Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauri jiki na rawa Raliya ta nufi, fridge ɗin dake cikin falon, goran ruwa ta ɗauko, saboda tsabar sauri kuwa har tana haɗawa da tuntuɓe. Ummi ne ta karɓi goran ruwan, jiki na rawa ta ɓalle murfin tare da zuba ruwan ahannunta, ta watsa a fuskar Zaleeha, ko motsi batayi ba bare su saka ran farfaɗowanta, ganin haka yasa Ummi sake watsa mata wani ruwan, nan ma shiru, babu alaman cewa numfashinta zai dawo jikinta, hakanne yasa arikice Ummi ta ɗago da kanta ta kalli Adda Rahama, wanda itama gaba ɗaya ta gama tsorata da sha'anin Zaleehan, sake ɗebo ruwan Ummi tayi akaro na uku ta watsa da ƙarfi akan fuskar Zaleeha'n, minti ɗaya kacal taja wani irin ajiyar zuciya me ƙarfin gaske, wanda hakanne yasa Ummi dasu Adda Rahama wanda suke amugun tsorace suka sauƙe wasu tagwayen ajiyar zuciya masu nauyi.
Batare da ta buɗe idanunta ba, sheshsheƙan kukanta ya soma tashi, kanta dake matuƙar sarawa da wani irin matsanancin ciwo ta shiga jujjuyawa tare dasa hannu ta riƙe kan, lokaci guda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya, hannu Ummi tasa ta tallafota, cikin kulawa tashiga shafa bayanta,
jinta ajikin Ummi yasa tasake jin wani irin fitinannen kukan tausayawa rayuwarta ya taso mata, hakan yasa ƙam ta rungume Ummin tana kuka sosai, kuka take mai tsananin zafi da gigita, kukane irin mai ɗauke da tsananin dana sani, haɗi da zallan na dama, kukane me ɗauke da zallan baƙincikin rayuwa, haka zalika kukane dake bayyana, gaskiyar abun dake cikin rai da zuciyarta, sannan kuma yake bayyana zallan tashin hankalinta.

Cikin matsanancin tausayinta Adda Rahama ta miƙe tsaye, kaitsaye gaban fridge ta nufa, goran ruwa me ɗan sanyi ta ɗauko, hannu tasa taɗan dafa kafaɗan Zaleeha'n, wanda har yanzu take nan a jikin Ummi, kuka take sosai kamar ranta zai fita. Asanyaye Adda Rahama tace.
"Kukan ya isa haka Zaleeha, dubi yanda jikinki duk ya ɗauki zafi jau, zakije kisawa kanki wani ciwon, kisha ruwa ko abun zai ɗanyi miki sauƙi."

Kai Ummi ta jinjina cike da tausayin Zaleehan ta karɓi goran ruwan, ɗago Zaleehan tayi tare da cewa.
"Karɓi ruwa kisha Zaleeha nasan zakiji sanyi acikin rai da zuciyarki, sannan kada ki manta kuka baya maganin komai, ki ya waita yin addu'a, hakan zaisa kiji sanyi acikin ranki, yanzu dai kidaina wannan kukan, karɓi ruwa kisha kinji." Kanta ta shiga girgizawa, take kuma numfashinta ya soma wani irin fusga kaman zai ɗauke, sosai jikinta ke ɓari, kukan ta shigayi kaman zata shiɗe, gefe guda kuwa ga wani irin masifaffen ciwon kai da yasa takejin kaman kanta zai rabe gida biyu.
Ganin haka ne yasa Ummi ta kamo kafaɗunta, soma jijjigata tayi, hankali amatuƙar tashe tace.
"Kinutsu Zaleeha, ki dawo cikin hayyacinki, kidaina wannan kukan, Insha Allahu Baba Malam zai yafe miki, dan Allah ki daina wannnan kukan kinji."
Ummi tafaɗi maganar, hawayen tausayin Zaleehan na sauƙa daga cikin idonta, sosai take matsanancin jin tausayin Zaleeha'n, ganin haka ne yasa Raleeya komawa gefe itama ta fashe da wani irin kuka, sosai takejin tausayin Zaleeha'n, saboda ba' a iya matar ɗan uwa kaɗai ta ɗauki Zaleehan ba, tana jintane kamar ƴar uwarta ta jini. Kana tasan zafi da ƙuna da ciwo da ƙuncin zuciyar da mutun keji lokacin daya rasa ɗan uwanshi, domin har yau in begen Ya Nuruddeen ɗinsu ya dawo musu kuka sukeyi koda hotonsa suka gani, shiyasa takeji tausayi Zaleeha.
Gaba ɗaya falon ya ɗauki shiru babu abun da ke tashi, sai sheshsheƙan kukan Raliya dana Zaleeha, wanda kuma takeyinsa cikin fitar hayyaci, duban Raleeya Ummi tayi, cikin sanyin murya tace.
"Haba Raleeya ya kukeso inyine kunsan bana son kukanku, madadin ki lallasarmin ita sai kema ki tasata gaba kuna kuka ya kukeso inyi.
Maza tashi ki haɗo mata tea me kauri tasha, dan nasan duk yau bataci komai ba."
Miƙewa tsaye Raleeya tayi tare da share hawayen dake kan fuskarta, kai tsaye ta wuce kitchine don haɗawa Zaleehan tea kaman yanda Ummi ta buƙata.

Ummi kuwa hannun Zaleehan ta kamo, tare da miƙar da ita, kaitsaye ta jata zuwa bedroom ɗinta, Adda Rahama wanda itama gaba ɗaya zuciyarta ta gama karyewa, ta rufa musu baya.
Akan gado Ummi ta zaunar da Zaleeha'n, tare da kamo hannuwanta, ta riƙe, cikin halin tausayawa tace.
"Kuka bashida amfani, sannan kuma baya magance damuwa, ki riƙa faɗin kalmar Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un, insha Allah zakiji sauƙi acikin zuciyarki."
Cikin sheshsheƙan kuka ta jinjina kanta, ahankali ta soma motsa laɓɓanta wanda sukayi mata nauyi, so take ta furta kalman, amma harshenta rawa yake, kamar yanda duka ilahirin jikinta ke rawa.
Ganin haka ne yasa Ummi soma faɗin kalman abakinta, take kuwa ta amsa, nan ta jingina kanta da cinyar Ummi tana faɗin 'Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un."
tana magananne cikin matsanancin kuka da rawan murya.
Dai-dai nan Raleeya ta shigo hannunta ɗauke da cup ɗin tea.

Hannu Ummi tasa ta amshi cup ɗin, ɗan ɗago Zaleehan tayi, cikin kulawa tace.
"Tashi kisha kinji, nasan ayanda kike ɗinnan, koda kika je gidan nakuma bakici komai ba."
Cikin kuka ta girgiza kanta, don batajin akwai wani abu aduniya da take buƙata, batajin cewa zata iya sanya wani abu abakinta yayi mata daɗi, matuƙar kuwa Baba Malam bai yefe mata ba, yafiyar Baba Malam shi kawai take buƙata ayanzu da yafiyar wandake matsayin mijinta.
Cikin muryarta dake rawa haɗi da sarƙewa tace. "Ummi bazan iya shaba, banason komai, bana sha'awar komai ayanzu idan ba yafiyar Baba Malam ba, dan Allah Ummi ki roƙeshi ya yafemin."

Hawayene suka kuma cika idanun Ummi, amma saita shanye su, sam bata bari sun fito kowa ya gani ba, sake tallafo Zaleehan tayi, cikin sanyi, da lalllami tace.
"Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu kiyi haƙuri kisha ko kaɗanne, kinga shima zai taimaka sosai wajen ɗan baki ƙarfin jiki, gashi kuma naji jikin naki ma ya ɗauki zafi jau kamar wuta, buɗe baki kisha ko kurɓi biyune, yafi ace bakici komai ba." Ummi ta ƙare maganar cikin kulawa.
Haƙiƙa Ummi nada matuƙar daraja da ƙima a idanunta, saboda haka batajin akowani yanayi take ciki zata iya yi mata musu, ganin ta buɗe baki ne, yasa Ummi da kanta ta shiga bata tea ɗin abaki, kurɓan farko da tayi haka taji tea ɗin kaman an surkashi da maɗaci, sam babu wani ɗanɗano acikinsa, wanda kuma ta tabbatar cewa rashin ɗanɗanon daga bakinta ne, bawai daga tea ɗin ba, kurɓa uku kawai tayiwa shayin ta kauda kanta gefe, cikin sanyin murya hawaye na zuba tace.
"Ummi na ƙoshi".
Gyada mata kai Ummi tayi, ita kuma zamewa tayi ta kwanta luf akan gadon Ummi, cikin sanyi take faɗin kalman "Innalillahi wa'inna Ilaihirraju'un." tana faɗi kana tana sakin sheshsheƙan kuka, Ummi kuwa ahankali take shafa lallausar sumar kanta, wanda gaba ɗaya ya baje akan pillow'n da ta ɗaura kanta akai, ko mintuna goma ba'a rufa ba kuwa bacci ya ɗauketa, wanda dagani kasan na dole ne, don ko acikin bacci'n sheshsheƙan kuka kawai take saki.

Jigum haka Ummi da Adda Rahama suka zauna, tare da sakata gaba, sosai sukejin tausayinta, lokaci ɗaya gaba ɗaya ta rame ta fita hayyacinta, idanunta sun kumbura kamar wanda ta shekara guda tana kuka, wani abun mamakin da suka gani kuwa, shine har yanzu bacci take, amma kuma hawaye ne kebin gefen fuskarta, kamar ruwa, sai faman sakin sheshsheƙa take, ita dai Ummi al'amarin Zaleeha na matuƙar bata tausayi, sannan kuma zuciyarta me raunice.

Can Ɓangaren Saifuddeen kuwa, tunda yabar falon na Ummi, kaitsaye side ɗinsa ya nufa, ɗakinsa ya wuce yayi kwanciyarsa, koda yaga lokacin sallan azahar yayi, banɗaki ya shiga tare da ɗauro alwala.
Koda yaje masallaci ana idar da sallah, baiwani ɓata lokaci ba ya kamo hanyar gida. kaitsaye ɓangaren Ummin sa ya nufa, dan kuwa atunaninsa zuwa yanzun Zaleehan ta jima da komawa inda ta fito, ganin babu kowa acikin falon ne yasa shi nufar ɗakin Ummi'n, koda ya ƙarasa jikin ƙofar hannunsa yasa ya ɗan bubbuga ƙofar, Ummi da Adda Rahama wanda suke zaune sun saka Zaleehan agaba, sam aransu basu kawo cewa shi ne ke bugun ƙofar ba, atunaninsu Hayatuddeen ne ko kuma Raleeya, ataƙaice Ummi ta bada izinin shigowa.
Shikuwa Saifuddeen ganin ba'abuɗe masa kofar ba, ya sashi jan handle ɗin ƙofar ahankali ya tura ta ciki, cikin nutsuwa ya turo kekensa zuwa cikin ɗakin, ganin su Ummi zaune akan gado jigum-jigum ya sashi ƙarasowa cikin ɗakin, daf daya kusa iso Ummin nasa ne, idanunsa suka sauƙa akan Zaleeha, dake bacci tana sakin sheshsheƙan kuka, ɗan zaro idanunsa waje yayi da alaman mamaki, dan duk atunaninsa bata gidan.
harzuwa yanzu idanunta basu daina zubar da hawaye ba, kansa ya kawar gefe tare da taɓe bakinsa.

Adda Rahama ne ta dubeshi, cikin sanyi da matuƙar tausayi tace. "Saifuddeen yarinyar nan tana da matsananciyar damuwa, baƙinciki ya mata yawa, wallahi tausayinta nakeji, ka duba fa kaga, lokaci ɗaya tafige ta fita hayyacinta, bata da wani abunyi sai kuka kowa nata ya juya mata baya."

Fuska ya ya mutsa tare da sake taɓe bakinsa,
bata damu da yanayin yanda taga fuskar tasa ba, ta sake cewa. "Yanzu ya za'ayi da ita kenan? kuma ma naji jikinta da zafi sosai, kodai zaka ƙira Abban su Faruq ne yazo ya duba ta."

Cikin halin ko inkula ya ɗage kafaɗunsa sama, alaman.
"Shifa babu ruwansa da duk wani abu daya shafeta."
Baki Adda Rahama ta saki tana kallonsa, dan kuwa koda wasa bata taɓa tunanin zaiyi fushi da Zaleehan har haka ba, tunda yake a duniya bai taɓa nuna ƙulafacinsa kan komaiba sai a kanta.
Shikuwa Saifuddeen ganin irin duban da Umminsa keyi masa ne,ya sashi murza wheelchair ɗinsa, kai tsaye ya fice daga cikin ɗakin, ko kallon inda Zaleehan ke kwance bai sake yi ba.
Ganin ya fita ne yasa Ummi sakin ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, hannunta takai inda ta shiga ɗan jijjiga Zaleeha'n.

Ahankali taɗan buɗe idanunta wanda suka ƙanƙance saboda tsabar kuka, da wani irin firgici haɗi da tsananin tsoro ta tashi, ɗan lumshe idanunta tayi, take mafarkin da tayi yanzun yadawo cikin tunaninta, kasancewar aɗan kwanciyan da tayi har tayi mafarki wai tasake komawa gidan Baba Malam, sannan awannan karon shi da kansa yaja hannunta ya fitar da ita daga gidan, tare dayin mummunan furuci agareta, inda yace.
"Daga yau ta cire kanta daga sahun ƴaƴansa, ta manta da cewa shiɗin mahaifinta ne, saboda shi ya jima da manta cewa ya haifi wata ƴa me suna Zaleeha."
wannan mafarkin shiya daɗa hautsuna tunaninta, kana ya ƙara mata fargaba me yawa acikin ranta, ƙoƙarin sakin wani sabon kuka take, Ummi ta dafa ta, cikin sanyi tace.
"Dan Allah na roƙeki Zaleeha kibar kukan nan haka, kuka baya taɓa maganin damuwa, addu'a shi ya kamata kiyi ako da yaushe, nasan da cewa Baba Malam na fushi dake, amma hakan bawai yana nufin cewa bazai taɓa yafe miki ba ne. Insha Allah zai yafe miki, sannan kada ki manta Baba Malam yana fushi dake ne saboda kin baƙanta ransa, kin kuma ƙi yi masa biyyya, to idan har Baba Malam zaiyi fushi dake har haka, Allah' n daya halicceki kuma fa, wani irin fushi kike tunanin yakeyi dake? nasan kinsan da cewa fushin Allah Yana tare da fushin iyaye da miji, saboda haka kiyi sallah ki roƙi Allah gafara, sanadin haka sai kiga Allah yasa Baba Malam ya yafe miki, sannan kisawa zuciyarki nutsuwa, da salama, tashi maza kije ki ɗauro alwala kizo kiyi sallah." Ummi ta faɗi maganar cikin yanayin lallashi. cikin sheshsheƙa ta gyaɗa kanta, tare da soma yunƙurin tashi daga kan gadon, sai-dai gaba ɗaya babu ƙarfi ajikinta, Adda Rahama ne ta taimaka mata, ita ta kamata ta kaita har cikin bathroom.
acikin toilet ɗin ma kuka take haka ta ɗauro alwala. Koda ta fito nan ta samu Ummi ta shumfuɗa mata darduma tare da aje mata sabon hijab, ganin bakowa acikin ɗakinne yasa, jiki asanyaye ta ƙarasa ta ɗauki hijab ɗin ta sanya, tare da tada sallah.
Da ƙyar ƙafafunta suke iya ɗaukanta, saboda yanda takejin jikinta ba ƙarfi.
Koda takai sujjadar ƙarshe na cikin sallan nata, fashewa tayi da wani irin kuka mai tsananin taɓa zucia, kuka take sosai tana me neman gafara awajen Allah, saida tayi kuka sosai har da shiɗewa kafun ta ɗago daga sujjadan, tana sallame sallan kuwa ta jingina bayanta da jikin gado. Ummi da tunɗazu ke tsaye abakin ƙofar shigowa duk wani kukan na Zaleeha akan kunnenta, hawayen da suka cika idanun ta ne suka samu daman gangarowa, saurin share hawayen nata tayi tare da ƙarasowa cikin ɗakin. Zama tayi tare da aje plate ɗin abincin dake hannunta, cikin sanyi ta ƙira sunan Zaleeha'n. Ɗago jajayen idanunta tayi ta kalli Umm'in, plate ɗin abincin Ummi ta turo mata gabanta, cikin kulawa tace. "Kukan ya isa haka, ki samu kici abinci." girgiza kanta tayi cikin muryarta dake rawa, haɗe da sarƙewa tace. "Bazan iyaba Ummi, bazan iya cin abinci ba, banajin daɗin bakina, komai na duniya baya min daɗi, inajin kamar ma babu yawu acikin bakina, banajin komai acikin zuciyata sai ƙunci da baƙincikin rayuwa, bana sha'awar komai yanzu aduniyata sai yafiyan Baba Malam da Hamma Saif, bazan taɓa iya cin abinci naji daɗinsa abakina ba harsai ranan da Baba Malam ya yafemin, zuciyata zafi takemin Ummi, Babana mafi soyuwa agareni yana fushi dani, Ummi Baba Malam bayason ganina, naje gidansa yasa Ya Habu ya koreni, ƴan uwana duk sun tsaneni, gashi ƴar uwata ta tafi tabarni, Adda Maryam ta bar duniya batare dana sake sanyata acikin idanuna ba, shikenan yanzu bani da wata Adda aduniya, Inama mutuwa ni ta ɗauka ba ita ba, inama da ace mutuwa zatamin gata wajen kusantani da ƴar uwata, bazan iya jure fushin Baba Malam akaina ba Ummi, nima mutuwa zanyi Ummi.....".
Kasa ƙarasa maganan tayi, sakamakon kukan me tsananin ƙarfi da ya ƙwace mata, Ummi kanta kasa daurewa tayi, hakanne yasa ta jawo Zaleehan jikinta ta rungume.
Jinta ajikin Ummi yasa ta ƙanƙame Ummin tana kukan fitar hayyaci, mai ɗauke da tsananin dana sanin abun da ta aikata a baya.

Hawayene suka silalo daga cikin Idanun Hayatuddeen, wanda duk wani kalaman da Zaleehan ke faɗa, ya jisu raɗau akan kunnuwansa, dan yajima tsaye abakin ƙofar batare da sun san da zuwan sa ba, sosai jikinsa yayi sanyi, dajin kalaman nata, domin dama Raleeya ta faɗa masa cewa, Zaleehan har suma tayi ɗazu, shine Ummi ta ɗauketa takaita ɗakinta, jin cewa Adda Zaleehan na ɗakin Ummin ne yasashi nufo ɗakin, saboda halin ko inkula daya nuna mata ɗazu, yasan dole zataji ba daɗi acikin ranta.

Ahankali ya shiga taka ƙafafunsa wanda sukayi masa nauyi, ƙarasawa inda suke yayi, tare da zubewa akan guiwowinsa, cikin wata irin murya dake fitar da tsananin rauninsa yace "Adda Zaleeha, meya sameki? meyasa kike kuka, dan Allah kibar kuka kinji."

Jin sauƙar Muryar Hayatuddeen acikin kunnuwanta yasa, ta juyo da sauri, ganin shine kuwa yasa ta zare jikinta daga na Ummi, faɗawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi, tare da sakin kukan da yafi wanda tayi abaya ciwo, dan jin Hayatuddeen takeyi tamkar Zakariyya. Shima Hayatuddeen ɗin kukane ya ƙwace masa, cikin kukan nata tace. "Hayatuddeen ya zanyi Baba Malam yayi fushi dani, haka Ya Ahmad ma da Aunty Lubna duk sunyi fushi dani, babu wani wanda yake saurara ta, basason ko ganina akusa dasu, Mamy ma fushi take dani, gashi Ya Ameenu ya zama abun tausayi, Adda Maryam ta tafi ta barmu."
Ɗagowa daga jikinsa tayi tare da kamo hannayensa, cikin kuka taci gaba da cewa. "Baba Malam yace kar na sake zuwa gidansa, hatta Ziyada ƙanwata ma fushi take dani, Zakariyya ma nasan adole yake kulani, Hayatuddeen ya zanyi? ina zansa rayuwata? kowa baya sona, kowa guduna yake, babu wasu wanda ke rarrashina sai su Ummi, inajin kamar zuciyata zata fashe, duk wani majinginan danake tinƙaho dashi ya ruguje, rayuwata tayi mini zafi, har inajin gwamma mutuwa ta da rayuwata." taƙare maganar tana me sake komawa ta raɓa jikinsa ta riƙesa ƙam, kuka kuwa yinshi take harda majina.
Duk yanda yaso shanye kukansa kasawa yayi, hakan yasa ya sake rungumeta ya fashe da kuka, saida yayi kuka sosai sannan ahankali ya shiga shafa bayanta, cikin sanyin murya yace. "Kiyi haƙuri kinji Adda Zaleeha, ki daina kuka, idan duka mutanen duniya zasu ƙiki, ni da Zakariyya bazamu taɓa kinki ba, kiyi shiru kinji, nasan Baba Malam yayi fushi, amma zai yafe miki."
Kai Ummi ta jinjina cikin son kwantar mata da hankali tace.
"Ƙwarai kuwa Insha Allah Baba Malam zai yafe miki, yanzu dai ki samu kici abincin kinji." Cikin sheshsheƙan kuka tace.
"Ummi bazan iya ci ba, ko tea ɗin ɗazu dana sha haka najisa kaman maɗaci, gaba ɗaya kaman yanda zuciyata take babu ɗanɗano acikinta, haka bakina ma, banajin daɗin komai."
cikin tausayawa Ummi tace.
"To akawo miki fresh milk kisha ko kaɗanne?"
Batason yawaita yin musu da Ummi hakan yasa ta ɗan gyaɗa kanta, dai-dai lokacin kuwa Raleeya ta shigo, nan Ummi tace da ita, ta kawowa Zaleehan fresh milk.
Babu ɓata lokaci kuwa takawo fresh milk ɗin me sanyi.
Karɓan cup ɗin Hayatuddeen yayi, cike da tausayinta yace. "Adda Zaleeha, ki tashi kisha kinji."
bazata iya janye jikinta daga garesa ba, saboda tanajin ya zame mata kamar majingina, hakan yasa ahankali taɗan ɗago kanta dake masifar sarawa, cikin kulawa Hayatuddeen ya shiga bata fresh milk ɗin abakinta, sam kwata kwata batajin daɗi ko ɗanɗano abakinta, jima take kamar magani take sha, kurɓo huɗu kawai tayi ta janye bakinta daga jikin ƙofin, har yanzu sheshsheƙan kuka take, gashi jikinta ya sake ɗaukan zafi sosai, komawa jikin Hayatuddeen ɗin tayi ta kwanta, tana ta faman fusgar numfashinta dake neman ƙwace wa. Ummi, Adda Rahama, Raleeya, har zuwa kan Hayatuddeen babu wanda ya gusa da ga kusa da ita, wani irin kulawa haɗi da tattali na musamman suke bata, sosai suke faɗa mata kalaman dazai kwantar mata da hankali..
Suna nan azaune har aka ƙirayi sallan la'asar, Ummi ne tace da Adda Rahama da kuma Raliya su shiga kitchine su ɗaura abinci, kasancewar tunda akayi rasuwa'n kullum sai sunkai abinci gidan su Zaleeha.
Nandai Hayatuddeen ma ya tashi ya wuce massallaci, itama Zaleehan sallah tayi, nan kan carpet ta kwanta tana masassara saboda zazzafan zazzaɓin ya soma cin ƙarfinta.
Su Adda Rahama kuwa suna kammala girkin, nan cikin wasu manyan food flask suka juye abincin.
Kamar kullum dama Hayatuddeen da Raleeya ne ke kai abincin, to yau ɗin ma dai hakanne, ta kasance dan sune suka kai abincin, Hayatuddeen ne ke driving, kasancewar yanzu hannunsa yaɗan faɗa wajen iya tuƙin mota, saboda Khamis na koya masa tuƙin time to time, babu laifi kuma yaɗan iya.
Koda suka ƙarasa gidan su Zaleehan bayan sun sake yi musu gaisuwa, Hayatuddeen ne ya kamo hannun Zakariyya da Imran ƙanin Ishaq wanda da Babansu yazo, zagawa sukayi wajen da babu yalwar mutane. ɗan karyar da wuya Hayatuddeen yayi, cikin sanyi haɗi da damuwar dake bayyane akan fuskarsa yace. "Zakariyya Adda Zaleeha taje gida bata da lafiya sosai, gaba ɗaya jikinta zafi kaman wuta, har suma tayi, dan Allah abawa Baba Malam haƙuri ya yafe mata, tana cikin matsanancin damuwa, kuka yazama tamkar abinci agareta."

Idanun Zakariyya ne suka cicciko da ƙwallan tausayin ƴar uwartasa, ɗan lumshe idanunsa yayi, yana mejin tausayinsu su dukansu, tabbas yasan akwai ƙauna me zafi atsakaninsu, wanda koda ace babu auren Hamma Saifuddeen akan Zaleeha, idan Hayatuddeen yaganta cikin damuwa zai ji ƙanta, kuma gashi nan damuwa ta bayyana ƙarara akan fuskarsa, sunyi imani cewa duk wani damuwan ɗayansu nasune su duka.
Cikin sanyi yasa hannu ya share hawayensa, muryarsa asanyaye yace. "Hayatuddeen nima bansan ya zanyi ba, Baba Malam yace. Bayason sake ganinta, yana fushi da ita sosai, kuma ta basa haƙuri ma yaƙi haƙura."
Sosai jikin Hayatuddeen da Imran yayi sanyi, dole da addu'a kawai zasu taya ta, dan basu da wani zaɓin daya wuce hakan.

Fitowar Adda Raleeya daga cikin gidan ne, yasa sukayi shiru da zancen, ƙarasowa wajen da su Zakariyyan suke tayi, ganinta yasa Hayatuddeen duban Zakariyya murya asanyaye yace.
"Mu zamu wuce."
Har bakin mota Zakariyya da Imran suka rakasu, saida yaga tafiyarsu sannan suka komawa cikin gida, zuciyarsa gaba ɗaya ba dadi, sosai tausayin Zaleehan ke damunsa.

Koda su Hayatuddeen suka koma gida kuwa kai tsaye ɗakin Ummi suka wuce. Har yanzun Zaleeha na duƙunƙune waje ɗaya, gefenta Ummi da Adda Rahama ne zaune.
Ƙarasowa cikin ɗakin Hayatuddeen yayi tare da zama akusa da ita, hannunta ya kamo, hakan yasa ta ɗago ta dubeshi da idanunta wanda sukai jajur, murmushi yaɗan ƙaƙalo akan fuskarsa, cikin kulawa yace.
"Adda Zaleeha kukan ki ya kusa ƙarewa Insha Allah, Baba Malam zai yafe miki nan bada jimawa ba, kuma Ya Ahmad ma da kansa yace agaisheki."
Zabura tayi tare da matsowa gab dashi, idanunta ta zuba masa, kansa ya jinjina mata alaman dagaske yake, idanunta ta lumshe, take kuma wasu sabin hawaye suka zubo mata, matsawa kusa dashi tayi tare da ɗaura kanta akan kafaɗansa, hannunsa ta riƙe ƙam tana sauƙe ajiyar zuciya.
Ganin haka yasa su Ummi sakin ajiyar zuciya suma, dan gaba

Please Login or Register in order to submit comment