kayan akan wani babban tray, duban Hayatuddeen tayi tare dayi masa alama akan yazo ya tayata ɗauka, aikuwa shi ya kwashe komai inda ya jere musu break fast ɗin akan dinning table, ita kuwa Zaleeha har yanzu tana kitchine, fruit salad ta haɗa, inda ta zubashi cikin wani babban glass bowl, tunanin haɗa chocolate fudge cake ne yazo mata, nan ta duba taga akwai komai na buƙata, kanta ta jinjina, sannan tashiga ƙoƙarin haɗawa, cikin mintuna ƙalilan kuwa ta kammala, ita kanta saida tayaba da ƙamshin chocolate fudge cake ɗin, Hayatuddeen dake falo kuwa koda ƙamshin yaje masa, saida yakasa haƙuri ya biyota zuwa kitchine ɗin, ganin, fudge cake ɗin yasan yashi cewa.
"Wow fantastic, Aunty Zalee dama wai kin iga girki har haka ne?, na ɗauka a faɗa da masifa chart da zuwa wurin aiki kawai kika iya."
Hannu tasa takai masa bugu, da sauri ya kauce yanayi mata dariya, hararan wasa ta watsa mai, tare da cewa. "Kaɗauka yanda kuke sakarkaru kaida Zakariyya haka kowa ma yake ne baku da aikin sai yawo a gari dama tsokana da ci."
Taƙare maganar tana me miƙo masa, wani haɗaɗɗen tray wanda ciki tashirya chocolate fudge cake ɗin, amsa yayi yana wani malau malau da baki, tare da cewa.
"Hmmm ai yanzune ma zakuga tashen jami'a zakusha mmki bari dai in gama sabawa da jami'ar kin san banfi sati ɗaya da fara zuwa ba."
Dariya ta ɗanyi tare da cewa.
"Yo ai da an ganka ansan kanka na fizga da igiyar iskar sabin shiga jami'a ka dai yi a hankali yaro dan ita jami'a gidan ban kashine."
Murmushi ya ɗanyi tare da cewa.
"Gobe zan kawo miki sabon abo kina Khamis ku gaisa. kiga irin salon takun mu, yaseen ki kuma cewa mijinki ya saya min mota.
Dan ni ba yaro bane da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni kamar wani ɗan primary ko kayan wonki da za'a rinƙa kaini ana ɗaukoni".
Ya ƙarishe mgnar yana wuce zuwa dinning, food flask ɗin dake gefenta wanda ciki ta shiryawa Raliya abinci ta ɗauka.
Koda ta fito falo, nan ta iske Ummi, da kuma Saifuddeen, da Ahmad, Hayatuddeen kuwa tuni ya baje kan dinning, inda ya turo baki gaba, wai don saboda yace suzo suci, sunce yajira Zaleehan tagama sai suci tare, sam shi gaba ɗaya yaƙosa yaji yana tauna abincin, musamman ma da ƙamshin abincin ya cika masa hanci.
Zaleeha na fitowa daga kitchine ɗin ta dubi Hayatuddeen, fuskarta ɗauke da murmushi tace.
"Autan Ummi sarkin ci!."
Baki Hayatuddeen yaƙara turowa gaba, ashagwaɓe yace.
"Eh naji, amma please kice musu suzo muci, I swear am feeling hungry fa!."
yafaɗi maganar yana me shafa cikinsa, wanda hadda ganin abincin ma yaƙara masa jin yunwa.
Murmushin daya bayyana zallan cute face ɗinta tayi, tare da girgiza kanta.
Ummi ne tayi murmushi tare da duban Zaleehan, cikin so da ƙaunar yarinyar tace.
"Sannu da aiki, Allah yasaka miki da al'khairi, ya kuma baki ƴaƴa masu al'barka, wanda zasuyi miki fiye da haka."
Saɗa kai kasa Zaleeha tayi tare da ɗan sakin guntun murmushi a kunyace murya a sanyayaye tace,
"Amin Ummi."
Saifuddeen kuwa a fakaice ya ƙura mata idanu, yana kallon duk wani motsinta sosai yake mamakinta, har yau har yanzu ya rasa ita wace irin mutum ce mai fuska biyu da jujjuyawa tamkar hawainiya, ji yanda take ta murmushi tare da sakewa dasu, tanayin komai kamar wata wanda keson zama dasu da gaske.
Shi mamakinta ma yake, tawani irin sakewa sai kace ba itace, su keta gantalin nema ba jiya.
Kawar da kansa yayi daga kallonta, tare da maida hankalinsa, ga laptop ɗinsa,
wanda a zahiri laptop yake kallo a baɗiri kuwa fuskata yake kallo ta cikin madubin system ɗin,
rumtse ida nunshi yayi a hankali tare da sauƙe nannauyan ajiyan zuciya,
"To ina take zuwa ta kwana dasu waye take kwana, me take aikatawa a inda take kwanan?."
haka yaji waɗannan tambayoyin sun cika mishi zuciyarshi dake cike da azabebben kishi, gaba ɗaya ya rasa wani irin kishi Allah ya ɗora mishi a kanta ji yake tamkar zai faɗi ya mutu dan baƙin ciki.
Ahmad kuwa dubanta yayi tare da sakin murmushi, cikin ransa yayi ƙwafa, ahankali yace.
"Zaki sanine yarinya."

Duban Ummi Zaleeha tayi tare da ɗan rusunawa, cikin nutsuwa tace.
"Ummi bari na kaiwa Raliya abincinta, tunda batajin daɗi nasan ba lallaine tasamu fitowa ba."

Sosai Ummi taji daɗin kulawan da Zaleehan ta nuna ga Raliya'n, amma sai tace.
"A'a Zaleeha da kanki, bazaki bari Hayatuddeen yakai mata ba."
Murmushi Zaleeha tayi tare da cewa.
"Bakomai Ummi, kinga Hayatudeen ɗin yace bazai iya komaiba sai yaci abinci,inaga bazai iya matsawa akan dinning ɗinnan batare daya lodawa cikinsa abinci ba, kin sanshi acicine kazar birni!."
Zaleehan tafaɗa tana kallon Hayatuddeen, ba iya Ummi ba harta Ahmad saida yaɗanyi murmushi sabida sunan data kira Hayatuddeen Acici kazar birni, Ummi ce tace, idan takaiwa Raliyan abincin ta dawo suci abincin, nan tace zasuci da Raliyan acan.

Koda ta ƙarasa ɓangaren Raliyan, akwance ta isketa, nan ta shiga ɗan kimtsa mata ɗakin, daga nan kuma ta zuba musu abincin inda suke ta hira ita da Raliya'n sosai Raliyan ta sake da ita har taji ciwon kan nata ya saketa.

A falon Ummi kuwa, tuni Ummi tayi serving ɗin kowa, nan fa Hayatuddeen yasoma kai loma, yana me jijjiga kansa.
Saifuddeen kuwa ahankali yake tsakuran abincin yana kaiwa bakinsa, idanunsa kawai yake lumshewa sabida ƙuna da zuciyarshi keyi na kishi,
tabbas ya yaba da iya girkinta domin sosai abincin yayi masa daɗi, sam koda wasa bai taɓa tunanin cewa Zaleeha ta iya girki har haka ba.
Ummi ma sosai ta yaba da abincin,
Hayatuddeen kuwa cikin santi ya ɗago kai inda ya dubi Ahmad, cikin halinsa na tsokana yace.
"Wallahi Aunty Zalee ta iya abinci, mai daɗi kaman kunnena zai fita, hmmmm ai daga yau ita zatana mana girki, don sosai tafi su wance iyawa."
Dariya ne ya ƙwacewa Ummi, dan tasan tabbas Hayatuddeen dan tsokana yayi maganan da Raliya yake.
Harara Ahmad ya watsa masa tare da taɓe baki, cikin nuna cewa shima matarsa gwanace yace.
"Oho dai, da makaho ya rasa ido sai yace da wari, wannan har wani abinci ne, an haɗamu da tarkace saikace wasu yaran larabawa, jifa wani cake na chocolate, ko ance mu yaran larabawa ne, ai dai Raliya tafita iya girki ko Ummi."
Ahmad ya faɗa yana me duban Ummi.
Murmushi Ummi tayi tare da gimtse dariyarta, ita dai bata da tacewa, to ma mezatace komai tace yanzu zasuce tayi sonkai.
Hayatuddeen kuwa dariya yadinga yi, don yasan maganan Ahmad ɗin, a iya laɓɓan baki kawai take, ba taje zuci ba, ya faɗane kawai don ya kare matarsa, amma yasan cewa koma waye yaci girkin dole ya yaba, musamman ma spearmint tea ɗin dake ta ƙamshin kayan haɗi, uwa uba kanasha kanajin wani irin ɗan ɗanon zuma aciki.

Ahaka suka kammala cin abincin, inda Ummi tasa Hayatuddeen ya kwashe kwanukan yakai kitchine.

Acan gidan Baba Malam kuwa, tuni Baba Malam ya ƙira Habu, inda yace yaje gidan Zaleeha ya taho masa ita.
Babu ɓata lokaci kuwa, Ya Habu yashiga cikin motarsa, kai tsaye ya nufi gidan su Saifuddeen.

Aƙofar gidan yayi parking motarsa, inda yayi knocking gate ɗin gidan, maigadi ne ya leƙo tare da buɗe masa, duban maigadin Ya Habu yayi tare da basa hannu suka gaisa, dai-dai lokacin kuma Ahmad yafito daga part ɗin Ummi zaiyi nasu sashin, ganin Ya Habu yasanyashi ƙarasowa wajen daɗan sauri, nan yabawa Ya Habu hannu sukayi musabaha koda Habun ya gaya mishi saƙon Baba Malam, Ahmad ɗinne yayi masa jagora har zuwa part ɗin Ummi, amutunce suka gaisa da Ummi, bayan sun gama gaisawanne yayi musu bayanin cewa Baba Malam ne yaturosa akan cewa ya tafi da Zaleeha, aikuwa sosai zuciyar Ahmad tayi fess, Ummi ne tace da Hayatuddeen yaje yaƙirawo Zaleehan, don kuwa har yanzu tana nan a part ɗin Raliya.
Koda Hayatuddeen yaje part ɗin Raliya, nan ya iskesu sunata hira, shaida mata ƙiranta da akeyi yayi,
"Aunty Zaleeha Ya Habu yazo yana falon Ummi yace kije."
Cikin tsoro da fargaba tace.
"Ya Habu kuma! Shi da waye?."
murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ya Habu fa nace ba dodoba, shi kaɗai mana yazo, kinga yace kiyi sauri gida zakuje tare."
Ƙulullluuuu cikin Zaleeha ya bada sautin murɗa a take cikinta ya ɗuri ruwa, nan ta cika da fargaba haɗi tsoro,
cikin tankwashe wuya ta kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"Pleees je kace baka ganni ba."
Sosai suka cika da mamaki,
Kai Raliya ta sunkuyar dan kar dariyan da ke sun kubce mata ya baiyana a fuskarta, cikin mmki tace.
"Ya kuma zaije yace bakyanan bayan kuma gaki?."
kwaɓe fuska tayi tare da cewa.
"Eh yaje yace ina bacci to."
sosai tsoronta ya baiyana a fuskarta ganin hakan yasa yakoma falon Ummi yafaɗi cewa.
"Bai ganta ba." Hararan da Ahmad ya watsa masa ne, yasan yashi faɗin gaskiya inda yace.
"Tace nace banganta ba, ko kuma ince tayi bacci."
Nanfa Ya Habu yacika da mamaki, take kuma yaji ransa ya ɓaci, ta tabbata mara gaskiya kenan, sake tura Hayatuddeen ɗin yayi akan tazo, nan ma Hayatuddeen yaƙara dawowa, yace tace wai batanan, haka akayi juyin duniya akan Zaleeha tazo, amma ina sam taƙi zuwa, daga ƙarshema ɗakin Raliya ta gudu ta ɓuya.
Rai aɓace Ya Habu yafito yabar gidan.

Yana zuwa gida ya iske Ya Ameenu da Baba Malam azaune, cikin ƙunan zuciya ya kwashe duk abun da ya faru ya faɗawa Baba Malam,
sosai Ya Aminu ya hatsalo gaba ɗaya jikinshi rawa ya ɗauki saboda matsanancin ɓacin rai da zafin zuciya irin nasu na sojoji da kuma fulani ji yake muddin gata gashi zai kakkarya mata ƙafafuwa yaga gobe da wanne sawun zataje yawon.
Me Zaleeha takeson maidasu ne?, me take nufi dasu? Wai ko dai gani take tafi ƙarfinsu ne? miƙewa yayi tare da cewa.
"Bari inje in taho da ita!."
Kai Baba Malam ya gyaɗa mishi dan fitinar Zaleeha tana tafasa mishi zuciya tana gab da ƙureshi.


Ahmad na zaune afalo suna mamakin halin na Zaleeha, saiga ƙiran wayar Ya Aminu yashigo wayarsa, ɗauka yayi ko gaisawa Ya Ameenu bai bari sunyi ba, yace da Ahmad ɗin yana ƙofar gida,
cikin jin daɗi Ahmad ɗin yasanar dasu Ummi da Saifuddeen.
Sannan yafita ya shigo da Ya Ameenu'n, gaisawa sukayi sannan Ahmad ɗin ya dubi Saifuddeen, cikin nutsuwa yayi wa Saifuddeen ɗin alama kan cewar yayi haƙuri, zasu tafi da Zaleehan, Baba Malam ne ke nemanta, cikin body language Saifuddeen yace.
"Bakomai" dan shi kanshi yana cike da son sanin ina take zuwa ta kwana.
Shikuwa Ya Ameenu kai tsaye cewa kawai yayi anuna masa ɗakin da Zaleehan take, a bashi izinin shiga zata fito, nan Ahmad mugu yace.
"Ba komai ya Ameena ai kai ba baƙo bane, tana ɗakin Raliya muje in nuna maka ɗakin".
cikin zafin jini Ya Ameenu yabi bayan Ahmad da yake ta dariyar zuci so yake adaka mishi hegiyar yarinyar nan mai ladabin kura
Zaleeha na rakuɓe ajikin bango suna magana da Raliya sai gani tayi an turo ƙofar ɗakin, koda takai dubanta ga ƙofar kuwa saida numfashinta yakusan ɗaukewa ganin Ya Ameenu a bayan Ahmad sam bata tsammaci ganinsa ba, aruɗe tasoma ƙoƙarin guduwa, taku ɗaya yayi ya cafkota tare da wanka mata wani irin gigitaccen mari, wanda yasanya tasaki wata irin razanannen ƙara, take tasoma ƙoƙarin shiɗewa, aharzuƙe Ya Ameenu yace.
"Wato har kinyi girman da Baba Malam zai aiko ƙiranki kiƙi zuwa ko?, wuce muje kona kakkaryaki anan wajen, mahaukaciya kawai muje yau sai kin gaya mana gidan ubanwa kike zuwa ki kwana?!!."
Cikin ɗimaucewa Zaleeha ta wuce gaba, tare da fara tsalle tana yarfa hannu cikin kukan gano yau sai dai buzunta dan ta lura zargin yawo Ya Aminu da sauran ƴan uwanta suke mata.
jin ya sake yarfa mata wasu tagwayen marukane tare da ce mata.
"Gidan ubanwa kike zuwa ki kwana? Wato mu zaki maida sakarkaruko? Wato yawon lalata kikeson ki koyaka?."
wani irin tsalle ta rinƙayi tana yarfa hannu cikin tsananin kuka da tsoro tace.
"Wallahi Ya Ameenu ba yawon lalata nakeyiba, a cikin gidannan nake kwana cikin garden nake kwana wlh bana fita ko ƙofar gidan."
Ummi kam dake falonta jin kukan Zaleeha ne yasata saurin juyowa ta kalli Saifuddeen dake kallonta tace.
"Kai Saifuddeen dukanta fa sukeyi ,kada ka bari su tafi da ita zasu illatata,wannan sojanefa ya saba dukan garadai kar ya illatamin yarinya mai biyayya."
kai ya jujjuya mata tare da haɗe hannunshi wuri ɗaya ya mata alamun dan Allah kada ta fita ta barsu su tafi da ita.

Shikuwa Ya Ameenu a zafafe yace.
"Maza mu tafi gida ba ni zakiyiwa bayani ba."
da sauri-sauri gudu-gudu tayi hanyar fita, kana shi kuma biyo ta.
Suna ƙarasawa wajen motarsa ya buɗe tare da hankaɗata ciki, ransa amatuƙar ɓace ya ja motar sukabar ƙofar gidan.

Gudu yake sosai hakan yasa cikin mintuna kaɗan suka iso G.R.A yana gama dai-dai-ta fakin ɗin motar, ya fito tare da zare belt ɗin wandonsa, ƙofar da take ya buɗe tare da figota waje, nan yashiga zuba mata belt ɗin ajikinta, kuka da ihu mai firgitarwa Zaleeha keyi tare da gudu ta nufi cikin gidan, kai tsaye ɓangaren Baban nata ta nufa.
Tana shiga tafaɗa bayan Mamy dake tsaye acikin falon, gefe kuma Baba Malam ne zaune, sai kuma Ya Ahmad da kuma Mama wanda tacika tayi fam, ƙiris take jira ta fashe ta tarwatsa musu buhun bala'i.

A harzuƙe Ameenu yashigo cikin falon, ganin haka yasa Zaleeha yin tsalle ta faɗa jikin Ya Ahmad ɗinta, ƙan ƙamesa tayi ƙam tare da ɓoye fuskarta a ƙirjinsa, kuka take sosai kamar ranta zai fita don sosai ya tsutstsula mata bel ɗin,
Ya Ameenu na ƙoƙarin ƙara mata wani dukanne, Ahmad ya girgiza masa kai, alaman yabarta hakanan, da ƙyar Ahmad ya iya lallashinta tayi shiru, nan Baba Malam ya tambayeta ina take zuwa da bata kwana agidan aurenta?.
Cikin matsanancin kuka tare da tsoro murya na rawa take cewa.
"A garden nake kwana, Baba Malam wallahi ko ƙofar gidan ban taɓa fitowa ba ,
wallahi Baba Malam babu inda nake zuwa, a cikin gidan nake kwana."
Sosai sukasha mamaki, amma sanin halinta da taurin kae irin nata yasa suka yarda cewa zata aikata hakan, a hatsale Habu yace.
"To meyasa bazaki kwana cikin ɗakin kiba ko dai ƙarƙashin sirran aka nuna miki akace miki nanne ɗakin kwananki?."
kai ta jujjuya cikin tsananin tsoro dan a duniya dai Zaleeha bata son abinda zai taɓa mata lafiyan jikinta murya na rawa tace.
"Ni tsoronshi nakeji shiyasa nake fita woje."
kai kawai Baba Malam ya jujjuya dan har ga Allah shi ya yarda Zaleeha tsoron takeji dan ya santa matsoraciyace bata son abinda zai taɓa lfyarta, kana kuma duk mace budurwa akwai tsoron namiji a ranta musamman in ance mijintane tofa akwai wannan tsoron da taraddin haɗuwar forko dana biyu wasu harma na uku.
Wannan tunanin yasa Baba Malam yayimata faɗa tare da Nasiha, haka tayi kuka harta godewa Allah.
Mama kuwa yau saboda tsaban ɓacin ran dake cinta kasa cewa komai tayi, tuni ma tabar musu falon, don idan ta tsaya zata iya dannawa Ameenu daya dakar mata ƴa ashar babu ruwanta da surkuntaka.

Nan take Baba Malam yasa Mamy tashirya inda taɗauki Zaleehan ita da Ya Ameenun suka maida ita gidan su Saifuddeen, har gaban Ummi suka kaita, nan sukaiwa Ummi bayanin cewa wai agarden take kwana, nan sukaita bawa Ummi da shi Saifuddeen ɗin haƙuri, suka sa itama ta basu haƙurin

Please Login or Register in order to submit comment