Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan datake zaune suka kaita har cikin d'akin ta kasancewar itaba cikin hostel takeba

Tofa kubiyoni

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI ♠♥♣

Comments plsss
[01/05 4:45 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠RUFAFFIYAR ZUCIYA♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵

Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My hajjaju

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

G.W.F

Home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫


ANA TARE 🤝🏻😍🌹

🅿 { 9 to 10 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Afurgice Affan yatashi Sabida sautin kukan yarinyar dayakeji cikin kunnuwan shi tashi yayi yaje yayaye labulayen d'akin haske yagarwaye ko ina dubanshi yamaida kan bed d'in cikin sauri ya kauda idanun shi sabida yadda bedsheet d'in dukya 'baci da jini kallon jallabiyar jikin shi yayi itama akwai jini jikin ta zama yayi yadafe kanshi yanajin zafi aranshi cikin sauri yami'ke yace

" tabbas wannan shiryamin akayi kumasena gano kosu ubanwaye waiyo Allah sun cutar dani sun cutar da yarinyar dabatajiba bataganiba sabida babu yadda za'ayi dasaninta takawo kanta ayimata irin wannan mugun aykin inazan ganta dan nasan ayanzu haka tana bu'katar kulawa ta gaggawa akaro nafarko bayan wasu shekaru naji tausayin wata 'ya mace Sabida nasan tabbas na illata rayuwar ta tabbas dake yadace nayi rayuwa kemad'in badan inason kiba sedan nakareki daga cinzarafin wani d'a namiji Sabida duk namijin daya aureki yaji bakikai budurcin kiba seya wula'kantaki idan ko aka wula'kantaki asanadina bazan yafe makaina ba

Kuma Abbana bazaiyi alfahari daniba Abba kayafemin ba'ason raina had'in tafaruba "

Cikin sauri yashiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shirya a gaggauce yafita yaso yayi ma Securities d'in gurin tambaya amma seyafasa kai tsaye wannan restaurant d'in yanufa neman wanda yakawo mishi abinci jiya yashiga yi amma babu shi zama yayi yayi 'kudirin koda zaikai dare to yananan seya ganshi

Cikin jin matsanan cin zafi Kausar tasaki kuka jin kukan ta yasa 'kawarta Amina dasuke d'aki d'aya tayi saurin tashi gurin ta tanufa ganin halin datake ciki yasa Amina rud'ewa tace

" Kausar maiyasame ki ? ina kikaje tun d'azu ? "

Cikin kuka Kausar tace

" Amina Ameera tacutar dani cuta mafi muni tasa anrabani da budurcina Amina danasan wannan ranar zatazo dana ro'ki mutuwa kafin zuwan ta Amina kalli yadda sukasa yayi min Allah ya'isa tsakanina daku musamman wancan mugun dabazan iyagane waye shiba Amina k....... "

Kukane yaci 'karfin ta takasa 'karasawa itama Amina kuka takeyi sosai kamata tayi takai ta toilet ruwan zafi tahad'a mata sannan ta taimaka mata sosai Kausar kejin zafi amma hakanan tadaure tsayin lokaci tanacijin ruwan zafi sannan Amina takamata suka fito jin jikin ta akwai zazza'bi yasa Amina ta'bare magani tabata tasa cikin wata irin murya Kausar tace

" Amina nagode sosai dataimakon da kikayi min bazan mantaba amma ina ro'kon wata alfarma agunki dan Allah banason kowa yasan abinda yafaru dani ko iyayena bazan bari susani ba idan suka sani zasu kasance a cikin ba'kin ciki nahar abada zanfison ba'kin cikin nayishi ni kad'ai "

Cikin tausayawa Amina tace

" in sha Allah Kausar nayimiki al'kawarin haka babu wanda zai sani dama ina gayamiki kifita harkar Ameera bata 'kaunar farincikin ki ke kina ganin kamar son gaskiya takeyi miki Wllh senasa an d'auki mataki akan ta "

Cikin sauri Kausar tace

" a'a Amina idan muka d'aga wannan maganar to kowaseyasan abinda yafaru dani kibarta ay Allah yananan shi zaiyimin sakayya akan ta "

Jinjina kai Amina tayi tanajin matu'kar tausayin Kausar tabbas anyi mata cuta mafi muni

Misalin 2 Affan yaga wannan saurayin yashigo cikin restaurant d'in cikin hikima yakirashi ganin Affan yasashi tsorata Sabida tabbas yagane shi murmushi Affan yayi yace

" haba abokina maiye natsorata wannan had'in najiya nikeson kasake yimin dan naji dad'in shi sosai "

Murmushi yayi cikin zuciyar shi yace

" kaima ashe d'an hannune "

Zama yayi kusa dashi yace sede

" babu kayan dama wasune suke zuwada abunsu in saka musu "

Murmushi Affan yasake yimai yace

" kas nikuma inadasu amma kazo muje nabaka sabida akwai inda zanje idan nadawo senazo nasha zanyi maka biya mafi tsoka "

Cikin murna ya amince cikin sand'a yabi Affan Sabida kada ma'aykatan gurin suganshi suna shiga cikin motar Affan yajata aguje kai tsaye cikin hotel d'in yanufa yana shiga yayi parking suka fito room d'in shi suka shiga suna shiga Affan yayi saurin kulle 'kofar

Wani irin wawan mari Affan yashiga sauke mishi cikin tashin hankali darazana wannan saurayin yashiga bashi ha'kuri cikin fusata Affan yashiga cewa

" wato kai ne babban d'an iska ko kai ke sakamusu irin wannan mummunar 'kwayar cikin abin sha suna lalata 'ya'yan mutane gashini banjiba ban ganiba itama yarinyar batasan hawaba batasan saukaba kunsa nacutar da ita to kayi gaggawar sanar dani inda wannan samarin suke ko nasakayin nadamar rayuwar ka "

Cikin tsoro yace

" kayi ha'kuri yalla'bai Wllh bansan inda zan samesu ba idan sunzo nan kawai muke had'uwa kuma yanzu nasan senakai wasu watanni bansake ganin suba "

Jin haka yasa Affan cire belt yafara zanar shi amma amsa d'aya yake bashi shine baisan inda suke ba dena dukan shi yayi cikin takaici yace

" kaga wannan bedsheet d'in kaine zaka wankeshi da waccan rigar zan 'kulle ka a ciki har senaje indazani nadawo katabbatar ka wankesu sunbushe kafin nadawo "

Cikin kuka yace

" dan Allah karufamin asiri Wllh zan iya rasa aykina kuma idan na wanke ina zan shanyasu subushe ? "

Wani irin kallo Affan yayi mishi sannan yace

" wannan kuma matsalar kace kai ayki karasa ita yarinyar fa kunsa tarasa abunda bazata ta'ba iya 'kara samunshi ba har abada yatafi kenan sannan nikuma kunjefa rayuwa ta cikin tashin hankalin tunanin halinda yarinyar zata shiga a dalilin fayd'en danayi mata kuma kunsa nakasa cika burin mahaifina kasan Allah seka nemosu kona zanzamaka kamanni "

Affan yana gama fad'ar haka yafita kulle shi yayi yanufi ma'aykatar su

Cikin tashin hankalin Hajiya Aysha ke neman ta'kardun Company ta amma tarasa ganin takasa koda zama yasa Abdulhakim cewa

" Momy mai kike nemane ? "

Sauke ajiyar zuciya tayi sannan tace

" Abdul wasu takardu ne nawa masu mihimmanci "

Kallon ta Abdul yasakeyi yace

" naga Abba yana neman wasu takardu shine nanuna mishi inda kika 'boye "

Zaro ido Hajiya Aysha tayi tace

" amma kaikam Abdul mugun wawane 16 years gareka amma babu wayo atare dakai har yanzu to Wllh daga yau idan kasake ka'kara nunama Abban ka inda wani abu nawayake senama dukan tsiya cikin gidan nan kanaganin baisan cinmuba baisan shanmuba hatta kud'in Skul d'inka nike biya wawa kawai kazama kamar yayan ka mana takan yabaiyana inda dukiyar mahaifin shi take yabar gida amma kai bama a tambaye kaba amma kanuna "

Cikin damuwa Abdul yace

" Momy har yanzu kin'ki kaini inda yayana yake "

Cikin matsanan ciyar damuwa tace

" zan kaika kaji bari yadawo "

Cikin bedroom tashiga tasaki kukan da ayanzu yazamai mata jiki dankam tayi muguwar nadamar abinda tayima Affan gashi yanzu batasan inda yake ba


Cikin munafurci Ameera tashigo cikin d'akin da Kausar take kukan munafurci tashigayi cikin tsawa Amina tace

" Ameera kifita idan kuma baki fitaba Wllh senasa abu nafasamiki kai banza kawai maciya amana kisani ko ayanzu Kausar tafiki komi bazaki ta'ba iya goge mata kimartaba agurin zama'a sannan bazaki hana dubban jama'a su sotaba "

Dariya Ameera tayi hadda shewa tace

" naji tafini kyau dakuma masoya sannan gidansu akwai kud'i to ammafa kisani tarasa abunda duk wata 'ya mace zatayi tutiya dashi idan da za'ace tabada adawo mata da budurcin ta to natabbata zata bada gashi abin haushin nikaina bansan waye yayi wannan fayd'an ba amma dukda haka ni ay bu'katata tabiya "

Fita Ameera tayi tana wani shi'umin murmushi itako Amina badan Kausar ta hanata aywatar da komiba dase kowa yajisu kuka Kausar tasaki tana fad'in kin cuce ni Ameera

Se bayan magrip Affan yakoma hotel izuwa yanzu wannan matashin yagama galabai ta ga jikin shi duk yayi tsami sabida dukan dayasha ga yunwa ko Kallon shi Affan baiyiba yashige toilet tsayin lokaci sannan yafito seda yagama shiryawa sannan yasa aka kawai abinci yabashi


Bayan yagamaci yacigaba da tuhumar shi amma amsa d'ayace hakan ba'karamin haushi yabama Affan ba katin shi Affan yaciro yami'ka mishi yace

" nayarda bakasan inda sukeba zanbarka katafi ga katina nan dazaran kagansu kayi gaggawar sanar dani nayi magana da wajan aykin naka bazasu korekaba zaka iya tafiya "

Cikin sauri yami'ke cikin zuciyar shi yana fad'in


" shikam wannan wane iri ne ga zafin rai kuma ga kirki ayko sena tayaka neman su "


Binshi Affan yayi da Kallo cikin zuciyar shi yace

" zanta bibiyar ka harse nagano su "

Cikin kuka Seeyama tace

" Ummi nibanason wani d'an wan Dady Wllh idan ba DON ba sede namutu babu aure "

Ri'ke baki Ummi tayi tace

" to ayko baki isaba wannan al'kawarin tun kina ciki akayi shi seyanzu kice zaki canza tobari Dadyn naki yadawo seki sanar dashi "

Zum'bura baki Seeyama tayi tace


" kunwani nace se Affan shidako nan baita'ba zuwaba nide bazan auri wani ba se DON "


Afurgice Affan yafarka daga baccin dayakeyi ga mafarki dayayi da Abban shi akan maganar auran shi da Seeyama sekuma sautin kukan yarinyar dayayima fayd'e wata irin zufa tashiga keto mishi maimatawa yayi Sudan Seeyama ni Aure

" haba Abba bazan iya ba bana bu'katar wata mace ni a cikin rayuwa ta se waccan da 'kaddara tasa nayimata fayd'e "

Haka Affan ya'karashe wannan daren batare daya koma bacci ba yau kimanin kwanaki 6 dafaruwar wannan abun amma har yanzu babu labarin wa'innan samarin Kausar taji sau'kin jikinta sosai amma ta'kara zama silent


Rurin da wayar Affan keyi yasa Affan dawowa daga tunanin dayakeyi ganin Dady yasashi saurin d'agawa

daga can 'bangaran Barrister yace

" DON kace kwanaki 4 zakayi kashigo Kaduna amma yau gashi har 6 Allah yasade lafiya kasan muna kewar ka "

Cikin 'karfin hali Affan yace

" lafiya lau Dady wani abune yatsareni amma inanan shigowa "

Murmushin jin dad'i Barrister yayi sannan yace

" to Alhamdulilah kafin kataho kaje kaduba 'kanwar ka Kausar a skul danaso idan kadawo kuje kaida Ashiraf to kai d'inma idan kaje yayi kadaure kashiga gobe "

Badan ranshi yasoba ya'amsa da

" in sha Allah zanje "

Cikin 'bacin rai Affan yakashe wayar sannan yafesar dawata iska yace

" gaskiya antakurani "

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI ♠♥♣

Comments plsss
[02/05 6:56 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠RUFAFFIYAR ZUCIYA♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵

Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My hajjaju

🌟GORGEOUS WRITERS FORUM🌟

G.W.F

Home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫


ANA TARE 🤝🏻😍🌹

🅿 { 11 to 12 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

'Karar shigowar text Affan yaji cikin wayar shi dubawa yayi wani irin tsaki yaja Sabida address d'in Kausar Barrister yaturo mai

Cikin damuwa Affan yace

" wai maiyasa nakasa samun wa'innan sha shashun ne ? amma in sha Allah senagano inda suke "

Misalin 2 Affan yayi parking d'in motar shi dede 'kofar gidan da Kausar take kimanin 20 minutes yana cikin motar bai fitoba Sabida shi bashida number ta kuma bazai iya aykar wani kiran taba

Wayar Ashiraf yakira bugu biyu yad'aga sallamar kawai ya amsa yace

" kirata kace ina 'kofar gidan "

Daga haka yakashe wayar bai jira mai Ashiraf d'in zece ba girgiza kai Ashiraf yayi yace

" DON kenan bazaka canzaba "

Babu jimawa dakiran Ashiraf Kausar tafito itada Amina zuciyar ta cike da mamaki Sabida bata ta'ba tunanin Affan zai iya zuwa inda takeba hankalin take tafiya tanad'an d'ingisawa Sabida har yanzu batagama komawa dede Kallo d'aya Affan yayi musu ya kaudakai amma cikin zuciyar shi cewa yayi

" mai yasame ta take tafiya haka kuma yama akayi Dady yabarta tana zama awajan Skul mace ba namiji ba bazai yiyu ba "

Sallamar su tadawo dashi daga tunanin dayakeyi bud'e motar yayi yafito fuskar nan tashi a tamke adede lokacin Ameera tafito itada 'kawayen ta su biyu

Ganin Affan yasa Ameera saurin tsayawa wani irin kallo tashiga yimai cikin matu'kar rud'ewa tace

" woow kunga wani had'add'an gaye gaskiya nikam naga mijin aure barima kugani "

Nufar gurin tayi cikin ladabi Kausar ke gaidashi amma babu alamar zaima amsa latsa wayar shi kawai yakeyi annun shi d'aya nacikin aljihun wandan shi zuwa can yace

" nemo wa'inda zasu kwasar miki kaya nizan koma daga yanzu bana bu'katar zamanki a wannan gidan kikoma cikin hostel "

Kafin tace wani abu yad'aga wayar shi dake ruru komawa sukayi ciki dan kiran sauran 'kawayensu sutayata kwasar kayan adede lokacin Ameera ta iso wani irin kallo Kausar da Amina sukayi mata itako ko ajikin ta cikin sauri Amina tace

" Kausar wajan yayan kifa taje "

Murmushi Kausar tayi tace

" barta inde yaya DON ne seyabata mamaki "

Cikin wata irin tafiya Ameera ta'isa kusada shi numshe idanun ta tayi sabida kamshin turaran shi mai sanyaya zuciya ahankali tabud'e idanunta tazubasu kanshi sannan tace

" barka dazuwa yayan mu yakamata ay kashiga ciki "

Wani irin kallo Affan yayi mata sannan yajuya bayanshi yana cigaba da latsa wayar shi komawa tayi inda yajuya tafuskan ceshi sosai tace

" haba yaya bagirman kabane irin wannan abun koda......... "

Wani irin mari yasakar mata azafafe yace

" wannan shine girmana kona 'kara nuna miki ne kinzo karatu amma kina bibiyar maza kinga nayimiki kamada sa'anki kinbar gurin nan kosena canza miki kama "

Dariya 'kawayenta suka saki su Kausar dasuka iso dede lokacin da yasauke mata marin Amina tace

" Amma yaya DON kayimin dede "

Afusace Affan yami'ka ma Kausar wasu 'kud'ad'e masu yawa sannan yashiga mota bud'e musu bot d'in yayi yana ganin sungama fitar dakomai yafigi motar shi cikin zafin rai yake fad'in


" gaskiya niba'a kyauta minba maike nan waini wannan kutsakar yarinyar zata kalla tace wai bagirmana bane hmmm "

Cikin 'bacin rai Ameera tazo indasu Kausar suke tace

" wato kunji dad'i yamareni ko ? toke Kausar kisani sena zama matar wannan kyakkyawan yayan naki nanbada jimawaba "

Murmushi Kausar tayi tace

" idan har yaya DON ne sede nace miki sorry Sabida shiba irin sha shashun samarin kibane idan kuma kince zaki'iya to gafili nan "

Gaba sukayi suka barta nan sake maimaita sunan tayi

" DON woow gaskiya komi naka yayi wannan marin dakayimin sekabani ha'kuri watarana DON sena mallakeka kota halin yayane "

Har tsawon 2 Weeks amma Affan bai shiga Kaduna ba yauma afurgice yatashi dafe kanshi yayi cikin wahalalliyar murya yace

" Abba kayi ha'kuri in sha Allah nanda wasu kwanaki zanje Sudan wajan cika wasiyyar daka barmin amma bazan ta'ba son taba Abba wai Allah yazanyi dakukan yarinyar nan da duk kwanciya bacci sena jishi cikin kunnuwana haba maiye haka nimafa ba'a son raina nacutar dakeba "

Ganin bazai iya komawa bacci ba yasa yayi alwala yafarayin nafulfuni yau takama juma'a kuma yaune Affan keshirin tafiya Kaduna cikin farin ciki Barrister yashigo cikin tsakiyar babban parlour shi ganin fuskar shi cike da annashiwa yasa Momy da Ashiraf saurin cewa

" tasamune wannan irin gari'a haka ? "

Zama Barrister yayi sannan yace

" babar samuwama kuwa wani babban albishir ne nazo muku dashi kuma mai matu'kar bazata "

Cikin zubud'i Momy tace

" dan Allah kasanar damu munmatsu muji "

Kallon su yayi duka sannan yace

" a yau a yau ne aka d'aura auran Affan da Kausar wanda yasami halartar dubban jama'ar dasuka halacci sallar juma'a cikin babban masallacin ....... "

Tashi momy tayi cikin tashin hankalin tace

" haba Ibrahim wannan wane irin d'anyen hukunci ne to inamai tabbatar maka dole a warware wannan auran danni banshirya kashe 'yata ba "

Murmushi Barrister yayi yace

" idan kikaga wannan auran yamutu sede idan Kausar mutuwa tayi koshi Affan d'in yace bayaso "

Yana gama fad'ar haka yatashi yanufi cikin bedroom d'in shi rai 'bace shima Ashiraf baiji dad'in wannan hukuncin da mahaifin shi yazartar ba dan yafikowa sanin waye DON tabbas Kausar zatasha wahala lallashin Momy Ashiraf yashigayi

Misalin 6mp Affan ya'iso cikin gidan jin sallamar shi yasa barrister saurin mi'kewa cikin jindad'i damurna yataro shi suka shiga cikin babban parlour kiran Momy da Ashiraf Barrister yashiga yi atare suka fito

Dukda Momy na cikin jin haushin abinda barrister yayi hakan baihanata sakar ma Affan fuska da nuna tsantsar farin cikin dawowar shi misalin 9pm sun kammala cin abinci barrister yayi gyaran murya yace

" DON nagode ma Allah daya kawoni wannan lokacin ayau insha Allah zan mi'ka maka kaf dukiyar ka dake hannuna Sabida nasan yanzu zaka iyakulada abunka "

Cikin rashin jin dad'i Affan yace

" a'a Dady kabarta a hannun ka zaifi "

girgiza kai barrister yayi yace

" a 'a DON bazan iya cigaba dari'ke wannan dukiyar ba kai marayane kuma ri'ke dukiyar maraya babban abune kasan tsawon shekarun dana d'auka bana'iya baccin kirki Sabida dukiyar ka Affan ayanzu zaka iya gabatar dakomi a rayuwa 30 years garekafa ayanzu dan Allah ka amsa dukiyar ka sannan iname ro'kon afuwarka na yanke maka wani hukunci batare dasanin kaba amma dan Allah idan baka ra'ayin haka kasanar dani bazanyi maka dole ba ayau na d'aura maka aure da 'kanwarka Kausar idan takammala Skul d'inta za'ayi hidimar bikin da ba'ayiba k.......... "

'Kwarewar da Affan yayi daruwan dayasha yasa Barrister dakatawa dayin maganar shi wani irin mugun tari Affan yashiga yi tun yana kan cushion harya sauka 'kasan Capet cikin sauri Ashiraf yaruga d'akin su cikin bag d'in Affan yashiga duba maganin shi cikin sa'a kuwa ya ganshi yana kawowa akayi saurin bashi yasha sannan suka kamashi aka kaishi cikin bedroom harkan bed suka zaunar dashi yajingina dan babu hakin ya kwanta seta lafa

Cikin tashin hankalin momy tace

" kaga abinda nike gudu kasan yadda Affan yatsani mace amma katashi kayimai auran bazata kumama da Kausar yarinyar dako muryar ta Affan bayasonji haba Ibrahim Affan bayason wannan auran kabashi umarnin sakin Kausar ay........ "

Muryar Affan yasa Momy dakatar dazancanta cikin wahalalliyar murya yace

" har abada Momy bazan iya sakin Kausar ba niba butulu bane kunyimin halacci bazan manta dahakan ba Dady har namutu kai mahaifine agareni kacancanci yanke duk wani hukunci akaina amma ina tunanin yadda zanyi rayuwa da mata 2 ne Sabida Abba yabarmin wasiyyar naje Sudan na amso auran 'yar 'kanin shi kuma ajibi nikeson tafiya "

Cikin mugun 'bacin rai Momy tace

" tab ayko 'yata bazata ta'ba zama da kishiyaba dolema kasake ta "

Tsawa Barrister yasakar mata sannan yace duk sufita duban shi yamaida kan Affan yace

" karkadamu DON tare zamutafi kuma aykai cikakken namiji ne koda mace 4 zaka'iya ri'kewa Allah yatayaka ru'ko "

Cikin zuciyar Affan cewa yayi

" kowacce da'kafarta zata gudu banida ra'ayin zamada ko wacce mace ni DON babu mace a cikin tsarina se wacce nazama silar rabatada abumai daraja Dady bazan iya yimaka musuba amma bazan iya rayuwar aure dasuba daga za'binka harna Abba ni Affan bazan ta'ba Kallon su amatsayin matana ba "

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI ♠♥♣

COMMENTS PLSSS
[09/06 1:20 pm] 😊 NPEEDY A AJI🌹💖: ♠ RUFAFFIYAR ZUCIYA ♥♠♠♠♠♠♠
🔷🔴🔵🔶
♠♣♥
🔴🔵

Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🤫

Ina kuke masoya to ganifa 😊 ana mugun tare 🤝🏻🌹

Ina godiya a gareku masoya baki d'aya masu kirana damasu turomin text jinjina naso na zayyanoku baki d'aya amma yawanku yasa hakan bazai yiyuwa sedenace Allah yabar zumunci 🤝🏻kuyi ha'kuri yanayin jikina yasa kukajini shiru to Alhamdulilah nasamu sau'ki sed'an abunda ba'a rasaba zancigaba kamar yadda kuka roki alfarmar haka amma danaso senan gaba kad'an nagode da nuna kulawarku a gareni 👍🏻 to mucigaba da kaftawa masoya 😍

ANA TARE 🤝🏻😍🌹

🅿 { 13 to 14 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Kallo shi Barrister yayi nadan wasu da'ki'ku sannan yashafa sumar kanshi yace

" Allah yayimaka albarka Affan please kacire duk wata damuwa kodan lalurar ka kayi bacci sosai zakasamu sau'kin wasu abubuwan mukwana lafiya my son "

Bin bayan barrister Affan yayi da kallo batare dayace komiba bayan fitar barrister babu jimawa Ashiraf yashigo fira yashiga jan Affan dashi amma ko sauraran shi bayayi ganin haka yasa Ashiraf kwanciya zuciyar shi cike da tausayin Affan musamman idan yatuna abinda mahaifiyar shi tayimai gashi tasa rayuwar shi tazama wata iri da wannan tunanin bacci yad'auke shi

Kallon inda yake Affan yayi ahankali yace

" dama nazama kamarka Ashiraf nakasance babu damuwa atare dani se yaushene zansamu farinciki a cikin rayuwa ta ? Momy kin kwace farincikina ni Affan bazan ta'ba komawa garekiba har namutu bakuma zan sassautama duk wata 'ya mace ba "

Ahaka Affan yakwana batare daya ko runtsaba idanun shi duk sun canza launi sabida 'bacinran dayake ciki koda sukaje masallaci shi kama acan su barrister sukabar shi yanata lazimi

Cikin damuwa barrister yace

" Ashiraf Affan yasamu bacci jiya kuwa ? "

Girgiza kai Ashiraf yayi sannan yace

" a'a Dady duk farkawar dazanyi a zaune nike ganinshi "

Jinjina kai barrister yayi sannan yace

" Allah yasa yarinyar dazamuje amsomai auranta ta iya jawo hankalin shi kozai samu sau'ki cikin ranshi "

Cikin nuna damuwa Ashiraf yace

" amma Dady ni inaga kamar zaman Affan da mace wata gagarumar matsalace Dady kanagani sabida 'kiyayyar da

Please Login or Register in order to submit comment