Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fitowarsa compound ɗin gidan ne, ya hango Sule driver, hakanne ya sashi ƙarasawa wajen Sule driver'n, cikin kulawa Sule driver'n, yayi masa barka da fitowa, da kai ya amsa masa kamar koda yaushe. Buɗe murfin motar yayi, nan ɓangaren gidan baya ya shiga, dan dama shi baicika zama agaba ba, akomansa yafison sirri, musamman ma yanzu da yake mazaunin jami'in sirri, yana shiga ya jawo murfin motar ya rufe, wayarsa ya laluɓo daga cikin aljihunsa, cikin text message ya shiga, ataƙaice ya rubuta cewa. _"Ummi kice mata tayi sauri, dan tana ɓatamin lokaci."_
yana gama rubutun yayi sending, tare da maida wayan ya ajiye, laptop ɗinsa ya ɗauko yana dannawa.
Ummin kuwa dama tuntuni tasa Zaleehan ta shirya, tsab cikin ɗaya daga cikin sabin rigunan da tasa aka sayo mata, duk da cewa akwai yanayin damuwa mai yawa akan fuskarta, amma hakan baihana kayan yi mata kyau ba, saboda doguwar rigace irin abaya ɗinnan ta larabawa me kyau, yayinda ta yane kanta da ɗan kwalin kayan, wanda ya sauƙo har zuwa ƙirjinta.
Tunda ta gama shiryawan take zaune abakin gado, gaba ɗaya ta rasa mekeyi mata daɗi, tsoro da fargaba ne suka cika zuciyarta, ga kuma yawan faɗuwar gaba da takeji, ƙirjinta ne ke wani irin duka, gaba ɗaya atsorace take, koda tayi ƙoƙarin bawa kanta ƙarfin guiwa kuwa hakan baya yiwuwa, saboda fargaban daya cika zuciyarta.
"Me zata tarar agidan Baba Malam? wata ƙila ma yaƙi yafe mata ya kuma sake koranta." Wannan abun shine abun daya tsaya mata arai, duk yanda taso jin sauƙi azuciyarta abun yaci tura, hakanne yasa kawai ta fashe da kuka, dai-dai lokacin Ummi ta turo ƙofar ɗakin ta shigo, ganin Zaleehan na kuka yasa ta ɗan dafe kanta, sam batason yawan kukan na Zaleeha, jin an shigo ɗakin ne yasata ɗago kanta, ganin Ummi yasa cikin hanzari ta tashi tare da ƙarasa gareta, cikin muryarta dake rawa tace.
"Wallahi Ummi tsoro nakeji , idan mukaje Baba Malam ya koreni sannan yaƙi yafemin ya zanyi? shikenan nikam rayuwata tana cikin garari." taƙare maganar hawaye na silalowa daga cikin idanunta, Ɗan bubbuga bayanta Ummi tayi, cikin son kwantar mata da hankali tace. "Kada ki faɗi haka Zaleeha, share hawayenki, insha Allah Baba Malam zai yafe miki, nasan nanda ƴan wasu awanni zaki kasance cikin farincikin yafiyar Baba Malam, yanzu taho muje Hammanku nacan mota yana jiranki."
Idanunta ta ɗan lumshe, ahankali taɗan gƴaɗa kanta kamar wata ƙaramar yarinya, haka hawaye ke tsiyaya daga cikin cikin idanunta, hannunta Ummi ta kama suka fice daga cikin ɗakin, anan falo suka samu Raleeya tsaye. Ummi na riƙe da hannunta, yayinda Raleeya ka biye dasu abaya, haka suka fito zuwa compound ɗin gidan, har jikin motar tasa suka ƙarasa, still hawaye Zaleeha take, Ummi kuwa na riƙe da hannunta, murfin motar Ummi ta buɗe tare da sanya Zaleehan aciki, ganin ankawo masa ita kusa dashi ne, ya sashi ɗago kansa ya dubi Ummi, amatuƙar shagwaɓe ya ɓata fuska, cikin body language ɗinsa yace wa Ummi da ke kallonsa,
"Ni Ummi me yasa zaki kawomin ita kusa dani, baganan gidan gaba ba, dan Allah Ummi kisata agaba, ni banason ta zauna akusa dani." Daƙuwa Ummi tayi masa, tare da kama haɓanta, sosai take mamakinsa itakam, musamman ma yanzu da ya ari halin da ba nasa ba ya yafa. Sake ƙara shagwaɓe fuska yayi, cikin ransa yake ta ƙunƙuni, wanda ko bakin zuciyarsa bai je ba, dan duk abun da yakeyi pretending ne kawai, sam baisa azuciyar sa ba.
Allah ya kiyaye Ummi tayi musu sannan Sule driver yaja motar suka fita daga gidan. Saida su Ummi suka ga, fitansu kafun suke komawa cikin gida.

Koda tafiyan nasu tayi nisa, ƙanƙame jikinta waje ɗaya tayi, saboda sanyin AC'n dake tashi acikin motar yaso ya yiwa jikinta yawa, gaba ɗaya bata wani cikin nutsuwarta, domin suna fita daga cikin gidan na Ummi taji gaba ɗaya zuciyarta ya karye, haka hawaye keta fita daga cikin idanunta, yana sauƙa akan fuskarta, daga gefe guda kuwa daddaɗan ƙamshin turarensa ne ya gauraye numfashinta, haka take ta sakin sheshsheƙan kuka ahankali.

Saifuddeen kuwa, duk da kasancewar bai ɗago kai ya kalleta ba, amma duk wani abu da takeyi, yana lure da ita, amma azahirance yi yayi kamar baisan da wata halitta agefensa ba, itakuwa gaba ɗaya damuwa ya cika mata zuciya, hakanan taji tana son kallonsa, amma wani irin abu me kama da tsoro ya hanata kallon sa, wanda kuma tunda take dashi bata taɓa jin irin hakan a dangane dashi ba.
Cusa kanta atsakankanun cinyoyinta tayi, tana me sake sakin sheshsheƙa, can cikin zuciyarta kuwa sunan Allah. take ta faman ambato.

Shikuwa Saifuddeen text message ya turawa Dirankadi kan cewa. "Yana neman al'farma idan yana gida, yanaso yazo ya ɗaukesa, akan maganan Zaleeha, dan suje su bawa Baba Malam haƙuri, saboda yana fushi da'ita sosai, sannan kuma idan yaje shi kaɗai baisan mezai faɗawa Baba Malam ɗin ba, wataƙila ma balallai Baba Malam ɗin ya sauraresu ba."
Cikin fahimta kuwa Dirankadi yace masa. "Babu damuwa Sai sunzo ɗin, dama fita zaiyi, amma zaijirayi zuwansu.."

Sosai kuwa Saifuddeen yaji daɗi, hakan yasa ya ɗan taɓa Sule driver, Juyowa Sule driver'n yayi yana fuskantar sa, miƙawa Sule driver'n wayarsa wanda yayi rubutu akan screen ɗin Yayi,
koda Sule driver ya karanta saƙon jinjina kansa yayi, cikin kulawa yace.
"Angama ranka ya daɗe."
Nan take kuwa ya karkata akalar motar suka nufi gidansu Ishaq.
Koda suka ƙarasa gidan nasu Ishaq kuwa, nan suka samu harma Dirankadi'n ya shirya, su kawai yake jira, koda Saifuddeen ɗin ya buƙaci da Dirankadi'n ya shiga motarsa, cewa yayi dashi.
"A'a zaije da tasa motar, saboda daga gidan su Zaleehan zai wuce wajen aiki, saboda haka amotarsa zai tafi." Saifuddeen ne yayiwa Sule driver, alamar cewa ya yiwa Zaleehan magana tazo ta gaida Dirankadi ɗin, haka kuwa akayi Sule driver da kansa ya buɗe mata murfin motar ta fito, har ƙasa kuwa ta durƙusa ta gaishe da Dirankadi'n. Fuska asake ya amsa mata, tare dayi mata ta'aziyyan rasuwar Adda Maryam, haka ta amsa masa cikin yanayin sanyi, dan aɗan kukan nan da tayi, har muryarta ta dashe.
Haka dai Dirankadi ya shiga motarsa, itakuma Zaleehan ta koma motar su ta zauna tare dayin jigum, saboda zuciyarta dake ƙara tsinkewa, Nan dai suka kama hanyar gidansu Zaleehan, inda motar Dirankadi ce agaba. Basuyi wani tafiya me nisaba suka iso gidan, jin motar ta tsaya ne yasata ɗago kanta amasifar tsorace, aikuwa ganinta acikin compound ɗin gidansu yasa gaba ɗaya duk wani kuzarinta ya kau, yanayin yanda zuciyarta ke bugawa kuwa, idan kaji zakai tunanin cewa faso ƙirjinta zatayi ta fito waje, sosai jikinta ya ɗauki rawa, tsoro ne yagama lulluɓeta, makomarta kawai take tunawa. Dirankadi ne yafara fitowa daga cikin motarsa, ƙarasowa jikin motar Saifuddeen ɗin yayi, cikin kulawa yace. "Saifuddeen ku zauna kada ku fito, duk yanda ake ciki zan maka text sai ku shigo."
Kai Saifuddeen ya jinjina masa alamar gamsuwa, Nan Dirankadi ya nufi cikin gidan, kaitsaye ɓangaren Baba Malam ya nufa.
Acikin falon Baba Malam kuwa, shi da Ya Ahmad, da kuma Malam Adam ne zaune, gefe dasu kuwa Ya Ameenu ne wanda ayanzu ya zama kamar wani mutum mutumi, komai nasa ya sanja, ya zama wani mutum me sanyi, magana kuwa inbanda "Eh, da kuma A'a."
ba bu abun da yake iya fitawo daga bakinsa, sosai mutuwar Adda Maryam ɗin ya maidashi wani silently, hakanne ma yasa gaba ɗaya dangim suke masifar jin tausayinsa.

Dirankadi ne ya shigo cikin falon bakinsa ɗauke da sallama, amutunce su Baba Malam da kuma Malam Adam suka amsa masa, cikin mutum tawa Baba Malam ya taso ya tarosa, tare da basa hannu sukayi musabaha, kujera Baba Malam ya nuna masa, zama yayi tare da bawa su Yaya Ameenu hannu suka gaisa, sake musu sabon gaisuwa yayi, tare da sake bawa Baba Malam hannu suka gaisa amutunce, hira kaɗan sukayi, kafun Dirankadi ya gyara zamansa, cikin nutsuwa ya dubi Baba Malam, a mutumce yace.
"Kayi haƙuri Malam Bashir, domin ba haka kawai nake tafe ba, alfarma muka zo nema awajenka, wanda kuma nake saka ran cewa Insha Allah, zaka mana ita."

Ɗan jim Baba Malam yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, tabbas Dirankadi nada kima da kuma mutumci a idanunsa, saboda haka zai iya yimasa alfarma kuwa kowacce iri ce, saidai kuma ayanzu baisan yaya girman alfarmar take ba, cikin halin dattako da nutsuwa irin nasa yace.
"Ai Dirankadi kafi ƙarfin al'farma awajena, saidai kuma bazanyi hanzari ba, ina jinka wace al'farma ce wannan, dahar yasa ka taso da kanka kazo, ai da ko awaya kaƙira ka sanar dani zan iya yi maka ita."
Kai Dirankadi ya jinjina cikin jin daɗi yace, "Nagode ƙwarai da wannan karramawar Malam Basheer, yanzu kuwa zanyiwa abokan tafiyana magana dan su samu shigowa."
Nan ya ciro wayarsa ya turawa Saifuddeen text akan cewa.
"Su shigo."
Koda Saifuddeen ya karanta text ɗin na Dirankadi, buɗe murfin motar yayi ya fita, dan dama tuni Sule ya fito masa da wheelchair ɗinsa, ganin haka yasa Sule zagayawa ɓangaren da Zaleehan take ya buɗe mata murfin motar, asanyaye kuwa ta fito daga cikin motar, gaba ɗaya jikinta rawa yake saboda fargaba da kuma tsoro.
Haka suka nufi ɓangaren Baba Malam ɗin, Saifuddeen na gaba, ita kuma tana biye dashi abaya, da ƙyar take iya taka ƙafafunta da suka mata nauyi, ga kuma wani masifaffen tsoro haɗi da faɗuwar gaba da takeji.
Dai-dai sun kawo ƙofar shiga falon ne, tayi saurin kamo hannun sa, ɗan tsayawa yayi tare da juyowa ya kalleta, wasu irin hawaye masu zafi ne suka silalo daga cikin idanunta, sosai jikinta ke rawa, harta laɓɓan bakinta ma rawa suke, idanunsa ya ɗan lumshe jin yadda ta rumtse tafin hannunshi cikin nata tana mammatse mishi hannun da jan yatsunshi cikin yanayin tsoro, ajiyan zuciya ya sauƙe tare da girgiza mata kansa, hannunta yaɗan murza sannan suka nufi cikin falon Baba Malam ɗin.
Jin an taɓa ƙofar falon yasa dukansu suka zubawa ƙofar idanu, dan ganin me shigowa, Ganin Saifuddeen Yasa Baba Malam ɗan sakin murmushi, take kuma saiga Zaleeha ta biyo baya, dan dama har yanzu Saifuddeen ɗin na riƙe da hannunta, da sauri Baba Malam ya ɗauke kansa daga kallonta, take yanayin annurin fuskarsa ya sauya, jiyayi kwata kwata ma bayason ganinta hakan yasa ya kawar da kansa gefe.
Saifuddeen na riƙe da hannunta suka ƙaraso cikin falon, har gaban Baba Malam ɗin ya ƙaraso, ita kuwa Zaleeha kanta na ƙasa, hawayene kawai keta tsiyaya daga cikin idanunta, sake hannunta Saifuddeen yayi tare da sauƙa akan wheelchair din nasa, ya yasa guiwowinsa aƙasa, itama Zaleehan zubewa tayi aƙasa, wanda hakan yasa kusan rabin jikinta ya shiga jikin Saifuddeen, gaba ɗaya idanunta sun rufe, ƙwalla ne kawai acikinsu, hawaye wani na koran wani kaman an kunna sabon famfo.
Kifa kanta tayi akan ƙafafun Baba Malam dake zaune, lokaci guda ta saki wani irin kuka mai taɓa zuciya, cikin kukan tace.
"Dan Allah Baba Malam kayi haƙuri ka yafemin, kar in mutu da fushinka na tuba ka yafemin ko zan samu kekyawan rayuwa, Idan baka yafemin ba nima mutuwa zanyi, wallahi nayi nadamar abun da na aikata, na tuba Ka jiƙaina ka yafemin!!."
Taƙare maganar tana Kuka sosai kamar ranta zai fita.
Cikin fushi Baba Malam ya janye ƙafansa baya, hakanne yasa ta ɗago da kanta, tana kuka sosai haɗe hannuwanta waje ɗaya tayi alaman roƙo, cikin matsanancin kukan ta ɗaga idanu ta kalli Malam Adam, da kuma Ya Ahmad gani tayi sun kauda kansu daga kallonta, alaman har yanzu suna fushi da ita, duƙar da kanta tayi tana wani irin kuka mai taɓa zuciya, hakanne yasa Saifuddeen ɗaura hannunsa akan nata ya riƙe ƙam, jin haka yasa ta sake mannewa a jikinsa, tare da kama hannunsa tana jijjigawa kuka take sosai, wanda hakan yasa yakejin wani abu na taɓa zuciyarsa, kowani ɗigan hawayenta ɗaya tamkar ɗigan narkakken dalma ne, akan zuciyarsa haka yakeji.
Dirankadi ne ya gyara zama zuciyar sa cike da tausayin Zaleehan, saboda yanda take kuka, wanda dagani kasan daga cikin ƙarƙashin zuciyarta da kuma ranta yake fitowa.
Asanyaye yace.
"Yafiya ga Zaleeha itace al'farmar da nake nema awajenka Malam Basheer, haƙiƙa Zaleeha ta aikata ba dai-dai ba, wanda alokacin ni kaina saida naji babu daɗi, amma ayanzu tabbas ta gane kuskurenta kuma tayi na dama, shikansa wanda ta gudawa ɗin na tabbatar da cewa ya yafe mata, tunda gashi shida kansa ya ɗaukota dan su zo su baka haƙuri, dan Allah Malam Basheer ku yafe mata, kada ku manta fa cewa ita macece me raunin zuciya, rashin yafe mata zai iya haifar da wata sabuwar matsalan, abun zaiyi mata yawa, har yanzu Zaleeha yarinyace ƙara ma, damuwa kaɗan zai iya haifar mata da matsala, da wanne ɗaya zataji? da rashin ƴar uwarta ko kuwa da fushin da kukeyi da ita, ayanzu Al'barkarku take nema, bawai ɓacin rai da fushi ba, nidai ina roƙa mata al'farma dan Allah ayafe mata."
Kai Baba Malam ya girgiza, tare da miƙewa tsaye, sam bayajin zai yafewa Zaleeha'n, saboda har yanzu akwai ƙunci da baƙin cikin da ta shayar dashi kwance acikin zuciyarsa, kuma ma baisan niyartaba dole yayi wani abu dan gano meke cikin ranta.
Juyawa yayi da niyar barin falon, cikin bazata yaji an riƙe hannunsa, ɗan juyowa yayi afusace dan yasan cewa Zaleehan ce kawai zatayi mishi haka, amma ga mamakinsa sai yaga Saifuddeen ne, wanda idanunsa gaba ɗaya sun ciko da ƙwalla, sannan sunyi jajir, sakin hannu Baba Malam ɗin yayi, tare da haɗe hannuwansa waje ɗaya alaman roƙo, kansa ya rinƙa jujjuya wa yayinda wayenshi ke gab da zubowa.
Zaleeha kuwa sake shigewa jikin Saifuddeen ɗin tayi, tare da ɗaura kanta akan kafaɗansa, tana wani irin kuka me matuƙar tsuma zuciya, kukanta kuwa shikesa Saifuddeen yaji kansa kamar zai fashe, haka kuma har cikin ransa yakejin kukan nata, ci gaba yayi da jijjigawa Baba Malam kai, alaman yayi haƙuri yayi musu afuwa.

Jikin Baba Malam ne yayi matuƙar sanyi, ganin hawaye acikin idanun Saifuddeen yasa yaji gaba ɗaya tunaninsa ya tsaya, idanunsa yaɗan lumshe tare da komawa ya zauna akan kujera inda ya yi ƙasa da kansa tare dayin shiru. Ya Ahmad kuwa duk yanda yaso shanye kukansa abun yaci tura, dole haka ya saki kuka kaman ƙaramin yaro, dama shi tun farko zuciyarsa me raunice akan Zaleeha, tausayinta ne ke maye ko ina najikinsa, ga kuma jimamin rasuwar Adda Maryam wanda yakejin ta dawo masa sabuwa, kansa ya kifa da jikin kujera yana kuka. Ya Ameenu dake zaune acan gefe kaman mutum mutumi kuwa idanunsa kawai ya zuba musu, shikam aduniya yanajin cewa tunda matarsa ta rasu ta barsa, shikenan duk wani jin daɗi da farinciki sun ƙare masa. Ɗago kai Baba Malam yayi da idanunsa wanda sukai jajur, cikin sanyin murya yace.
"Tabbas kin shayar dani baƙinciki marar misaltuwa, kinyimin abun da duk acikin ƴaƴana babu wanda ya ta ɓamin, kin ƙi zaɓina sannan kika gudu kikabar gidan mijinki ɗanki aurenki ba tare da izinin mijinki ba." farin handkerchief ɗin dake hannunsa yasa, inda ya share ƙwallan dake ƙoƙarin fitowa daga cikin idanunsa. Ajiyar zuciya ya sauƙe, sannan yace.
"Bani zaki bawa haƙuriba, shi kika saɓa kika wulaƙanta aureshi, shine al'jannarki take ƙarƙashin diga-diginsa dan haka shi zaki bawa haƙuri ba niba yafiyarsa zaki nema da kika fita bada izininshi ba, sai ya yafe miki kafin ni in yafe miki".
Da sauri ta juyo ta fuskanci Saifuddeen murya na rawa kana murya a disashe tace.
"Kayi hakuri Hamma Saif ka yafe min in sha ALLAH har iya raina da mutuwata bazan sake fita ba saida izininka ko bakin gate bazan sake zuwaba saida izininka".
Haɗe hannayenta tayi alamu roƙo kana hawaye na kwaranya a fuskarsa, kanshi ya rinƙa jujjuya mata yana mai jin zazzafan tausayi ya, murya na rawa ta kuma cewa.
"Dan Allah Hamma Saif ka yafe min".
Kanshi ya kuma jujjuya tare da mata alamun ya yafe mata duniya da ƙiyama,
sai kuma ta juyo da sauri ta kalli Baba Malam murya a harde tace.
"Baba Malam ka yafe min shi yace ya yafe min".
Gyara zama Baba Malam yayi kana yace.
"To in na yafe miki me kuma shirinki na gaba zaki sake, gudawa ne? Ko dai kinyi tuba na gaskiya ne zaki zauna ɗakinki, ko bazaki zauna ba?."
A hankali ta sunkuyar da kanta zazzafan hawaye na zuba murya na rawa tace.
"Har Abadan bazan sake guduba, zan zauna iya raina da mutuwata har sai dai in na mutune zan bar gidanshi babu inda zanje duk rintsi koda ko ba daɗi zan zauna Baba malam zanyi biyayya kwatankwacin wanda Adda Maryam tayi maka, koda daɗi ko ba daɗi zan zauna."
Gaba ɗaya jikinsu yayi sanyi hatta shi kanshi Baba malam tausayi ta ya rufeshi,
cikin sanyi yace.
"Kin san yayi aure bayan guduwanki?".
Cikin kuka tace.
"Ban saniba saida naje gidanshi naga matar da ɗanshi."
Kai ya jinjina tare da cewa.
"To ki koma gidanki ɗakinki, ban kuma yarje miki fitina da abokiyar zama kina ki zauna lafiya da ita da ƙanneshi da yayunshi, kada inji wani abu tsakanin ki da abokiyar zamanki, kada ki tsokaneta ko kaɗan in kuma itace ta tsokaneta ki mata uzuri ki yafe mata kada kice zaki rama duk abinda tayi miki".
Cikin wani masifeffen kuka tace.
"To Baba Malam in sha Allah zaka sameni mai bin umarni ka".
Kanshi ya gyaɗa cikin tausayinta a ranshi sabida kukanta na ƙunshi da abubuwa da dama, cikin sanyi yace.
"Koda ki tauye haƙƙin mijinki a kanki Zaleeha kada ki haneshi abinda duk Allah ya halattamishi a kanki".
Cikin rawan murya tace.
"To in sha Allah zan zauna dashi sai kuma in shine yace baya sona."
Wani irin tausayinta ne ya rufesu baki ɗaya cikin taushin lafazi Baba Malam yace.
"Tabbas kinci al'barkacin Dirankadi da kuma Saifudddeen, saboda haka kije na yafemiki duniya da ƙiyama, ina roƙon Allah Ubangiji kuma ya shiryeki, Ya sa miki imani azuciyarki ya baki zaman lfy da mijinki da abokiyar zamanki,
haƙiƙa kin ƙuntatawa zuciyata, kin shayar da ahalinki baƙin ciki, Maryam harta koma ga ubangijinta bata taɓa saɓawa maganata ba koda kuwa sau ɗaya ne, na aurar da ita ga zaɓina, kuma ta amince duk da cewa bataso amma tayi Mini biyayya, haka kuma bata taɓa saɓawa mijinta ba, gashi Allah ya ɗauketa adai-dai lokacin da kowa yake da buƙatanta, Ya Allah kajiƙan Maryam kasa al'janna tazamo makoma agareta...".
Kukane ya ƙwacewa Baba Malam ɗin, wanda hakan kuwa yayi matuƙar taɓa zuciyoyinsu, hakanne kuma yasa hawayen dake cikin idanun Saifuddeen samun daman gangarowa, zuwa kan ƙuncinsa, Zaleeha kuwa kuka take sosai kaman ranta zai fita, haka ma Ya Ahmad, wannan karon harta Malam Adam da Dirankadi saida sukayi hawayen, tausayin ahalin.
Ya Ameenu kam, bai iyayin kuka ba, saboda ayanzu kukan zuci yake, wanda yafi na fili ciwo, adai-dai wannan lokacin kuwa shi kaɗai yasan me yakeji. Cikin matsanancin kukan, ta rarrafa inda ta ƙarasa gaban Ya Ahmad wanda ke kuka sosai, tana zuwa ta kifa kanta akan cinyansa, tana kuka sosai har kaman zata shiɗe, hannu Ya Ahmad ɗin yasa ya dafa kanta, lokaci guda kuwa ƙarfin kukansa ya ƙaru, gaba ɗaya falon haka ya ɗauki shiru babu abun dake tashi sai sautin kuka anrasa me rarrashin wani, hatta Malam Adam da Dirankadi gaba ɗaya jikinsu amace yake, gaba ɗaya zuciyoyinsu sunyi rauni.

Da ƙyar Baba Malam ya iya share hawayensa, cikin muryarsa da ta ɗan dashe yace.
"Nayafe miki Allah ya yafe mana baki ɗaya, ki tashi ki koma ɗakin mijinki, Sannan in mijinki ya amince miki duk sanda kuka samu lokaci kuje gidan Maryam ta barmin wasiyar tayi miki ajiya cikin durowar ta ta jikin gado."
Hannu yasa ya share hawayenshi kana yaci gaba da cewa.
"Kuma matuƙar kika sake mugun saɓawa Saifuddeen ba irin wanda dole akwaishi tsakanin ma'aurataba wallahi! bazan taɓa yafe miki ba Zaleeha, kuma daga wannan lokacin kiceri kanki daga mazaunin ƴata!!!."

Jin furucin Baba Malam ɗinne yasanya cikin kuka ta ɗago daga jikin Ya Ahmad, dawowa gaban Baba Malam ɗin tayi tare da durƙusa guiwowinta a ƙasa, kanta ta ɗaura ajikin Baba Malam ɗin tana wani irin kuka me ɗaga hankali, gaɓa ɗaya jikinta rawa yake, ga kuma wani sheshsheƙa da take saki wanda yasa numfashinta keyi kaman zai ɗauke. Cikin kukan da kuma muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Nagode Baba Malam! Nagode sosai da ka yafemin, kuma insha Allah zaka sameni me biyayya agareka dashi Hamma Saif..."
Kuka take sosai harda majina, Ahankali Saifuddeen ya haɗe hannuwansa, tare da ɗan lumshe idanunsa, alaman godiya, still kuma hawayene kwance akan fuskarsa. Murmushi Baba Malam yayi tare da sanya hannu ya shafi kan Saifuddeen ɗin, tabbas Saifuddeen mutunne me nagarta, da kuma zuciyar imani, sai yanzu yake ƙara aminta cewa bazai taɓa

Please Login or Register in order to submit comment