Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

how are you?."
Elizabet tafa ɗa tana me kallon Zaleeha'n, wanda take ta faman ƙarewa ɗakin kallo.

"Am fine!" Zaleeha tafaɗa tana me ƙarewa kofin da aka kawo mata ruwa aciki kallo, Allah Yasani itakam ƙyanƙyaminsu takeji, hakanan take ganin komai nasu yafita daban, komai nasu ba irin na sauran mutane ba, shiyasa ma kwata kwata bata fiye shiri da dangin mahaifiyarta ta ba, domin ita sam batason zama da su, saboda zama da waƴanda hasken addinin musulunci bai cimmusu ba, sai ahankali, zakaga kwaɓa da kuma shirme kala-kala.

Duk da kasancewar tanajin ƙishin ruwa, amma kasa shan ruwan tayi, don sam bata yarda ma da tsabtan gidan ba.
Hira kaɗan suka ɗan taɓa da Uncle din nata, nan yace da ita zai tafi gona, yana tafiya ta jawo akwatunanta, zanin gadon dake kan katifan da take kai ta yaye, nan taciro wani bedsheet mai ɗan taushi wanda baida nauyi ta shumfuɗa, kimtsa akwatunanta tayi agefe kana ta fito da sallayanta da komai na buƙatan musulmi ta a dana,
hand bag ɗinta ta zuge, nan ta ciro wasu diary milk chocolate guda biyu, tare da wani cake, nan ta kwanta tare da jawo wayarta, power bank dinta ta ɗauko inda ta saƙala wayarta a charge, kwanciya tayi tana mecin chocolate ɗin ahankali, hakanan dai ta gwammace gwara zaman nan dana gidan SAIFUDDEEN dake cike da jin daɗin daular duniya.

Acan Gombe kuwa, Haka su Ya Ameenu suka ƙare yawonsu har suka gaji, dawowa gida sukayi inda sukayi jigum jigum.
Baba Malam ma haka ya dawo daga Dukku zuciyarsa duk ba daɗi.

Ganin yanda gaba ɗaya dangin suka tashi hankalinsu ne yasanya wani tunani ya faɗowa Ahmad, nan yaƙira Ya Ameenu yasanar masa cewa, lokacin da Zaleeha zata tafi, tabbas yaga Zaheera tazo a napep inda ta bata wani abu a jaka, sannan ita Zaleehan tatafi, ita kuwa Zaheera ta shiga napep din daya kawota, saboda haka atambayi Zahira ko tasan inda Zaleehan taje.
Habawa ae Ya Ameenu kaman kububuwa haka yaji ransa ya ɓaci, atake ya gayawa Baba Malam, nan Baba Malam yace da Zakariyya wanda tun safe yake gidan, cewa yaje ya ƙira masa Zahira, Zakariyya na zuwa ƙiranta, Mama ta buga tsalle inda ta kama hannun Zahira, tare da cewa tare zasu je, nan Mama tace da Zahiran ko kasheta zasuyi, kada ta sake tafaɗi inda Zaleeha take, dayake Zahiran ma zuciyar arna gareta, take ta kafe kan cewa bazata faɗa ba.
Atare suka shiga falon ita da Mama, cikin zafin nama Ya Ameenu ya damƙo Zahira, wani lafiyayyen mari ya sauƙe mata akan fuskarta, take tafasa wani uban ƙara, tare da buga tsalle tasoma yayyarfa hannuwanta, cikin zafin zuciya yace.
"Ina Zaleeeha ta tafi?." Bata iya basa amasa ba saboda marin ya matuƙar gigitata.
Cikin fushi haɗi da ɓacin rai Mama tace.
"Maganar banza ma kenan, wannan ai kora kunya da hauka kuke ƙoƙarin yi min, ku da kanku kuka salwantar min da rayuwar ƴata, sannan yanzu kuzo kuna tambayan Zahira, wallahi Ameenu kakiyaye ni kada kasake ka ƙara kai hannunka jikin Zahira tam!!."
Mama tafaɗa ranta amatuƙar ɓace, zuciyarta kuwa cike da fargaban kada zafin mari yasa Zahira faɗin gaskiyan inda Zaleeha take.

Ran Baba Malam a ɓace ya dakawa Mama tsawa, cikin faɗa yace.
"Ina ki ka kai Zaleeha?."
Afusace Mama tace.
"Bansan inda takeba!!."
Cikin ɓacin rai Baba Malam yace.
"Na baki nanda kafun gari ya waye, duk inda Zaleeha tashiga ki tabbatar kin dawo da ita ɗakin mijinta, idan kuwa ba haka ba, ki tattara komai naki kibarmin gidana, kuma sannan idan kin tashi tafiya ki haɗa da Zahira karkiyi kuskuren barmin ita agidana, don bana ƙaunar zama da munafuki!, kada ki manta koki ƙira Zaleeha ta dawo ko kuma kibarmin gidana ayu basai gobe ba!!!." Yana gama faɗin haka ya wuce ɗakinsa, amatuƙar fusace.
Wani irin masifeffen tsorone ya rufe Mama kadafa Baba Malam ya saketa ta koma ƙauyensu noma, wani sashin na zuciyarta kuwa zugar ruda ce ta ratsota haka yasa ta ɗan ja tsaki tare da kamo hannun Zahira, cikin ɓacin rai tace.
"Mu tafi ai nima inada gidan uba, saboda haka kwana ɗaya bazamu ƙara ba, Zaleeha ne kuma bamusan inda take ba, kuma ko sama da ƙasa zasu haɗe, aurenta da nakasashshen gurgu ya ƙare kenan har gaban abadan."





Littafina na kuɗine in kin gashi a wojema na satane. Turo katin Mtn na ɗari 300 kacal ta wannan number 09097853276 ko ka/koyi min transfer ta asusuna na 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa kana ki turo min shaidar biyan ki.

   By
*GARKUWAR FULANI*
[05/09, 7:46 pm] اسماء بشير: Hannun Zahira Mama ta kama, cikin fushi haɗi da ƙunan zuciya ta fita daga cikin falon, tabbas ita kam ta gwammacewa tafiya, da dai ta barin Zaleeha ta cigaba da zama da Saifuddeen, cikin ranta take cewa.
"Miye agidan naka banda baƙin ciki, da kuma tursasa mutum dole, dan mun bar gidanka, ae ba rayuwarmu muka bari ba."
Nan tasanya Zahira ta haɗa kayanta, itama duk wani abubuwan buƙata nata ta haɗa, Zahira kuwa ganin dagaske tafiya zasuyi yasa, ta fashe da kuka, cikin fargaba haɗi da tsoro, tace.
"Banason tafiya Mama, banason yin nesa da gida, bani da wani waje wanda yafimin gida, kinsan banason ƙauye, nikam wallahi zanje na bawa Baba Malam haƙuri, bazan iya tafiya nabar gida ba..."
Wani wawan tsawa Mama ta daka mata, cikin takaici haɗi da ɓacin rai tace.
"Zakimin shiru ne ko sai na kakkaryaki, banza wacce bata kishin mahaifiyarta da ƴan uwanta, ko anfaɗa miki nan ɗin aljannar duniya ce, da har idan muka barsa zamu tagayyara, to kiji da kyau, kamar yanda yace baya buƙatarmu, muma haka bama buƙatar kowa dake cikin gidan."
Haka Mama taja hannun Zahira, suka fita, kuka sosai Zahira keyi, har cikin ranta batason barin gida da kuma ƴan uwanta.
Suna fita Mama ta tara musu mai napep, nan tace.
"Ya kaisu bakin tashar Gombe line".
Inda ananne zasu samu motar da zata kaisu Ɓilliri.
Suna zuwa kuwa suka samu mota, dama mutum biyu rak, ya rage motar ta tashi, suna shiga kuwa, aka kama hanyar Ɓilliri dasu.

Can gidan su Saifuddeen kuwa, har yanzu hankalin su Ummee atashe yake, sosai ɓatan Zaleehan ya jijjiga zuƙatansu, don ɓatan mutum ba abun wasa bane,  gaba ɗaya farin ciki da walwalan gidan ya ƙaura, damuwa ne yacika zuciyoyinsu, sam Saifuddeen kuwa ya ƙi aminta wajen sanyawa zuciyarsa damuwa, gashi kuma ko kaɗan baison ganin Umminsa cikin wani hali.
Haka ya Ameenu da Habu haɗi da Ahmad suka zama basu da wani aiki sai neman Zaleeha'n, duk wani waje dasuke tunanin zata iya zuwa, harma da wanda basa tunani saida sukaje.
, inda yazamana kullum sai sun fita nemanta.

Acan Numan kuwa, tunda Zaleeha tazo, babu abun dake fitar da ita, aɗakin sai Alwala, don dama da butar ta tazo, saboda tasan bazata taɓa samun buta awajensu ba, daga kan sallaya Qur'an sharbi,  babu abun da ta bari, wanda tasan dole zata buƙacesu,  koda dare yayi, haka Elizabet ta kawo mata, tuwo miyar shuwaka, sam bata ko kalli abincin ba, don kuwa batasa aranta cewa zata ci ba, kwanciya tayi tare da jawo jakarta, sweet ta ɓare inda ta jefa abakinta,  wayarta da ta cika da charge ta ɗauka, nan ta kunna data'nta, kai tsaye Instagram ta shiga, nan ta tarar da saƙon fans ɗinta, kala-kala, babu ɗaya da ta bawa amsa, haka tashiga duba hotuna, wanda su suka ɗebe mata kewa, gajiya da Instagram ɗinne, yasa ta faɗa Youtube, nan tayi downloading wani series film ɗin da tasaba gani kwanakin baya, wato Money Heist,  kallo ne ya taimaka inda ya rage mata kaɗaicin da take ciki, ahaka har bacci ɓarawo ya ɗauketa.

Abuja Nigeria.

Duk da kasancewar dare ya raba, amma duk yanda taso bacci ya ɗauketa abun ya ci tura,  sosai takejin tarin damuwa acikin zuciyarta, hawayen da suka cika idanunta ne suka samu daman gangarowa kan fuskarta, ahankali takai hannunta kan fuskarta ta inda ta share hawayen,  ganinta ta ƙara mayarwa ga screen ɗin wayar ta, wanda ke riƙe ahanunta,  hoton kyakkyawar fuskarsa ne bayyane akan fuskar wayar,  sosai yayi kyau cikin shigar ƙananan kaya dake jikinsa, wanda rigane da wando, masu kalan pink yasanya a jikinsa, sun kuwa matuƙar amsar jikin nasa,  idanunta ta lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya tana mai jin kishi da jin tsanar matar daya auran, har zuwa yau takasa ciresa aranta, ba tasan wani irin so ne takeyi masa ba, domin kuwa har wani zafi takeji azuciyarta, aduk sanda ta tuna da cewar yana da mata, taso zama wani ɓangare na rayuwarsa, amma burinta bai cika ba, sai dai tasa aranta cewa idan da rai to da rabo,  idan tana da rabon raɓan jikinsa, watarana zata zamo matarsa, wani ɗan guntun murmushi ne ya bayyana akan ƴar kyakkyawar fuskarta, wata zuciyarta ce tace da'ita.
"Ameena ba kyaji, shin bayan Saifuddeen babu wasu mazan ne aduniya?."
Sake faɗaɗa murmushin dake kan fuskarta tayi, ahankali tace.
"Bayan shi akwai wasu maza masu tarin yawa, saidai shiɗin na musammanne,  irinsa guda ɗaya ne, acikin maza, bayanshi babu waninsa, wannan dalilin shiyasa nake matsanancin so da kishinsa wata can ta malliki abinda duk nake bege da so daga gareshi."
a bayyane tayi maganar, domin gaba ɗaya ta faɗa cikin shauƙin ƙaunarsa, aranta ji take inama inama, da ace Saifuddeen zai zama mallakinta, to tabbas da sai tafi kowa murna da kuma farin ciki, duk da cewar tasan shiɗin ya girmewa ajinta, amma ba laifi itama ta yarda da kanta, don kuwa babu laifi, tasan  tana da nata kyau'n, domin Allah yayi mata sura, ɗan dadai haɗi da kyaun fuska, duk da kasancewar kai tsaye baza'a ƙirata da sunan kyakkyawar gaske ba, da ka nutsa da kallonta sosai kuwa, to  anan ne zaka fahimci irin nata sirrin kyaun,  domin kuwa sam ba baƙa bace, haka zalika bata kasance fara ba, saidai tana da kala mai kyau, domin  takasance tana da  brown skin mai kyau musamman dayake tana ɗan ƙara farin da mai, sannan afuskarta tana da ɗan madaidaicin hanci, mai ɗan tsawo kaɗan kuma karan hancin ba sosaiba, sai kuma ƴan saffa-saffan idanunta, masu ƴan siraran gashi a samansu, babu laifi domin tana da ɗan gashin gira iya dai-dai gwargwado,   sannan bakinta ma bashi da wani girma sosai, daga ɓangaren gashin kai kuwa, tana dashi dai-dai misali amman baida laushi, , kuma shima bashi da tsawo sosai.
A taƙaice dai Ameena itama kyakkyawar mace ce, amma kuma ko kusa bata tako Zaleeha akyau ba, balle kuma aje ga uban gayyan wato Handsome guy ɗin Saifuddeen kenan.

Don kuwa har yanzu da mutane sun kasa tantance tsakanin shida Zaleeha wa yafi wani kyau, sai-dai  idan za'a misalta tsananin kyawun  da Zaleeha'n, ke dashi,  koda  zata ɗarasa kyau ma ƙaɗan ne, domin kasancewarta mace, dole tsarin halittarsu ya banbanta.

Gyara kwanciyarta tayi tare da jawo pillow tayi hugging ɗinsa,  cikin zuciyarta tace.
"Ya Allah Ina roƙonka ka cigaba da zama gatana ako da yaushe,  Ya Allah Ka mallakamin Saifuddeen, amatsayin mijina, Ya Allah Kadubi zuciyata!."
Ajiyar zuciya ta sauƙe, tare da ɗaukan wayarta ta manna a ƙirjinta, hakanan takejin wani irin nishaɗi acikin ranta.
Da tarin tunaninsa a haka bacci ɓarawo ya ɗauketa.

GOMBE NIGERIA

Abubuwa da yawa sunata wakana acikin garin Gombe, inda gaba ɗaya yakasance a tsakanin gidan su Saifuddeen da kuma nasu Zaleeha, sam babu kwanciyar hankali, don kuwa yau kimanin kwana bakwai kenan da ɓatan Zaleeha, amma shiru har yanzu babu wani labari, wayoyinta kuwa har zuwa yau suna shiga, amma abu ɗaya ne har yau, shine bata ɗaukan ƙiran kowa, saƙonnin text message kuwa na ban tsoro da gargaɗi, akan duk inda take ta dawo gida, babu kalan wanda Ya Ameenu da kuma Ya Habu basu tura mata ba, amma Zaleeha da ta gani ko bin takansu batayi.

Messages ɗin Ya Ahmad kuwa sunfi 20 wanda da ya tura mata, wanda suke cike da tsantsar lallashi haɗi da ban-baki yake bata, tare dayi mata al'ƙawarurruka da dama akan idan ta dawo zai yi mata, ba irin al'ƙawarin da baiyi mata ba, har cewa yayi da ita.
"Pleess Zaleeha ki dawo gida hankali kowa ya tashi sabida rashinki,
wlh idan kika amince kika dawo gida, to zan sa araba aurenki da Saifuddeen, sannan kuma zan ɗaukeki mu koma Abuja, zan sama maki aiki acan."
Koda ta karanta murmushi kawai tayi, sanin cewa hakan abune mai wahala, domin tasan cewa Yayan nata bashi da wani abun da yakeso, sai wanda Baba Malam yakeso, farin cikin Baba Malam shine nasa, tasan cewa bazai taɓa iya raba auren ta da Saifuddeen ba, domin yin hakan zaisa ya faɗa cikin fushin Baba Malam, wanda tasan da Ya Ahmad ɗin  da ya faɗa cikin fushin Baba Malam, tasan zai gwammace gwara mutuwarsa.
Haka koda ta karanta text ɗin, ta watsar tare da gogewa, don kuwa sun cika mata inbox da saƙonninsu, ita harma ta gaji a can ƙasan zuciyanta kuwa ji take kamar taita kuka.

Ɓangaren Ya Habu kuwa, yau yagama shirinsa tsab, inda ya ƙudurta aransa cewa, yau zai je Doho, wajen Yayar mahaifiyar tasu, wato Aunty Ruda, domin ransa amatuƙar ɓace yake da ita, saboda yasan cewa, duk wani abu da maman tasu keyi, da sanya hannunta, kasancewar kowa yasan cewa, ita ɗince ke zugata  akan wasu abubuwa itace ke gurɓata komai na Mamansu.

Ya Ameenu kuwa yanzu damuwar rashin lafiyar matarsa ne ya damesa, don kuwa tun randa Zaleeha ta gudu, Maryam ta kwanta zazzaɓi da ciwon kai, kasancewar bata da wani aiki kullum sai kuka, sosai ɓatan ƴar uwartata ya shiga jikinta, gefe guda kuwa ga Baba Malam daya shiga halin baƙin ciki,  kowa ya gansa yasan da cewa yana cikin damuwa,  kasancewarsu Yara masu biyayya hakan yasa basa ƙaunar ganin damuwar mahifinsu, uwa uba ga Mama da ta bar gidan, wannan abu na damun Maryam sosai, ganin lokaci ɗaya zuri'arsu naneman watsewa komai ba daɗi ga ɓatan ƴar uwa ga saɓani tsakanin iyayenta ga ɓacin ran mahaifinta damuwa dai ta taru ta cika zuciyar baiwar Allah.

Ƙarfe 10 na safiyar ranan dai-dai Ya Habu ya kama hanyar zuwa Doho.


Zaune yake akan wheelchair ɗinsa mai kalan silver gold,  sanye yake da wani army jeans, sai kuma wata farar long sleeve wanda ya nannaɗe hannun rigar zuwa guiwar hannunsa, aƙafansa kuwa, wasu fararen  bedroom slippers ne masu kyau,  kamar koda yaushe laptop ɗinsa ne, ɗaure akan cinyarsa, sosai ya bata hankalinsa gurin binciken da yakeyi.
Gefensa Ummi ne wanda tayi jigum, duk damuwan ɓatan Zaleeha ya isheta, kusa da ita kuwa Hayatuddeen ne zaune yana ta faman latsa wayarsa, inda ya ɗan kaucewa ganin idanunsu ya matsa can gefe, chatting yake sosai, da wani sabon abokinsa da yayi acikin G.S.U, wanda yakasance department ɗinsu ɗaya, sunan abokin nasa Khamis, sosai Hayatuddeen yasoma shaƙuwa da Khamis, wanda yake kuma Khamis, yaro ne wanda bayajin magana sam, babansa mai kuɗin gaske ne, gidansu yana nan cikin New G.R.A, gaba ɗaya Khamis asangarce yake, kasancewarsa shine  ɗa namiji agidansu, hakan yasa gaba ɗaya iyayensa suka sakar masa yarda, tare da bashi daman yin duk abun da yake so,  shikuwa Khamis tun da yaga Hayatuddeen, yaji cewar yana sonsa da abota, kasancewar Hayatuddeen ba laifi yana shiga mai kyau da burgewa, sannan yana ɗan chilling ɗinsa, da sabuwar iphone ɗinsa,  makaranta kuwa kaisa ake amotar gida sannan driver ya ɗauko sa, shikuwa Khamis jibgegiyar motace ahannunsa,  hakan yasa ko zaman school ɗin bayayi, da yazo sai yawo kawai, kamar da wasa kuma suka fara abota da Hayatuddeen wanda gashi kuma zuwa ayanzun abotan nasu ya soma ƙarfi.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi ya sauƙe tare da lumshe kyawawan idanunsa, buguun zuciyarsa ne ya ɗan sassauta ahankali, hannunsa yasanya inda ya kama ƙasan haɓarsa, numfashi ya sauƙe, tare da fesar da wani irin iska mai zafi ta bakinsa, 
*"NUMAN"* shine abun daya faɗa acikin zuciyarsa, sake duba inda location ɗin  ya tsaya,  kansa yajinjina tare da ɗan cije laɓɓansa, tabbas tana can Adamawa cikin Numan domin kuwa, haka sakamakon tracker ɗin da yayi ya nuna mishi.
Ɗan jim yayi tare da lumshe idanunsa, 
"Tabbas tana can Numan, amma kuma waye nata acan, da zata je ta zauna?."
Tambayar da yayiwa kansa kenan, sanin cewa bashi da amsa yasa shi, sakin ɗan guntun murmushi,  wato da zama dashi ne ta gwammace rayuwa a wancan ƙauyen mai cike da yawan ƙabilu arnataku, hmmmm shikuwa zai zuba mata ido ya gani, bakuma zai faɗawa kowa inda take ba, sannan zaiyi duk yanda zaiyi wajen ganin, ya cire Umminsa adamuwa, dan tasanya ɓatan Zaleeha'n, sosai acikin ranta.

Ta gigita mishi ƴan uwa da abokai gaba ɗaya, Ishaq Salisu Warisu Mudassir Aziz hatta Saminu Hishsm, Jabeer, da baya garin duk ta tashi hankalin kowa.

Yasan ko ahaka Allah bazai bar Zaleeha ta zauna cikin farin ciki ba, saboda yasan ta ɗauki al'hakin iyayenta, sannan ga igiyar aurensa dake kanta, wanda take ta walagigi dashi.
Wheelchair ɗinsa ya danna inda ya ƙarasa har gaban Umminsa, hannunsa ya ɗaura akan na Ummi'n, cikin kulawa ya karyar da kansa, tare da ɗan marairaice fuska, anutse yayi mata alama, cikin body language cewa.
"Ta daina sa kanta adamuwa, Zaleehan zata dawo nan bada jimawa ba."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe, cikin rauni ta dubeshi, murya asanyaye tace.
"Banajin daɗi Saifuddeen, idan na tuna da cewar sanadiyar aurenka Zaleeha ta gwammace barin iyayenta, yayunta, ƙannenta, aikinta, mahaifanta, da duka danginta, wannan abun shine abun danake ta gudu tun farko, shiyasa naso afasa auren,  gashi yanzu an nemeta an rasa, babban tashin hankalina ma, shine bamu da tabbacin cewa ko lafiya take!."
Kansa ya girgizawa Ummin nasa, tare dayi mata alaman cewa.
"Zaleehan tana nan lafiya ƙalau aduk inda take."
Kai kawai Ummi ta jinjina masa don bata iya cewa komai.

Can Doho kuwa, Ya Habu na isa gidan Aunty Ruda yayiwa tsinke,  Aunty Ruda na ganinsa ta taɓe baki, don tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi,  first abun da Ya Habu ya fara tambayarta shine.
"Ina suka kai Zaleeha?."
Shewa tayi tare da cewa.
"Ae baku bani ajiyan Zaleeha ba, balle kuce zaku zo nemanta, abu mafi sauƙi ku shiga uwa duniya ku nemeta kawai, tun da kune kuka salwantar da rayuwarta."
Wannan abun shiya ƙara harzuƙa Ya Habu, nan take ransa ya ƙara baci, haka yayiwa Aunty Ruda'n tas, inda ya wanketa soso da sabulu, ya ɗora da cewar.
"Ita ke zuga mamansu akan komai, kuma wallahi su fito da Zaleeha, duk ma inda suka kaita suka ɓoyeta, kuma ta daina zuga musu uwa tana tura mata halinsu na arna ya ƙara da cewa kada tayi zaton basu gane ita ke zuga Mamaba."
Haka yabaro Doho'n ransa amatuƙar ɓace, domin yasan da cewa sunsan inda Zaleehan take faɗa ne kawai bazasuyi ba.

Bayan kwana 5 da dawowan Ya Habu daga Doho, Baba Malam ya kwanta rashin lafiya, inda ciwon hawan jininsa ne ya tashi,  nanfa gaba ɗaya ahalin suka sake shiga cikin tashin hankali, ga jikin Maryam ma da yaƙi daɗi, bata da wani zance saina ƙanwarta Zaleeha.

Saifuddeen dake zaune afalon Ummi ne, ya kwantar da kansa ajikin kujera,  yanzu labarin rashin lafiyar Baba Malam ya iskesa, hakanne yasa yaji babu daɗi acikin ransa, sam ada baiyi niyar faɗawa kowa inda Zaleehan take ba, yaso barinta ne idan tagaji don kanta zata dawo, amma ayanzu yazama dole ya faɗa, kodan saboda rashin lafiyar Baba Malam ɗin ma.
Computer ɗinsa ya ɗauka, inda yayi rubutu mai ɗan tsawo, sannan ya nunawa Ahmad,  bai jirayi Ahmad yagama karanta saƙon ba, ya ciro wayarsa inda ya turawa Ya Ameenu saƙo,  wanda ya rubutashi ataƙaice.
Ahmad nagama karanta saƙon ya ɗago ya dubi Saifuddeen, kai Saifuddeen ɗin ya jinjina masa, ajiyar zuciya Ahmad ɗin ya sauƙe, nan yakai dubansa ga Ummi, sai kuma Adda Rahama dake zaune, cikin nutsuwa Ahmad yace.
"Ummi Saifuddeen ya ganno inda Zaleeha take fa."
cikin mamaki Ummi tace.
"Ta ina? Tana ina? ko wani abune ya sameta?."
Kai Ahmad ya girgiza, cikin nutsuwa yace.
"Uhmmm Ummi kenan wato dai kuna ganin kaman Zaleeha ɓata tayi ko, hmmm to wlh Zaleeha ba ɓata tayi ba, guduwa tayi da ƙafafunta, sannan yanzu haka tana can Numan, halan akwai wasu ɓoyayyun ƴan uwanta acanne, wanda tunanin su Ya Ameenu da Habu baije can ba, amma dai yanzu Saifuddeen ya faɗawa Ya Ameenu'n."
Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayin hamdala acikin ranta, tabbas ta ɗanji sanyi acikin ranta,don dama ɓatan Zaleehan yayi mata tsaye acikin rai, itakuwa Adda Rahma shiru tayi tana meyin wasu nazari,  hakanan Zaleehan ta soma sanewa acikin ranta, tabbas ita duk wani wanda baison Saifuddeen, to fa itama bata
ƙaunarsa ko kaɗan. Raihana kuwa da dama can bata wani sake da Zaleeha a rantaba, sai taji ta fice mata a rai haushinta kawai takeji har ita waye da zatace bata son Hammanta me ya rasa dame sauran maza suka fishi haka dai taketa ƙunƙuninta.


Ƙiran Ya Ameenu ne yashigo wayan Ahmad, da sauri Ahmad ya ɗaga wayan.
Daga ɓangaren Ya Ameenu, wanda ke zaune acikin falon Baba Malam, kasancewar dukaninsu suna cikin falon, hakan yasashi sanya wayar a speeker,  yanda kowa zaiji, tambayar Ahmad yayi akan saƙon dayaga Saifuddeen ya turo masa, nan take Ahmad yayi masa bayanin dukkan abun da Saifuddeen ya faɗa masa, inda yace ta hanyar yin tracker Saifuddeen ɗin ya gano inda take.
Nan take gaba ɗaya suka cika da mamaki, domin koda wasa basu taɓa zaton cewa zataje Numan ɗinba, saboda su kwata-kwata ma sun manta da cewa Mama tana da ɗan uwa acan, domin kuwa ba zuwa take ba, suma kuma ba zuwa suke ba.
Ya Ameenu na kashe wayan, Baba Malam dake kishingiɗe yana shan fruit salad, ɗin da Mamy ta haɗa masa ya saki ɗan guntun murmushi irin nasu na manƴan dottijai murmushi mai cike da ma'anoni da manufa masu tarin yawa,
  cikin baƙin ciki Ya Ameenu ya rusuna gaban Baba Malam ɗin cikin neman izini yace.
"Kayi haƙuri Baba idan kayimin izini kabarni naje ayau ɗinnan na taho da ita gida."
Ahankali Baba Malam ya aje bowl ɗin dake hannunsa kai ya jujjuya mishi alaman a a,  cikin kulawa ya dubi Ya Ahmad, wanda yayi jigum, anutse yace.
"Ahmad ka ɗauki matarka gobe ku koma, banason zamanka hakanan, saboda haka ka koma bakin aikin ka."
Cikin salon bada umarni wa yaran nashi ya kalli Habu dake jin tamkar yayi fiffige ya fire yaje Numan cikin haiba da kamala yace.
"Kai kuma Habu nabaka izinin gobe kaje can Numan ɗin, badai kasan gidan yayan Mamar taku dake can ba?."
Kai Ya Habu ya jinjina tare da cewa,
"Eh."
Ajiyar zuciya Baba Malam ya sauƙe tare da cewa.
"To nayi maka izini kaje, duk wani abu dakasan na Saifuddeen ne wanda Zaleeha tatafi dashi ka ƙwatosa ka kawomin, sannan ka ɗauko masa kayayyakin aurensa wanda ta tafi dashi, amma kuma koda wasa kada kace zaka ɗauko ta, badai ta zaɓi guduwa da zaman can ba, shikenan kubarta ta zauna acan ɗin, da sannu duniya zata koya mata hankali, kadai ji abun dana faɗa maka ko?".
Da sauri Habu ya gyaɗa kanshi alamun eh, shi kuwa Baba Malam a kausashe yace.
"Bana buƙatar ta saboda haka koda wasa kada kayi kuskuren ɗauko min ita, kabarta acan, amma kaya dai dayake mallakin Saifuddeen kada kabar ko abu ɗaya awajenta."
Cike da gamsuwa Ya Habu ya jinjina kansa don shima, zaifison abar Zaleeha'n, ta ɗana ƙunci da baƙin ciki data ɗana musu.
Duban Ya Ameenu Baba Malam yayi cikin kulawa, ya dafa kafaɗunsa, kana yace.
"Matarka bata da isashshen lafiya Ameenu, saboda haka ku koma gida kaje ka kula da ita, saboda tana buƙatar kulawanka, in sha Allah Maryam ƴar aljannace, domin takasance ƴa mai biyayya ga mahaifinta, haka kuma ga mijinta, tabbas Maryam ƴa ɗayace tamkar da dubu, sannan itaɗin mafi soyuwa ce agareni, saboda haka bazanso ace kayi mata nisa, ka ɗauketa ku koma gida kaji!."
Cikin yanayin gamsuwa Ya Ameenu yace.
"To."
Gyara zama Baba Malam yayi, cikin nutsuwa yace.
"Kudukan ku idan kuka sake sanya damuwar Zaleeha a cikin ranku, to tabbas zanyi fushi daku, haka ta zaɓa haka kuma take ganin yafi mata, saboda haka mu ƙyaleta, ita da kanta wata rana zata dawo, kutashi kuje kowa yayi sabgogin gabansa, ko da ita ko babu ita zamu rayu."
Haka dukansu suka

Please Login or Register in order to submit comment