Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bai mancetaba, da sauri ya bata hanya tare da cewa.
"Hajia barka da hanya. An dawo lfy?".
Kai kawai ta iya gyaɗa mishi a wani sashin na zuciyarta kuwa ta ɗanji sauƙin tsoronta na kada su Ummi su koreta, taku takeyi a hankali yayinda hawayenta ke kwaranya, jin muryar mai gadin nasu na cewa.
"Ya mukaji da haƙuri Allah ya jiƙanta da rahma".
a hankali tace.
"Amin Amin."
kana ta ci gaba da nufar sashin Ummi.


Acan cikin gidan Hamma Saifuddeen kuwa Gabaki ɗayansu suna tare a falon Ummi, banda Ameena wanda tun da sassafe data dawo ta ɗan huta so ta koma dan zasuyi wani taro da manyansu shiyasa tatafi wajen aiki, Saifuddeen, Ummi, Ahmad, Raliya, Hayatuddeen, sai kuma Adda Rahama, wanda dawowanta kenan daga gidan su Zaleehan, inda taje tayi musu ta'aziyya, yanzu ma zaune suke suna ƙara jajanta rasuwan Maryam ɗin, duban Ummi Adda Rahama tayi kana tace.
"Wallahi Ummi na tausayawa Ya Ameenun su Zaleeha ƙwarai, domin tabbas yayi rashin mace ta gari, kinga fa ko ranan nan nakaiwa Abban su Akih abinci, kasancewar yana sauri, hakan yasa ya fita batare da yayi break fast ba, nan asibitin nasu na haɗu da ita taje awu, ashe haɗuwan mu na ƙarshe kenan, Allah sarki Maryam, wallahi mace ce me hankali da nutsuwa, babu ruwanta, ta iya zama da mutane, kowa nata ne, gata da fara'a da kuma kyautata wa, insha Allah halinta na gari zai bita, Allah Ubangiji kuma ya jiƙanta da rahama." Nan suka amsa da Ameen su dukansu, Hayatuddeen kuwa, miƙewa yayi daga zaunen da yake, kaitsaye yafice daga falon, so yake yaɗanje shagon nan dake ƙarshen titin gidan nasu ya sayo rechard card.
Dai-dai ya kawo ƙofar fita daga falon, ita kuma Zaleeha ta kawo kai, hakan yasa sukayi karo da juna, da sauri yaja baya, idanunsa ya waro cike da mamakin ganin Zaleehan agidansu.
Ita Zaleeha kuwa idanu ta ƙura masa, hawaye na bin fuskarta, lokaci guda kuwa Hayatuddeen ya sanja fuska, tare da ɗauke kansa, yi yayi ma kamar baisanta ba, kana ya raɓa ta gefenta ya wuce, batare da yace da ita ƙala ba, hakan ne yasa jikin Zaleehan yayi wani irin mugun sanyi, take kuma hawayenta suka ƙaru fargaba da tsoro ya ƙara rufeta, haka dai da ƙyar take iya ɗaga ƙafafunta ta nufi cikin falon Ummi zuciyarta na duka tara-tara, koda ta ƙarasa bakin ƙofar shiga falon, hakanan taji ƙirjinta na wani irin bugu, kuka ne me ƙarfi keson ƙwace mata, cikin wata irin dashashshiyar murya wanda bata fita sosai tayi sallama, tare da shigowa cikin falon!.
Cikin mamaki su duka suka ɗago kansu suna kallonta kusan a tare sukace,
"Laaaaa."
Saifuddeen ne ya fara ganinta, kasancewar dama shi yana facing ɗin ƙofar shigowan falon ne shiyasa ya rigasu ganinta.
Taku ɗaya tayi tana ƙoƙarin shigowa cikin falon Saifuddeen yayi wani irin tsuke fuska cikin yanayin zafi ya ɗaga mata hannu, alaman dakatarwa.
Hawayen dake cikin idanunta ne suka kuma gangarowa har zuwa kan ƙirjinta kai ta fara jujjuyawa cikin kiɗima ganin ya ɗago, Hannunsa ya yana me yi mata alama akan cewa kada tayi kuskuren shigowa cikin falon, ta koma inda ta fito.
Wani marayan kuka ta saki tare yayyarfa hannu alamun bata cikin haiyacintama bisa alamu duk a gigice take.

Dubansa Ummi tayi tare da cewa.
"Lafiyanka kuwa Saifuddeen, akan me zaka koreta?"
Rumtse idanunsa yayi tare da girgizawa Ummin nasa kai, alaman cewa bayason ganin Zaleehan. Kukan daya zo mata ne takasa dannewa, hakan yasa ta sakeshi da tsananin ƙarfi a hankali jiki na rawa ta shiga takowa, tana ƙarasowa gaban Ummi.
Ganin halin da take cikine yasa Ummi miƙo mata hannu alamun tazo.
ai kuwa ganin haka yasa da sassarfa ta ƙaraso gaban Ummi cikin kuka ta zube akan guiwowinta, tare da ɗaura kanta akan cinyar Ummin, nan ta saki wani irin gigitaccen kuka, mai ratsa zuciya, da kuma ban tausayi, Shiru sukayi gaba ɗayansu falon sai sautin kukan Zaleeha'n ne kawai ke tashi, wanda hakanne ya sanya gaba ɗaya jikin su Adda Rahama Ahmad Raliya yayi sanyi, Kuka take kamar ranta zai fita, cikin kukan tare da sarƙaƙƙiyar muryarta wanda bata fita sosai tace.
"Na shiga uku Ummi Baba Malam yayi fushi dani, naje gidansa ya koreni, yace baya ko son ganina, Ummi kowa baya sona, kowa guduna yake, Ummi ya zanyi, yazanyi da rayuwata, Ƴar uwata tatafi ta barni, Babana kuma yana fushi dani, duka ƴan uwana suna fushi dani, ina zansa rayuwata, Ina ma da ace mutuwa ni ta ɗauka ba Adda Maryam ba, ina ma ace mutuwa zata ɗaukeni!!!." ta ƙare maganar tana sakin wani irin gigitaccen kuka, harda shiɗewa.
Jin abun da Zaleeha'n ke faɗa ne yasa Ummi taji idanunta sun kawo ƙwalla, wani irin tausayin Zaleehan ne ya kamata,
Cikin wani irin yanayi Numfashin Zaleehan ya sarƙe aƙirjinta,
Ummi ne tasanya hannu ta ɗan ɗagota, hakan kuwa yayi dai-dai da ɗaukewar numfashinta, take ta tafi luuuu ta faɗi ƙasa summamiya.
Hankalin Ummi da su Adda Rahama ne yayi wani irin masifaffen tashi, da sauri sukayo kanta.
Ganin Haka yasa Saifuddeen rumtse idanunsa, wanda lokaci guda sukayi ja, bayajin zai iya cigaba da zama acikin falon baya jin zuciyarshi nada ƙarfi da taurin da zata juri ganin halin da Zaleeha ke cikiba, hakan yasa ya danna madannin kekensa, batare dasu Ummi sun farga ba ya fice daga cikin falon.




Littafin nan na ƙuɗine


By
*GARKUWAN FULANI*

[14/09, 11:38 am] +234 706 370 3964: Sbpejtt Kai kawai Ummi ta girgiza tare da tashi kaitsaye ta wuce ɗakinta, Hayatuddeen ma dake zaune ji yayi gaba ɗaya jikinsa yayi sanyi, sam baiso hakan ba, yaso ace Hamman nasa ya amince, saboda shima ya gamsu cewa, da taimakon Hamman nashi ne kaɗai Baba Malam zai iya haƙura ya yafewa Adda Zaleeha'n.
Haka dai suka kammala cin abincin nasu duk jikinsu asanyaye, acan ɓangaren Saifuddeen kuwa yana barin falon nasa, kaitsaye ɓangarensa ya nufa, sauƙa daga kan wheelchair ɗinsa yayi, tare da haurawa saman ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon ya kwanta, idanunsa ya lumshe yana jin zuciyarsa nayi masa wani iri, maganganun Ummin ne ya dawo cikin tunaninsa, ahankali ya girgiza kansa, cikin zuciyarsa yace.
"Ada ni ba komai bane awajenta, bata ɗaukeni matsayin komai ba, kullum idan akwai wata magana da zai fito abakinta, wanda ta shafeni to baiwuce kalmar ƙiyayya ba, matsalar da ta faɗa ayanzu, shiyasa ta ɗaukeni wani me mahimmanci agareta, ta gudu ne saboda batason aurena, yanzu kuma gashi ta dawo tana zaune aƙarƙashin inuwata, ahaka kuwa shine har da wani neman alfarmarta."
wani murmushi me ciwo yayi tare da girgiza kansa, shiba sakarai bane, ita tayi amanta saboda haka ita kaɗai zata lashe.
Yana gama tunanin ya gyara kwanciyarsa, tare da sake lumshe idanunsa, yana sakin ajiyar zuciya.
Acan ɓangaren Part ɗin Ummi kuwa baccin Zaleeha baiyi wani nisa sosai ba ta farka, Hayatuddeen ne ya kawo mata abinci, haka ya sakata gaba dolen ta saida taci, tana kammalawa kuwa ya miƙo mata ruwa da magungunanta tasha, nan ƙasan carpet ya zauna, ita kuwa tana kwance akan gado, ganin cewa akwai damuwa atattare da itane yasa shi, soma bata labarai wanda yasan dole zasu ɗebe mata kewa, suna zaune ahaka Raleeya ta shigo, akusa da Zaleehan ta zauna, cikin kulawa tace "Aunty Zaleeha ya jikin naki?".
ɗan jinjina kanta tayi, asanyaye tace.
"Da sauƙi." Murmushi Raleeya tayi, tare da faɗin.
"Masha Allah, Allah Ya ƙarasa sauƙi."
Da "Ameen" Zaleehan ta amsa, haka dai suka ci gaba da hiransu, Ita dai Zaleeha idanu kawai ta zuba musu, sau dayawa dramer'n Hayatuddeen da Raleeyan na burgeta. Duk dama har yanzu akwai damuwa kwance aƙasan zuciyarta.
Suna ahaka Ummi tashigo cikin ɗakin, ganinsu atare ne yasata sakin murmushi, sake gaisheta Zaleehan tayi, ta amsa mata fuska asake, har cikin ranta kuwa taji daɗin ganin Zaleehan cikin ɗan yanayi me kyau, kallon kayan dake jikin Zaleehan tayi, take wani tunani yazo mata hakan yasa tace da Hayatuddeen yazo zata aikeshi.
Babu musu ko ya tashi yabi bayanta.
Kaitsaye ɗakinta suka wuce, nan kan gado ta zauna, tare da jawo jakarta ta zage zip ɗin, duban Hayatuddeen tayi, cikin kulawa tace. "Makay zan aike ka ne, ko San Hussain Super Market?".
ta tambayesa da yanayi na ɗan tunani, zama yayi akusa da ita, tare da cewa.
"Wani abu za a sayo miki ne?".
"Kaya nakeson kasayowa Zaleeha, kaga dai bata zo da kayanta ba, part ɗin ta kuma akulle yake, na kuma ce Hammanku ya bada key yayimin biris, dama daya ba da key ɗin sai nasa ko Raleeya ne ta ɗebo mata sauran kayanta." cikin zumuɗi Hayatuddeen yace. "Ummi Makay zanje, wallahi dama ina kwaɗayin strowberry cake, kinga kawai sai na shiga Makay shawarma na saya, nasan itama Adda Zaleehan idan na sayo mata zataci." Hararansa Ummi tayi tare da cewa.
"To sarkin kwaɗayi, an faɗa maka cewa dama kowa irinka ne, koko ance maka kowa kwaɗayi kawai yasa agaba?."
Murmushi yayi, cikin zaƙuwa yace.
"Hmm Ummi bakisan wacece Adda Zaleeha ba kenan, ai shan zaƙinta ko shazumami sai haka, yanzu kawo kuɗin naje na sayo mata kayan."

Kai kawai Ummi ta girgiza tare da zaro Kuɗin da aƙalla zasu kai 70k, acikin jakanta ta miƙa masa, cikin kulawa tace.
"Kanutsu dan Allah Hayatuddeen, dogayen riguna nakeson kasayo mata masu kyau, ni hankalina ma kwata kwata bai kwanta da aikanka ka ba, dan tunda ka iya mota kuma shikenan ka zama ayawo, dan ma ana zaman makokin nan ne da da Zakariyya zakuje, saboda hankalina zaifi kwanciya, saboda ya fika nutsuwa wani lokaci'n."
Ɗan bakinsa ya turo gaba, cikin halin sakalcinsa yace. "Yanzu Ummi dan Allah Zakariyya'n ne ya fini nutsuwa." Murmushi Ummi tayi, tana me zuge zip ɗin jakarta tace.
"Ni maza yi sauri ka kawomin aikana, sannan kuma katabbatar kayi driving cikin nutsuwa."
Haka yafita daga ɗakin yanata wani shagwaɓa, da turo baki gaba, tuno da cewa zaije ya saya strowberry cake yasan yashi sakin murmushi, haka ya fice daga cikin falon, yana karkaɗa ɗan makullin motar dake hannunsa.

Zaleeha da Raleeya kuwa har yanzu suna tare, hira Raleeya ke tayiwa Zaleeha'n, ahaka har wani sabon bacci ya ɗauketa, ganin tayi bacci ne yasa Raleeya sakin murmushi, nan tatashi ta fice daga ɗakin dan zuwa kitchine ɗaura lunch.

Ummi kuwa ganin fitan Hayautuddeen yasa, ta ɗauki wayarta, text ta turawa Saifuddeen akan cewa tana son ganinsa, tana nan zaune kuwa ko mintuna 7 ba acika ba, sai gashi ya shigo cikin ɗakin.
Har gaban Ummin ya ƙaraso da kekensa, sai wani shagwaɓe fuska yake, saboda yasan bai wuce maganan Zaleeha Ummin zatayi masa. Ummi kuwa ɗago kai tayi ta dubesa, cikin nutsuwa tace.
"Wai Saifuddeen me kake nufi da Zaleeha ne? tunfa jiya nake binka da ka bani key ɗin ɗakinta amma kaƙi, ko anan kakeso ta zauna mana bayan gacan ɗakinta?" Ɗan kwaɓe fuska yayi, cikin body language ɗinsa yace.
"Nifa Ummi bansan inda key ɗin ɗakinta yake ba." gane abunda yake nufi yasa Ummi ɗan buɗe baki, da mamaki tace. "Bakasan inda key ɗin yake ba kuma.?"
Kansa ya jinjina alamar "Eh" kuma har ga Allah ya mance inda ya ake key ɗin. Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Sannu uban maƙaryata, Saifuddeen yaushe ka fara yimin ƙarya? wato ma sokake kace key ɗin ya ɓata ko? hmmm inace nan da Addarku Rahama ta amshi key ɗin tatafi dashi, ko wata ɗaya baicika ba kaje har gidan ta ka amso, ko kana tunanin banida labari ne? kaga tunkan raina ya ɓaci Saifuddeen ka buɗewa yarinyar nan ɗakinta ta koma tayi zamanta." bakinsa ya turo gaba, sam shi baisoma Ummi tanayi masa maganan Zaleeha'n, ai koma me yafaru itace ta jawo, hakanan saboda ta ɗaukesu sakarkaru saita gudu ta kuma dawo alokacin da take so. Kuma zancen gaskiya harga Allah ya mance in da ya ɓoye key ɗin side ɗinta, amman gashi Ummi gani take ƙarya yayimata abinda bai taɓata kwatanta yimataba.
Hararansa Ummi tayi tare da ɗanyin ƙwafa tace.
"Ayi mutum da taurin kai da riƙo sai kace mutanen farko, wallahi ka tabbatar ka kawomin key ɗinnan tunkan raina ya ɓaci, idan kaƙi kuwa zansa a ɓalla ƙofan da ƙarfi, ta koma ɗaƙinta ta zauna."
Idanunsa yaɗan zaro waje, jin cewa za'a ɓalla ƙofar, tuna cewa ma ƙofar bazata taɓa ɓalluwa bane ya sashi ɗan sakin ajiyar zuciya, hannuwansa ya haɗe waje ɗaya, alaman Ummin tayi haƙuri, kuma shi ya mance inda key ɗin yake ne.
Haranshi tayi sannan tace.
"To batun rakata gidansu ta bawa Babanta haƙurifa ko shima ka mance hanyar gidan ne?".
A hankali ya jujjuya mata kai alamun bai mance ba, sai kuma yayi ƙasa da kanshi.
Ganin cewa bazai biyu ta sauƙi ba yasa Ummi'n, cewa ya tashi yaje kawai.
Yana fita kuwa Ummi tayi ƙwafa tare da cewa. "Ɗan nema zan yi maganinka ne."
Daga haka ta-tashi ta wuce toilet dan ɗauro al'walan sallan azahar.

Can ɓangaren Hayatuddeen kuwa saboda tsabar kwaɗayi yaci ransa saida ya fara zuwa makay shawarma ya sayi strowberry cake ɗinsa, ya kuma haɗa da roasted fish, saboda yasan Adda Zaleehan naso kuma idan ya kai mata zata ci.
Saida ya gama ƙwalamarsa kafun yafito daga Makay Shawarma ɗin, kaitsaye ya nufi cikin Makay Super Market, ɓangaren da dogayen rigunan mata suke ya nufa, sosai ya darje wajen zaɓawa Adda Zaleehan nasa dogin riguna masu kyau, bai tsaya anan ba kuwa harda wasu riga da sket ƴan kanti masu kyau kusan kala uku ya zaɓa mata, haka dai ya gama sayayyyan cikin nutsuwa, sannan ya ƙarasa wajen biyan kuɗi, koda akayi lissafin kayan kuɗin sun haura wanda Ummi ta basa, dan 70k Ummi ta basa, kayan da ya saya kuwa sun haurawa haka, dan kuɗinsu 77k ne, baiwani damu ba, haka ya zaro ATM card ɗinsa dake cikin aljihunsa ya basu, kasancewar dama yana aje ƴan kuɗaɗensa anan cikin asusun banki, dan sau dayawa kuɗin da Hammansa ke basa ba kashewa yake ba, yakan tarasu ne idan sun ɗanyi yawa sai yakai ƙaramin account ɗinsa na bank ba asalin babba da ake sa mishi kason dukiyarsa ba a ƙaramin yake ɗan gutun ajiyarsa, haka dai suka zare 7k ɗinsu suka basa ATM card ɗinsa, daganan kuma suka zuba masa kayan acikin leda.
Har mota kuwa sukasa aka kai masa kayan, haka ya ɗauki hanyar gida, sai ciye ciye yake acikin motar.
Koda ya ƙarasa gida kuwa, Ummi ya bawa kayan, dan har zuwa lokacin Zaleeha bata tashi abacci ba, babu laifi kuma Ummi ta yaba da rigunan dan sunyi kyau sosai.

Saifuddeen kuwa tunda yabar part ɗin Ummi ɓangarensa ya koma, al'wala yayi sannan ya nufi masallaci, tunda yayi sallan azahar kuwa bai dawo gidan ba, Sule driver yaƙira suka ɗan fita, saboda wani aikin daya taso masa, dole saida yaje office ɗinsu, saida aka kusa sallan la'asar sannan ya dawo, anan masallacin ƙofar gidansu yayi sallan la'asar, sannan ya shigo cikin gidan, ɓangaren Ummin nasa ya sake nufa, dan kuwa ɗazu koda yana zaune a office saida yaga text message ɗinta, kancewa
"Lallai ya kawo mata key ɗin ɗakin Zaleeha, sannan kuma ya tabbatar yazo yakai Zaleehan gida ta bawa Baba Malam haƙuri."
Shidai kam yama rasa yanda zaiyi.
Yana shiga falon kuwa ya iske Ummi da Ahmad, sai kuma Hayatuddeen dake zaune ƙasan turkish carpet yana ta faman lodawa cikinsa abinci. Ganin yanda fuskar Ummi take babu wani walwala asamanta yasa yaji jikinsa yayi sanyi, ƙarasowa cikin falon yayi tare da bawa Ahmad hannu suka gaisa, saboda yau duk basu haɗuba. duban Ummin nasa yayi, asanyaye cikin body language ɗinsa yayi mata sannu da gida.
Kai kawai ta jinjina masa, ko kallonsa batayi ba, hakanne yasa jikinsa ƙarayin sanyi, sam baisom fushin Ummin nasa. Ummi kuwa da gangan ta nuna cewar tana fushi dashi, saboda tasan idan ba haka tayi masa ba bazai taɓa yin abun da ta sakashi ba.
Raleeya wanda shigowarta falon kenan, ganin Hamman nata yasa ta wuce kitchine, abinci da drinks ta zubo masa, saboda yau ɗin favorite food ɗinsa ta dafa. nan gabansa ta ƙaraso tare da ɗan durƙusawa, ƙoƙarin aje plate ɗin abincin agabansa take, cikin sauri yaɗan riƙe hannunta tare da girgiza mata kai, alaman ya ƙoshi, kallon sa tayi fuskarta ɗauke da ɗan damuwa, kansa ya jinjina mata alaman cewa. "Tayi haƙuri bayajin yunwa."
Asanyaye ta ɗaga kanta ta kalli Ummi, gani tayi fuskar Ummin atsuke, hakanne yasa ta juyawa ta maida abincin kitchine.
Cikin sanyin jiki ya danna madannin wheelchair ɗinsa tare da ƙarasawa gaban Ummin nasa, hannunta ya kamo tare da ɗan shagwaɓe fuska, ɗago kai tayi ta dubesa. Rau-rau yayi da idanunsa, tare da yi mata alama kancewar
"Tayi haƙuri karta ce zatayi fushi da shi." gane hakanne yasa Ummi ta sake haɗe fuska, tare da ɗan kau da kanta gefe, cikin haɗe fuska tace.
"Idan ma nayi fushi dakai ae kai ka nema, meyasa zanta maimaita maka magana ɗaya, amma ka kasa aiwatarwa, tunjiya naketa binka, akan maganan key ɗin ɗakin Zaleeha, sannan ga kuma maganar rakata ta bawa Babanta haƙuri, amma gaba ɗaya ka share maganta, bansan yaushe kazama haka ba Saifuddeen, bansan kuma meke damunka da har yasa ka kasa jin tausayin Zaleeha acikin ranka ba, To Wallahi matuƙar ba ɓacin raina kakeson gani ƙiri-ƙiri ba, tun wuri kaɗauki yarinyarnan kuje ku bawa Baba Malam haƙuri, tun da dai idan har dakai taje, baban nata zai iya yafe mata."
Idanunsa ya rumtse, lokaci guda yaji zuciyarsa na bugawa da ƙarfi, ɗanjan kekensa baya yayi, tare da zamewa ya durƙusa akan guiwowinsa, sake kamo hannun Ummin nasa yayi, lokaci guda ya shiga girgiza mata kai, sosai rauni ya bayyana akan fuskarsa, cikin body language ɗinsa yace. "Dan Allah Ummi kiyi haƙuri, ki bani ko wani irin umarni ne zan bi, sannan kuma bazan taɓa bijiremiki ba, amma dan Allah kada ki tursasani kan cewa na raka Zaleeha ta bawa Baba Malam haƙuri, idan nayi hakan Ummi zan cutu, tunda batasan ina da ƙima ba sai yanzu da matsala ta taso mata? kuma ma Ummi lokacin da tayi lefinta tare dani tayi ne? ai ita kaɗai tayi lefinta, da tazo guduwa kuma bata shawarceni ba, tanajin cewa ta isa shiyasa ta gudu alokacin da takeso, ta kuma dawo alokacin da takeso, ni nasan sam bata shirya yin nadama ba, kawai dan rasuwar Adda Maryam ne, amma bacin haka ai bazata dawo ba."

Dubansa Ummi tayi tare da ɗan girgiza kai, sam bata taɓa tunanin cewa wai Saifuddeen zaiyi fushi akan maganar Zaleeha ba, amma babu komai tayi masa uzuri, saboda tasan ba har zuciyarsa maganar da yake faɗi take fitowa ba, gyara zamanta tayi, cikin son nusar dashi da kuma yanda zai fahimta tace.
"Koma me Zaleeha ta maka, bai kamata kayi irin wannan fushin da ita ba, sannan kuma kaima shaida ne akan irin damuwar da take ciki, ca nake jiya anan gabanka ta suma, ko so kake mu barta haka, mu zuba mata idanu ciwon zuciya ya kamata? ko kuwa so kake mubar rayuwarta cikin garari?, kakuwa san halin da take ciki? bata da wani abunyi sai kuka dare da rana, bata da wani sauran farinciki, da wanne zataji, mutuwar ƴar uwarta ko kuwa ƙunci da baƙin cikin rayuwa? ko Allah ma muna masa laifi me girma, amma damunyi kyakkyawan tuba yake yafe mana, saboda meyasa to mu bazamu yafe mata ba?."

Rumtse idanunsa yayi da ƙarfi tare da tattauna lips ɗinsa, sosai yakejin wani abu azuciyarsa, wanda shikansa bazai iya fassara sa kaitsaye ba.

Raleeya wanda tuni idanunta sun ciko da ƙwalla ne ta ɗan matsa kusa da Ahmad, cikin sanyi tayi masa alamar cewa.
"Ya taimaka yasa baki, Hamma Saifuddeen ɗin ya raka Zaleeha ta bawa Baba Malam ɗin haƙuri, saboda rashin agaza mata zai iya sawa ta kamu da wani ciwon, musamman ma idan akayi la'akari da yanda take wuni kuka."
Jinjina mata kai Ahmad ɗin yayi alaman
"Yaji kuma zaiyi wa Saifuddeen ɗin magana. Hayatuddeen dake zaune shikansa saida yaji hawaye sun cika masa ido.

Ummi kuwa gaba ɗaya ranta ya gama ɓaci, domin shirun da Saifuddeen ɗin yayi, alamace dake nuna cewa, har yanzu yana kan bakansa, hakan ne yasa cikin fushi ta tashi ta nufi ɗakinta.

Cikin sauri Zaleeha dake tsaye jikin ƙofa ta koma ɗakinta, dan batason wani daga cikinsu ya ganta, saboda tunda suka fara magana'n harzuwa yanzu tana jinsu, duk da cewa Saifuddeen ɗin baya magana, amma

Please Login or Register in order to submit comment