Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Affan keyima duk wata mace ko abincin da mace tayi bayaci kanagani jiya sede yasha fruit fa dukda yana ganin darajar Momy amma bayacin abincin ta sabida kasancewar ta mace kuma Dady abaya ko hutu mukazo sedefa Momy tatura Kausar Abuja gurin kaka sabida muguwar tsanarda Affan ke nuna mata afili amma wai yanzu itace matar shi sannan kuma hadda wata "

Dan murmushi Barrister yayi ya kalli dan nashi yace

" yaro kenan dakai da mahaifiyar ka bazaku fahimci dalilinaba ayanzu amma da sannu zakugane hakan shine dede Affan tamkar kai yake agareni yazama dole nasamamai hanyar da farincikin shi zai dawo mahaifin shi yayimin halaccin dabazan mantaba koda Affan zai wahalar da Kausar bazan ta'ba zargin shiba nasan zai bari wata rana kuma hakan zaisa yagane baduka mata halinsu yake d'ayaba idan nabarshi babu aure bazai ta'ba dena tsanar mace ba "

Sanyi jikin Ashiraf yayi cikin sanyin murya yace

" hakane Dady amma bana tunanin yadda Affan yayima mace muguwar tsana zai so wata 'ya mace anan gaba ni kam nasan Kausar zata d'and'ani ba'kin ciki mai tarin yawa a rayuwar ta rayuwar mace da Affan hmmm "

Cigaba da tafiya barrister yayi sannan yace

" maiyasa ? 'Kanwarka kad'ai kake tunani koka manta gobe zamuje amso auran wata ? maiyasa ita baka tausayin ta se Kausar wannan badede bane nuna sonkai kacire wannan tunanin daga ranka sannan karka sake ka kalli rayuwar cikin gidan DON tareda iyalinshi kaide kazama maibashi shawara dajan hankalin shi cikin hikima bada matsawaba "

Jinjina kai Ashiraf yayi sannan suka 'karasa ciki se wajan 9 sannan Affan yafito yanufi cikin gidan kai tsaye bedroom d'in su yanufa sabida wani irin bacci daya kama idanun shi yana shiga yahau saman bed ya kwanta yaja blanket yarufa babu jimawa bacci mai nauyi yayi gaba dashi shiko Ashiraf yana canyana motsa jiki shiga cikin bedroom d'in barrister yayi sabida yaga shigar shi ganin yana bacci yasa yasauke wata irin ajiyar zuciya kallon fuskarshi yayi natsawan wasu da''ki'ku yanayin nazarin halin da yake ciki sannan ya'isa gareshi gyaramai blanket d'in yayi sannan yashafi sumar shi sannan yajuya yafita ha'ki'ka yanayima Affan wani irin so namusamman

Sudan

" Haba Alhaji tayaya zaka ma'kale akan dole se Seeyama ta auri d'an yayanka baci har yanzu babu wani labarinsu kusan shekaru nawa yanzu sabida koda kaje Nigeria ansanar dakai mutuwar Alhaji Isma'il bayan wasu shekaru kakoma amma matarshi taci mutuncin ka shi d'an nashi kanada masaniyar mahaifin nashi yasanar dashi wannan al'kawarin kuma idan yasanar dashi zai yadda balle yanzu yaga mahaifin nashi bashida rai haba Alhaji yarinyar nan nace tasamu wanda takeso to kabarta mana "


Cikin daga murya yace

" ke bulkisu kishaga hankalin ki dani akan wannan lamarin wallahi zanyi mugun 'batamiki rai nasan yaya bazai yadda wasiyyar mahaifiyar muba haka shima dan nashi bazai bar wasiyyar mahaifin shiba zezo insha Allah kekuma Seeyama koda zaki mutu sekin auri Affan barima kiji duk ranar dayazo to wannan ranar itace ranar auran ki "

Cikin zafin rai yafita daga babban parlour kuka Seeyama tasaki mai tsuma zuciya kwantar da kanta tayi kan cinyar mahaifiyar ta cikin kuka tace

" Ammi dan Allah kiceci rayuwata ni DON nikeso idan bashiba bazan iya rayuwa dawani namiji ba idan ba DON ba banason Affan d'in da Abba keson had'ani dashi dan Allah Ammi kiceceni "

Dan had'a rai Ammi tayi tace

" gaskiya Seeyama nagaji da wannan zancen naki ni namafara tunanin anya ba gamo kikayiba nace kituromin shi DON din amma kince bakisan indama zakiganshi to yakikeson muyi inamai baki shawara kituro DON nikuma zansan yadda zanyi da mahaifin naki yafahimta "

Kuka Seeyama tasake saki tace

" Ammi to dan Allah kibari nakoma Saudiyya nasamo cikakken 'kasarda DON d'inayake "

Cikin 'bacin rai Ammi tace

" Amma ke Seeyama kinfara haukako ashema abin naki duk shashanci ne to bari kiji nima nagoyi bayan mahaifin ki Allah yakawo Affan 'kasar na "

Tashi Ammi tayi tabata guri cikin damuwa da 'bacin rai Seeyama tami'ke cikin bedroom d'inta tashiga kwanciya tayi saman d'an madedecin bed d'inta lumashe idanunta tayi tashiga cikin tunanin daya zamaimata abokin rayuwa ayanzu surar DON tashiga hangowa cikin idanunta hannu tasa tashafi kumatunta tuno marinda yayimata tashigayi wani irin sassanyan murmushi tashigayi afili tace

" gaskiya bazan iya auran wani idan ba DON ba "

Cikin damuwa Amina ke kallon Kausar sannan tasauke wata irin ajiyar zuciya ta'karasa gurinta zama tayi kusada ita cikin shigar lallashi tace

" haba Kausar yakamata kidena wannan tunanin ki rungumi kaddara Allah shi kad'e yasan dalilin faruwar haka kinji Aminiya ta wannan damuwar zata'iya haddasa miki ciwo "

Wasu zafafan hawaye suka gangaro daga idanun Kausar cikin sanyin murya tace

" Amina inatunanin ranar da iyayena zasusan mummunan abinda yafarudani wane irin ba'kin ciki zasushiga sannan wane namijine zai yarda cutar dani akayi wajan rabani da budurcina Amina "

Hawaye masu zafi sukashiga gangarowa daga idanun Kausar itama Amina kukan tashigayi hannunta Amina takamo tace

" Kausar ni inaganin asanar dasu dady wannan lamarin kinga su zasusan abinyi kuma tunda akwai aure a tsakaninku da yaya DON kuma nasan bazaiso kitozarta ba kin......... "

Cikin sauri Kausar tadakatar da ita tace

" kirufama rayuwata asiri bazan iya yadda na auri yaya DON ba kinsan kuwa yadda yatsani mace hmmm Amina wannan sirrinane banason kowa yasani yazauna a tsakanin nidake bazan iya yadda anemi kaidaniba sabida 'kaddara tafad'amin a a Amina "

Jinjina kai Amina tayi sannan tami'kama Kausar wani kyakkyawan zobe tace

" Amshi wannan zoban Kausar nasan shine zaifitardake cikin wannan damuwar wata rana "

Cikin rashin fahimta Kausar ta amsa sannan tace

" bangane mai kike nufiba ? "

Murya a sanyaye Amina tace

" lokacin da kika dawo ranarda wannan mummunan abun yafaru naganshi cikin gashin kanki inada tabbacin wannan zoban na wannan mutuminne daya aykatamiki wannan zalincin "

Kallon zoban Kausar tashigayi cikin zuciyar ta tace

" Amma dagani wannan zoban yanada matu'kar tsada stones d'in jikin shima aynihin daymonne ne "

Wani irin tsanar zoban Kausar taji amma yazama dole tari'keshi kozai zamar mata hujja anan gaba maganar Amina tadawo da'ita cikin duniyar tunanin datake

" daganin wannan zoban zakasan wanda yayi wannan abun d'an gidan manyane sabida tsananin tsadar shi "

Kallon ta kawai Kausar tayi batare datace komiba cikin sauri wata daga cikin 'kawayen Ameera ta'isa gunta tace

" Ameera ke kinanan zaune ana shirin shirya wani mugun abu "

Cikin sauri Ameera tace

" kamarya ? "

Cigaba tayi dacewa

" yanzu naji Kausar da Amina sunayin magana wai ashe DON ba mahaifin su d'ayaba da Kausar akwai aure tsakaninsu kin........ "

Cikin sauri Ameera tami'ke tace

" tab bazai ta'ba yiwuwa ba ina duniya dan ya auri Kausar ina duk hanyar dazanbi yasan Kausar tarasa budurcin ta senayi zansa yayi mata muguwar tsana tayadda bazai ta'ba shi'awar auran taba "

Afurgice Affan yatashi gawata irin zufa dake keto mushi dafe kunnuwanshi yayi yana sauke wani irin wahalallan numfashi cikin zafin rai yace

" wannan wane irin jarabace ? tayaya haba nimafa ba'asonraina nayimiki hakan ba kidena damuna haka kibarni naji da ba'kincikin dakika'karasa zuciyata aciki "

Hannun shi yakalla cikin muguwar damuwa yace

" a sanadinki narasa zoban mahaifina maidaraja da matu'kar mahimmanci amma kin hana zuciyata da kunnuwana sukuni duk inda mace take setazajamaka matsala ni Affan wallahi natsani mace duk wani ba'kinciki mace i......... "

" kaidawa kake magana ne DON ? "

Cewar Ashiraf kallon shi kawai Affan yayi yatashi yashiga toilet girgiza kai Ashiraf yayi yafita

Yau takama safiyar Sunday Barrister da Affan da Ashiraf harda Momy sungama shirinsu tsaf natafiya Sudan zuciyar Affan duk babu dad'i jiyake kamar zuciyar shi zata 'kone sabida mugun zafin datakeyi kamar karyaje to Amma babu yadda zaiyi yabar umarnin mahaifin shi

Kodasuka isa Sudan basusha wahalar gane idan Alhaji Umar ba sabida fitaccene sannan sunsamu cikakken address d'in cikin mihimman Document dinda Alhaji Isma'il yabarma Affan suna shiga sukasa maigadi yayi musu iso gurin mai gidan

Adede lokacin Alhaji Umar yana zaune a cikin babban parlour shi gefan shi hajjaju bulkisu se 'kanwar Seeyama dake zaune 'kasan carpet daga can gefe kuwa yayan Seeyama ne Ayman yanata faman yin game cikin phone d'inshi cikin hanzari Seeyama tafito gurin yayan ta tanufa jin abinda mai gadi yake fad'ima Abban nasu yasa Seeyama saurin juyowa sabida idan taji ance anayin sallama da Abbansu gabanta mugun fad'uwa yakeyi sabida gudin zuwan yaron wan Abban su cikin hanzari Alhaji Umar yafita

Itako Seeyama zuwatayi bakin 'karfar parlour tanajin wani irin bugun zuciya Abba nafita idanun shi suka sauka kan Affan tsananin kamar shi da mahaifin shi yasa Alhaji Umar ganeshi shima Affan gani yayi tamkar mahaifin shine cikin in'ina Alhaji Umar yace

" Affan kaine ? Alhamdulilah damanasan zakazo d'an albarka "

Cikin sauri danuna tsananin farinciki Alhaji Umar yabasu umarnin shiga ciki hannun shi nari'ke dana Affan kamar wani zai 'kwacemai shi tun cikin harabar gidan Alhaji Umar yake 'kwalama Hajiya kira yana fad'in

" Hajiya bulkisu yauga d'ana Affan Allah yakawo shi "

Jin hakan yasa Seeyama juyawa dagudu cikin bedroom d'in ta tana shiga tasaki kuka mai sauti


Daga Al'kalamin ✍🏻
NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments plsssssss
[11/06 10:04 am] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE 🀝🏻😍🌹

πŸ…Ώ { 15 to 16 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin farinciki Hajiya bulkisu ta tarbesu suka zauna shiko Alhaji Umar yakasa rube bakin shi sabida tsabar murna cikin girmamawa suka shiga gaisawa cikin lokaci kad'an aka kawo musu abinci da abubuwan motsa baki

Sun dad'e suna tahira tsakanin barrister da Alhaji Umar Affan da Ashiraf da Ayman suna gefe d'aya suma hira sukeyi amma banda Affan wayar shi kawai yake latsawa itako Hajiya bulkisu jan Momy tayi suka nufi d'akinta ganin momy ta tada sallah yasa Hajiya bulkisu fita kai tsaye bedroom d'in Seeyama tanufa kwance tasameta sefaman sauke ajiyar zuciya takeyi alamar tasha kuka girgiza kai Hajiya bulkisu tayi sannan tace

" amma kekam Seeyama bansan irinkiba wato sokike kijamana abin magana ko ? ace kinajin ba'ki amma ki'ki fitowa gaidasu to wallahi idan mahaifin ki yatasaki yanafad'a babu ruwana inamai Umar tarki dakiyi maza kije ki gaidasu "

Jin Ammi tafita yasa Seeyama sake fashewa dakuka sannan tatashi toilet tashiga tayo wanka sannan tayi sallah simple makeup tayi tafesa turarukanta masu dad'in kamshi sannan tafito

Koda tafita kowa yana wajan dinner amma banda Affan cikin ladabi tashiga gaidasu kanta na 'kasa murmushi Momy tayi tace

" zonan 'yata masha Allah "

Cikin ladabi Seeyama tanufi gurin Momy amma cikin zuciyarta jitake kamar tace bazataba shiko Ashiraf kallonta yakeyi yanason tuno inda yata'ba ganin wannan fuskar amma yakasa tunowa cikin karamci Momy tarungumo Seeyama tana sakamata albarka maganar Ammi tasa Seeyama jin muguwar damuwa

" ke Seeyama jeki had'ama Affan abinci kikaimai yana part d'in yayanki "

Cikin rashin kuzari tami'ke tanufi kitchen cikin zuciyar ta tana fad'in

" amma wannan mugun d'an isane kowa yana nan amma shi yawani ware kanshi hmmm "

Cikin zolaya Alhaji Umar yace

" kai Ashiraf babu ruwanka amma shi d'an'uwanka yakasa sakin jikinshi "

Murmushi Ashiraf yayi sannan yace

" ayshi Affan hakayake bayason hayaniyane Abba ko agida hakayake "

Cigaba sukayi dacin abinci cikin 'bacin rai Seeyama ke had'a abincin tsayin lokaci seda Ammi tasakeyin magana sannan tafito cikin sanyin jiki tanufi part d'in Ayman kodata isa bakin door d'in seda tad'an jima sannan tashiga ko sallama babu

Zaune Affan yake kan d'aya dagacikin cushion d'in madaidaicin parlour kanshi da kafad'unshi kawai Seeyama ke iya hangowa sabida yajuya bayanshi jin 'karar bud'ewar 'kofar yasa Affan jin 'bacinrai dan yasan tabbas itace Seeyama cikin kakkausar muryar shi yace

" ko waye yakoma yayi sallama kokuma yakoma "

Tsuki Seeyama tayi ta'idasa shiga ciki batare datayi sallamar ba har gabanshi ta'isa amma kanta adu'ke ta'aje tiran abincin sannan tace

" dan Allah bawan Allah kataimakeni kajanye maganar aure na inada wanda nikeso dan Allah karka cutar da rayuwa ta "

Wata irin sassanyar ajiyar zuciya Affan yasauke tsayin lokaci danhar tacire rai dazaiyi magana sannan yace

" Alhamdulilah kinrufama kanki asiri nima bana bu'katar auranki dama danna cika umarnin mahaifinane yasanazo inaso kisanar musu bakya sona ni DON bazan ta'ba son wata 'ya mace ba "

Jinya ambaci wannan sunan yasa Seeyama saurin d'agowa cikin sauri tami'ke nunashi tayi tace

" kai kai kaine ? "

wani irin murmushi Seeyama tasaki cikin rawarjiki tanufeshi babu zato yaji tarungume shi dede kunnan shi tace

" kai nakejira My DON kai..... "

Wani irin hankad'ata yayi harseda tafad'i azafafe yace

" wannan wane irin wawancine kiyi gaggawar shiga hankalin ki idan bahakaba senayi mugun wula'kantaki kuma kiyi gaggawar sanar d'azu bakison aure na idan bahakaba to wallahi zakiyi nadama "

Cikin sauri Seeyama tami'ke tace

" bazan ta'ba janye maganar auran kaba koda idan anyi auran zaka rabani da rayuwa ta ne danke nace bazan auri Affan ba to ashe Affan shine DON d'ina gaskiya wannan turaran naka ina matu'kar sonshi kamar karnabar saman 'kirjin ka my Husband "

Cikin mugun ba'kin ciki DON yayo kanta cikin sauri tajuya tafita tanajin wani matsanancin farinciki komawa yayi yazauna yadafe kanshi yanajin zafi cikin zuciyar shi

Yanayin da Seeyama tashiga parlour yasa Ammi yin mamaki amma setabar abin cikin ranta misalin 09:30 Ashiraf yaja hannun Ayman sukafita waje cikin mamaki Ayman yace

" Ashiraf inakake son muje ayanzu ? "

d'an shiru Ashiraf yayi yana nazarin abincewa sannan yace

" wajan mai tea zakarakani "

Kallon shi Ayman yayi cikin mamaki sannan yace

" amma de idan tea kake son sha aybasemunje kan titiba se asa Seeyama tahad'amaka ko Zarah mazata'iya "

Girgiza kai Ashiraf yayi yace

" kaide muje kawai "

Badan Ayman yasoba haka yarakashi tea yasa akahad'a mai kauri da kwai da breed sannan sukataho kasa ha'kuri Ayman yayi yace

" dama baka 'koshiba kabarcin abincin ? "

Murmushi Ashiraf yayi sannan yace

" Ayman banizanciba nasan d'an uwana bai cikomiba ayanzu koda ankaimai abinci nasan baicishiba "

Cikin mamaki Ayman yabishi da kallo kawai cikin zuciyar shi yana tunanin akwai abindake damun Affan koda sukashiga baya parlour kai tsaye suka nuficiki adede lokacin yafito daga toilet dagani wanka yayi jikin shi sanye da farar jallabiya

Fita Ayman yayi yakawoma Ashiraf flet da Cup yafita abincin da akakawo ma Affan Ayman yafita dashi part d'in su Ammi yakaishi kitchen yadawo jin maganar da Ashiraf keyima Affan yasa Ayman juyawa sabida bayason jin abunda baishafeshiba

" haba DON kadaure ka'aje komi har mubar 'kasarnan kanaganin yadda Abba yanuna yadda yake 'kaunarka afili bazaiso ganin wannan yanayin nakaba kadingacin abincin da akakawo maka ko....... "

" bazan ta'ba cin abincin wata mace ba Ashiraf kuma bazan iyacire komi daga rainaba lallene nayi maganin Seeyama sabida naga kanta yanayimata rawa 'kila setasake shan marina a Sudan kamar yadda tasha a Saudiyya karona 2 "

Jin wannan furucin yasa Ashiraf tuna Seeyama a hankalin Affan keshan tea d'in Ayman da Ashiraf se janshi da hira sukeyi amma ya'ki kulasu

Ammi kam takasa ha'kuri tashi tayi tanufi bedroom d'in Seeyama jin alamar bud'e 'kofa yasa Seeyama saurin waigowa ganin Ammi yasa Seeyama saurin nufota cikin tsantsar farinciki tarungume ta tace

" Ammi Affan shine DON d'ina Ammi shine nake matu'kar so nake burin yazama ubana 'ya'yana "

'Dan tureta Ammi tayi tace

" tafican dawannan rashinkunyar taki amma dase wahalar dakanki kike "

Cikin zuciyar Ammi kuwa farinciki ne sosai takeji aranta zamatayi tafarayimata nasiha mairatsa zuciya sannan tafita washegari Seeyama dakanta tashiga kitchen dan had'ama DON breakfast kallon takwai Ammi keyi Zarah ma abin mamaki yabata bayan tagama takoma bedroom d'in ta wanka tayi sannan tazo gaban mirror tsayin lokaci tana makeup wasu riga da sikat nawata kyakkyawar atamfa tasha d'inkin yayi matu'kar amshar jikinta

Cikin wani irin taku tafito sezuba kamshi takeyi kallon ta Ayman yayi yace

" Seeyama wannan kwalliya haka gaskiya sirikinnan nawa yanada sa'a "

Saurin du'kar dakanta tayi sabida su Abba duk suna gurin gaishesu tayi shima Abba farincikin hakan yayi sosai yace

" Seeyama kije kikaima Affan breakfast yanzu yagaidamu yafita shibazai iyazama cikinmu yaci abinciba mijin naki bayason hayaniya "

Jin haka yasa Seeyama nufar hanyar kitchen dan dama abindatake sonji kenan cikin wata irin tafiya ta'isa part d'in awannan lokacin bakinta d'auke da sallama yanzuma zaune tasameshi yana kallon News hannun shi ri'ke da Cup yanashan tea har gabanshi ta'aje tiran breakfast d'in cikin wata irin murya tace

" barka da safiya my baby "

Cigaba dashan tea d'in shi yayi kamarma baijitaba murmushi Seeyama tayi tace

" baby gaskiya kayi matu'kar kyau wannan saddar tayima kyau sosai kamar ranar angoncinmu "

Ganin bashida niyyar koda kallonta yasa tazauna kusadashi hannunta tad'aura saman 'kafad'arshi cikin 'bacin rai yawatsa mata sauran tea d'in dake hannun shi sannan yasauke mata wani mugun mari har 2 baiko tsaya sake kallon taba yafita daga part d'in kai tsaye part d'in su Abba yanufa

Wani irin mugun ba'kinciki Seeyama keji cikin 'bacinrai tace

" ni kayiwa haka DON nasha alwashin sekabani ha'kuri akan wannan abun aure nidakai babu bashi senasa kasan mace ba abar wula'kantawa bace "

Bin bayanshi tayi Affan nashiga yasamu dady da Abba cikin ladabi yace

" dady kugafarceni zankoma yau sabida zangabatar dawani ayki nagaggawa "

Murmushi dady yayi yace

" haba Son yakamata kabari agama wannan hidimar bikin ko ? "

Cikin rashin damuwa Abba yace

" a'a Alhaji Ibrahim kabarshi yatafi aykinshi yanada matu'kar mihimmanci zamuyi komi koda bayanan sekutafimai da matar shi babu komi Affan katafi Allah yamaka albarka bayan wannan bikin zamuzo ganin mahallinka nida Amminku da 'yan'uwanka "

Tashi Affan yayi yamusu sallama dede 'kofar fita yaci karo da Seeyama wani irin kallo yayimata wanda yasa dole seda ta kauda idanunta bin bayanshitayi tasha gabanshi cikin raunanniyar murya tace

" baby karka tafikabarni dan Allah idan bakason inazuwa inda kakene bazan kuma zuwaba "

Wani irin kallo yayimata har yayigana seya tsaya yace

" kitaimaki kanki kicemusu bakison aurena dan idan kikabari ba'kinciki da damuwa sune zasuzama abokan rayuwar ki "

Yanagama fad'ar haka yanifi part d'in Ayman dan had'a kayanshi cikin kuka Seeyama tajuya tana shiga tanufi bedroom d'in ta kan bed tafad'a tasaki kuka amma cikin ranta tasha alwashin setasa DON yasota somai tsanani

Har airport su dady suka raka Affan kiran Affan dady yayi yace

" DON nasan babu wani aykAdazakayi amma kace haka nasan sabida bakason wannan auranne to amma yazakayi shikenan zamutahoma da matarka idan kaje kaje kagano matarka kotana bu'katar wani abu "

Jinjina kai kawai yayi zuciyar shi cikeda kunci yajuya yashiga jirgi cikin mamaki Ayman yananata zancan

" Matarshi ? kenan Affan yanada wata matar amma shine babu wanda yasanar shiyasa ya'ki sakinjikin shi da 'kanwata lalle hakan bazai ta'ba yiyiwaba "

Suna isa Ayman yashiga cikin bedroom d'in Ammi zaune yasameta cikin takaici yace

" Ammi wallahi bazamu yardaba ashe Affan yanada mata ? " shin..... "

Cikin sauri Ammi tami'ke azafafe tace

" mata ? lalle to 'yata bazata zaunada kishiyaba sede afasa wannan auran ko yasaki waccan matar tashi barinasamu Abban naku inah........ "

" karku sake wannan auran babu fashi kuma bazai rabuda matarshiba akan tamu 'yar sannan karku sake kubari kowa yasan wannan maganar ciki hadda Seeyama "

Cikin 'bacin rai Alhaji Umar yafita azafafe Ammi tace

" lalle wallahi bazan ta'ba yardaba idan kunsan wata aybakusan wataba "

Nigeria yau kwanaki 3 da dawowar DON amma baije gurin Kausar ba tuna maganar Dady yasa yashirya yanufi skul d'in nasu cikin wani had'add'an yadi mai kyau da tsada kallon d'aya zakayimai kace masha Allah

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A Aji ♣β™₯β™ 

Love u all sisters comments
Shere
[13/06 11:43 am] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE 🀝🏻😍🌹

πŸ…Ώ { 19 to 20 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Kuka sosai Kausar keyi dandanan wani irin ciwon kai yakamata cikin kuka tace

" innalinlahi wa'inna ilaihirraju'u yanzu wannanne mijina marar imani da tausayi ? yazanyi a ranar dayasan banida budurci tayaya zan'iya wanke kaina awajan wanda babu tausayin mace a zuciyar shi ko kad'an Allah kaceceni "

Sake fashewa tayi da kuka had'ida dafe kanta shiko DON wurin wani ayki dayabada yawuce tunkafin yayi parking zugar ma'aykatan gurin sukanufoshi bud'e murfin motar yayi yaziro 'kafarshi batare dayafitoba kallon su yayi tsayin lokaci sannan yace

" ina fatan kunjuya ginin kamar yadda nace ? "

'Daya dagaciki yace

" rankashi dade anjuya kuma in sha Allah nanda 3 weeks zamu kammala ginin zaka iyashiga kagani "

Maida 'kafarshi ciki DON yayi yace

" banida lokacin tsayawa gani yanzu amma idan naga baiyiba to zaku kuma rusheshi dan haka seku kiyaye "

Rufe motar shi yayi yafigeta kallon bayan motar sukayi d'aya daga ciki yace

" yaro amma Allah yabashi mugun kud'i kaga wannan gidan mukammu masuyinshi munsan yashihara "

Ganin tunkarowar jerin wasu motoci yasa sukayi shiru nesadasu sukayi parking Alhaji Sambo ne da abokanshi kaitsaye gurinsu suka nufo cikin yatsina fuska Alhaji Sambo yace

" waye yabaku kwangilar wannan ginin sannan waye mamallakin wannan katafaran gidan "

'Daya daga cikinsu wanda shine oga yace

" Alhaji gaskiya bamusan waye mai wannan gidan ba kuma musede akiramu tawaya abamu umarni "

Tsawa Alhaji bala yayimai yace

" wanda yabarnan yanzufa waye shi ? maiyasa baifito daga motar ba ? karku renamana wayo mana duk maihawa waccan dan'kareriyar motar shine mai wannan gidan karku 'batamana lokaci ku'batama kanku waye mai wannan ginin dakukeyi ? "

Cikin 'bacin rai wani yace

" haba Alhaji gaskiya muwannan tuhumar ta'ishemu haka kudakuke manyan 'yan kwangila kunkasa sanin mai wannan gidan semu dan Allah kuzomuje kan aykinmu "

Juyawa sukayi suduka sukabarsu anan tsaye cikin 'bacinrai Alhaji Hamisu yace

" barsu semun gano wanda akaba kwangilar wannan katafaran ginin dan wallahi sede ayi 50 50 komu tasa 'keyarshi zuwa kiyama bashikad'e zeci wannan arzikinba "

DON yana shiga yanufi cikin bedroom d'in da Kausar take haryanzu shasshekar kuka takeyi babu alamar damuwa cikin ranshin yace

" Kifito kikwashi kayanki gasunan a parlour "

Daganan besakecewa komiba yajuya yafita kai tsaye cikin bedroom d'in shi yashiga toilet yashiga yayi wanka yasa kayan shan iska yafito parlour TV yakunna yafara kallon news gurin daya aje kayan Kausar yakalla ganin basu gurin yasashi girgiza kai

Please Login or Register in order to submit comment