Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register



Misalin 8pm Kausar tafito daga cikin bedroom fuskarta tayi matu'kar kumbura gawata irin yunwa datakeji kitchen tanufa amma taduba ko ina babukomi na sarrafawa aciki dole tadawo parlour tazauna cikinta sefaman 'kugi yakeyi ga ciwon kai

Babu jimawa dazaman Kausar DON yashigo hannunshi ri'ke dawasu ledoji bedroom d'in shi yanufa ko kallon inda Kausar take baiyiba cikin damuwa tabishi dakallo ganin yunwa naneman kassarata yasa tami'ke cikin sanyin jiki tanufi bedroom d'in shi

Tsaye tayi bakin 'kofar tafarayin sallama amma shiru babu amsa har sau 4 tabud'e baki zatasake yadakamata wata irin tsawa

" wannan wane irin wawancine kinyi d'aya na amsa amma se maimaitawa kikeyi idan babu abinda yakawoki kiyi gaggawar fita "

Cikin sanyin jiki tashiga cikin zuciyarta kuwa cewa takeyi

" sede idan aljanun dake cikin bedroom d'inne sukaji amsawar ka "

amma azahiri cewatayi

Yaya barkada dare dan Allah yaya kataimakamin damagani kaina ciwo yakeyi kuma inajin yunwa naduba kitchen babu komi nasarrafawa "

Wani irin kallo yayi mata kamar bazaiyi maganaba zuwacan yace

" tashi kibani guri kije wajan 'yan'iskan samarinki subaki "

Dagahaka baisake cewakomiba yamaida hankalin shi kan system d'in shi jiki a sanyaye Kausar tabar cikin bedroom d'in d'ayan bedroom d'in tanufa cikin mamaki ta'idasa shiga sabida hango wata leda datayi saman freezer cikin bedroom d'in cikin sauri takai hannu wani had'ad'an abincine da yoghurt

girgiza kai tayi tace

" gaskiya yaya Affan mugun miskilancinka yayi yawa yaushema yashigo ciki oho Allah kabani juriyar zamadakai yaya Affan "

Dukda yunwar datakeji amma bata'iyacin abincin sosaiba tashi tayi tayowanka tayi shirin bacci kwanciya tayi amma takasa rintsawa tunanin abubuwa dayawa sunhanata bacci wasu irin hawaye suka shiga gangaro mata cikin shasshekar kuka tace

" Dady wane lefi na'aykata maka kahad'ani da wanda zai'iyayin ajalina kamar yadda yakeda ciwon zuciya nasan nima senakamu dashi sabida ba'kin cikin dazaita dasamin Allah kasakamin akan wannan sar'ka'kiyar da'aka kullamin "

Rurin da wayar shikeyi yasashi maida dubanshi kan phone d'in ganin maikiran wayar yasa yakai hannu yad'auka cikin girmamawa yayi sallama dagacan 'bangaran akace

" my son an kammala komi gamaida auranka yanzu Seeyama tazama matarka zamutaho nanda kwanaki 2 zamukaima amaryar ka saban gidanka dake cikin Kaduna kafin akammala wannan ginin naka na Abuja kayi 'ko'kari kazo tarbar amaryarka Allah yabaka ikonyin adalci a tsakaninsu "

Wani irin kululin ba'kin ciki DON yaji yatasomai yatekare mishi wuya da'kyar yace

" kayi ha'kuri Dady bazan samuzuwa a wannan lokacin ba sabida aykin danikeyi amma idan nakammala zanyi 'ko'karin zuwa "

Murmushi dady yayi sannan sukayi sallama ture system d'in DON yayi sabida wata sabuwar damuwa yakeji

" wai Amaryata ? ni Affan tayaya zan'iya gudanar da rayuwa tareda mace macanma har 2 ? "

Jin zuciyar shi naneman fara ciwo yasa yashiga toilet yasakarma kanshi ruwa cikin 'bacin rai Alhaji Sambo yashiga cikin parlour Hajiya Aysha zibewa yayi kan cushion batare dayace mata komiba

Kallon shi Abdulhakim yayi yamaida duban shikan TV batare dayacemai komiba cikin tuhuma Hajiya Aysha tace

" Alhaji lafiya ? tund'azu kainike jira natambayeka amma kashigo babuko sallama maiyafaru ? "

Girgiza kai Alhaji Sambo yayi sannan yace

" inafa lafiya Aysha ansamu wani saban d'an kwangila yafara mamaye komi gashi har yanzu munkasa gano wayeshi cikin lokaci kad'an zaimaye gurbin Alhaji Isma'il komi nawa yafarayin 'kasa dole nami'ke dan tunkarar abinda zaizamarmin barazana gabada gaba "

Jinjina kai Hajiya Aysha tayi sannan tace

" to Allah yakyauta ashe akwai babban 'kalubale agabanmu kaida mukeso kazama tamkar Alhaji Isma'il amma abin yagagara se yanzu rana tsaka asamu wani gaskiya dasake amma Alhaji dukba wannan ba tukun banga takardun d'ayan Company ninaba karde suna gurinka gas....... "

Cikin tsawa yadakatar da ita dafad'in

" Kai Hajiya Aysha karki maidani matsiyaci mana tayaya duk abinda bakiganiba naki sekikama tambayata kinta'ba bani ajiyar wasu dagacikin kadarorinki ? to daga yau idan kika sake tambayata wani abu dayashafi kadararki sena baki mamaki "

Tashi yayi yafita afusace cikin ba'kin ciki tabishi da kallo kallonta Abdulhakim yayi yace

" Momy Dadyne yad'auka "
Cikin takaici da'bacinrai tace

" rufemin baki shasha kawai bazaka'iya karemin dukiyataba haba Abdulhakim kanaganin yadda mahaifin ka keson tsiyatani amma baka iya hanawa ? kefa bayaran goge bane kasanwasu abubuwan narayuwa amma kake bari mahaifin ka nacutar dani akan idanun ka "

Cikin dakewar zuciya Abdulhakim yace

" Momy bazan iyasaka baki ko hannu akan dukiyarki ba dakuma tsakaninki da dady ba sabida banason na'bace a duniya kamar yadda brother na ya'bace acikinta sanadin son kud'inki Momy kinza'bi kud'i akan Brother na gashi yatafi har yanzu babu labarinshi kuma banga kinyi nadamaba tayaya zansa kaina cikin lamarin dukiyar ki nima kiturani duniy........ "

Wani zazzafan mari tad'auke shi dashi tace

" a'ina kaji wannan labarin ? sannan kakalli tsabar idona kake gayamin haka "

Juyawa Abdulhakim yayi yanufi bedroom d'in shi batare dayace mata komiba kaikomo Hajiya Aysha tashigayi a tsakiyar parlour ta afili tace

" waya sanar da Abdulhakim wannan labarin ? Waya gayama bana tunanin Affan kodan tarin dukiyar shi danikeso dole nayi tunanin ina yake amma bazan gaji daneman barrister Ibrahim ba dan nasan dukiyar Affan tana gurinshi idan Affan yamutu nice mai hak'kin mallakar dukiyar shi hmmm dole nasake mi'kewa wajan neman barrister "

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A Aji β™ β™₯♣

Comments and shine plssss
[13/06 6:57 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE 🀝🏻😍🌹

Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci

Am dan Allah fan's indena wuta ana binada fetir sisters 😊 idan na'kone tayazan'iya typing 😊 ana tare

πŸ…Ώ { 21 to 22 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Tunda safe DON yafita babu jimawa yadawo tare dawata Doctor fuskar nan tashi atamke yanufi cikin bedroom d'in tsakiyar gado yahanko Kausar tadu'kun'kune se rawar sanyi takeyi cikin sauri ya'karasa hannun shi yad'aura saman goshinta cikin sauri yajanye hannun shi sabida tsananin zafin dakan yad'auka juyawa yayi zaisauka daga kan bed d'in cikin rawar jiki Kausar takamo hannun shi cikin galabaitacciyar murya tace

" yaya Affan dan Allah kabani magani kayimin dan Allah badanniba yayana "

Kallon cikin idanunta yayi karo na 2 dayaji tausayin wata 'yamace tuno yarinyar dayayima fayd'e yayi jiyayi tamkar muryarta batare da saninshiba yashafi fuskarta sannan yajinjina mata kai yafito tare yakoma cikin bedroom d'in da doctor hard'e hannuwan shi yayi gefe yana kallon yadda take duba Kausar bayan tagaka tadubeshi tace

" ranka shidad'e matarka tanafama da matsananciyar damuwa wadda zata iyahaddasa mata jininta yahau gaskiya tana bu'katar kulawa kuma yakamata tadingacin abinci sosai kuma akan lokaci asiyomata wa'innan magungunan " taci abinci tasha "

Amsar paper yayi sukafita tare komawa Kausar tayi takwanta maida doctor yayi sannan yasiyo magungunan yabiya Restaurant yasiyo mata abinci yadawo kamar yadda yabarta haka yadawo yasameta ganin shi yasa tayun'kura tatashi zaune mi'ka mata magungunan da abincin yayi yafita batare dayace komiba kallo tabishi dashi

Shiko yanafita yawuce bedroom d'in shi wanka yayi yafita yana cikin driving yaji shigowar text cikin wayar Kausar bud'ewa yayi text ne daga Amina kamar haka

" Aminiyata nasan duk inda kike kinacikin damuwa kiyi ha'kuri dawannan mugun sharrin da akayimiki in sha Allah Allah zaitona asirinsu kibama yaya DON ha'kuri kidawo Skul koda bazaki zauna cikin Skul ba kinsan yanzune lokacin jajircewa wajan karatunmu kinji Aminiya ta

Parking DON yayi yakashe motar yajinginar dakanshi jikin kujerar motar yalumshe idanunshi yana nazarin wannan text d'in afili yace

" idan har hakane to waye yayimata sharri ? Kay karyane wannan Plan ne amma zansa ido akan komi nata "

Tada motar yayi yanufi office kad'an Kausar taci abincin tasha magungunan zuwa can tami'ke toilet tanufa tayi wanka ahankali take shiryawa wata had'ad'iyar joguwar riga tasaka jin nan knocking yasata jumbula hijab d'inta tafito bud'ewa tayi wani dagacikin ma'aykatan gidan ne yace

" sannu Hajiya dama yalla'baine yace mushigo dakaya "

Basu hanya tayi sukafara shiga dakayan abinci kalakala komawa ciki Kausar tayi zuwacan tafito kitchen d'in tashiga sun shiryakomi bud'e freezer kitchen d'in tayi shima ancikashi dakayan bu'kata hakama freezer parlour

'Dan murmushi Kausar tayi har cikin ranta tajidad'in haka kobabukomi dalilinta yakawo duk wannan cikin natsuwa tad'aura abinci tanayi tana tuna yadda yashafi fuskarta d'azu dandanan gidan yabud'e da kamshi cikin wani lokaci takammala abincin tashirya kan dining sannan tanufi bedroom d'in shi gyaramai ko ina tayi tasakemishi bedsheet dukda d'akin babu datti kamar macace aciki macanma mai tsananin tsabta wani irin kamshi maidad'i yagarwaye cikin bedroom d'in fitowa tayi tagyara parlour shima yad'au kamshi sannan takoma bedroom d'in ta

Wani wanka takumayi simple makeup tayi tafesa turarukanta masu sanyin kamshi sannan tafito parlour zamatayi kan cushion d'in dake kallon 'kofar shigowa parlour misalin 06:30 DON yadawo idan bacikin natsuwa kakeba bazakaji sallamar shiba

Cikin sauri Kausar tami'ke amsar bag d'in hannun shi tayi kamar bazai bataba sekuma yasakar mata cikin siririyar muryarta tace

" sannu da dawowa yaya "

Batare daya amsaba yace

" yajikin naki ? "

ahankali tace

" Alhamdulilah yayi sau'ki "

Wucewa yayi kaitsaye cikin bedroom d'in shi cikin mamaki Kausar tabishi da kallo dan bata ta'ba tunanin zai iyatambayarta ya jikintaba bin bayanshi tayi koda tashiga baya cikin bedroom jin 'karar saukar ruwa yasatasan yanacikin toilet ke'babban guri tasamu ta'ajemai bag d'in sannan tad'akko mai wasu kaya mararsa nauyi ta'ajemai kan bed tafita

Yajima cikin toilet sannan yafito ganin kaya saman bed d'in shi yajiwani 'bacinrai gaban mirror yanufa yashafa 'kyatattun mayukanshi had'ida fesa turaruka haryasa hannu zai d'akko wasukayan seyatuna zancan doctor afili yace

" har abada bazan zama silar saka koda ma'aykacin gidan Dady ne amatsalaba balle yarshi jininshi koda raina bayaso zansa wannan kayan "

'D'aukar kayan yayi yasa sannan yazauna kan sofa system d'in shi yabud'e yafara ayki aciki jin shiru bai fitoba yasa Kausar shiga kitchen fruit tayayyanka mishi kalakala had'ida lemon mango tanufi bedroom d'in bakinta d'aukeda sallama

Ahankali ya'amsa amma idanun shi nakan system d'in aje tiran tayi agaban shi tace

" yaya sannu dahutawa please nasan bakaci komiba ga fruit nasan kanasonsu nashiryamaka dinner dan Allah yaya karka'ki ci danson da kakema Allah da manzon shi dakuma Abba bai kalletaba amma yakasa cigaba da aykinshi

Juyawa Kausar tayi hartakai bakin door d'in yace

" zonan "

Cikin sanyin jiki da fargaba tadawo wayarta yami'ka mata had'ida key d'in mota yace

" dawannan motar zakidinga zuwa Skul amma tareda security idan kingadama kicigaba da shashanci bawai nabarki bane kiguji ranar dazamuyi karo na 2 kince sharri akayimiki ko ? tozanyi bincike akan haka kitabbatar kinsha magungunan ki kafin ki kwanta zaki iya tafiya "

Tashi Kausar tayi cikin zuciyar ta tace

" Alhamdulilah tunda baka hanani zuwa Skul ba Allah yabaka ikon bincikawa nafita daga zargi "

Bayan fitar Kausar DON yakalli fruit d'in gabanshi wani irin damuwa yaji tunawa da mahaifin shi yayi tare sukeshan fruit afili yace

" Allah yaji'kanka Abba na Momy maiyasa kikamin haka ? kindasamin 'kiyayyar duk wata 'ya mace acikin raina amma nakasa mantaki Momy maiyasa maiyasa ? "

Wasu zafafan hawaye suka gangaro saman fuskar shi rufe system d'in yayi yajinginar dakanshi yalumshe idanunshi yana tunanin rayuwar shi tabaya

Sudan

Cikin 'bacin rai Ammi tacema Hajiya Saratu wato 'kanwar ta

" wallahi idan har nabari Seeyama tazauna da kishiya to basunana bulkisu ba ina bazai ta'ba yiyuwaba "

Ta'be baki Hajiya Saratu tayi tace

" Amma nikam kinbani mamaki baikamata kiyita kishirta yanzuba ni aganina wannan tarin dukiyar tashi ita yakamata musan yadda zamuyi mukwashi rabanmu sannan semu dawo kan kishiyar tata "

Jinjina kai Ammi tayi tace

" yauwa 'kanwata to tayaya ? "

Murmushi tayi sannan tace

" bayan ankai amarya koda da wata 1 ne semuje akan ganin d'aki semu tafida Ayman da jabir idan mukaje semuce zasu zauna agunshi sutayashi kulada dukiyar shi kinga bazai'ki jinin shiba daganan semusasu ahanyar damukeso nasan yaranmu bazasu bamu kunyaba sannan munemi maganin dazamu bama Seeyama dataje tasamu ciki kinga shikenan mun tattare komi "

Wata irin shewa suka saki

Ya Allah Allah kashiryar damu

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A Aji β™ β™₯♣

Comments & shere plsssss
[15/06 3:26 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE 🀝🏻😍🌹

Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci

πŸ…Ώ { 23 to 24 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Misalin 11pm Kausar tafito daga bedroom d'in ta kitchen tashiga d'akko Lipton sabida sabo datayi dashanshi duk dare sanye take dawata doguwar rigar bacci marar hannu mai taushi da santsi wani 'karamin gyale ne tayafa saman kanta sumar kanta takwanta lif saman bayanta sezuba kamshi takeyi

Cikin natsuwa tagama had'a Lipton d'in wanda yaji kayan kamshi har tasa cup 1 sekuma tazuba awani cup d'in yazama 2 saman 'karamin tire tasa ahankali take tafiya kamar maijin tausayin 'kasa cikin bedroom d'in DON tanufa takoyi sa'a abud'e yake

Bakinta d'auke da sallama tashiga yanayin data ganshi yasa yasata saurin ajiye tiran hannun ta saman tebur batare dajin wani tsoroba tanufi inda yake cikin gigita tad'aura hannunta saman 'kirjin shi dede setin zuciyar shi kamar yadda taga yad'aura wani irin bugu taji zuciyar shi tayi cikin tashin hankalin tace

" yaya ina maganin ka ? dan Allah kasanar dani inda yake ? "

Kallonta yakeyi amma yakasa magana se jawo numfashin shi yakeyi da'kyar tashi tayi tanufi bincikawa amma babu alamar zata ganshi gabad'aya tagama rud'ewa sabida wani irin nishi dataji yanayi cikin sauri tabud'e freezer shi cikin sa'a taganshi

Cikin sauri taciri yadda yake sha Lipton d'in tada kawo tad'akko sannan tanufi gunshi nufar bakinshi tayi da maganin amma ya'ki bud'e bakin hannu yami'ka mata tasame maganin sannan ya amshi cup d'in Lipton d'in yasha amshar cup d'in tayi ta'aje tacigaba dayi mai sannu amma kamar badashi takeba cikin zuciyar ta tace

" kana cikin rashin lafiya ma sekayi miskilanci Allah yasauwa'ke "

Tsayin lokaci sannan DON yafara samun sau'ki wani irin zazza'bi ne kuma yataso mai wata irin rawar sanyin yashigoyi cikin rawar jiki yaja blanket yarufe jikin shi hadda kanshi amma dukda haka rawar sanyi yakeyi har ha'koranshi nahad'uwa

Cikin tausayawa Kausar ta d'an dafa jikin shi jin hannunta ajikin shi yasa yajanye blanket d'in daga saman fuskar shi kallon ta yayi da nuna alamar tacire hannunta amma ita bata fahimci maiyake nufiba ganin batada niyyar janye hannunta shikuma gawani mugun sanyi dayakeji yasa yatashi zaune cikin sauri ganin haka yasa Kausar furgita da razana tafad'a kanshi batare da saniba

Wani irin zafi taji jikinshi yad'auka shiko DON wani irin d'umi yaji yanashigar shi wanda koda yarufa baiji rabin hakaba kasa yimata magana yayi cikin tsoro Kausar tafara 'ko'karin tashi d'ago kantatayi takalli fuskar shi girgiza mata kai yayi ahankali alamar karta tashi

Sauke ajiyar zuciya Kausar tayi cikin sanyin jiki tamaida kanta saman 'kirjinshi jin d'umin bai garwaye jikin shiba yasa yazagayo da hannuwan shi bayanta yamatse ta tsam wani irin tsoro Kausar taji yakamata

Ahankali DON ya gyara kwanciyar shi yanamai sake rungumeta tsayin lokaci suna ahaka wani irin baccine yayi gaba da DON itako Kausar takasa rintsawa ganin baccin shi yayi nisa yasa tafara 'ko'karin janye jikinta amma setaji yasake rungumeta sosai fuskarsu na kallon juna zubamai ido Kausar tayi cikin zuciyar ta tace

" masha Allah lalle Allah yayi kyakkyawar halitta anan Allah yabaka komi DON amma yahanaka farinciki ni Kausar nayi al'kawarin samarmaka dafarin ciki dauwamamme in sha Allah Allah kabani iko "

Jin kiran sallar asuba yasa DON bud'e idanun shi ahankali cikin mamaki yake kallon Kausar dake shan baccinta hankalinta a kwance kamshin jikinta yabugi hancin shi kallon sumar kanta yayi cikin sauri yarumtse idon shi sannan yasake bud'esu yanayin rungumar dayayi mata yakalla take nan abinda yafaru jiya yadawo mai rumtse idon shi yayi yace

" oh my God tayaya haka ? mai kenan nayi ? "

Cikin zafin rai yayi yun'kurin tashi amma ina yakasa kwatakwata jikin shi babu 'karfi gawani irin yanayi dayakeji zuba mata idanun shi yayi yakasa kaudasu tuni yaji kamar ya ....... Bud'e idon da Kausar tayi yasa tunanin shi tsayawa ganin yana kallon ta yasatayin mutuwar kwance tamke fuska yayi yace

" se yaushe zakigamajin d'umin jikin nawa ? "

Cikin mamaki Kausar takalli yadda yarungume ta tsam cikin sanyin jiki tajanye jikinta akunyace tami'ke hanyar fita tanufa har takai bakin 'kofa yace

" Idan kinyi salla kidawo kisanar dani dalilin dayasa kika shigomin cikin bedroom cikin dare "

Karasa fita tayi tana maimaita kalaman shi cikin ranta tana fita tasauke ajiyar zuciya had'ida dafe 'kirjinta tace

" yaya Affan yananufin tuhumata zaiyi ? waima yaushe zangamajin d'umin jikin shi bayan shine yari'keni amma ya'ki yarda dahakan sabida miskilancin shi "

Shiko DON tashi yayi zaune yadafe kanshi yana tuhumar kanshi maiye wannan ya aykata ? wani irin takaici yakeji afili yace

" yau nine tareda mace a kan bed d'aya ? kuma rungume kay gaskiya ina akwai abinda keshirin faruwa dani "

Tashi yayi fuskar nan tashi amatu'kar d'aure yashiga toilet seda yayi wanka sannan yayi alwala yanufi masallaci

Cikin sanyin jiki Kausar tafito kitchen tanufa doya tafere ta d'aura sannan tafito tanufi bedroom d'in shi cikin sauri tagyara mai shi tsaf sannan tafito kitchen takoma lokacin doyar tadahu kunun gyad'a ta d'aura cikin lokaci kad'an tadama sannan tafasa 'kwai tafara suyar doyar cikin natsuwa takeyin komi had'a mishi nashi tayi dukda tasan balallene yaciba har cikin bedroom takaimai sannan takoma tad'uki nata tanufi bedroom d'in ta

Wanka tafarayi cikin sauri sabida lecture d'in safe gareta batad'au lokaci ba wajan shiryawa bayan tagama tazauna wajan yin breakfast shima cikin sauri agaggauce tafito parlour ri'ke da bag d'inta bedroom d'in DON tanufa amma cikin mamaki baidawoba tunda yafita masallaci

Cikin damuwa tazauna kan sofa tanamai addu'ar Allah yasa yashigo yanzu kimanin 15 minutes dazamanta yashigo kallon d'akin yayi cikin ranshi yace

" lalle yarinyar nan "

Jin sautin muryarta tana gaidashi yasan tanacikin bedroom d'in ko kallonta baiyiba yanufi bakin bed d'in shi yazauna wayarshi yad'akko yafara latsawa ajiyar zuciya Kausar tasauke cikin sakka tace

" yaya zantafi Skul nakusa rasa lecture "

Kamar bazaiyi magana ba zuwa can yace

" idan kinfad'amin dalilin dayasa kika shigomin cikin bedroom jiya sekitafi "

Cikin wani irin yanayi tace

" nazo kawo maka Lipton ne shine naga bakada lafiya "

Kwanciya yayi yalumshe idanun shi sannan yace

" tunda bazaki fad'i gaskiyaba tashi kibani guri ay kinsan banacin abinda duk wata 'ya mace tadafa dan haka wannan bashibane dalili tashi kikoma bedroom d'inki bana bu'katar wata magana kuma "

Dan danan idanun Kausar sukacika da hawaye jiki a sanyaye tami'ke kamar yadda yace cikin bedroom d'inta takoma batasan lokacin da hawaye suka shiga gangarowa daga idanun taba

Ajiyar zuciya DON yasauke idanun shi alumshe tuno surar jikin Kausar yashigayi sekuma yayi saurin jan tsuki tashi yayi yashiga toilet wanka yayi yafito cikin sauri yashirya cikin 'kananun kaya sosai yayi matu'kar yin kyau key d'in motar shi yad'auka yafito

Cikin bedroom d'in Kausar yanufa zaune take tayi tagumi duk takaici ya'isheta cikin yanayin miskilancin shi yace

" idan kingama kukan kitaso mutafi ki d'akko key d'in motar ki "

Yana gamafad'ar haka yajuya jin wannan furucin nashi yasa Kausar jinwani irin sanyi cikin ranta cikin sauri tad'auki bag d'in ta da key d'in tafita yana gaba tana bayanshi kusan tare suka isa jikin motar shi

Cikin girmamawa ma'aykatan gidan suka fara gaidasu hannu yami'ka mata fuskar shi atamke ganin tana kallon shi yasa cikin d'an fad'a yace

" kibani key d'in motar ki "

Mi'ka mishi tayi cikin zuciyar ta tace

" ikon Allah sekace nasan gaibune "

'Daya dagacikin ma'aykatan yaba yace

" kashiga waccan motar kabimu abaya ku kuma nasanar daku daga yau kune masu tsaron lafiyar ta kuma nace komi 'kan'kantar abu idan har yafaru to asanar dani maza kushiga mota muje "

Kallon ta yayi alamar tashiga jiki babu 'kwari tashiga shima yashiga driver yatada mota motoci hudu 2 ta Security se tashi seta Kausar ta security d'aya nagaba seta su sannan dayarta security a baya

Suna shiga cikin harbar Skul d'in idanun jama'a dayawa sukayo kansu cikin sanyin jiki Kausar tafito adede lokacin da Ameera tazo wucewa kallonta ta tsayayi sabida batayi tunanin dawowar Kausar cikin Skul d'in ba

Ahankali DON yafito daga cikin mota kud'i yami'ka mata cikin yanayin maganar shi mai cike da izza yace

" karki fasayin abinda kikaga dama nikuma bazan fasayin hukunci ba "

kallon security d'in yayi yace

" duk namijin dakuka gani yazo kusada ita nabaku umarnin kuyimai mugun duka kod'an gidan ubanwaye "

Yana gama fad'ar haka yakoma cikin mota drive yaja sukajuya tareda motar security d'aya kallon securities d'in Kausar tayi cikin zuciyar ta tace

" inama amfanin wannan abun sekace watamarar gaskiya anhad'ani da wa'innan 'kattin dababu alamar imani atare dasu "

Jin ihun Amina da sauran 'kawayenta yasa Kausar juyowa cikin farinciki suka rungume juna Ameera da 'kawayen ta sunagefe suna yimusu kallon banza ganin haka yasa Amina tace

" wai harna fara kallon 'kyallin amarci a fuskarki gaskiya garada mijin ki yamaidake kusadashi kinga kyasamu cikakkiyar kulawa "

Dariya suka saki dukansu cikin mugun ba'kin ciki da razanar abinda kunnuwanta sukaji tayo gunsu tana huci tace

" Ke Amina wace banzar magana kikeyi ? kina nufin wai DON d'ina shine mijin Kausar ? "

Murmushi Amina tayi tace

" gyara maganarki DON d'in Kausar zakice banakiba tuni DON yazama mallakin Kausar ita kad'ai dan haka kisamama kanki lafiya "

Cikin zafin rai tasha'ko wuyan hijab d'in Amina wata irin tsawa d'aya dagacikin Security d'in yayi sannan yace

" idan baki saketaba senayi miki muguwar zana ko kallon banza kikayima 'kawar matar boss wallahi sena canzamiki halitta "

Wani irin mugun tsoro yakama Ameera sabida taga babu alamar wasa cikin idanun shi sakinta tayi tabar gurin cikin takaici da mugun ba'kinciki

suma su Kausar tafiya d'aukar lecture sukayi suna tafiya suna hira bayan sunfito sukanemi guri suka zauna kallon Kausar Amina tayi tace

" Kausar kidage wajan janyo hankalin mijinki mace zata'iya sauya ra'ayin mijinta karki bari wata tacinasara akan mijnki "

Ajiyar zuciya Kausar tasauke sannan tace

" zan iyayin komi dan ganin nasaka yaya Affan cikin

Please Login or Register in order to submit comment