Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

farinciki amma inajin tsoran ranarda zamu sha'ku yanemi hak'kin shi aguna tayaya zan'iya fahimar dashi idan yasan banida abindazanyi tun'kaho dashi adaran farkon tarayyata dashi Amina yayazanyi "

Wasu hawaye masuzafi sukashiga gangarowa daga idanun ta cikin tausayin Aminiyar tata Amina tace

" karda wannan yasa kikasa janyo hankalin DON zuwa kanki mudage da addu'a in sha Allah kafin zuwan lokacin gaskiya zata bayyana idanma bata bayyana ba Allah zaisa yafahimceki karki sare Allah yasani cutarki akayi kuma bazaibari ki tozartaba mudage da Addu'a in sha Allah komi zaizo cikin sau'ki sannan kar kiga ba'ayi hidimar bikinkuba ki'ki bama mijinki kulawa wannan wani abune dayazama al'adarmu aure de yariga ya d'auru kuma kinzama halak agurinshi shima yazama halak agurinki kidage Kausar Allah yabaki irin namijin dako wace mace keso karki kula da yadda yanayinshi yake kinfini sanin halin yaya DON tare kuke tsayin wasu shekaru dan Allah kikula Aminiya ta ki'aje komi kulada mijin ki sannan kidinga jawo hankalin shi kan mahaifiyar shi baikamata yagujetaba dukda cewa ita takoreshi uwa uwace tafigaban wasa "

Murmushi Kausar tayi sabida taji dad'in wannan shawarwarin da Amina tabata shiko DON daganan office yawuce yana shiga yatadda wasu najiran shi seda yasha ruwan tea sannan yabada umarnin sushigo wani dattijone dawani matashin saurayi umarnin zama yabasu sannan yace yana sauraransu

cikin matu'kar damuwa wannan dattijon yace

" dan Allah yalla'bai kataimakemu wasune sukeson cinye mana dukiya sun siya company na amma sunhanani kud'in wata kwangila suka amsa zasuyi agurin suka matsamin sena siyar musu ganin idan bansiyarba zan'iya rasawa duka shine nasiyar musu amma shiru idan naje gurinsu basuma bari abarni nashiga dan Allah yalla'bai idan babu wannan company bamusan yazamuyiba "

Pen d'in hannunshi ya'aje saman paper dayake rubuta bayanan shi yace

" kasan sunayensu dagurin zaman su ? "

'Daga kai yayi yace

" Alhaji Sambo da Alhaji bala "

" Alhaji Sambo ? "

DON yasake maimaita sunan sallamar su yayi bayan sunbar number waya da address d'in su ajiyar zuciya yasauke yace

" dama ina jiran ranar da wani zai kawo mana 'karar Alhaji Sambo "

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine plasss
[16/06 4:51 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE 🀝🏻😍🌹

Assalama alaikum ina godiya agareku maitarin yawa masoya Allah yabar zumunci

πŸ…Ώ { 25 to 26 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Yau ne aka tahoda amaryar DON daga Sudan wato Seeyama cikin gidanshi na Kaduna babban gidane mai d'auke da part 2 kowane 'bangare kashiga sekaji kamar karka fito sabida tsaruwar shi da kayan more rayuwa dake cikin harabar gidan kanta abin kalloce kowane part yana d'auke da babban parlour se 4 bedroom daga ciki ma wani parlour ne madedeci mai d'auke da 2 bedroom se sama mai 1 bedroom da 'karamin parlour duk yadda zan maka tsarin wannan gidan yawuce nan

Cikin shagwa'ba Seeyama tace

" Umma wato 'kanwar mahaifiyar ta kalli yanzu har 8pm fa amma banga DON ba "


Ta'be baki Hajiya Saratu tayi tace

" ayko bazakiga DON ayau ba sabida ance wai yana wajan aykinshi bazai samuzuwaba se nan dawasu kwanaki sabida rashin darajar ki amma ace akawoma Amarya kowane irin aykine ay kad'auki hutun shi "

Wani irin ba'kin ciki Seeyama taji cikin fusata tace

" kenan nikad'e zanzauna idan kuka tafi gobe maiye nufin DON akaina to wallahi yadda yasani ba'kin ciki shima sena sakashi komin dad'ewa dole zaizo ay "

Dafata Hajiya Saratu tayi tace

" kwantar da hankalin ki 'yata ayni babu inda zani inanan kinga dama mijina yarasu yarana guda 2 nataho dasu girman gidan nan yayi yawan dazaki zauna ke d'aya dukda cewa waccan idan tazo d'a........ "

Katseta Seeyama tayi dafad'in

" wacece zatazo ? "

Cikin d'an daburcewa da nadamar su'butar bakin datasoyi tace

" a a wacce kuma kinga zancan zuciyata ne yafito fili kinsan mu yanzu ba'a rasamu da yawan tunani "

Kallo ta Seeyama tayi sannan tasake cewa

" amma gaskiya Umma zamanki anan baiyiba taya zaki zauna agidana kuma hadda yaranki gaskiya a 'a "

Salati Hajiya Saratu tasa had'ida ri'ke baki sannan tace

" amma bansan bakida tunaniba se yau amma nasan kinasane da d'inbin dukiyar da Affan kedashi ko ? kina tunanin wa'innan mari'kan nashi dan Allah suke zaune dashi ? to idan wani nakibaizo yazauna dakeba tosu zasusa nasu dukdan suci dukiya sannan kawo kunnanki kiji "

Cikin 'kasada muryar takeyi mata magana akunne kamar suna tare dawani dariya Seeyama tasaki hada shewa tace

" gaskiyane Umma nagane kiza'bi duk part d'in dayamiki acikin gidannan "

Cigaba da tattauna yadda zasugudanar da al'amuransu sukayi

Tofa

Cikin damuwa Momy tace

" gaskiya Alhaji zuciyata takasa natsuwa da wannan auran na Affan bana zargin Alhaji Umar amma matarshi banyarda da itaba idan basu cutar da Affan ba to zasu cutarmin da Kausar ita kanta Seeyama nalura batada kirki gaskiya karaba auran Kausar da Affan sabida nalura Hajiya bulkisu tanaganin kamar dan dukiyar Affan mukabashi auran Kausar sannan haryanzu ita Seeyama batasan Affan yanada wata matar ba "

Wani irin kallo yayi mata sannan yace

" duk wanda zaice dan dukiyar DON nabashi auran Kausar yaje yaitafad'a sannan duk wani mai nufin wani da sharri Allah baya bacci shine maikare wanda aka zalinta dan haka karki sake zuwamin da maganar raba auran DON da Kausar mutukaraba idan zakibi 'yarki da addu'a to kibita idan kuma zakitsaya tsegumi to kitayi "

Daga haka Barrister yafita yabar parlour kiran wayar DON yayi sukayi magana sannan yashiga motar shi yafita

Kimani kwanaki 6 kenan dakawo amarya Seeyama amma DON bai taka hanyar Kaduna ba cikin takunshi na isa DON yafito daga bedroom d'in shi cikin shirin fita office hannun shi ri'keda bag d'in system cikin sanyin jiki Kausar dake jiran fitowar shi tund'azu dan yanzu idan har yananan bata shiga bedroom d'in shi tun wannan ranar

Cikin girmamawa tace

" barka da fitowa yaya "

Gaba yayi har seda yakai bakin 'kofa yace

" da yaushe kike da lecture yau ? "

Cikin sanyin murya tace " 9 zuwa 11"

Jinjina kai yayi sannan yace

" yau zanzo daba'ki inaso kihad'a dinner kamarta mutun 6 akwai kud'i cikin bedroom d'in kid'auka kibawa tabawa tasiyo miki abubuwan da babu saura kiyimin shirmai "

Baijira maizatace ba ya'idasa fita murmushi tayi sannan tanufi bedroom d'in nashi DON yana isa office babu jimawa yafito yana kallon agogon hannun shi cikin sauri aka bud'emai mota yashiga kallon driver yayi yace

" yimaza nakusa makara wajan taron nan zaka kaini "

Daga haka baisake cewa komiba suna isa biyu daga cikin security d'in shi sukabi bayan shi yana shiga yadakatar dasu daga 'kofa taron manyan attajiraine masu jidakansu matasa da dattije ciki haddasu Alhaji Sambo kowoyabi DON da kallo sabida sunga ba'kuwar fuska acikin su kowa yatashi yagabatar da kanshi kamar yadda suka saba gaba'kinsu kallon DON sukayi sunason jin sunanshi batare daya tashiba cikin harshen turanci yace

" Sunana DON Ibrahim "

Jin sunanshi yasa wasu daga ciki sake maimaitawa kowa bud'e system d'in shi yayi yana nuna irin aykinshi ana zuwa kan DON yajuya musu system d'in shi mamaki kowa yashigayi domin irin aykin dasuka d'ad'e suna neman meyi musune tun bayan rasuwar Alhaji Isma'il d'ayadagacikin manyan ba'kin yace

" DON kanada ala'ka da margayi Alhaji Isma'il ne ? "

Kallon shi DON yayi sannan yace

" a'a asalima tarihinshi natadda cikin manyan 'yan kwangila sannan naji inason gudanar da harkar kamar yadda yagudanar "

Tuni wajan yad'auki tafi d'aukacin gurin masoyan margayi Alhaji Isma'il ne wasukuma ma'kiyan shi su Alhaji Sambo sunyi tafine kawai sabida karsujawo idanun jama'ar gurin kansu

Cikin jindad'i ba'kin sukace

" yalla'bai DON kaine zamuba wannan kwangilar idan angama akwai wasu za'a samu kaso nakimanin million 100 semu 'karashe sauran maganar daga baya "

Daga nan taro yatashi tabbas yau DON yaji wani irin farinciki bawai dan dukiyar dazai samuba sedan yadda yaga su Alhaji Sambo sun rud'e

Kuyi ha'kuri da wannan wayana babu caji sosai yau

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

Comments and shine plsss
[17/06 12:55 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯°

πŸ…Ώ { 27 to 28 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Misalin 4 Kausar tashiga kitchen cikin natsuwa takeyin komi nau'ikan abinci kala 3 tayi shinkafa wadda taji kayan lambu da hanta se tuwon shinkafa da miyar agushi wanda taji naman rago se alkubus da miyar kwai se farfesun dankalin turawa da kaza

Nau'ika jus ma 3 lemon kwakwa dabino da madara se had'add'an sobo wanda yaji kayan kamshi se kunun aya wanda yasamu had'i na musamman

Misalin 7 takammala komi ta jera saman dining da taimakon tabawa tagyara gidan dandanan ya garwaye da kamshi cikin bedroom d'in ta tashiga kai tsaye toilet tashiga tayo wanka yaban tafito d'an 'kara karfin AC tayi sabida jikinta yasamu iska isassa

Gaban mirror tatsaya 'kayatattun mayukanta tashafa had'ida turarukan jiki sannan tayi makeup bud'e wardrobe tayi cikin mamaki ta tsaya tana kallon wata bag a saman kayanta wata farar paper tagani saman bed d'in cikin sanyin jiki tad'auka d'an gajeran burutune kamar haka

" kisa kayan cikin bag d'innan lokacin tarbar ba'kin daga DON "

Ajiyar zuciya Kausar tayi had'ida murmushi afili tace

" nagode ma Allah dakake nunamin matsayi agaban idanun jama'a Allah yasa inga ranar dazaka kuladani alokacin dayazama dagani se kai oh Allah ko yaushe yakawo kayannan bansaniba ? Yaya Affan kenan "

Wata had'ad'iyar Arabiagwan ce mai matu'kar kyau da tsada da wata irin sarka da takalmi se wani tsadadjen turare cikin farin ciki Kausar tagama shirin ta kallon kanta tayi a mirror itada kanta sedatace masha Allah fitowa parlour tayi sezuba kamshi takeyi jin 'karar tada motar shi yasata saurin le'kawa ta window cikin mamaki tace

" Yaushe yashigo "

Bedroom d'in shi tanufa jinjina kai tayi tace

" wanka kawai yayi inaga ba'kin yaje d'akkowa "

Komawa parlour tayi misalin 8pm taji tsayiwar motar shi babu jimawa taji knocking cikin takunta na natsuwa ta'isa bakin door d'in tabud'e dashi tafara had'a ido cikin sakin fuska tace

" barka da dawowa Sweety na manyan ba'ki sannunku dazuwa "

Murmushi DON yasakar mata hannunta yakamo yasumbace shi yace

" ina fatan kina lafiya hayateey ? "

Wani irin mamakine yakama Kausar amma cikin dakewa danuna ba'abubane sabo tayi murmushi tace

" bayan kafita nakasance cikin rashin lafiya mai tsanani amma kana dawowa nafi d'azu kafin kafita lafiya "


Murmushi yasake sakar mata had'ida d'an jawota jikin shi yace

" to kwantar da hankalinki hayateey bazan sake fitaba senan da 2 days kin........ "

'Daya dagacikin ba'kin yayi murmushi cikin nuna shi'awar yanayin dasuke yace

" mude yakamata aji damu indan mukatafi seku cinye kanku wannan irin soyayya haka "

Kallon shi DON yayi yad'an saki murmushi yace

" ayya kuyi ha'kuri kunsan idan kanatare da farincikin ka mantawa kakeyi dakomi mukarasa ciki "

'Dan duka d'ayan yakaimai yace

" wai kaine kuwa DON ? "

DON yace

" gani kuwa hayateey na kad'e take iyaganin wannan murmushi kuma darajarta kuka samu "

Dariya suka saki dukansu nuna fad'in lalle madam kinada sa'a zama sukayi suka fara tattaunawa cikin mamaki d'aya daga ciki yace

" DON gaskiya nayi mamakin yadda kasamu wannan kwangilar cikin sauri haka bayan baka ta'bayin harkar ba sannan kanuna irin aykin dakakeyi bayan babu kod'aya wanda kayi aciki "

Kallon shi DON yayi sannan yace

" idan banta'bayiba ay inaganin masuyi ko ? "

" to ayni yadda kafitar da tsaretsaran ne yabani mamaki tayaya "

'Dan tamke fuska DON yayi yace

" wannan kuma sirrinane bana bu'katar kowa yasani "

Murmushi yayi yace

" haba DON wato haddani za'a nunama aykin SSD d'in bayan nima aykinane "

Banza DON yayi mishi yakalli Kausar dake manne jikin 'kafad'ar shi yace

" hayateey tashi muje mubasu dinner "

Cikin mamaki wani yace

" had'a abincinma seka tayata ? "

'Dan juyowa DON yayi yace

" idan kafad'i haka banga lefinkaba sabida bakayiba kaga bakasan mahimmancinsuba "

Dariya suka saki sannan suka nufi babban dining d'in cikin natsuwa Kausar tabubbud'e musu kalolin abincin cikin muryarta mai sanyi tace

" ga abinci nasankowa da ra'ayinshi "

Kallon juna sukayi d'aya yace

" nikam duka ina bu'kata wannan irin kamshi haka daganin wannan dinner zatayi santi dan yau inaga sena manta hotel d'in dana sauka "

Duka DON yakaimai yace

" kai de bazaka canza haliba hayateey bar kowa yayi Saving d'in kanshi ga plates nan kowa yayi dakanshi "

Murmushi Kausar tayi tace

" hakan yayi Sweety bari nabaka nasan kana bu'katar hakan "

Wani iri DON yaji amma ayau kam babu yadda zaiyi murmushi yasakar mata farfesun dankalin da kaza tazubamai had'ida tsiyayame lafiyayyan kunun ayar dakanta tashiga bashi ahankali yake amsar abincin ganin ita bataci yasa shima yashiga bata shiru gurin yayi bakajin sautin komi sena spoons da plates tsayin lokaci sannan Abubakar yace

" gaskiya DON kayi sa'a banga lefinkaba idan kanunama madam soyayya agaban kowa wannan irin abinci haka kay masha Allah idan natashi aure sena kawo matar kinkoya mata irin wa'innan had'addun girkin "

" hmmm Abubakar kenan ayni tun yanzu zan dinga kawai budurwata takoya lalle Aminu kai nakama da saura kenan ayni 'kafata 'kafar DON kullum ana zand'inga cin abinci "

Tamke fuska DON yayi yace

" to duk baku isaba hayateey na ba baywarku bace kuje kawai Allah yabaku sa'ar kuma "

Tashi DON yayi yakoma tsakiyar parlour suma tasowa sukayi suna cigaba da yaba girkin Kausar har cikin zuciyar DON yaji dad'in haka shi kanshi jiyayi kamar karya dena cin wannan daddad'an abincin

Ganin har 10 tawuce yasa suka mi'ke cikin sakin fuska Abubakar yace

" madam ga wannan tunda DON baiyi niyyar gayyatarmu bikin ba amma gashi munzo mun gwashi had'add'an girki "

Suma sauran kyaututtuka sukabama Kausar sosai sukayimata alheri har wajan motocinsu sukarakasu DON nari'ke da hannun Kausar seda motocin su sukagama fita sannan kallon Kausar DON yayi yasaki hannun ta yajuya ciki

Bin bayan shi tayi tana mai saukin abubuwan dasuka faru yanzu tana shiga zaune tasameshi gun dining tanufa dan gyara gurin cikin wata irin murya yace

" hayateey "

Cikin matu'kar mamaki Kausar tajuyo d'an kauda kanshi DON yayi dan shi kanshi baiyi tunanin wannan kalmarce zata fito daga bakin shiba fuskewa yayi yace

" zo nan "

Cikin sanyin jiki Kausar ta'karaso zama tayi kusa dashi cikin shakka sabida yadda taga fuskar shi babu alamar wasa d'an Jim yayi sannan yace

" kin kyauta kin fitar dani kunya yadda banyi tsammaniba tabbas yau kinsa nayi farinciki zanje Kaduna gobe Dady yana nemana idan akwai abinda kike bu'kata kisanar dani "

Cikin in ina tace

" dan Allah yaya katafi dani munyi hutu yau dama inason sanar da kai "

Kallon ta yayi yahad'a rai sannan yace

" zanyi tunani zuwa safe jeki had'amin Lipton kimatsamin lemon tsami guda 3 "

Tashi tayi tanufi kitchen zuciyar ta cike damamaki

" wai yau yaya Affan ne da kanshi yace nakawo mai wani abu abunma nasha oh Allah amma kuma lemon tsami har 3 "

Tana barin gurin ya yadafe mararshi had'ida rintse ido ahankali yatashi yanufi bedroom d'in shi kwanciya yayi d'ago hannun shi yayi tuno irin laushin hannun Kausar yasashi sake runtse idanunshi juya kwanciyar shi yayi yayi rufdaciki ya 'kwa'kube pillow

Yad'an jima da shiga cikin bedroom sannan Kausar tashiga hannun ta d'auke da cup d'in Lipton d'in umarnin ajiyewa yabata batare daya tashiba yayi hakanne dan bayason sake kallon surar jikinta dan yin hakan zaisake sashi cikin matsala

A wannan daran haka DON yakwana da tunanin surar jikin Kausar daya rimtse ido ita yake kallo kamshin jikinta yakeji " Sweety " yasake maimaita kalmar tunda wuri Kausar tashiga kitchen had'a musu breakfast yana dawowa masallaci yace

" kiyi sauri ki shirya idan kuma kika zauna zanyi tafiyata "

Daga haka yashige bedroom d'in shi toilet yashiga cikin sauri Kausar tahad'a breakfast d'in kan dining sannan tanufi bedroom d'in ta cikin lokaci kad'an tagama shiri harma tarigashi fitowa zaune tayi kan cushion tana jiran fitowar shi

Zuwa can yafito kallon ta yayi yai saurin kauda kanshi sabida wani irin abu dayaji ya tsarga dukkan ilahirin jikinshi tasowa tayi tace

" yaya please kayi breakfast kafin mutafi "

Shiru yayi kamar bazaiyi magana ba sannan yace

" kawomin nan "

Zama yayi kan cushion ahankali yakeyi break d'in har yagama itako tea kawai tasha bayan sungama suka kulle ko ina sannan yakira tabawa yasanar da ita motocin 3 d'aya daga driver se wasu ubankaya d'aya kuma driver da su d'aya Security

Suna isa Kaduna Kausar taji wani irin farinciki cikin sauri maigadi yawangale musu get sunayin parking Kausar tafito tanufi cikin gidan aguje kallo DON yabita dashi yayi 'kwafa

Adede lokacin Momy da Dady suna zaune a parlour shikuma Ashiraf yana cikin bedroom jin ihun Kausar yasa Ashiraf fitowa cikin murna Kausar tafad'a jikin Momy murmushin farinciki barrister yashigayi shima Ashiraf haka ganin wasu had'add'un akwaituna da'ake shigowa dasu yasa kowa baida dubanshi da hankalin shi Kansu

Seda aka gama shigowa dasu sannan DON yashigo akwaiti har set 4 ko wanne 6 6 yana shigowa ya shiga gaidasu cikin girmamawa bayan sun gaisa DON ya kalli Barrister yace

" Dady wannan kayan lefan Kausar ne Momy kuyi magana da ita tafad'i irin kayan datake bu'kata na gida an kammala ginin wannan gidan na Abuja inaso nayi Oder kayan daga Italy "

Yana gama fad'ar haka yami'ke ciki yanufa sabida duk bayajin jikin shi dede tsananin farin ciki yasa barrister kasayin magana sede murmushi itama Momy haka shiko Ashiraf bin bayanshi yayi yana fad'in ango

Tunda DON yashiga ciki bai fitowa seda akafara kiran sallar azahar yana fitowa barrister

" DON yakamata kaje kaga Amaryar ka tsawon 1 week fa da kawota ? "

Cikin razana Kausar takalli DON shima d'in ita yakalla cikin in'ina tace

" dady Amarya kuma yaya Affan ? "

Jinjina mata kai Dady yayi dandanan hawaye suka taru cikin idanunta Kausar tashi tayi aguje tanufi bedroom d'in Momy sake binta da kallo DON yayi murmushi barrister yayi yace

" karka damu my son kaje zamu lallasheta "

Idasafita yayi yana tunanin abubuwa dayawa cikin zafin rai yake drive shi kad'e yana isa maigadi yabud'e mai get ko gama gyara parking baiyiba yakashe motar yafito sabida jikin shi babu karfi cikin muryar shi ta miskilanci yayi sallama saurin juyowa Seeyama tayi

Ganin shine yasa tajuya cigaba da kallon ta tayi ko sallamar bata amsaba ita adole tayi fushi

Shima ko kallon ta baiyiba yanufi bedroom d'in shi

Tofa

Daga Al'kalamin ✍🏻

NPEEDY A AJI β™ β™₯♣

comments and shine plsss
[18/06 2:28 pm] 😊 NPEEDY A AJIπŸŒΉπŸ’–: β™  RUFAFFIYAR ZUCIYA β™₯β™ β™ β™ β™ β™ β™ 
πŸ”·πŸ”΄πŸ”΅πŸ”Ά
♠♣β™₯
πŸ”΄πŸ”΅
β™ 
Story & Written
By
NPEEDY A AJI

Dedicated to
My Hajjaju

🌟GORGEOUS WRITTEN FORUM🌟

G.W.F

home of gorgeous intelligent and expert writers we the best among the rest

KAFA'DI ALKHAIRI KO KAYI SHIRU 🀫

ANA TARE All SISTERS 🀝🏻😍🌹

Ha'ki'ka inajin comments d'inku Fans inajin dad'in haka Allah yabar 'kauna 😊 muna tare 🀝🏻πŸ₯°

πŸ…Ώ { 29 to 30 }

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

Cikin mugun ba'kinciki DON yashiga bedroom d'in zama yayi bakin bed yadafe kanshi rintse idanun shi yayi fukar Kausar yake hangowa cike taf dahawaye afili yace

" mai hakan kenufi ? taya zatayi kuka dan an ambaci Amarya to ayni babu wacca nikeso a cikinsu amma meyasa naji babu dad'i lokacin danaga idanunta suncika da hawaye taya nike kallon surar j........ " turo 'kofar Seeyama yasa tunanin da DON keyi tsayawa

Ko sallama babu tace

" kazo Umma nakira "

Daga haka tajuya wani mugun tsaki yaja hayewa saman bed ma yayi yai kwanciyar shi babu alamar ma zaitashi jin shirun yayi yawa yasa Hajiya Saratu tanufi bedroom d'in dakanta

Knocking tashigayi amma shiru jin shirun yasata turawa tashiga cikin mamaki take kallon shi baccin shi kawai yakeyi 'kwafa tayi tafita a parlour tasamu Seeyama tace

" ke Seeyama dagaske kike lokacin da kikaje kiranshi idanun shi biyu ? "

Jinjina mata kai tayi alamar tabbas idanun shi biyu girgiza kai Hajiya Saratu tayi sannan tace

" wato ni ban'isa dashiba kenan ko zetashi yasameni "

Jinjina kai yaron Hajiya Saratu yayi yace

" wato Umma badan kudin danike hangowa ba da wallahi se kaddamar mai "

" gaskiyar ka jabir nima badan hakaba hmmm "

Cewar Ayman d'an zaro ido Seeyama tayi tace

" a 'a ina son shi fa mude samu dukiyar amma banda kisa "

Harararta Hajiya Saratu tayi tace

" kaji banza dakud'i da shi wanne kikafi so idan yamutu ga jabir nan dama yadad'e yana sonki dande wannan kaddararan had'in ne da kakanninku sukayi kukuma kubi ahankali kuna ganin wa'innan mugayen security d'in dayake tare dasu zasu ragamuku idan kukamai koda kallon banza ne to kubi ahankali "

Haka sukacigaba da kulla makircinsu afurgice DON yatashi hannun shi yasa yashare zufar data mamaye fuskarshi ajiyar zuciya yasauke cikin wahalalliyar murya yace

" haba taya wannan mafarkin zaidawomin ? bayan nayi kwanaki banyiba nikam ina zanganki baiwar Allah ? "

Hannu yasa yadafe mararshi yace

" yazanyi dawannan muguwar shi'awar dake damuna musamman cikin kwanakin nan gaskiya babu macan dazan iya tarayya da'ita sede namutu "

Jiki a sanyaye yatashi toilet yashiga wanka yayi yacanza kaya sannan yafito se zuba kamshi yakeyi a babban parlour yasamesu dukansu

Please Login or Register in order to submit comment