Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 61 to 62 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Fitowa DON da Abdulhakim sukayi cikin zafin rai DON yabada damar afito dakowane ma'aykaci nacikin gidan haka kuwa akayi cikin lokaci kad'an kowa ya bayyana marassa gaskiya zuciyoyin su cike suke dafarga sukuma sauran suna murna dan sunyi zaton irin kyautar dayasaba yimusu zaiyi

Cikin matu'kar zafin rai DON yasha'ko wuyan wannan mutumin wani irin naushi yasakar mishi wanda yasashi bajewa 'kasa ganin haka security sukayi saurin tasowa tunkafin DON yabasu umarnin sukafara dukan shi tunyana ihu har ihun yagagara ganin haka DON yadakatar dasu

Sawa yayi aka mi'karmai dashi kallon fuskar shi DON yayi cikin zafin rai yace

" ubanwa yasaka le'ken asirin cikin gidana sannan inaso kasanar dani wakasanar mawa maganar dakaji yanzu idan ka'ki sanar dani wallahi kasheka zanyi kumanayi binciken nagane komawaye kaga katafi abnza nadad'e ina lura da dukwani marar gaskiya acikin ku kuma wallahi duk wanda nagano senasashi yayi nadamar zuwan shi duniya "

Cikin wata irin wahalalliyar murya yafara fad'in gaskiyar abinda yasani

" Oga dan Allah karka kasheni zansanar da kai komi Alhaji Sambo shine yasamu muyumai bincike akanka munkai mu 8 a cikin gidannan ciki harda d'an shi gashi nan Abdulhakim wanda kad'aukeshi tamkar jininka eh kusan haka tunda mahaifiyar ku d'aya ayanzu Alhaji Sambo yasan kaine Affan d'an gidan margayi Alhaji Isma'il kwangila kumayasa akasheka sannan yatura akashe mahaifiyar ka sede ansamu rashin sa'a bata cikin gidan amma yasamu labarin cewa d'ayar matarka tana hospital ayanzu haka kuma yasa aje asaceta sannan nasanar dashi labarin wannan CD kuma nasan ayanzu haka yakusa isa gidan "

Sha'ko wuyan shi DON yayi yana fad'in " kasani idan wani abu yasamu Seeyama wallahi sena kasheka kukaishi dashida sauran tawagar tashi ku kullemin su kuyimusu mugun duka "

Daga haka yanufi mota shida Abdulhakim wasu daga cikin Security suka biyo bayan shi dakatar dasu yayi yabama 2 daga cikin umarnin subiyoshi suna fita sukanufi hanyar Hospital adede lokacin Ammi takira wayar DON cikin kuka take sanar dashi wasu sunzo suntafi da Seeyama wani irin 'bacin rai DON yasakeji ciki zuciyar shi

'Dan dakewa yayi yace karsu damu zai dawo da ita ayau in sha Allah sukuma yanzu zaituro da mota akaisu gida bayan yakashe kiran Ammi takalli Umma tasaki wani shi'umin murmushi tace

" Saratu kisa ido yanzu zakiga irin aykina kinsan dama ance sedad'angari kanci gari kinga wannan Alhajin makiyin DON ne sosai nace suka 'kud'i masu yawa wajan amsar Seeyama kuma nasan shizai biya sannan idan yaje kasheshi zasuyi kinga sauran ayki yarage mana Hajiya Aysha da Abdulhakim da ita Kausar cikin sau'ki zamugama dasu kinga dukiyar DON tazama ta Mijina shima semu aykashi inda muka tura sauran kinga shikenan dukiya tazama tamu jabir seya auri Seeyama shikenan "

Wata irin shewa sukayi suka tafa tofa Allah karabamu da'irin wannan zuciyar Ameen

Kodasu DON suka isa gidan maigadi yahanasu shiga sabida bayan tafiyar su Alhaji Sambo da tawagar shi mai gidan yatsorata sosai hakanyasa yace karya 'karabarin kowa yashiga ganin maigadin yana neman bata musu lokaci yasa DON sawa akari'ke mishi shi suka shiga sosai suke knocking kafin mai gidan yafito

I D Card d'in shi DON yanuna mishi ganin haka yasa shi sauke ajiyar zuciya basu umarnin shiga yayi zama sukayi a parlour cikeda izza DON yake magana

" kamar yadda kagani sunana Affan Isma'il kwangila d'a gamai wannan gidan da Alhaji Sambo yashiyar maka abisa cuta dan haka inaso kasanar dani kimanin nawa yashiyar maka da gidan nikuma zan ninka maka sau 2 kaje kasiyi wani bazan iya barin wani acikin wannan gidan ba anan mahaifin yarasu bazan iya manta gidan ba inaso mahaiyata tacigaba dazama a cikin shi har 'karshen ranta sannan kabar gidan nan ayau sabida kare lafiyar ka dan nasan Alhaji Sambo zai'iya dawowa zaiyi tunanin zaisamu wani abu na'karin bayani agurinka idan ka'ki zai'ya kasheka wannan shawarace nabaka dan inada tabbacin yasan munzo ga katina idan katashi amsar kud'in gidan ka iya nemana idan kuma ka'ki to zakarasa duka babu gida babu kud'i "

Mi'kewa DON yayi yacema Mai gidan " kayi ha'kuri zanshiga cikin gidan ka har cikin d'aki bincike ne yakawo banason kowa yabiyoni se kai Abdulhakim "

Shiga sukayi mamaki sosai Abdulhakim yayi dayaga wannan d'akin dan idan zaka shekara bazakasan da d'aki agurin ba cikin sa'a kuwa suka ga CD murmushi DON yayi sannan yacema Abdulhakim zanfita tana kai kuma kafita kukoma gida sabida nasan Alhaji Sambo yana nemana sabida wannan CD banaso yasan nagan shi harsena ga abindake cikin shi nasan zasu biyoku idan sun tareku sukaga bana tare daku zasu barku sutaho nemana zuwa lokacin nima nakoma gida "

Jinjina kai yayi yafito shikuma yafita tacan koda Abdulhakim yafito cikin mamaki suke kallon shi ganin babu DON basu umarnin tafiya yayi yakalli mai gidan yace " karka damu brother na yana ayki aciki muzamu tafi yanzu idan yagama zaitaho d'aya gada cikin security d'in yayi saurin d'aga waya yakira DON dan tunda yaji wannan yace Abdulhakim d'an Alhaji Sambo ne yaji bai yarda da Abdulhakim d'inba d'aga wayar DON yayi yamai bayanin komi sannan yagamsu fitowa sukayi suka shiga cikin mota

Aguje suka figi motar wani dake zaune daga can nesa yayi saurin kiran Alhaji Sambo yasanar dashi sun fito dagacan yabama wasu umarnin su tare motar su DON musamman dayaji bada security suka fitaba

Babu zato wata mota tasha gaban tasu Abdulhakim tsayawa sukayi batare dasun fitoba wa'inda ke cikin waccan motar suka fito hannun su ri'keda makamai nufo motar sukayi seda suka iso bakin motar Abdulhakim yafito sauran security d'in ma suka fito

Le'ka motar sukayi ganin babu DON aciki yasa d'aya daga cikinsu d'aga hannu zai kifama Abdulhakim mari jin 'karar harbin bindigu a bayansu yasashi dakatawa yajuya cikin sauri wani irin fitsari yaji yatahomai sabida ganin jami'ay masu yawa sun kewayesu cikin lokaci kad'an kowa d'auke da bindiga yadda makamansu sukayi duka suka kamasu suka tafi dasu

Komawa mota su Abdulhakim sukayi suna isa gida yanufi ciki shiko DON tuni yarigasu isa Abdulhakim yana shiga yarungumai DON yana sauke numfashi sannan yace

" Brother nagode ma Allah dakayi hikimar turo mana Security dayau mun bani " dariya DON yayi yace

" haba Abdul karka bani kunya mana badai tsoro kake nufin kajiba ? Ni dason ra'ayinane da Soja kaje amma gashi kaid'in matsoracine "

Dariya Abdulhakim yayi yaturo baki murmushi Momy tayi tace

" maza kayi shagwa'ba agaban matarka koka manta yanzu ka girma ? "

Jin haka yasa shi saurin tamke fuska itako Ameera kallon shi tashigayi afakaice dan ayanzu wani irin sonshine cikin ranta tuni taha'kura da DON dan tasan yariga yafi karfin ta tashi DON yayi yasaka CD ganin mutanan da yadda sukayi kisan yasa kowa dake gurin zubda hawaye musamman Abdulhakim dashi ayanzu ne yaga yadda akayi kisan mahaifin shi

Duk fuskokin su arufe suke se mutun d'aya da Alhaji Isma'il yafizge nad'in fuskar shi dede lokacin Barrister yashigo shida Ashiraf ganin yanayin dasuke ciki yasashi kashe system d'in lallashin su yashigayi seda yaga sun bar kukanan sannan barrister yace

" DON ka kwantar da hankalin ka ni nasan wa'inda sukasa aka kashe mahaifin ku yanzu lokaci yayi dazaka d'auki fansar ranshi akansu abaya banida mafita illah naboyeka nima naboye kaina sabida kudin karsu halakamu amma yanzu basuda yadda zasuyi damu DON Alhaji Sambo da Alhaji bala da Alhaji sammani sune sukasa aka kashe mahaifin ku sannan ya auri mahaifiyar ku dan yacinye dukiyar mahaifin ku gaba d'aya amma ke Hajiya Aysha kika kasa gane hakan kuma........ "

Kiran wayar DON da'akayi yasa barrister yayin shiru daga wayar yayi dagacan akayi magana kamar haka

" Alhaji Affan Isma'il kwangila wanda akafi sani da DON gidan kud'i to DON munsan bazaka bamu wahalaba wajan bamu abinda zamu bu'kata dan fansar matarka Seeyama sabida gidan kud'ine to kajini da kyau million 100 zaka bamu idan Bahakaba zamu kashe ta mun baka nanda 24 hours kahad'a wa'innan kud'in muna jira sannan idan zakazo karka sake kazoda jami'an tsaro kai kad'ai muke bu'kata ko kaida 'kaninka Abdulhakim zamu kiraka zuwanan da lokacin "

Kashe wayar sukayi bin wayar DON yayi da kallo cikin tashin hankali Hajiya Aysha tami'ke tana salati sabida sunji komi dan a bayyane yayi wayar dede lokacin su Ammi suka shigo kuka suka sani sosai ha'kuri DON da barrister suka basu cikin kukan munafurci Ammi tace

" mun shiga Uku Affan ina mukaga wa'innan makud'an Kud'in haka har million 100 ? "

Cikin ta kaici DON yace " karku damu nide fatana karsuyima Seeyama komi " cikin sauri har tana in'ina Umma tace " DON kana nufin nanda 24 hours zaka kai musu million 100 ? "

Jinjina kai DON yayi yace " in sha Allah " wata irin ajiyar zuciya Umma tasauke ta kalli Ammi kashe mata ido tayi setasaki kuka sake kallon Ammi barrister yayi yana nazarin irin kallon cikin zuciyar shi yace " tabbas akwai wani abu amma zansa ido "

Zuwa dare DON yasa duk ankamo mai su Alhaji Sambo har anshigar da 'kara a kotu sawa DON yayi aka fitomai dasu duksun sha mugun duka ganin Abdulhakim da Momy yasa Alhaji Sambo saurin cewa " ki kaimin d'ana gida wajan sauran 'yan'uwanshi dan nariga nasan ni kasheni za'ayi nace ku kasheni anan base anje kotu ba banason ku'batamin sunan zuri'a "

Murmushin takaici Momy tayi tace

Dole kaje kotu azzalumin banza sannan Abdulhakim dakake i'kirarin d'ankane to bad'an kabane shid'in d'an Alhaji Isma'il ne zamusa a d'ibi jinin ka agwada dana Abdulhakim danka tabbatar shid'in ba d'an kabane "

Tuni Alhaji Sambo yaji wata irin juwa tana d'ibar shi kuka yakamayi sosai danshi yana tunanin zasu'iya ragamai sabida Abdulhakim segashi yaji bama d'an shi bane sawa DON yayi aka maidasu sannan yakoma Office su Momy suka koma gida su 5 cikin Office d'in DON sunabin didd'i'kin number da aka kirashi da ita amma sun kasasamu

Kuka sasai Seeyama takeyi musamman dataji dasa hannun Ammi da Umma wajan saceta sabida abin duniya sawa tayi sukakiramata Ammi sannan tace subata guri bayan Ammi tad'aga kiran Seeyama tafashe dakuka tana fad'in

" haba Ammi wannan wace irin rayuwa ce ? takan kud'i kisa asaceni bakya tsoran sucutar dani Ammi har kun manta da abinda yafaru a Hospital haba Ammi dan Allah kubarni nayi rayuwar aure cikin jindad'i mana nikam inason mijina kuma wallahi idan nafito sena nasar dashi kune kukasa aka saceni "

Murmushi Ammi tayi amsar wayar Umma tayi tace

" amma ke Seeyama yaushe kika zama shasha sha ne ? duk badan ke mukeyin komiba kimanin million 60 fa zamusamu su mubasu 40 million haba Seeyama kar kiyi mana ba'kin ciki mana nan bada jimawaba zaki mallaki DON ke kad'ai "

Wani kuka Seeyama tasake saki tace

" idan kuka kashe min Aure dan son ranku tofa kusani kuda Allah kuma Allah bazai barkuba shiyasa tun farko banso zamanki a gidanaba dan nasan halinki Umma ke kikayi sanadiyyar mutuwar mijin ki gsshi yanzu nikuma kinason kashemin aure Wallahi ban ta'ba ganin iyaye masu RUFAFFIYAR ZUCIYA ba irinku "

Seeyama nakaiwa nan takashe kiran cikin sauri tashiga turama DON text sanar dashi inda take tayi amma bata sanar dashi hadda sa hannun su Umma wajan sacetaba tana turawa tagoge text d'in ganin text d'in Seeyama yasa DON sauke ajiyar zuciya cikin sauri aka shirya jami'an hadda sojoji cikin wannan daran suka nufi gurin sannan DON yabada umarnin duk wanda suka gani agurin su kashe shi kawai

Haka kuwa akayi babu zato sukaji ankawo musu farmaki kashesu akwai aka shigayi tsautsayi yaritsa da Jabir yaje yababda kama yayima Seeyama fayd'e kuma dasanin Umma don ita tasanar dasu subarshi cikin rashin sa'a bulet yafasa kanshi take anan yace ga garinku nan an kashe wasu dayawa daga cikin su wasu kuma sun gudu an kama 2 amma sunyi matu'kar jiggata dan sede aka wuce dasu Hospital daga nan

Sosai DON yarazana daganin gawar Jabir Allah sarki Seeyama dukda abinda yazo yimata amma seta rufamai asiri tace

" yazo kwata tane daga hannun su ashe zairasa ranshi sosai take kukan takaici ha'kuri DON yashiga bata rungume ta yayi sosai cikin kuka tace

" Baby dan Allah ko sau d'aya ne kace kana sona wallahi Umma ce take shirya komi dan Allah kayafemin " sosai DON yasake rungumo ta cikin jikinshi

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters😘
[18/07 4:04 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 63 to 64 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin sanyin murya DON yace

" Ina sonki Seeyama taya zan'ki yar uwata kuma matata " wani irin farin ciki Seeyama taji wanda raban dataji irin shi ta manta lokacin tareda gawar Jabir suka taho cikin mamaki Ammi da Umma suke kallon Seeyama saurin dakewa sukayi suka shiga nuna farincikin kamar da gaske zama DON yayi cikin jimami yace

" munsamu nasarar d'akko Seeyama amma anyi rashin sa'a Jabir yarasa ranshi ayanzu haka gawar shi tana parlour 'kasa "

Wata irin fad'uwar gaba Umma taji cikin gigita da rud'ewa tashiga sambatu dako taga gawar suma tayi itako Ammi mamaki takeyi sosai mai yakai Jabir wajan doctor aka kira tashiga dubata allura akayi mata wadda zata samu bacci sosai

Washe gari har aka kai Jabir makwancin shi Umma bata tashiba sosai DON yasa akayima Su Alhaji Sambo mugun duka amma suna tabbatar ma DON basuda masaniya akan sace Seeyama sosai Don yake mamaki kanshi yashiga tambaya " to suwaye sukayi haka ? Kenan akwai wasu ma'kiyan yaban su Alhaji Sambo "

Sosai Umma take kuka tana kiran Jabir se'a lokacin wata irin nadama tazo mata ha'kuri akai bata amma takasa dena kukan

Dafata Seeyama tayi tace

" Umma kinga aykata sharri bashida amfani yanzu gashi kin rasa Jabir d'anda kikafi so fiye da kowa a duniya dan Allah Umma kugyara halinku "

wani irin kallo Ammi tayi mata tace

" ke Seeyama idan kikasake kikayimana su'butar baki senayi mugun sa'ba miki kibarmu muji da abinda yadamemu tashi kishiga ciki "

Cikin tsoro da fargaba Ameera tazauna kusada Abdulhakim shiko ko kallon ta baiyiba cikin sanyin murya tace

" Dear nayarda nakuma amince kaid'in mijine agareni kuma nayima Al'kawarin zanyima biyayya nayarda da wannan kalmar ta namiji baya kad'an ina sonka "

Tashi Abdul yayi ya kalleta yayi murmushi yace

" nikuma bana sonki zuwa nangaba kad'an zan auri yarinya 'karama dedeni ke kuma zansan abinyi akanki bayan ki haifamin yarona kingama renarmin shi "

Daga haka yatashi yanufi bedroom kallo Ameera tabishi dashi dafe kanta tayi tanajin wani irin zafi cikin zuciyar ta

Kanciyar DON Kausar ke zaune ahankali take magana

" dan Allah Sweety kacire damuwa cikin ranka kaduba kaga kukeyin nasara akan komi dasannu komi zai wuce "

Rungumota DON yayi yana sha'kar kamshin jikin ta awata irin murya yace

" Hayateey mutuwar Jabir ta'ki wucewa cikin zuciyata gashi ina gurin amma yarasa ranshi tayazan manta "

Sosai Kausar take lallashin shi har seda taga ya seseta zuciyar shi rungume ta yayi yajuyar da'ita yana shirin hayewa samanta tayi saurin cewa

" kayi ha'kuri Sweety am kamanta yau a gurin Seeyama kake dan Allah karmu shiga cikin hak'kin ta "

Jin haka yasa shi tashi zama yayi bakin bed d'in sannan yace

" kinyi gaskiya Hayateey nagodema Allah dayabani ke matsayin mata mai neman nasamu aljanna sumbatar kumatunta yayi sannan yayi mata sallama yafita bedroom d'in shi yanufa kiran wayar Seeyama yayi cikin zolaya yace

" haba baby tund'azu ke nake jirafa kokin manta yau kece wadda hak'kina yake kanta ? ina bu'katar ganinki cikin bedroom d'ina "

Wani irin farin ciki Seeyama taji har cikin zuciyar ta da duk wani sassa najikinta shiri tayi namusamman tanufi bedroom d'in DON amma tanajin kunyar DON dukda har yanzu baice mata komiba akan 'karyar cikin da sukayi mai gashi yanunamata babukomi tana shiga cikin bedroom d'in DON yatashi yarungumota har zuwa kan bed du'kowa yayi dede kunnan ta yace

" ki tayani addu'a Allah yabani ikon baki baby yau kinga se zuciyar ki tadena kuka "

Cikin wani yanayi Seeyama tabud'e baki zatayi maga DON yasakar mata murmushi yahad'e bakinsu guri d'aya a wannan daran tabbas Seeyama ta tabbatar da DON yana son ta amma tasan bazai ta'ba sonta kamar yadda yakeson Kausar ba

Kwanan su Alhaji Sambo 3 aka shiga kotu angabatar da 'kwararan hujjoji kuma sun amsa lefinsu anyanke musu hukuncin kisa tahanyar rataya sannan kotu ta tabbatar dacewa Abdulhakim bad'an Alhaji Sambo bane d'an Alhaji Isma'il ne sosai su DON sukayi farinciki Momy har kuka sedatayi

Washegarin addu'ar 7 Jabir Ammi tanufi Part d'in Kausar hannun ta ri'ke da Cup d'in fura mai d'auke da guba zaune tasamu Kausar akan cushion zama tayi kusada ita cikin kunya Kausar tashiga gaidata bayan sungama gaisawa tami'ka mata wannan cup d'in tace

" 'yata ga fura nadama miki mai sanyi nasan zaki bu'kaceta " amsa Kausar tayi tanayimata godiya sosai seda taga tasha sannan tatashi tayi saurin fita "

Tana shiga cikin part d'in Seeyama taganta ri'keda d'ayan Cup d'in furar dariya Ammi tayi tace " My Seeyama furar tayi dad'i ko "

Murmushi Seeyama tayi tace

" sosai makuwa Ammi ay wadda kika ajiye a kitchen na d'akko nakai miki nawa dan nasan wannan setafi dad'i tundaki ka kai tahhhh....... "

Yadda Cup d'in tayi sabida wani irin ciwo da cikinta yashigayi ihu Ammi tasaki cikin gigita take fad'in

" haba Seeyama nashiga uku wannan dakika d'akko akwai guba aciki haba........ ". Ganin Seeyama tafad'o daga kan cushion d'in yasa Ammi sake sakin wani ihun


Daga Al'kalamin ✍🏻


NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine please

Love u all sisters 😘
[20/07 3:03 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌸 NOORUL HAYAT 🌸 WRITERS ASSOCIATIONS

🌹Expressions and heed Searching Sweet Story Novels writers 🌹
>>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
We are together all fans 🀝🏻πŸ₯°

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

My Novels
1 NAYI RAYUWA DAKE
2 SANADIN ACCIDENT
2019
3 SAKAYYAR CUTA
4 RUFAFFIYAR ZUCIYA
typing...... ✍🏻

HAYATUL MAHAYAT
Coming soon
After RUFAFFIYAR ZUCIYA in sha Allah

πŸ…Ώ { 65 to 66 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Jin ihun Ammi yasa DON 'karasa shigowa cikin sauri dama yana gaf dashiga cikin parlour ganin yadda Seeyama take kwance tana ri'ke da cikin ta yasa DON saurin 'karasawa cikin sauri

Rungumo ta yayi cikin gigita yashiga tambayar ta

" maiyasameki ? Baby please kigayamin " saurin ciro wayar shi yayi daga aljihun yakira driver cewa yayi maza yatada mota gashi nan fitowa yun 'kurawa yayi zai d'auketa cikin 'karfin hali tad'aga hannuwanta duka biyu ta d'aurasu kan fuskar shi gefe da gefe cikin wahalalliyar muryar tace

" baby karka kaini Hospital nasan bazan rayuba nasha guba batare danasan gubar bace baby karkayi ba'kin ciki ko yanzu naci ribar zamada kai tunda kasoni kuma kacika umarnin Abba baby zanbar ku dama Kausar itakad'e tadace data zauna dakai

Nasoka so mai tsanani cikin rayuwata kumagashi zanmutu dason naka amma ina maifarin ciki tunda hak'kina yarataya a wuyan wasu naso haifamaka d'ah daga gareni ashe hakan bazai samuba ina matu'kar sonka dan Allah kobayan namutu karka had'a Kausar dawata ita kad'ai yadace kazauna da ita

Zuwa nan gaba idan Aunty Kausar tahaifi d'iya mace please baby kasamata sunan Seeyama dan karka manta dani dan Allah baby inayi muku fatan alhairi du.......... "

Wasu hawaye DON yaji sunfara sakkowa daga cikin idanun shi saurin d'aukar ta yayi yana fad'in

" bazaki mutuba Baby suwaye suka baki guba dan Allah kisanar dani ? karki mutu wallahi ina sonki kuma ke wasiyyar mahaifina ce karki tafi Seeyama "

Dahaka suka isa mota yana shiga drive yafigeta aguje izuwa wannan lokacin Seeyama takasa magana se kallon fuskar DON kawai takeyi fuskarta d'auke da murmushi aguje Ammi tafito itada Umma amma kafin su iso tuni motar su DON tayi gaba cikin sauri sukaba wani driver umarnin tada mota suka shiga yabi bayan motar su DON

Suna isa Asibiti akayi gaggawar shiga da ita amma 'kinyarda tayi DON yatsaya awaje ri'kemishi hannu tayi kam cikin raunanniyar murya tace

" bazan iya sakin hannun kaba har se lokacin da numfashina yabar jikina nagayama mutuwa zanyi zanso yakasance ina kallon fuskar ka ina murmushi lokacin da numfashina zai d'auke "

Sake ri'ke hannun ta DON yayi ahaka doctor sukafara dubata amma kafin sugama aykinsu tuni Seeyama tace ga garinkunan dafashi doctor yayi yace

" DON sede ha'kuri Allah yayi mata rasuwa "

Wata irin razana DON yayi girgiza ta yashigayi yana kiran sunanta amma ina babu Seeyama a sosai DON yarud'e basu Ammi umarnin shiga akayi cikin kuka Ammi tayi kan Seeyama afusace DON yace

" karku ta'bamin gawar mata nasan kune kuka kashemin ita Umma zamanki gurin Seeyama babu abinda ya'affanar zai tashin hankali da damuwa kinhanani zamada Seeyama cikin aminci da soyayya ke kuma Ammi kinzo kin'kara rikita komi nasha alwashin duk wanda yake da hannu akan mutuwar matata shima sena rabashi da duniya "

Daga haka DON yafita mota yasa aka juya dan d'aukar gawar Seeyama wani irin kuka Ammi keyi tanakiran Seeyama hakama Umma amma ina Seeyama babu halin amsawa da'kyar su Ammi suka saki gawar Seeyama aka nufo gida da ita cikin motama Ammi 'kan'kame Umma tayi tana fad'in

" Saratu nashiga uku nakashe Seeyama da hannuna yarinyar danafi so duk cikin yarana waiyo Allah tabbas nima mutuwa zanyi Saratu "

Jin irin 'barin bakin da Ammi keyi yasa Umma rufemata baki tana lallashin ta haka suka isa gida ganin yadda suketa ihu yasa DON kulle cikin bedroom d'in dasuke dan shikam ayanzu yatsani koda ganin

Please Login or Register in order to submit comment