Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saƙon idanunsa ya lumshe tare dayin shiru, kamar zaice wani abu kuma, ataƙaice ya rubuta.
"Okay saida safe jekiyi bacci."
Daga haka ya kashe data'n sa, tare da aje wayan gaba ɗaya.
Inda ya haurawa saman gado ya kwanta.
A ranshi yake cewa.
"Hmmmm kina dai da abin da kikeso a jikina, fitinanniya kawai mai idon cin maza."

Ameena kuwa ganin ya sauƙa online yasa ta lumshe idanunta, daɗi da farin ciki su suka cika zuciyarta, haka tayita juyi akan gadon, wani irin shauƙinsa ne ke damunta, da haka tayi bacci.

Tabbas akullum kwanaki ƙarewa suke, haka kuma lokaci na shuɗewa, akwana atashi asaran me rai, yau dai ya kama saura kwana uku kacal bikin Ameena da Saifuddeen.
Inda daga ɓangare biyu na gidajen duk shirye shiryen bikin suke.
Babu ma kamar gidansu Ameena, inda Ameena'n ke karɓan gyara na musamman, sosai ake mata gyaran jiki, hakan yasa fatarta tayi fresh.

Ɓangaren gidansu Saifuddeen kuwa, su Ummi ne kaɗai ke kiɗa da rawansu, Saifuddeen iyakacinsa ido, tunkuwa ranan da yayiwa Ameenan magana ta Whatsapp baisake bi ta kanta ba.

Zaune suke su dukansu Afalon Ummi, nan Ahmad ya shigo inda yake ƙara sanar dasu batun tashinsu don dama ya kammala gidansa tuntuni, Nan fa Saifuddeen ya kafe kan cewar Ahmad ɗin babu inda zaije, ae tunda ya saka baki ake ƙoƙarin yi masa auren dole dolensa kuwa ya zauna agidan.
Duk kuwa yanda Ahmad yaso Saifuddeen da Ummi su barshi ya koma gidansa sun ƙiya.
Nandai Saifuddeen yace Hayatuddeen ya dawo ƙasa, su kuma Ahmad ɗin su koma sama.
Hakan kuwa akayi, inda aka gyara duka ɓangare biyun, Raliya ta tattaro kayanta suka dawo sama.
Hayatuddeen kuwa ƙasa ya dawo.

Can ɓangaren su Ahmad ɗin kuwa aka gyarawa Amarya Ameena.

Sannu-sannu bata hana zuwa saide adaɗe ba'a je ba.
Rana kuwa bata ƙarya.
Yau yakasance Alhamis, inda gobe Jumma'a ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena.
Acan Abuja yau Ameena ta gudanar da walima, inda aka yi wa'azi mai ratsa jiki, sosai kuwa waliman ya ƙawatar, don Ahmad dakansa ya tura mata kuɗi a account ɗinta, inda yace tayi duk wani hidima da takeso. Kana kuma yaune akaiwa Amarya jere, domin kuwa Babanta da kansa yayiwa kamfanin masu saida furnitures magana, ta online suka sai kayan, wanda Ameenan da kanta ta zaɓi kalan da takeso.
Ma'aikatan kamfanin kuwa suda kansu suka zo har gidan su Saifuddeen ɗin suka jera mata kayanta, sosai kuma yayi kyau.

Washegari.
Jumma'a.

Ranan yau takasance jumma'a, wanda kuma ayau ɗinne za'a ɗaura Auren Saifuddeen da kuma Ameena.
Tun safe kuwa Saifuddeen yaƙi fitowa, inda ya ce bashi da lafiya, sanin cewa Ameenan ba budurwa bace, kana kuma ba agari za'ai ɗaurin auren ba, yasa sam su Bappa Ali basu matsa masa ba.

Ƙarfe tara dai-dai jirginsu zai tashi.
Baba Malam, Bappa Ali, Dirankadi, Malam Adam, Baba Bello, Ishaq, Ahmad, Wareesu, Saleesu, Hayatuddeen, sune waƴanda zasuje ɗaurin auren, sai kuma Adda Rahama da Aunty Meena, wanda sune zasu ɗauko amarya.
Ƙarfe tara acikin jirgi tayi musu, inda suka ɗaga zuwa garin na Abuja.

Sun isa Abuja ƙarfe goma dai-dai, inda kuma za'a ɗaura auren ƙarfe 11 na rana dai-dai.
Ya Ahmad ne yazo ɗaukansu kai tsaye Asokoro gidansu Amarya suka nufa.
Nan suka tarar da ƙofar gidan ɗinke da jama'a, ƴan ɗaurin aure.
Alhaji Naseer da kuma mahaifin Ameena Alhaji Sadam su suka tarbesu cikin mutum tawa, inda su Adda Rahama kuwa suka wuce cikin gidan.

Kamar yanda aka sanya lokaci, ƙarfe sha ɗaya dai-dai jama'an dake wajen suka shaida ɗaurin auren Saifuddeen da Ameena, akan sadaki naira dubu hamsin.
Nan fa jama'a suka dinga sanya alkahiri, da nema musu zaman lafiya.

Acan cikin gida kuwa, amarya Ameena tayi kyau don an tsantsara mata meckup dai-dai misali, inda ta suturce jikinta da shiga ta al'farma, balaifi tayi kyau don kuwa sam bata da muni, saidai kuma bata da azababben kyau.

Jirgin ƙarfe ɗaya zasu biyo don dawowa Gombe, hakan yasa Dady wato Alhaji Naseer da kuma mahaifinta suka jata gefe inda sukayi mata nasiha sosai mai ratsa jiki.
Harma da ɗan guntun ƙwallanta.
Daga haka su Adda Rahama suka kamata, inda aka sanyata a mota, ƴan uwanta biyu ne zasuyi mata rakiya.
Akwai auntynta wanda ake ƙira da Aunty Zubaida, sai kuma ƙanwar mamanta, Aunty Zainab, nan dai suka ɗunguma dukansu zuwa airport.
Ƙarfe ɗaya kuwa dai-dai jirginsu ya tashi, zuciyar Ameena cike da kewar gida.

Sun iso cikin garin Gombe lafiya, inda lafiyayyun motoci har guda shida suka zo ɗaukarsu, Baba Malam dai kaitsaye gidansa aka wuce dashi shida Malam Adam, sai kuma Dirankadi da Ishaq, wanda suma kaitsaye gida suka wuce.

Koda suka ƙaraso, sosai ƴan uwan Ameenan suka yaba da kyaun gidan nasu Saifuddeen, nan dai kaitsaye part ɗin Ummi aka wuce da ita.
Tarba mai kyau Ummi tayi musu, tare da nuna musu ƙauna, haka ta jawo Ameenan jikinta cikin kulawa tayi musu addu'an samun zaman lafiya, da kuma zuri'a ta gari.

Daga nan kuma Adda Rahama tayi musu jagora zuwa ɓangaren Ameenan.
Nan ma sun yaba da tsaruwan part ɗin nata.

Kasancewar waƴanda sukai mata rakiyan ba kwana zasuyi ba, ƙarfe 5 na yammaci dai-dai sukabi jirgi inda suka koma Abuja.

Nan fa akabar Amarya Ameena ita kaɗai aɗakinta.

Yayinda ƴan tsirarun mutanen da sukazo bikin, tuni suma sun koma, domin dama Ummi batayi wani gayya ba, Aunty Mina ma tabi Bappa Ali sun koma dukku.
Haka gidan ya rage, daga Ummi, Adda Rahama, sai Raliya da kuma Hayatuddeen.
Shikuwa Saifuddeen tuni dama yana ƙule acikin ɗakinsa.


Koda akayi sallan Isha kuwa, saiga su Ahmad da Ishaq wai sunzo yi masa rakiya zuwa ɗakin amarya, abun ma dariya ya basa, nan dai ya haɗe gabar da yamma, inda yace.
"Baya buƙatar rakiyan nasu."
Duk yanda sukaso rakasa wajen Amaryar ƙiyawa yayi.
Haka suka tafi suna masa dariya.

Part ɗin Ummi ya nufa inda yasamesu zaune su dukansu afalo.
Cikin salon shagwaɓansa, ya dubi Ummin, gane abun dayake nufi yasa tace da Raliya ta ɗauko masa flask ɗin coffe ɗinsa, don dama tuni ta haɗa masa.
Yana amsa kuwa ya juya inda ya nufi part ɗinsa.
Ta ɓangaren Zaleeha yabi inda yashiga falonsa, kai tsaye ɗaki ya wuce, kayan jikinsa yaɗan rage sannan yasha coffee ɗin, kan gadonsa ya haye tare da rufawa kansa blanket, sam babuma maganar zuwa wajen Ameena acikin ransa, don kuwa ko Zaleeha dayake mutuwar so, ranan farko baije ɗakinta ba balle wata Ameena da yasan jira take ta ganshi ta mishi fyaɗe dan ya dai san abinda take so.

Can ɓangare Ameena kuwa koda tayi sallan isha, komawa tayi ta zauna jigum, kaɗaici ne ya dameta, tun tana zaune harta gaji ta kwanta, take kuwa bacci ya ɗauketa.

Washegari.

Tunda ya fita sallan asuba bai dawo gidan ba, can ya zauna amasallaci inda ya shiga rera karatun alƙur'ani.

Ameena kuwa tana idar da sallah, ɗakinta ta kimtsa, sannan ta zura doguwar hijabinta ta fito.
Nanne ta shiga ƙarewa ɓangaren nata kallo.
Ganin wata ƙofa acikin falon nata yasata buɗewa, nan ta tsinci kanta cikin wani haɗaɗɗen falo wanda haɗuwarsa ya zarce misali, ƙamshinsa kaɗai da taji yasa ta fahimci cewa ɗakinsa ne.
Ƙarewa falon kallo tayi sosai, sannan aɗaɗare ta nufi wata ƙofa dake cikin falon, wanda tana kyautata zaton cewa bedroom ne.
Aɗan ɗaɗare tayo knocking, amma shiru ba'a amsa mata ba, tunowa da tayi cewar bazai jita ba koda yana ciki hakan yasa tatura ƙofar ahankali tare da tura kanta ciki, ni'imtaccen ƙamshin daya daki hancinta ne yasata lumshe ido, ƙara kutsawa cikin ɗakin tayi, baki ta buɗe tana ƙarewa aljannar duniyar ɗakinnasa kallo, komai dake cikin ɗakin ya haɗu, ganin baya cikin ɗakinne yasa taɗan sauƙe ajiyar zuciya.
Komai dake cikin ɗakin nead, kan gadonne kawai dayake aɗan hargitse, cikin nutsuwa ta shiga kimtsa masa gadon nasa, sabon bedsheet ta shumfuɗa masa, kana ta sake share ɗakin.
Nan ta fesa air freshner'n da ta gani asaman mirror'n ɗakin.
Take ɗakin yasake ɗaukan ƙamshi.

Fita tayi daga ɗakin inda kaitsaye ta wuce ɓangaren Ummi don ta gaida ita.
Tana shiga kuwa ta samu Ummin afalo.
Cikin ladabi ta rusuna har ƙasa tagaishe da Ummin, cikin jindaɗi haɗi da ƙaunarta Ummi ta amsa mata, tare da tambayanta ya kwanan baƙunta.
Cikin al'kunya tace.
"Alhamdulillah."
Dai-dai lokacin kuwa saiga Saifuddeen din yashigo wanda dawowansa daga masallaci kenan.
Afakaice Ameena tasaci kallonsa, shikuwa bai kalli inda take bama saima gaishe da Ummi da yayi.
Fuska ɗauke da murmushi Ummin ta amsa.
Cikin matsanancin nuna girmamawa Ameena.
Tayi ƙasa da murya aladafce tace dashi.
"Ina, kwana!."

Muskarshi ya ɗan yamutsa tare da taɓe fuska, a hankali ya ɗan ɗago ida nunshi ya kalli fuskarta, kauda kanshi yayi dasauri kana ya...!





By
*GARKUWAR FULANI*
[8/25, 1:58 PM] A: Speɗɗbl
Ya buɗe lips ɗinshi a hankali tare da haɗesu alamar lfy.
Lumshe idanunta tayi ganin yadda ya motsa jajayen laɓɓansa tabbas tasan zuciyarta tayi kewar ganinsa, sosai taga ya ƙara kyau da kuma cikar haiba, kwarjininsa ya sake bayyana acikin idanunta, don kuwa ga sajen dake kwance akan fuskarsa ya kwanta lub-lub, gwanin ban sha'awa.
Aladaf ce ta miƙe daga durƙuson da take, cikin nutsuwa ta nemi hanyar fita daga cikin falon.
Har zuwa yanzu ko inda take bai kuma kalla ba, Ummi kuwa tana kula dashi sarai.
Ameenan na fita Ummi ta dubeshi da kyau, cikin kulawa da nazartan shi da kyau tace.
"Bazan dai gaji da tuna maka cewar Ameena amana ce agare ka, saboda duk wata matar mutum amanarsa ce, saboda haka kada kace wai don itaɗin ba zaɓinka bace zaka wuƙalanta-ta."

Ɗan ɓata fuska yayi tare da shagwaɓewa, kana ya gyaɗa kanshi alamu to ƙoƙarin ƙarasawa dinning area ya somayi, duban tsab Ummi tayi masa, cikin kulawa tace.
"Ina kuma zaka? ai dai mungama yin break fast da kai, kana da mata saboda haka nasa Raliya ta sa muku abincinku daban a food flask ta kai maka kaje can kaci abincin da matarka."

Kasancewar yana kallon fuskar Ummin tasa, hakan yasa shi fahimtar me take cewa.
Shagwaɓe fuska yayi, tare da ɗan waro idanunsa waje.
Sam bai tsammaci haka ba, haƙiƙa yafara tunanin cewa. Aurensa da Ameena zaisa su Ummi su ɗauke duk wani tallafin da suke basa.

Kamar wani ƙaramin yaro haka ya ɗan tura baki.
Dai-dai lokacin Raliya tafito daga cikin kitchine hannunta ɗauke da babban food flask ɗin da abincin nasu ke ciki.

Dubanta Ummi tayi tare da ƙwalawa Hayatuddeen ƙira, cikin mintuna kaɗan Hayatuddeen ya fito daga cikin ɗakinsa.
Kulan Ummi tace da Raliya ta basa, yakai can ɓangaren Ameena'n.
Hakan kuwa akayi inda Hayatuddeen ya karɓi kulan ya fita.
Ganin da gaske suke, yasa Saifuddeen ɓata fuska, ganin yanda Ummin nasa ta tsaresa da ido ya sa shi tura kekensa, kai tsaye ya nufi hanyar barin falon.

Ameena kuwa tana barin part ɗin Ummi kai tsaye part ɗinsu ta dawo, anan cikin falonta ta zauna, inda ta kunna babban tv plasma ɗin dake cikin falon, ɗan lumshe idanunta tayi, tare da sauƙe ajiyar zuciya, har zuwa yanzu tana mamaki, wai ita Ameena ce ke zaune cikin gidan su Saifuddeen kuma take amsa sunan matarsa tabbas wanda ya mance Allah ya wahala.

Hayatuddeen ne ya shigo cikin falon bakinsa ɗauke da sallama.

Fuska cike da murmushi Ameeena'n ta amsa masa.
Ƙarasowa cikin falon yayi, tare da aje mata haɗaɗɗiyar kulan dake hannunsa agabanta.
Cikin kulawa yace.
"Matar Hamma na ina kwana."
Hararan wasa ta watsa masa, tare da cewa.
"Yau kuma da wani salon ka ɓullo."

Ɗan dariya yayi tare da kama waist ɗinsa, cikin salon tsokana irin nasa yace.
"Eh mana, nasan ae yanzu haka daɗi kikeji kin auri min Hammana ko, shiyasa ae na faɗa miki hakan, don ki ƙara jin daɗi da kyau."

Murmushi tayi tare da cewa.

"Nidai zan so ganin ranar da zaka zamo very gentle man Hayatu."

Idanu Hayatuddeen ya ɗan zaro, cikin sangarta yace.
"Hayatu? nine ma Hayatu, gaskiya banson Hayatu, ae da Hamma ne bazaki ce masa Saifu ba."

Dariya sosai Ameena tayi, don dama ta faɗi hakanne don kawai taga rigiman Hayatuddeen ɗin, sosai sakalci da kuma sangartansa na auta ke burgute.

Cikin zunɓura baki Hayatuddeen yace.
"Dama hira nazo tayaki tunda kuwa kika ƙirani da Hayatu na fasa."

Cikin dariya tace.
"To menene sunanka idan ba Hayatu ba? dan ma banƙiraka da Hayatutu ba."
Jin haka yasa Hayatuddeen ƙulewa, bakinsa ya turo gaba, cikin halayensa na auta, yace.
"Keda Hamma na."
Daga haka yafice daga cikin falon.
Murmushi Ameena tayi tare da girgiza kanta, sosai takejin dadin hira da Hayatuddeen din.

Duban kulan daya kawo tayi, tare da buɗewa.
Kasancewar kula ce irin me hawa huɗun nan, hakan yasa ko wanni ɓangare da kalan abincin dake cikinsa.
Ganin abincin nada yawa ne hakan yasa ta tabbatar da cewa, bana ta ita kaɗai bane, jitayi zuciyarta tayi mata sanyi domin koba komai zasu keɓe waje guda dashi.
Komawa tayi ta zauna tana me jiran shigowansa.

Saifuddeen kuwa yana barin falon Ummin nasa, ta ɓangaren Zaleeha yabi inda ya wuce part ɗinsa.
Afalonsa ya zauna, bayan ya ƙarasa gaban fridge ya ɗauki goran fresh milk, ahankali yake shan fresh milk ɗin, kana yana ɗan lumlumshe idanunsa, yana kammalawa ya ɗauki laptop ɗinsa, nan ya maida hankalinsa sosai wajen bin diddigin layukan da ƴan kinnafin ɗin da suka sace babbar jikar Matawallen gombe,
wanda shine sabon aiki da DSS suka bashi kuma al'ahamadulilla ya gano komai ya kuma miƙashi hannun SS.
sam baiji cewa zai je wajen Ameenan cin abinci ba, fresh milk ɗin daya sha ma ya ishesa.
Dan yana sane da ita kallon kura da akuya take mishi, ya lura ji take kamar ta cinyeshi ɗanye.

Can ɓangaren Ameena kuwa, tun tana zaune har ta gaji ta kwanta, duk kuwa zaman jiran zuwansa take.
Abu kamar wasa, sai gashi ana neman share kusan awa ɗaya babu ƙyallinsa, jikinta ne yayi sanyi, hakan yasa taɗan tsakuri abincin kaɗan taci.
Tana kammala wa kuwa ta wuce ɗaki.
Kwanciya tayi zuciya tasan ta cike da saƙe-saƙe kala kala, so take tasan ina matarsa da ya aura wata daya baya, dam taji zuciyarta ta buga sabida tuno da kyau da tsari da haibar Zaleeha da ta gani a status ɗin Hayatuddeen, to ina taje? Wa zata tamɓaya taji ina take dan ranta na raya mata wani abun akan matar da take tsananin jin kishinta.
Ahaka bacci ɓarawo ya ɗauketa.

Ba itace ta farka ba kuwa saida aka soma ƙiraye ƙirayen sallan Azahar sannan ta-tashi tayi sallah.
Wanka tayi inda ta tsantsara adonta cikin atamfarta me kyau, mayafi ta yafa ajikinta, kana ta nufi ɓangaren Ummi.

Nan ta iske Ummi zaune a falo, Raliya kuwa na kitchine tana ta faman hada-hadan abincin rana.
Cikin jin dadin sake ganinta Ummi ta tarbeta, hira kaɗan suka ɗan taɓa, sannan ta bi Raliya zuwa kitchine, inda ta shiga tayata suka haɗa abincin rana me rai da lafiya, koda suka kammala ɗakinta ta sake komawa.

Ahaka dai Ameena ta ƙare wunin wannan ranan, inda tana idar da sallan isha ta kwanta.

Ɓangaren Saifuddeen kuwa gaba ɗaya wunin yau ɗin aɗakinsa ya ƙaresa, saboda ko kaɗan bama yason yaje ɓangaren Ummi, tayi masa maganar Ameena.

Washe gari da safe kuwa, kamar yanda tayi jiya haka tayi yau ɗin, domin kuwa tana idar da sallan Asuba, karatu taɗan taɓa, sannan kai tsaye ta wuce ɓangaren nasa.
Tana shiga kuwa ta samu baya nan, yauma kimtsa masa ɗakin nasa tayi, inda ta gyara komai yayi nead.
Turaren wuta me ƙamshin gaske yau tasanya masa aɗakin nasa.
Nan ta wuce ɓangaren Ummi don miƙa gaisuwa.

Tana shiga cikin falon Ummi, idanunta suka sauƙa akanshi, wani irin kifiyar ƙaunarsa ce taji ta cake ta aƙirji, saurin sadda kanta ƙasa tayi.
Haka ta durƙusa har ƙasa ta gaishe da Ummi, kana shima ta gaidashi.
Saboda ganin fuskar Ummi yasashi amsa mata, bisa dole yaɗan kalleta.
Miƙewa tayi inda yau dakanta tace da Ummi zata shiga kitchine.
To, Ummi tace don bata hanata ba, nan dai ta haɗa musu break mai rai da lafiya, don babu laifi wajen girki kam bata da makusa, ta iya abinci kala-kala.
Saifuddeen kuwa ganin cewa yau ita kaɗai tayi girkin, ya sashi guduwa part dinsa, inda ya ƙule cikin ɗaki, bama yaso aƙirasa cin abinci.

Taɗan jim a ɓangaren Ummi kafun ta koma sashinta.

Koda dare yayi kuwa, zaman kaɗaici gaba ɗaya ya isheta, sosai ta takura da zaman ɗakin, idanuwanta kuwa sun zaƙu dason ganinsa, saidai kuma sam taga alaman babu daman hakan.

Saifuddeen kuwa dawowansa daga sallan isha kenan.
Kaitsaye ɓangaren Ummi ya nufa.
Kamar koda yaushe tana zaune tana lazumi ya sameta.
Ganinsa kaɗai yasa ta gane cewar me yazo ɗauka.

Dubansa tayi tare da cewa.
"Kaje can ɓangaren ku za'a kawo ma Coffee ɗin."
Idanunsa yaɗan zaro alaman mamaki, kasancewar ya saba, koda yaushe ko wani dare ita ke haɗa masa coffee ɗin, kana ya amsa ya tafi dashi.

Sake cewa da tayi yaje za a kawo masa coffee ɗinne yasa shi juyawa ya koma ɓangarensa.
Ummi kuwa kaitsaye wayar Ameena taƙira, bugu ɗaya kuwa Ameenan ta ɗauka, nan Ummi tace da ita.
"Tazo ta ɗauki kayan haɗin coffee din, idan yaso taje can ta haɗa masa."

Jin cewar zata samu ganinsa, yasa taji sanyi acikin ranta, nan ta zura takalmin ta ta fito.

Koda ta isa ɓangaren Ummin tasamu tuni an haɗa kayan haɗin coffee ɗin nasa, cikin wani tray na glass me kyaun gaske.
Ɗauka tayi inda ta koma ɓangaren nasu.
Kasancewar ta falonta ta bi, hakan yasa saida ta tsaya taɗan fesa turare ajikinta sannan ta nufi ɗakin nasa.
A hankali ta kutsa kanta cikin side ɗin nasa falon nasa shiru , babu motsin komai sai sautin Ac dake tashi, ko ina tsab tsab, sai ƙamshin air freshner ke tashi.
Cikin nutsuwa ta ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar tare da buɗewa, taɗan tura kanta kaɗan, hangosa tayi zaune akan wheellchair ya bawa ƙofar baya.
Hakanne yasa sauƙe akiyan zuciya kana ta ƙarasa shigowa cikin ɗakin.
Ƙarasowa tayi kusan shi, hakanne ya sashi ɗan waigawa, nan fa ya sauƙe idanunsa akanta, dama kuwa tun kan taƙaraso sa hancinsa ya jiye masa baƙon ƙamshi, hakan yasa ya gane cewa, anshigo ɗakin nasa ne.
Haɗuwar idanunsu waje ɗaya yasa tayi ƙasa da kanta.
Ajiye tray tayi bisa stoll ɗin dake gabanshi.
Cikin nutsuwa ta ɗan sunkuyo a hankali ta fara haɗa masa coffee ɗin.
Shi kuwa Saifuddeen hannunta ya tsurawa ido zuciyarsa na raya masa abubuwa da yawa, wani irin abu yakeji, wanda shi kansa baisan dame zai ƙirasa ba, kishi ne koko haushi yakasa tantancewa.
Musamman ma da yake tuna cewa, kafun shiɗin ta taɓa haɗawa wani abu da hannunta, sannan kuma kafun shiɗin wani ya taɓa mallakarta a matsayin mata duk abinda zatayi mishi ta taɓa yiwa wani ƙaton, Allah ya sani shi dai yanada zafin kishi, shiyasa har kishi yake taya Zaleeha na aure mata shi da Amina tayi.
Ɗan taɓe lips ɗinsa yayi kana ya ɗan kawar da kansa gefe.

Anutse ta ɗago kofin tea ɗin, ɗan rusunawa tayi tare da miƙa masa.
Hannunsa yasa ya amsa.
Ɗan dubansa tayi tare da yin ƙasa da kai cikin sanyin murya tace.
"Bayan wannan akwai wani abun da kake buƙata ne?." ta ƙare mgnar da mishi misali da hannu.
Kansa ya girgiza mata alaman, "A'a"
Dubansa tayi inda asanyaye tace dashi.
"Saida safe."
Still kansa ya jinjina mata.
Haka ta juya ta fice daga cikin ɗakin.

Ɗakinta ta koma ta kwanta cike da matsanancin begensa, kullum ta ganshi sai taji ƙarin sonsa da kishinsa acikin ranta.

Shikuwa baiwani sha coffee ɗin sosai ba, yana kammalawa kuwa ya kwanta.

Yau kwana uku kenan da zuwan Ameena cikin gidan amma kuma, ko ka ɗan bata wani samun sakin fuska daga garesa, hasalima sosai zaman kaɗaici ke damunta, donma wani lokaci Hayatuddeen na ƙoƙarin ɗebe mata kewa, daga ɓangaren Ummi dasu Raliya kuwa, suna nuna mata ƙauna dai-dai gwargwado.

Yau kuwa gidan nasu ya karɓi baƙoncin Adda Rahama, wacce tazo duba Ummi da zazzaɓin mura ke damunta jin labarin zuwan Adda Rahma a bakin Raliya ne yasa Ameenan tatafi takanas har zuwa part ɗin Ummi inda suka ɗan taɓa hira da Adda Rahaman.

Ameenan na fita dan ta koma ɓangarensu ne Adda Rahama ta gyara zama tare da fuskantan Ummi cikin kulawa tace.
"Nikuwa Ummi anya Saifuddeen yana kulawa da yarinyar nan?,
ki duba fa shigowarsa ɗazun yasame mu dukan mu, amma ko kallonta baiyi ba anya zaman nasu da daɗi."
Ɗan jim Ummi tayi tare da cewa.
"Nima ina tunanin haka, domin kuwa kullum idan tazo gaisheni ta iskesa, anan part ɗin nawa take gaishesa, hakan kuwa kinga alama ne dake nuna cewa ba'a ɗaki ɗaya ma suke kwana ba."
Gyara zama Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Ae kuwa bai isa ba, hakanan bazai kunyata mu idon mutane ba, wanda yake haukan so da ƙulafashinta ɗin ba ita ke gudunshi ba, yasamu wacce zata zauna dashi kuma shi sai yafara gudunta.
Ina a nan Zaleehan ke kwanan garden duk dan kada ta haɗa makwanci dashi, hmm bari zanyi maganinsa ne ɗan nema."
Nan ta zaro wayarta, inda ta tura Saifuddeen ɗin text, kan cewar tana son ganinsa afalon Ummi, sannan kuma ya taho mata da key ɗin part ɗin Zaleeha.

Ganin saƙonta yasa Saifuddeen ya shiga mamaki me zatayi da key ɗin side'n Zaleeha, haka dai ya ɗauko key ɗin ya nufo ɓangaren na Ummi.
Yana zuwa kuwa Adda Rahama ta amshi key ɗin, dubansa tayi tare da cewa.
"Daga yau zan kulle part ɗin Zaleeha tunda dai bata nan, sannan kuma zan tafi da key ɗin na ajiye, daga yau kuma idan zaka shiga side ɗinka, sai ka nabi ta ɓangaren Ameena tunda duk nan ma hanya ne."
Idanunsa yaɗan zaro waje, cikin yanayin mamaki, tabbas abun nasu yanason shallakewa tunaninsa.
Fuska ya ɓata cikin body language yace.
"Haba Adda Rahama, wai me yasa kukemin haka ne, hanya ma sai an zaɓamin wanda zanbi, kamar wani ƙaramin yaro."
Hararansa Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Ƙwarai kuwa dole in zaɓa maka inda zakabi."
Ummi dai ido ta zuba musu.
Ita kuwa Adda Rahama
miƙewa tayi ta fice daga cikin falon, ta nufi part ɗin Saifuddeen da matan nashi.

Shikuwa Saifuddeen duban Ummi yayi tare da marairaice fuska, kau da kai Ummi tayi, don sam bazata ɗauki excuse ɗinsa ba.
Ganin haka ya gane abin nasu haɗin bakine, a ranshi yace.
"Sai ta cinye muku ni ai kun huta."

Adda Rahama kuwa jawo ƙofar part ɗin Zaleeha tayi ta kullesa.
Nan ta wuce ɓangaren Ameena.
Afalo ta sameta, tayi jigum ganin Adda Rahaman yasa Ameena sakin murmushi tare da cewa.
"Sannu da zuwa.
ɗanmurmushi tayi cikin sakin fuska ta zauna kusa da Aminan,
A hankali tace.
"Ke kaɗai ne ma?."
Da sauri ta gyaɗa mata kai tare da cewa.
"Eh ni kadai gidan shiru."
Ɗan gyara zama tayi kana tace.
"Gsky kam gashi kin saba zuwa aikin nan kuma shiru,
Amman dama Ya Adnan yace in sanar miki shida da Dr Aliyu sun sa an miki transfer zuwa nan F,M,C Gombe, in kin gama hutun bikin dai zakici gaba da zuwa aikinki a nan."
Cikin tsananin jin daɗi tace.
"Kai naji daɗi ngd matuƙa Allah ya saka da al'khairi."
Amin Amin Adda Rahma tace kana ta fuskanceta da kyau
cikin kulawa ta ƙira sunanta.
"Ameena." jin yadda ta kiratanne yasa ta
ɗago kai a hankali ta dube ta.
Gyara zama Adda Rahama tayi tare da sanya hannu ta dafa kafaɗan Ameenan.
Cikin kulawa tace.
"Ban san irin zaman da kukeyi da ɗan uwana ba kuma basai namiki dogon tambaya ko bindiddiba, ko ko nace ki faɗamin sirrinku ba."
Shiru ta ɗanyi ta zubawa Amina ido,
Ita kuwa Amina shiru tayi a ranta kuwa cewa take ina na ganshi mutumin da guduna yakeyi.
Ganin tayi shirunne yasa Adda Rahma taci gaba da cewa.
"Amma tabbas nasan dacewa, har zuwa yau babu wani abu da ya shiga tsakaninki da Saifuddeen, kiyi haƙuri wani zubin hakanan yake, bai fiye son shiga rayuwar kowa ba, bai shiga harkan mutun kai tsaye, kuma baida saurin sabo,
amma kuma kema ya zama dole kitashi tsaye, ke dai ba ƙaramar yarinya bace Ameena, saboda haka ke zaki zage ki jawosa jikin ki, kada kuma kijira cewa sai yazo, ko ko sai ya miki magana kafun ki amsa masa, a'a koda bai gayyaceki ba kije garesa, sabida ke halaliyanshi ne.
Haka yake duk yadda yake son abu baya nuna kulafashinsa, tunda yake a tsawon rayuwarsa kan abu ɗaya, abu ɗaya tai ya taɓa nuna mana kulafashinsa a kanta.
Tun yana yaro koda wani abin cine duk yadda yake son abin in dai ba an bashi bane bazai taɓa roƙaba ko ya nuna yana so.
Dan haka na roƙeki da Allah kada ki bari kinesanta kanki dashi idan dare yayi,

Please Login or Register in order to submit comment