Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da murzarta tun Seeyama tana daurewa har yakai takasa kuka tasakarmai amma ko sauraranta baiyiba seko dayaji anfara kiran sallar farko sannan yarabu da ita amma dukda haka bai kusancetaba murza kawai tasha tashi yayi yashiga toilet yayo alwala Sallar nafila yatada kafin ashiga masallaci har lokacin Seeyama takasa ko motsi sabida duk illahirin jikinta ciwo yakeyi

Bayan ya idar yatashi zaitafi masallaci cikin dakakkiyar muyar yace

" kibar bedroom d'in nan kafin nadawo idan kuma bahakaba tozanyi miki abinda yafi na d'azu "

Daga haka yasakai yafita

Kallo tabishi dashi dankam ayanzu mugun tsoranshi takeji cikin ranta tace

" mugu kawai se Allah yasakamin "

Cikin matu'kar ciwon jiki tami'ke da'kyar tamaida rigarta tabar bedroom d'in tana shiga nata tahau saman bed d'in ta blanket taja tarufe jikinta sabida wani irin sanyi dayafara kad'ata ga masifar zugin da Breast d'inta keyi ga lips dinta dasu har sun kumbura

Koda DON yadawo ganin bata bedroom d'in yasashi girgiza kai afili yace

" dakin bari nadawo nasameki marar kunya kawai "

Misalin 9am Hajiya Saratu tashiga cikin bedroom d'in Seeyama ganinta a lullu'be yasata saurin 'karasawa cikin farinciki tace

" masha Allah Seeyama komi yayi dede ay tunda naka bakifitoba nasan komi yafaru ina fatande kinsamu kin gasa jikinki ? "

Ganin batace mata komiba sema had'a fuska datayi yasa Hajiya Saratu yin murmushi tasake cewa

" ayya Seeyama dole kiyi ha'kuri zakiji sau'ki kinji bari nabarki kihuta Allah ya inganta mana wannan baby "

Wata irin harara Seeyama tabita dashi misalin 10am DON yafito cikin shirin tafiya ganin Hajiya Saratu a parlour yasashi nufar gurinta gaidata yayi sannan yace

" to Umma nizan tafi ga wannan kozaku bu'kaci wani abu "

Cikin rawar jiki ta'amshi rafar 'yan 1000 daya mi'kamata cikin 'kasa da murya tace

" Allah yatsare amma kayi sallama da matar taka ? gashima batada lfy "

Cikin rashin sonyin magana yace

" zan shiga yanzu "

Daga haka yayi gaba kai tsaye yashiga bedroom d'in nata zaune take tsakiyar gado ta jingina kanta jikin gadon kallo d'aya yayi mata yad'auke kai kud'i yaciro aje mata saman bed d'in sannan yace

" ni natafi zanbar security 4 sabida naga kuna bu'katar tsaro "

Daga haka yajuya yafita kallo Seeyama tabishi dashi had'in rumtse idonta cikin ba'kin ciki tace

" Wato bamazai yimin sannuba amma nasan sabida nice nakai kaina hmmm DON nayi al'kawarin seka nemeni kana zubda hawaye amma na'kibaka kaina ni kad'aice matarka dole kadawo gareni DON "

Cikin muryar shi mai taushi DON yashiga cikin parlour cikin girmama yagaida su Dady sannan suka gaisa da Ashiraf zama yayi kusada Ashiraf cikin farinciki Dady yace

" DON inaga za'ayi hidimar bikinku kawai Kausar tatare tunda takusa kammalawa kuma sunyi maganar da mahaifiyar ta akan yanayin kayan datake bu'kata to tace duk wa'inda kaga sunyi maka amma DON wa'innan kayan da kajibgoma Kausar sunyi yawa inaga arage wasu a'karama Seeyama tunda nata basukai wa'innan ba "

'Dago kai DON yayi sabida yadda yaji maganar Dady kallon hanyar bedroom d'in Kausar yayi sannan yace

" a'a Dady baza'ayi hakaba lefan Seeyama kune kuka had'ashi wannan kuma nine nahad'a kaga babu maganar rashin adalci sannan maganar hidimar bikin inaga idan ankammala komi nacikin gidan nanda 1 week kawai akawota basai anyi wata bidi'aba tunda nima yanzu bawani lokaci gareni ba "

Murmushi Momy tayi tace

" hakane amma zamuyi taro koda walimace ayi sabida tabbatar ma 'yan uwa auran auta "

Jinjina kai DON yayi sannan yace

" hakane momy idan kuna bu'katar wani abu dan Allah asanar dani "

Murmushi Dady yayi yace

" haba my son kana nufin akan hidimar bikinka sena nemi wani abu daga gurinka Allah yasauke maiye afmanin dukiyata "

Shiru DON yayi dan yasan duk abinda zaice Dady bayarda zaiyiba shiru nawani lokaci sannan DON yace

" Dady zuwa anjima zantafi sabida zanje nayi wani ayki na gaggawa sannan zan tantance ma'aykatan dazan d'auka masu hidimar gidan "

Jinjina kai Dady yayi sannan yace

" Allah yakaika lafiya Son amma dan Allah karkace zaka bar Seeyama a wancan gidan kamaidata can kahad'a kan matanka ana kammala komi takoma can "

Shiru DON yayi amma baiji dad'in hakanba amma babu yadda zaiyi jinjina kai yayi alamar hakan za'ayi amsar wayar Ashiraf yayi cikin hikima yad'auki number Kausar

Tashi DON yayi yace

" Dady bari nad'a shiga ciki zuwa anjima nawuce "

Murmushi yayi shida Momy shikuma Ashiraf cewa yayi

" haba brother kaide kace zaka shiga ganin matarka "

Wani irin kallo yayima Ashiraf cikin murmushi Dady yace

" Eh ay garashi kaifa gouron banza kawai ay nakusa zuwa kanka garama kafiyar da matar aure tunkafin nafitar maka "

Jin haka yasa Ashiraf tashi yafita dan yasan idan suka fara badad'i zaijiba DON nashiga bedroom d'in Ashiraf yadanna kiran Kausar

Cikin sakka tad'aga sabida ita tanada number shi cikin lallausar muryar ta tace

" Assalama alaikum my Sweety barka da safiya "

Shiru yayi nad'an lokaci zuwacan yace

" bakisan nashigobane ? ki kawomin breakfast ina cikin bedroom d'in Ashiraf "

Kafin tace wani abu yakashe kiran bin wayar tayi da kallo afili tace

" bansan lokacin da zaka rage wannan miskilancin ba kenan bakaci abincin Amarya ba "

Fitowa tayi tanufi kitchen abu mai sau'ki tayimai babu jimawa tagama cikin matu'kar jin kunyar shi tashiga cikin bedroom d'in zaune yake akan sofa agabanshi ta'aje cikin girmamawa

Kallon ta yayi sannan yace

" bakibar kukan bako ? "

Girgiza kai tayi alamar tabari shiru yayi baisake cewa komi ba cikin sanyin jiki tazauna tana fuskantar shi bashi break d'in tashiga yi har yagama seda yasata itama taci sosai sannan yabarta tamaida kayan kitchen bayan tadawo shiru babu mai magana sannan yami'ke kud'i ya aje mata sannan yace

" zantafi se kinji saka makon bincikena "

Daga haka yafita sallama yayi masu Momy Dady kuma sede yakirashi a waya sabida yariga yafita cikin sanyin jiki Kausar tafito har bakin mota tarakashi sannan takoma

Zaune DON yake cikin mota amma tunanin abubuwa dayawa yaketayi

Kai tsaye office yace sunufa anayin parking yafito ganin yadda security ke korar wani yaro yasa DON tsayawa cikin tamke fuska yace

" maiye haka ? kubarshi "

'Daya daga cikin Security d'in yace

" wallahi ranka shidad'e wannan yaron yacika naci tun jiya yadamemu waishi kai yakeson gani "

Cikin bada umarni yace

" kubarshi kushiga dashi ciki zuwa anjima zan ganshi "

Cikin masifa Hajiya Aysha tace

" wallahi Alhaji Sambo baka isaba d'an nawa shikad'e zaka d'auka kakai ma mahaifiyar ka kumama a 'kauye wallahi bazan yardaba seka dawomin da Abdulhakim "

Cikin tsawa Alhaji Sambo yace

" amma de kinsan Abdulhakim d'anane ko kuma nafiki iko dashi to babu wanda ya 'isa yahanani kaishi inda nagadama idan kinason nuna isa akan d'a to sede kinemo Affan shine wanda zaki nunamin iko akanshi amma ba Abdulhakim ba "

Cikin tsawa tace

" to ay shima Abdulhakim d'in ba d......... "

Saurin rufe bakinta tayi cikin sauri yajuyo yace

" mai kike son cewa ? "

Gaba tayi tashige cikin bedroom 'kwafa yayi yace

" kitsaya ki maimaita mana shashasha kawai "

Tofa su'butar bakin mai Hajiya Aysha tasoyi

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please love u all sisters
[22/06 4:26 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯° all sisters love u

πŸ…Ώ { 35 to 36 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Hajiya Aysha nashiga cikin bedroom d'in ta tazauna bakin bed kallon picture d'in Alhaji Isma'il tayi cikin damuwa tace

" katafi kabarni da kwantaccen cikin Abdulhakim amma sabida 'kingaskiya na halattama Alhaji Sambo shi amatsayin nashi gashi zai rabani dashi bayan yasa narabu da yayan shi sannan duk ya kwashe dukiyata se 'kalilan daga ciki innalinlahi wa'inna ilaihirraju'uuun tayaya zan fiddo gaskiya akan Abdulhakim ba d'an Alhaji Sambo bane d'an Alhaji Isma'il kwangila ne ?

Tsayin lokaci Hajiya Aysha tana neman mafita amma takasa samu cikin matu'kar tamke fuska DON yace

" kutafi maza ku d'akkomin Ameera "

Cikin sauri suka fita kallon sauran yayi yace

" ku kawomin yaron nan "

Fita sukayi babu jimawa suka shigo dashi kallon shi yayi sannan yacigaba da rubutu tsayin lokaci wani daga cikin ma'aykatan yashigo yace

" Oga wa'innan almajiran sun iso "

Jinjina kai yayi sannan yafiddo wallet d'in shi duka yaciro kid'in ciki yami'ka mishi aje katinshi yayi saman teburin yashiga kallon wannan abinda Amina tabashi na nannad'e a takarda idanun Abdulhakim suka kai kan wannan katin ganin sunan dake jiki yasa Abdulhakim sake maimaitawa

" Affan Isma'il kwangila Alhamdulilah Allah yakawoni gurin d'an uwana yau gaskiya Dady kayi kuskure dama nayi niyyar sanar da DON 'kudirin ku segashi ashe DON shine brother na gaskiya Dady bazanyi maka biyayya ba akan wannan zan taya d'an uwana ya'ki zanshiga gidan shi kamar yadda kasani Dady amma kareshi zanyi ba cutarwa ba duk da kake mahaifina bazan goyi bayan cutaba kumama ga brother na ? ina bazan s........... "

Maganar DON yasa Abdulhakim dakata zancen zuciyar shi

" maiye sunan ka ? Abdulhakim Isma'il "

Cikin sauri yadubeshi sabida jin sunan mahaifin shi sekuma yacigaba dacewa

" lafiya kake son ganina tun jiya gaka yaro dan nasan bazaka wuce 15 years ba maiye matsalar ka Abdulhakim "

Kuka Abdulhakim yasaki sosai hadda yin kamar zai shid'e tuni yabama DON tausayi tun kafin yacemai komi cikin kuka Abdulhakim yace

" Brother dan Allah kataimakeni 'yanfashi sunkashe iyayena kuma bansan kowaba a 'kasarnan bansan inda danginsu sukeba dama ni'kad'ai garesu dan Allah brother nadad'e inazuwa nan ina ganin yadda kake taimakon jama'a dan Allah brother "

Sake fashewa yayi dakuka tabbas DON yatausayama Abdulhakim sosai musamman yatunomai da mahaifin shi yadda 'yanfashi suka kasheshi tuni yaji damuwar shi tadawo sabuwa cikin 'karfin hali yace

" Abdulhakim kayi ha'kuri kaji zaka zauna taredani amma zanyi binciken lamarin naka "

Kiran wani daga cikin ma'aykatan yayi yace

" wannan 'kaninane Abdul kaje dashi abashi duk abinda yake bu'kata kafin natashi tafiya "

Ana tafiya da Abdulhakim DON yakoma yazauna dafe kanshi yayi cikin damuwa

" sunjefa rayuwar 'karamin yaro cikin garari nima haka Momy taso nayi amma Dady yahana faruwar hakan "

Shiko Abdulhakim binciken da DON yace zaiyi shine yad'aga hankalin shi har office d'in DON aka kai Ameera ciki hadda Amina dan itama yana bu'katar sanin wasu abubuwa game da ita ganin in da aka kawo Ameera yasata sakin ajiyar zuciya dan da gabanta yayi muguwar fad'uwa amma ganin DON yasata jin cewa zata iyar jure komi

Tamke fuska DON yayi sannan yacema sauran ma'aykatan duk sufita bayan fitar su tsayin lokaci sannan cikin murya mai tsauri yace

" Ameera bashir mai Kausar tayi miki dahar kike binta da mugun sharri ? Ciki hadda aykata mata mugun zalinci "

Jin haka yasa Ameera d'an razana amma seta dake tace

" ni banyi mata komiba hasalima duk cikin Skul itace babbar 'kawata "

Jinjina kai DON yayi sannan yayi kira bayan anshigo yace akawo wa'innan samarin hadda wanda aka tahodashi taredasu Kausar babu jimawa aka shigo dasu ganin su yayi matu'kar tada hankalin Ameera musamman dataga hadda Jamilu kallon su DON yayi yace

" ku maimaita mata bayani "

shiko wanda aka kamo yanzu cikin matu'kar razana yace

" Yallabai dama kai ne ? "

'Kara tamke fuska DON yayi sannan yace

" ina kasanni ? "

Cikin in'ina yace

" aykai mukakai ma Kausar cikin hotel a ranar 16 ga watan 4 bayan kasha wasu 'kwayoyi cikin abinsha a Restaurant bam........ "

Dakatar dashi DON yayi cikin wata irin murya wadda seda kowannensu ya furgita sha'ko wuyan jamilu yayi cikin mugun 'bacin rai yace

" kune nake nema dama ku kukayi sanadin sakani cikin damuwa Ameera kisani baki cutar da Kausar ba domin kuwa Kausar matatace kuma duk duniya babu mace cikin raina se Kausar wannan abin da kikayima Kausar kin'kara kimarta darajar martabar da Tsantar soyayyar cikin zuciya ta ni DON sena jiyar Kausar dad'i da farinciki marar misali

Zanyi muku hukunci dede da abinda kuka aykata agaban Kausar sannan zaku biya tara cikin tsawa DON yayi kira yace aje a ajiyesu sannan asanar da iyayensu "

Kallon shi Ameera tayi tasaki murmushi tace

" DON naji dad'i dakace kaine zakayimin hukunci domin ina jin matu'kar farinciki idan ina kallon kyakkyawar fuskar ka sannan ada banyima Kausar mugun abuba amma ayanzu zanyi musamman data shigarmin cikin babban hurumina dan wallahi DON kai nawane ni 'kad'e duk macan da tara'beka senayi mugun 'kuntata mata "

Cikin fad'a DON yace

" idan bakubar min nan da wannan ballagazar yarinyar ba senayi sanadin aykinku "

Zama yayi cikin muguwar damuwa da tsananin tausayin Kausar cikin ranshi kallon Amina yayi yace

" maiyasa baku sanar da hukumaba lokacin da abin yafaru ? bayan kunsan wadda tasa hakan tafaru sannan idan da bansamu damar sanin komiba yaya kenan ? kusa nadinga zargin matata ko sabida babu wata alamar dazan gane batada lefi "

Cikin damuwa Amina tace

" nasan komin dad'ewa zakasan gaskiya idan har kaga Ring d'inka dake hannun Kausar "

Dubanta DON yayi sosai yace

" Ring d'ina a hannun Kausar ? "

Jinjina mishi kai Amina tayi sannan tace

" eh yaya shine wanda nabaka a nad'e cikin paper "

Cikin sauri yad'akko yafara bud'ewa tabbas shine cikin zuciyar shi yafad'i haka

Cikin mutuwar jiki Seeyama tafito daga bedroom cikin sauri Hajiya Saratu tanufo gurin Seeyama kamo hannun ta tayi har suka isa cikin tsakiyar parlour seda suka zauna sannan Hajiya Saratu tace

" hannu Seeyama yaya jikin ? kinde shiga ruwan d'umiko ? "

had'a fuska tayi sannan tace

" Umma nifa babu abinda yafaru tsakanina dashi fa sema mugun wula'kanci da yayi min "

Cikin mamaki Hajiya Saratu tace

" dagaske kike ? Seeyama amma kinbani mamaki dakika kasa shawo kanshi akan wannan lamarin hmmm amma idan yasan wata ay baisan wataba bari yasake dawowa "

Fans kuyi ha'kuri da wannan ina busy ne please afuwan dan karkuji shirun tayi yawa

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters πŸ₯°
[24/06 3:16 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯° all sisters love u

πŸ…Ώ { 37 to 38 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin damuwa da 'bacin rai DON yafito daga office d'in shi sawa yayi aka kiramai Abdulhakim kai tsaye mota aka bud'e musu suka shiga wajan seda kaya yasa aka kaisu ba Abdulhakim umarnin za'ban wa'inda yake yayi shi kuma yakoma gefe yana kallon yaron cikin tausayawa

Ganin baya wani za'ban kayan yasa DON nufar gurin shida kanshi yashiga za'barmai sosai ya lodarmai kaya masu matu'kar kyau da tsada sannan yabiya suka fito kai tsaye saban katafaran gidan shi suka nufa

Ganin motocin shi yasa security d'in dake ba'kin 'katon get d'in saurin wangale get d'in motocin suka sakai ciki woow harabar gidan kawai abin kalloce

Anayin parking akayi saurin bu'demai get batare dawani jinkiriba DON yafito sabida ranshi dake 'bace cikin sauri yanufi cikin kyakkyawan lambun takemai baya Security sukayi gefanshi kuma Abdulhakim

Zama yayi akan 'kayatattun kujerun gurin wata irin iska mai dad'i ke kad'awa agurin gawani irin sanyi mai dad'i marar cutarwa had'ida kukan tsintsaye masu saka nishid'i da dad'in sauraro

Umarnin gabatar mai da ma'aykatan da aka d'auka DON yayi cikin sauri aka kirasu suka fara gabatar mai da kansu bayan kowa yagama DON yayi jim natsayin lokaci sannan yace

" akwai doka duk wanda yakarya to zai amshi hukunci bana soncin amana kuma banason 'karya sannan natsani sata babu shayeshaye koda sigarice idan nakama d'ayanku da wannan to zaisha mamaki mata masuyin abinci zakuyi abincine ga Security da sauran ma'aykatan amma banda ni da matata dakuma brother na gashi nan Abdulhakim sannan bana bu'katar wata mace ko namiji a bedroom d'ina dan gyarashi

Idan waninku yanada wata matsala ko tacikin gidan su yasanar dani in sha Allah zanyi mai maganin ta idan batafi karfina ba zanbama kowa albashin shi tun kafin yafara ayki zaku iya tafiya "

Bayan tafiyarsu DON yakira waya cikin yanayin 'kaguwa yace

" maganar Oder kayannan a gaskiya banason yawuce nan da 2 days "

Jinjina kai yayi dajin bayanin wancan sannan ya kashe wayar wayar kallon Abdulhakim yayi cikin mamaki yace

" lafiya kake zufa duk iskar dake kad'awa cikin lambun nan ? "

Murmushin dole yayi sannan yace

" wanka nike sonyi "

Yade fad'i hakane amma abinda yasashi zufa furucin DON dayace bayason karya shikuma gashi yayi sannan yace bayason shayeshaye shikuma gashi yana masifar shan sigari wannan abin yasa Abdulhakim yin zufa dan yasan zai iya sani watarana

Jin hakan dayace yasa DON tashi yace

" zomuje gida "

Gun motar shi yanufa aka bud'e mai yashiga shima Abdulhakim yashiga sannan driver yaja suka tafi d'an madedecin gidan shi suka nufa suna shiga akayi parking suka fito cikin yanayin takunshi yake tafiya suna shiga cikin parlour DON yakira tabawa yace tabama Abdulhakim key d'in wancan bedroom yayi mata nuni da hannu sannan ya kalli Abdulhakim yace

" Wannan shine bedroom d'in dazaka zauna kafin mukoma waccan gidan zasu shigoma da kayanka "

Daga haka DON yajuya zuwa bedroom d'in shi yana shiga yafad'a kan bed rumtse idanun shi yayi fuskar Kausar kawai yake Kallo yanajin wata irin tsananin 'kaunarta naratsa jini da jijiyoyin jikin shi cikin sanyin jiki yaciro wayar shi kiran number ta yayi bugu 2

Cikin zazza'kar muryarta mai taushi gakuma fargabar tace

" Assalama alaikum Sweety na ina fatan kana lafiya "

Wani irin sanyi DON yaji cikin ranshi da zuciyar shi seda yad'an nisa sannan yace

" Amin wa'alaiki salam my Hayateey yanabar ki amma nikam babu lafiya "

Cikin razana tace

" subahanannahi maike damunka ? "

Sauke ajiyar zuciya yayi sannan yace

" cuwo 2 ke damuna kuma duk narasa maganin su duk inda nake tunanin zansamu babu duk wani Doctor yakasa bani magani Hayateey yazanyi ? "

Cikin rud'ewa Kausar tace

" innalillahi wa'inna ilaihirraju'un Sweety wannan wane irin ciwone ? kasanar ma Dady ? "

Murmushi DON yayi jin yadda taru'de sannan yace

" kece maganin lalurata duk duniya babu wanda zai iyabani wannan maganin se ke my hayateey kizo gareni a irin wannan lokacin zansanar dake wani sirri amma se ranar da muka kasance a gado d'aya hayateey Assshhhhh "

Cikin sauri Kausar takashe wayar sabida jin abinda yafi karfinta murmushi DON yasaki afili yace

" watoma kunyako ? Hmmm zakizo hannu ne zancire wannan kunyar "

Itako Kausar cikin wani irin yanayi tajawo pillow dake gefanta tarungume tana jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyar ta a fili tace

" Alhamdulilah yagane babu lefina kuma natabbatar yaya Affan yana sona to amma yaya zamanmu zai kasance tsakanina da matar shi dukda na fahimci yanasona to amma baisameni da wannan darajar dakowace 'ya mace kezuwa gidan miji da'itaba amma ita nasan tazo da ita dole setafini daraja a idan shi "

Matu'kar yin sanyi jikinta yayi data tuna wannan lamarin

Kwanaki 5 kenan da zuwan DON Kaduna kullum cikin tunanin Kausar yake gidan shi kuwa angama kammala komi kuma ayane su Seeyama ke komowa saban gidan DON na Abuja zaune DON yake cikin office d'in shi Dady yakira wayar shi yace

" DON yanzu Hajiya Saratu takirani tace takira wayarka amma baka d'agaba haba DON 'yanzu har 7 amma bakaje kayimasu sannu dazuwaba kaje katarbi matarka nasan sekafi samun natsuwa yanzu ga matar ka agusa da kai "

Wani irin ba'kin ciki DON yaji cikin dakewa yace

" to Dady zanje ita Kausar d'infa ? "

Cikin mamaki Barrister yace dan baiyi tunanin zai iya tambayar shi Kausar ba

" Kausar senan da sati nasama sabida kasan hidimar mata "

Cikin rashin jin dad'in zancan yace

" Allah yakai mu "

Murmushi Dady yayi sannan ya kashe wayar cikin 'bacin rai Seeyama tace

" Umma kinga har yanzu DON bai shigo ba wai mai yad'aukeni ne Umma ? to wallahi duk ranar da yashigo hannuna bazan raga mishiba "

Cikin 'bacin rai itama Umma tace

" ay bake kad'ai yanunama halin ko in kulawa ba haddani "

Cigaba da 'korafinsu sukayi

Cikin sauri Abdulhakim ya jefar da sauran tabar dake hannun shi sabida ganin shigowar motocin DON wani Sweet yaciro daga aljihun shi yajefa cikin bakin shi mai kamshi sannan ya iso gurin shi cikin ladabi yakema sannu dazuwa bag d'in hannun shi ya amsa suka shiga ciki

Linta suka hau har zuwa benan 'karshe na 6 har cikin bedroom d'in shi Abdulhakim yashiga ajemai bag d'in shi yayi harya juya zai fita DON yace

" kacanza wannan turaran da kake sawa bashida dad'in kamshi "

Cikin sauri ya amsa da to sannan yafita zama DON yayi yana tunanin yadda zaiyi rayuwa dawata bayan Kausar jin hayaniya a cikin part d'in dayake na Kausar yasashi fita cikin mamaki yake Kallon su d'aya bayan d'aya ganin shi tsaye bakin 'kofar yasa Seeyama nufoshi cikin kiss

" welcome back my baby "

Hannu yanuna mata yace

" dakata wannan part d'in hayateey nane ki koma part d'in 'kasan wannan shine naki nasan Abdulhakim yasanar dake haka amma shine zaki zonan to idan kina neman ma kanki farinciki kibar part d'in nan yanzu "

Daga haka DON yajuya yafita cikin razana da mamaki Seeyama tace

" Umma wacece hayateey nashiga uku "


Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters
[25/06 3:34 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅


Please Login or Register in order to submit comment