Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dana nemi yasakeni zan bashi nera million 50 zanzauna dashi bisa ladabi da tsananin biyayya da sanina dakuma yardata muka janye batun rabuwa bayan na warke "

Wani irin d'agowa Ameera tayi amatu'kar razane zatayi magana idanun ta suka sauka akan DON kasacewa komi tayi dan gani take kamar mafarki takeyi d'ayar takardar Abba yafara karantawa

" ni Salimat Aminu nayarda kuma nasan ina d'auke da cikin mijina Abdulhakim na tsawon wata 2 idan nabari wani abu yasamu cikin zan biyashi nera million 60 na amince da wannan yarjejeniyar "

Murmushi Kausar tasaki kowa yaji dad'in haka itako Ameera daskarewa tayi awajan kamar babu jini jikinta murmushi Abdulhakim yayi yace


" Abba muje can part d'in nasan Ameera tanaso ke'bewa daku sabida akwai kewarku tareda ita "

Hannun ta Ummi takama se'a lokacin Ameera tafashe dakuka bubbuga bayanta Ummi tayi dan ita tayi tunanin kukan kewar sune dakuma jin abinda yafaru da ita abaya yaban sun fita DON yami'ke zai shiga cikin bedroom d'in shi dan yayi shirin fita ayki

Jin sallamar Umma yasa DON tsayawa cikin fad'a tace

" Kausar kijama waccan matar kunne tadena zuwa cikin gidan nan dan nalura munafukace "

Cikin mamaki Kausar tace

" wacece Umma ? waccan banzar Hajiya Aysha mana "

Dede lokacin Hajiya Aysha tayi sallama tashigo Cikin parlour cikin zafin rai Abdulhakim yace

" Umma mahaifiyar tawa kike kirada munafuka kuma banza hannu Abdulhakim yad'aga zai dallamata mari Hajiya Aysha tayi saurin ri'ke hannun shi "

Murmushi Umma tayi tace

" barshi yajama kanshi bala'i dama d'ankine haba shiyasa ashe gadon munafurci yayi k.... "

Murza idanun shi DON yashigayi cikin wata irin murya yace

" Momy "
Wani irin kuka DON yasaki yajuya zaibar gurin Cikin sauri Momy tacafko hannun shi tace

" haba Affan Ashe zansake ganinka ? "

Fizge hannun shi yayi yasake yunkurin barin gurin Kausar tayi saurin shangaban shi tace

" dan Allah Sweety karka'ki saurarar Momy sannan ayau ne zanyima albashir sabida nasan zai sanyaya zuciyar ka ina d'auke da ciki har tsayin 4 months kuma yana cikin 'koshin lafiya "

cire hijab d'in jikinta tayi tace

" Sweety kalli babyn ka harya baiyana dama ayau nikeda niyyar sanar da kai shiyasa nakira Momy dan taci albarkacin jikanta dakuma daraja da girman haihuwarka datayi shiyasa nasa kayanda zasu baiyana maka babyn ka kaganshi kwance cikin cikin mahaifiyar shi kuma Hayateey ka wadda kake matu'kar son ganin ta haifamaka 'ya'ya dan Allah Sweety "

Cikin wani irin yanayi DON yazibe gaban Kausar hannun shi yad'aura saman cikin ta duka biyu yana shafawa wasu manyan hawaye masu sanyi sukafara kwararowa daga cikin manyan idanun DON

Seeyama datun bayan shigowar Umma itama tashigo akan idanunta komi yake faruwa hannu tad'aura akai tasaki wani irin ihu tafad'i asumai

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A A JI β™ β™₯♣


Comments and shine please

Love u all sisters 😘🌹
[15/07 1:23 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 57 to 58 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin gigita Umma tayi kan Seeyama shiko DON baimasan Seeyama tafad'i ba yawo Kausar yayi jikin shi yayimata wata irin runguma wani irin farin ciki Momy taji yana ratsa zuciyar ta itama Momyn zuyawa tayi kan Seeyama sosai Umma tarud'e kamata suka akan daurata kan cushion anayimata fifita

Cikin kunnan DON Kausar tace

" Hayateey Seeyama tafad'i tasuma "

Ko motsawa DON baiyiba seda Kausar tasakeyin magana

" Sweety kana ganin su Momy fa kuma kaga fa Seeyama bata motsi "
'Dago kanshi yayi yace
" Abdulhakim kira doctor "

Jin haka yasa Umma saurin kallon DON tace
" a'a bari nakira doctor "

Had'a fuska DON yayi zaiyi magana Abdulhakim yami'ka mishi wayar shi wani videos ya kunna mai duk abinda su Umma ke kullawane akan cikin karyar jikin Seeyama se yadda suka shiryama Kausar wannan sarrin amma babu bayanin shirin da Ammi zatazo dashi

Wani irin murmushi DON yayi wanda shikad'ai yasan manufar shi kallon Kausar yayi yasakar mata wani kyakkyawan murmushin d'aukar ta yayi cak yanufi cikin bedroom da ita ganin haka yasa Umma sauke ajiyar zuciya

Cikin ba'kinciki da wata irin fad'uwar gaba Umma tad'auki Seeyama suka nufi part d'in ta cikin damuwa Momy tabi bayan su maganar Abdulhakim yasata tsaya

" Momy please kirabu dasu dan wallahi idan Umma tasake gayamiki maganar banza sena bata mamaki "

Cikin sanyin jiki Momy tadawo ciki parlour zama tayi kam Cushion shima zama yayi jiki a sanyaye Ameera tanufo gurin Momy zama tayi 'kasa ta gaidata Cikin farin ciki da sakin fuska Momy ta 'amsa gaisuwar Ameera

Murmushi Abdulhakim yayi yace

" Momy yau gaki ga brother bayan wasu shekaru masu yawa ? "

Shafa kanshi Momy tayi tace
" Abdulhakim ina matu'kar farin ciki awannan ranar ashe dama DON shine Affan d'ina amma shine kuka 'boyemin ? kasan irin ba'kincikin danike ciki asanad'in rashin Son ? tabbas nayi nadamar irin abinda nayi abaya Allah yasa Son zai iya yafemin "

Murmushi Abdulhakim yasakeyi dan shima yau yana cikin farin ciki matsananci zama yayi kusada'ita yakwanta d'aura kanshi yayi kan cinyar Momy yana sauke ajiyar zuciya

Yace " in sha Allah Momy nasan Aunty Kausar zatasa brother yagane ked'in Uwace ba'a fushi da iyaye "

itako Ameera tamarasa maike mata dad'i takasayin tunanin komi

Sosai DON yake 'kara rungume Kausar yanaji kamar yamaidata cikin shi yakasa fad'in komi sai sauke ajiyar zuciya yakeyi cikin sanyin murya Kausar tace

" Sweety please dan Allah kaje gurin Momy kayafe mata karka matan itad'in uwace bakada wadda tafita kuma bazaka iya canzataba Sweety babu Abba se Momy karka bari zuciya da hud'ubar shed'an suka kabar Aljannar ka koda abinda Momy tayima yafi haka muni bakada hujjar yin fushi da ita balle kaguje mata idan har kanaso muyi farinciki nida babyn mu dakuma Abdulhakim wanda yake d'an uwankane najini uwa d'aya uba d'aya to kayafema Momy sannan karo'ki gafararta dan kaima kayimata ba daidaiba daka barta haran tsayin wa'innan shekarun kuma...... "

Katseta DON yayi dafad'in

" Hayateey mai kikeson cewa ? taya Abdulhakim yazama uwarmu d'aya ? bayan lokacin da Abba yarasu babu alamar samun wani d'ah cikin gidanmu "

Sake kwantar da kanta Kausar tayi cikin 'kirjin shi sannan tashiga sanar dashi yadda abin yake da irin cutar da Alhaji Sambo yayima Momy kwantar da ita DON yayi yatashi afili yace

" lalle sena gwadama Alhaji Sambo shi 'karamin macucine Hayateey kiyafemin nagane komi akan wannan maganin dana dad'e ina ganin lefinki hmmm Umma zaku gane DON bashida sabo idan akaci amanar shi "

Kama hannun Kausar yayi suka fito parlour tsayawa yayi yana kallon yadda Abdulhakim yayi kwance kan cinyar Momy kallon fuskar ta yayi wani irin yaji cikin zuciyar shi danya hangi muguwar damuwa sosai akan fuskar Momy cikin sauri yanufi gurin Momy hannun Abdulhakim yajawo harseda Abdulhakim yarazana mi'kar dashi yayi tsaye zama yayi kusada Momy yakwanta kan cinyar Momy cikin rawar murya yace

" Abdulhakim yau nikeda wannan cunyar ba kaiba danna fika yin missing d'inta " yakarashe fad'in haka dasakin murmushi d'aga kanshin yayi yakalli fuskar Momy yasakar mata murmushi cikin matu'kar farinciki da tsananin soyayya Momy tarungume shi sosai hawaye taji sunfara sakkowa daga idanunta

Cikin kuka Momy tashiga ro'kon DON akan yayafe mata tashi yayi yasa hannun shi yarufe bakin ta yana girgiza mata kai shima kukan yafarayi sannan yace

" a'a Momy banason ganin wannan hawayen kibar kuka ga Affan d'inki yadawo gareki kiyafemin Momy nikam nayafe miki Momy a yau natashi daga mai RUFAFFIYAR ZUCIYA Momy "

Sake gungumai shi Momy tayi tace

" Son nice mai RUFAFFIYAR ZUCIYA bakaiba Dana za'bi dukiya akan gudan jinina naza'bi abin duniya akan d'an dana haifa namanta cewa dukiya zata iya barina amma d'ana bazai iya barinaba yau gashi dukiyar tagudu amma d'ana yadawo gareni godiya ga Allah danasake ganinka kafin nabar duniya inaso kahukunta Alhaji Sambo sannan kasanar dashi yadda yake zatan cewa Abdulhakim d'anshi ne to Bahakaba bane "

Shigowar Ammi wadda ta'iso babu jimawa yasa Momy yin shiru fuska sake Ammi tashigo cikin sakin fuska Kausar da Ameera suka tarbeta murmushi Momy tayi tace

" wai Hajiya bulkisu nike gani haka lalle mutanan Sudan maraba "

Murmushi tayi sannan tazauna tashi DON yayi suka gaisa wani irin 'bacin rai yaji daganin Ammi tashi yayi yayima Kausar nuni da ido alamar tabiyoshi sannan yashiga cikin bedroom

Shima Abdulhakim mi'kewa yayi yanufi hanyar fita d'an tsayawa yayi yace

" Ameera zoki had'ama Momy launch kibar kibar Aunty Kausar tahuta "

Daga haka yafita tashi Ameera tayi cikin sanyin jiki cikin zuciyar ta tace

" lalle wai kamar wannan yaron shine mijina nashiga uku ni Salimat "

Bayan duksun fita Ammi tadubi Momy sosai tace

" gaskiya Hajiya Aysha bakida kirki ko irin ziyaranan babu shiyasa yara basu ganekiba gaskiya banji dad'in abinda Saratu tayimikiba rashin sanin ked'in wacece yasa haka tasanar dani komi dan Allah kiyi ha'kuri "

Murmushi Hajiya Aysha tayi tace

" ayya babu komi amma yakamata tasan dukwani d'an Adam ba'abun wula'kantawabale sabida bakasan halin rayuwa ba babu komi yawuce "

Ajiyar zuciya Ammi tasauke tace " hakane in sha Allah zata kiyaye " toya jikin Seeyama ? "

Dasauri Ammi tace " Alhamdulilah yayi sau'ki sosai kafin tarufe baki Ayman yashigo a rikice yace

" Ammi Seeyama tasake suma jini yanata ziba mata sosai amma Umma tad'auketa sun tafi Asibiti da Jabir shine tace nasanar dake "

Cikin sauri Ammi tami'ke itama Momy arud'e tami'ke d'aukar wayar ta tayi takira number Kausar cikin wani yanayi Kausar tasa hannu ta d'akko wayar dan DON dukya kashemata jiki ganin number Momy yasa saurin tayi zaune seseta natsuwarta tayi sannan tad'aga

" kicema Son Seeyama jikin ya'ki antafi Asibiti da ita yafito muje "

Koda DON yaji haka sake rungumo Kausar yayi cikin mamakin Kausar tace

" haba Sweety katashi muje kodan Momy "

Kallon ta DON yayi yace

" zanje dan Momy kuma dan nanuna musu ni ba'a cin amanata nabari "

Tashi yayi yashiga toilet ita kuma tafito ganin su Momy yasata jin kunya sosai cikin kunyar tace "gashinan fitowa "

Cikin bedroom d'in ta tashiga a gaggauce tashirya tafito su Abdulhakim ta tadda a parlour dasu Momy shiko DON baifitoba har yanzu kiran wayar shi Kausar tayi sannan yafito

Fuskar shi a tamke yace

" wane Hospital ne ? " Ayman yabashi amsa kallon Momy yayi yace " Momy kuyi zaman ku zamuje nida Abdulhakim da Kausar "

Girgiza kai Momy tayi tace yakamata muje jinjina kai yayi sannan yanufi hanyar fita suma fita sukayi ahankali Ammi tayi 'kwafa cikin zuciyar ta tace

" hmmm wallahi duk sena baku mamaki " mota 3 sukafita da ita suna isa hospital suka shiga jabir yana ganin su yamusu jagora zuwa room d'in da Seeyama take kwance take hannun ta sanye da drip tana bacci Umma na gefanta tanafaman sharar hawayen 'karya cikin nuna damuwa Ammi tace

" haba Saratu maiye na kukan kuma ? Allah zaibata lafiya in sha Allah " sake fashewa da kuka Umma tayi tace
" dole nayi kuka Aunty Cikin jikin Seeyama yazi'be ina tunanin yadda Seeyama zataji idan tafarka dan duk duniya babu abinda takeso kamar wannan cikin gashi yanzu babu yaz........ "

Cikin tamke fuska DON yace
" kamarya Umma kina nufin cikin jikin Seeyama babu ? "

Sake fashewa dakuka Umma tayi tace " babu Affan dan har Doctor tayi mata wankin ciki wani irin murmushi DON yayi cikin zuciyar shi yace yau zakusha mamaki zaro ido yayi yace

" anyimata wankin ciki ? da izinin wa tab Umma cewa zakiyi anzibar da cikin jikin Seeyama kai jabir kaini office d'in Doctor "
Ganin yana ne'kewa yasa DON dakamai wata irin tsawa datasa Jabir zabura yafita yana kaishi ko sallama baiyiba yashiga cikin zabura Doctor tami'ke tace

" lafiya DON ? ko sallama babu "

Murmushi yayi yadafa hannun duka biyu kan teburin gabanta yace
" waye yasa hannu akan paper yima Seeyama wankin ciki ? " razana sosai Doctor tayi tace
" ay emergency aka jawota shiyasa akayi kuma naga nice nike dubata shiyasa "

Jinjina kai DON yayi yasake cewa " kenan babu wanda yasa hannu naga duk abinda yashafi irin haka se sha'ki'kin mutun yasa hannu ko amma ku bakwayin haka kenan ? toma taya kika tabbatar cikin jikinta ya lalace gaskiya kinde zubarmin da cikin mata kinsan yadda nikeson wannan babyn kuwa ? dan haka bazan ta'ba yardaba done nayishari'a dake dan haka u are under arrest
_________________________

Zaro ido Doctor tayi cikin matu'kar furgita shiko jabir jabaya yafarayi Wayar shi DON yaciro yakira Security d'in shi dasuke waje yabasu umarnin shigowa

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters
[17/07 3:52 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 59 to 60 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin in ina Doctor tace haba DON wace irin magana ce wannan Hajiya Saratu tabani damar yima Seeyama duk abinda yakamata ka tambayeta "

Wani irin murmushi DON yayi yaja kujera yazauna yadubeta sosai yace

" Hajiya Saratu itake auran Seeyama ? niban bata damar takawomin mata hospital ba dan haka babu ruwana da duk abinda tasaki nike zan tuhuma amma afuwa d'aya ku kawomin babyn dan nasan dole se angan shi kimanin wata 4 kenan kok....... "

Kafin yasake cewa komi Umma tashigo cikin office ganin Umma yasa doctor saurin cewa

" yauwa Hajiya Saratu kiyima DON bayanin komi akan zubar cikin Seeyama dan lamarin yana neman sakani cikin masifar dazatasa narasa aykina "

Cikin lallashi Umma tacema DON

" Affan nasan akwai damuwa atare dakai sabida kasaka rai akan cikin Seeyama to amma ha'kuri yazama dole kuma ayga Kausar nan da ciki ko ? dan Allah ka kwantar da hankalin ka kaga idan Seeyama tafarka taganka cikin wannan yanayi zatakuma shiga cikin matsananciyar damuwa "

Mi'kewa DON yayi yasakar ma Umma murmushi wanda yasa zuciyar ta razana hanyar fita yayi sedayakai bakin 'kofar yatsaya yace

" idan aka nunamin babyna nada 10 minutes zanmanta dakomi amma idanba hakaba senasa duk wanda yakeda hannu akan zubarda cikin Seeyama nadamar rayuwar shi "

Kasa maga su Umma sukayi sebin bayan shi dasukayi da kallo wata irin fad'uwar gaba Umma taji dalilin wata irin tsawa da doctor tayima Umma tace

" Hajiya Saratu ashe kinsan DON bashida mutunci akan lamarin shi shine kika bari nasaka kaina cikin masifa to wallahi idan kikamin sanadin aykina sena jazamiki gagarumar matsala cikin rayuwar ki "

Afusace Umma tanuna Doctor dayatsa tace

" sauraramin karki sakeyimin tsawa lokacin danike baki kud'ad'e ay bakice nasaki cikin masifaba se yanzu dan haka ki saurara munefi mafita idan kuma bahaba dukammu mushiga cikin masifar "

Cin haka yasa doctor komawa tazauna cire tabaran idanta tayi tashare zufar saman fuskarta shiru natsayin lokaci sannan Hajiya Saratu tace

" mafita d'ayace ay mahaifiyar shi tana nan cikin Asibiti zomuje "

Taresuka nufi room d'in da Seeyama take ganin DON da Abdulhakim basaciki yasa Umma sauke ajiyar zuciya zama tayi kusada Momy akunyace dan batamanta da irin cin mutuncin datayi mataba tace

" Hajiya Aysha dan Allah kifahimtar da DON danyanason taramana jama'a cikin hospital d'in nan akan zubewar cikin Seeyama yace baiyardaba se'an nunamai babyn tukun idan Bahakaba zaikulle Doctor "

Girgiza kai Momy tayi sannan tace

" idan banda abinku ayseku nuna mishi kuhuta tunda shi cikin ba d'an wata 2 bane balle ace iya jinine kawai ayko wata 3 ne za'aga gudan shi balle wata 4 kununamishi mana doctor "

Dakewa Doctor tayi tace

" a gaskiya Hajiya lokacin da aka kawo Seeyama babyn cikinta yarigada yafad'i tun kafin Suzi Asibiti dan haka sede kuduba acan gidan badai nanba "

Jinjina kai Momy tayi sannan tace babu komi bari yashigo kuka Ammi tasaki tanafad'in

" wannan wane irin abune haka kubar yarinyar nan da damuwar datake ciki mana Hajiya Aysha dan Allah kisa Affan yabar wannan maganar sekace wadda akace ta haihu babu rai ? daza'a tada hankali akan 'barin cikin wata 4 haba sekace babu yarda "

" rashin yarda yasa nike son ganin babyna koda kuwa idan naganshi zuciya ta zata buga dole sena ganshi idan kuma Bahakaba nad'auki mataki akan abin cewar DON daya shigo yanzu "

" Kai Son maiye haka ? " Momy tafad'a tareda kamo hannun shi sumar kanshi tashafa tace

" haba Son nasan karfin zuciyar ka akan komi karayu natsayin shekaru cikin karfin zuciya batareda jin dad'in rayuwa ba kacinye waccan jarabawar se akan wannan zaka gaza haba Son karka manta mahaifin ka yabarka kuma kaha'kura se wannan dako kamshin duniya baijiba ina baka ha'kuri a matsayina na mahaifiyar ka daka ha'kura Allah yakar'bi cikin jikin Seeyama amma yabar maka na Kausar wannan ba wata ni'imar bace Son ? "

Murmushi DON yayi yace

" Momy babbar ni'imace samun Kausar kawai matsayin mata amma ita Seeyama su Umma sin'ki bari naga ribar za'bin mahaifina Momy dama babu wani ciki ajikin Seeyama plan suka shirya sunmanta cewa shi Allah ba'ayimai haka

Sunyi haka danna wula'kanta Kausar sun shirya komi son ransu sunsa nayima Kausar abinda ba daidai ba segashi itadata dogara ga Allah Allah ya'isarmata ita dabasuson ta haihu har suka shirya zamana agurin Seeyama harna tsawon 3 months amma ashe sun makara Allah yanunamusu iyakar su "

Cikin borin kunya Umma tashiga cewa " wannan wane irin abune sabida kana neman zautuwa akan zubewar ciki shine kake fad'in irin wannan maganganun haka ? "

Murmushi DON yayi yace " to tunda zautuwa nayi bari nagani ko cikin zautuwar naga duk wannan "

Kuka Seeyama tasaki sosai tarungume Ammin ta sosai tana fad'in Ammi dan Allah kitaimakeni cikin sauri Ammi tarufe bakinta dan tanajin tsoran kartayi wani furucin daba daidaiba danta lura a rikice take

Wayar shi DON yaciro wannan video yakunna musu tunkafin yakai karshe Doctor tazi'bai gyuwa biyu tana ro'kon DON yafiya itako Umma zaro ido kawai takeyi se wata irin zufa datayimata wanka Seeyama suma tasakeyi sabida matu'kar razana "

Jinjina kai Momy tayi cikin mamaki itako Ammi fad'a tashiga yima su Hajiya Saratu wanda yakenuna cewa batasan komiba cikin wata irin murya da matu'kar al'ajabi Momy tace

" Son barsu Allah yamisu hukunci da kanshi wannanma ya'ishesu ishara idan sunada hankali sannan karka saki Seeyama kodan mahaifin ka da darajar jini d'aya dakuke "

Murmushi DON yayi yace

" shikenan Momy zomukoma gida nasan kina bu'katar hutu hannun Kausar yakama ya kalli Abdulhakim yace " Abdul d'inbin kud'in nan namarayu da'akace kad'auka hmmm suna gurin Umma ta adanamusu "

Daga haka yafita hannun shi ri'ke dana Kausar itama Momy fita tayi haka Abdulhakim cikin sauri Ameera tari'ko hannun Abdulhakim kallon ta yayi yatamke fuska sakin hannun nashi tayi cikin sanyin jiki bayan fitar su Hajiya Saratu tabuga 'kirji tace

" nashiga uku duk ya'akayi yasan komi ? "
Tsaki Ammi tayi tace " ay bansan ke shasha sha bace se yau kinkasa aywatar da komi amma tunda nazo yanzu nizanyi komi sena raba Kausar da duniyar baki d'aya wallahi banzauna da kishiya ba dan haka itama 'yata bazata zauna da itaba sannan se Seeyama ta mallaki DON da duk wata dukiyar shi senasa yarabu dakowa nashi musamman wannan shegen 'kanin nashi Abdulhakim "

Jin haka yasa Umma yin matu'kar farin ciki itako doctor data fita tunbayan fitarsu DON godiya taketayi gurin Allah dayima Allah al'kawarin bazata sake aykata irin wannan abunba

Bayan su DON sun isa gida suna zaune a parlour tsakiya Momy tadubi DON tace

" Son akwai wani abu mihimmi acikin wancan gidan da Alhaji Sambo yasiyar wani faifan CD ne wanda yake d'auke da fuskokin wa'inda suka kashe mahaifin ka nabama Alhaji Sambo d'aya akan yakaima jami'an tsaro amma yacemin yafad'i dahar zanbashi d'ayan sekuma nafasa yana cikin wannan 'boyayyan d'akin na mahaifin ka nasan dukda wasu nacikin gidan yanzu bazasu gane inda d'akin yakeba "

Zumbur DON yami'ke hannushi nadama yad'un'kule yakaima nahagu naushi yace " abinda nadad'e ina nema yau nasamu wallahi duk Wanda yakeda hannu akan kashe mahaifina to wallahi bazan garamishi ba "

Saurin fita DON yayi ganin wucewar wani cikin sauri yasa DON saurin iran Abdulhakim " maza kadubamin CCTV CAMERA gidan nan lalle akwai wanda yaji abinda muka tattauna yanzu yisauri muje kafin maganar tafita "

'Daya daga cikin yaran Alhaji Sambo ne yaji wannan maganar tun kafin yasauka yakira wayar Alhaji Sambo yasanar dashi komi cikin sauri suka duba sunkoyi sa'ar ganin shi Security d'in cikin gidan DON yakira yabasu umarnin karsu bari kowa yafita

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters 😘
[18/07 2:27 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA


Please Login or Register in order to submit comment